Radio راديو
Telly تلفاز
Your Prayer Time توقيتك للصلاة
Menu قائمة
Live! حيًّا
 
Gaban Shafin Samiya Goma Sabon Kanun Labarai Takardun Labari Cagiya Hausa Wani Ajali Ambatacce Hausa Ciki
Rattaba Hannu A

  Create an account

Babban Shafin

Gungumen Da

Sakonninka \'Yan Hausa Yakan Yi Bitar Mujallan Kissoshi Dakin Littattafai Yanar Gizon Na Da Alaka Da Sami Ceto Kayayyakin

 

 
 
                  
 

Mahadin Kafada Kissoshin

 
 

Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi
[ Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi ]

·MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 17
·MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 16
·MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 15
·MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 14
·MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 13
·MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 12
·MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 11
·MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 10
·MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 9
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
                  
 

Cagiya

 
 


 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
                  
 

Random Fatwas Updates

 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
                  
 

Babobi Kafa Hanya

 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
                  
 

Luggogi

 
 
Tsina Sarke Harshe:

 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
                  
 

Wa Ya Ke A Dandali

 
 
Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
                  
 

Da Makalolin

 
 
Tuesday, May 09
· MARABA DA WATAN RAMADAN [4]
· MARABA DA WATAN RAMADAN [3]
· MARABA DA WATAN RAMADAN [2]
· MARABA DA WATAN RAMADAN [1]
· AL KITAB WAL ''ITRA'' KO AL KITAB ''WAS SUNNAH
· AL KITABU WAL ''ITRA'' KO ALKITABU ''WAS SUNNAH
· AL KITABU WAL ''ITRA'' KO AL KITABU WAS ''SUNNAH&#
· AL KITABU WAL ''ITRA'' KO AL KITABU WAS ''SUNNAH&#
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 17
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 16
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 15
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 14
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 13
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 12
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 11
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 10
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 9
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 8
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 7
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 6
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 5
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 4
· MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 3
· ME YA FARU A KARBALA? 2 Wane ne YAZIDU?
· MEYA FARU A KARBALA?
· MUNAFUKAI BA SAHABBAI BANE GABATARWA
· GUZURI GA MANIYYATA AIKIN HAJJI
· SALLAH MAFIFICIYAR IBADAH !!! FITOWA TA 8
· SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!! FITOWA TA 7
· SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!! FITOWA TA 6

Babban Makaloli
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
                  
 

Your Local Time

 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Ga Da Tsakar Kissoshi Girma A Yau, Lalle Diwani Saka Ko Ya Zama Wakiliya.

 

Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

KEBANTACCIYAR SALLAH A DAREN NISFU SHA'ABAAN
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 7343 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

Dr. Mansur Sokoto

KEBANTACCIYAR SALLAH A DAREN NISFU SHA'ABAAN.

Malaman hadisi sun ce:

Babu wani hadisin da ya tabbata daga Manzon Allah (saw) game da wannan sallar da ake kira Salatul Alfiyya. Sai hadisai qagaggu da raunana. Kadan daga cikin irin wadannan hadisai akwai hadisin da aka jinginawa Sayyadina Aliyyu wai ya ce: Manzon Allah (saw)
ya ce; ﺇﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﻨﺼﻒ ﻣﻦ ﺷﻌﺒﺎﻥ ، ﻓﻘﻮﻣﻮﺍ ﻟﻴﻠﻬﺎ ﻭﺻﻮﻣﻮﺍ ﻧﻬﺎﺭﻫﺎ ، ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻨﺰﻝ ﻓﻴﻬﺎ ﻟﻐﺮﻭﺏ ﺍﻟﺸﻤﺲ ﺇﻟﻰ ﺳﻤﺎﺀ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ، ﻓﻴﻘﻮﻝ ﺃﻻ ﻣﺴﺘﻐﻔﺮ ﻓﺄﻏﻔﺮ ﻟﻪ ، ﺃﻻ ﻣﺴﺘﺮﺯﻕ ﻓﺄﺭﺯﻗﻪ ، ﺃﻻ ﻣﺒﺘﻠﻰ ﻓﺄﻋﺎﻓﻴﻪ ، ﺃﻻ ﺳﺎﺋﻞ ﻓﺄﻋﻄﻴﻪ ، ﺃﻻ ﻛﺬﺍ ﺃﻻ ﻛﺬﺍ ﺣﺘﻰ ﻳﻄﻠﻊ ﺍﻟﻔﺠﺮ Ma'ana:


''Idan daren Nisfu Sha'aban ya zo ku raya darensa da Qiyamullaili, kuma ku azumci yininsa, domin Allah Madaukakin Sarki yana saukowa zuwa saman duniya daga zarar rana ta fadi, yana cewa: shin akwai mai neman gafara ana gafarta masa, ina mai neman arziki na arzuta shi, ina wanda Allah ya jarrabe shi na yaye masa, ina mai kaza da kaza har zuwa ketaowar alfijir." Amma sallar da ake kira Salatul Alfiyya, salla ce da ba ta da asali a cikin addinin musulunci, kuma an rawaito hadisai masu yawa game da bayanin siffarta da falalarta, sai dai dukkaninsu babu wanda ya tabbata daga Manzon Allah (saw).

Daga cikin wadannan hadisan akwai hadisin da aka jinginawa Sayyadina Aliyyuyu Ibn Abi Dalib wai ya ce:

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 7343 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

TAMBAYOYI DA AMSA RANCEN AIRTIME (MTN, GLO DSS) DAGA SERVICE PROVIDERS HALAS NE
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 4054 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

SHEIKH DR. MANSUR IBRAHIM SOKOTO

RANCEN AIRTIME (MTN, GLO DSS) DAGA SERVICE PROVIDERS HALAS NE KO HARAM?

 Sheikh Dr. Mansur Ibrahim Sokoto

 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Na karanta rubutun da dan uwa Shehun Malami Dr. Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi akan wannan lamari kuma har na yi sharing tare da dan ta'aliki a kai. Na so na wadatu da wannan, amma sai na ga a wasu shafukan yan uwa ana ta tafka muhawara da sa bakin masu masaniya a Fikihu da wadanda ma ba su da ita sam.

