Allah bai sanya zũciya biyu ba ga wani namiji a cikinsa, kuma bai sanya mãtanku
waɗanda kuke yin zihãri daga gare su, su zama uwãyenku ba, kuma bai sanya ɗiyan
hankãkarku su zama ɗiyanku ba. wannan abu nãku, maganarku ce da bãkunanku alhãli
kuwa Allah na faɗar gaskiya, kuma Shĩ ne ke shiryarwa ga hanyar ƙwarai.
Ku kira su ga ubanninsu, shi ne mafi ãdalci a wurin Allah. To, idan ba ku san
ubanninsu ba, to, 'yan'uwanku ga addini da dĩmajojinku. Kuma bãbu laifi a gare
ku ga abin da kuka yi kuskure da shi, kuma amma (akwai laifi) ga abin da
zukãtanku suka ganganta, kuma Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
Annabi ne mafi cancanta ga mũminai bisa ga su kansu, kuma mãtansa uwãyensu ne.
Kuma ma'abuta zumunta waɗansunsu sun fi waɗansu a cikin Littãfin Allah bisa ga
mũminai da Muhãjirai, fãce fa idan kun aikata wani alhẽri zuwa ga majiɓintanku.
Wancan yã kasance a cikin Littafi, rubũtacce.
Kuma a lõkacin da Muka riƙi alkawarin Annabawa daga gare su, kuma daga gare ka,
kuma daga Nũhu da Ibrãhĩm da Mũsa da kuma Ĩsã ɗan Maryama,kuma Muka riƙi wani
alkawari mai kauri daga gare su.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da waɗansu
rundunõni suka zo muku, sai Muka aika wata iskã a kansu da waɗansu rundunõni
waɗanda ba ku gani ba, Kuma Allah Yã kasance Mai gani ga abin da kuke aikatãwa.
A lõkacin da suka zo muku daga samanku da kuma ƙasa daga gare ku, kuma a lõkacin
da gannai suka karkata kuma zukãta suka kai ga maƙõsai, kuma kuka yi zaton
zace-zace, game da Allah.
Kuma a lõkacin da wata ƙungiya daga gare su, ta ce, "Ya mutãnen Yasriba! Bã ku
da wani matsayi, sabõda haka ku kõma." Kuma wata ƙungiya daga gare su na nẽman
izni ga Annabi sunãcẽwa, "Lalle gidãjenmu kuranye suke," alhãli kuwa bã kuranye
suke ba, bã su da nufin kome fãce gudu.
Kuma dã an shige ta (Madĩna) a kansu, daga sasanninta, sa'an nan aka tambaye su
fitina (kãfirci), lalle dã sun jẽ mata, kuma dã ba su zauna a cikinta (Madĩna)
ba fãce kaɗan.
Ka ce: "Wãne ne wanda yake tsare ku daga Allah, idan Yã yi nufin wata cũta game
da ku?" Kuma bã zã su sãmar wa kansu wani majiɓinci ba, banda Allah, kuma bã zã
su sãmar wa kansu wani mataimaki ba.
Suna mãsu rõwa gare ku, sa'an nan idan tsõro ya zo, sai ka gan su sunã kallo
zuwa gare ka, idãnunsu sunã kẽwaya, kamar wanda ake rufe hankalinsa sabõda
mutuwa. Sa'an nan idan tsõron ya tafi,sai su yi muku miyãgun maganganu da
harussa mãsu kaifi, sunã mãsu rõwa a kan dũkiya. Waɗannan, ba su yi ĩmani ba,
sabõda hakaAllah Ya ɓãta ayyukansu. Kuma wannan ya kasance mai sauƙi ga Allah.
Sunã zaton ƙungiyõyin kãfirai ba su tafi ba. Kuma idan ƙungiyõyin kãfirai sun
zo, sunã gũrin da dai sun zama a karkara a cikin ƙauyãwa, sunã tambayar
lãbãranku. Kuma kõ dã sun kasance a cikinku, bã zã su yi yãƙi ba, fãce kaɗan.
Lalle, abin kõyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya
kasanee yanã fãtan rahamar Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya ambaci Allah da yawa.
Kuma a lõkacin da mũminai suka ga ƙungiyõyin kãfirai, sai suka ce, "Wannan ne
abin da Allah da ManzonSa suka yi mana wa'adi, Allah da ManzonSa sunyi gaskiya."
Kuma wannan bai ƙãra musu kõme ba fãce ĩmãni da sallamãwa.
