Kuma Mun yi wa mutum wasiyyar kyautatãwa ga uwayensa, kuma idan sun tsananta
maka dõmin ka yi shirki da Ni game da abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada
ka yi musu ɗã'ã. Zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbari ga abin
da kuka kasance kunã aikatãwa.
Kuma daga cikin mutãne akwai mai cẽwa, 'Mun yi ĩmãni da Allah" sa'an nan idan
aka cũce shi wajen aikin Allah, sai ya sanya fitinar mutãne kamar azãbar Allah
kuma lalle idan taimakon Ubangijinka ya zo, haƙĩƙa, ya kan ce: "Lalle mũ mun
kasance tãre da ku." shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga abin da ke a cikin
ƙirãzan halittunSa?
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Ku bi hanyarmu,
kuma Mu ɗauki laifuffukanku," alhãli kõwa ba su zamo mãsu ɗauka da a kõme ba
daga laifuffukansu. Lalle sũ maƙaryata ne.
Kuma lalle sunã ɗaukar kãyan nauyinsu da waɗansu nauyãyan kãya tãre da kãyan
nauyinsu, kuma lalle zã a tambaye su a Rãnar ¡iyama game da abin da suka kasance
sunã ƙirƙirãwa na ƙarya.
Kuma lalle Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya zauna a cikinsu shẽkara dubu
fãce shẽkara hamsin, sa'an nan cikowar (¦ũfãna) ta kãmã su, alhãli kuwa sũ ne
mãsu zãlunci.
"Abin da dai kuke bautãwa, baiein Allah, gumaka ne, kuma kun ƙirƙira ƙarya.
Lalle waɗannan da kuke bauta wa baicin Allah, bã su mallakã muku arziki. Sabõda
haka ku nẽmi arziki a wurin Allah kawai, kuma ku bauta Masa, kuma ku yi gõdiya
zuwa gare Shi. Zuwa gare Shi ake mayar da ku.
"Kuma idan kun ƙaryata, to, lalle waɗansu al'ummõmi a gabãninku sun ƙaryata,
kuma bãbu abin da ke kan Manzo, fãce iyar da manzanci, iyarwa bayyananna."
Ka ce: "Ku yi tafiya cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda (Allah) Ya fãra yin
halitta, sa'an nan kuma Allah Yanã ƙãga wata halittar mayarwa. Lalle Allah Mai
ikon yi ne a kan kõme.
Sa'an nan bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa (Ibrãhĩm) fãce dai suka ce:
"Ku kashe shi kõ, ku ƙõnã shi," Sai Allah Ya tsĩrar da shi daga wutã. Lallea
cikin wannan akwai ayõyi ga mutãnen da ke yin ĩmãni.
Kuma Ibrahĩm ya ce "Bãbu abin da kuka yi sai dai kub bar Allah kun riƙi gumãka
sabõda sõyayyar tsakãninku a cikin rãyuwar dũniya, a'an nan a Rãnar ¡iyãma
sãshinku zai kãfirce wa sãshi, kuma makõmarku ita ce wutã kuma bã ku da waɗansu
mataimaka."
Kuma Muka bã shi Ishãƙa da Ya'aƙũba, kuma Muka sanya Annabci da littãfi a cikin
zuriyarsa. Kuma Mun bã shi sakamakonsa a dũniya, kuma lalle shĩ a Lãhira,
tabbas, yanã a cikin sãlihai.
"Ashe, lalle kũ kunã je wa maza, kuma ku yi fashin hanya kuma ku je, a cikin
majalisarku da abin da bã shi da kyau? To, jawãbin mutãnensa bai kasance ba fãce
dai sun ce: 'Ka zo mana da azãbar Allah, idan ka kasance daga mãsu gaskiya.'"
Kuma a lõkacin da ManzanninMu suka jẽ wa Ibrãhĩm da bushãra suka ce: "Lalle mu
mãsu halaka mutãnen, wannan alƙarya ne. Lalle mutãnenta sun kasance mãsu
zãlunci."
Ya ce: "Lalle akwai Lũɗu a cikinta!" Suka ce: "Mũ ne mafiya sani ga waɗanda suke
a cikinta, lalle munã tsĩrar da shi da mutãnensa, fãce fa mãtarsa ta kasance a
cikin mãsu wanzuwa."
Kuma a lõkacin da ManzanninMu suka je wa Lũɗu ya ɓãta rai sabõda su, kuma yã
ƙuntata ga kirji sabõda su. Kuma suka ce: "Kada ka ji tsõro kuma kada ka yi
baƙin ciki lalle mũ mãsu tsĩrar da kai ne da iyãlanka, fãce dai matarka ta
kasance daga mãsu wanzuwa.
