Ya ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa Wanda Ya halitta ku daga rai guda,
kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza mãsu
yawa da mãtã. Kuma ku bi Allah da taƙawa Wanda kuke rõƙon jũna da (sũnan), shi,
da kuma zumunta . Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne.
Kuma ku bai wa marãyu dũkiyõyinsu, kuma kada ku musanya mummuna da mai kyau.
Kuma kada ku ci dũkiyõyinsu zuwa ga dũkiyõyinku. Lalle shi, yã kasance zunubi ne
mai girma.
Kuma idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba a cikin marãyu, to, (akwai yadda
zã a yi) ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da
huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri)
guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi
kusantar zama ba ku wuce haddi ba.
Kuma ku bai wa mãtã sadãkõkĩnsu da sauƙin bãyarwa. Sa'an nan idan suka yãfe muku
wani abu daga gare shi, da dãɗin rai, to, ku ci shi da jin dãɗi da sauƙin
haɗiya.
Kada ku bai wa wãwãye dũkiyarku, wadda Allah Ya sanya ta a gare ku, kunã mãsu
tsayuwa (ga gyãranta). Kuma ku ciyar da su a cikinta, kuma ku tufãtar da su,
kuma ku gaya musu magana sananniya ta alhẽri.
Kuma ku jarraba marãyu, har a lõkacin da suka isa aure. To, idan kun lura da
shiriya daga gare su, to, ku mĩƙa musu dũkiyõyinsu. Kada ku cĩ ta da ɓarna, kuma
da gaggawa kãfin su girma. Kuma wanda yake wadãtacce, to, ya kãma kãnsa, kuma
wanda yake faƙĩri, to, ya ci, gwargwadon yadda ya kamata. To, idan kun mĩƙa musu
dũkiyõyinsu, sai ku shaidar a kansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai bincike.
Maza suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, kuma
mãtã suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, daga
abin da ya ƙaranta daga gare shi kõ kuwa ya yi yawa, rabo yankakke.
Kuma waɗanda suke dã sun bar zuriyya mãsu rauni a bãyansu, zã su ji tsõro a
kansu, su yi sauna, sa'an nan su bi Allah da taƙawa, kuma su faɗi magana
madaidaiciya.
Allah Yanã yi muku wasiyya a cikin 'ya'yanku; namiji yanã da rabon mãtã biyu.
Idan sun kasance mãtã ne fiye da biyu kuwa, to, suna da biyu daga kashi uku ɗin
abin da ya bari, kuma idan ta zama guda ce (kawai) to, tana da rabi. Kuma
iyãyensa biyu kõwane ɗaya daga cikinsu yanã da ɗaya daga kashi shida ɗin abin da
ya bari idan wani rẽshe ya kasance gare shi, to, idan rẽshe bai kasance gare shi
ba, kuma iyãyensa ne (kawai) suka gãje shi, to, uwa tanã da sulusi (ɗaya daga
cikin kashi uku). Sa'an nan idan 'yan'uwa sun kasance gare shi, to, uwarsa tana
da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida) daga bayan wasiyya wadda ya yi kõ kuwa
bãshi. Ubanninku da 'yã'yan ku, ba ku sani ba, wannensu ne mafi kusantar amfani,
a gare ku. Yankawa daga Allah. Lalle ne, Allah Yã kasance Masani Mai hikima.
Kuma kunã da rabin abin da mãtanku na aure suka bari idan rẽshe bai kasance gare
su ba. Sa'an nan idan rẽshe ya kasance gare su, to, kunã da rubu'i (ɗaya daga
cikin kashi huɗu) daga abin da suka barin, daga bãyan wasiyya wadda suka yi kõ
kuma bãshi. (Sũ) kuma suna da rubu'i daga abin da kuka bari idan rẽshe bai
kasance ba gare ku, idan kuwa rẽshe ya kasance gare ku, to, sunã da sumuni (ɗaya
daga cikin kashi takwas) daga abin da kuka bari, daga bãyan wasiyya wadda kuka
yi kõ kuwa bãshi. Idan wani namiji ya kasance ana gãdon sa bisa kalãla, ko kuwa
wata mace alhãli kuwa yana da ɗan'uwa kõ 'yar'uwa to, kõwane ɗaya daga cikinsu
yana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida), sai idan sun kasance mafi yawa
daga wannan, to, sũ abõkan tãrayya ne a cikinsulusi (ɗaya bisa uku), daga bãyan
wasiyya wadda aka yi kõ kuma bãshi. Bã da yana mai cũtarwa ba, ga wasiyya, daga
Allah. Kuma Allah Masani ne Mai haƙuri.
