Kuma da sãɓawar dare da yini da abin da Allah Ya saukar daga sama na arziki,
sa'an nan Ya rãyar da ƙasa game da shi a bãyan mutuwarta, da jũyawar iskõki,
akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali.
Gaba gare su (a Lãhira) akwai Jahannama, kuma abin da suka sanã'anta bã ya
wadãtar da su daga kõme, kuma abũbuwan da suka riƙa majiɓinta, baicin Allah, bã
su wãdatar da su daga kõme. Kuma sunã da wata azãba mai girma.
Kuma Ya hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasa, gabã
ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne
waɗanda ke yin tunãni.
Ka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, su yi gãfara ga waɗanda bã su fãtan rahama ga
kwãnukan Allah, dõmin (Allah) Ya sãka wa mutãne da abin da suka kasance sunã
aikatãwa.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai (wa Bãnĩ Isrã'ĩla Littãfi da hukunci da Annabci,
Kuma Mun azurta su daga abũbuwa mãsudãɗi, Kuma Mun fĩfta su a kan mutãnen dũniya
(a zãmaninsu).
Kuma Muka bã su hujjõji na umurni. Ba su sãɓa ba fãce bãyan ilmi ya jẽ musu,
sabõda zãlunci a tsakãninsu. Lalle ne, Ubangijinka zai yi hukunci a tsakãninsu,
a Rãnar ƙiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa (jũna).
Lalle ne sũ, bã zã su wadãtar da kai da kõme ba daga Allah. Kuma lalle ne
azzãlumai sãshensu majiɓintan sãshe ne. Kuma Allah ne Majiɓincin mãsu taƙawa.
Kõ waɗanda suka yãgi miyãgun ayyuka sunã zaton Mu sanyã su kamar waɗanda suka yi
ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, su zama daidai ga rãyuwarsu da
mutuwarsu? Abin da suke hukuntãwa yã mũnanã!
Alhãli kuwa Allah ne Ya halitta sammai da ƙasã sabõda gaskiya, Kuma dõmin a sãka
wa kõwane rai da abin da ya sanã'anta, kuma su, bã zã a zãlunce su ba.
Shin, kã ga wanda ya riƙi son zũciyarsa sĩh ne abin bautawarsa, kuma Allah Ya
ɓatar da shi a kan wani ilmi, Kuma Ya sa hatini a kan jinsa, da zũciyarsa, kuma
Ya sa wata yãnã ã kan ganinsa? To, wãne ne zai shiryar da shi bãyan Allah? Shin
to, bã zã ku yi tunãni ba?
Kuma suka ce: "Bãbu kõme fãce rãyuwarmu ta dũniya; munã mutuwa kuma munã rãyuwa
(da haihuwa) kuma bãbu abin da ke halaka mu sai zãmani." Alhãli kuwa (ko da suke
faɗar maganar) bã su da wani ilmi game da wannan, bã su bin kõme face zato.
Kuma idan anã karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu, bãbu abin da ya kasance
hujjarsu fãce suka ce: "Ku zo mana da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."
Ka ce: "Allah ne ke rãyar da ku kuma Shĩ ne ke matarda ku, sa'an nan Ya tãra ku
zuwa ga Rãnar ¡iyãma, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne ba su
sani ba."
"Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne, Shĩ kaɗai. Kuma rãnar da Sa'a ke
tsayuwa, a rãnar nan mãsu ɓãtãwã (ga hujjõjin Allah dõmin su ki bin sharĩ'arSa)
zã su yi hasãra."
Kuma zã ka ga kõwace al'umma tanã gurfãne, kõwace al'umma anã kiran ta zuwa ga
littãfinta. ( A ce musu) "A yau anã sãka muku da abin da kuka kasance kunã
aikatãwa."
Kuma amma waɗanda suka kãfirtã (Allah zai ce musu): "Shin, ãyõyĩNã ba su kasance
anã karãnta su ã kanku ba sai kuka kangare, Kuma kuka kasance mutãne mãsu
laifi?"
"Kuma idan aka ce, lalle wa'ãdin Allah gaskiya ne, kuma Sa'a, bãbu shakka a
cikinta sai kuka ce, 'Ba mu san abin da ake cẽwa Sa'a ba, bã mu zãto (game da
ita) fãce zato mai rauni, Kuma ba mu zama mãsu yaƙni ba."'
"Wancan dõmin lalle kũ, kun riƙi ãyõyin Allah da izgili, Kuma rãyuwar dũniya ta
rũɗe ku. To, a yau bã zã su fita daga gare ta ba, Kuma bã zã su zama waɗanda ake
nẽman yardarsu ba."