Prev  

10. Surah Yűnus سورة يونس

  Next  




1st Ayah  1  الأية ١الأولي
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الر ۚ تِلْكَ آيَاتُ الْكِتَابِ الْحَكِيمِ
Alif-lam-ra tilka ayatualkitabi alhakeem

Hausa
 
A. L̃. R. Waɗancan ăyőyin littăfi ne kyautatacce.

Ayah  10:2  الأية
أَكَانَ لِلنَّاسِ عَجَبًا أَنْ أَوْحَيْنَا إِلَىٰ رَجُلٍ مِّنْهُمْ أَنْ أَنذِرِ النَّاسَ وَبَشِّرِ الَّذِينَ آمَنُوا أَنَّ لَهُمْ قَدَمَ صِدْقٍ عِندَ رَبِّهِمْ ۗ قَالَ الْكَافِرُونَ إِنَّ هَٰذَا لَسَاحِرٌ مُّبِينٌ
Akana linnasi AAajabanan awhayna ila rajulin minhum an anthiriannasa wabashshiri allatheena amanooanna lahum qadama sidqin AAinda rabbihim qala alkafiroonainna hatha lasahirun mubeen

Hausa
 
Shin, yă zama abin mămaki ga mutăne dőmin Mun yi wahayi zuwa ga wani namiji daga gare su cẽwa, "Ka yi gargaɗi ga mutăne kuma ka yi bushăra ga waɗanda suka yi ĩmăni da cẽwa: Lalle ne sună da abin gabătarwar gaskiya a wurin Ubangijinsu."Kăfirai suka ce: "Lalle ne wannan, haƙĩƙa, masihirci ne bayyananne."

Ayah  10:3  الأية
إِنَّ رَبَّكُمُ اللهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَىٰ عَلَى الْعَرْشِ ۖ يُدَبِّرُ الْأَمْرَ ۖ مَا مِن شَفِيعٍ إِلَّا مِن بَعْدِ إِذْنِهِ ۚ ذَٰلِكُمُ اللهُ رَبُّكُمْ فَاعْبُدُوهُ ۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Inna rabbakumu Allahu allatheekhalaqa assamawati wal-ardafee sittati ayyamin thumma istawa AAalaalAAarshi yudabbiru al-amra ma min shafeeAAin illamin baAAdi ithnihi thalikumu Allahu rabbukumfaAAbudoohu afala tathakkaroon

Hausa
 
Lalle Allah ne Ubangijinku wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwăna shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi Yană gudănar da al'amari. Băbu wani macẽci făce a bayan izninSa. Wannan ne Allah, Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Shin fa, ba ku tunăni?

Ayah  10:4  الأية
إِلَيْهِ مَرْجِعُكُمْ جَمِيعًا ۖ وَعْدَ اللهِ حَقًّا ۚ إِنَّهُ يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ لِيَجْزِيَ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ بِالْقِسْطِ ۚ وَالَّذِينَ كَفَرُوا لَهُمْ شَرَابٌ مِّنْ حَمِيمٍ وَعَذَابٌ أَلِيمٌ بِمَا كَانُوا يَكْفُرُونَ
Ilayhi marjiAAukum jameeAAan waAAda Allahihaqqan innahu yabdao alkhalqa thumma yuAAeeduhu liyajziyaallatheena amanoo waAAamiloo assalihatibilqisti wallatheena kafaroo lahumsharabun min hameemin waAAathabun aleemunbima kanoo yakfuroon

Hausa
 
zuwa gare Shi makőmarku take gabă ɗaya, wa'adin Allah gaskiya ne. Haƙĩƙa, Shi ne Yake fara halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita dőmin Ya săka wa waɗanda suka yi ĩmăni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai da ădalci, kuma waɗanda suka kăfirta sună da abin sha daga ruwan zăfi, da azăba mai raɗaɗi, sabőda abin da suka kasance sună yi na kăfirci.

Ayah  10:5  الأية
هُوَ الَّذِي جَعَلَ الشَّمْسَ ضِيَاءً وَالْقَمَرَ نُورًا وَقَدَّرَهُ مَنَازِلَ لِتَعْلَمُوا عَدَدَ السِّنِينَ وَالْحِسَابَ ۚ مَا خَلَقَ اللهُ ذَٰلِكَ إِلَّا بِالْحَقِّ ۚ يُفَصِّلُ الْآيَاتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ
Huwa allathee jaAAala ashshamsadiyaan walqamara nooran waqaddarahu manazilalitaAAlamoo AAadada assineena walhisabama khalaqa Allahu thalika illa bilhaqqiyufassilu al-ayati liqawmin yaAAlamoon

Hausa
 
Shĩ ne wanda Ya sanya muku rănă, babban haske, da wată mai haske, kuma Ya ƙaddara shi ga Manzilőli, dőmin ku san ƙidăyar shẽkaru da lissăfi. Allah bai halitta wannan ba, făce da gaskiya, Yană bayyana ăyőyi daki-daki dőmin mutăne waɗanda suke sani.

Ayah  10:6  الأية
إِنَّ فِي اخْتِلَافِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَمَا خَلَقَ اللهُ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَّقُونَ
Inna fee ikhtilafi allayli wannahariwama khalaqa Allahu fee assamawatiwal-ardi laayatin liqawmin yattaqoon

Hausa
 
Lalle ne a cikin săɓăwar dare da yini, da abin da Allah Ya halitta a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙaakwai ăyőyi ga mutăne waɗanda suke yin taƙawa.

Ayah  10:7  الأية
إِنَّ الَّذِينَ لَا يَرْجُونَ لِقَاءَنَا وَرَضُوا بِالْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَاطْمَأَنُّوا بِهَا وَالَّذِينَ هُمْ عَنْ آيَاتِنَا غَافِلُونَ
Inna allatheena la yarjoona liqaanawaradoo bilhayati addunyawatmaannoo biha wallatheenahum AAan ayatina ghafiloon

Hausa
 
Lalle ne waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mũ, kuma suka yarda da răyuwar dũniya kuma suka natsu da ita, da waɗanda suke gafalallu ne daga ăyőyinMu,

Ayah  10:8  الأية
أُولَٰئِكَ مَأْوَاهُمُ النَّارُ بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ
Ola-ika ma/wahumu annarubima kanoo yaksiboon

Hausa
 
Waɗannan matattărarsu Jahannama ce sabőda abin da suka kasance sună tsirfătawa.

Ayah  10:9  الأية
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ يَهْدِيهِمْ رَبُّهُم بِإِيمَانِهِمْ ۖ تَجْرِي مِن تَحْتِهِمُ الْأَنْهَارُ فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِ
Inna allatheena amanoowaAAamiloo assalihati yahdeehim rabbuhumbi-eemanihim tajree min tahtihimu al-anharufee jannati annaAAeem

Hausa
 
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmăni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, Ubangijinsu Yană shiryar da su sabőda ĩmăninsu, ƙőramu sună gudăna daga ƙarƙashinsu, a cikin gidăjen Aljannar ni'ima.

Ayah  10:10  الأية
دَعْوَاهُمْ فِيهَا سُبْحَانَكَ اللهُمَّ وَتَحِيَّتُهُمْ فِيهَا سَلَامٌ ۚ وَآخِرُ دَعْوَاهُمْ أَنِ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ
DaAAwahum feeha subhanakaallahumma watahiyyatuhum feeha salamunwaakhiru daAAwahum ani alhamdu lillahirabbi alAAalameen

Hausa
 
Kiransu a cikinta, "TsarkinKa yă Allah!" Kuma gaisuwarsu a cikinta,"Salămun", kuma ƙarshen kiransu, cẽwa, "Gődiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu."

Ayah  10:11  الأية
وَلَوْ يُعَجِّلُ اللهُ لِلنَّاسِ الشَّرَّ اسْتِعْجَالَهُم بِالْخَيْرِ لَقُضِيَ إِلَيْهِمْ أَجَلُهُمْ ۖ فَنَذَرُ الَّذِينَ لَا يَرْجُونَ لِقَاءَنَا فِي طُغْيَانِهِمْ يَعْمَهُونَ
Walaw yuAAajjilu Allahu linnasiashsharra istiAAjalahum bilkhayri laqudiyailayhim ajaluhum fanatharu allatheena layarjoona liqaana fee tughyanihimyaAAmahoon

Hausa
 
Kuma dă Allah Yana gaggăwa ga mutăne da sharri kamar yadda Yake gaggauta musu da alhẽri, haƙĩƙa dă an hukunta ajalinsu zuwa gare su. Sabőda haka Mună barin waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mu, a cikin kangararsu sună ta ɗimuwa.

Ayah  10:12  الأية
وَإِذَا مَسَّ الْإِنسَانَ الضُّرُّ دَعَانَا لِجَنبِهِ أَوْ قَاعِدًا أَوْ قَائِمًا فَلَمَّا كَشَفْنَا عَنْهُ ضُرَّهُ مَرَّ كَأَن لَّمْ يَدْعُنَا إِلَىٰ ضُرٍّ مَّسَّهُ ۚ كَذَٰلِكَ زُيِّنَ لِلْمُسْرِفِينَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Wa-itha massa al-insana addurrudaAAana lijanbihi aw qaAAidan aw qa-imanfalamma kashafna AAanhu durrahu marra kaanlam yadAAuna ila durrin massahu kathalikazuyyina lilmusrifeena ma kanoo yaAAmaloon

Hausa
 
Kuma idan cũta ta shăfi mutum, sai ya kirăye Mu, yană (kwance) ga săshensa kő kuwa zaune, kő kuwa a tsaye. To, a lőkacin, da Muka kuranye cũtar daga gare shi, sai ya shũɗe kamar ɗai bai kirăye Mu ba zuwa ga wata cũta wadda ta shăfe shi. Kamar wannan ne aka ƙawăta ga maɓannata, abin da suka kasance sună aikatăwa.

Ayah  10:13  الأية
وَلَقَدْ أَهْلَكْنَا الْقُرُونَ مِن قَبْلِكُمْ لَمَّا ظَلَمُوا ۙ وَجَاءَتْهُمْ رُسُلُهُم بِالْبَيِّنَاتِ وَمَا كَانُوا لِيُؤْمِنُوا ۚ كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْقَوْمَ الْمُجْرِمِينَ
Walaqad ahlakna alquroona minqablikum lamma thalamoo wajaat-humrusuluhum bilbayyinati wama kanooliyu/minoo kathalika najzee alqawma almujrimeen

Hausa
 
Kuma, haƙĩƙa, Mun halakar da al'ummomi daga gabăninku, a lőkacin da suka yi zălunci, kuma manzanninsu suka jẽ musu da hujjőji bayyanannu, amma ba su kasance sună ĩmăni ba. Kamar wannan ne, Muke săkăwa ga mutăne măsu laifi.

