1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الر ۚ كِتَابٌ أُحْكِمَتْ آيَاتُهُ ثُمَّ فُصِّلَتْ مِن لَّدُنْ حَكِيمٍ خَبِيرٍ
Alif-lam-ra kitabun ohkimatayatuhu thumma fussilat min ladun hakeeminkhabeer
Hausa
A. L̃. R. Littăfi ne an kyautata ăyőyinsa, sa'an nan an bayyană su daki-daki,
daga wurin Mai hikima, Mai ƙididdigewa.
|
Ayah 11:2 الأية
أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا اللهَ ۚ إِنَّنِي لَكُم مِّنْهُ نَذِيرٌ وَبَشِيرٌ
Alla taAAbudoo illa Allahainnanee lakum minhu natheerun wabasheer
Hausa
Kada ku baută wa kőwa făce Allah. Lalle ne ni a gare ku mai gargaɗi ne kuma mai
bushără daga gare Shi.
|
Ayah 11:3 الأية
وَأَنِ اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ ثُمَّ تُوبُوا إِلَيْهِ يُمَتِّعْكُم مَّتَاعًا
حَسَنًا إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى وَيُؤْتِ كُلَّ ذِي فَضْلٍ فَضْلَهُ ۖ وَإِن
تَوَلَّوْا فَإِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ كَبِيرٍ
Waani istaghfiroo rabbakum thumma toobooilayhi yumattiAAkum mataAAan hasanan
ilaajalin musamman wayu/ti kulla thee fadlin fadlahuwa-in tawallaw fa-inee
akhafu AAalaykum AAathabayawmin kabeer
Hausa
Kuma ku nẽmi găfara gun Ubangijinku. Sa'an nan ku tũba zuwa gare Shi, Ya jiyar
da ku dăɗi, jiyarwa mai kyau zuwa ga ajali ambatacce, kuma Ya bai wa dukkan
ma'abucin, girma girmansa. Amma idan kun jũya, to, lalle nĩ, ină tsőron azăbar
yini mai girma a kanku.
|
Ayah 11:4 الأية
إِلَى اللهِ مَرْجِعُكُمْ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Ila Allahi marjiAAukum wahuwaAAala kulli shay-in qadeer
Hausa
Zuwa ga Allah makőmarku take, kuma Shĩ a kan kőmeMai ĩkon yi ne.
|
Ayah 11:5 الأية
أَلَا إِنَّهُمْ يَثْنُونَ صُدُورَهُمْ لِيَسْتَخْفُوا مِنْهُ ۚ أَلَا حِينَ
يَسْتَغْشُونَ ثِيَابَهُمْ يَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ ۚ إِنَّهُ
عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ
Ala innahum yathnoona sudoorahumliyastakhfoo minhu ala heena yastaghshoona
thiyabahumyaAAlamu ma yusirroona wama yuAAlinoona innahuAAaleemun bithati
assudoor
Hausa
To, lalle sũ sună karkatar da ƙirjinsu dőmin su ɓőye daga gare shi. To, a
lőkacin da suke lulluɓẽwa da tufăfinsu Yană sanin abin da suke ɓoyewa da abin da
suke bayyanăwa. Lalle Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirăză.
|
Ayah 11:6 الأية
وَمَا مِن دَابَّةٍ فِي الْأَرْضِ إِلَّا عَلَى اللهِ رِزْقُهَا وَيَعْلَمُ
مُسْتَقَرَّهَا وَمُسْتَوْدَعَهَا ۚ كُلٌّ فِي كِتَابٍ مُّبِينٍ
Wama min dabbatin fee al-ardiilla AAala Allahi rizquha wayaAAlamumustaqarraha
wamustawdaAAaha kullun fee kitabinmubeen
Hausa
Kuma băbu wata dabba a cikin ƙasa făce ga Allah arzikinta yake, kuma Yană sanin
matabbatarta da ma'azarta, duka sună cikin littăfi bayyananne.
