Yanã sassaukar da malã'iku da Rũhi daga umurninSaa kan wanda Yake so daga
bãyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni,
sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa.
Kuma sunã ɗaukar kãyanku mãsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance mãsu isa
gare shi ba, fãce da tsananin wahalar rãyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa,
Mai tausayi, Maijin ƙai.
Yanã tsirar da shũka game da shi, dõminku zaitũni da dabĩnai da inabai, kuma
daga dukan 'yã'yan itãce. Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne
waɗanda suke yin tunãni.
Kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni da rãnã da watã kuma taurãri hõrarru ne da
umurninSa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke
hankalta.
Kuma Shĩ ne Ya hõrẽ tẽku dõmin ku ci wani nama sãbõ daga gare shi, kuma kunã
fitarwa, daga gare shi, ƙawã wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirãge
sunã yankan ruwa a cikinsa kuma dõmin ku yi nẽman (fatauci) daga falalarSa. Kuma
mai yiwuwa ne kuna gõdẽwa.
Dõmin su ɗauki zunubansu cikakku a Rãnar ¡iyãma, kuma daga zunuban waɗanda suke
ɓatarwa bã da wani ilmi ba. To, abin da suke ɗauka na zunubi ya mũnana.
Lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci, sai Allah Ya je wa gininsu
daga harsãshensa, sai rufi ya fãɗa a kansu daga bisansu, kuma azãba ta jẽ musu
daga inda ba su sani ba.
Sa'an nan a Rãnar ¡iyãma (Allah) Yanã kunyatã su, kuma Yanã cẽwa: "Inã abõkan
tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã gãbã a cikin ɗaukaka sha'aninsu?" Waɗanda
aka bai wa ilmi suka ce: "Lalle ne wulãkanci a yau da cũta sun tabbata a kan
kãfirai."
Kuma aka ce wa waɗanda suka yi taƙawa, "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Suka ce,
"Alhẽri Ya saukar, ga waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya akwai wani abu
mai kyau, kuma haƙĩƙa, Lãhira ce mafi alhẽri." Kuma haƙĩƙa, mãdalla da gidan
mãsu taƙawa.
Waɗanda malã'iku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu jin dãɗin rai, malã'ikun sunã
cẽwa. "Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna sabõda abin da kuka kasance
kuna aikatãwa."
Shin sunã jiran wani abu? Fãce malã'iku su jẽ musu kõ kuwa umurnin Ubangijinka.
Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu, suka aikata. Kuma Allah bai zãlunce su
ba, kuma amma kansu suka kasance sunã zãlunta.
Kuma waɗanda suka yi shirki suka ce: "Dã Allah Yã so, dã bamu bautã wa kõme ba,
baicinSa, mũ ko ubannimmu kuma dã ba mu haramta kõme ba, baicin abin da Ya
haramta." Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka aikata. To, shin, akwai
wani abu a kan Manzanni, fãce iyarwa bayyananniyã?
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce):
"Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ¦ãgũtu." To, daga gare su akwai wanda Allah
Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda ɓata ta wajaba a kansa. Sai ku yi
tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance.
Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu (cẽwa) Allah bã ya tãyar da wanda
yake mutuwa! Na'am, Yanã tãyarwa. Wa'adi ne (Allah) Ya yi a kanSa tabbatacce,
kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin sha'anin Allah daga bãyan an zãlunce su,
haƙĩƙa Munã zaunar da su a cikin dũniya da alhẽri kuma lalle lãdar Lãhira ce
mafi girmã, dã sun kasance sunã sani.
Da hujjõji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka,
dõmin ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don
ɗammãninsu su yi tunãni.
Shin fa, waɗanda suka yi mãkircin mũnãnan ayyuka sun amince da Allah, bã zai
shafe ƙasa da su ba ko kuwa azãba bã zã ta je musu daga inda ba su sani ba?
Shin, ba su Iura ba da abin da Allah Ya halitta kõ mene ne inuwõyinsu suna
karkata daga dãma da wajãjen hagu, suna masu sujada ga Allah, alhãli suna masu
ƙasƙantar da kai?
Kuma sunã sanya rabõ ga abin da ba su sani ba daga abin da Muka azurtã su.
Ranstuwa da Allah! Lalle ne zã a tambaye ku daga abin da kuka kasance kunã
ƙirƙirãwa.
Yanã ɓõyẽwa daga mutãne dõmin mũnin abin da aka yimasa bushãra da shi. Shin, zai
riƙe shi a kan wulãkanci kõ zai turbuɗe shi a cikin turɓãya To, abin da suke
hukuntãwa ya mũnana.
Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne da zãluncinsu, dã bai bar wata dabba ba a kan
ƙasa. Kuma amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajali ambatacce. Sa'an nan idan
ajalinsu ya zo, bã zã a yi musu jinkiri ba kõ da sa'a guda, kuma bã zã su gabãta
ba.