Ayah  10:14  الأية
ثُمَّ جَعَلْنَاكُمْ خَلَائِفَ فِي الْأَرْضِ مِن بَعْدِهِمْ لِنَنظُرَ كَيْفَ تَعْمَلُونَ
Thumma jaAAalnakum khala-ifafee al-ardi min baAAdihim linanthura kayfataAAmaloon

Hausa
 
Sa'an nan kuma Muka sanya ku măsu mayẽwa a cikin ƙasa daga băyansu, dőmin Mu ga yăya kuke aikatăwa.

Ayah  10:15  الأية
وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا بَيِّنَاتٍ ۙ قَالَ الَّذِينَ لَا يَرْجُونَ لِقَاءَنَا ائْتِ بِقُرْآنٍ غَيْرِ هَٰذَا أَوْ بَدِّلْهُ ۚ قُلْ مَا يَكُونُ لِي أَنْ أُبَدِّلَهُ مِن تِلْقَاءِ نَفْسِي ۖ إِنْ أَتَّبِعُ إِلَّا مَا يُوحَىٰ إِلَيَّ ۖ إِنِّي أَخَافُ إِنْ عَصَيْتُ رَبِّي عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ
Wa-itha tutla AAalayhim ayatunabayyinatin qala allatheena layarjoona liqaana i/ti biqur-anin ghayri hathaaw baddilhu qul ma yakoonu lee an obaddilahu min tilqa-inafsee in attabiAAu illa ma yooha ilayyainnee akhafu in AAasaytu rabbee AAathabayawmin AAatheem

Hausa
 
Kuma idan ană karatun ăyőyĩnMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda bă su ƙaunar gawuwa da Mu, su ce: "Ka zo da wani Alƙur'ăni, wanin wannan, ko kuwa ka musunyă shi." Ka ce: "Bă ya kasancẽwa a gare ni in musanyă shi da kaina. Bă ni biyar kőme făce abin da aka yiwo wahayi zuwa gare ni. Kuma, haƙĩƙa ni ină tsőro idan na săɓă wa Ubangijina, ga azăbar wani yini mai girma."

Ayah  10:16  الأية
قُل لَّوْ شَاءَ اللهُ مَا تَلَوْتُهُ عَلَيْكُمْ وَلَا أَدْرَاكُم بِهِ ۖ فَقَدْ لَبِثْتُ فِيكُمْ عُمُرًا مِّن قَبْلِهِ ۚ أَفَلَا تَعْقِلُونَ
Qul law shaa Allahu matalawtuhu AAalaykum wala adrakum bihi faqadlabithtu feekum AAumuran min qablihi afala taAAqiloon

Hausa
 
Ka ce: "Dă Allah Ya so dă ban karanta shi ba a kanku, kuma dă ban sanar da kũ ba gameda shi, dőmin lalle ne nă zauna a cikinku a zămani mai tsawo daga gabănin (făra saukar) sa. Shin fa, bă ku hankalta?"

Ayah  10:17  الأية
فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَىٰ عَلَى اللهِ كَذِبًا أَوْ كَذَّبَ بِآيَاتِهِ ۚ إِنَّهُ لَا يُفْلِحُ الْمُجْرِمُونَ
Faman athlamu mimmani iftaraAAala Allahi kathiban aw kaththababi-ayatihi innahu la yuflihualmujrimoon

Hausa
 
"Sabőda haka wăne ne mafi Zălunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kő kuwa ya ƙaryata ăyőyinSa? Haƙĩƙa, măsu laifibă su cin nasara!"

Ayah  10:18  الأية
وَيَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللهِ مَا لَا يَضُرُّهُمْ وَلَا يَنفَعُهُمْ وَيَقُولُونَ هَٰؤُلَاءِ شُفَعَاؤُنَا عِندَ اللهِ ۚ قُلْ أَتُنَبِّئُونَ اللهَ بِمَا لَا يَعْلَمُ فِي السَّمَاوَاتِ وَلَا فِي الْأَرْضِ ۚ سُبْحَانَهُ وَتَعَالَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ
WayaAAbudoona min dooni Allahi mala yadurruhum wala yanfaAAuhum wayaqooloonahaola-i shufaAAaona AAinda Allahiqul atunabbi-oona Allaha bima la yaAAlamufee assamawati wala fee al-ardisubhanahu wataAAala AAamma yushrikoon

Hausa
 
Kuma sună baută wa, baicin Allah, abin da bă ya cũtar dasu kuma bă ya amfăninsu, kuma sună cẽwa: "Waɗannan ne macẽtanmu a wurin Allah."Ka ce: "Shin, kună bai wa Allah lăbări ne, ga abin da bai sani ba, a cikin sammai ko a cikin ƙasa? TsarkinSa ya tabbata kuma Yă ɗaukaka daga gabin da duk suke yin shirki da Shi."

Ayah  10:19  الأية
وَمَا كَانَ النَّاسُ إِلَّا أُمَّةً وَاحِدَةً فَاخْتَلَفُوا ۚ وَلَوْلَا كَلِمَةٌ سَبَقَتْ مِن رَّبِّكَ لَقُضِيَ بَيْنَهُمْ فِيمَا فِيهِ يَخْتَلِفُونَ
Wama kana annasuilla ommatan wahidatan fakhtalafoo walawlakalimatun sabaqat min rabbika laqudiya baynahum feemafeehi yakhtalifoon

Hausa
 
Kuma mutăne ba su kasance ba făce al'umma guda, sa'an nan kuma suka săɓă wa jũna, kuma ba dőmin wata kalma ba wadda ta gabăta daga Ubangijinka, dă an yi hukunci a tsakăninsu a kan abin da yake a cikinsa suke săɓă wa jũna.

Ayah  10:20  الأية
وَيَقُولُونَ لَوْلَا أُنزِلَ عَلَيْهِ آيَةٌ مِّن رَّبِّهِ ۖ فَقُلْ إِنَّمَا الْغَيْبُ لِلَّهِ فَانتَظِرُوا إِنِّي مَعَكُم مِّنَ الْمُنتَظِرِينَ
Wayaqooloona lawla onzila AAalayhi ayatunmin rabbihi faqul innama alghaybu lillahi fantathirooinnee maAAakum mina almuntathireen

Hausa
 
Kuma sună cẽwa: "Don me ba a saukar da wata ăyă ba a gare shi, daga Ubangijinsa?" To, ka ce: "Abin sani kawai, gaibi ga Allah yake. Sai ku yi jira. Lalle ne nĩ, tăre da ku, ină daga măsu jira."

Ayah  10:21  الأية
وَإِذَا أَذَقْنَا النَّاسَ رَحْمَةً مِّن بَعْدِ ضَرَّاءَ مَسَّتْهُمْ إِذَا لَهُم مَّكْرٌ فِي آيَاتِنَا ۚ قُلِ اللهُ أَسْرَعُ مَكْرًا ۚ إِنَّ رُسُلَنَا يَكْتُبُونَ مَا تَمْكُرُونَ
Wa-itha athaqna annasarahmatan min baAAdi darraa massat-hum ithalahum makrun fee ayatina quli AllahuasraAAu makran inna rusulana yaktuboona matamkuroon

Hausa
 
Kuma idan Muka ɗanɗană wa mutăne wata rahama, a băyan wata cũta tă shăfe su, sai gă su da măkirci a cikin ăyőyinMu. Ka ce: "Allah ne mafi gaggăwar (sakamakon) măkirci." Lalle ne ManzanninMu sună rubũta abin da kuke yi na măkirci.

Ayah  10:22  الأية
هُوَ الَّذِي يُسَيِّرُكُمْ فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا كُنتُمْ فِي الْفُلْكِ وَجَرَيْنَ بِهِم بِرِيحٍ طَيِّبَةٍ وَفَرِحُوا بِهَا جَاءَتْهَا رِيحٌ عَاصِفٌ وَجَاءَهُمُ الْمَوْجُ مِن كُلِّ مَكَانٍ وَظَنُّوا أَنَّهُمْ أُحِيطَ بِهِمْ ۙ دَعَوُا اللهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ لَئِنْ أَنجَيْتَنَا مِنْ هَٰذِهِ لَنَكُونَنَّ مِنَ الشَّاكِرِينَ
Huwa allathee yusayyirukum feealbarri walbahri hatta ithakuntum fee alfulki wajarayna bihim bireehin tayyibatinwafarihoo biha jaat-ha reehunAAasifun wajaahumu almawju min kulli makaninwathannoo annahum oheeta bihimdaAAawoo Allaha mukhliseena lahu addeenala-in anjaytana min hathihi lanakoonanna mina ashshakireen

Hausa
 
Shĩ ne wanda Yake tafiyar da ku a cikin tudu da (kuma) tẽku, sai idan kun kasance a cikin jirăge, su gudăna tăre da su da iska mai dăɗi, kuma su yi farin ciki da ita, sai wata gũguwa ta je wa jirăgen, kuma tăguwar ruwa ta jẽ musu daga kőwane wuri, kuma su tabbata cẽwa sũ, an kẽwaye su, sai su kirăyi Allah, sună măsu tsarkake addini gare Shi, (sună cẽwa): Lalle ne idanKa kuɓutar da mu daga wannan, haƙĩƙa mună kasancẽwa daga măsu gődiya.

