Madaidaici, dõmin Ya yi gargaɗi da azãba mai tsanani daga gare shi, kuma Ya yi
bushãra ga mũminai, waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai da (cẽwa) sunã da wata
lãdã mai kyau.
Ba su da wani ilmi game da wannan magana, kuma iyãyensu bã su da shi, abin da ke
fita daga bãkunansu ya girma ga ya zama kalmar faɗa! Ba su faɗan kõme fãce
ƙarya.
A lõkacin da samarin suka tattara zuwa ga kõgon, sai suka ce: "Ya Ubangijinmu!
Ka bã mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana (sãmun) shiriya daga
al'amarinmu."
Kuma Muka ɗaure a kan zukãtansu, a lõkacin da suka tsayu, sa'an nan suka ce:
"Ubangijinmu Shĩ ne Ubangijin sammai daƙasa. Bã zã mu kirãyi waninSa abin
bautawa ba. (Idan mun yi haka) lalle ne, haƙĩƙa, mun faɗi abin da ya ƙẽtare
haddi a sa'an nan."
"Ga waɗannan mutãnenmu sun riƙi waninSa abin bautãwa! Don me bã su zuwa da wata
hujja bayyananna a kansu (waɗanda ake bautawar) ? To, wãne ne mafi zãlunci daga
wanda ya ƙãga ƙarya ga Allah?"
"Kuma idan kun nĩsance su sũ da abin da suke bautãwa,fãce Allah, to, ku tattara
zuwa ga kõgon sai Ubangijinku Ya watsa muku daga rahamarSa kuma Ya sauƙaƙe muku
madõgara daga al'amarinku."
Kuma kanã ganin rãnã idan ta fito tanã karkata daga kõgonsu wajen dãma kuma idan
ta fãɗi tanã gurgura su wajen hagu, kuma su, sunã a cikin wani fili daga gare
shi. Wannan abu yanã daga ãyõyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar, to shĩ ne mai
shiryuwa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmar masa wani majiɓinci mai
shiryarwa ba.
Kuma kanã zaton su farkakku ne, alhãli kuwa sũ mãsu barci ne. Munã jũya su wajen
dãma da wajen hagu, kuma karensu yanã shimfiɗe da zirã'õ'in ƙafãfuwansa ga
farfãjiya (ta kõgon). Dã ka lẽka (a kan) su (dã) lalle ne, ka jũya daga gare su
a guje kuma (dã) lalle ne ka cika da tsõro daga gare su.
Kuma kamar wannan ne Muka tãyar da su, dõmin su tambayi jũna a tsakãninsu. Wani
mai magana daga cikinsu ya ce: "Mẽne ne lõkacin da kuka zauna?" suka ce: "Mun
zauna yini ɗaya ko sãshen yini." Suka ce: "Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da
kuka zauna. To, ku aika da ɗayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin.
Sai ya dũba wanne ne mafi tsarki ga abin dafãwa, sai ya zo muku da abinci daga
gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum."
Kuma kamar wancan ne, Muka nũna su (gare su) dõmin su san lalle wa'adin Allah
gaskiya ne, kuma lalle ne Sa'a bãbu shakka a cikinta. A lõkacin da suke jãyayyar
al'amarinsu a tsakãninsu sai suka ce: "Ku gina wani gini a kansu, Ubangijinsu ne
Mafi sani game da su." Waɗanda suka rinjãya a kan al'amarinsu suka ce: "Lalle mu
riƙi masãllãci a kansu."
Zã su ce: "Uku ne da na huɗunsu karensu."Kuma sunã cẽwa, "Biyar ne da na
shidansu karensu," a kan jĩfa a cikin duhu. Kuma sunã cẽwa, "Bakwaine da na
takwas ɗinsu karensu."Ka ce: "Ubangijĩna ne Mafi saniga ƙidãyarsu, bãbu wanda ya
san su fãce kaɗan."Kada ka yi jãyayya bayyananna. Kuma kada ka yi fatawa ga kõwa
daga gare su a cikin al'amarinsu.
Fãce idan Allah Ya so. Kuma ka ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce:
"¦ammãni ga Ubangijĩna, Ya shiryar da ni ga abin da yake shi ne mafi kusa ga
wannan na shiriya."
Ka ce: "Allah ne Mafi sani ga abin da suka zauna. Shĩ ne da (sanin) gaibin
sammai da ƙasa. Mũne ne ya yi ganinSa da jinSa! Bã su da wani majiɓinci baicinSa
kuma bã Ya tãrayya da kõwa a cikin hukuncinsa."
