Kõ sunã cẽwa (Muhammadu ne) ya ƙirƙira shi? Ã'a, shĩ ne gaskiya daga
Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda wani mai gargaɗi bai je musu
ba a gabãninka, fãtan zã su shiryu.
Allah ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu a cikin
kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaita a kan Al'arshi. Bã ku da, baicin Shi, wani
majiɓinci kuma babu wani maceci. Shin, bã zã ku yi tunãni ba?
Yanã shirya al'amari daga sama zuwa ga ƙasã, sa'an nan ya tãka zuwa gare Shi a
cikin yini, wanda gwargwadonsa shẽkaru dubu ne ga abin da kuke lissafãwa.
Kuma suka ce: "Shin, idan mun ɓace a cikin ƙasã, shin, lalle mu, tabbas ne munã
zama a cikin wata halitta sãbuwa?" Ã'a, su game da gamuwa da Ubangijinsu kãfirai
Kuma da kã gani a lõkacin da mãsu laifi suke mãsu sunkuyar da kawunansu a wurin
Ubangijinsu, "Ya Ubangijinmu! Mun gani, kuma mun ji, to, Ka mayar da mu mu
aikata aiki na ƙwarai. Lalle mũ mãsu yaƙĩni ne."
Kuma dã Mun so dã Mun bai wa kõwane rai shiriyarsa to, amma magana ta tabbata
daga gare Ni! Lalle ne Inã cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya.
To, ku ɗanɗana sabõda abin da kuka manta na haɗuwa da ranarku wannan. Lalle Mũ
mã Mun manta da ku, kuma ku dãnɗani azãbar dawwama sabõda abin da kuka kasance
kunã aikatãwa.
Waɗanda ke ĩmãni da ãyõyinMu kawai, sũ ne waɗanda idan aka karanta musu ãyõyinMu
sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma su yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu,
alhãli kuwa su bã su yin girman kai.
Amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwafai, to, sunã da gidãjen
Aljannar makõma, a kan liyãfa sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Kuma waɗanda suka yi fãsiƙanci to makõmarsu ita ce wuta, kõ da yaushe suka yi
nufin su fita daga gare ta, sai a mayar da su a cikinta, kuma a ce musu: "Ku
ɗanɗana azãbai wutã, wadda kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita."
Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda aka tunãtar da ãyõyin Ubangijinsa,
sa'an na ya bijire daga barinsu? Lalle Mũ, Mãsu yin azãbar rãmuwa ne ga mãsu
laifi.
Kuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littafi, sabõda haka kada ka kasance a cikin
shakka daga haɗuwa da shi. Kuma Mun sanya shi ya zama shiriya ga Banĩ Isrã'ĩla.
Shin, ba ya shiryar da su cẽwa da yawa Muka halakara gabãninsu, daga al'ummõmi
sunã tafiya a cikin masaukansu? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi. Shin, ba su jĩ
ne?
Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle Mũ, Munã kõra ruwa zuwa ga ƙasã
ƙeƙasasshiya, sa'an nan Mu fitar, game da shi, wata shũka wadda dabbõbinsu, da
su kansu ke ci daga gare ta? Ashe fa ba su gani ba?