Ayah  10:23  الأية
فَلَمَّا أَنجَاهُمْ إِذَا هُمْ يَبْغُونَ فِي الْأَرْضِ بِغَيْرِ الْحَقِّ ۗ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّمَا بَغْيُكُمْ عَلَىٰ أَنفُسِكُم ۖ مَّتَاعَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۖ ثُمَّ إِلَيْنَا مَرْجِعُكُمْ فَنُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Falamma anjahum ithahum yabghoona fee al-ardi bighayri alhaqqi yaayyuha annasu innama baghyukum AAalaanfusikum mataAAa alhayati addunyathumma ilayna marjiAAukum fanunabbi-okum bimakuntum taAAmaloon

Hausa
 
To, a lőkacin da Ya kuɓutar da su, sai, gă su sună zălunci a cikin ƙasa, bă da wanĩ hakki ba. Yă ku mutăne! Abin sani kawai, zăluncinku a kanku yake, a bisa răyuwar dũniya. Sa'an nan kuma zuwa gare Mu makőmarku take, sa'an nan Mu bă ku lăbări game da abin da kuka kasance kună aikatăwa,

Ayah  10:24  الأية
إِنَّمَا مَثَلُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا كَمَاءٍ أَنزَلْنَاهُ مِنَ السَّمَاءِ فَاخْتَلَطَ بِهِ نَبَاتُ الْأَرْضِ مِمَّا يَأْكُلُ النَّاسُ وَالْأَنْعَامُ حَتَّىٰ إِذَا أَخَذَتِ الْأَرْضُ زُخْرُفَهَا وَازَّيَّنَتْ وَظَنَّ أَهْلُهَا أَنَّهُمْ قَادِرُونَ عَلَيْهَا أَتَاهَا أَمْرُنَا لَيْلًا أَوْ نَهَارًا فَجَعَلْنَاهَا حَصِيدًا كَأَن لَّمْ تَغْنَ بِالْأَمْسِ ۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ الْآيَاتِ لِقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ
Innama mathalu alhayatiaddunya kama-in anzalnahu mina assama-ifakhtalata bihi nabatu al-ardi mimmaya/kulu annasu wal-anAAamu hattaitha akhathati al-ardu zukhrufaha wazzayyanatwathanna ahluha annahum qadiroonaAAalayha ataha amruna laylan aw naharanfajaAAalnaha haseedan kaan lam taghnabil-amsi kathalika nufassilu al-ayatiliqawmin yatafakkaroon

Hausa
 
Abin sani kawai, misălin răyuwar dũniya kamar ruwa ne Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsiron ƙasa ya garwaya da shi. Daga abin da mutăne da dabbőbi suke ci, har idan ƙasa ta riƙi zinăriyarta kuma ta yi ƙawa, kuma mutănenta suka zaci cẽwa sũ ne măsu ĩkon yi a kanta, sai umurninMu ya je mata da dare kő kuma da răna, sai Mu maishẽta girbabba kamar ba ta wadăta ba a jiya. Kamar wannan ne Muke rarrabe ăyőyi, daki-daki, ga mutăne waɗanda suke tunăni.

Ayah  10:25  الأية
وَاللهُ يَدْعُو إِلَىٰ دَارِ السَّلَامِ وَيَهْدِي مَن يَشَاءُ إِلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Wallahu yadAAoo ila dariassalami wayahdee man yashao ila siratinmustaqeem

Hausa
 
Kuma Allah Yană kira zuwa ga gidan aminci, kuma, Yană shiryar da wanda Yake so zuwa ga tafarki madaidaici.

Ayah  10:26  الأية
لِّلَّذِينَ أَحْسَنُوا الْحُسْنَىٰ وَزِيَادَةٌ ۖ وَلَا يَرْهَقُ وُجُوهَهُمْ قَتَرٌ وَلَا ذِلَّةٌ ۚ أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Lillatheena ahsanoo alhusnawaziyadatun wala yarhaqu wujoohahum qatarun walathillatun ola-ika as-habu aljannatihum feeha khalidoon

Hausa
 
Waɗanda suka kyautata yi, sună da abu mai kyăwo kuma da ƙari, wata ƙũra bă ta rufe fuskőkinsu, kuma haka wani ƙasƙanci. waɗancan ne abokan Aljanna, sună madawwama a cikinta.

Ayah  10:27  الأية
وَالَّذِينَ كَسَبُوا السَّيِّئَاتِ جَزَاءُ سَيِّئَةٍ بِمِثْلِهَا وَتَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ ۖ مَّا لَهُم مِّنَ اللهِ مِنْ عَاصِمٍ ۖ كَأَنَّمَا أُغْشِيَتْ وُجُوهُهُمْ قِطَعًا مِّنَ اللَّيْلِ مُظْلِمًا ۚ أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Wallatheena kasaboo assayyi-atijazao sayyi-atin bimithliha watarhaquhum thillatunma lahum mina Allahi min AAasimin kaannamaoghshiyat wujoohuhum qitaAAan mina allayli muthlimanola-ika as-habu annari humfeeha khalidoon

Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi tsirfar mũnanan ayyuka, sakamakon mummuna da kamarsa yake, kuma ƙasƙanci yană rufe su. Bă su da wani matsari daga Allah, kamar an rufe fuskokinsu da guntăyen ƙirăruwa daga dare mai duhu. Waɗannan ne abőkan wuta, sună madawwama a cikinta.

Ayah  10:28  الأية
وَيَوْمَ نَحْشُرُهُمْ جَمِيعًا ثُمَّ نَقُولُ لِلَّذِينَ أَشْرَكُوا مَكَانَكُمْ أَنتُمْ وَشُرَكَاؤُكُمْ ۚ فَزَيَّلْنَا بَيْنَهُمْ ۖ وَقَالَ شُرَكَاؤُهُم مَّا كُنتُمْ إِيَّانَا تَعْبُدُونَ
Wayawma nahshuruhum jameeAAan thummanaqoolu lillatheena ashrakoo makanakum antumwashurakaokum fazayyalna baynahum waqalashurakaohum ma kuntum iyyanataAAbudoon

Hausa
 
Kuma a rănar da Muke tăra su gabă ɗaya, sa'an nan kuma Mu ce wa waɗanda suka yi shirki, "Ku kăma matsayinku, kũ da abũbuwan shirkĩnku." Sa'an nan Mu rarrabe a tsakăninsu, kuma abũbuwan shirkinsu su ce: "Bă mũ kuka kasance kună bauta wa ba."

Ayah  10:29  الأية
فَكَفَىٰ بِاللهِ شَهِيدًا بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ إِن كُنَّا عَنْ عِبَادَتِكُمْ لَغَافِلِينَ
Fakafa billahishaheedan baynana wabaynakum in kunna AAan AAibadatikumlaghafileen

Hausa
 
"To, kuma Allah Yă isa zama shaida a tsakăninmu da tsakăninku. Haƙĩƙa mun kasance ba mu san kőme ba na bautăwarku a gare mu!"

Ayah  10:30  الأية
هُنَالِكَ تَبْلُو كُلُّ نَفْسٍ مَّا أَسْلَفَتْ ۚ وَرُدُّوا إِلَى اللهِ مَوْلَاهُمُ الْحَقِّ ۖ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا يَفْتَرُونَ
Hunalika tabloo kullu nafsin maaslafat waruddoo ila Allahi mawlahumu alhaqqiwadalla AAanhum ma kanoo yaftaroon

Hausa
 
A can ne kőwane rai yake jarraba abin da ya băyar băshi, kuma aka mayar da su zuwa ga Allah, Majiɓincinsu Tabbatacce kuma, abin da suka kasance sună ƙirƙirăwa ya ɓace musu.

Ayah  10:31  الأية
قُلْ مَن يَرْزُقُكُم مِّنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ أَمَّن يَمْلِكُ السَّمْعَ وَالْأَبْصَارَ وَمَن يُخْرِجُ الْحَيَّ مِنَ الْمَيِّتِ وَيُخْرِجُ الْمَيِّتَ مِنَ الْحَيِّ وَمَن يُدَبِّرُ الْأَمْرَ ۚ فَسَيَقُولُونَ اللهُ ۚ فَقُلْ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Qul man yarzuqukum mina assama-iwal-ardi amman yamliku assamAAa wal-absarawaman yukhriju alhayya mina almayyiti wayukhriju almayyitamina alhayyi waman yudabbiru al-amra fasayaqooloona Allahufaqul afala tattaqoon

Hausa
 
Ka ce: "Wăne ne Yake azurtă ku daga sama da ƙasa? Shin kő kuma Wăne ne Yake mallakar jĩ da ganĩ, kuma Wăne ne Yake fitar da mai rai daga mamaci, kuma Ya fitar da mamaci daga mai rai, Kuma Wăne ne Yake shirya al'amari?" To, ză su ce: "Allah ne." To, ka ce: "Shin fa, bă ză ku yi taƙawa ba?"

Ayah  10:32  الأية
فَذَٰلِكُمُ اللهُ رَبُّكُمُ الْحَقُّ ۖ فَمَاذَا بَعْدَ الْحَقِّ إِلَّا الضَّلَالُ ۖ فَأَنَّىٰ تُصْرَفُونَ
Fathalikumu Allahu rabbukumualhaqqu famatha baAAda alhaqqi illa addalalufaanna tusrafoon

Hausa
 
To, Wancan ne Allah, Ubangijinku Tobbatacce. To, mẽne ne a băyan gaskiya făce ɓăta? To, yăya ake karkatar da ku?

Ayah  10:33  الأية
كَذَٰلِكَ حَقَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ عَلَى الَّذِينَ فَسَقُوا أَنَّهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ
Kathalika haqqat kalimaturabbika AAala allatheena fasaqoo annahum layu/minoon

Hausa
 
Kamar wancan ne kalmar Ubangijinka, ta tabbata a kan waɗanda suka yi făsiƙanci, cẽwa haƙĩƙa sũ, bă ză su yi ĩmăni ba.

Ayah  10:34  الأية
قُلْ هَلْ مِن شُرَكَائِكُم مَّن يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ ۚ قُلِ اللهُ يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ ۖ فَأَنَّىٰ تُؤْفَكُونَ
Qul hal min shuraka-ikum man yabdaoalkhalqa thumma yuAAeeduhu quli Allahu yabdao alkhalqathumma yuAAeeduhu faanna tu/fakoon

Hausa
 
Ka ce: "Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake făra halitta, sa'an nan kuma ya mayar da ita?" Ka ce: "Allah ne Yake făra halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita. To, yăyă akejũyar da ku?"