|
Ayah 11:7 الأية
وَهُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ وَكَانَ
عَرْشُهُ عَلَى الْمَاءِ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ۗ وَلَئِن
قُلْتَ إِنَّكُم مَّبْعُوثُونَ مِن بَعْدِ الْمَوْتِ لَيَقُولَنَّ الَّذِينَ
كَفَرُوا إِنْ هَٰذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ
Wahuwa allathee khalaqa assamawatiwal-arda fee sittati ayyamin wakanaAAarshuhu
AAala alma-i liyabluwakum ayyukum ahsanuAAamalan wala-in qulta innakum
mabAAoothoona min baAAdi almawtilayaqoolanna allatheena kafaroo in hatha
illasihrun mubeen
Hausa
Kuma shi ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwanaki shida, kuma
Al'arshinSa ya kasance akan ruwa, dőmin Ya jarrabă ku, wannan ne daga cikinku
mafi kyăwon aiki. Kuma haƙĩƙa idan ka ce: "Lalle kũ waɗanda ake tăyarwa ne a
băyan mutuwa," haƙĩƙa waɗanda suka kăfirta sună cẽwa: "Wannan bai zama ba făce
sihiri bayyananne."
|
Ayah 11:8 الأية
وَلَئِنْ أَخَّرْنَا عَنْهُمُ الْعَذَابَ إِلَىٰ أُمَّةٍ مَّعْدُودَةٍ
لَّيَقُولُنَّ مَا يَحْبِسُهُ ۗ أَلَا يَوْمَ يَأْتِيهِمْ لَيْسَ مَصْرُوفًا
عَنْهُمْ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ
Wala-in akhkharna AAanhumu alAAathabaila ommatin maAAdoodatin layaqoolunna ma
yahbisuhuala yawma ya/teehim laysa masroofan AAanhum wahaqabihim ma kanoo bihi
yastahzi-oon
Hausa
Kuma lalle ne idan Mun jinkirta da azăba gare su zuwa ga wani lőkaci ƙidăyayye,
haƙĩƙa sunăcẽwa me yake tsare ta? To, a rănar da ză ta je musu, ba ta zama abin
karkatarwa ba daga gare su. Kuma abin da suka kasance suna yin izgili da shi, yă
wajaba a kansu.
|
Ayah 11:9 الأية
وَلَئِنْ أَذَقْنَا الْإِنسَانَ مِنَّا رَحْمَةً ثُمَّ نَزَعْنَاهَا مِنْهُ إِنَّهُ
لَيَئُوسٌ كَفُورٌ
Wala-in athaqna al-insanaminna rahmatan thumma nazaAAnahaminhu innahu layaoosun
kafoor
Hausa
Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sa'an nan kuma
Muka zăre ta daga gare shi, lalle ne shĩ, hakĩka, mai yanke tsammănine, mai
yawan kăfrci.
|
Ayah 11:10 الأية
وَلَئِنْ أَذَقْنَاهُ نَعْمَاءَ بَعْدَ ضَرَّاءَ مَسَّتْهُ لَيَقُولَنَّ ذَهَبَ
السَّيِّئَاتُ عَنِّي ۚ إِنَّهُ لَفَرِحٌ فَخُورٌ
Wala-in athaqnahu naAAmaabaAAda darraa massat-hu layaqoolanna thahabaassayyi-atu
AAannee innahu lafarihunfakhoor
Hausa
Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana masa ni'ima a băyan cũta ta shăfe shi, Yana cẽwa
mũnanan halaye sun tafi daga wurina. Lalle shi mai farin ciki ne, mai alfahari.
|
Ayah 11:11 الأية
إِلَّا الَّذِينَ صَبَرُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أُولَٰئِكَ لَهُم مَّغْفِرَةٌ
وَأَجْرٌ كَبِيرٌ
Illa allatheena sabaroowaAAamiloo assalihati ola-ika lahummaghfiratun waajrun
kabeer
Hausa
Sai waɗanda suka yi haƙuri kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai. Waɗannan sună da
găfara da lăda mai girma.