 Akwai masu ra'ayin cewa, an dulmuyar da Dr. Sani ne har ya canja fatawa. Ina son in fada ma wadannan cewa, sun jahilci wane ne Dr. Sani a kaifin basirarsa da bincikensa na ilimi. Ba na maganar wani dan bokon da bai san kimar ilimin annabawa ba don ya ce masa "Dan Arabiyya zalla" ko "Mai ido daya" . Domin ko ya sani ko bai sani ba da annabin Allah yake. Shi ne mai Arabiyya zalla. Kuma idonsa mai tsarki da tarin albarka bai taba kallon wani bokon da shi wannan jahilin yake takama da shi ba. Littafin Allah da ya zo da shi Arabiyya ce zalla, haka ma hadisansa Arabiyya ne zalla. Ashe wanda ya sha su ya koshi shi ke zama dan Arabiyya zalla. Mai sukar sa ta wannan fuska kuma ya san ko waye yake suka. Allah ya shirye mu.

 A nan dai ina son ne in dan kara haske a kan matsalar don masu neman bayani tsakani da Allah ko za su gane:

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 4054 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)
 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

KANA SADA ZUMUNTA?
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 1879 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

KANA SADA ZUMUNTA ?

1-Allah taala yayi Umarni da sada zumunta.

Suratul bakara 36, Suratul Isra'i 26, Suratul Rum 38, Suratul bakara 210, Suratul Nisa'i 2 .

2- Sada zumunta yana kara tsawon rai, Bukari 5986, Muslum 2557.

3- sada zumunta yana kara arziki, Bukari 5986 


4- sada zumunta yana cikin abubuwan da akayi Umarni dashi, tun farkon musulunci, bayan tauhidi, Bukari 7 

5- sada zumunta dalili ne na shiga Aljannah, Bukari 5983 

6- sada zumunta yana cikin abubuwan da Allah yake so. Sahihut-targib 2/667.

7- sada zumunta yana tseratarwa daga azaba, Abu Dauda 4902 

8- sada zumunta wasiyyar da Annabi saw yayi wa Al'ummarsa. Sahihut-targib 2/669 

9- Sada zumunta siffar muminai ce.

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 1879 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)
 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

SHAWARWARI 60 GA MATAN AURE
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2861 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

SHAWARWARI 60 GA MATAN AURE

Shawarwari 60 ga matan aure domin samun zamantakewa mai inganci, da aure mai albarka, kamar yadda muka Bawa maza suma shawara 60.

1.Ta rike masa amana, 2. Tayi masa biyayya akan duk abinda ba sabon Allah bane.

3. Ta kula da dukiyarsa 4. Ta kula da Sallah akan lokaci. Da addua zaman lafiya 5. TA girmama shi a gaban idansa 6. TA kare girmansa a bayan idansa 7. Ta so abinda yake so, koda ba abin so bane a wajenta 8. Ta ki abinda yake ki, koda ba abin ki bane awajenta 9. Ta damu da duk abin da ya damu dashi.

10. Ta kau da kai daga abinda ya kauda kai, daga gareshi 11.Tayi fushi , da dukkan abinda yayi fushi da shi .

12.Ta yarda da duk abinda ya yarda da shi 13.Idan ya bata kadan taga yawansa 14.Idan ya bata da yawa tayi godiya 15.Ta farka daga bacci kafin ya farka 16.Sai yayi bacci kafin tayi 17.Tayi hakuri idan yayi fushi 18 Tayi taushi idan yayi tsauri 19.Ta lallashe shi idan ya hasala 20.kada ta nuna raki a gabansa 21.kada tayi kuka alhali yana dariya 22.kada tayi dariya alhali yana kuka 23.kada ta tsaya kai da fata sai yayi mata wani abu 24.kada ta matsa masa da bukatu 25.kada ta dinka ganinsa kamar yaran gida 26.kada ta dinka yi masa gyara barkatai 27.kada ta dinka kushe tsarinsa 28.Ki dinka zuga shi a gaban danginta 29.

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2861 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

ABUBUWAN DA ANNABI (SAW) YA NEMI TSARI DA SU
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2730 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 2)

DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

ABUBUWAN DA ANNABI (SAW) YA NEMI TSARI DA SU

WADANNAN ABUBUWA DA SUKAZO A HADISAI ANNABI SAW YA NEMI TSARI DA SU.

1, ZUCIYAR DA BATA TSORAN ALLAH.

2, FITINAR ZUCIYA 3, SHARRIN, JI ,DA GANI 4, TSORO 5, ROWA 6, BAKIN CIKI 7, DAMUWA 8, BACIN RAI 9, HASARA 10, SABON ALLAH 11, KASALA 12, GAJIYAWA 13, KASKANCI 14, KARANCI 15, TALAUCI, 16, FITINAR KABARI, 17, ZUCIYAR DA BATA KOSHI 18, YUNWA 19, CIN AMANA 20, TABEWA 21, MUNAFINCI 22, BASHI 23, FITINAR WADATA 24, FITINAR DUNIYA 25, SHARRIN MAZAKUTA 26, KAFURCI 27, BATA 28, RINJAYAN MAKIYA 29, DARIYAR MAKIYA 30, MUMMMUNAN TSUFA 31, MUMMUNAR HUKUNCI 32, TABEWA A RAYUWA 33, CIWON HAUKA 34, KAMBUN BAKA 35, KASKANCIN RAYUWA 36, KOMAWA BAYA A RAYUWA 37, ADDU'AR WANDA AKA ZALUNTA 38, MUMMMUNAR MAKOMA 39, MUMMUNAN MAKOCI 40, RINJAYAN MAZAJE 41, FITINAR DUJAL 42, AZABAR JAHANNAMA 43, SHARRIN SHEDANUN MUTANE 44, FITINAR RAYUWA 45, FITINAR MUTUWA 46, AZABAR KABARI, 47, SHARRIN ABINDA AKA SANA ANTA.

48, SHARRIN ABINDA AKA AIKATA 49 , SHARRIN ABINDA MUTUM BAIYI BA 50, SHARRIN GIRGIZAR KASA 51, GANGAROWA DAGA TUDU 52, RUSOWAR GINI AKA 53, NEMAN TSARI DA YARDAR ALLAH DAGA FUSHIN SA.

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2730 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 2)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

IMANI DA RASSAN SA GUDA 67, NAWA KAKE DA SU A CIKI.?
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 3520 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

IMANI DA RASSAN SA GUDA 67, NAWA KAKE DA SU A CIKI.?

Manzon Allah saw yace: Imani yana da rassa guda Sitttin bakwai , ko sabain da bakwai, mafi daraja, shine ,Lailaha illalahu, mafi karanta dauke abu mai cutarwa daga hanya, kunya tana daga cikin imani. Muslum ya ruwaito Malamai sunyi bincike domin gano wadannan rassa, sun wallafa littafai da dama akan haka, abinda suka kawo, daga Alkur'ani mai girma, da ingatattun hadisai, kuma sun gaya mana cewa wadannan rassa sun fito daga aiyukan zuciya, da aiyukan harshe, da aiyukan gabbai, kuma imani yana karuwa yana raguwa.

