Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! ku cika alkawurra. An halatta muku dabbobin jin
dãɗi fãce abin da ake karantãwa a kanku, bã kunã mãsu halattar da farauta ba
alhãli kuwa kunã mãsu harama. Lalle ne, Allah Yanã hukunta abin da yake nufi.
Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! kada ku halattar da ayyukan ibãdar Allah game da
hajji, kuma da watã mai alfarma, kuma da hadaya, kuma da rãtayar raƙuman hadaya,
kuma da mãsu nufin ¦ãki mai alfarma, sunã neman falala daga Ubangijinsu da
yarda. Kuma idan kun kwance harama, to, ku yi farauta. Kuma kada ƙiyayya da wasu
mutãne ta ɗauke ku, dõmin sun kange ku daga Masallãci Mai alfarma, ga ku yi
zãlunci. Kuma ku taimaki junã a kan aikin ƙwarai da taƙawa. Kuma kada ku taimaki
juna a kan zunubi da zãlunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai
tsananin uƙũba ne.
An haramta muku mũshe da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin
Allah a gare shi, da mãƙararriya da jefaffiya da mai gangarõwa da sõkakkiya, da
abin da mãsu dãgi suka ci, fãce abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan
gunki (shĩ ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na cãca wannan
fãsiƙanci ne, A yau waɗanda suka kãfirta sun yanke ƙauna daga addininku. Sabõda
haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõroNa. A yau Nã kammalã muku addininku,
Kuma Nã cika ni'imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare
ku. To, wanda aka sanya wa lalũra a cikin yunwa mai tsanani, bã yana mai karkata
zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Suna tambayar ka cewa mene ne aka halatta musu? Ka ce: "An halatta muku abũbuwa
mãsu dãɗi da abin da kuka sanar (farauta) daga mãsu yin mĩki, kunã mãsu sakinsu
daga hannuwanku, kunã sanar da su daga abin da Allah Ya sanar da ku. To, ku ci
daga abin da suka kama sabõda ku, kuma ku ambaci sunan Allah a kansa, kuma ku bi
Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai gaugawar sakamako da yawã ne.
A yau an halatta muku abũbuwa mãsu dãɗi kuma abincin waɗanda aka bai wa Littãfi
halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su, da mãtã mãsu kãmun kai
daga muminai da mãtã 'yã'ya daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku idan kun
je musu da sadãkõkinsu, kuna mãsu yin aure, ba masu yin zina ba, kuma bã mãsu
riƙon abõkai ba. Kuma wanda ya kãfirta da ĩmãni to, lalle ne aikinsa yã ɓãci,
kuma shĩ, a cikin Lãhira, yanã daga mãsu hasãra.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni ! idan kun tãshi zuwa ga salla, to, ku wanke
fuskõkinku da hannuwanku zuwa ga magincirõri, kuma ku yi shãfa ga kãnunku, kuma
ku (wanke) ƙafãfunku zuwa idãnun sãwu biyu. Kuma idan kun kasance mãsu janaba,
to, ku yi tsarki, kuma idan kun kasance majinyata, kõ kuwa a kan tafiya, kõ kuwa
ɗaya daga gare ku ya zo daga kãshi, kõ kuka yi shãfayyar junã da mãtã, sa'an nan
ba ku sãmi ruwa ba to ku yi nufin wuri mai kyau, sa'an nan ku yi shãfa ga
fuskõkinku da hannuwanku daga gare shi. Allah bã Ya nufi dõmin Ya sanya wani
ƙunci a kanku, kuma amma Yanã nufi dõmin Ya cika ni'imarSa a kanku, tsammãninku
kunã gõdewa.
Kuma ku tuna ni'imar Allah akanku da alkawarinku wanda Ya ɗaure ku da shi, a
lõkacin da kuka ce: "Mun ji kuma mun yi ɗã'a Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle
ne Allah Masani ne ga abin da ke a cikin zukata."
