Muhawara Hausa
 



SAKON KHUDUBAR JUMU'AH DAGA MASALLACIN MANZON ALLAH (SAW) DAKE MADINAH DAGA
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen SAKON KHUDUBAR JUMU'AH DAGA MASALLACIN MANZON ALLAH (SAW) DAKE MADINAH DAGA BAKIN SHEIKH ABDULMUHSIN BN MUHAMMAD AL-QASIM (HZ) A YAU RANAR

ISA ALI IBRAHIM PANTAMI

Limamin a ranar wannan Jumu'ah yayi Khudubar ne akan "ILMI, DARAJARSA DA MATSAYIN MA'ABOTANSA." Ga sakon kamar haka 1) Babban limamin ya fara da al-Khudubatul-Hajah, wacce itace khudubar da Annabi (SAW) yake fara wa'azi ko huduba da ita.

Tana karantar da kadaita Allah, da nuna shiriya ta Allah ne, kuma ribar rayuwa na cikin Taqwa.

2) Sannan Limamin yayi umurni da "Taqwa" wato cikakkiyar biyayya ga Allah (SWT). Domin Taqwa itace hasken da ake gani da shi, kuma Taqwa ke rayar da zuciya. Allah yana cewa: "Lalle wanda yafi daraja gun Allah shine wanda yafi Taqwa." 3) ILMI DA TAQWA ke shiryar da bawa zuwa ga MahaliccinSa.

Domin da ilmi da Taqwa ake banbancewa tsakanin HALAL da HARAM.

4) Ma'abota Ilmi da su ake samun shiriya. Imam Ahmad Bn Hambal (RH) yana cewa: "Mutane suna da bukatar Ilmi fiye da abinci. Domin abinci akan bukace shi ne sau 2 ko sau 3 a wuni, amma ILMI ana bukatarsa a kowane lokaci a kowace rana." 5) Allah ya siffata kan Sa da ilmi. Allah yana cewa: "(Allah) ya ilmantar da mutum abun da bai sani ba." 6) ILMI HIKIMA CE, da Allah ke baiwa bayinSa. Allah yana cewa:

"Yana bada hikima ga wanda ya so, duk wanda aka ba shi hikima, hakika an ba shi alheri mai yawa." 7) Allah ya fifita dan Adam da ilmi akan Malaa'ika. "Wa 'allama Adamal Asma'a kullaha thumma arabhahum alal Malaa'ikati....." 8) Allah ya bawa Yusuf (AS) ilmi. Allah yace: "Lokacin da ya kai karfinsa, mun ba shi hukunci da ilmi." 9) Allah ya daukaka darajar wasu Annabawa sosai kuma ya bayyana cewa ya ba su ilmi. Daga cikinsu, akwai Musa, Is'haq, Daud, Sulayman, da Isa (AS).

10) Duk da darajar Annabi Musa (AS) yaje wajen Khidr neman ILMI kamar yadda Qur'ani ya bayyana cikin Suratul Kahf. (Wannan ke bayyanawa cewa DARAJA ko daukaka ba sa hana neman ilmi).

11) Qissar Annabi Sulayman a Suratun-Naml ta karantar da mu cewa, lalle mai Ilmi yafi mai karfi da bai da ilmi. (Kamar yadda Qur'ani ya nuna mana cewa, Aljanin da ke da "Ilmun Minal Kitaabi" yafi "Ifritu" da ke da karfi, samun nasara wajen ayyuka).

12) Allah ya karantar da mu cewa shi ya ILMANTAR da Annabinmu (SAW). Allah SWT yana cewa: "Ya ilmantar da kai abun da ba ka sani ba. Lalle falalar Allah akan ka mai girmace." 13) Annabi (SAW) bai nemi karin wata ni'imah ba a duniya sai ILMI.

Yana adduah da cewa: "Rabbi zid niy ILMA." 14) Annabi (SAW) yana cewa: "Malamai magada Annabawa ne.

Kuma Annabawa ba su gadar da zinare ko azurfa ba, sai dai sun gadar da ILMI...."(Tirmizhiy ya ruwaito).