Ayah  10:35  الأية
قُلْ هَلْ مِن شُرَكَائِكُم مَّن يَهْدِي إِلَى الْحَقِّ ۚ قُلِ اللهُ يَهْدِي لِلْحَقِّ ۗ أَفَمَن يَهْدِي إِلَى الْحَقِّ أَحَقُّ أَن يُتَّبَعَ أَمَّن لَّا يَهِدِّي إِلَّا أَن يُهْدَىٰ ۖ فَمَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ
Qul hal min shuraka-ikum man yahdeeila alhaqqi quli Allahu yahdee lilhaqqiafaman yahdee ila alhaqqi ahaqqu anyuttabaAAa amman la yahiddee illa an yuhdafama lakum kayfa tahkumoon

Hausa
 
Ka ce: "Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya?" Ka ce: "Allah ne Yake shiryarwa zuwa ga gaskiya. Shin fa, wanda Yake shiryarwa ne mafi cancantar a bi Shi, ko kuwa wanda bă ya shiryarwa făce dai a shiryar da shi? To, mẽne ne a gare ku? Yăya kuke yin hukunci?"

Ayah  10:36  الأية
وَمَا يَتَّبِعُ أَكْثَرُهُمْ إِلَّا ظَنًّا ۚ إِنَّ الظَّنَّ لَا يُغْنِي مِنَ الْحَقِّ شَيْئًا ۚ إِنَّ اللهَ عَلِيمٌ بِمَا يَفْعَلُونَ
Wama yattabiAAu aktharuhum illathannan inna aththanna layughnee mina alhaqqi shay-an inna Allaha AAaleemunbima yafAAaloon

Hausa
 
Kuma mafi yawansu bă su biyar kőme făce zato. Lalle ne zato bă ya wadătar da kőme daga gaskiya. Lalle Allah ne Masani ga abin da suke aikatăwa.

Ayah  10:37  الأية
وَمَا كَانَ هَٰذَا الْقُرْآنُ أَن يُفْتَرَىٰ مِن دُونِ اللهِ وَلَٰكِن تَصْدِيقَ الَّذِي بَيْنَ يَدَيْهِ وَتَفْصِيلَ الْكِتَابِ لَا رَيْبَ فِيهِ مِن رَّبِّ الْعَالَمِينَ
Wama kana hatha alqur-anuan yuftara min dooni Allahi walakin tasdeeqaallathee bayna yadayhi watafseela alkitabi larayba feehi min rabbi alAAalameen

Hausa
 
Kuma wannan Alƙur'ăni bai kasance ga a ƙirƙira shi ba daga wanin Allah, kuma amma shi gaskatawar wannan ne da yake a gabăninsa da bayănin hukuncin littăffan Allah, Băbu shakka a cikinsa, daga Ubangijin halittu yake.

Ayah  10:38  الأية
أَمْ يَقُولُونَ افْتَرَاهُ ۖ قُلْ فَأْتُوا بِسُورَةٍ مِّثْلِهِ وَادْعُوا مَنِ اسْتَطَعْتُم مِّن دُونِ اللهِ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Am yaqooloona iftarahu qul fa/toobisooratin mithlihi wadAAoo mani istataAAtum mindooni Allahi in kuntum sadiqeen

Hausa
 
Kő sună cẽwa, "Yă ƙirƙira shi?" Ka ce: "Ku zo da sũra guda misălinsa, kuma ku kirăyi wanda kuka iya duka, baicin Allah, idan kun kasance măsu gaskiya."

Ayah  10:39  الأية
بَلْ كَذَّبُوا بِمَا لَمْ يُحِيطُوا بِعِلْمِهِ وَلَمَّا يَأْتِهِمْ تَأْوِيلُهُ ۚ كَذَٰلِكَ كَذَّبَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۖ فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الظَّالِمِينَ
Bal kaththaboo bima lam yuheetoobiAAilmihi walamma ya/tihim ta/weeluhu kathalika kaththabaallatheena min qablihim fanthurkayfa kana AAaqibatu aththalimeen

Hausa
 
Ă'a, sun ƙaryata game da abin da ba su kẽwaye da saninsa ba, kuma fassararsa ba ta riga ta jẽ musu ba. Kamar waɗancan ne waɗanda suke a gabăninsu. Sai ka dũba, yăya ăƙibar azzălumai ta kasance?

Ayah  10:40  الأية
وَمِنْهُم مَّن يُؤْمِنُ بِهِ وَمِنْهُم مَّن لَّا يُؤْمِنُ بِهِ ۚ وَرَبُّكَ أَعْلَمُ بِالْمُفْسِدِينَ
Waminhum man yu/minu bihi waminhum man layu/minu bihi warabbuka aAAlamu bilmufsideen

Hausa
 
Kuma daga cikinsu akwai wanda yake yin ĩmăni da Shi, kuma daga cikinsu akwai wanda bă ya yin ĩmăni da Shi. Kuma Ubangijinka ne Mafi sani ga maɓarnata.

Ayah  10:41  الأية
وَإِن كَذَّبُوكَ فَقُل لِّي عَمَلِي وَلَكُمْ عَمَلُكُمْ ۖ أَنتُم بَرِيئُونَ مِمَّا أَعْمَلُ وَأَنَا بَرِيءٌ مِّمَّا تَعْمَلُونَ
Wa-in kaththabooka faqul lee AAamaleewalakum AAamalukum antum baree-oona mimma aAAmalu waanabaree-on mimma taAAmaloon

Hausa
 
Kuma idan sun ƙaryata ka, to, ka ce: "Ină da aikĩna kuma kună da aikinku, kũ kuɓutattu ne daga abin da nake aikatăwa kuma ni kuɓutacce ne daga abin da kuke aikatăwa."

Ayah  10:42  الأية
وَمِنْهُم مَّن يَسْتَمِعُونَ إِلَيْكَ ۚ أَفَأَنتَ تُسْمِعُ الصُّمَّ وَلَوْ كَانُوا لَا يَعْقِلُونَ
Waminhum man yastamiAAoona ilayka afaantatusmiAAu assumma walaw kanoo layaAAqiloon

Hausa
 
Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke saurare zuwa gare ka. Shin fa, kai kana jiyar da kurma, kuma kő dă sun kasance bă su hankalta?

Ayah  10:43  الأية
وَمِنْهُم مَّن يَنظُرُ إِلَيْكَ ۚ أَفَأَنتَ تَهْدِي الْعُمْيَ وَلَوْ كَانُوا لَا يُبْصِرُونَ
Waminhum man yanthuru ilaykaafaanta tahdee alAAumya walaw kanoo la yubsiroon

Hausa
 
Kuma daga cikinsu akwai wanda yake tsőkaci zuwa gare ka. Shin fa, kai kana shiryar da makăfi, kuma kő dă sun kasance bă su gani?

Ayah  10:44  الأية
إِنَّ اللهَ لَا يَظْلِمُ النَّاسَ شَيْئًا وَلَٰكِنَّ النَّاسَ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
Inna Allaha la yathlimuannasa shay-an walakinna annasaanfusahum yathlimoon

Hausa
 
Lalle ne Allah ba Ya zăluntar mutăne da kőme, amma mutănen ne ke zăluntar kansu.

Ayah  10:45  الأية
وَيَوْمَ يَحْشُرُهُمْ كَأَن لَّمْ يَلْبَثُوا إِلَّا سَاعَةً مِّنَ النَّهَارِ يَتَعَارَفُونَ بَيْنَهُمْ ۚ قَدْ خَسِرَ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِلِقَاءِ اللهِ وَمَا كَانُوا مُهْتَدِينَ
Wayawma yahshuruhum kaan lamyalbathoo illa saAAatan mina annahariyataAAarafoona baynahum qad khasira allatheena kaththaboobiliqa-i Allahi wama kanoo muhtadeen

Hausa
 
Kuma rănar da Yake tăra su, kamar ba su zauna ba făce sa'a guda daga yini. Sună găne jũna a tsakăninsu. Haƙĩƙa, waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasăra. Kuma ba su kasance măsu shiryuwa ba.

Ayah  10:46  الأية
وَإِمَّا نُرِيَنَّكَ بَعْضَ الَّذِي نَعِدُهُمْ أَوْ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِلَيْنَا مَرْجِعُهُمْ ثُمَّ اللهُ شَهِيدٌ عَلَىٰ مَا يَفْعَلُونَ
Wa-imma nuriyannaka baAAdaallathee naAAiduhum aw natawaffayannaka fa-ilaynamarjiAAuhum thumma Allahu shaheedun AAala mayafAAaloon

Hausa
 
Kuma imma dai, haƙĩƙa, Mu nũna maka săshen abin da Muke yi musu alkawari, kő kuwa Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu makőmarsu take. Sa'an nan kuma Allah ne shaida a kan abin da suke aikatăwa.

Ayah  10:47  الأية
وَلِكُلِّ أُمَّةٍ رَّسُولٌ ۖ فَإِذَا جَاءَ رَسُولُهُمْ قُضِيَ بَيْنَهُم بِالْقِسْطِ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ
Walikulli ommatin rasoolun fa-itha jaarasooluhum qudiya baynahum bilqisti wahum layuthlamoon

Hausa
 
Kuma ga kőwace al'umma akwai Manzo. Sa'an nan idan Manzonsu ya je, sai a yi hukunci a tsakăninsu da ădalci, kuma sũ, bă a zăluntar su.

Ayah  10:48  الأية
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا الْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Wayaqooloona mata hathaalwaAAdu in kuntum sadiqeen

Hausa
 
Kuma sună cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi zai auku, idan kun kasance măsu gaskiya?"

Ayah  10:49  الأية
قُل لَّا أَمْلِكُ لِنَفْسِي ضَرًّا وَلَا نَفْعًا إِلَّا مَا شَاءَ اللهُ ۗ لِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٌ ۚ إِذَا جَاءَ أَجَلُهُمْ فَلَا يَسْتَأْخِرُونَ سَاعَةً ۖ وَلَا يَسْتَقْدِمُونَ
Qul la amliku linafsee darranwala nafAAan illa ma shaa Allahulikulli ommatin ajalun itha jaa ajaluhum falayasta/khiroona saAAatan wala yastaqdimoon

Hausa
 
Ka ce: "Ba na mallaka wa kaina wata cũta, haka kuma wani amfăni, sai abin da Allah Ya so. Ga kőwace al'umma akwai ajali, idan ajalinsu ya zo, to, bă ză su yi jinkiri daga gare shi ba, kő dă să'ă guda, kuma bă ză su gabăta ba."