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayin daka dõmin Allah mãsu shaida
da ãdalci. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutane ta ɗauke ku a kan bã zã ku yi ãdalci
ba. Ku yi ãdalci Shĩ ne mafi kusa ga taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle
Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da wasu
mutãne suka yi niyyar su shimfiɗa hannuwansu zuwa gare ku sai Ya kange
hannuwansu daga gare ku, kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma sai muminai su dogara
ga Allah kawai.
Kuma lalle Allah Yã riƙi alkawarin Banĩ lsrã' ĩla kuma Muka ayyana wakilai gõma
shã biyu daga gare su kuma Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Inã tãre da ku, haƙĩƙa,
idan kun tsayar da salla, kuma kun bãyar da zakka, kuma kun yi ĩmani da
manzannĩNa, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙĩƙa,
Inã kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙĩƙa, Inã shigar da ku gidãjen
Aljanna (waɗanda) ƙõramu sanã gudãna a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kãfirta a
bãyan wannan daga gare ku, to, lalle ne, yã ɓace daga tsakar hanya."
To, sabõda warwarewarsu ga alkawarinsu Muka la'ane su, kuma Muka sanya zukãtansu
ƙeƙasassu, sunã karkatar da magana daga wurãrenta, kuma suka manta da wani yanki
daga abin da aka tunãtar da su da shi, kuma bã zã ka gushe ba kana tsinkãyar
yaudara daga gare su fãce kaɗan daga gare su. To, ka yãfe laifi daga gare su,
kuma ka kau da kai. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu kyautatãwa.
Kuma daga waɗanda suka ce: "Lalle ne mu Nasãra ne" Mun riƙi alkawarinsu, sai
suka manta da wani yanki daga abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka
shushuta adãwa da ƙeta a tsakãninsu har ya zuwa ga Rãnar ¡iyãma. Kuma Allah zai
bã su lãbari da abin da suka kasance sunã sanã'antawa.
Yã Mutãnen littãfi! Lalle ne, ManzonMu yã je muku, yanã bayyana muku abu mai
yawa daga abin da kuka kasance kunã ɓõyewa daga Littãfi, kuma yanã rangwame daga
abu mai yawa. Haƙĩƙa,wani haske da wani Littafi mai bayyanãwa yã je muku daga
Allah.
Dashĩ, Allah Yanã shiryar da wanda ya bi yardarsa zuwa ga hanyõyin aminci, kuma
Yanã fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izninsa, kuma Yanã shiryar da su
zuwa ga hanya madaidaiciya.
Lalle haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle Allah Shĩ ne Masĩhu ɗan Maryama," sun
kãfirta. Ka ce: "To, wane ne ke iya mallakar wani abu daga Allah, idan Yã nufi
Ya halakar da Masĩhu ɗanMaryama da uwarsa da wanda yake a cikin ƙasa gabã ɗaya?"
Kuma Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, Yanã
halitta abin da Yake so. Kuma Allah a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne.
Kuma Yahudu da Nasãra sun ce: "Mu ne ɗiyan Allah, kuma masõyansa." Ka ce: "To,
don me Yake yi muku azãba da zunubanku? Ã'a ku mutãne ne daga waɗanda Ya
halitta, Yanã gãfartãwa ga wanda Yake so, kuma Yanã azabta wanda Yake so. Kuma
Allah ne da mulkin sammai da ƙasa da abin da ke tsakãninsu kuma zuwa gare shi
makomã take."
Yã Mutãnen Littãfi! Lalle ManzonMu yã je muku yanã bayyana muku, a kan lõkacin
fatara daga manzanni, dõmin kada ku ce: "wani mai bayar da bushãra bai zo mana
ba, kuma haka wani mai gargaɗi bai zo ba." To, haƙĩƙa, mai bãyar da bushãra da
mai gargaɗi sunje muku. Kuma Allah ne, a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi.
