Kuma suka ce: "Zukatanmu nã a cikin kwasfa daga abin da kake Kiran mu zuwa gare
shi, kuma a cikin kunnuwanmu akwai wani nauyi, kuma daga tsakaninmu da
tsakaninka akwai wani shãmaki. sahõda haka ka yi aiki, lalle mũ mãsu aiki ne."
Ka ce: "Nĩ mutum kawai ne kamarku, ãnã yin wahayi zuwa gare ni cẽwa abin
bautãwarku, abin bautãwa guda ne. Sai ku daidaitu zuwa gare Shi, kuma ku nẽmi
gafararSa." Kuma bone ya tabbata ga mãsu yin shirki.
Ka ce: "Ashe lalle kũ, haƙĩƙa, kunã kafurta a game da wanda Ya halitta kasã a
cikin kwanuka biyu, kuma kunã sanya Masa kĩshiyõyi? Wancan fa, shĩ ne Ubangijin
halittu."
Kuma Ya sanya, a cikinta, dũwatsu kafaffu daga samanta, kuma Ya sanya albarka a
cikinta, kuma Ya ƙaddara abũbuwan cinta a cikinta a cikin kwanuka huɗu mãsu
daidaita, dõmin matambaya.
Sa'an nan Ya daidaita zuwa ga sama alhãli kuwa ita (a lõkacin) hayãƙi ce, sai Ya
ce mata, ita da ƙasã "Ku zo, bisa ga yarda kõ a kan tĩlas." Suka ce: "Mun zo,
munã mãsu ɗã'ã. "
Sai Ya hukunta su sammai bakwai a cikin kwãnuka biyu. Kuma Ya yi wahayi, a cikin
kõwace sama da al'amarinta, kuma Muka kãwata sama ta kusa da fitilu kuma don
tsari. Wancan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani.
A lõkacin da Manzanninsu suka je musu daga gaba gare su kuma daga bãyansu, "Kada
ku bauta wa kõwa fãce Allah." suka ce: "Dã UbangiJinmu Yã so, lalle dã Ya saukar
da malã' iku, sabõda haka lalle mũ, mãsu kafirta ne a game da abin da aka aiko
ku da shi."
To, amma Ãdãwa, sai suka yi girman kai a cikin kasã, bã da wani hakki ba, suka
ce: "Wãne ne mafi tsananin ƙarfi daga gare mu?" Ashe, kuma ba su gani ba cẽwa
Allah, wanda Ya halitta su Shĩne Mafi ƙarfi daga gare su, kuma sun kasance a
game da ãyõyinMu suna yin musu?
Sai Muka aika, a kansu, da iska mai tsananin sauti da sanyi, a cikin kwãnuka na
shu'umci, dõmin Mu ɗanɗana musu azãbar wulãƙanci, a cikin rãyuwar dũniya, kuma
lalle azãbar Lãhira ita ce mafi wulãƙantarwa, kuma sũ bã zã a taimake su ba.
Kuma amma Samũdãwa, sai Muka shiryar da su, sai suka fi son makanta a kan
shiriya, dõmin haka tsawar azãbar wulãkanci, ta kamã su sabõda abin da suka
kasance sunã aikatãwa (dõmin nẽman wata fã'ida).
Kuma suka ce wa fãtunsu, "Don me kuka yi shaida a kanmu?" Suka ce: "Allah, Wanda
ke sanya kõwane abu ya yi furuci, Shĩ ne Ya sanya mu mu yi furuci, kuma Shĩ ne
Ya halitta ku can da farko, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku."
"Ba ku kasance kunã sani ba a ɓõye, cẽwa jinku zai yi shaida a kanku kuma
ganinku zai yi, kuma fãtunku za su yi. Kuma amma kun yi zaton cẽwã Allah bai san
abũbuwa mãsu yawa daga abin da kuke aikatãwa ba."
Kuma Muka sallaɗar da mabiya a gare su, sai suka ƙawãta musu abin da ke a
gabansu da abin da ke a bãyansu. Kuma kalmar azãba ta wajaba a kansu, a cikin
wasu al'ummõmi da suka shũɗe a gabãninsu daga aljannu da mutãne. Lalle sũ, sun
kasance mãsu hasãra.
Kuma waɗanda suka kafirta suka cc, "Kada ku saurãra ga wannan Alkur' ãni, kuma
ku yi ta yin kuwwa a ckin (lõkacin karãtun) sa, ɗammãninku zã ku rinjaya."
Sabõda haka, lalle zã Mu ɗanɗana wa waɗanda suka kafirta wata azãba mai tsanani,
kuma lalle zã Mu sãka musu da mafi mũnin abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Wancan shĩ ne sakamakon makiyan Allah, watau wuta. Sunã a gidan dawwama a
cikinta, dõmin sakamako ga abin da suka kasance sunã yin musu game da ãyõyinMu.
Kuma waɗanda suka kafirta suka ce: "Yã Ubangijinmu! Ka nũnã mana wadannan biyun
da suka batar da mu daga aljannu da mutãne, mu sanya su a karkashin, ƙafãfunmu,
dõmin su kasance daga ƙaskantattu."