Waɗancan iyãkõkin Allah ne. Wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai
shigar da shi gidãjen Aljanna (waɗanda) ɗõramu suna gudana daga ƙarƙashinsu,
suna madawwama a cikinsu, kuma wannan shi ne rabo babba.
Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, kuma ya ƙẽtare iyãkõkinSa, zai shigarda
shi wuta, yana madawwami a cikinta, kuma yana da wata azãba mai walãkantarwa.
Kuma waɗanda suka je wa alfãsha daga mãtanku, to, ku nẽmi Shaidar mutãne huɗu
daga gare ku a kansu. To, idan sun yi shaida, sai ku tsare su a cikin gidãje har
mutuwa ta karɓi rãyukansu, ko kuwa Allah Ya sanya wata hanya a gare su.
Kuma waɗanda (mazã biyu) suka je mata daga ku, to, ku cũtar da su, sa'an nan
idan sun tũba kuma suka kyautata hãlãyensu, sai ku kau da kai da ga barinsu.
Lalle ne Allah Yã kasance Mai kaɓar tũba ne, Mai jin ƙai
Abar da take tũba kawai ga Allah, ita ce ga waɗanda suke aikatãwar mugun aiki da
jãhilci sa'an nan su tũba nan kusa to, waɗannan Allah Yanã karɓar tũ barsu kuma
Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.
Bã tũba ba ce ga waɗanda suke aikatãwar mũnanan ayyuka har idan mutuwa ta
halarci ɗayansu ya ce: "Lalle ne ni, na tũba yanzu," kuma bã tũba ba ce ga
waɗanda suke mutuwa alhãli kuwa sunã kãfi rai Waɗannan mun yi musu tattalin wata
azãba mai raɗaɗi
Ku waɗanda suka yi ĩmãni! Bã ya halatta a gare ku, ku gãji mãtã a kan tĩlas kuma
kadaku hana su aure dõmin ku tafi da sãshen abin da kuka ba su, fãce idan suka
zo da wata alfãsha bayya nanniya kuma ku yi zamantakẽwa da su da alhẽri sa'an
nan idan kun ƙĩ su, to akwai tsammãnin ku ƙi wani abu alhãli kuwa Allah Ya sanya
wani alhẽri mai yawaa cikinsa.
Kuma idan kun yi nufin musanya mãta a matsayin wata mãta, alhãli kuwa kun bai wa
ɗayarsu ƙinɗari to kada ku karɓi kõme daga gare, shi, shin, zã ku karɓe shi da
ƙarya da zunubi bãyyananne?
Kuma kada ku auri abin da ubanninku suka aura daga mãtã, fãce abin da ya shige.
Lalle ne shi, ya kasance alfãsha da abin ƙyãma. Kuma ya mũnana ya zama hanya.
An haramta muku uwãyenku, da 'yã'yanku, da 'yan'uwanku mãtã, da goggonninku, da
innoninku, da 'yã'yan ɗan'uwa, da 'ya'yan 'yar'uwa, da uwãyenku waɗanan da suka
shãyar da ku mãma, da 'yan'uwanku mãtã na shan mãma, da uwãyen mãtanku, da
agõlolinku waɗanda suke cikin ɗãkunanku daga mãtanku, waɗanda kuka yi duhũli da
su, kuma idan ba ku yi duhũli da sũ ba, to, bãbu laifi a kanku, da mãtan
'yã'yanku waɗanda, suke daga tsatsonku, kuma kada ku haɗa tsakanin 'yan'uwa biyu
mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne, Allah Yã kasance Mai gãfara ne Mai jin
ƙai.
Da tsararrun auren wasu maza, fãce dai abin da hannuwanku suka mallaka. (Ku
tsare) Littãfin Allah a kanku. Kuma an halatta muku abin da yake bayan wancan.