1- Imani da Allah, shi yayi halitta, shi ya mallaka. shi yake gudanarwa.shi ya cancanci bauta. Da sunayansa da siffofinsa.

2- Imani da Mala'ikun Allah, da siffofin su da aiyukan su, da sunayansu.

3- Imani Da Manzannin Allah swt.

4- Imani da littafan Allah swt, 5- Imani da ranar Lahira.

6- Imani da kaddara mai dadi da mara dadi.

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 3520 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

MANYAN LAIFUFFUKA 70 NAWA KAKE AIKATAWA DAGA CIKI?
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2612 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

MANYAN LAIFUFFUKA 70 NAWA KAKE AIKATAWA DAGA CIKI ?

Manyan malamai sunyi kokarin tattara, manyan laifukkuka, a guri guda domin sanin su, da fahimtar munin su, da yadda zaa guje musu.

Allah ya bamu ikon kiyayewa.

1- Shirka da kashe-kashenta 2- kisan kai 3 – Tsafi 4- Wasa da sallah 5- Hana zakka 6- Sabawa iyaye 7- Cin riba 8- Cin dukiyar marayu 9- yiwa Annabi saw karya 10- Karya Azumi da gangan 11- Gudu daga filin daga ana yakin kare addini.

12- Yin Zina 13- Shugaba mai hainci ga talakawansa.

14- Shan giya da sarrafata 15- Girman kai da takama da jiji da kai 16- Shedar Zur 17- Luwadi da mdigo 18- Yin kage ga muminai 19- Satar dukiya daga baitul mali 20- Zaluncin cin dukiyar jamaa, ta algus da manuba.

21- Sata, da sane.

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2612 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

FARKON SHIGA ALJANNAH (SAWW)
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2841 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

FARKON SHIGA ALJANNAH (SAWW)

Farkon wanda zai shiga Aljannah aranar Alqiyamah shine Annabinmu Muhammadu (saww)
kamar yadda Imamu Muslim ya ruwaito daga Sayyiduna Anas bn Malik (rta) yace Manzon Allah (saww) yace:

"ZAN ZO KOFAR ALJANNAH ARANAR ALQIYAMAH, SAI IN KWANKWASA, SAI MAI TSARONTA (WATO MALA'IKA RIDHWAN)
YACE : "KAI WANENE?".

ZAN CE MASA "MUHAMMADU NE". SAI YACE : "SABODA KAI AKA UMURCENI KAR IN BUDE MA WANI KAFIN KA".

Acikin wata ruwayar kuma yace: "NINE NAFI DUKKAN ANNABAWA YAWAN MABIYA, KUMA NINE FARKON WANDA ZAI KWANKWASA (KOFAR ALJANNAH)." (Muslim ne ya ruwaitoshi).

Acikin ruwayar Abu Hurairah kuma Annabi (saww) yace: "MUNE NA KARSHE KUMA MUNE NA FARKO ARANAR ALKIYAMAH. KUMA MUNE FARKON WADANDA ZASU SHIGA ALJANNAH".

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2841 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA, TSARABAN RAMADAN
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 9126 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA, TSARABAN RAMADAN

(1) Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawa 6/505:-

(( ﻭﺍﻟﺨﻴﺮ ﻛﻞ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻓﻲ ﺍﺗﺒﺎﻉ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ ﻭﺍﻻﺳﺘﻜﺜﺎﺭ ﻣﻦ ﻣﻌﺮﻓﺔ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺍﻟﻔﻘﻪ ﻓﻴﻪ ﻭﺍﻻﻋﺘﺼﺎﻡ ﺑﺤﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﻼﺯﻣﺔ ﻣﺎ ﻳﺪﻋﻮ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ﻭﺍﻷﻟﻔﺔ ﻭﻣﺠﺎﻧﺒﺔ ﻣﺎ ﻳﺪﻋﻮ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻼﻑ ﻭﺍﻟﻔﺮﻗﺔ ﺍﻻ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﺃﻣﺮﺍ ﺑﻴﻨﺎ ﻗﺪ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻓﻴﻪ ﺑﺄﻣﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺠﺎﻧﺒﺔ، ﻓﻌﻠﻰ ﺍﻟﺮﺃﺱ ﻭﺍﻟﻌﻴﻦ )).

Ma'ana: ((Sannan alheri kuma dukkan alheri yana cikin bin magabata na gari, da kuma yawaita ilmin hadithin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah, da kyakkyawar fahimta cikinsa, da yin riko da igiyar Allah, da lazimtar abin da ke kira zuwa ga jama'a da hadin kai, da nisantar abin da ke kira zuwa ga sabani da rarraba, sai fa abin da ya kasance al'amari ne bayyananne da tabbas Allah da manzonSa ne suka yi umurni cikinsa da wani umurni na a nisanta, to wannan kam biyayya sau da kafa)).

(2) Alhaafiz Ibnu Rajab ya ce cikin littafinsa Alhikamul Jadiiratu Bil Izaa'ah shafi na 12:-

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 9126 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH FATAWOYIN LAYYA2
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 10870 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH FATAWOYIN LAYYA2

SHEIKH ABDULWAHHAB ABDULLAH

A wannan darasi za mu amsa tambayoyi kamar haka; *Tambaya:

Mene ne sharuddan layya?

AMSA:

Yana daga cikin sharuddan layya:

abin da za a yanka, lallai ya kasance daga cikin ''bahimatul anʿām'' (dabbobin ni'ima), irin su:

rakuma da shanu da awaki da tumaki). Domin haka, ba ya cikin sharuddan layya, a yi ta da namun daji, kuma ba za a yanka kaji da sauran tsuntsaye ba, kamar yadda wasu daga cikin 'yan Zahiriyyah suka tafi a kai.

Dalili kuwa fadin Ubangiji subhanahu wa ta'ala cewa:

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 10870 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH FALALAR SAHABBAI
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 1925 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

SHEIKH ABDULWAHHAB ABDULLAH

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH FALALAR SAHABBAI

Alhamdu lillahi rabbil A'lamin, wa Sallallahu wa sallama ala Nabiyyina Muhammadin Wa ala a'alihi wa sahbihi ajma'in.

