Muhawara Hausa
 



ARBA'UNA HADITH (17) HADISI NA SHA BAKWAI
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji ARBA'UNA HADITH (17) HADISI NA SHA BAKWAI

An karbo daga Abu 'ya'ala shaddadu bin Ausi R.A daga Annabi s.a.w yace Allah ta'ala ya wajabta kyautatawa ga kowanne irin abu (da mutum zai yi a duniya) idan kuka yi nufin kisa ku kyautatawa kinsan idan, kun yi nufin yanka (dabba ku kyautatawa yankan, kowanne dayanku(dan zai yi yankan) ya wasa wukarsa ya huta da abin yankasa> Muslim 1955 ya rawaito shi.

Ma'ana Ubangiji ya wajabta kyautatawa; ga kowanne irin abu da mutum zai a duniya ya zamanto ya kyautatashi, kowanne irin abu dan Adam ne babba ne yana bukatar ihsaninka don haka sai Annabi s.a.w zai kawo misali daya wanda ya shafi dan Adam , na biyu kuma wanda ya shafi dabba, yace, idan kuka yi nufin kisa to ku kyautata kisan, wato mutum ne yayi laifin kisa kuka zo za ku kasha shi wannan kisan ku kyautata shi abin nufi, ku yi amfani da abin da zai zare ransa nan take, ba wai ku daure shi da igiya ku rataye ba, ya dade bai mutu ba, wannan idan kukayi haka, kun sabawas wannan hadisin ba a ratayewa a musulunci, sai dai a fille kai, ko a yi amfani da dukkan wani abu wanda nan da nan zai dauke numfashi cikin kankanen lokaci.

Cikn sakan ko abin da bai kai sakan ba, nan da nan ya dauke ran mutm ya huta. Amma ba mutum ya jigata kafin ya mutu, wannan bai halatta ba.

Sannan kuma baya halatta ku yi mus;a, wato kacancana gawa mutum ko da kafiri ne kuka zo kasha shi in dai kun sare masa rai to ya riga ya gabata, ba sai kun fille kai, kun yanke hannu kun yanka kafa, kun ja a kasa, wannan duk ta'addanci ne wanda sharia' tace Kada ku yi ta'adanci hakika Allah bay a son 'yan ta'adda)
(Al-bakara)
Amma malamai sun ce in mutun ya kashe dan uwansa musulmi kisa na ganganci, aka zo ayi masa kisasi yayin to shi ma in anzo kasha shi babu laifi a kacancana gaward don ya zamnto kisasi ya tabbata, kamar yadda Allah ya fada. Ko kuma sai dai mu kasha shi shi kadai, ba bai sai mun rama abin da yayi wad an uwansa ? Malik da Ahmad bin Hambal da Shafi'I suka ce ina! Ai yadda yayi wad an uwansas shi ma sai an yi masa wannan shi ne kisasi!

Haka idan kun yi nufin yanka dabba kuma, to ku kyautata yankan wannan dabbar din

 Posted By Aka Sanya A Sunday, February 26 @ 05:29:34 PST Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji



"ARBA'UNA HADITH (17) HADISI NA SHA BAKWAI" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com