Daga mũminai akwai waɗansu mazãje da suka gaskata abin da suka yi wa Allah
alkwari a kansa, sa'an nan a cikinsu, akwai wanda ya biya bukãtarsa, kuma daga
cikinsu akwai wanda ke jira. Kuma ba su musanya ba, musanyawa.
Dõmin Allah Ya sãka wa masu gaskiya da gakiyarsu, kuma Ya azabtar da munafukai
idan Ya so, ko Ya karɓi tũba a kansu. Lalle, Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai
jin ƙai.
Kuma Allah Yã mayar da waɗanda suka kãfirta da fushinsu, ba su sãmi wani alhẽri
ba. Allah Ya isar wa mũminai daga barin yãƙi. Kuma Allah Ya kasance Mai ƙarfi,
Mabuwãyi.
Kuma Ya saukar da waɗannan da suka taimake su daga mazõwa Littãfi, daga
birãnensu, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukatansu; wata ƙungiya kunã kashẽwa, kuma
kunã kãma wata ƙungiyar.
Yã kai Annabi! Ka ce wa matanka, "Idan kun kasance kunã nufin rãyuwar dũniya da
ƙawarta, to, ku zo in yi muku kyautar ban kwãna kuma in sake ku, saki mai kyau."
"Kuma idan kun kasance kunã nufin Allah da Manzonsa da gidan Lãhria, to, lalle,
Allah Yã yi tattalin wani sakamako mai girma ga mãsu kyautatãwa daga gare ku."
Kuma wadda ta yi tawãli'u daga cikinku ga Allah da ManzonSa, kuma ta aikata aiki
na ƙwarai, zã Mu bã ta sakamakonta ninki biyu, kuma Mun yi mata tattalin arziki
ma karimci.
Yã mãtan Annabĩ! Ba ku zama kamar kõwa ba daga mãtã, idan kun yi taƙawa, sabõda
haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cũta a cikin zuciyarsa ya yi
ɗammani, kuma ku faɗi magana ta alheri.
Kuma ku tabbata a cikin gidãjenku, kuma kada ku yi fitar gãye-gãye irin fitar
gãye-gãye ta jãhiliyyar farko. Kuma ku tsaĩ da salla, kuma ku bãyar da zakka, ku
yi ɗã,ã ga Allah da ManzonSa. Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga
gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa.
Lalle, Musulmi maza da Musulmi mãtã da muminai maza da muminai mãtã, da mãsu
tawãli'u maza da mãsu tawãlĩu mãtãda mãsu gaskiya maza da mãsu gaskiya mãtã, da
mãsu haƙuri maza da mãsu haƙuri mãtã, da mãsu tsõron Allah maza da mãsu tsõron
Allah mãtã, da mãsu sadaka maza da mãsu sadaka mãtã, da mãsu azumi maza da mãsu
azumi mãtã da mãsu tsare farjõjinsu maza da mãsu tsare farjõjinsu mãtã, da mãsu
ambaton Allah da yawa maza da mãsu ambatonsa mãtã, Allah Ya yi musu tattalin
wata gãfara da wani sakamako mai girma.
Kuma ba ya halatta ga mũmini kuma haka ga mũmina, a lõkacin da Allah da Manzonsa
Ya hukunta wani umurni, wani zãɓi daga al'amarinsu ya kasance a gare su. Kuma
wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, to, yã ɓace, ɓacẽwa bayyananna.
Kuma a lõkacin da kake cẽwa ga wanda Allah Ya yi ni'ima a gare shi kai kuma ka
yi ni'ima a gare shi, "Ka riƙe mãtarka, kuma ka bi Allah da taƙawa," kuma kana
ɓõyẽwa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana shi, kanã tsõron mutãne, alhãli
kuwa Allah ne Mafi cancantar ka ji tsõronSa. to a lõkacin da zaidu ya ƙãre
bukãtarsa daga gare ta, Mun aurar da kai ita, dõmin kada wani ƙunci ya kasance a
kan mũminai a cikin (auren mãtan) ɗiyan hankãkarsu, idan sun ƙãre bukãta daga
gare su. Kuma umurnin Allah yã kasance abin aikatãwa.
Wani ƙunci bai kasance a kan Annabi ba ga abin da Allah Ya faralta a kansa, a
kan ƙã'idar, Allah a cikin (Annabãwa )waɗanda suka shige daga gabãninsa. Kuma
umurnin Allah yã kasance abin ƙaddarãwa tabbatacce.
(Allah) Shĩ ne Wanda ke tsarkake ku, da mala'ikunSa (sunã yi muku addu'a), dõmin
Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske. Kuma (Allah) Yã kasance Mai Jĩn ƙai ga
mũminai.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! idan kun auri mũminai mãtã, sa'an nan kuka sake su
a gabãnin ku shãfe su, to, bã ku da wata idda da zã ku lissafa a kansu, kuma ku
yi musu kyautar jin dãɗi kuma ku sake su saki mai kyau.