Amma ba'ad, hakika hadisi ya tabbata daga Anas Bin Malik radhiyallahu anhu ya ce; ﻛﺎﻧﺖ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺨﻨﺪﻕ ﺗﻘﻮﻝ ﻧﺤﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺑﺎﻳﻌﻮﺍ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻣﺎ ﺣﻴﻴﻨﺎ ﺃﺑﺪﺍ ﻓﺄﺟﺎﺑﻬﻢ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﻋﻴﺶ ﺇﻻ ﻋﻴﺶ ﺍﻵﺧﺮﻩ ﻓﺄﻛﺮﻡ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻭﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻩ Ma'ana Ansar sun kasance a yayin da suke haka ramin khandaku suna cewa;

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 1925 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH MECE CE ALAMAR SON MANZON ALLAH (S.
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 6024 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

SHEIKH ABDULWAHHAB ABDULLAH

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH MECE CE ALAMAR SON MANZON ALLAH (S.A.W)?

Amsa:

Kafin mu amsa wannan tambayar ya na da kyau muyi wa kanmu wadannan tambayoyin:

-Mece ce soyayya?

-Mene ne yake sa a so mutum?

-Mene ne rabe- raben so?

-Mece ce alamar so?

Daga nan kuma sai musan mece ce hakikanin soyayyar Manzon Allah (S.A.W)?

Mece ce soyayya?

Hafiz Ibin hajar babban malamin hadisin nan da yayi sharhin sahihul bukhari yace:

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 6024 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

MARABA DA WATAN RAMADAN
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 4971 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

LAILATUL QADR

MARABA DA WATAN RAMADAN

LAILATUL QADR: shine Qaddararren dare, dare mai daraja mai girma, daren alkhayri, dare mai albarka, dare ne wanda misali bazai gama rarrabe abunda wannan dare ya qunsa ba face ALLAH (SWT) shine masani.

•••FALALAR DAREN LAILATUL QADR••• .

Falalar wannan dare mai girma ce domin an shedar da sauqar al'qur'ani acikinsa, kuma ALLAH (SWT) Ya ambace sa acikin LittafinSa a wurare daban-daban, daga cikinsu akwai fadar ALLAH (SWT):

"lallai mu muka sauqar da shi (Alqur'ani) acikin daren Lailatul Qadr, me ya sanar da kai abunda ake qira Lailatul Qadr, Daren Lailatul qadr yafi daraja akan wata dubu, saboda mala'iku suna sauqa acikinsa tare da ruhu (jibril) da izinin Ubangijinsu ga kowane al'amari, Amincin ALLAH ne wannan daren (da abinda ke cikinsa) har 6ullowar alfijir" .

(Surah ta 97 aya ta 1 zuwa 5)
Haqiqa daukakar daraja ta isa ga wannan dare na Lailatul Qadr acikin wadannan ayoyi cewa yafi watanni dubu, Haka kuma sauqar mala'iku acikinsa har da Mala'ika Jibrilu (AS) wata falala ce ta wannan daren.

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 4971 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH YAUSHE NE YA FI DACEWA A YI SAHUR?
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 1880 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

SHEIKH ABDULWAHHAB ABDULLAH

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH YAUSHE NE YA FI DACEWA A YI SAHUR?

Alhamdu lillahi rabbil A'lamin, Wa sallallahu wa sallama ala Nabiyyina Muhammad wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Amma ba'ad; Lallai wanda yake son Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama zai fifita shi akan duk abin da yake da girma ko daraja ko tsada a gunsa.

Domin son Allah da manzonsa sune imani, kuma imanin bawa bazai cika ba sai da su. Allah subhanahu wa ta'ala yace:

'' kace idan har iyayenku da 'ya'yanku da 'yan uwanku da matanku da danginku da dukiyar da kuka tsuwurwurta da kasuwancin da kuke jin tsoron tasgaronsa da gidaje da kuke yarda dasu sune suka fi soyuwa a gareku daga Allah da Manzonsa da jihadi saboda Allah ;to ku zauna har Allah ya zo da al'amarinsa, allah baya shiryar da fasikai'' {Tauba :24} Wannan ayar nassi ce karara a bisa wajibcin kaunar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama,da wajibcin gabatar da wannan kaunar akan duk wani abin kauna.

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 1880 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH IDAN MUTUM YANA CIKIN YIN SAHUR, SA
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 1592 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH IDAN MUTUM YANA CIKIN YIN SAHUR, SAI YA JI KIRAN SALLAH YAYA ZAI YI?

SHEIKH ABDULWAHHAB ABDULLAH

AMSA:

A irin wannan hali mutum zai qarasa abin da ke hannunsa ne.

Domin hadisi ya tabbata daga Abu Huraira radhiyallahu anhu ya ce:

Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce:

Ma'ana:

Idan dayanku ya ji kiran sallah alhali qwarya tana hannunsa, kada ya ajiye ta, har sai ya biya buqatarsa .

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 1592 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

TAMBAYOYI DA AMSA MUTUMIN DA KE DA MATA 4 SANNAN YA YI WA DAYANSU YANKAKKEN SAKI
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 3292 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

DR. IBRAHIM JALO JALINGO

TAMBAYOYI DA AMSA MUTUMIN DA KE DA MATA 4 SANNAN YA YI WA DAYANSU YANKAKKEN SAKI KO ZAI HALATTA YA AURI WATA MATAR KAFIN IDDAR WANNAN TA CIKA?

1. Babu sabani tsakanin Malamai cewa: ba ya halatta ga namiji ya hada Ya da Kanwa karkashin aurensa a lokaci guda. Haka nan ba ya halatta gare shi ya daura wa mace ta biyar aure koda kuwa akwai wacce ya saka saki na kome matukar dai ba ta gama iddarta ba. Wannan mas'ala babu sabani a cikinta tsakanin Malaman Sunnah; saboda dalilai da yawa daga cikinsu akwai: Fadar Allah cikin surar Nisaa'i aya ta 23 ((Kuma kada ku hada tsakanin Ya da Kanwa saifa abin da ya riga ya wuce)). Da kuma wasu hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah, daga cikinsu akwai hadithi na 2243 da Imam Abu Dawud ya ruwaito, da hadithi na 1952 da Imam Ibnu Majah ya rueaito, da hadithi na 4631 da Imam Ahmad ya ruwaito, da hadithi na 4156 da Imam Ibnu Hibban ya ruwaito dukkansu da isnadi sahihi cewa Sahabi Wahb Al-Asadiy ya musulunta alhalin yana da mata 8 sai Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce da shi ya zabi 4 kawai daga cikinsu. Haka nan ya faru da sahabi Gailan Bin Salamah, haka nan ya faru da sahabi Qais Bin Al-Harith.

