Kuma ku nẽmi gãfara gun Ubangijinku. Sa'an nan ku tũba zuwa gare Shi, Ya jiyar
da ku dãɗi, jiyarwa mai kyau zuwa ga ajali ambatacce, kuma Ya bai wa dukkan
ma'abucin, girma girmansa. Amma idan kun jũya, to, lalle nĩ, inã tsõron azãbar
yini mai girma a kanku.
To, lalle sũ sunã karkatar da ƙirjinsu dõmin su ɓõye daga gare shi. To, a
lõkacin da suke lulluɓẽwa da tufãfinsu Yanã sanin abin da suke ɓoyewa da abin da
suke bayyanãwa. Lalle Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãzã.
Kuma shi ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwanaki shida, kuma
Al'arshinSa ya kasance akan ruwa, dõmin Ya jarrabã ku, wannan ne daga cikinku
mafi kyãwon aiki. Kuma haƙĩƙa idan ka ce: "Lalle kũ waɗanda ake tãyarwa ne a
bãyan mutuwa," haƙĩƙa waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Wannan bai zama ba fãce
sihiri bayyananne."
Kuma lalle ne idan Mun jinkirta da azãba gare su zuwa ga wani lõkaci ƙidãyayye,
haƙĩƙa sunãcẽwa me yake tsare ta? To, a rãnar da zã ta je musu, ba ta zama abin
karkatarwa ba daga gare su. Kuma abin da suka kasance suna yin izgili da shi, yã
wajaba a kansu.
Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sa'an nan kuma
Muka zãre ta daga gare shi, lalle ne shĩ, hakĩka, mai yanke tsammãnine, mai
yawan kãfrci.
Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana masa ni'ima a bãyan cũta ta shãfe shi, Yana cẽwa
mũnanan halaye sun tafi daga wurina. Lalle shi mai farin ciki ne, mai alfahari.
Sabõda haka tsammãninka kai mai barin sãshen abin da aka yi wahayi zuwa gare ka
ne, kuma mai ƙuntata ƙirjinka da shi ne dõmin sun ce: "Dõmin me ba a saukar masa
da wata taska ba, kõ kuma Malã'ika ya zo tãre de shi?" Kai mai gargaɗi ne kawai.
Kuma Allah ne wakili a kan kõme.
Kõ sunã cewa: "Yã ƙirƙira shi ne."Ka ce: "Sai ku zo da sũrõri gõma misãlinsa
ƙirƙirarru, kuma ku kirãyi wanda kuke iyãwa, baicin Allah, idan kun kasance mãsu
gaskiya."
To, idan ba su amsa muku ba, to, ku sani cẽwa an saukar da shi kawai ne da sanin
Allah, kuma cẽwa bãbu abin bauta wa fãce Shi. To, shin, kũ mãsu sallamãwa ne?,
Waɗannan ne waɗanda bã su da kõme a cikin Lãhira fãce wuta, kuma abin da suka
sanã'anta a cikinta (dũniya) yã ɓãci, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa
ɓãtacce ne.
Shin, wanda ya kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijinsa, kuma wata shaida
tanã biyar sa daga gare Shi, kuma a gabãninsa akwai littãfin Mũsãabin kõyi da
rahama? Waɗannan sunã yin ĩmãni da shi, kuma wanda ya kãfirta da shi daga
ƙungiyõyi, to, wutã ce makõmarsa. Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka
daga gare shi. Lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka, amma kuma mafi yawan
mutãne bã su yin ĩmãni.
Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah? Waɗannan anã
gitta su ga Ubangijinsu, kuma mãsu shaida su ce: "Waɗannan ne suka yi ƙarya ga
Ubangijinsu. To, la'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai."
Waɗannan ne ba su kasance mabuwãya ba a cikin ƙasa, kuma waɗansu masõya ba su
kasance ba a gare su, baicin Allah. Anã ninka musu azãba, ba su kasance sunã iya
ji ba, kuma ba su kasance sunã gani ba.
