A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, "Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na
tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in
sãmi wata shiriya a kan wutar."
"Cẽwa, Ki jẽfa shi a cikin akwatin nan, sa'an nan ki jẽfa shi a cikin kõgi,
sa'an nan kogin ya jefa shi a gãɓa, wani maƙiyi Nãwa kuma maƙiyi nãsa ya ɗauke
shi.' Kuma Na jẽfa wani so daga gare Ni a kanka. Kuma dõmin a riƙe ka da kyau a
kan ganiNa."
"A sa'ad da 'yar'uwrka ke tafiya har ta ce, shin, in shiryar da ku ga wanda ke
rẽnonsa?' Sai Muka mayar da kai zuwa ga uwarka dõmin idonta ya yi sanyi kuma bã
zã ta yi baƙin ciki ba. Kuma kã kashe wani rai, sa'an nan Muka tsẽrar da kai
daga baƙin ciki, kuma Muka fitine ka da waɗansu fitinõni. Sa'an nan ka zauna
shẽkaru a cikin mutãnen Madyana. Sa'an nan kuma ka zo a kan wata ƙaddara, yã
Mũsã!
"Sai ku jẽ masa sa'an nan ku ce, Lalle mũ, Manzanni biyune na Ubangijinka, sai
ka saki Banĩ Isrã'ĩla tãre da mu. Kuma kada ka yi musu azãba. Haƙĩƙa mun zomaka
da wata ãyã daga, Ubangijinka. Kuma aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya."
"Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyõyi a cikinta,
kuma Ya saukar da ruwa daga sama." Sa'an nan game da shi Muka fitar da
nau'i-nau'i daga tsirũruwa dabam-dabam.
"To, lalle ne munã zo maka da wani sihiri irinsa. Sai ka sanya wani wa'adi a
tsakãninmu da tsakãninka bã mu sãɓa masa mũ kai kuma, bã ka sãɓãwa, a wani wuri
mai dãcẽwa."
"Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata.
Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin
nasara a duk inda ya je."
Ya ce: "Kun yi ĩmãni sabõda shi a gabãnin in yi muku izni? Lalle shĩ, haƙĩƙa,
babbanku ne wanda ya sanar da ku sihirin! To, lalle ne zan kakkãtse hannayenku
da ƙafãfunku a tarnaƙi kuma lalle zan tsĩre ku a cikin kututturan itãcen dabĩno,
kuma lalle zã ku sani wanenmu ne mafi tsananin azãba kuma wãne ne mafi wanzuwar
(azãba)."
Suka ce: "Bã zã mu fĩfĩta ka ba faufau a kan abin da ya zo mana na hujjõji. Munã
rantsuwa da wanda Ya ƙãga halittarmu sai ka hukunta abin da kake mai hukuntãwa,
ai kanã ƙãre wannan rãyuwar dũniya kawai ne."
"Lalle mũ, mun yi ĩmãni da Ubangijinmu dõmin Ya gãfarta mana laifuffukanmu da
abin da ka tĩlasta mu a kansa na sihiri. Kuma Allah ne Mafi alhẽri, kumaMafi
wanzuwa."
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa, "Ka yi tafiyar dare da
bãyiNa. Sa'an nan ka dõka musu hanya a cikin tẽku tana ƙẽƙasasshiya, bã ka
tsõron riskuwa, kuma bã ka fargabar nutsẽwa."
Yã Banĩ Isrã'ĩla! Lalle Mun tsẽrar da ku daga maƙiyinku, kuma mun yi muku wa'adi
a gẽfen Dũtsen nan na dãma, kuma Mun sassaukar da darɓa da tattabaru dõminku.
Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurtã ku kuma kada ku ƙẽtare haddi a cikinsa
har hushĩNa ya sauka a kanku. Kuma wanda hushĩNa ya sauka a kansa, to, lalle ne,
ya fãɗi.