2. Amma su Malaman Sunnah sun yi sabani game da idan mai mata 4 ya saki guda a cikinsu saki yankakke watau: saki na 3 ko kuwa sakin Khul'i, ko yana da damar ya daura wa wata matar aure kafin iddar wannan da ya saken ta kare? Akwai mazhabobi biyu na Malamai cikin wannan mas'ala:-

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 3292 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [19]
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2573 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

I'ITIKAFI DA HUKUNCE- HUKUNCENSA ....[3]

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [19]

ABUBUWANDA BAYA HALATTA GA MAI I'ITIKAFI

1• JIMA'I: Yin jima'i da sumbatar mace da wasa da ita baya halatta ga mai i'itikafi da dare ko da rana, idan kuma har hakan ya faru to i'itikafin ya 6aci, saboda hani akan wannan yazo cikin alqur'ani mai girma, ALLAH (SWT) Yana cewa: "kada kuyi mubashara da mata alhali kuna masu i'itikafi acikin masallatai" .

(Surah ta 2 aya ta 187)

2• FITA DOMIN GANIN MARAR LAFIYA: Ba ya halatta ga mai i'itikafi ya fita zuwa ganin marar lafiya a gida ko a asibiti.

3• JANA'IZA: Ba ya halatta ga mai i'itikafi ya halarci sallar gawa sai dai idan sallar gawar ta kasance acikin masallacin da yake i'itikafi ne to zai iya yin sallar gawar tare da Liman. Kar ya fita sai fitar da bata da makawa, saboda Aisha (RA) tace:

"Abunda yake sunnah ga mai i'itikafi kar ya gaida marar lafiya, kar ya halarci jana'iza (sallar gawa) kar yayi jima'i da mace, kuma kar ya shafeta shafar jin dadi" .

(Abu-dawud ya fitar dashi)

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2573 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [18]
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2903 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

I'ITIKAFI DA HUKUNCE- HUKUNCENSA ....[2]

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [18]

SHARUDAN I'ITIKAFI

1• MASALLATAI: Yin i'itikafi baya inganta sai acikin masallatai.

Saboda ALLAH (SWT)
Yace: "Kada ku yi mubashara da mata alhali kuna masu i'itikafi acikin masallatai" .

(surah ta 2 aya ta 187)
Amma ba kowane masallaci ake i'itikafi acikinsa ba, domin yazo acikin Hadith cewa:

"Babu i'itikafi (cikakke)
sai a masallatai uku" wato Masallacin Makkah, Masallacin Qudus da Masallacin Madina" (Hadith ne ingantacce malamai sun inganta shi)
Amma wannan Hadith ba yana kore yin i'itikafi bane acikin wanin wadannan masallatai bane, sai dai yana kore cikar ladar i'itikafi a wani masallacin na daban.

2• MUSULUNCI: sharadi ne mai i'itikafi ya kasance musulmi domin ba'a kar6an i'itikafin Kafiri.

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2903 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [17]
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2282 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

I'ITIKAFI DA HUKUNCE- HUKUNCENSA ....[1]

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [17]

•I'ITIKAFI: malamai sunyi bayanin ma'anar i'itikafi cewa shine tsayuwa akan wani abu, ta wannan ma'anar ne ake cewa wanda ya zauna masallaci yana ibada acikinsa, wanda ya ke6e domin bautar ALLAH (SWT).

•••HIKIMAR YIN I'ITIKAFI••• .

Haqiqa ALLAH (SWT) Ya shar'antawa bayinsa yin i'itikafi, wanda manufar hakan ita ce komawar zuciya ga ALLAH (SWT)
domin neman kusanci da neman yardarSa, Kuma ALLAH ne ke debewa mai i'itikafi kewa a lokacin da ya nisanci mutanen dake debe masa kewa domin zai ke6antu ne da ambaton ALLAH, kuma haqiqa ALLAH yana son masu ambatonsa.

•••ZAMAN I'ITIKAFI••• .

ALLAH (SWT) Yace:

"Kada ku yi mubashara (hada jiki) da mata alhali kuna masu yin i'itikafi a masallatai" .

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2282 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

MARABA DA WATAN RAMADAN [16]
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2271 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

FALALAR KWANA GOMA (10) NA QARSHEN WATAN RAMADAN !!!

MARABA DA WATAN RAMADAN [16]

Kwanakin watan Ramadan dukkansu akwai falala acikinsu, sai dai mafi falalarsu sune kwanaki 10 na qarshe. Saboda ayoyin Alqur'ani da Hadithai ingantattu sun zo da bayanin falalarsu. Daga cikin falalar wadannan kwanaki akwai:-

1• Acikinsu ne ake dacewa da daren Lailatul Qadr, ba a nemansa acikin sauran kwanaki face acikin kwana 10 na qarshen Ramadan, saboda Hadithin Aisha (RA)
tace:

Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Ku nemi Lailatul Qadr acikin marar kwanaki 10 na qarshen watan Ramadan" .

(Bukhari 4/225, Muslim 1169)
2• Lallai Manzon ALLAH (SAW) Ya himmantu kuma ya kula sosai da wadannan kwanaki 10 na qarshen watan Ramadan, saboda idan suka zo Manzon ALLAH (SAW) Yana daura gyautonsa (damara) ya dage da ibada ya nisanci iyalansa, yayi ta ayyukan alkhayri da Da'a zuwa ga Ubangijinsa a Masallacinsa.

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2271 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

MARABA DA WATAN RAMADAN [15]
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2222 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

FIDIYA/FANSA (CIYARWA)

MARABA DA WATAN RAMADAN [15]

•FIDIYA: Shine ciyar da abincin mabuqaci matalauci a kowani wuni na Ramadan saboda rashin samun damar yin azumin ko kasa yinsa saboda girman shekaru da sauran uzurorin shari'ah.

Asalin wannan mas'ala shine fadar ALLAH (SWT) da Yace: "Akan wadanda basa iya yin azumi, azumi yana basu wahala, to sai suyi Fidiya (ciyarwa) wato fansar kai, ciyar da abincin miskini daya a kullum" .

(Surah ta 2 aya ta 184)
Ma'abota ilimi sun samu sa6ani a game da wannan ayar, wasu suna ganin shafaffiya ce, wasu kuma suna ganin ba shafaffiya bace .