Kuma a lõkacin da Musa ya ce wa mutãnensa: "Yã ku mutãnena! Ku tuna ni'imar
Allah a kanku; dõmin Yã sanya annabãwa a cikinku, kuma Yã sanya ku sarãkuna,
kuma Yã bã ku abin da bai bai wa kõwa ba daga tãlikai."
Suka ce: "Ya Musã! Lalle ne, a cikinta akwai wasu mutãne mãsu ƙarfi kuma lalle
ne bã zã mu shige ta ba sai sun fice daga gare ta, to, idan sun fice daga gare
ta, to, lalle ne mu, masu shiga ne."
Wasu maza biyu daga waɗanda suke tsõron Allah, Allah Yã yi ni'ima a kansu, suka
ce: "Ku shiga gare su, daga ƙõfar, dõmin idan kuka shige shi, to, lalle ne ku,
mãsu rinjãya ne, kuma ga Allah sai ku dogara idan kun kasance muminai."
Suka ce: "Ya Musa! Lalle ne mu, bã za mu shige ta ba har abada matuƙar sun
dawwama a cikinta sai ka tafi kai da Ubangijinka dõmin ku yi yãƙi. Lalle ne mu,
munã a nan zaune."
(Allah) Ya ce: "To, lalle ne ita abar haramtãwa ce a gare su, shekara arba'in,
sunã yin ɗimuwa a cikin ƙasa. Sabõda haka kada ka yi baƙin ciki a kan mutãne
fãsiƙai."
Kuma karantã musu lãbãrin ɗiya biyu na Ãdamu, da gaskiya, a lõkacin da suka
bãyar da baiko, sai aka karɓa daga ɗayansu kuma ba a karɓa daga ɗayan ba, ya ce:
"Lalle ne zan kashe ka." (¦ayan kuma) ya ce: "Abin sani dai, Allah Yana karɓã
daga mãsu taƙawa ne."
"Lalle ne idan ka shimfiɗa hannunka zuwa gare ni dõmin ka kashe ni, ban zama mai
shimfiɗa hannuna zuwa gare ka ba dõmin in kashe ka. Lalle ne nĩ inã tsõron Allah
Ubangijin tãlikai.
Sai Allah Ya aiki wani hankãka, yanã tõno a cikin ƙasa dõmin ya nuna masa yadda
zai turbuɗe gãwar ɗan'uwansa. Ya ce: "Kaitõna! Nã kãsa in kasance kamar wannan
hankãka dõmin in turbuɗe gãwar ɗan'uwana?" Sai ya wãyi gari daga mãsu nadãmã.
Daga sababin wannan, Muka rubuta a kan Banĩ lsrã'ĩla cewa, lalle ne wanda ya
kashe rai bã da wani rai ba, ko ɓarna a cikin ƙasa, to kamar yã kashe mutãne
duka ne, kuma wanda ya rãya rai, to, kamar yã rãyar da mutãne ne gabã ɗaya. Kuma
lalle ne, haƙĩƙa, ManzanninMu sun je musu da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuma
lalle ne, mãsu yawa daga gare su, a bãyan wannan, haƙĩƙa, mãsuɓarna ne a cikin
ƙasa.
Abin sani kawai sakamakon waɗanda suke Yãƙin Allah da Manzonsa, kuma sunã aiki a
cikin ƙasa dõmin ɓarna a kashe su ko kuwa a ƙere su, kõ kuwa a kakkãtse
hannuwansu da ƙafãfunsu daga sãɓãni, ko kuwa a kõre su daga ƙasa. Sannan gare su
wulakanci ne a cikin rãyuwar duniya, kuma a Lãhira sunã da wata azãba mai girma.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku nemi tsari zuwa gare
shi, kuma ku yi jihãdi a cikin hanyarsa, tsammãninku, za ku ci nasara.