15) Allah ya nuna darajar shaidar masu ilmi. Allah yana cewa: Allah yayi shaidar babu abun bautawa da gaskiya sai Shi, haka Malaa'iku da ma'abota ilmi, cewa Allah yana tsaye da adalci." 16) Allah ya nuna mana cewa Malaman (gaskiya) sune masu tsoron Allah.

17) Masu daraja idan sun nemi ilmi wannan na kara musu daraja.

Annabi (SAW) yana cewa: "Zababbunku a jahiliya su ne zababbunku a musulunci idan sun fahimci addini." 18) Ba'a samun ingantacciyar Aqeedah da Ikhlasi dole sai da ilmi.

Allah yana cewa: "Ka sani babu abun bautawa da gaskiya sai Allah." 19) Darajar mai ilmi bata zama daya da darajar jahili.

20) ILMI HASKE NE. Allah yace: "shi (ilmi) ayoyi ne bayyanan nu a cikin zukatan wadanda aka bawa ilmi." 21) ILMI SHI YAKE DAIDAITA HANKALI. Allah yace: "Wadancan misalai ne muke bugawa don mutane, amma babu masu hankalta sai masu ilmi." 22) ilmi ya halatta ayi tsere-tsere cikin neman sa.

23) Hanyar ilmi, hanya ce ta Aljannah. Annabi (SAW) yana cewa:

"Duk wanda ya kama hanya don neman ilmi, Allah ya sauwake masa hanyar zuwa Aljannah." (muslim ya ruwaito)
24) Imam Malik RH yana cew: "ilmi kariya ne daga FITINTINU." 25) Annabi (SAW) yana cewa: "Ku isar da ga gare ni, ko aya daya." 26) Allah ya umurce mu, mu rika tambayar masu ilmi kan kowace matsala.

27) Annabi ya kan yi adduah ga duk wanda yake so, da Allah ya kara masa ilmi. Kamar yadda yayi wa Abdullahi bn Abbas (RA)
adduar Allah ya kara ma sa fahimtar addini.

28) Allah yana daukaka masu ilmi da imani.

29) Annabi (SAW) yana cewa idan mutum ya mutu, duk ayyukansa sun yanke amma ban da guda uku, daga cikinsu akwai ilmi mai amfani.

30) Mafi girman Ilmi shi ne ilmin sanin Allah, da sunayenSa da SiffofinSa, da kadaituwarSa.

31) Duk lokacin da ilmi ya karu, daraja tana karuwa.

32) Malamai sune kan gaba wajen sanin Allah (SWT).

33) Girmama Malamai (na kwarai) wani bangare ne na addini.

Saboda sune Waliyan Allah kamar yadda Imam Shaafiiy RH yake fada.

34) Allah yayi umurni da yiwa AnnabinSa salaati. (Allahumma Salli ala Muhammadin, wa ala..)
35) Ya Allah ka kara yarda da Abubakar, da Umar, da Uthman da Aliyyu da sauran Sahabbai (Radhiyal Lahu Anhum ajma'in).

36) Allah ka taimaki Musulunci da Musulmai.

37) Allah ka albarkaci garuruwanmu kuma ka kara mana wadata.

38) Allah ka gyara kasashen dake cikin Fitintinu da damuwa.

39) Yaa Allah ka datar da Shugabanmu cikin yin dai dai, Yaa Allah ka datar da shi cikin aiki da littafinKa da Sunnar AnnabinKa (SAW).

Yaa Allah ka taimaki sojojinmu kuma ka basu ikhlasi.

40) Yaa Allah ka shayar da mu ruwan sama.

41) Yaa Allah lalle mun zalunci kawunanmu, idan ba ka gafarta mana ba, kuma baka mana rahama ba, zamu kasance cikin masu asara, Yaa Allah ka bamu ikon aiki da khudubar, Yaa Allah ka amsa mana addu'o'inmu,....

 Posted By Aka Sanya A Sunday, February 26 @ 04:25:28 PST Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 3
Kurioi: 1


Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen



"SAKON KHUDUBAR JUMU'AH DAGA MASALLACIN MANZON ALLAH (SAW) DAKE MADINAH DAGA" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com