Muhawara Hausa
 



MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 11
 
Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi DR. MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 11

ME YA FARU A KARBALA? 11 Husaini Ya Isa Karbala Da sayyadi Husaini ya kusa isa Kufa sai ya gamu da Umar bin Sa'ad dauke da sakon kaninsa Muslim wanda sai yanzu ne ya san cewa an kashe shi. Muslim ya nemi Husaini da ya koma abinsa tunda mutanen Kufa ba da gaske suke ba. Shi dai Umar bin Sa'ad daman yana cikin 'yan Shi'ar Ali kamar yadda shi ma wannan sabon gwamna Ubaidullahi bin Ziyad yake. Duba KITABUR RIJAL na TUSI Shafi na 54 don haka Bin Sa'ad sai ya bada labarin kashe Muslim yana kuka ta yadda ya zaburar da 'yan uwansa, ya kuma ja hankalinsu ga daukar fansa. Husaini ya so ya komawarsa amma sauran dangi na ganin dole ne a isa Kufa zuwa daukar fansar jinin dan uwansu.

Duk mai hankali zai iya lura da hannun kaddara a cikin wannan lamari.

Domin kuwa ya za a iya daukar fansar wanda hukuma ta kashe shi?

Kuma a kan wa za a dauki fansa? Sannan su waye zasu dau fansar?

Husaini ba wani shirin yaki da ya zo da shi. Bil hasili ma kaffatanin na tare da shi mata ne da kananan yara.

Abinda ya fi kome ban mamaki shi ne dawowar Umar bin Sa'ad bayan ya koma Kufa, a yanzu wai ya zo ne yana jagorancin wani ayari na dakaru 4000 dauke da umurnin Ubaidullahi bin Ziyad na a kama Husaini! Sun tarar da Husaini ya karaso hanyar Kufa har ya sauka a Karbala.

Bayan wasu muhawarori a tsakanin su sayyidina Husaini ya aminta da komawa inda ya fito. Umar bin Sa'ad ya ce, sai mun nemi amincewar gwamna Ubaidullahi.

Da farko da aka sanar da shi, Ubaidullahi ya ce ba damuwa a bar shi ya komawarsa. Amma wani fitaccen dan Shi'ah, makiyin Allah, maras imani, shine Shamru bin Dhil Jaushan wanda ya kasance cikin sojojin sayyidina Ali kamar yadda Shahrudi ya fada a cikin littafinsa MUSTADRAK ILMI RIJALIS HADITH (4/224)
, wannan munafukin dan Shi'an sai ya yi fadanci zuwa ga Ubaidullahi da cewa, ai har yanzu Husaini na da hadari ga mulkin Yazid, domin akwai yiwuwar in ma ya tafi ya dawo.

Don haka babu mafita in ban da a kama shi.

Da aka ki karbar bukatar Husaini ta komawa Makka sai ya ba da wasu zabi guda biyu; ko dai ya tafi wurin masu jihadi a matsayin daya daga cikin sojoji ko kuma ya tafi wurin Yazidu da kansa ya yi mubaya'a.

Amma dai duk wadannan muradun basu samu ba ﻟﻴﻘﻀﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻣﺮﺍ ﻛﺎﻥ ﻣﻔﻌﻮﻻ don Allah ya zartar da kaddarar da ya hukunta.

Ya zama dole bayan haka ta faru Husaini ya shirya don kare kansa daga wulakanci. A nan ne ya yi wata huduba a daren Tasu'a wadda a cikinta ya fada ma 'yan rakiyarsa cewa fa yana ganin akwai arangama a tsakaninsa da wadannan mutane gobe. Sannan ya yi izni ga duk wanda ke da bukatar juyawarsa ya tafi. Nan wasu suka yi amfani da wannan dama kafin a wayi sun tafi abinsu.

Wayuwar garin Ashura Husaini ya shirya tare da mutanen da basu wuce 50 ba daga asalin 72 da ya fito da su domin su fuskanci rundunar gwamnatin Ubaidullahi mai soji 4000.

Abin tambaya a nan shi ne, ya aka yi aka samu wannan adadin sojoji a Kufa garin da yake na Shi'ah ne zalla amma ga su sun zo su yaki ko su kama Husaini? Ina duk magoya bayan da suka sa hannu a kan takarda? Ina masu mubaya'a 18,000 da suka damka hanayensu ga Muslim dan Aqilu a madadin Husaini?

Wannan shi ya sa malaman Shi'a suka tuhumci mabiyansu da aikata danyen aikin da zamu yi magana a kan sa. Kafin mu kawo maganganunsu bari mu kammala fadin wannan abin kunya, abin takaici da ya cimma al'ummar musulmi.

A lokacin da aka ja daga tsakanin rundunonin guda biyu, Shamru ne ya bada koren haske sai aka fara karawa. Kuma akalla soji 88 sun kwanta dama daga cikin wannan tsinanniyar runduna. Ganin irin hasarar soji da suka yi kuma ba wani alamun saranda daga sayyidina Husaini sai Zur'atu At Tamimi wanda shi ma dan Shi'ah ne ya kai sara ga Husainin a kafadarsa, Sinanu dan Anas -wani dan Shi'ar shi ma – ya kai ma Husaini hari ga makogaronsa, Sannan ya sare shi a kirji. Kafin Husaini ya kai kasa wani shaidani ana ce masa Khuli Al Asbahi – dan Shi'ah – ya sa takobi ya cire kansa. Kada Allah ya yarda da su baki daya.

Zamu kawo sharhin malaman Shi'ah kan wannan lamari daga littafansu Sannan mu je birnin Sham don mu ji yadda Yazidu ya tari wannan mugun labari.

Ku ci gaba da biyo mu.

 Posted By Aka Sanya A Tuesday, May 09 @ 05:23:43 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi:
Son Maso Wani Koshin Yunwa!: Gidan Annabi Mohammad (SAW)


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi



"MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 11" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com