Lalle ne waɗanda suka kãfirta, lalle dã sunã da abin da ke a cikin ƙasa gabã
ɗaya da misãlinsa tãre da shi, dõmin su yi fansa da shi daga azãbar Rãnar
¡iyãma, bã a karɓarsa daga gare su, kuma sunã da azãba mai raɗadi.
Shin, ba ka sani ba cewa lalle ne, Allah Shi ne da mulkin sammai da ƙasa, Yanã
azãbtar da wanda Yake so, kuma Yanã yin gãfara ga wanda yake so, kuma Allah a
dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne?
Yã kai Manzo! Kada waɗanda suke tseren gaugawa a cikin kãfirci su ɓãta maka rai,
daga waɗanda suka ce: "Mun yi ĩmãni" da bãkunansu, alhãli zukatansu ba su yi
ĩmãnin ba, kuma daga waɗanda suka tuba (watau Yahudu) mãsu yawan saurare ga wasu
mutane na dabam waɗanda ba su je maka ba, sunã karkatar da zance daga bãyan
wurarensa, sunã cewa: "Idan an bã ku wannan, to, ku karɓa, kuma idan ba a bã ku
shĩ ba, to, ku yi sauna."Kuma wanda Allah Ya yi nufin fitinarsa, to bã zã ka
mallaka masa kõme ba, daga Allah. Waɗannan ne waɗanda Allah bai yi nufin Ya
tsarkake zukãtansu ba. Sunã da kunya a cikin duniya, kuma sunã da wata azãba mai
girma a cikin 1ãhira.
Mãsu yawan saurãre ga ƙarya ne, mãsu yawan ci ga haram, to, idan sun zo maka,
sai ka yi hukunci a tsakãninsu kõ ka bijira daga gare su. Kuma idan ka bijira
daga gare su, to, bã zã su cuce ka da kõme ba, kuma idan ka yi hukunci, to, sai
ka hukunta a tsakãninsu da ãdalci. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu ãdalci.
Kuma yãya suke gabãtar da kai ga hukunci, alhãli a wurinsu akwai Attaura, a
cikinta akwai hukuncin Allah, sa'an nan kuma sunã karkacewa a bãyan wannan?
waɗannan bã muminai ba ne!
Lalle ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske Annabãwa
waɗanda suke sun sallamã, sunã yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu),
da mãlaman tarbiyya, da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga
Littãfin Allah, kuma sun kasance, a kansa, mãsu bã da shaida. To, kada ku ji
tsõron mutãne kuma ku ji tsõroNa kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyoyiNa.
wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne kafirai.
Kuma Mun rubuta a kansu, a cikinta cewa, lalle (anã kashe) rai sabõda rai, kuma
(anã ɗebe) idõ sabõda idõ, kuma (ana katse) hanci sabõda hanci, kuma kunne
sabõda kunne kuma haƙori sabõda haƙõri kuma a raunuka a yi sakayya. To, wanda ya
yi sadaka da shi, to, shi kaffãra ce a gare shi. Kuma wanda bai yi hukunci ba da
abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne azzãlumai.
Kuma Muka biyar a kan gurãbansu da Ĩsa ɗan Maryama, yãnã mai gaskatãwa ga abin
da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma Muka bã shi Injĩla a cikinsa akwai
shiriya da haske, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga
Attaura, kuma shi shiriya ne da wa'azi ga mãsu taƙawa.
Kuma sai mutãnen injĩla su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a cikinta. Kuma
wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to, waɗannan su ne fãsiƙai.
Kuma Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka da gaskiya, yanã mai gaskatãwa ga abin
da yake a gaba gare shi daga Littãfi (Attaura da Injĩla), kuma mai halartãwa a
kansa. sai ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka
bĩbiyi son zũciyõyiniu daga abin da ya zo maka daga gaskiya . Ga kõwanne daga
gare ku Mun sanya sharĩa da hanya (ta bin ta). Kuma dã Allah Yã so, dã Yã sanya
ku al'umma guda, kuma amma dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku. Sai ku
yi tsere ga ayyukan alheri. Zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya
bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance kunã sãɓãwa a cikinsa.