Ku nẽma da dukiyõyinku, kunã mãsu yin aure, bã mãsu yin zina ba. sa'an nan abin
da kuka ji daɗi da shi daga gare su, to, ku bã su ijãrõrinsu bisa farillar
sadãki. Bãbu laifia gare ku ga abin da kuka yi yardatayya da shi a bãyan
farillar sadãki. Lalle ne Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.
Kuma wanda bai sãmi wadãta ba daga cikinku bisa ga ya auri 'ya'ya mũminai, to,
(ya aura)daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, daga kuyanginku mũminai.
Kuma Allah ne Mafi sani ga ĩmãninku, sãshenku daga sãshe. Sai ku aurẽ su da
izinin mutãnensu. Kuma ku bã su ijãrõrinsu bisa ga abin da aka sani, suna mãsu
kamun kai bã mãsu zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. To, idan aka aure su,
sai kuma suka zo da wata alfãsha, to, akwai a kansu rabin abin da ko a kan,
'ya'ya daga azãba. wancan (auren kuyanga) ga wanda ya ji tsõron wahala ne daga
gare ku. Kuma ku yi haƙuri shi ne mafi alhẽri a gare ku. Kuma Allah Mai gãfara
ne Mai jin ƙai.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci dũkiyõyinku a tsakãninku da yaudara,
fãce idan ya kasance, daga fatauci ne, bisa yardatayya daga gare ku. Kuma kada
ku kashe kãnku. Lalle ne Allah Yã kasance, game da ku, Mai jin ƙai ne.
Kuma kada ku yi gurin abin da Allah Ya fifita sãshenku da shi a kan sãshe; maza
suna da rabo daga abin da suka tsirfanta, kuma mãtã suna da rabo daga abin da
suka tsirfanta. Ku rõƙi Allah daga falalarSa. Lalle ne Allah Yã kasance ga
dukkan kõme, Masani.
Kuma ga kõwa, Mun sanya magada daga abin da mahaifa da mafiya kusancin zumunta
suka bari. Kuma waɗanda rantsuwõyinku suka ƙulla ku bã su rabonsu. Lalle ne,
Allah Yã kasance, a kan dukkan kõme, Mahalarci.
Maza mãsu tsayuwa ne a kan mãtã, sabõda abin da Allah Ya fifita sãshensu da shi
a kan sãshe kuma sabõda abin da suka ciyar daga dũkiyõyinsu. To, sãlihanmãtã
mãsu ɗã'a ne, mãsu tsarẽwa ga gaibi sabõda abin da Allah Ya tsare. Kuma waɗanda
kuke tsõron bijirewarsu, to, ku yi musu gargaɗi, kuma ku ƙaurace musu a cikin
wurãren kwanciya, kuma ku dõke su. Sa'an nan kuma, idan sun yi muku ɗa'a, to,
kada ku nẽmiwata hanya a kansu. Lalle ne Allah Yã kasance Maɗaukaki, Mai girma.
Kuma idan kun ji tsõron sãɓãwar tsakãninsu to ku aika da wani mai sulhu daga
mutãnensa da wani mai sulhu daga mutãnenta. Idan sun yi nufin gyãrãwa, Allah zai
daidaita tsakãninsu (ma'auran). Lalle ne Allah Yã kasance Masani Mai jarrabãwa.
Kuma ku bauta wa Allah kuma kada ku haɗa wani da Shi, kuma ga mahaifa ku yi
kyautatãwa, kuma ga ma'abũcin zumunta da marãyu da matalauta, da maƙwabci
ma'abũcin kusanta, da maƙwabci manĩsanci, da abõki a gẽfe da ɗan hanya, da abin
da hannuwanku na dãma suka mallaka. Lalle ne Allah bã Ya son wanda ya kasance
mai tãƙama, mai yawan alfahari.
Waɗanda suke yin rõwa, kuma sunã umurnin mutãne da yin rõwa, kuma suna ɓõyewar
abin da Allah Ya bã su na falalarSa. Kuma Mun yi tattali, sabõda kãfirai, azãba
mai walãkantarwa.