Kuma sunã sanyã wa Allah abin da suke ƙi, kuma harsunansu na siffanta ƙarya cẽwa
lalle ne sunã da abũbuwa mãsu kyau. Bãbu shakka lalle ne sunã da wuta, kuma
lalle sũ, waɗanda ake ƙyãlẽwa ne (a cikinta) .
Rantsuwar Allah! Lalle ne haƙĩƙa Mun aika zuwa ga al'ummomi daga gabãninka, sai
Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka shĩ ne majiɓincinsu, a yau, kuma
sunã da azãba mai raɗaɗi.
Lalle ba Mu saukar da Littafi ba a kanka, fãce dõmin ka bayyanã musu abin da
suka sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke
yin ĩmãni.
Kuma Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa da shi a
bãyan mutuwarta. Lalle ne a cikin wannan haƙĩƙa akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke
saurãre.
Kuma lalle ne, kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'ima;Munã shãyar da ku daga
abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakãnin tukar tumbi da jini nõno tsantsan
mai sauƙin haɗiya ga mãsu shã.
Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye da
abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke
hankalta.
"Sa'an nan ki ci daga dukan 'ya'yan itãce, sabõda haka ki shiga hanyõyin
Ubangijinka, sunã hõrarru." Wani abin shã yanã fita daga cikunanta, mai sãɓãwar
launukansa a cikinsa akwai wata warkewa ga mutãne. Lalle ne, a cikin wannan,
haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.
Kuma Allah ne Ya halicce ku, sa'an nan Yanã karɓar rãyukanku, kuma daga gare ku
akwai wanda ake mayarwã zuwa ga mafi ƙasƙncin rãyuwa, dõmin kada ya san kõme a
bãyan dã ya zama mai ilmi. Lalle Allah ne Masani Mai ĩkon yi.
Kuma Allah Ya fifita sãshenku a kan sãshe a arziki. Sa'an nan waɗanda aka fĩfĩta
ba su zama mãsu mayar da arzikinsu a kan abin da hannãyensu na dãma suka mallaka
ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni'imar Allah suke musu?
Kuma Allah Yã sanya muku mãtan aure daga kãwunanku, kuma Ya sanya muku daga
mãtan aurenku ɗiyã da jĩkõki, kuma Ya arzũta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Shin fa,
da ƙarya suke yin ĩmãni, kuma da ni'imar Allah sũ, suke kãfirta?
Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da yake bã ya mallakar wani arziki
dõminsu, daga sammai da ƙasa game da kõme, kuma bã su iyawa (ga aikata kõme) .
Allah Yã buga wani misali da wani bãwa wanda bã ya iya sãmun ĩko a kan yin kõme,
da (wani bãwa) wanda Muka azurtã shi daga gare Mu da arziki mai kyau. Sa'an nan
shĩ yanã ciyarwa daga arzikin, a asirce da bayyane. Shin sunã daidaita? Gõdiya
ta tabbata ga Allah. Ã'a mafi yawansu ba su sani ba.
Kuma Allah Ya buga wani misãli, maza biyu, ɗayansu bẽbe ne, ba ya iya sãmun ikon
yin kõme, kuma shi nauyi ne a kan mai mallakarsa, inda duk ya fuskantar da shi,
bã ya zuwa da wani alhẽri. Shin, yanã daidaita, shi da (namiji na biyu) wanda
yake umurni da a yi ãdalci kuma yanã a kan tafarki madaidaici?
Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake, kuma al'amarin Sã'a bai zama ba fãce
kamar walƙãwar gani, kõ kuwa shĩ ne mafi kusa! Lalle Allah a kan dukan kõme Mai
ikon yi ne.
Shin ba su ga tsuntsãye ba sunã hõrarru cikin sararin sama bãbu abin da yake
riƙe su fãce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne
waɗanda suke yin ĩmãni.
Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku
daga fatun dabbõbin ni'ima wasu gidãje kunã ɗaukar su da sauƙi a rãnar tafiyarku
da rãnar zamanku, kuma daga sũfinsu da gãshinsu da gẽzarsu (Allah) Ya sanya muku
kãyan ɗãki da na jin dãɗi zuwa ga wani lõƙaci.
Kuma Allah ne Ya sanyã muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanyã muku
ɗãkuna daga duwãtsu, kuma Ya sanyã muku waɗansu riguna sunã tsare muku zãfi, da
waɗansu rĩguna sunã tsare muku makãminku. Kamar wancan ne (Allah) Yake cika
ni'imarSa a kanku, tsammãnin ku, kuna sallamawa.
Kuma a rãnar da Muke tãyar da mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan kuma bã
zã a yi izni ba ga waɗanda suka kãfirta, kuma ba su zama ana nẽman kõmawarsu ba.
