Sanã mãsu shagaltacin zukãtansu, kuma su asirta gãnãwa: Waɗanda suka yi zãlunce
(sunã cẽwa) "Wannan bã Kõwa ba ne fãce mutum misãlinku. Shin, to, kunã jẽ wa
sihiri, ahãli kuwa kũ, kunã fahimta?"
Kuma shĩ ne da mallakar wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma waɗanda suke
wurinSa (watau malã'iku), bã su yin girman kai ga ibãdarSa. kuma bã su gajiya.
Dã waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da ƙasa) fãce Allah,
haƙĩƙa dã su biyun sun ɓãci. Sabõda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin
Al'arshi daga abin da suke siffantãwa.
Kõ sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa baicinSa? Ka ce: "Ku kãwo hujjarku, wannan
shi ne ambaton wanda yake tãre da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabãnĩna.
Ã'a, mafi yawansubã su sanin gaskiya, sabõda haka sũ mãsu bijirẽwa ne."
Shin kuma waɗanda suka kãfirta ba, su gani da cẽwa lalle sammai da ƙasa sun
kasance ɗinke, sai Muka bũɗe su, kuma Muka sanya dukan kome mai rai daga ruwa?
Shin, bã zã su yi ĩmãni ba?
Kuma Mun sanya tabbatattun duwãtsu a cikin ƙasa dõmin kada ta karkata da su kuma
Mun sanya ranguna, hanyõyi, a cikinsu (duwãtsun), tsammãninsu sunã shiryuwa.
Kuma idan waɗanda suka kãfirta suka gan ka, bã su riƙon ka fãce da izgili (sunã
cẽwa), "Shin, wannan ne ke ambatar gumãkanku?" Alhãli kuwa sũ, ga ambatar Mai
rahama, mãsu kãfirta ne.
Dã waɗanda suka kãfirta sunã sanin lõkacin da bã su kange wuta daga fuskõkinsu,
kuma haka daga bãyayyakinsu, alhãli kuwa ba su zama ana taimakon su ba.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili ga waɗansu Manzanni daga gabãninka, sai abin
da suka kasance sunã izgili da shi ya auku ga waɗanda suka yi izgilin daga gare
su.
Ã'a, Mun yalwata wa waɗannan da ubanninsu ni'imarMu, har rãyuwa ta yi tsawo a
kansu. Shin, to, bã su ganin cẽwa lalle Mũ, Munã je wa ƙasarsu, Munã rage ta
daga sãsanninta? Shin, to, su ne marinjaya?
Kuma Munã aza ma'aunan ãdalci ga Rãnar ¡iyãma, sabõda haka ba a zãluntar rai da
kõme. Kuma kõ dã ya kasance nauyin ƙwãya daga kõmayya ne Mun zo da ita. Kuma Mun
isa zama Mãsu hisãbi.
Kuma Muka sanya su shugabanni, sunã shiryarwa da umurninMu. Kuma Muka yi wahayi
zuwa gare su da ayyukan alhẽri da tsayar da salla da bãyar da zakka. Kuma sun
kasance mãsu bauta gare Mu.
Kuma Lũɗu Mun bã shi hukunci da ilmi. Kuma Mun tsĩrar da shi daga alƙaryar nan
wadda ke aikata mũnãnan ayyuka. Lallesũ, sun kasance mutãnen mũgun aiki,
fãsiƙai.
Kuma Dãwũda da Sulaimãn sa'ad da suke yin hukunci a cikin sha'anin shũka a
lõkacin da tumãkin mutãne suka yi kiĩwon dare a cikinsa. Kuma Mun kasance Mãsu
halarta ga hukuncinsu.
Sai Muka fahimtar da ita (mats'alar) ga Sulaiman. Kuma dukansu Mun bã su hukunci
da ilmi kuma Muka hõre duwatsu tãre da Dãwũda, sunã tasbĩhi, da tsuntsãye. Kuma
Mun kasance Mãsu aikatãwa.
Kuma (Muka hõre) wa Sulaimãn iska mai tsananin bugãwa, tanã gudãna da umuruinsa
zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta. Kuma Mun kasance Masana ga
dukkan Kõme.