Ayah  10:50  الأية
قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِنْ أَتَاكُمْ عَذَابُهُ بَيَاتًا أَوْ نَهَارًا مَّاذَا يَسْتَعْجِلُ مِنْهُ الْمُجْرِمُونَ
Qul araaytum in atakum AAathabuhubayatan aw naharan matha yastaAAjilu minhualmujrimoon

Hausa
 
Ka ce: "Shin, kun gani, idan azăbarSa ta zo muku da dare ko da răna? Mẽne ne daga gare shimăsu laifi suke nẽman gaggăwarsa?"

Ayah  10:51  الأية
أَثُمَّ إِذَا مَا وَقَعَ آمَنتُم بِهِ ۚ آلْآنَ وَقَدْ كُنتُم بِهِ تَسْتَعْجِلُونَ
Athumma itha ma waqaAAa amantumbihi al-ana waqad kuntum bihi tastaAAjiloon

Hausa
 
Shin sa'an nan kuma idan har ya auku, kun yi ĩmăni da shi? Ashe? Yanzu kuwa, alhăli kun kasance game da shi kună nẽman gaggăwar aukuwarsa?

Ayah  10:52  الأية
ثُمَّ قِيلَ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا ذُوقُوا عَذَابَ الْخُلْدِ هَلْ تُجْزَوْنَ إِلَّا بِمَا كُنتُمْ تَكْسِبُونَ
Thumma qeela lillatheena thalamoothooqoo AAathaba alkhuldi hal tujzawna illabima kuntum taksiboon

Hausa
 
Sa'an nan kuma aka ce ga waɗanda suka yi zălunci, "Ku ɗanɗani azăbar dawwama! Shin, ană săka muku făce da abin da kuka kasance kuna aikatăwa?"

Ayah  10:53  الأية
وَيَسْتَنبِئُونَكَ أَحَقٌّ هُوَ ۖ قُلْ إِي وَرَبِّي إِنَّهُ لَحَقٌّ ۖ وَمَا أَنتُم بِمُعْجِزِينَ
Wayastanbi-oonaka ahaqqun huwa qul eewarabbee innahu lahaqqun wama antum bimuAAjizeen

Hausa
 
Kuma sună tambayar ka: Shin gaskiya ne? Ka ce: "Ĩ, ina rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle gaskiya ne, kuma ba ku zama măsu buwăya ba."

Ayah  10:54  الأية
وَلَوْ أَنَّ لِكُلِّ نَفْسٍ ظَلَمَتْ مَا فِي الْأَرْضِ لَافْتَدَتْ بِهِ ۗ وَأَسَرُّوا النَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُا الْعَذَابَ ۖ وَقُضِيَ بَيْنَهُم بِالْقِسْطِ ۚ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ
Walaw anna likulli nafsin thalamatma fee al-ardi laftadat bihi waasarroo annadamatalamma raawoo alAAathaba waqudiya baynahum bilqistiwahum la yuthlamoon

Hausa
 
Kuma dă kőwane rai wanda ya yi zălunci yă mallaki duka abin da yake a cikin ƙasa, to, dă yă yi fansa da shi. Kuma suka dinga nadăma a lőkacin da suka ga azăba. Sa'an nan aka yi hukunci a tsakăninsu da ădalci, kuma bă ză a zălunce su ba.

Ayah  10:55  الأية
أَلَا إِنَّ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۗ أَلَا إِنَّ وَعْدَ اللهِ حَقٌّ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Ala inna lillahi ma feeassamawati wal-ardi alainna waAAda Allahi haqqun walakinnaaktharahum la yaAAlamoon

Hausa
 
To! Haƙĩƙa Allah Ya mallaki abin da yake a cikin sammai da ƙasa. To! Haƙĩƙa wa'adin Allah gaskiya ne. Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.

Ayah  10:56  الأية
هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Huwa yuhyee wayumeetu wa-ilayhiturjaAAoon

Hausa
 
Shi ne Yake răyarwa kuma Yake matarwa. Kuma zuwa gare Shi ne ake mayar da ku.

Ayah  10:57  الأية
يَا أَيُّهَا النَّاسُ قَدْ جَاءَتْكُم مَّوْعِظَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ وَشِفَاءٌ لِّمَا فِي الصُّدُورِ وَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِّلْمُؤْمِنِينَ
Ya ayyuha annasuqad jaatkum mawAAithatun min rabbikum washifaonlima fee assudoori wahudan warahmatunlilmu/mineen

Hausa
 
Ya ku mutăne! Lalle wa'azi yă jẽ muku daga Ubangijinku, da waraka ga abin da yake a cikin ƙirăza, da shiriya da rahama ga muminai.

Ayah  10:58  الأية
قُلْ بِفَضْلِ اللهِ وَبِرَحْمَتِهِ فَبِذَٰلِكَ فَلْيَفْرَحُوا هُوَ خَيْرٌ مِّمَّا يَجْمَعُونَ
Qul bifadli Allahi wabirahmatihifabithalika falyafrahoo huwa khayrun mimmayajmaAAoon

Hausa
 
Ka ce: "Da falalar Allah da rahamarSa. Sai su yi farin ciki da wannan." Shĩ ne mafi alhẽri daga abin da suke tărăwa.

Ayah  10:59  الأية
قُلْ أَرَأَيْتُم مَّا أَنزَلَ اللهُ لَكُم مِّن رِّزْقٍ فَجَعَلْتُم مِّنْهُ حَرَامًا وَحَلَالًا قُلْ آللهُ أَذِنَ لَكُمْ ۖ أَمْ عَلَى اللهِ تَفْتَرُونَ
Qul araaytum ma anzala Allahulakum min rizqin fajaAAaltum minhu haraman wahalalanqul allahu athina lakum am AAala Allahitaftaroon

Hausa
 
Ka ce: "Shin, kun ga abin da Allah Ya saukar sabőda ku na arziki, sai kuka sanya hukuncin haramci da halacci a gare shi?" Ka ce: "Shin, Allah ne Ya yi muku izni, ko ga Allah kuke ƙirƙirăwar ƙarya?"

Ayah  10:60  الأية
وَمَا ظَنُّ الَّذِينَ يَفْتَرُونَ عَلَى اللهِ الْكَذِبَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۗ إِنَّ اللهَ لَذُو فَضْلٍ عَلَى النَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَشْكُرُونَ
Wama thannu allatheenayaftaroona AAala Allahi alkathiba yawmaalqiyamati inna Allaha lathoo fadlinAAala annasi walakinna aktharahum layashkuroon

Hausa
 
Kuma mẽne ne zaton waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, a Rănar ˇiyăma? Lalle haƙĩƙa,Allah Ma, abũcin falala ne a kan mutăne, amma kuma mafi yawansu bă su gődẽwa.

Ayah  10:61  الأية
وَمَا تَكُونُ فِي شَأْنٍ وَمَا تَتْلُو مِنْهُ مِن قُرْآنٍ وَلَا تَعْمَلُونَ مِنْ عَمَلٍ إِلَّا كُنَّا عَلَيْكُمْ شُهُودًا إِذْ تُفِيضُونَ فِيهِ ۚ وَمَا يَعْزُبُ عَن رَّبِّكَ مِن مِّثْقَالِ ذَرَّةٍ فِي الْأَرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ وَلَا أَصْغَرَ مِن ذَٰلِكَ وَلَا أَكْبَرَ إِلَّا فِي كِتَابٍ مُّبِينٍ
Wama takoonu fee sha/nin wamatatloo minhu min qur-anin wala taAAmaloona minAAamalin illa kunna AAalaykum shuhoodan ithtufeedoona feehi wama yaAAzubu AAan rabbika minmithqali tharratin fee al-ardi walafee assama-i wala asghara min thalikawala akbara illa fee kitabin mubeen

Hausa
 
Kuma ba ka kasance a cikin wani sha'ani ba, kuma ba ka karanta wani abin karatu daga gare shi ba, kuma ba ku aikata wani aiki ba, făce Mun kasance Halarce a lőkacin da kuke zubuwa a cikinsa. Kuma wani ma'aunin zarra bă zai yi nĩsa ba daga Ubangijinka a cikin ƙasa, haka kuma a cikin sama, kuma băbu wanda yake mafi ƙaranci daga haka, kuma băbu mafi girma, făce yana a cikin littăfi bayyananne.

Ayah  10:62  الأية
أَلَا إِنَّ أَوْلِيَاءَ اللهِ لَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ
Ala inna awliyaa Allahila khawfun AAalayhim wala hum yahzanoon

Hausa
 
To, Lalle ne masőyan Allah băbu tsőro a kansu, kuma bă ză su kasance sună yin baƙin ciki ba.

Ayah  10:63  الأية
الَّذِينَ آمَنُوا وَكَانُوا يَتَّقُونَ
Allatheena amanoo wakanooyattaqoon

Hausa
 
Waɗanda suka yi ĩmăni kuma suka kasance sună yin taƙawa.

Ayah  10:64  الأية
لَهُمُ الْبُشْرَىٰ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَفِي الْآخِرَةِ ۚ لَا تَبْدِيلَ لِكَلِمَاتِ اللهِ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
Lahumu albushra fee alhayatiaddunya wafee al-akhirati latabdeela likalimati Allahi thalika huwaalfawzu alAAatheem

Hausa
 
Sună da bushăra a cikin răyuwar dũniya da ta Lăhira.Băbu musanyăwa ga kalmőmin Allah. Wancan shi ne babban rabo mai girma,

Ayah  10:65  الأية
وَلَا يَحْزُنكَ قَوْلُهُمْ ۘ إِنَّ الْعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًا ۚ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Wala yahzunka qawluhum innaalAAizzata lillahi jameeAAan huwa assameeAAualAAaleem

Hausa
 
Kada maganarsu ta sanya ka a cikin baƙin ciki. Lalle ne alfarma ga Allah take gaba ɗaya. Shi ne Mai jĩ, Masani.

Ayah  10:66  الأية
أَلَا إِنَّ لِلَّهِ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَمَن فِي الْأَرْضِ ۗ وَمَا يَتَّبِعُ الَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِ اللهِ شُرَكَاءَ ۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا الظَّنَّ وَإِنْ هُمْ إِلَّا يَخْرُصُونَ
Ala inna lillahi man fee assamawatiwaman fee al-ardi wama yattabiAAu allatheenayadAAoona min dooni Allahi shurakaa inyattabiAAoona illa aththanna wa-inhum illa yakhrusoon

Hausa
 
To! Haƙĩƙa Allah Yană da mulkin wanda ke a cikin sammai da wanda ke a cikin ƙasa kuma waɗanda suke kiran wanin Allah, bă su biyar waɗansu abőkan tarẽwa (ga Allah a MulkinSa). Bă su biyar kőme făce zato. Kuma ba su zama ba făce sună ƙiri faɗi kawai.

