To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã
Shi ba, (sunã cẽwa) "Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga
Allah, kusantar daraja." Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka
zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya,
mai kãfirci.
Dã Allah Yã yi nufin Ya riƙi ɗã, to, lalle sai Ya zãɓa daga abin da Yake
halittãwa abin da Yake so. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Shĩ ne Allah,
Makaɗaici, Mai tĩlastãwa.
Ya halitta sammai da ƙasã da gaskiya. Yanã shigar da dare a kan rãna, kuma Yanã
shigar da rãnã a kan dare kuma Yã hõre rãnã da watã, kõwannensu yanã gudãna zuwa
ga ajali ambatacce. To, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai gãfara.
Yã halitta ku daga rai guda, sa'an nan Ya sanya ma'auranta daga gare shi. Kuma
ya saukar muku daga dabbõbin gida nau'i takwas Yanã halitta ku a cikin cikunnan
uwayenku, halitta a bãyan wata halitta, a cikin duffai uku. Wannan shĩ ne Allah
Ubangijinku. Mulki a gare shi yake. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake
karkatar da ku?
Idan kun kãfirta to, lalle Allah Wadãtacce ne daga barinku, kuma bã Shi yarda da
kãfirci ga bãyinSa, kuma idan kun gõde, Zai yarda da ita (gõdiyar) a gare ku,
kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani. Sa'an nan kuma
makõmarku zuwa ga Ubangijinku take, dõmin Ya bã ku lãbãri game da abin da kuka
kasance kunã aikatãwa. Lalle Shĩ, Masani ne ga abin da yake a ainihin zukata.
Kuma idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kira Ubangijinsa, yanã mai mai da
al'amari zuwa gare Shi, sa'an nan idan Ya jũyar da cũtar da ni'ima ta daga gare
Shi, sai ya manta da abin da ya kasance yanã kira zuwa gare shi a gabãnin haka,
kuma ya sanya wa Allah waɗansu abõkan tarẽwa dõmin ya ɓatar (da su) daga
hanyarSa. Ka ce (masa), "Ka ji dãɗi da kãfircinka, a ɗan lõkaci, lalle kai daga
'yan wutã ne."
Shin, wanda yake mai tawãli'u sã'õ'in dare, yanã mai sujada kuma yanã mai tsayi
ga salla, yanã tsõron Lãhira, kuma yanã fãtan rahamar Ubangijinsa, (yanã daidai
da waninsa?) Ka ce: "Ashe, waɗanda suka sani, sunã daidaita da waɗanda ba su
sani ba?" Mãsu hankali kawai ke yin tunãni.
Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ĩmãni!Ku bi Ubangijinku da
taƙawa. Waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya sunã da sakamako mai kyau,
kuma ƙasar Allah mai fãɗi ce. Mãsu haƙuri kawai ake cika wa ijãrarsu, bã da wani
lissãfi ba.
"To, ku bauta wa abin da kuke so, waninSa." Ka ce: "Lalle mãsu hasãra, sũ ne
waɗanda suka yi hasarar rãyukansu da iyãlansu, a Rãnar ¡iyãma. To, waccan fa,
ita ce hasãra bayyananna."
Sunã da waɗansu inuwõwi na wutã daga samansu, kuma daga ƙasansu akwai waɗansu
inuwõwi. Wancan Shĩ ne Allah ke tsõratar da bãyinSa da shi. Yã bãyĩNa! To, ku bĩ
Ni da taƙawa.
Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa, sunã da bẽnãye, daga samansu akwai
waɗansu bẽnãye ginannu, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Alkawarin Allah.
Allah bã Ya sãɓã wa alkawarinSa.
Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Yã
gudãnar da shi yanã marẽmari a cikin ƙasã sa'an nan Yã fitar da shũka game da
shi, launukan shũkar mãsu sãɓãnin jũna sa'annan shũkar ta ƙeƙashe har ka gan ta
fatsifatsi, sa'an nan Allah Ya sanya ta dandaƙaƙƙiya? Lalle ne ga wancan akwai
tunãtarwa ga mãsu hankali (ga iyãwar gudãnar da ruwa a cikin gidãjen Aljanna).
Shin fa, wanda Allah Ya buɗa ƙirjinsa, dõmin Musulunci sa'an nan shi yanã a kan
haske daga Ubangijinsa, (zai zama kamar waninsa)? To, bone yã tabbata ga
maƙeƙasa zukãtansu daga ambaton Allah. Waɗancan sunã a cikin wata ɓata
bayyananna.
Allah Ya sassaukar da mafi kyaun lãbãri, Littãfi mai kama da jũna, wanda ake
konkoma karãtunsa fãtun waɗanda ke tsõron Ubangijinsu, sunã tãƙura sabõda Shi,
sa'an nan fãtunsu da zukãtansu su yi laushi zuwa ga ambaton Allah. Waccan ita ce
shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Ya so game da ita. Kuma wanda Allah Ya
ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa.
Shin fa, wanda ke kãre mũguwar azãba da fuskarsa (yanã zama kamar waninsa) a
Rãnar ƙiyãma? Kuma a ce wa azzãlumai, "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã
aikatãwa."