Kuma ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi
son zũciyõyinsu, kuma ka yi saunar su fitine ka daga sãshen abin da Allah Ya
saukar zuwa gare ka. To, idan sun juya bãya, to, ka sani cewa, kawai Allah yana
nufin Ya sãme su da masĩfa ne sabõda sãshen zunubansu. Kuma lalle ne, mãsu yawa
daga mutãne, haƙĩƙa, fãsiƙai ne.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi Yahudu da Nasãra majiɓinta. Sãshensu
majiɓinci ne ga sãshe. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shĩ,
yanã daga gare su. Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
Sai ka ga waɗanda a cikin zukatansu akwai cuta, sunã tseren gaugawa a cikinsu,
sunã cewa: "Munã tsõron kada wata masĩfa ta sãme mu." To, akwai tsammãnin Allah
Ya zo da buɗi, kõ kuwa wani umurni daga wurinSa, har su wãyi gari a kan abin da
suka ɓõye a cikin zukatansu, sunã mãsu nadãmã.
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cewa: "Shin, waɗannan ne waɗanda suka yi
rantsuwa da Allah iyãkar rantsuwõyinsu, cewa su, lalle sunã tãre da ku?"
Ayyukansu sun ɓãci, sabõda haka suka wãyi gari sunã mãsu hasãra.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! wanda ya yi ridda daga gare ku daga addininSa, to,
Allah zai zo da wasu mutãne, Yanã son su kuma sunã son Sa, mãsu tawãlu'i a kan
muminai mãsu izza a kan kãfurai. Sunã yin, jihãdi a cikin hanyar Allah, kuma bã
su tsõron zargin wani mai zargi. Waccan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga
wanda Yake so. Kuma Allah Mayalwaci ne, Mai ilmi.
Abin sani kawai, majiɓincinku Allah ne da ManzonSa da waɗanda suka yi
ĩmãni,waɗanda suke sunã tsayar da salla kuma sunã bãyar da zakka kuma sunã
ruku'i,
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi waɗanda suka riƙi addininku bisa
izgili da wãsa, daga waɗanda aka bai wa Littãfi daga gabãninku da kãfirai,
masõya, Kuma ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai.
Ka ce: "Ya Mutãnen Littãfi! Shin, kunã ganin wani laifi daga gare mu? Fãce dai
dõmin mun yi ĩmãni da Allah da abin da aka Saukar zuwa gare mu da abin da aka
saukar daga gabãni, kuma dõmin mafi yawanku fãsiƙai ne."
Ka ce: "Shin, in gaya muku mafi sharri daga wannan, dõmin sakamako daga wurin
Allah? wanda Allah Ya la'ane shi kuma Ya yi fushi da shi, kuma Ya sanya daga
gare su birai da aladai, kuma ya bauta wa ¦ãguta. Waɗannan ne mafiya sharrin
wuri, kuma mafiya ɓata daga tsakar hanya."
Kuma idan sun zo muku sai su ce: "Mun yi ĩmãni." Alhãli kuwa haƙĩƙa, sun shigo
da kãfirci,kuma su lalle ne, sun fita da shi, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da
suka kasance sunã ɓõyewa.
Kuma kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã tseren gaugawa a cikin zunubi da
zãlunci da cinsu ga haram. Haƙĩƙa, tir da abin da suka kasance suna aikatãwa.
Don me Malaman Tarbiyya da manyan malamai (na Yahudu) ba su hanã su daga faɗarsu
ga zunubi da cinsu ga haram ba? Haƙiƙa, tir daga abin da suka kasance sunã
sanã'antãwa.