Ayah  10:67  الأية
هُوَ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ اللَّيْلَ لِتَسْكُنُوا فِيهِ وَالنَّهَارَ مُبْصِرًا ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَسْمَعُونَ
Huwa allathee jaAAala lakumu allaylalitaskunoo feehi wannahara mubsiran innafee thalika laayatin liqawmin yasmaAAoon

Hausa
 
Shĩ ne wanda Ya sanya muku dare, dőmin ku natsu a cikinsa, da yini mai sanya a yi gani. Lalle ne a cikin wannan akwai ăyőyi ga mutăne waɗanda sukẽ ji.

Ayah  10:68  الأية
قَالُوا اتَّخَذَ اللهُ وَلَدًا ۗ سُبْحَانَهُ ۖ هُوَ الْغَنِيُّ ۖ لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۚ إِنْ عِندَكُم مِّن سُلْطَانٍ بِهَٰذَا ۚ أَتَقُولُونَ عَلَى اللهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ
Qaloo ittakhatha Allahuwaladan subhanahu huwa alghaniyyu lahu ma fee assamawatiwama fee al-ardi in AAindakum min sultaninbihatha ataqooloona AAala Allahi ma lataAAlamoon

Hausa
 
Suka ce: "Allah Ya riƙi ɗa." Tsarkinsa yă tabbata! Shi ne wadătacce Yană da mallakar abin da yake, a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, A wurinku băbu wani dalĩli game da wannan! Shin, kună faɗar abin da ba ku sani ba game da Allah?

Ayah  10:69  الأية
قُلْ إِنَّ الَّذِينَ يَفْتَرُونَ عَلَى اللهِ الْكَذِبَ لَا يُفْلِحُونَ
Qul inna allatheena yaftaroona AAalaAllahi alkathiba la yuflihoon

Hausa
 
Ka ce: "Haƙĩƙa waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, bă ză su ci nasara ba."

Ayah  10:70  الأية
مَتَاعٌ فِي الدُّنْيَا ثُمَّ إِلَيْنَا مَرْجِعُهُمْ ثُمَّ نُذِيقُهُمُ الْعَذَابَ الشَّدِيدَ بِمَا كَانُوا يَكْفُرُونَ
MataAAun fee addunyathumma ilayna marjiAAuhum thumma nutheequhumu alAAathabaashshadeeda bima kanoo yakfuroon

Hausa
 
Jin dăɗi ne a cikin dũniya, sa'an nan kuma makőmarsu zuwa gare Mu take, sa'an nan Mu ɗanɗana musu azăba mai tsanani sabőda abin da suka kasance sună yi na kăfirci.

Ayah  10:71  الأية
وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ نُوحٍ إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ يَا قَوْمِ إِن كَانَ كَبُرَ عَلَيْكُم مَّقَامِي وَتَذْكِيرِي بِآيَاتِ اللهِ فَعَلَى اللهِ تَوَكَّلْتُ فَأَجْمِعُوا أَمْرَكُمْ وَشُرَكَاءَكُمْ ثُمَّ لَا يَكُنْ أَمْرُكُمْ عَلَيْكُمْ غُمَّةً ثُمَّ اقْضُوا إِلَيَّ وَلَا تُنظِرُونِ
Watlu AAalayhim nabaa noohinith qala liqawmihi ya qawmi in kanakabura AAalaykum maqamee watathkeeree bi-ayatiAllahi faAAala Allahi tawakkaltu faajmiAAooamrakum washurakaakum thumma la yakun amrukumAAalaykum ghummatan thumma iqdoo ilayya wala tunthiroon

Hausa
 
Kuma ka karanta musu lăbărin Nũhu, a lőkacin da ya ce wa mutănensa, "Ya mutănẽna! Idan matsayĩna da tunătarwata ameda ăyőyin Allah sun kasance sun yi nauyi a kanku, to, ga Allah na dőgara. Sai ku tăra al'amarinku, kũ da abũbuwan shirkinku, sa'annan kuma kada al'amarinku ya kasance rufaffe a kanku, sa'an nan kuma ku kashe ni, kada ku yi mini jinkiri."

Ayah  10:72  الأية
فَإِن تَوَلَّيْتُمْ فَمَا سَأَلْتُكُم مِّنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِيَ إِلَّا عَلَى اللهِ ۖ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ الْمُسْلِمِينَ
Fa-in tawallaytum fama saaltukum minajrin in ajriya illa AAala Allahi waomirtuan akoona mina almuslimeen

Hausa
 
"Kuma idan kuka jũya băya, to, ban tambaye ku wata ijăra ba. ljărata ba ta zama ba făce daga Allah, kuma an umurce ni da in kasance daga măsu sallamăwa."

Ayah  10:73  الأية
فَكَذَّبُوهُ فَنَجَّيْنَاهُ وَمَن مَّعَهُ فِي الْفُلْكِ وَجَعَلْنَاهُمْ خَلَائِفَ وَأَغْرَقْنَا الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا ۖ فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُنذَرِينَ
Fakaththaboohu fanajjaynahuwaman maAAahu fee alfulki wajaAAalnahum khala-ifawaaghraqna allatheena kaththaboo bi-ayatinafanthur kayfa kana AAaqibatualmunthareen

Hausa
 
Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka kuɓutar da shi da wanda yake tăre da shi, a cikin jirgi, kuma Muka sanya su măsu mayẽwa, kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata ăyőyinMu. Sai ka dũba yadda ăƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.

Ayah  10:74  الأية
ثُمَّ بَعَثْنَا مِن بَعْدِهِ رُسُلًا إِلَىٰ قَوْمِهِمْ فَجَاءُوهُم بِالْبَيِّنَاتِ فَمَا كَانُوا لِيُؤْمِنُوا بِمَا كَذَّبُوا بِهِ مِن قَبْلُ ۚ كَذَٰلِكَ نَطْبَعُ عَلَىٰ قُلُوبِ الْمُعْتَدِينَ
Thumma baAAathna min baAAdihi rusulanila qawmihim fajaoohum bilbayyinatifama kanoo liyu/minoo bima kaththaboobihi min qablu kathalika natbaAAu AAalaquloobi almuAAtadeen

Hausa
 
Sa'an nan kuma Muka aika waɗansu Manzanni daga băyansa zuwa ga mutănensu, suka jẽmusu da hujjőji bayyanannu, to, ba su kasance ză su yi ĩmăni ba sabőda sun ƙaryata shi a gabani. Kamar wannan ne Muke rufẽwa a kan zukătan măsu ta'addi.

Ayah  10:75  الأية
ثُمَّ بَعَثْنَا مِن بَعْدِهِم مُّوسَىٰ وَهَارُونَ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِ بِآيَاتِنَا فَاسْتَكْبَرُوا وَكَانُوا قَوْمًا مُّجْرِمِينَ
Thumma baAAathna min baAAdihim moosawaharoona ila firAAawna wamala-ihi bi-ayatinafastakbaroo wakanoo qawman mujrimeen

Hausa
 
Sa'an nan kuma a băyansu Muka aika Mũsa da Hărũna zuwa ga Fir'auna da mashăwartansa, tăre da ăyőyinMu. Sai suka kangara kuma sun kasance mutăne măsu laifi.

Ayah  10:76  الأية
فَلَمَّا جَاءَهُمُ الْحَقُّ مِنْ عِندِنَا قَالُوا إِنَّ هَٰذَا لَسِحْرٌ مُّبِينٌ
Falamma jaahumu alhaqqumin AAindina qaloo inna hatha lasihrunmubeen

Hausa
 
Sa'an nan a lőkacin da gaskiya ta jẽ musu daga gare Mu, suka ce: "Wannan haƙĩƙa sihiri ne bayyananne."

Ayah  10:77  الأية
قَالَ مُوسَىٰ أَتَقُولُونَ لِلْحَقِّ لَمَّا جَاءَكُمْ ۖ أَسِحْرٌ هَٰذَا وَلَا يُفْلِحُ السَّاحِرُونَ
Qala moosa ataqooloona lilhaqqilamma jaakum asihrun hatha walayuflihu assahiroon

Hausa
 
Mũsă ya ce: " Shin, kună cẽwa ga gaskiya a lőkacin data zo muku? Shin, sihiri ne wannan? Lalle masihirci, bă ya cin nasara."

Ayah  10:78  الأية
قَالُوا أَجِئْتَنَا لِتَلْفِتَنَا عَمَّا وَجَدْنَا عَلَيْهِ آبَاءَنَا وَتَكُونَ لَكُمَا الْكِبْرِيَاءُ فِي الْأَرْضِ وَمَا نَحْنُ لَكُمَا بِمُؤْمِنِينَ
Qaloo aji/tana litalfitanaAAamma wajadna AAalayhi abaanawatakoona lakuma alkibriyao fee al-ardi wamanahnu lakuma bimu/mineen

Hausa
 
Suka ce: "Shin, ka zo mana ne dőmin ka jũyar da mu daga abin da muka iske ubanninmu a kansa, kuma girma ya kasance gare ku, ku biyu a cikin ƙasa? Bă ză mu zama măsu ĩmăni ba sabőda ku."

Ayah  10:79  الأية
وَقَالَ فِرْعَوْنُ ائْتُونِي بِكُلِّ سَاحِرٍ عَلِيمٍ
Waqala firAAawnu i/toonee bikulli sahirinAAaleem

Hausa
 
Kuma Fir'auna ya ce: "Ku zo mini da dukan masihirci, masani."

Ayah  10:80  الأية
فَلَمَّا جَاءَ السَّحَرَةُ قَالَ لَهُم مُّوسَىٰ أَلْقُوا مَا أَنتُم مُّلْقُونَ
Falamma jaa assaharatuqala lahum moosa alqoo ma antum mulqoon

Hausa
 
To, a lőkacin da masihirta suka je, Mũsă ya ce musu,"Ku jẽfa abin da kuke jẽfăwa."