Dan Abbas (RA) Yace:

"wannan ayah ba a shafeta ba, ta sauqa ne akan tsofaffi masu shakaru da yawa wadanda basa iya yin azumi, sai su ciyar da abincin miskini guda daya a kullum" .

(Bukhari 8/135)
Wadanda suka tafi akan cewa ayar shafaffiya ce sun kafa hujja da cewa: akwai ayar da ta shafe ta inda ALLAH (SWT) Yace: "Duk wanda ya kasance mazaunin gida acikin watan daga cikinku to ya azumce shi" .

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2222 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

MARABA DA WATAN RAMADAN [14]
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 3226 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

AZUMIN MARAR LAFIYA, MATA MASU HAILA DA MASU JININ BIQI (NIFAS), TSOFFI, MAI CIKI DA MAI SHAYARWA A WATAN RAMADAN !!!

MARABA DA WATAN RAMADAN [14]

••MARAR LAFIYA•• .

Marar lafiya shine wanda ya kasance cikin wani yanayi na rashin lafiya wanda ya kai bazai iya azumtar azumi ba.

Haqiqa ALLAH (SWT) Ya halatta wa marar lafiya ya ajiye azumi domin tausayawa da sauqaqa ga lamarinsa, sai dai rashin lafiyar dake sa ajiye azumi shine wanda yake cutar da maras lafiya a jikinsa, ko kuwa yin azumin agare shi zai qara masa wata rashin lafiya ta daban ko jinqirin warkewa.

•HUKUNCINSA: ALLAH (SWT) Yace: "Duk wanda ya kasance maras lafiya daga cikinku,ko a halin tafiya to sai ya rama kwanakin da yasha azumin" .

(Surah ta 2 aya ta 185)
Zai ajiye azumin ya rinqa irga abunda yasha, idan ALLAH Ya bashi lafiya zai rama bayan Ramadan, idan kuma rashin lafiya ne wanda bazai iya yin azumi ba koda bayan Ramadan ne to zai ciyar da miskini a kowace rana. ALLAH shine mafi sani.

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 3226 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

MARABA DA WATAN RAMADAN [13]
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2496 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

AZUMIN MATAFIYI !!!

MARABA DA WATAN RAMADAN [13]

MATAFIYI: shine wanda zai tashi daga wani gari zuwa wani gari, amma a zamanin Annabi (SAW) Matafiya suna kama hanyar tafiya ne da qafa ko akan wata dabba, amma a wannan Zamanin Matafiya suna tafiya ne a Mota ko a Jirgi wata motar ma hada AC.

ALLAH (SWT) Yace: "duk wanda ya kasance daga cikinku a halin rashin lafiya ko halin tafiya to sai ya qirga kwanakin da yasha Azumi domin ya rama daga baya, saboda ALLAH yana son sauqi gareku baya son ku da wahala ko tsanani" .

(Surah ta 2 aya ta 185)
•ZABI GA MATAFIYI:

Haqiqa Hadithai ingantattu sunzo da dama akan za6i ga matafiyi, ko yayi azumi ko yasha bayan Ramadan ya biya.

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2496 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

MARABA DA WATAN RAMADAN [12]
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 5007 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

FALALAR CIYAR DA MAI AZUMI !!!

MARABA DA WATAN RAMADAN [12]

Haqiqa ayoyin alqur'ani mai girma sun zo da kwadaitar da Musulmi akan ciyarwa saboda ALLAH a lokacin Azumi da lokacin da bana Azumi ba, da taimakawa matalauta da mabuqata domin yaqar talauci a tsakanin al'ummar musulmai, kuma yin haka na qara tabbatar da 'yan uwantakar musulunci a tsakanin musulmai.

Daga cikin wadannan ayoyi akwai fadar ALLAH (SWT) cewa:

"wadanda suke ciyar da dukiyoyinsu dare da rana , 6oye da bayyane, suna da sakamakon lada a wurin Ubangijinsu kuma basu tare da kowane irin tsoro ko baqin ciki (a ranar alqiyama) (Surah ta 2 aya ta 274)
"(Ku ciyar) daga Abunda muka fitar muku na (tsirrai) daga qasa, kada ku nufi maras kyau acikinsa kuna ciyar dashi, alhali ku baku kar6arsa, sai in (kun daure) kun runtse ido, ku sani ALLAH (SWT)
mawadaci ne ga abinda duk zaku ciyar kuma wanda ya cancanci yabo ne acikin ko wani hali" .

(Surah ta 2 aya ta 267)
"Ba zaku samu cikakkiyar lada, har sai kun ciyar da abunda kuke so, abunda duk kuka ciyar na alkhayri, to ALLAH Masani ne game dashi" .

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 5007 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

MARABA DA WATAN RAMADAN [11]
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 4026 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

SALLAR TARAWIHI (Asham)

MARABA DA WATAN RAMADAN [11]

Haqiqa wannan sallar sunnah ce daga cikin sunnonin Annabi (SAW), kuma an shar'anta sallar Tarawihi acikin jama'a saboda Hadithin Aisha (RA) da tace:

"Lallai Manzon ALLAH (SAW) Ya fito wata rana a tsakiyar dare, yayi sallah a masallaci, sai wasu mazaje suka yi koyi da sallarsa, washe gari magana ta yadu, a wani daren sai jama'a suka taru sosai, sai Manzon ALLAH (SAW) Yayi sallah, suka yi sallah tare dashi, washe gari kuma labari ya qara yaduwa akan haka, a dare na uku kuma aka cika masallaci, sai Manzon ALLAH (SAW) yayi sallarsa suka yi sallah bayansa, a dare na hudu masallaci ya kasa daukar jama'a, Manzon ALLAH (SAW) bai fito ba sai a lokacin sallar asuba, bayan ya qare sallar asuba tare da su sai ya fuskance su Yace:

"Ban rena qoqarinku ko matsayinku ba, amma ina jin tsoron a farlanta ta agareku ku kasa aiwatar da ita. Al'amarin sallar Tarawihi bai gushe ba akan haka har Manzon ALLAH (SAW)
Ya rasu" .

(Bukhari 3/220, Muslim 761)
Manzon ALLAH (SAW)
bayan tabbatar da shari'ah kuma tsoron da Annabi yake yiwa al'ummarsa kada a wajabta musu sallar tarawihi ya gushe, domin haka damar cigaba da tarawihi acikin jam'i ta tabbata.