Kuma Yahudu suka ce: "Hannun Allah abin yi wa ƙuƙumi ne. " An sanya hannuwansu a
cikin ƙuƙumi! Kuma an la'ane su sabõda abin da suka faɗa. Ã'a, hannuwanSa biyu
shimfiɗaɗɗu ne, Yanã ciyarwa yadda Yake so. Kuma lalle ne abin da aka saukar
zuwa gare ka yanã ƙãra wa mãsu yawa daga gare su, girman kai da kãfirci. Kuma
Mun jefa a tsakãninsu, ƙiyayya da ƙeta, zuwa Rãnar ¡iyãma, kõ da yaushe suka
hura wata wuta dõmin yãƙi, sai Allah Ya bice ta. Sunã aiki a cikin ƙasa dõmin
ɓarna, alhãli kuwa Allah bã Ya son mãsu fasãdi.
Kuma dã dai lalle Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, kuma sun yi taƙawa, haƙĩƙa, dã
Mun kankare miyãgun ayyukansu daga gare su, kuma dã Mun shigar da su gidãjen
Aljannar Ni'ima.
Kuma dã dai lalle su, sun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa
gare su daga Ubangijinsu, haƙĩƙa, dã sun ci daga bisansu da kuma daga ƙarƙashin
ƙafãfunsu. Daga gare su akwai wata al'umma mai tsakaitãwa kuma mãsu yawa daga
gare su, abin da suke aikatawa yã munana.
Yã kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka. Kuma
idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da manzancinSa ba ke nan. Kuma Allah Yanã
tsare ka daga mutãne. Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai.
Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi! Ba ku zama a kan kõme ba, sai kun tsayar da
Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku."Kuma
lalle ne, abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, yanã ƙara wa mãsu
yawa daga gare su girman kai da kãfirci. To, kada ka yi baƙin ciki a kan mutãne
kãfirai.
Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni da waɗanda sukatuba (Yahũdu) da Karkatattu da
Nasãra, wanda ya yi ĩmãni da Allahda Rãnar Lãhira, kuma ya aikata aiki na
ƙwarai, to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su zamo sunã baƙin ciki ba.
Lalle ne haƙĩƙa Mun riƙi alkawarin Bani Isrã'ĩla, kumaMun aiki manzanni zuwa
gare su, ko da yaushe wani manzo ya je musu da abin da rãyukansu bã su so, wani
ɓangare sun ƙaryata, kuma wani ɓangare sunã kashewa,
Kuma suka yi zaton cewa wata fitina bã zã ta kasance ba sai Suka makanta, kuma
suka kurubta, sa'an nan Allah Ya karɓi tuba a gare su, sa'an nan suka makanta
kuma suka kurunta mãsu yawa daga gare su, alhãli Allah Mai gani ne ga abin da
suke aikatãwa.
Lalle ne haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle ne Allah, shĩne Masĩhu, ɗan Maryama,"
sun kãfirta. Alhãli kuwa Masĩhu yã ce: "Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku bauta wa Allah
Ubangijina, kuma Ubangijinku." Lalle ne shĩ, wanda ya yi shirki da Allah, to,
lalle ne, Allah Yã haramta masa Aljanna. Kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai.
Lalle ne, haƙĩƙa, waɗanda suka ce: "Allah na ukun uku ne," sun kãfirta, kuma
babu wani abin bautãwa fãce Ubangji Guda. Kuma idan ba su hanu daga abin da suke
faɗa ba, haƙĩƙa, wata azãba mai raɗaɗi tãnã shãfar waɗanda suka kãfirta daga
gare su.
Masĩhu ɗan Maryama bai zama ba fãce Manzo ne kawai, haƙĩƙa, manzanni sun shige
dage gabãninsa, kuma uwarsa siddika ce. Sun kasance sunã cin abinci. Ka duba
yadda Muke bayyana musu ãyõyi. Sa'an nan kuma ka duba yadda ake karkatar da su.