|
Ayah 11:12 الأية
فَلَعَلَّكَ تَارِكٌ بَعْضَ مَا يُوحَىٰ إِلَيْكَ وَضَائِقٌ بِهِ صَدْرُكَ أَن
يَقُولُوا لَوْلَا أُنزِلَ عَلَيْهِ كَنزٌ أَوْ جَاءَ مَعَهُ مَلَكٌ ۚ إِنَّمَا
أَنتَ نَذِيرٌ ۚ وَاللهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ وَكِيلٌ
FalaAAallaka tarikun baAAda mayooha ilayka wada-iqun bihi sadruka anyaqooloo
lawla onzila AAalayhi kanzun aw jaamaAAahu malakun innama anta natheerun
wallahuAAala kulli shay-in wakeel
Hausa
Sabőda haka tsammăninka kai mai barin săshen abin da aka yi wahayi zuwa gare ka
ne, kuma mai ƙuntata ƙirjinka da shi ne dőmin sun ce: "Dőmin me ba a saukar masa
da wata taska ba, kő kuma Mală'ika ya zo tăre de shi?" Kai mai gargaɗi ne kawai.
Kuma Allah ne wakili a kan kőme.
|
Ayah 11:13 الأية
أَمْ يَقُولُونَ افْتَرَاهُ ۖ قُلْ فَأْتُوا بِعَشْرِ سُوَرٍ مِّثْلِهِ
مُفْتَرَيَاتٍ وَادْعُوا مَنِ اسْتَطَعْتُم مِّن دُونِ اللهِ إِن كُنتُمْ
صَادِقِينَ
Am yaqooloona iftarahu qul fa/toobiAAashri suwarin mithlihi muftarayatin
wadAAoomani istataAAtum min dooni Allahi in kuntum sadiqeen
Hausa
Kő sună cewa: "Yă ƙirƙira shi ne."Ka ce: "Sai ku zo da sũrőri gőma misălinsa
ƙirƙirarru, kuma ku kirăyi wanda kuke iyăwa, baicin Allah, idan kun kasance măsu
gaskiya."
|
Ayah 11:14 الأية
فَإِلَّمْ يَسْتَجِيبُوا لَكُمْ فَاعْلَمُوا أَنَّمَا أُنزِلَ بِعِلْمِ اللهِ
وَأَن لَّا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ۖ فَهَلْ أَنتُم مُّسْلِمُونَ
Fa-illam yastajeeboo lakum faAAlamooannama onzila biAAilmi Allahi waan la
ilahailla huwa fahal antum muslimoon
Hausa
To, idan ba su amsa muku ba, to, ku sani cẽwa an saukar da shi kawai ne da sanin
Allah, kuma cẽwa băbu abin bauta wa făce Shi. To, shin, kũ măsu sallamăwa ne?,
|
Ayah 11:15 الأية
مَن كَانَ يُرِيدُ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا وَزِينَتَهَا نُوَفِّ إِلَيْهِمْ
أَعْمَالَهُمْ فِيهَا وَهُمْ فِيهَا لَا يُبْخَسُونَ
Man kana yureedu alhayataaddunya wazeenataha nuwaffi ilayhim aAAmalahumfeeha
wahum feeha la yubkhasoon
Hausa
Wanda ya kasance yă yi nufin răyuwar dũniya da ƙawarta, Mună cika musu ayyukansu
zuwa gare su a cikinta, kuma a cikinta bă ză a rage su ba.
|
Ayah 11:16 الأية
أُولَٰئِكَ الَّذِينَ لَيْسَ لَهُمْ فِي الْآخِرَةِ إِلَّا النَّارُ ۖ وَحَبِطَ مَا
صَنَعُوا فِيهَا وَبَاطِلٌ مَّا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Ola-ika allatheena laysa lahumfee al-akhirati illa annaru wahabitama sanaAAoo
feeha wabatilun makanoo yaAAmaloon
Hausa
Waɗannan ne waɗanda bă su da kőme a cikin Lăhira făce wuta, kuma abin da suka
sană'anta a cikinta (dũniya) yă ɓăci, kuma abin da suka kasance sună aikatăwa
ɓătacce ne.