Ayah  10:81  الأية
فَلَمَّا أَلْقَوْا قَالَ مُوسَىٰ مَا جِئْتُم بِهِ السِّحْرُ ۖ إِنَّ اللهَ سَيُبْطِلُهُ ۖ إِنَّ اللهَ لَا يُصْلِحُ عَمَلَ الْمُفْسِدِينَ
Falamma alqaw qala moosama ji/tum bihi assihru inna Allahasayubtiluhu inna Allaha la yuslihuAAamala almufsideen

Hausa
 
To, a lőkacin da suka jẽfa, Mũsa ya ce: "Abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai ɓăta shi. Haƙĩƙa Allah bă Ya gyăra aikin maɓarnata.

Ayah  10:82  الأية
وَيُحِقُّ اللهُ الْحَقَّ بِكَلِمَاتِهِ وَلَوْ كَرِهَ الْمُجْرِمُونَ
Wayuhiqqu Allahu alhaqqabikalimatihi walaw kariha almujrimoon

Hausa
 
"Kuma Allah Yană tabbatar da gaskiya da kalmőminSa, kő dă măsu laifi sun ƙi."

Ayah  10:83  الأية
فَمَا آمَنَ لِمُوسَىٰ إِلَّا ذُرِّيَّةٌ مِّن قَوْمِهِ عَلَىٰ خَوْفٍ مِّن فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِمْ أَن يَفْتِنَهُمْ ۚ وَإِنَّ فِرْعَوْنَ لَعَالٍ فِي الْأَرْضِ وَإِنَّهُ لَمِنَ الْمُسْرِفِينَ
Fama amana limoosa illathurriyyatun min qawmihi AAala khawfin minfirAAawna wamala-ihim an yaftinahum wa-inna firAAawna laAAalinfee al-ardi wa-innahu lamina almusrifeen

Hausa
 
Sa'an nan băbu wanda ya yi ĩmăni da Mũsa făce zuriya daga mutănensa, a kan tsőron kada Fir'auna da shũgabanninsu su fitinẽ su. Lalle, haƙĩƙa, Fir'auna marinjăyi ne a cikin ƙasa, kuma lalle shĩ haƙĩƙa, yană daga măsu ɓarna.

Ayah  10:84  الأية
وَقَالَ مُوسَىٰ يَا قَوْمِ إِن كُنتُمْ آمَنتُم بِاللهِ فَعَلَيْهِ تَوَكَّلُوا إِن كُنتُم مُّسْلِمِينَ
Waqala moosa ya qawmiin kuntum amantum billahi faAAalayhitawakkaloo in kuntum muslimeen

Hausa
 
Kuma Mũsă ya ce: "Yă kũ mutănena! Idan kun kasance kun yi ĩmăni da Allah, to, a gare Shi sai ku dőgara, idan kun kasance Musulmi."

Ayah  10:85  الأية
فَقَالُوا عَلَى اللهِ تَوَكَّلْنَا رَبَّنَا لَا تَجْعَلْنَا فِتْنَةً لِّلْقَوْمِ الظَّالِمِينَ
Faqaloo AAala Allahitawakkalna rabbana la tajAAalnafitnatan lilqawmi aththalimeen

Hausa
 
Sai suka ce: "Ga Allah muka dőgara. Yă Ubangijinmu! Kada Ka sanyă mu fitina ga mutăne azzălumai.

Ayah  10:86  الأية
وَنَجِّنَا بِرَحْمَتِكَ مِنَ الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ
Wanajjina birahmatika minaalqawmi alkafireen

Hausa
 
"Kuma Ka kuɓutar da mu dőmin RahamarKa, daga mutăne kăfirai."

Ayah  10:87  الأية
وَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ مُوسَىٰ وَأَخِيهِ أَن تَبَوَّآ لِقَوْمِكُمَا بِمِصْرَ بُيُوتًا وَاجْعَلُوا بُيُوتَكُمْ قِبْلَةً وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ ۗ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ
Waawhayna ila moosawaakheehi an tabawwaa liqawmikuma bimisrabuyootan wajAAaloo buyootakum qiblatan waaqeemoo assalatawabashshiri almu/mineen

Hausa
 
Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsă da ɗan'uwansa, cẽwa: Kũ biyu, ku zaunar da mutănenku a Masar a cikin wasu gidăje. Kuma ku sanya gidăjenku su fuskanci Alƙibla , kuma ku tsayar da salla. Kuma ku băyar da bushăra ga măsu ĩmăni.

Ayah  10:88  الأية
وَقَالَ مُوسَىٰ رَبَّنَا إِنَّكَ آتَيْتَ فِرْعَوْنَ وَمَلَأَهُ زِينَةً وَأَمْوَالًا فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا رَبَّنَا لِيُضِلُّوا عَن سَبِيلِكَ ۖ رَبَّنَا اطْمِسْ عَلَىٰ أَمْوَالِهِمْ وَاشْدُدْ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ فَلَا يُؤْمِنُوا حَتَّىٰ يَرَوُا الْعَذَابَ الْأَلِيمَ
Waqala moosa rabbanainnaka atayta firAAawna wamalaahu zeenatan waamwalanfee alhayati addunya rabbanaliyudilloo AAan sabeelika rabbana itmis AAalaamwalihim washdud AAala quloobihim falayu/minoo hatta yarawoo alAAathaba al-aleem

Hausa
 
Sai MũSă ya ce: "Yă Ubangijinmu! Haƙĩƙa Kai ne Ka bai wa Fir'auna da majalisarsa ƙawa da dũkiyőyi a cikin răyuwar dũniya, yă Ubangijinmu, dőmin su ɓatar (damutăne) daga hanyarKa. Yă Ubangijinmu! Ka shăfe a kan dũkiyarsu kuma Ka yi ɗauri a kan zukătansu yadda bă ză su yi ĩmăni ba har su ga azăba mai raɗaɗi."

Ayah  10:89  الأية
قَالَ قَدْ أُجِيبَت دَّعْوَتُكُمَا فَاسْتَقِيمَا وَلَا تَتَّبِعَانِّ سَبِيلَ الَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ
Qala qad ojeebat daAAwatukumafastaqeema wala tattabiAAannisabeela allatheena la yaAAlamoon

Hausa
 
(Allah) Yă ce: "Lalle ne an karɓi addu'arku. Sai ku daidaitu kuma kada ku bi hanyar waɗanda ba su sani ba."

Ayah  10:90  الأية
وَجَاوَزْنَا بِبَنِي إِسْرَائِيلَ الْبَحْرَ فَأَتْبَعَهُمْ فِرْعَوْنُ وَجُنُودُهُ بَغْيًا وَعَدْوًا ۖ حَتَّىٰ إِذَا أَدْرَكَهُ الْغَرَقُ قَالَ آمَنتُ أَنَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا الَّذِي آمَنَتْ بِهِ بَنُو إِسْرَائِيلَ وَأَنَا مِنَ الْمُسْلِمِينَ
Wajawazna bibanee isra-eelaalbahra faatbaAAahum firAAawnu wajunooduhu baghyanwaAAadwan hatta itha adrakahu algharaqu qalaamantu annahu la ilaha illa allatheeamanat bihi banoo isra-eela waana minaalmuslimeen

Hausa
 
Kuma Muka ƙẽtărar da Banĩ Isră'ila tẽku sai Fir'auna da rundunarsa suka bĩ su bisa ga zălunci da ƙẽtare haddi, har a lőkacin da nutsẽwa ta riske shi ya ce: "Nă yi ĩmăni cẽwa, haƙĩƙa, băbu abin bautawa făce wannan da Banũ Isră'il suka yi ĩmăni da Shi, kumanĩ, ina daga Musulmi."

Ayah  10:91  الأية
آلْآنَ وَقَدْ عَصَيْتَ قَبْلُ وَكُنتَ مِنَ الْمُفْسِدِينَ
Al-ana waqad AAasaytaqablu wakunta mina almufsideen

Hausa
 
Ashe! A yanzu! Alhăli kuwa, haƙĩƙa ka săɓa a gabăni, kuma ka kasance daga măsu ɓarna?

Ayah  10:92  الأية
فَالْيَوْمَ نُنَجِّيكَ بِبَدَنِكَ لِتَكُونَ لِمَنْ خَلْفَكَ آيَةً ۚ وَإِنَّ كَثِيرًا مِّنَ النَّاسِ عَنْ آيَاتِنَا لَغَافِلُونَ
Falyawma nunajjeeka bibadanikalitakoona liman khalfaka ayatan wa-inna katheeran mina annasiAAan ayatina laghafiloon

Hausa
 
To, a yau Mună kuɓutar da kai game da jikinka, dőmin ka kasance ăyă ga waɗanda suke a băyanka. Kuma lalle ne măsu yawa daga mutăne, haƙĩƙa, gafalallu ne ga ăyőyinMu.

Ayah  10:93  الأية
وَلَقَدْ بَوَّأْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ مُبَوَّأَ صِدْقٍ وَرَزَقْنَاهُم مِّنَ الطَّيِّبَاتِ فَمَا اخْتَلَفُوا حَتَّىٰ جَاءَهُمُ الْعِلْمُ ۚ إِنَّ رَبَّكَ يَقْضِي بَيْنَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِيمَا كَانُوا فِيهِ يَخْتَلِفُونَ
Walaqad bawwa/na banee isra-eelamubawwaa sidqin warazaqnahum mina attayyibatifama ikhtalafoo hatta jaahumualAAilmu inna rabbaka yaqdee baynahum yawma alqiyamatifeema kanoo feehi yakhtalifoon

Hausa
 
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun zaunar da Banĩ Isră'ilamazaunar gaskiya kuma Muka arzũta su daga abũbuwa măsu dăɗi. Sa'an nan ba su săɓa ba har ilmi ya jẽ musu. Lalle ne Ubangijinka Yană yin hukunci a tsakăninsu a Rănar Kiyăma a cikin abin da suka kasance sună săɓa wa jũna.

