Wannan kuwa sabõda lalle, waɗanda suka kãfirta sun bi ƙarya, kumar lalle waɗanda
suka yi ĩmãni, sun bi gaskiya daga Ubangijinsu. Kamar wannan ne Allah Yake
bayyana wa mutãne misãlansu.
Sabõda haka idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta, sai ku yi ta dũkan wuyõyinsu
har a lõkacin da suka yawaita musu kisa, to, ku tsananta ɗaurinsu sa'an nan imma
karimci a bãyan' haka kõ biyan fansa, har yãƙi ya saukar da kayansa mãsu nauyi.
Wancan, dã Allah nã so da Ya ci nasara a kansu (ba tare da yaƙin ba) kuma amma
(ya wajabta jihadi) dõmin Ya jarraba sãshenku da sãshe. Kuma waɗanda zaka kashe
a cikin tafarkin Allah, to, bã ai ɓatar da ayyukansu ba.
Shin, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa, dõmin su gani yadda ãƙibar waɗanda ke a
gabãninsu ta kasance? Allah Ya darkãke a kansu. Kuma akwai misãlan wannan ãƙibar
ga kãfirai (na kõwane zãmani).
Lalle ne, Allah nã shigar da waɗanda suka yi ĩmani kuma suka aikata ayyukan
ƙwarai a gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudana daga ƙarƙashinsu, kuma waɗanda
suka kãfirta sunã jin ɗan daɗi (adũniya) kuma sunã ci, kamar yadda dabbõbi ke
ci, kuma wutã ita ce mazauni a gare su.
Kuma da yawa akwai alƙarya, ita ce mafi tsanani ga ƙarfi daga alƙaryarka wadda
ta fitar da kai, Mun halaka ta, sa'an nan kuwa bãbu wani mai taimako a gare su.
Misãlin Aljanna, wadda aka yi wa'adinta ga mãsu taƙawa, a cikinta akwai waɗansu
kõguna na ruwa ba mai sãkẽwa ba da waɗansu kõguna na madara wadda ɗanɗanonta bã
ya canjãwa, da waɗansu kõguna na giya mai dãɗi ga mashãya, da waɗansu kõguna na
zuma tãtacce kuma suna sãmu, a cikinta, daga kõwane irin 'ya'yan itãce, da wata
gãfara daga Ubangijinsu. (Shin, mãsu wannan ni'ima nã daidaita) kamar wanda yake
madawwami ne a cikin wutã kuma an shãyar da su wani ruwa mai zãfi har ya
kakkãtse hanjinsu?
Kuma daga cikinsu akwai wanda ke saurare zuwa gare ka, har idan sun fita daga
wurinka, su ce wa waɗanda aka bai wa ilmi "Mẽne ne ( Muhammadu) ya fãɗa ɗazu?"
Waɗannan ne waɗanda Allah Ya shãfe haske daga zukãtansu, kuma suka bi son
zũciyõyinsu.
Sabõda hakaa ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa fãce Allah, kuma ka nẽmi gãfara ga
zunubin, ka, (kuma sabõda mũminai maza da mũminai mãtã kuma Allah Ya san
majũyaiku da mazauninku.
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cẽwa: "Don mẽne ne ba a saukar da wata sũra ba?
"To idan aka saukar da wata sũra, bayyananna, kuma aka ambaci yãƙi a cikinta, zã
ka ga waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukatansu sunã kallo zuwa gare ka,
irin kallon wanda aka rufe da mãgãgi sabõda mutuwa. To, abin da yake mafĩfĩci a
gare su:
Wancan, dõmin lalle sũ sun ce wa waɗanda suka ƙi abin da Allah Ya saukar: "Za mu
yi muku ɗã'ã ga sãshen al'amarin," alhãli kuwa Allah Yanã sane da gãnawarsu ta
asĩri.
Kuma dã Munã so, dã lalle Mun nũna maka su. To, lalle kanã sanin su game da
alãmarsu. Kuma lalle kanã sanin su ga shaguɓen magana, alhali kuwa Allah Yanã
sanin ayyukanku.
Lalle ne, waɗanda suka kãfirta, kuma suka kange daga tafarkin Allah, kuma suka
saɓa wa Manzon sa a bãyan shiriyar ta bayyana a gare su, bã za su cũci Allah da
kõme ba, kuma zã Ya ɓãta ayyukansu.
Lalle ne waɗanda suka kãfirta sa'an nan kuma suka kange (mutãne) daga tafarkin
Allah, sa'an nan suka mutu, alhãli kuwa sunã kãfirai, to, Allah bã zai yi gãfara
ba a gare su.
Sabõda haka kada ku yi rauni, kuma (kada) ku yi kira zũwaga sulhi alhãli kuwa kũ
ne mafiɗaukaka kuma Allah na tãre da ku, kuma bã, zai naƙasa muku ayyukanku ba.
Rãyuwar dũniya, wãsã da abin shagala kawai ce, kuma idan kun yi ĩmãni, kuma kun
yi taƙawa, Allah zai kãwo muku ijarõrinku, kuma bã zai tambaye ku dũkiyarku ba.
Ga ku, ya ku waɗannan! Anã kiran ku dõmin ku ciyar ga tafarkin Allah, sa'an nan
daga cikinku akwai mai yin rõwa. Kuma wanda ke yin rõwa, to, yanã yin rõwar ne
ga kansa. Kuma Allah ne wadãtacce alhãli kuwa kũ fãƙĩrai ne. Kuma idan kuka jũya
(daga yi Masa ɗã'a), zai musanya waɗansu mutãne waɗansunku sa'an nan bã zã su
kasance kwatankwacinku ba.