Sayyidina Umar dan Khattab (RA) ya rayar da wannan sunnah kamar yadda Abdurrahman dan Abdullah Al-kari yace:

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 4026 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

MARABA DA WATAN RAMADAN [10]
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2523 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

ABUBUWAN DA SUKA WAJABA MAI AZUMI YA NISANTA

MARABA DA WATAN RAMADAN [10]

Haqiqa dole ne mu sani mai azumi na gaskia shine wanda dukkan ga66ansa suke azumi tare dashi, wajen barin sa6on ALLAH, kuma ya hana cikinsa daga dangogin abinsha da abinci, ya kare farjinsa daga jima'i kuma idan yayi magana bazai yi wadda zata 6ata masa azuminsa ba, sai maganarsa ta zamo mai kyau, ayyukansa su zamo kyawawa. Wannan shine azumi na haqiqa na shari'ah.

Haqiqa Manzon ALLAH (SAW) Ya kwadaitar da mai azumi ga siffantuwa da halaye nagari da kyawawan dabi'u, ya nisanci munanan halaye, da alfasha da surutan banza, duk da kasancewar miyagun halaye an umurci musulmi ya nisance su a kowane lokaci na rayuwarsa, sai dai hani a kansu da nisantarsu acikin wannan wata mai Alfarma lokacin ibadar Azumi yafi tsanani domin haka ne yake wajaba ga musulmi mai azumi ya nisanci, al'amura guda uku ya barsu gaba daya, wadannan abubuwa basa haduwa da azumi a lokaci daya, sune kamar haka:- .

1• FADAR QARYA: wannan yana lalata azumi, kuma yana yanke ladar mai azumi, qarshe ma, ya maida Azumi, tamkar ba ayi ba. Saboda Hadisin Abu- Huraira (RA) Yace: . Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Duk wanda bai daina qiran qarya ba a lokacin azumi to ALLAH (SWT) ba yi da buqatar azuminsa, ko yaci abincinsa ko yasha abun shansa duk daya ne a wurin ALLAH (SWT). . (Bukhari 4/99)

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2523 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

MARABA DA WATAN RAMADAN [8]
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2987 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

ABUBUWANDA AKA HALATTAWA MAI AZUMI !!!

MARABA DA WATAN RAMADAN [8]

Haqiqa saboda tausayin ALLAH (SWT) ga bayinsa, yana nufinsu da sauqi, baya nufin ya tsananta musu, saboda haka ne ya halatta wa mai Azumi wasu al'amura, kuma ya dauke masa laifi idan ya aikata su, ga wasu daga ciki:-

1• YIN ASWAKI GA MAI AZUMI: Aswaki yana cikin sunnar Annabawa, wanda Annabi (SAW)
yayi umurni da ita kamar yadda yace:

"Badon kar na tsanantawa al'ummata ba dana umurce su da yin Aswaki acikin alwala" (Bukhari 2/311, Muslim 202)
Abunda wannan hadith ke nunwa shine Manzon ALLAH (SAW) bai ke6ance mai azumi ba daga waninsa ba domin haka mai azumi da maras azumi duk zasu iya yin aswaki a kowace alwala.

2• WAYEWAR GARIN MAI AZUMI DA JANABA: Ya kasance Annabi (SAW) Alfijir na riskarsa alhali yana da janaba daga iyalinsa, sai yayi wanka bayan 6ullowar alfijir ya cigaba da azuminsa.

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2987 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

MARABA DA WATAN RAMADAN [7]
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2684 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

SAHUR DA HUKUNCE- HUKUNCENSA

MARABA DA WATAN RAMADAN [7]

•SAHUR: Shine abincin da Musulmi ke ci a qarshen rabin kashin daren Azumi, kafin 6ullowar alfijir.

Annabi (SAW) yayi umurni da sahur domin bambantawa tsakanin Azuminmu da Azumin ma'abota littafi (Yahudu da Nasara)
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Banbancin Azuminmu dana ma'abota littafi (Yahudu da Nasara) shine cin abincin Sahur" (Dabarani 6127)
•FALALAR YIN SAHUR:

Akwai albarka cikin yin sahur, wannan kuma yazo a hadith masu yawa, daga cikinsu akwai Hadithin Salman (RA) Yace:

Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Ana sanya albarka acikin abubuwa guda 3:- daga cikinsu akwai sahur" (Dabarani 6127)
Da kuma Hadithin Abu- Hurayrah (RA) Yace:

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 2684 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

MARABA DA WATAN RAMADAN [6]
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 3086 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

BUDA BAKI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA

MARABA DA WATAN RAMADAN [6]

Haqiqa buda baki yana daga cikin Sunnar Annabi (SAW).

•BUDA BAKI: shine mai Azumi ya buda baki (Yaci wani abu) idan rana ta fadi, yini ya bada baya dare kuma ya gabato, daga wannan lokacin buda baki yayi ga mai Azumi.

•GAGGAUTA BUDA BAKI:

Gaggauta buda baki yana kawo wa al'ummar musulmi alkhayri, saboda Hadithin Sahal dan Sa'ad (RA) ya tabbatar cewa:

Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Mutane ba zasu gushe tare da alkhayri ba matuqar suna gaggauta buda baki" (Bukhari 4/173, Muslim 1093)
Idan al'ummar Musulmi suna gaggauta buda baki to haqiqa sun wanzar da Sunnar Annabi (SAW), Yazo a hadithin Sahal dan Sa'ad (RA) cewa:

Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Al'ummata ba zata gushe a kan sunnata ba matuqar bata jiran 6ullowar taurari, a wajen buda bakinta ba" (Ibn Hibban 891 ya ruwaito shi da ingantaccen isnadi)
kuma an ruwaito Hadith daga Abu Hurayrah (RA)
cewa:

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 3086 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

MARABA DA WATAN RAMADAN [5]
(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 3998 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

FA'IDODIN AZUMI TARE DA FALALARSA

MARABA DA WATAN RAMADAN [5]

Da yawa daga cikin ayoyin Alqur'ani da Hadithan Manzon ALLAH (SAW) sun bayyana Fa'idar Azumi da kuma Falalarsa, kamar haka:

• SAMUN GAFARA DA LADA MAI GIRMA GA MASU AZUMI MAZA DA MATA:

ALLAH mai Girma da daukaka Yace:" lallai musulmai maza da musulmai mata, da muminai maza da muminai mata, da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu haquri maza da masu haquri mata, da masu tsoron ALLAH maza da masu tsoron ALLAH mata, da masu sadaqa maza da masu sadaqa mata, da masu azumi maza da masu azumi mata da masu tsare farji su maza da masu tsare farjinsu mata da masu ambaton ALLAH maza da masu ambaton ALLAH mata,ALLAH yayi musu tattalin gafara da sakamako mai girma" .