Kuma waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu dõmin nũna wa mutãne, kuma bã su yin
ĩmãni da Allah, kuma bã su yin ĩmãnida Rãnar Lãhira kuma wanda Shaiɗan ya
kasance abõkin haɗi a gare shi, to, yã mũnana ga abõkinhaɗi.
Kuma mẽne ne a kansu, idan sun yi ĩmãni da Allah, kumada Rãnar Lãhira, kuma sun
ciyar da abin da Allah Yã azurtã su, kuma Allah Ya kasance, gare su, Masani?
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kusanci salla alhãli kuwa kuna mãsu mãye,
sai kun san abin da kuke faɗa kuma haka idan kuna mãsu janaba, fãce mai ƙẽtare
hanya, har ku yi wanka. Kuma idan kun kasance majinyata, ko kuwa a kan tafiya ko
kuwa wani daga cikinku, idan ya zo daga kãshi, kõ kuwa kun shãfi mãtã ba ku sãmi
ruwa ba, to ku nufi, fuskar ƙasa mai kyau, ku yi shãfa ga fuskokinku da
hannuwanku . Lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfẽwa Mai gãfara.
Daga waɗanda suka tũba (Yahũdu), akwai wasu sunã karkatar da magana daga
wurãrenta suna cẽwa: "Munjiya kuma mun ƙiya, kuma ka jiya a wani wurin jiyãwa,
kuma rã'ina (da ma'anar 'ruɓaɓɓe'), ka tsare mu," dõmin karkatarwa da
harsunansu, kuma dõmin sũkã a cikin addini. Kuma dã lalle sũ, sun ce: "Mun jiya
kuma mun yi ɗa'a, kuma ka saurãra kuma ka dãkata mana," haƙĩƙa, dã ya kasance
mafi alhẽri a gare su, kuma mafi daidaita; amma Allah Yã la'anẽ su, sabõda
kãfircinsu don haka bã zã su yi ĩmãni ba, sai kaɗan.
Yã kũ waɗanda aka bai wa Littãfi! Ku yi ĩmãni da abinda Muka saukar, yana mai
gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, tun gabanin Mu shãfe wasu fuskõki, sa'an
nan Mu mayar da su a kan bãyayyakinsu, ko Mu la'ane su kamar yadda Muka la'ani
masu Asabar. Kuma umurnin Allah ya kasance abin aikatãwa.
Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki game da Shi, kuma Yana gãfarta abin da
yake bãyan wannan ga wanda Yake so, kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle
ne ya ƙirƙiri zunubi mai girma.
Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke tsarkake kansu? Ã'a, Allah ne Yake
tsarkake wanda Yake so. Kuma ba za a zalunce su da zaren gurtsun dabĩno ba.
Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka bai wa rabõ da ga Littafi suna ĩmãni da
gunki da Shaiɗan kuma suna cẽwa ga waɗanda suka kãfirta: "Waɗannan ne mafiya
shiriya daga waɗanda suka yi ĩmãni ga hanya"?
Ko suna hãsadar mutãne ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle
ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfida hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.
Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ayõyinMu za Mu ƙõne su da wuta, kõ da yaushe
fãtunsu suka nuna, sai Mu musanya musu wasu fãtun, dõmin su ɗanɗani azãba. Lalle
ne Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.
Kuma waɗanda suka yiĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, zã Mu shigar da su
gidãjen Aljanna, (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã dawwamammu
a cikinsu har abada suna da, a cikinsu, mãtan aure mãsu tsarki, Kuma Munã shigar
da su a wata inuwa matabbaciyar lumshi.
Lalle ne Allah Yanã umurnin ku ku bãyar da amãnõni zuwa ga mãsu sũ. Kuma idan
kun yi hukunci a tsakãnin mutãne, ku yi hukunci da ãdalci. Lalle ne Allah
mãdalla da abin da Yake yi muku wa'azi da shi. Lalle ne Allah Yã kasance Mai ji
ne, Mai gani.
Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da
ma'abũta al'amari daga cikinku. Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku
mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da
Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.
Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke riyãwar cẽwa sunã ĩmãni da abin da aka
saukar zuwa gare ka da abin da aka saukar daga gabãninka, sunã nufin su kai ƙãra
zuwa ga ¦ãgũtu alhãli kuwa, lalle ne, an umurce su da su kãfirta da shi, kuma
Shaiɗan yanã nẽman ya ɓatar da su, ɓatarwa mai nĩsa.
To, yaya, idan wata masĩfa ta sãme su, sabõda abin da hannuwansu suka gabãtar
sa'an nan kuma su je maka sunã rantsuwa da Allah cẽwa, "Ba mu yi nufin kõme ba
sai kyautatawa da daidaitãwa."?
Waɗannan ne waɗanda Allah Ya san abin da ke cikin zukãtansu. Sabõda haka ka kau
da kai daga gare su, kuma ka yi musu gargaɗi, kuma ka gaya musu, a cikin
sha'anin kansu, magana mai nauyi da fasãha.
Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba fãce dõmin a yi masa ɗã'a da izinin Allah. Kuma dã
dai lalle sũ a lõkacin da suka zãlunci kansu, sun zo maka sa'an nan suka nẽmi
gãfarar Allah kuma Manzo ya nẽma musu gãfara, haƙĩƙa, dã sun sãmi Allah Mai
karɓar tũba Mai jin ƙai.
To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da
hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa'an nan kuma ba su sãmi wani ƙunci
a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamãwa.
Kuma dã dai lalle Mũ, Mun wajabta musu cẽwa, "Ku kashe kanku, ko kuwa ku, fita
daga gidãjenku," dã ba su aikata shi ba, fãce kaɗan daga gare su. Kuma dã dai
lalle sũ sun aikata abin da ake yi musu gargaɗi da shi, haƙĩƙa, dã yã kasance
mafi alhẽri dagagare su, kuma mafi tsanani ga tabbatarwa.
Kuma waɗannan da suka yi ɗã'a ga Allah da Mazonsa, to, waɗannan sunã tãre da
waɗanda Allah Ya yi ni'ima a kansu, daga annabãwa da mãsu yawan gaskatãwa, da
masu shahãda da sãlihai. kuma waɗannan sun kyautatu ga zama abõkan tafiya.
Kuma lalle ne daga cikinku akwai mai fãsarwa . To idan wata masĩfa ta sãme ku,
sai ya ce: "Lalle ne, Allah Ya yi mini ni'ima dõmin ban kasance mahalarci tãre
da su ba."
Kuma lalle ne idan wata falala daga Allah ta sãme ku haƙĩƙa, tabbas, yanã cẽwa,
kamar wata sõyayya ba ta kasance a tsakãninku da shi ba: "Yã kaitona! Dã na zama
tãre da su dai, dõmin in rabonta da rabõ mai girma!"
Sai waɗanda suke sayar da rayuwar dũniya su karɓi ta Lãhira su yi yãƙi, a cikin
hanyar Allah. Kuma wanda ya yi yãki a cikin hanyar Allah to a kashe shi ko kuwa
ya rinjãya, sa'an nan zã Mu ba shi ijãra mai girma.
Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã ku yin yãƙi a cikin hanyar Allah, da waɗanda aka
raunanar daga maza da mata da yãra sunã cewa: "Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu
daga wannan alƙarya wadda mutãnenta suke da zãlunci, kuma Ka sanya mana
majiɓinci daga gunKa, kuma Ka sanya mana mataimaki daga gunKa."?
Waɗanda suka yi ĩmãni, sunã yãki a cikin hanyar Allah, kuma waɗanda suka kãfirta
sunã yãƙi a cikin hanyar ¦ãgũtu (Shaiɗan). To, ku yãƙi majiɓintan Shaiɗan. Lalle
ne kaidin Shaiɗan yã kasance mai rauni.
Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: "Ku kange hannuwanku, kuma ku
tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka."? To a lõkacin da aka wajabta musu yãƙi
sai ga wani ɓangare daga cikinsu sunã tsõron mutãne kamar tsõron Allah kõ kuwa
mafi tsanani ga tsõron, kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yãƙi a
kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa?"Ka ce: "Jin dãɗin
dũniya kaɗan ne, kuma Lãhira ce mafi alhẽri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma bã a
zãluntar ku da sĩlĩlin hancin gurtsun dabĩno!