Kuma idan waɗanda suka yi shirka suka ga abũbuwan shirkarsu sai su ce: "Yã
Ubangijinmu! Waɗannan ne abũbuwanshirkarmu waɗanda muka kasance munã kira
baicinKa". Sai su jẽfamagana zuwa gare su, "Lalle ne ku, haƙĩƙa, maƙaryata ne."
Kuma a rãnar da Muke tãyar da shaidu a cikin kõwace al'umma a kansu daga
kãwunansu, kuma Muka zo da kai kanã mai bãyar da shaida a kan waɗannan, kuma Mun
saussaukar da Littãli a kanka dõmin yin bãyani ga dukkan kõme da shiriya da
rahama da bushãra ga mãsu mĩƙa wuya (Musulmi).
Lalle Allah nã yin umurni da ãdalci da kyautatãwa, da bai wa ma'abũcin zumunta,
kuma yanã hani ga alfãsha da abin da aka ƙi da rarrabe jama'a. Yanã yi muku
gargaɗi, ɗammãnin ku, kunã tunãwa.
Kuma ku cika da alkãwarin Allah idan kun yi alkawari, kuma kada ku warware
rantsuwõyinku a bãyan ƙarfafa su, alhãli kuma haƙĩƙa kun sanya Allah Mai
lãmuncẽwa a kanku. Kuma lalle Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatãwa.
Kuma kada ku kasance kamar wadda ta warware zarenta a bãyan tukka, ya zama
warwararku, kunã riƙon rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, dõmin
kasancẽwar wata al'umma tãfi rĩba daga wata al'umma! Abin sani kawai Allah Yanã
jarrabar ku da shi, kuma lalle ne yanã bayyana muku a Rãnar ¡iyãma, abin da kuka
kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wajũna.
Kuma dã Allah Ya so, haƙĩ ƙa, dã Ya sanya ku al'umma gudã, kuma Yanã ɓatar da
wanda Ya so. kuma Yanã shiryar da wanda Ya so. Lalle ne anã tambayarku abin da
kuka kasance kunã aikatãwa.
Kada ku riƙi rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, har ƙafa ta yi sulɓi a
bãyan tabbatarta, kuma ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kange daga hanyar
Allah. Kuma kunã da wata azãba mai girma.
Abin da yake a wurinku yanã ƙãrẽwa, kuma abin da yake a wurin Allah ne mai
wanzuwã. Kuma lalle ne, Munã sãka wa waɗanda suka yi haƙuri da lãdarsu da mafi
kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to,
haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da
mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Kuma idan Muka musanya wata ãyã a matsayin wata ãyã, kuma Allah ne Mafi sani ga
abin da Yake saukarwa sai su ce: "Abin sani kawai, kai, aƙirƙiri ne." Ã'a, mafi
yawansu bã swa sani.
Ka ce: "Rũhul ¡udusi ne ya sassaukar da shi, daga Ubangijinka da gaskiya, dõmin
ya tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma(dõmin) shiriya da bushãra ga
Musulmi."
Wanda ya kãfirta da Allah daga bãyan ĩmãninsa, fãce wanda aka tĩlasta alhãli
kuwa zũciyarsa tanã natse da ĩmãni kuma wanda ya yi farin ciki da kãfirci, to,
akwai fushi a kansa daga Allah, kuma sunã da wata azãba mai girma.
Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka yi hijirã daga bãyan an
fitine su, sa'an nan kuma suka yi jihãdi, kuma suka yi haƙuri, lalle ne
Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
A rãnar da kõwane rai zai je yanã jãyayyar tunkuɗẽwa daga kansa, kuma a cika wa
kõwane rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma sũ bã zã a zãlunce su ba.
Kuma Allah Ya buga misãli, wata alƙarya ta kasance amintacciyã, natsattsiyã,
arzikinta yanã je mata a wadãce daga kõwane wuri sai ta kãfirta da ni'imõmin
Allah, sabõda haka Allah ya ɗanɗana mata tufãfin yunwa da tsõro, sabõda abin da
suka kasance sunã sanã'antãwa.
Abin sani kawai (Allah) Ya haramta muku mussai da jini da nãman alade da abin da
aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan
jama'a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
Kuma kada ku ce, dõmin abin da harsunanku suke siffantawa da ƙarya, "Wannan
halas ne, kuma wannan harãmun ne." Dõmin ku ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne,
waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah bã zã su ci nasara ba.
Kuma kan waɗanda suka tũba (Yãhũdu) Mun haramta abin da Muka bãyar da lãbari a
gare ka daga gabãni, kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun kasance kansu suke
zãlunta.
Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki da
jãhilci, sa'an nan suka tũba daga bãyan wancan, kuma suka gyãra, lalle ne
Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.