|
Ayah 11:17 الأية
أَفَمَن كَانَ عَلَىٰ بَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّهِ وَيَتْلُوهُ شَاهِدٌ مِّنْهُ وَمِن
قَبْلِهِ كِتَابُ مُوسَىٰ إِمَامًا وَرَحْمَةً ۚ أُولَٰئِكَ يُؤْمِنُونَ بِهِ ۚ
وَمَن يَكْفُرْ بِهِ مِنَ الْأَحْزَابِ فَالنَّارُ مَوْعِدُهُ ۚ فَلَا تَكُ فِي
مِرْيَةٍ مِّنْهُ ۚ إِنَّهُ الْحَقُّ مِن رَّبِّكَ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ
لَا يُؤْمِنُونَ
Afaman kana AAala bayyinatinmin rabbihi wayatloohu shahidun minhu wamin qablihi
kitabumoosa imaman warahmatan ola-ikayu/minoona bihi waman yakfur bihi mina
al-ahzabi fannarumawAAiduhu fala taku fee miryatin minhu innahu alhaqqumin
rabbika walakinna akthara annasi layu/minoon
Hausa
Shin, wanda ya kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijinsa, kuma wata shaida
tană biyar sa daga gare Shi, kuma a gabăninsa akwai littăfin Mũsăabin kőyi da
rahama? Waɗannan sună yin ĩmăni da shi, kuma wanda ya kăfirta da shi daga
ƙungiyőyi, to, wută ce makőmarsa. Sabőda haka kada ka kasance a cikin shakka
daga gare shi. Lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka, amma kuma mafi yawan
mutăne bă su yin ĩmăni.
|
Ayah 11:18 الأية
وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَىٰ عَلَى اللهِ كَذِبًا ۚ أُولَٰئِكَ يُعْرَضُونَ
عَلَىٰ رَبِّهِمْ وَيَقُولُ الْأَشْهَادُ هَٰؤُلَاءِ الَّذِينَ كَذَبُوا عَلَىٰ
رَبِّهِمْ ۚ أَلَا لَعْنَةُ اللهِ عَلَى الظَّالِمِينَ
Waman athlamu mimmani iftaraAAala Allahi kathiban ola-ika yuAAradoonaAAala
rabbihim wayaqoolu al-ashhadu haola-iallatheena kathaboo AAala rabbihim
alalaAAnatu Allahi AAala aththalimeen
Hausa
Kuma wăne ne mafi zălunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah? Waɗannan ană
gitta su ga Ubangijinsu, kuma măsu shaida su ce: "Waɗannan ne suka yi ƙarya ga
Ubangijinsu. To, la'anar Allah ta tabbata a kan azzălumai."
|
Ayah 11:19 الأية
الَّذِينَ يَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللهِ وَيَبْغُونَهَا عِوَجًا وَهُم
بِالْآخِرَةِ هُمْ كَافِرُونَ
Allatheena yasuddoona AAansabeeli Allahi wayabghoonaha AAiwajan wahum
bil-akhiratihum kafiroon
Hausa
Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah kuma sună nẽman ta karkace, kuma sũ ga
Lăhira sună kăfirta.
|
Ayah 11:20 الأية
أُولَٰئِكَ لَمْ يَكُونُوا مُعْجِزِينَ فِي الْأَرْضِ وَمَا كَانَ لَهُم مِّن دُونِ
اللهِ مِنْ أَوْلِيَاءَ ۘ يُضَاعَفُ لَهُمُ الْعَذَابُ ۚ مَا كَانُوا
يَسْتَطِيعُونَ السَّمْعَ وَمَا كَانُوا يُبْصِرُونَ
Ola-ika lam yakoonoo muAAjizeena feeal-ardi wama kana lahum min dooni Allahimin
awliyaa yudaAAafu lahumu alAAathabu makanoo yastateeAAoona assamAAa wama
kanooyubsiroon
Hausa
Waɗannan ne ba su kasance mabuwăya ba a cikin ƙasa, kuma waɗansu masőya ba su
kasance ba a gare su, baicin Allah. Ană ninka musu azăba, ba su kasance sună iya
ji ba, kuma ba su kasance sună gani ba.