(surah ta 33 aya ta 35)

Kunga a wannan ayar azumi tazo acikinta.

• AZUMI GARKUWA NE DAGA WUTA KUMA KARIYA CE DAGA SHA'AWA:

(Karancea Fiye Da Wannan Labari... | 3998 Bytes Mafi | Lafiyata? | Ci: 0)

 
   
   
   
   
   
   
   

 

 
                  
 

EsinIslam Updates

 
 
Media Fora Networks
منتديات الشبكة الإعلامية

Video Muslim Channels
فيديو قناوات المسلمين

Audio Qur\'an Reciters
صوتيات القراء القرآنية

News Articles Writers
كٌتاب المقالات الأخبارية
 
Set Adhan Prayer Time
تعيين توقيت الصلوات

Newspapers & Magazines
جرائد ومجلات صحافية

Ramadan New Top Fatwa
فتاوى رمضان الجديدة الفائقة

Watch Live Muslim TVs
مشاهدة تلفزيون المسلمين الحي
 
 
 

Audio Qur\'an Recitations

  Abdul Basit Abdul Samad - Tajwid
  Mahm. Khalil Al-Hussary - Tajwid
  Mahmoud Ali Al-Banna - Tajwid
  Moh. Siddiq Al-Minshawi Tajweed
  Abdul Basit Abdul Samad - Tarteel
  Abdullah Bin Ali Basfer - Tarteel
  Abdullah Al-Khayyat - Tarteel
  Abdur-Rahman Alsudaes - Tarteel
  Abdul-Wadood Haneef - Tarteel
  Abu-Bakr Al-Shatri - Tarteel
  Adel Al-Kalbani - Tarteel
  Ali Jaber - Recites Tarteel
  \'Aliyy Al-Huthaifiyy - Tarteel
  Ahmad Al-\'Ajmy - Tarteel
  Ahmad Saud - For Children Tarteel
  Al-Husayni Al-Azazi - Tutorial
  Khalifah Al-Tunaiji - Tarteel
  Khalifah Al-Tunaiji -Tutorial
  Maher Al-Muaiqli - Tarteel
  Maher Al-Muaiqli -Tutorial
  Mahm. Khalil Al-Hussary Tarteel
  Mahmoud Ali Al-Banna Tarteel
  Mishary Al-\'Afasi - Tarteel
  Mohammed Al-Muhasny - Tarteel
  Mohammed Ayyub - Tarteel
  Mohammed Jebreel - Tutorial
  Moha. Siddiq Al-Minshawi Tarteel
  Moh. Siddiq Al-Minshawi - Tutorial
  Mustafa Ismaeel - Qur\'an Tarteel
  Saad Al-Ghamdi - Tarteel
  Sa\'ud Al-Shuraim - Tarteel
  Qur\'an Children Tutorial - Taaleem
  Other Reciters - Tartir And Tajwid
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 

 

 
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamic Forum, News Forums, Muslim News, Debate Fora, Discussions, Muslim Social Media In Arabic, English, Yoruba, Hausa, Indonesian Bahasa, Swahili, French, Urdu, Somali, Persian, Turkish, Arab Forums Writers On Wossam.Com, EsinIslam.Com And Muxlima.Com
 

  

 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Gaban Shafin :|: Samiya Goma :|: Sabon Kanun Labarai :|: Takardun Labari :|: BaHaushenka :|: Cagiya Hausa :|: Wani Ajali Ambatacce Hausa :|: 'Yan Hausa :|: Yakan Yi Bitar :|: Sakonninka :|: Bincike :|: Mujallan :|: Kissoshi Dakin Littattafai :|: Ciki :|: Yanar Gizon Na Da Alaka Da :|: Sami Ceto Kayayyakin :|: FAQ :|: Tsananta Mana :|: Mawsu'ah
 
Notebook :}-{: مذكرة
 
 
 

 Custom Search EsinIslam بحث مخصص

Google Yahoo Bing Excite Ask Yandex
 

 
← Go The Portal Home →
[] Go The Islamic Mobile & Tablet []
Get in Muslim Forums →
 

- About Us    - Explorer   - Writers   -Reciters   - Rulings   - Contact Us

About Us
من نحن
Our Sheikh
من شيخنا
Contact Us
اتصل بنا
Donate to Us
تبرع عندنا
Fatwa Request
الإستفتاء
Brought To You By The Awqaf London - The Society Of Students Of Sheikh Dr. Abu-Abdullah Adelabu
In partnership with - بالمشاركة مع
World's Scholars and Professionals for State Affairs and the Malikis (WOSSAM) Co-Chaired By Sheikh Dr. Abu-Abdullah Adelabu and Minister Ambassador Prof. Ahmad El-Ibraheemi
:: علماء العالم والمحترفون لشؤون الدول والمالكية يشاركان في رئاستها الشيخ الدكتور أبو عبد الله أديلابو والوزير السفيرالأستاذ أحمد الإبراهيمي

We Are EsinIslam Media Of The Awqaf Students Of Sheikh Abu-Abdullah Adelabu

 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 

Director Umm-Abdullah Adelabu Head Office admin@esinislam.com Amir (President) Sheikh Abu-Abdullah Adelabu (Ph D Damas) sheikh@esinislam.com

 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 

EsinIslam.Com And Muxlima.Com Designed And Produced By Awqaf London Copyright All Rights Reserved. Media contact publicrelations@esinislam.com

No copyright permission required for users whose works, activities and intentions are for purpose of Da'wah, Islamic studies and services to the Muslims. However The Awqaf's Majlis (Council) does review 'Given Permissions' and 'Media Engagements' as necessary

P. O. Box 46044, Maida Vale, London W9 3WN The United Kingdom Tel: +44 (0) 207 266 2207 Fax: +44 (0) 207 266 1289 / 266 3496

Please Pray For Us And For Our Sheikh - May Salawat Allah And Salaam Allah Be Upon Our Beloved Prophet Muhammad s.a.w

 

EsinIslam.Com - Muxlima.Com from The Awqaf London

 

الله أكبر :: Allah Is Great

 
 
 

    
    
 
Radio راديو
Telly تلفاز
Lots لائحة
List لوحة
Tanzeel التنزيل
Jedwell
Adhan
ẹBooks
Op-ẹds
ẹQuran القرآن
ẹTrend
ẹTrack
ẹFilm
ẹFind
Qunoot القنوت
Menu قائمة
Live! حيًّا
ẹStories
ẹFatwas
 
 
 
x