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi
tawãlu'i zuwa ga Ubangijinsu, waɗannan ne abõkan Aljanna, sunã madawwama a
cikinta.
Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta, daga mutãnensa, suka ce: "Bã mu ganin ka
fãce mutum kake kamarmu, kuma ba mu ganin wani ya bĩ ka fãce waɗanda suke sũ
ƙasƙantattunmu ne marasa tunani. Kuma bã mu ganin wata falalã agare ka a kanmu.
Ã'a, Munã zaton ku maƙaryata ne."
Ya ce: "Ya mutãnena! Shin, kun gani idan na kasance a kan wata hujja bayyananna
daga Ubangijina, kuma Yã bã ni wata Rahama daga wurinSa, Sa'an nan aka rufe ta
(ita Rahamar) daga gare ku, shin, zã mu tĩlasta mukuita, alhãli kuwa kũ mãsu ƙi
gare ta ne?
"Kuma yã mutãnena! Bã zan tambaye ku wata dũkiya ba akansa, ijãrata ba ta zama
ba, fãce daga Allah, kuma ban zama mai kõrar waɗanda suka yĩ ĩmãni ba. Haƙĩƙa
sũ, mãsu haɗuwa da Ubangijinsu ne, kuma amma ni, inã ganin ku mutãne ne
jãhilai."
"Kuma bã ni ce muku a wurĩna taskõkin Allah suke kuma bã inã sanin gaibi ba ne.
Kuma ba inã cẽwa ni Malã'ika ba ne. Kuma ba ni cẽwa ga waɗanda idãnunku suke
wulãkantãwa, Allah bã zai bã su alhẽri ba. Allah ne Mafi sani ga abin da yake
cikin zukatansu. Lalle ne ni, idan (nã yi haka) dã ina daga cikin azzalumai."
Suka ce: "Yã Nũhu, lalle ne kã yi jayayya da mu, sa'an nan kã yawaita yi mana
jidãli, to, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi idan kã kasance daga mãsu
gaskiya."
"Kuma nasĩhãta bã zã ta amfãne ku ba, idan nã yi nufin in yi muku nasĩha, idan
Allah Yakasance Yanã nufin Ya halaka ku. Shĩ ne Ubangijinku, kuma zuwa gare Shi
ake mayar da ku."
Ko sunã cẽwa: (Nũhu) ya ƙirƙira shi. Ka ce: "Idan nĩ (Nũhu) na ƙirƙira shi to,
laifĩnã a kaina yake, kuma nĩ mai barrantã ne daga abin da kuke yi na laifi."
Kuma aka yi wahayi zuwa ga Nũhu cẽwa: Lalle ne bãbu mai yin ĩmãni daga mutãnenka
fãce wanda ya riga ya yi ĩmãnin, sabõdahaka kada ka yi baƙin ciki da abin da
suka kasance sunã aikatãwa.
Kuma ka sassaƙa jirgi da kyau a kan idanunMu da wahayinMu, kuma kada ka yi Mini
magana a cikin sha'anin waɗanda suka kãfirta, lalle ne sũ, waɗanda akenutsarwa
ne.
Kuma Yanã sassaƙa jirgin cikin natsuwa, kuma a kõ yaushe waɗansu shugabanni daga
mutãnensa suka shũɗe a gabansa, sai su yi izgili gare shi. Ya ce: "Idan kun yi
izgili gare mu, to, haƙĩƙa mũ mã zã mu yi izgili gare ku, kamar yadda kuke yin
izgili.
Har a lõkacin da umurninMu ya je, kuma tandã ta ɓulɓula. Muka ce: "Ka ɗauka, a
cikinta, daga kõme, ma'aura biyu, da kuma iyalanka, fãce wanda magana ta gabãta
a kansa, da wanda ya yi ĩmãni." Amma kuma bãbu waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi
fãce kaɗan."