|
Ayah 11:21 الأية
أُولَٰئِكَ الَّذِينَ خَسِرُوا أَنفُسَهُمْ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا
يَفْتَرُونَ
Ola-ika allatheena khasirooanfusahum wadalla AAanhum ma kanoo yaftaroon
Hausa
Waɗannan ne wɗanda suka yi hasărar răyukansu, kuma abin da suka kasance sună
ƙirƙirawa ya ɓace musu.
|
Ayah 11:22 الأية
لَا جَرَمَ أَنَّهُمْ فِي الْآخِرَةِ هُمُ الْأَخْسَرُونَ
La jarama annahum fee al-akhiratihumu al-akhsaroon
Hausa
Băbu makawă cẽwa, haƙĩƙa, sũ a lăhira, sũ ne mafi hasăra.
|
Ayah 11:23 الأية
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَأَخْبَتُوا إِلَىٰ رَبِّهِمْ
أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Inna allatheena amanoowaAAamiloo asalihati waakhbatoo ilarabbihim ola-ika
as-habu aljannati hum feehakhalidoon
Hausa
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmăni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi
tawălu'i zuwa ga Ubangijinsu, waɗannan ne abőkan Aljanna, sună madawwama a
cikinta.
|
Ayah 11:24 الأية
مَثَلُ الْفَرِيقَيْنِ كَالْأَعْمَىٰ وَالْأَصَمِّ وَالْبَصِيرِ وَالسَّمِيعِ ۚ
هَلْ يَسْتَوِيَانِ مَثَلًا ۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Mathalu alfareeqayni kalaAAmawal-asammi walbaseeri wassameeAAihal yastawiyani
mathalan afala tathakkaroon
Hausa
Misălin ɓangaren biyu kamar makăho ne da kurmă, da mai gani da mai ji. Shin,
sună daidaita ga misăli? Ashe, bă ku yin tunăni?
|
Ayah 11:25 الأية
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِ إِنِّي لَكُمْ نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Walaqad arsalna noohan ilaqawmihi innee lakum natheerun mubeen
Hausa
Kuma haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutanensa, (ya ce): "Lalle ne ni, a gare ku
mai gargaɗi bayyananne ne."
|
Ayah 11:26 الأية
أَن لَّا تَعْبُدُوا إِلَّا اللهَ ۖ إِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ
أَلِيمٍ
An la taAAbudoo illa Allahainnee akhafu AAalaykum AAathaba yawmin aleem
Hausa
"Kada ku baută wa kőwa făce Allah. Lalle nĩ, ină jin tsőron azăbar yini mai
raɗaɗi a kanku."
|
Ayah 11:27 الأية
فَقَالَ الْمَلَأُ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن قَوْمِهِ مَا نَرَاكَ إِلَّا بَشَرًا
مِّثْلَنَا وَمَا نَرَاكَ اتَّبَعَكَ إِلَّا الَّذِينَ هُمْ أَرَاذِلُنَا بَادِيَ
الرَّأْيِ وَمَا نَرَىٰ لَكُمْ عَلَيْنَا مِن فَضْلٍ بَلْ نَظُنُّكُمْ كَاذِبِينَ
Faqala almalao allatheenakafaroo min qawmihi ma naraka illa basharanmithlana
wama naraka ittabaAAaka illaallatheena hum arathiluna badiya arra/yiwama nara
lakum AAalayna min fadlinbal nathunnukum kathibeen
Hausa
Sai mashăwarta waɗanda suka kăfirta, daga mutănensa, suka ce: "Bă mu ganin ka
făce mutum kake kamarmu, kuma ba mu ganin wani ya bĩ ka făce waɗanda suke sũ
ƙasƙantattunmu ne marasa tunani. Kuma bă mu ganin wata falală agare ka a kanmu.