Kuma zuwa ga Madyana, Mun aika ɗan'uwansu shu'aibu, sai ya ce: "Ya mutãnena! Ku
bauta wa Allah kuma ku yi fatan (rahamar) Rãnar Lãhira, kuma kada ku yi ɓarna a
cikin ƙasã, alhãli kuwa kunã mãsu lãlãtarwa."
Da Ãdawa da Samũdãwa alhãli kuwa lalle alãmun azãba sun bayyana a gare su daga
gidãjensu kuma Shaiɗan ya ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka ya kange su daga
hanyar Allah, kuma sun kasance mãsu basĩra!
Sabõda haka kõwanensu Mun kama shi da laifinsa. Watau daga cikinsu akwai wanda
Muka aika iskar tsakuwa a kansa kuma daga cikinsu akwai wanda tsãwa ta kãmã,
kuma daga cikinsu akwai wanda Muka birkice ƙasã da shi kuma daga cikinsu akwai
wanda Muka nutsar. Bã ya yiwuwa ga Allah Ya zãlunce su, amma sun kasance kansu
suke zãlunta.
Ka karanta abin da ake yin wahayi zuwa gare ka daga Littãfi, kuma ka tsayar da
salla. Lalle salla tanã hanãwa daga alfãsha da abni ƙyãma, kuma lalle ambaton
Allah ya fi girma, kuma Allah Yanã sane da abin da kuke aikatãwa.
Kada ku yi jayayya da mazowa Littãfi sai fa da magana wadda ta fi kyau, sai fa
waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, kuma ku ce, "Mun yi ĩmãni da abin da aka
saukar a gare mu kuma aka saukar a gare ku, kuma Abin bautãwarmu da Abin
bautãwarku Guda ne, kama mũ mãsu sallamãwa ne a gare shi."
Kuma kamar haka Muka saukar da Littafi a gare ka, to, waɗannan da Muka bai wa
Littãfi sanã ĩmãni da shi, daga cikin wãɗannan akwai mai ĩmãni da shi, kuma bãbu
mai musun ãyõyinMu, fãce kãfirai.
Kuma suka ce: "Don me ba a saukar masa da ãyõi ba daga Ubangijinsa? "Ka ce: "Su
ãyõyi a wurin Allah kawai suke, kuma lalle ni mai gargaɗi kawai ne, mai
bayyanãwa."
Shin bai ishe su ba cẽwa lalle Mũ, Mun saukar da Littãfin akanka, anã karanta
shi a kansu? Lalle a cikin wancan haƙĩƙa akwai rahama da tunãtawa ga mutanen da
ke yin ĩmãni.
Ka ce: "Allah Yã isa shaida a tsakãnĩna da tsakãnĩnku Yanã sane da abin da ke a
cikin sammai da ƙasã, kuma waɗanda suka yi ĩmãni da ɗarya kuma suka kãfirta da
Allah, waɗannan sũ nemãsu hasãra."
Kuma suna nẽman ka da gaggauta azãba, to, bã dõmin ajali ƙayyadadde ba, dã azãba
ta jẽ musu kuma lalle dã tanã iske su bisa ia abke, alhãli kuwa sũ ba su sani
ba.
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zã Mu zaunar
da su daga cikin Aljanna a gidãjen bẽne, ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã
madawwama a cikinsu. To, madalla da sakamakon mãsu aikin ƙwarai.
Kuma lalle idan ka tambaye su. "Wãne ne ya saukar da ruwa daga sama, har ya
rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta?" Lalle sunã cẽwa, "Allah ne." Ka
ce: "Gõdiya tã tabbata ga Allah." Ã'a, mafi yawansu bã su hankalta.
To, a lõkacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirãyi Allah sunã mãsu
tsarkake addini a gare shi, to, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudun ƙasã,
sai gã su sunã shirki.
Shin, ba su ga cẽwa, lalle Mun sanya Hurumi amintacce ba alhãli kuwa anã fisge
mutãne a gẽfensu? Shin, da ɓãtaccen abu suke ĩmãni kuma da ni'imarAllah suka
kãfirta?
Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga
Allah, kõ kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta je masa? Ashe a cikin
Jahannama bãbu mazauna ga kãfirai?
Kuma wadannan da suka yi ƙõƙari ga nẽman yardarMu, lalle Munã shiryar da su ga
hanyõyinMu, kuma lalle Allah, tabbas, Yanã tãre da mãsu kyautatãwa (ga
addĩninsu).