Muhawara Hausa
 



ZUNUBI CUTANE, TUBA KUMA MAGANINE
 
Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai ZUNUBI CUTANE, TUBA KUMA MAGANINE

Kowanne cuta da Allah Subhanahu Wata'ala Ya yita ya sanya abinda ya kasance shine maganin wannan cutar sai dai ba dolene dan Adam Ya kai ga wannan Maganin a lokacin da yake bukata kodai saboda karancin ilimin mu ko kuma rauninmu.

Mafi girman cuta dake halaka bawa itace zunubi (sabon Allah) domin bata gushe wajen jefa mutum kunci anan duniyaba hasalima mai wannan cutan zaifi cutuwa a bayan Mutuwarsa, Cikin Falalar Allah Da RahmanSa Wannan cuta ya san mata abinda ya zama magani har ma da rigakafin don kaucema kamuwa da ita.

Maganin wannan cuta kuwa shine TUBA DA NEMAN GAFARAR ALLAH a cikin dukkan zunubanmu wadanda muka sani da wadandama bamu san mun aikataba.

Allah Subhanahu Wata'ala Yace; ‎ﻭﺗﻮﺑﻮﺍ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪﺟﻤﻴﻌﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻮﻥﻟﻌﻠﻜﻢﺗﻔﻠﺤﻮﻥ Kutuba Zuwa ga Allah gaba daya yaku Muminai tabbas zaku rabauta. {suratul Nur 31} Allah Subhanahu Wata'ala Yace; ﺇﺳﺘﻐﻔﺮﻭﺍ ﺭﺑﻜﻢﺛﻢﺗﻮﺑﻮﺍ ﺇﻟﻴﻪ ku nemi gafarar ubangijinku sannan ku tuba gareshi. {Suratul hud 3} ﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ ﻳﻘﻮﻡ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﺣﺘﻰ ﺗﻨﻔﻄﺮ ﻗﺪﻣﺎﻩﻓﻘﻠﺖ ﻟﻪ: ﻟﻢ ﺗﺼﻨﻊ ﻫﺬﺍ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪﻭﻗﺪ ﻏﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻚ ﻣﺎ ﺗﻘﺪﻡ ﻣﻦ ﺫﻧﺒﻚ ﻭﻣﺎ ﺗﺄﺧﺮ!

ﻗﺎﻝ'' : ﺃﻓﻼ ﺃﺣﺐ ﺃﻥ ﺃﻛﻮﻥ ﻋﺒﺪﺍ ﺷﻜﻮﺭﺍ'' ( (ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ .


Ummuna A'isha Allah Ya kara ya kara yarda a gareta tace; Annabi Muhammad Sallallahu Alayhi Wasallam Yana yin sallah a cikin dare har duga-duganSa su kumbura, Sai tace Masa, Donme kake yin Wannan Ya manzon Allah Hakika an gafarta maka abinda ka gabatarba na daga Zunuban Ka da wanda ka jinkirta? Sai Annabi Muhammad Sallallahu Alayhi Wasallam Yace; Shin bakyaso na zama bawa mai godiya. {bukhari da muslim} [Al-Bukhari].

ﻭﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ: ﺳﻤﻌﺖ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻮﻝ'' : ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺇﻧﻲ ﻷﺳﺘﻐﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺃﻛﺜﺮ ﻣﻦ ﺳﺒﻌﻴﻦ ﻣﺮﺓ '' ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ 
An karbo Daga Abu Harairah Allah Ya kara yarda A gareshi Yace; Naji manzon Allah Sallallahu Alayhi Wasallam Yace; Wallahi ni ina neman gafarar Allah kuma ina tuba Gare Shi a cikin wuni sama da sau Saba'in.

{Bukhari} ﻭﻋﻦ ﺍﻷﻏﺮ ﺑﻦ ﻳﺴﺎﺭ ﺍﻟﻤﺰﻧﻰ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ: ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ '' :

ﻳﺎﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺗﻮﺑﻮﺍ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﺳﺘﻐﻔﺮﻭﻩ ﻓﺈﻧﻰ ﺃﺗﻮﺏ ﻓﻲ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﻣﺎﺋﻪ ﻣﺮﺓ'' ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ 
An karbo daga Al aghar bin yasar Al Muzani Yace; Manzon Allah Sallallahu Alayhi Wasallam Yace; Yaku Mutane ku tuba zuwa ga Allah kuma ku Nemi gafararsa, Lallai ni ina tuba gareshi a cikin wuni sau Dari. {Muslim} ﻭﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻣﻮﺳﻰ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻗﻴﺲ ﺍﻷﺷﻌﺮﻯ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ'' : ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻳﺒﺴﻂ ﻳﺪﻩ ﺑﺎﻟﻠﻴﻞ ﻟﻴﺘﻮﺏ ﻣﺴﻲﺀ ﺍﻟﻨﻬﺎﺭ ﻭﻳﺒﺴﻂ ﻳﺪﻩ ﺑﺎﻟﻨﻬﺎﺭ ﻟﻴﺘﻮﺏ ﻣﺴﻲﺀ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﺣﺘﻰ ﺗﻄﻠﻊ ﺍﻟﺸﻤﺲ ﻣﻦ ﻣﻐﺮﺑﻬﺎ'' ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ An karbo daga Abi Musa Abdullahi Bin kais Yace; Manzon Allah Sallallahu Alayhi Wasallam Yace; Allah madaukakin Sarki Yana shimfida hannunSa a Cikin dare Saboda ya gafartama wadanda sukayi sabo (zunubi) da rana, Yan shimfida hannunSa da rana Saboda ya gafartama wadanda sukayi sabo (zunubi) A cikin Dare, harsai rana ta fito ta mafadarta. {Muslim} Allah SubhanahuWata'ala Ya gafartama Annabinsa Amma duk da haka yana yawaita tuba gare Shi da kuma bauta har takai ga wani sassa a jikinSa yana kumbura , ina kuma ga ni-da-kai da a kullum muna aikata aikin sabo kuma bamu da tabbacin karbuwar ayyukan mu na alkhairi, kenan Ya zama wajibi a garemu mu yawaita Neman Gafarar Allah Da Tuba Zuwa gare Shi domin samun Tsira a Ranar Sakamako.

Yana daga cikin sharudan tuba, Yin nadama akan aikin, kauracema Aikin ba tare da jinkiriba, Neman gafarar Allah Subhanahu Wa'ta Ala, Sannan idan Akwai hakkin wani ka mayar masa.

YA ALLAH MUNA NEMAN GARARKA KUMA MUNA TUBA DAGA DUKKAN ZUNUBANMU WADANDA MUKA SAN MUN AIKATA DA WADANDA BAMU SANI BA.

 Posted By Aka Sanya A Wednesday, October 04 @ 08:40:57 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 5
Kurioi: 1


Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai



"ZUNUBI CUTANE, TUBA KUMA MAGANINE" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com