Ă'a, Mună zaton ku maƙaryata ne."
|
Ayah 11:28 الأية
قَالَ يَا قَوْمِ أَرَأَيْتُمْ إِن كُنتُ عَلَىٰ بَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّي وَآتَانِي
رَحْمَةً مِّنْ عِندِهِ فَعُمِّيَتْ عَلَيْكُمْ أَنُلْزِمُكُمُوهَا وَأَنتُمْ لَهَا
كَارِهُونَ
Qala ya qawmi araaytum inkuntu AAala bayyinatin min rabbee waataneerahmatan min
AAindihi faAAummiyat AAalaykum anulzimukumoohawaantum laha karihoon
Hausa
Ya ce: "Ya mutănena! Shin, kun gani idan na kasance a kan wata hujja bayyananna
daga Ubangijina, kuma Yă bă ni wata Rahama daga wurinSa, Sa'an nan aka rufe ta
(ita Rahamar) daga gare ku, shin, ză mu tĩlasta mukuita, alhăli kuwa kũ măsu ƙi
gare ta ne?
|
Ayah 11:29 الأية
وَيَا قَوْمِ لَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مَالًا ۖ إِنْ أَجْرِيَ إِلَّا عَلَى
اللهِ ۚ وَمَا أَنَا بِطَارِدِ الَّذِينَ آمَنُوا ۚ إِنَّهُم مُّلَاقُو رَبِّهِمْ
وَلَٰكِنِّي أَرَاكُمْ قَوْمًا تَجْهَلُونَ
Waya qawmi la as-alukumAAalayhi malan in ajriya illa AAala Allahiwama ana
bitaridi allatheena amanooinnahum mulaqoo rabbihim walakinnee arakumqawman
tajhaloon
Hausa
"Kuma yă mutănena! Bă zan tambaye ku wata dũkiya ba akansa, ijărata ba ta zama
ba, făce daga Allah, kuma ban zama mai kőrar waɗanda suka yĩ ĩmăni ba. Haƙĩƙa
sũ, măsu haɗuwa da Ubangijinsu ne, kuma amma ni, ină ganin ku mutăne ne
jăhilai."
|
Ayah 11:30 الأية
وَيَا قَوْمِ مَن يَنصُرُنِي مِنَ اللهِ إِن طَرَدتُّهُمْ ۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Waya qawmi man yansurunee minaAllahi in taradtuhum afala tathakkaroon
Hausa
"Kuma ya mutănena! Wăne ne yake taimakőna daga Allah idan na kőre su? Ashe, bă
ku tunăni?"
|
Ayah 11:31 الأية
وَلَا أَقُولُ لَكُمْ عِندِي خَزَائِنُ اللهِ وَلَا أَعْلَمُ الْغَيْبَ وَلَا
أَقُولُ إِنِّي مَلَكٌ وَلَا أَقُولُ لِلَّذِينَ تَزْدَرِي أَعْيُنُكُمْ لَن
يُؤْتِيَهُمُ اللهُ خَيْرًا ۖ اللهُ أَعْلَمُ بِمَا فِي أَنفُسِهِمْ ۖ إِنِّي
إِذًا لَّمِنَ الظَّالِمِينَ
Wala aqoolu lakum AAindee khaza-inuAllahi wala aAAlamu alghayba wala aqooluinnee
malakun wala aqoolu lillatheena tazdareeaAAyunukum lan yu/tiyahumu Allahu
khayran AllahuaAAlamu bima fee anfusihim innee ithan lamina aththalimeen
Hausa
"Kuma bă ni ce muku a wurĩna taskőkin Allah suke kuma bă ină sanin gaibi ba ne.
Kuma ba ină cẽwa ni Mală'ika ba ne. Kuma ba ni cẽwa ga waɗanda idănunku suke
wulăkantăwa, Allah bă zai bă su alhẽri ba. Allah ne Mafi sani ga abin da yake
cikin zukatansu. Lalle ne ni, idan (nă yi haka) dă ina daga cikin azzalumai."
|
Ayah 11:32 الأية
قَالُوا يَا نُوحُ قَدْ جَادَلْتَنَا فَأَكْثَرْتَ جِدَالَنَا فَأْتِنَا بِمَا
تَعِدُنَا إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ
Qaloo ya noohu qad jadaltanafaaktharta jidalana fa/tina bimataAAiduna in kunta
mina assadiqeen
Hausa
Suka ce: "Yă Nũhu, lalle ne kă yi jayayya da mu, sa'an nan kă yawaita yi mana
jidăli, to, ka ző mana da abin da kake yi mana wa'adi idan kă kasance daga măsu
gaskiya."