Lalle waɗannan da suka ce: "Ubangjinmu, shĩ ne Allah," sa'an nan suka daidaitu,
malã'iku na sassauka a kansu (a lõkacin saukar ajalinsu sunã ce musu) "Kada ku
ji tsõro, kuma kada ku yi baƙin ciki, kuma ku yi bushãra da Aljanna, wadda kun
kasance anã yi muku wa'adi da ita."
"Mũ ne majibintanku a cikin rãyuwar dũniya da kuma a cikin Lãhira, kuma a
cikinta kunã da abin da rãyukanku ke sha'awa, kuma kunã da abin da kuke kira
(akawo muku) a cikinta.
Kuma wãne ne mafi kyau ga magana daga wanda ya yi kira zuwa ga Allah, kuma ya
aikata aiki na ƙwarai kuma ya ce: "Lalle nĩinã daga mãsu sallamãwar al'amari
zuwa ga Allah?"
Kuma kyautatãwa bã ta daidaita kuma haka mũnanãwa. Ka tunkuɗe cũta da abin da
yake mafi kyau, sai ga shi wanda akwai ƙiyayya a tsakaninka da tsakaninsa, kamar
dai shi majibinci ne, masoyi.
Kuma akwai daga ãyõyinSa, dare da yini, da rãnã da watã. Kada ku yi sujada ga
rãnã, kuma kada ku yi ga watã. Kuma ku yi sujada ga Allah wanda Ya halitta su,
idan kun kasance Shĩ ne kuke bauta wa.
Kuma akwai daga ãyõyinSa cẽwa lalle kai kanã ganin ƙasã ƙẽƙasasshiya, to, idan
Mun saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura. Lalle wannan da Ya
rãya ta, haƙĩƙa, Mai rãyar da matattu ne. Lalle Shĩ Mai ĩkon yi ne a kan kõwane
abu.
Lalle waɗannan da ke karkacẽwa a cikin ãyõyinMu, bã su fakuwa a gare Mu. Ashe
fa, wanda ake jẽfãwa a cikin Wutã ne mafĩfĩci kõ kuwa wanda zai je amintacce a
Rãnar ¡iyãma? Ku aikata abin da kuke so! Lalle Shĩ Mai gani ne ga abin da kuke
aikatãwa.
Bã zã a fada maka ba fãce abin da aka riga aka faɗa ga Manzannin da suke a
gabãninka. Lalle Ubangijinka, haƙĩƙa, Ma'abũcin gãfara ne, kuma Ma'abũcin azãba
mai raɗaɗi ne.
Kuma da Mun sanya shi abin karãtu na ajamanci, lalle dã sun ce, "Don me ba a
bayyana ãyõyinsa ba? Ashe, zai yiwu a sãmi littãfi ba'ajame da Manzo Balãrabe?"
Ka ce: "Shi, shiriya ne da warkewa ga waɗanda suka yi ĩmãni.Kuma wadanda ba su
yi ĩmãni ba akwai wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma shi wata makanta ne a
kansu. Waɗannan anã kiran su daga wuri mai nĩsa."
Kuma lalle Mun bai wa Mũsã Littãfi, sai aka yi ɗãɓãni a cikinsa, Kuma ba dõmin
wata kalma da tã gabata ba daga Ubangijinka, lalle dã an yi hukunci a
tsakãninsu. Kuma lalle sũ, haƙĩƙa sunã a cikin shakka daga, gare shi, mai sanya
kõkanto.
Zuwa gare Shi ake mayar da sanin Sa'a. Kuma waɗansu 'yã'yan itãce bã su fita
daga kwasfõfinsu, kuma wata mace bã ta yin ciki, kuma bã ta haihuwa, fãce da
saninSa, kuma a rãnar da Yake kiran su ( Ya ce): "Inã abõkan tãrayyaTa?" Sai su
ce, "Mun sanar da Kai bãbu mai bãyar da shaida da haka nan daga gare mu."
Kuma lalle idan Mun ɗanɗana masa wata rahama daga gareMu, daga bãyan wata cũta
ta shãfe shi, lalle zai ce, "Wannan (ni'ima) tãwa ce kuma bã ni zaton Sã'a mai
tsayuwa ce, kuma lalle idan aka mayar da ni zuwa ga Ubangijĩna, haƙĩƙa, inã da
makõma mafi kyau, a wurinSa." To, lalle zã Mu bã da lãbãri ga waɗanda suka
kãfirta game da abin da suka aikata, kuma lalle Munã ɗanɗana musu daga azãba,
Mai kauri.
Ka ce: "Ashe, kun gani! Idan (Alƙur'ãni) ya kasance daga Allah ne, sa'an nan kun
kãfirta a game da Shi, wãne ne mafi ɓata daga wanda yake yanã a cikin sãɓani
manisanci (daga gaskiya)?"
Zã Mu nũna musu ãyõyinMu a cikin sãsanni da kuma cikin rãyukansu, har ya bayyana
a gare su cẽwã lalle (Alƙur'ãni), shi ne gaskiya. Ashe, kuma Ubangijinka bai isa
ba, ga cẽwa lalle Shĩ halartacce ne a kan kowane abu ne?