Ayah  10:94  الأية
فَإِن كُنتَ فِي شَكٍّ مِّمَّا أَنزَلْنَا إِلَيْكَ فَاسْأَلِ الَّذِينَ يَقْرَءُونَ الْكِتَابَ مِن قَبْلِكَ ۚ لَقَدْ جَاءَكَ الْحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ الْمُمْتَرِينَ
Fa-in kunta fee shakkin mimma anzalnnailayka fas-ali allatheena yaqraoona alkitabamin qablika laqad jaaka alhaqqu min rabbika falatakoonanna mina almumtareen

Hausa
 
To, idan ka kasance a cikin shakka daga abin da Muka saukar zuwa gare ka, sai ka tambayi waɗanda suke karatun Littăfi daga gabaninka. Lalle ne, haƙĩƙa, gaskiya tă jẽ maka daga Ubangijinka dőmin haka kada ka kasance daga măsu kőkanto.

Ayah  10:95  الأية
وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِ اللهِ فَتَكُونَ مِنَ الْخَاسِرِينَ
Wala takoonanna mina allatheenakaththaboo bi-ayati Allahi fatakoonamina alkhasireen

Hausa
 
Kuma kada ka kasance daga waɗanda suke ƙaryatăwa game da ăyőyin Allah, har ka kasance daga măsu hasăra.

Ayah  10:96  الأية
إِنَّ الَّذِينَ حَقَّتْ عَلَيْهِمْ كَلِمَتُ رَبِّكَ لَا يُؤْمِنُونَ
Inna allatheena haqqatAAalayhim kalimatu rabbika la yu/minoon

Hausa
 
Lalle ne waɗanda kalmar Ubangijinka ta wajaba a kansu, bă ză su yi ĩmăni ba.

Ayah  10:97  الأية
وَلَوْ جَاءَتْهُمْ كُلُّ آيَةٍ حَتَّىٰ يَرَوُا الْعَذَابَ الْأَلِيمَ
Walaw jaat-hum kullu ayatin hattayarawoo alAAathaba al-aleem

Hausa
 
Kuma kő dă kőwace ăyă ta jẽ musu, sai sun ga azăba mai raɗaɗi.

Ayah  10:98  الأية
فَلَوْلَا كَانَتْ قَرْيَةٌ آمَنَتْ فَنَفَعَهَا إِيمَانُهَا إِلَّا قَوْمَ يُونُسَ لَمَّا آمَنُوا كَشَفْنَا عَنْهُمْ عَذَابَ الْخِزْيِ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَمَتَّعْنَاهُمْ إِلَىٰ حِينٍ
Falawla kanat qaryatun amanatfanafaAAaha eemanuha illa qawmayoonusa lamma amanoo kashafna AAanhum AAathabaalkhizyi fee alhayati addunyawamattaAAnahum ila heen

Hausa
 
To, dőmin me wata alƙarya ba ta kasance ta yi ĩmăniba har ĩmăninta ya amfăne ta, făcemutănen Yũnus? A lőkacin da suka yi ĩmăni, Munjanye azăbar wulăkanci daga gare su a cikin răyuwar dũniya. Kuma Muka jiyar da su dăɗi zuwa wani lőkaci.

Ayah  10:99  الأية
وَلَوْ شَاءَ رَبُّكَ لَآمَنَ مَن فِي الْأَرْضِ كُلُّهُمْ جَمِيعًا ۚ أَفَأَنتَ تُكْرِهُ النَّاسَ حَتَّىٰ يَكُونُوا مُؤْمِنِينَ
Walaw shaa rabbuka laamana manfee al-ardi kulluhum jameeAAan afaanta tukrihu annasahatta yakoonoo mu/mineen

Hausa
 
Kuma dă Ubangijinka Ya so, dă waɗanda suke a cikin ƙasa sun yi ĩmăni dukansu gabă ɗaya. Shin, kai kană tĩlasta mutănene har su kasance măsu ĩmăni?

Ayah  10:100  الأية
وَمَا كَانَ لِنَفْسٍ أَن تُؤْمِنَ إِلَّا بِإِذْنِ اللهِ ۚ وَيَجْعَلُ الرِّجْسَ عَلَى الَّذِينَ لَا يَعْقِلُونَ
Wama kana linafsin an tu/minailla bi-ithni Allahi wayajAAalu arrijsaAAala allatheena la yaAAqiloon

Hausa
 
Kuma ba ya kasancẽwa ga wani rai ya yi ĩmăni făce da iznin Allah, kuma (Allah) Yană sanya ƙazanta a kan waɗanda bă su yin hankali.

Ayah  10:101  الأية
قُلِ انظُرُوا مَاذَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَمَا تُغْنِي الْآيَاتُ وَالنُّذُرُ عَن قَوْمٍ لَّا يُؤْمِنُونَ
Quli onthuroo mathafee assamawati wal-ardi wamatughnee al-ayatu wannuthuru AAanqawmin la yu/minoon

Hausa
 
Ka ce: "Ku dũbi abin da yake cikin sammai da ƙasa."Kuma ăyőyi da gargaɗi bă su wadătarwa ga mutăne waɗanda bă su yin ĩmăni.

Ayah  10:102  الأية
فَهَلْ يَنتَظِرُونَ إِلَّا مِثْلَ أَيَّامِ الَّذِينَ خَلَوْا مِن قَبْلِهِمْ ۚ قُلْ فَانتَظِرُوا إِنِّي مَعَكُم مِّنَ الْمُنتَظِرِينَ
Fahal yantathiroona illamithla ayyami allatheena khalaw min qablihim qul fantathirooinnee maAAakum mina almuntathireen

Hausa
 
To, Shin sună jiran wani abu făce kamar misălin kwănukan waɗanda suka shũɗe daga gabăninsu? Ka ce: "Ku yi jira! Lalle nĩ tăre da ku, ină daga măsu jira."

Ayah  10:103  الأية
ثُمَّ نُنَجِّي رُسُلَنَا وَالَّذِينَ آمَنُوا ۚ كَذَٰلِكَ حَقًّا عَلَيْنَا نُنجِ الْمُؤْمِنِينَ
Thumma nunajjee rusulana wallatheenaamanoo kathalika haqqan AAalaynanunjee almu/mineen

Hausa
 
Sa'an nan kuma Mună kuɓutar da manzanninMu da waɗanda suka yi ĩmăni, kamar wannan ne, tabbatacce ne a gare Mu, Mu kuɓutar da măsu ĩmăni.

Ayah  10:104  الأية
قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِن كُنتُمْ فِي شَكٍّ مِّن دِينِي فَلَا أَعْبُدُ الَّذِينَ تَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللهِ وَلَٰكِنْ أَعْبُدُ اللهَ الَّذِي يَتَوَفَّاكُمْ ۖ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ
Qul ya ayyuha annasuin kuntum fee shakkin min deenee fala aAAbudu allatheenataAAbudoona min dooni Allahi walakin aAAbudu Allahaallathee yatawaffakum waomirtu an akoona minaalmu/mineen

Hausa
 
Ka ce: "Yă kũ mutăne! Idan kun kasance a cikin kőkanto daga addinĩna, to bă ni bauta wa,waɗanda kuke, baută wa, baicin Allah, kuma amma ina bauta wa Allah wanda Yake karɓar răyukanku. Kuma an umurce ni da in kasance daga măsu ĩmăni."

Ayah  10:105  الأية
وَأَنْ أَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفًا وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ الْمُشْرِكِينَ
Waan aqim wajhaka liddeeni haneefanwala takoonanna mina almushrikeen

Hausa
 
"Kuma (an ce mini ): Ka tsayar da fuskarka ga addini, kană karkatl zuwa ga gaskiya, kuma kada ka kasance daga măsu shirka.

Ayah  10:106  الأية
وَلَا تَدْعُ مِن دُونِ اللهِ مَا لَا يَنفَعُكَ وَلَا يَضُرُّكَ ۖ فَإِن فَعَلْتَ فَإِنَّكَ إِذًا مِّنَ الظَّالِمِينَ
Wala tadAAu min dooni Allahima la yanfaAAuka wala yadurruka fa-infaAAalta fa-innaka ithan mina aththalimeen

Hausa
 
"Kuma kada ka kirăyi, baicin Allah, abin da bă ya amfănin ka kuma bă ya cũtar ka. To, idan ka aikata haka, sa'an nan lalle kai, a lőkacin, kană daga măsu zălunci."

Ayah  10:107  الأية
وَإِن يَمْسَسْكَ اللهُ بِضُرٍّ فَلَا كَاشِفَ لَهُ إِلَّا هُوَ ۖ وَإِن يُرِدْكَ بِخَيْرٍ فَلَا رَادَّ لِفَضْلِهِ ۚ يُصِيبُ بِهِ مَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ ۚ وَهُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
Wa-in yamsaska Allahu bidurrinfala kashifa lahu illa huwa wa-in yuridkabikhayrin fala radda lifadlihi yuseebubihi man yashao min AAibadihi wahuwa alghafooru arraheem

Hausa
 
Kuma idan Allah Ya shăfe ka da wata cũta, to, băbu mai yăyẽ ta făce shi, kuma idan Yană nufin ka da wani alhẽri, to, băbumai mayar da falalarSa. Yană sămun wanda Yake so daga cikin băyinSa da shi. Kuma Shĩ ne Mai găfara, Mai jin ƙai.

Ayah  10:108  الأية
قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ قَدْ جَاءَكُمُ الْحَقُّ مِن رَّبِّكُمْ ۖ فَمَنِ اهْتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهْتَدِي لِنَفْسِهِ ۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيْهَا ۖ وَمَا أَنَا عَلَيْكُم بِوَكِيلٍ
Qul ya ayyuha annasuqad jaakumu alhaqqu min rabbikum famani ihtadafa-innama yahtadee linafsihi waman dalla fa-innamayadillu AAalayha wama ana AAalaykumbiwakeel

Hausa
 
Ka ce: "Yă ku mutăne! Lalle ne gaskiya, ta zo muku daga Ubangijinku. To, wanda ya shiryu, yă shiryu ne dőmin kansa kawai, kuma wanda ya ɓace yana ɓacewa ne a kansa kawai. Kuma ban zama wakĩli a kanku ba."

Ayah  10:109  الأية
وَاتَّبِعْ مَا يُوحَىٰ إِلَيْكَ وَاصْبِرْ حَتَّىٰ يَحْكُمَ اللهُ ۚ وَهُوَ خَيْرُ الْحَاكِمِينَ
WattabiAA ma yoohailayka wasbir hatta yahkumaAllahu wahuwa khayru alhakimeen

Hausa
 
Kuma ka bi abin da ake yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ka yi haƙuri har Allah Ya yi hukunci. Kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin măsu hukunci.





© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us