Yã kai Annabi! Lalle Mũ, Mun halatta maka mãtanka waɗanda ka bai wa sadãkõkinsu
da abin da hannun dãmanka ya mallaka daga abin da Allah Ya bã ka na ganĩma, da
'yã'yan baffanka,da 'ya'yan goggonninka da 'yã'yan kãwunka da 'yã'yan innõninka
waɗanda suka yi hijira tãre da kai, da wata mace mũmina idan ta bãyar da kanta
ga Annabi, idan shi Annabi yanã nufin ya aure ta (hãlin wannan hukunci) kẽɓe
yake gare ka,banda gamũminai. Lalle Mun san abin da Muka faralta a kansu
(smũminai) game da mãtansuda abin da hannayensu suka mallaka. Do min kada wani
ƙunci ya kasance a kanka, kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
Kanã iya jinkirtar da wadda ka ga dãmã daga gare su, kuma kanã tãro wadda kake
so zuwa gare ka. Kuma wadda ka nẽma daga waɗanda ka nĩsantar, to, bãbu laifi
agare ka. Wannan yã fi kusantar da sanyaya idãnunsu, kuma bã zã su yi baƙin ciki
ba, kuma su yarda da abin da ka bã su, sũ duka. Kuma Allah Yanã sane da abin da
yake a cikin zukãtanku. Kuma Allah Ya kasance Masani, Mai haƙuri.
Waɗansu mãtã bã su halatta a gare ka a bãyan haka, kuma ba zã ka musanya su da
mãtan aure ba, kuma kõ kyaunsu yã bã ka sha'awa, fãce dai abin da hannun dãmanka
ya mallaka. Kuma Allah Yã kasance Mai tsaro ga dukan kõme.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada kũ shiga gidãjen Annabi, fãce fa idan an yi
izni a gare ku zuwa ga wani abinci, bã da kun tsaya jiran nunarsa ba, kuma amma
idan an kira ku, to, ku shiga, sa'an nan idan kun ci, to ku wãtse, kuma bã da
kun tsaya kunã masu hĩra da wani Iãbãri ba. Lalle wannan yanã cũtar da Annabi,
to, yanã jin kunyarku, alhãli kuwa Allah bã Ya jin kunya daga gaskiya. Kuma idan
zã ku tambaye su waɗansu kãyã, to, ku tambaye su daga bãyan shãmaki. Wannan ya
fi muku tsarki ga zukãtanku da zukãtansu. Kuma bã ya halatta a gare ku, ku cũci
Manzon Allah, kuma bã ya halatta ku auri mãtansa a bãyansa har abada. lalle
wannan a gare ku yã kasance babban abu a wurin Allah.
Bãbu laifi a kansu game da ubanninsu, kuma bãbu game da ɗiyansu, kuma bãbu game
da 'yan'uwansu maza, kuma bãbu game da ɗiyan 'yan'uwansu maza, kuma bãbu game da
ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kuma bãbu game da mãtan mũminai, kuma bãbu game da abin
da hannãyensu suka mallaka, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Yã kasance
Mahalarci a kan kõme.
Yã kai Annabi! Ka ce wa mãtan aurenka da 'yã'yanka da mãtan mũminai su kusantar
da ƙasã daga manyan tufãfin da ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su dõmin
kada a cũce su. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai Jin ƙai.
Lalle, idan munãfukai da waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukãtansu, da mãsu
tsẽgumi a cikin Madĩna, ba su hanu ba (daga hãlãyensu), lalle, zã Mu shũshũta ka
a gare su, sa'an nan bã zã su yi maƙwabtaka da kai ba, a cikinta, fãce kaɗan.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kasance kamar waɗanda suka cũci Mũsã sa'an
nan Allah Ya barrantar da shi daga abin da suka ce. Kuma ya kasance mai daraja a
wurin Allah.
Lalle Mũ, Mun gitta amãna ga sammai da ƙasã da duwãtsu, sai suka ƙi ɗaukarta
kuma sukaji tsõro daga gare ta, kuma mutum ya ɗauke ta, lalle shĩ (mutum) ya
kasance mai yawan zãlunci, mai yawan jãhilci.
Dõmin Allah Ya azabta munãfukai maza da munãfukai mãtã, da mushirikai maza da
mushirikai mãtã, kuma Allah Yã karɓi tũba ga mũminai maza da mũminai mãtã. Kuma
Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.