|
Ayah 11:33 الأية
قَالَ إِنَّمَا يَأْتِيكُم بِهِ اللهُ إِن شَاءَ وَمَا أَنتُم بِمُعْجِزِينَ
Qala innama ya/teekum bihi Allahuin shaa wama antum bimuAAjizeen
Hausa
Ya ce: "Allah kawai ne Yake zo muku da shi idan Ya so. Kuma ba ku zama mabuwăya
ba."
|
Ayah 11:34 الأية
وَلَا يَنفَعُكُمْ نُصْحِي إِنْ أَرَدتُّ أَنْ أَنصَحَ لَكُمْ إِن كَانَ اللهُ
يُرِيدُ أَن يُغْوِيَكُمْ ۚ هُوَ رَبُّكُمْ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Wala yanfaAAukum nushee inaradtu an ansaha lakum in kana Allahuyureedu an
yughwiyakum huwa rabbukum wa-ilayhi turjaAAoon
Hausa
"Kuma nasĩhăta bă ză ta amfăne ku ba, idan nă yi nufin in yi muku nasĩha, idan
Allah Yakasance Yană nufin Ya halaka ku. Shĩ ne Ubangijinku, kuma zuwa gare Shi
ake mayar da ku."
|
Ayah 11:35 الأية
أَمْ يَقُولُونَ افْتَرَاهُ ۖ قُلْ إِنِ افْتَرَيْتُهُ فَعَلَيَّ إِجْرَامِي
وَأَنَا بَرِيءٌ مِّمَّا تُجْرِمُونَ
Am yaqooloona iftarahu qul iniiftaraytuhu faAAalayya ijramee waana baree-on
mimmatujrimoon
Hausa
Ko sună cẽwa: (Nũhu) ya ƙirƙira shi. Ka ce: "Idan nĩ (Nũhu) na ƙirƙira shi to,
laifĩnă a kaina yake, kuma nĩ mai barrantă ne daga abin da kuke yi na laifi."
|
Ayah 11:36 الأية
وَأُوحِيَ إِلَىٰ نُوحٍ أَنَّهُ لَن يُؤْمِنَ مِن قَوْمِكَ إِلَّا مَن قَدْ آمَنَ
فَلَا تَبْتَئِسْ بِمَا كَانُوا يَفْعَلُونَ
Waoohiya ila noohinannahu lan yu/mina min qawmika illa man qad amanafala
tabta-is bima kanoo yafAAaloon
Hausa
Kuma aka yi wahayi zuwa ga Nũhu cẽwa: Lalle ne băbu mai yin ĩmăni daga mutănenka
făce wanda ya riga ya yi ĩmănin, sabődahaka kada ka yi baƙin ciki da abin da
suka kasance sună aikatăwa.
|
Ayah 11:37 الأية
وَاصْنَعِ الْفُلْكَ بِأَعْيُنِنَا وَوَحْيِنَا وَلَا تُخَاطِبْنِي فِي الَّذِينَ
ظَلَمُوا ۚ إِنَّهُم مُّغْرَقُونَ
WasnaAAi alfulka bi-aAAyuninawawahyina wala tukhatibnee fee allatheenathalamoo
innahum mughraqoon
Hausa
Kuma ka sassaƙa jirgi da kyau a kan idanunMu da wahayinMu, kuma kada ka yi Mini
magana a cikin sha'anin waɗanda suka kăfirta, lalle ne sũ, waɗanda akenutsarwa
ne.
|
Ayah 11:38 الأية
وَيَصْنَعُ الْفُلْكَ وَكُلَّمَا مَرَّ عَلَيْهِ مَلَأٌ مِّن قَوْمِهِ سَخِرُوا
مِنْهُ ۚ قَالَ إِن تَسْخَرُوا مِنَّا فَإِنَّا نَسْخَرُ مِنكُمْ كَمَا تَسْخَرُونَ
WayasnaAAu alfulka wakullamamarra AAalayhi malaon min qawmihi sakhiroo minhu
qala intaskharoo minna fa-inna naskharu minkum kamataskharoon
Hausa
Kuma Yană sassaƙa jirgin cikin natsuwa, kuma a kő yaushe waɗansu shugabanni daga
mutănensa suka shũɗe a gabansa, sai su yi izgili gare shi. Ya ce: "Idan kun yi
izgili gare mu, to, haƙĩƙa mũ mă ză mu yi izgili gare ku, kamar yadda kuke yin
izgili.