Ka karanta abin da aka yi wahayi zuwa gare ka, na littãfin Ubangijinka. Bãbu mai
musanyãwa ga kalmõminSa kuma bã zã kã sãmi wata madõgara ba daga waninsa.
Ka haƙurtar da ranka tãre da waɗanda ke kiran Ubangijinsu, sãfe da maraice, sunã
nufin yardarSa. Kuma kada idãnunka su jũya daga barinsu, kanã nufin ƙawar
rãyuwar dũniya. Kuma kada ka biwanda Muka shagaltar da zũciyarsa daga
hukuncinMu, kuma ya bi son zuciyarsa, alhãli kuwa al'amarinsa ya kasance yin
ɓarna.
Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." Sabõda haka wanda ya so, to, ya yi
ĩmãni, kuma wanda ya so, to, ya kãfirta. Lalle ne Mũ, Mun yi tattali dõmin
azzãlumai wata wuta wadda shãmakunta, sun ƙẽwaye da su. Kuma idan sun nẽmi
taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yanã sõye fuskõki. Tir
da abin shansu, kuma wutar ta yi mũnin zama mahũtarsu.
Waɗannan sunã da gidãjen Aljannar zama, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, anã
sanya musu ƙawa, a cikinsu, daga mundãye na zinariya, kuma sunã tufantar waɗansu
tũfãfi kõre, na alharĩni raƙĩƙi da alharini mai kauri sunã kishingiɗe a
cikinsu,a kan, karagu. Mãdalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama
wurin hutãwa.
Kuma ka buga musu misãli da waɗansu maza biyu. Mun sanya wa ɗayansu gõnaki biyu
na inabõbi, kuma Muka kẽwayesu da itãcen dabĩnai, kuma Muka sanya shũka a
tsakãninsu (sũ gõnakin).
Kuma ɗan ĩtãce ya kasance gare shi. Sai ya ce wa abõkinsa, alhali kuwa yanã
muhãwara da shi, "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare ka a wajen dũkiya, kuma mafi izza a
wajen jama'a."
"Kuma bã ni zaton sa'a mai tsayuwa ce, kuma lalle ne, idan an mayar da ni zuwa
ga Ubangijiĩna, to, lalle ne, zan sãmi abin da yake mafi alhẽri daga gare ta ya
zama makõma."
Abõkinsa ya ce masa, alhãli kuwa yanã muhãwara da shi, "Ashe kã kãfirta da wanda
Ya halitta ka daga turɓaya, sa'an nan daga ɗigon maniyi, sa,an nan Ya daidaita
ka, ka zama mutum?"
"Kuma don me, a lõkacin da ka shiga gõnarka, ka, ce, 'Abin da Allah ya so (shi
ke tabbata) bãbu wani ƙarfi fãce game da Allah.' Idan ka gan ni, ni ne mafi
ƙaranci daga gare ka a wajen dũkiya da ɗiya."
"To, akwai fãtan Ubangijĩna Ya ba ni abin da yake mafi alhẽri daga gõnarka, kuma
ya aika azãba a kanta (ita gõnarka) daga sama, sai ta wãyi gari turɓãya mai
santsi."
Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itãcensa, sai ya wãyi gari yanã jũyar da tãfunansa
biyu, sabõda abin da ya kashe a cikinta, alhãli kuwa ita tanã kwance a kan
rassanta, kuma yanã cẽwa, "Kaitõna, dã dai ban tãra wani da Ubangijina ba!"
Ka buga musu misãlin rãyuwar dũniya, kamar ruwane wanda Muka saukar da shi daga
sama sa'an nan tsirin ƙasa ya garwaya da shi, sa'an nan ya wãyi gari dudduga,
iska tanã shiƙar sa. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan ĩkon yi ne a kan dukan
kõme.
Dũkiya da ɗiya, sũ ne ƙawar rãyuwar dũniya, kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai
sun fi zama alhẽri a wurin Ubangijinka ga lãda kuma sun fi alhẽri ga bũri.
Kuma a gittã su ga Ubangijinka sunã sahu guda, (Mu ce musu), "Lalle ne haƙĩƙa
kun zo Mana, kamar yadda Muka halitta ku a farkon lõkaci. Ã'a, kun riya cẽwa bã
zã Mu sanya mukuwani lõkacin haɗuwa ba."