Kuma ita tanã gudãna da su a cikin tãguwar ruwa kamai duwãtsu, sai Nũhu ya
kirãyi ɗansa alhãli, kuwa ya kasance can wuri mai nĩsa. "Yã ƙaramin ɗãnã! zo ka
hau tãre da mu, kuma kada ka kasance tãre da kãfirai!"
Ya ce: "Zan tattara zuwa ga wani dũtse ya tsare ni daga ruwan." (Nũhu) ya ce:
"Bãbu mai tsarẽwa a yau daga umurnin Allah fãce wanda Ya yi wa rahama." Sai
taguwar ruwa ta shãmakace a tsakãninsu, sai ya kasance daga waɗanda aka nutsar.
Kuma aka ce: "Yã ƙasa! Ki haɗiye ruwanki, kuma yã sama! Ki kãme."Kuma aka faƙar
da ruwan kuma aka hukunta al'amarin, kuma Jirgin ya daidaita a kan Jũdiyyi, kuma
aka ce: "Nĩsa ya tabbata ga mutãne azzãlumai."
Kuma Nũhu ya kira Ubangijinsa, sa'an nan ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne ɗãna na
daga iyãlĩna! Kuma haƙĩƙa wa'adinKa gaskiya ne, kuma Kai ne Mafi hukuncin mãsu
yin hukunci."
Ya ce: "Yã Nũhu! Lalle ne shi bã ya a ciki iyãlanka, lalle ne shĩ, aiki ne wanda
ba na ƙwarai ba, sabõda haka kada ka tambaye Ni abin da bã ka da ilmi a kansa.
Haƙĩƙa, Nĩ Inã yi maka gargaɗi kada ka kasance daga jãhilai."
Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, inã nẽman tsari gare Ka da in tambaye Ka
abin da bã ni da wani ilmi a kansa. Idan ba Ka gãfarta mini ba, kuma Ka yi mini
rahama, zan kasance daga mãsu hasãra."
Aka ce: "Ya Nũhu! Ka sauka da aminci da, a gare Mu da albarka a kanka, kuma
rahama ta tabbata a kan waɗansu al'ummõmi daga waɗanda suke tãre da kai. Da
waɗansu al'ummõmi da zã Mu jiyar da su dãɗi, sa'an nan kuma azãba mai raɗaɗi ta
shafe su daga gare Mu."
Waccan ƙissa tanã daga lãbãran gaibi, Munã yin wahayinsu zuwa gare ka
(Muhammadu). Ba ka kasance kanã sanin su ba, haka kuma mutãnenka ba su sani ba
daga gabãnin wannan. Sai ka yi haƙuri. Lalle ne ãƙiba tanã ga mãsu taƙawa,
Kuma zuwa ga Ãdãwa, (Mun aika) ɗan'uwansu Hũdu. Ya ce: "Yã kũ mutãnena! Ku bauta
wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Ba ku kasance ba fãce kunã mãsu
ƙirƙirãwa.
"Kuma, ya mutãnena! Ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare
Shi,zai saki sama a kanku, tanã mai yawan zubar da ruwa, kuma Ya ƙãra muku wani
ƙarfi ga ƙarfinku. Kuma kada ku jũya kunã mãsu laifi."
Suka ce: "Yã Hũdu! Ba ka zo mana da wata hujja bayyananna ba, kuma ba mu zama
mãsu barin abũbuwan bautawarmu ba dõmin maganarka, kuma ba mu zama mãsu yin
ĩmãni da kai ba."
"Bã mu cẽwa, sai dai kurum sashen abũbuwan bautawarmu ya sãme ka da cũtar
hauka." Yace: "Lalle ne nĩ, inã shaida waAllah, kuma ku yi shaidar cẽwa" lalle
ne nĩ mai barranta ne dagb abin da kuke yin shirki da shi."
"Haƙĩƙa, ni na dõgara ga Allah, Ubangijĩna kuma Ubangijinku. Bãbu wata dabba
fãce Shi ne Mai riko ga kwarkwaɗarta. Haƙĩƙa, Ubangijĩna Yanã (kan) tafarki
madaidaici."