Allah Yã buga misãli; wani mutum (bãwa) a cikinsa akwai mãsu tarayya, mãsu mũgun
hãlin jãyayya, da wani mutum (bãwa) dukansa ga wani mutum. Shin, zã su daidaita
ga misãli? Gõdiya ta tabbata ga Allah (a kan bayãni). Ã'a, mafi yawan mutãne ba
su sani ba.
To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya yi ƙarya ga Allah, kuma ya ƙaryata
gaskiya a lõkacin da ta jẽ masa? Shin bãbu mazauni a cikin Jahannama ga kãfirai?
Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wane ne ya halitta sammai da ƙasã?" Haƙĩƙa, zã
su ce, "Allah ne." Ka ce: "Ashe, to, kun gani abin da kuke kira, waɗanda suke
wanin Allah ne, idan Allah Ya nufe ni da wata cũta, shin sũ abũbuwan nan mãsu
kuranye, cutarsa ne? Kõ kuma Ya nufe ni da wata rahama, shin, su abũbuwan nan
mãsu kãme rahamarSa ne?" Ka ce: "Mai isata Allah ne, gare Shi mãsu tawakkali ke
dõgara."
Lalle Mũ Mun saukar da littãfi a gare ka dõmin mutãne da gaskiya. Sa'an nan
wanda ya nẽmi shiriya, to, dõmin kansa, kuma wanda ya ɓace, to, yanã ɓacẽwa ne a
kanta. Kuma ba ka zama wakĩli a kansu ba.
Allah ne ke karɓar rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a
cikin barcinsu. Sa'an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki
gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga
mutãne waɗanda ke yin tunãni.
Kuma idan aka ambaci Allah Shi kaɗai zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni ba da
Lãhira, su yi ƙiyãma, kuma idan an ambaci waɗanda suke kiran, wasunSa, sai gãsu
sunã yin bushãrar farin ciki.
Ka ce: "Ya Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasã, Masanin gaibi da bayyane!
Kai ne ke yin hukunci a tsakãnin bãyinKa a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa
wa jũna a cikinsa."
Kuma dã waɗanda suka yi zãlunci sunã da abin da ke cikin ƙasã gaba ɗaya, da
misãlinsa a tãre da shi lalle dã sun yi fansa da shi daga mummunar azãba, a
Rãnar ¡iyãma. Kuma abin da ba su kasance sunã zato ba, daga Allah, ya bayyana a
gare su.
To, idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, sa'an nan idan Muka canza
masa ita, ya sãmi ni'ima daga gare Mu, sai ya ce: "An bã ni ita ne a kan wani
ilmi nãwa kawai." Ã'a ita wannan (magana) fitina ce, kuma amma mafi yawansu ba
su sani ba.
Sai (sakamakon) mũnãnan abin da suka aikata ya same su. Kuma waɗanda suka yi
zãlunci daga waɗannan, (sakamakon) munãnan abin da suka aikata zai sãme su, kuma
ba su zama mabuwãya ba.
Ashe kuma ba su sani ba cẽwa Allah, na shimfiɗa arziƙi ga wanda Yake so, kuma
Yanã ƙuƙuntawa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin ĩmãni.
Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi barna a kan rãyukansu! Kada ku
yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle
Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."
Kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka, "Lalle
idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu
hasãra."
Kuma ba su ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin ĩkon yinsa ba: ¡asã duka damƙarSa ce, a
Rãnar ¡iyãma, kuma sammai abũbuwan naɗewa ne ga dãmanSa. Tsarki ya tabbata a
gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga barin abin da suke shirki da shi.
Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasã suka sũma sai
wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa'an nan aka hũra a cikinsa, wata hũrãwa,
sai gã su tsaitsaye, sunã kallo.
Kuma ƙasã ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littãfi, kuma aka zo
da Annabãwa da mãsu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakãninsu, da gaskiya, alhãli
kuwa, sũ, bã zã a zãlunce su ba.
Kuma aka kõra waɗanda suka kãfirta zuwa Jahannama, jama'a-jama'a har a lõkacin
da suka je mata, sai aka buɗe ƙõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Ashe,
waɗansu Manzanni, daga cikinku ba su je muku ba, sunã karanta ãyõyin Ubangijinku
a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin gamuwa da yininku wannan?" Suka ce, "Na'am,
"kuma amma kalmar azãba ita ce ta wajaba a kan kãfirai!"
Kuma aka kõra waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa zuwa Aljanna jama'a-jama'a
har a lõkacin da suka jẽ mata, alhãli kuwa an buɗe kõfõfinta, kuma matsaranta
suka ce musu, "Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji dãɗi, sabõda haka ku shige
ta, kunã madawwama( a cikinta)."
Kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya yi mana gaskiya ga wa'adinSa,
kuma Ya gãdar da mu ƙasã, munã zama a cikin Aljanna a inda muke so." To, madalla
da ijãrar ma'aikata.
Kuma kanã ganin malã'iku sunã mãsu tsayãwa da haƙƙoƙin da aka ɗõra musu daga
kẽwayen Al'arshi, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu. Kuma aka yi hukunci
a tsakãninsu da gaskiya. Kuma aka ce, "Gõdiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin
halittu."