Kuma aka aza littãfin ayyuka, sai ka ga mãsu laifi sunã mãsu jin tsõro daga abin
da ke cikinsa, kuma sunã cẽwa "Kaitonmu! Mẽne ne ga wannan littãfi, bã ya barin
ƙarama, kuma bã ya barin babba, fãce yã ƙididdige ta?" Kuma suka sãmi abin da
suka aikata halarce. Kuma Ubangijinka bã Ya zãluntar kõwa.
Kuma a lõkacin da Muka ce wa malãiku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi
sujada fãce Iblĩsa, yã kasance daga aljannu sai ya yi fãsiƙanci ga barin umurnin
Ubangijinsa, To fa, ashe, kunã riƙon sa, shi da zũriyarsa, su zama majiɓinta
baicin Ni, alhãli kuwa su maƙiya ne a gare ku? Tir da ya zama musanya ga
azzãlumai.
Ban shaida musu halittar sammai da ƙasa ba, kuma ban (shaida musu) halittar
rãyukansu ba kuma ban kasance mai riƙon mãsu ɓatarwa (da wani) su zama mataimaka
ba.
Kuma da rãnar da Allah Yake cẽwa, "Ku kirãyi abõkan tarayyãTa, waɗanda kuka
riya." Sai su kirãye su, sai bã zã su karɓa musu ba, kuma Mu sanya Maubiƙa
(Mahalaka) a tsakãninsu,
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun jujjũya, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane irin
misãli ga mutãne (dõmin su gãne, su bi sharĩ'a), kuma mutum yã kasance mafi
yawan abu ga jidãli.
Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni a lõkacinda shiriya ta zo musu,
kuma su nẽmi gãfara daga Ubangijinsu, fãce hanyar farko ta je musu kõ kuma azãba
ta jẽ musu nau'i-nau'i.
Kuma ba Mu aika Manzanni ba fãce sunã mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi,
kuma waɗanda suka kãfirta sunã jidãli da ƙarya dõmin su ɓãta gaskiya da ita,
kuma suka riƙi ãyõyiNa da abin da aka yi musu gargaɗi da shi abin izgili.
Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda aka tunãtar game da ãyõyin Ubangijinsa, sai
ya bijire daga barinsu, kuma ya manta abin da hannãyensa suka gabãtar? Lalle ne
Mũ, Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi, kuma a
cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi, kuma idan kã kĩrayẽ su zuwa ga shiriya,
to, bã zã su shiryu ba, a sa'an nan, har abada.
Kuma Ubangijinka Mai gãfara ne, Ma'abũcin rahama. Dã Yanã kãma su sabõda abin da
suka sanã'anta, lalle ne, dã Ya gaggauta azãba a gare su. Ã'a, sunã da lõkacin
alkawari,(wanda) bã zã su sãmi wata makõma ba, baicinSa.
(Yãron) ya ce: "Kã gani! A lõkacin da muka tattara zuwa ga falalen nan to, lalle
nĩ, na manta kĩfin, kuma bãbu abin da yamantar da nĩ shi, fãce Shaiɗan,dõmin
kada in tuna shi, sai ya kama tafarkinsa a cikin tẽku, da mãmãki!"
Sai suka tafi har a lõkacin da suka hau a cikin jirgi, ya hũje shi, ya ce, "Kã
hũje shi dõmin ya nutsar da mutãnensa? Lalle ne, haƙĩƙa,kã zo da wani babban
abu!"
Sai suka tafi, har suka haɗu da wani yãro, sai ya kashe shi. Ya ce: "Ashe kã
kashe rai tsarkakakke, bã da wani rai ba? Lalle ne haƙĩƙa ka zo da wani abu na
ƙyãma."
Sai suka tafi, har a lõkacin da suka je wa mutãnen wata alƙarya, suka nẽmi
mutãnenta da su bã su abinci, sai suka ƙi su yi musu liyãfa. Sai suka sãmi wani
bango a cikinta yanã nufin ya karye, sai (Halliru) ya tãyar da shi mĩƙe. (Mũsã)
ya ce: "Dã kã so, lalle ne dã kã karɓi ijãra a kansa."
"Amma Jirgin, to, ya zama na waɗansu matalauta ne sunã aiki a cikin tẽku, sai na
yi niyyar in aibanta shi, alhãli kuwa wani sarki ya kasance a gaba gare su, yanã
karɓẽwar kõwane jirgi (lãfiyayye) da ƙwãce.