"To! Idan kun jũya, haƙĩƙa, nã iyar muku abin da aka aiko ni da shi zuwa gare
ku. Kuma Ubangijĩna Yanã musanya waɗansu mutãne, waɗansunku su maye muku. Kuma
bã ku cũtar Sa da kõme. Lalle Ubangijina a kan dukkan kõme, Matsari ne."
Kuma a lõkacin da umurninmu ya je, Muka kuɓutar da Hũdu da waɗanda suka yi ĩmãni
tãre da shi, sabõdawata rahama daga gare Mu. Kuma Muka kuɓutr da su daga azãba
mai kauri.
Kuma an biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. To! Lalle ne
Ãdãwa sun kãfirta da Ubangijinsu. To, Nĩsa ya tabbata ga Ãdãwa, mutãnen Hũdu!
Kuma zuwa ga Samũdãwa (an aika) ɗan'uwansu Sãlihu. Ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta
wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Shĩ ne Ya ƙãga halittarku daga
ƙasa, kuma Ya sanya ku mãsu yin kyarkyara a cikinta. Sai ku nẽme Shi gãfara,
sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi. Lalle Ubangijina Makusanci ne Mai
karɓãwa."
Suka ce: "Ya Sãlihu! Haƙĩƙa, kã kasance a cikinmu, wanda ake fatan wani alhẽri
da shi a gabãnin wannan. Shin kana hana mu bauta wa abin da ubanninmu suke bauta
wa? Kuma haƙĩƙa mũ, munã cikin shakka daga abin da kake kiran mu gare shi, mai
sanya kõkanto."
Ya ce: "Ya mutãnẽna! Kun gani? Idan na kasance a kan hujja bayyananna daga
Ubangijina, kuma Ya bã ni rahama daga gare Shi, to, wane ne zai taimake ni daga
Allah idan nã sãɓa Masa? Sa'an nan bã zã ku ƙãre ni da kõme ba fãce hasãra."
"Kuma ya mutãnena! wannan rãƙumar Allah ce, tanã ãyã a gare ku. Sai ku bar ta ta
ci a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta kar azãba makusanciya
ta kãma ku."
To, a lõkacin da umurninMu ya je, muka kuɓutar da Sãlihu da waɗanda suka yi
ĩmãni tãre da shi, sabõda wata rahama daga gare Mu, kuma daga wulãkancin rãnar
nan. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMai ƙarfi, Mabuwãyi.
Kuma haƙĩƙa, manzanninMu sun je wa Ibrãhim da bushãra suka ce: "Aminci." Ya ce:
"Aminci (ya tabbata a gare ku)." Sa'an nan bai yi jinkiri ba ya je da maraƙi
ƙawãtacce.
Sa'an nan a lõkacin da ya ga hannayensu bã su sãduwa zuwa gare shi (maraƙin),
sai ya yi ƙyãmarsu, kuma ya ji tsõronsu. Suka ce, "Kada kaji tsõro lalle ne mũ,
an aiko mu ne zuwa ga mutãnen Lũɗu"
Suka ce: "Shin kinã mãmaki ne daga al'amarin Allah? Rahamar Allah da albarkarSa
su tabbata a kanku, ya mutãnen babban gida! Lalle ne Shĩ abin gõdewa ne, Mai
girma."
Ya Ibrãhĩm! Ka bijira daga wannan. Lalle shi, haƙĩƙa, umurnin Ubangijinka ne ya
zo, kuma lalle ne sũ, abin da yake mai je musu azãba ce wadda bã a iya hanãwa.
Kuma mutãnensa suka je masa sunã gaggãwa zuwa gare shi, kuma a gabãni, sun
kasance sunã aikatãwar mũnãnan ayyuka. Ya ce: "Yã mutãnẽna! waɗannan, 'yã'yã na
sũ ne mafiya tsarki a gare ku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku wulãkantã
ni a cikin bãƙĩna. Shin, bãbu wani namiji shiryayye daga gare ku?"