|
Ayah 11:39 الأية
فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ مَن يَأْتِيهِ عَذَابٌ يُخْزِيهِ وَيَحِلُّ عَلَيْهِ عَذَابٌ
مُّقِيمٌ
Fasawfa taAAlamoona man ya/teehi AAathabunyukhzeehi wayahillu AAalayhi AAathabun
muqeem
Hausa
"Sa'an nan da sannu ză ku san wanda azăba ză ta zo masa, ta wulakantă shi (a
dũniya), kuma wata azăba zaunanna ta sauka a kansa (a Lăhira)."
|
Ayah 11:40 الأية
حَتَّىٰ إِذَا جَاءَ أَمْرُنَا وَفَارَ التَّنُّورُ قُلْنَا احْمِلْ فِيهَا مِن
كُلٍّ زَوْجَيْنِ اثْنَيْنِ وَأَهْلَكَ إِلَّا مَن سَبَقَ عَلَيْهِ الْقَوْلُ
وَمَنْ آمَنَ ۚ وَمَا آمَنَ مَعَهُ إِلَّا قَلِيلٌ
Hatta itha jaaamruna wafara attannooru qulna ihmilfeeha min kullin zawjayni
ithnayni waahlaka illaman sabaqa AAalayhi alqawlu waman amana wama amanamaAAahu
illa qaleel
Hausa
Har a lőkacin da umurninMu ya je, kuma tandă ta ɓulɓula. Muka ce: "Ka ɗauka, a
cikinta, daga kőme, ma'aura biyu, da kuma iyalanka, făce wanda magana ta gabăta
a kansa, da wanda ya yi ĩmăni." Amma kuma băbu waɗanda suka yi ĩmăni tăre da shi
făce kaɗan."
|
Ayah 11:41 الأية
وَقَالَ ارْكَبُوا فِيهَا بِسْمِ اللهِ مَجْرَاهَا وَمُرْسَاهَا ۚ إِنَّ رَبِّي
لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ
Waqala irkaboo feeha bismi Allahimajraha wamursaha inna rabbeelaghafoorun raheem
Hausa
Kuma ya ce: "Ku hau a cikinta, da sũnan Allah magudănarta da matabbatarta. Lalle
ne Ubangijĩna, haƙĩƙa, Mai găfara ne, Mai jin ƙai."
|
Ayah 11:42 الأية
وَهِيَ تَجْرِي بِهِمْ فِي مَوْجٍ كَالْجِبَالِ وَنَادَىٰ نُوحٌ ابْنَهُ وَكَانَ
فِي مَعْزِلٍ يَا بُنَيَّ ارْكَب مَّعَنَا وَلَا تَكُن مَّعَ الْكَافِرِينَ
Wahiya tajree bihim fee mawjin kaljibaliwanada noohunu ibnahu wakana
feemaAAzilin ya bunayya irkab maAAana walatakun maAAa alkafireen
Hausa
Kuma ita tană gudăna da su a cikin tăguwar ruwa kamai duwătsu, sai Nũhu ya
kirăyi ɗansa alhăli, kuwa ya kasance can wuri mai nĩsa. "Yă ƙaramin ɗănă! zo ka
hau tăre da mu, kuma kada ka kasance tăre da kăfirai!"
|
Ayah 11:43 الأية
قَالَ سَآوِي إِلَىٰ جَبَلٍ يَعْصِمُنِي مِنَ الْمَاءِ ۚ قَالَ لَا عَاصِمَ
الْيَوْمَ مِنْ أَمْرِ اللهِ إِلَّا مَن رَّحِمَ ۚ وَحَالَ بَيْنَهُمَا الْمَوْجُ
فَكَانَ مِنَ الْمُغْرَقِينَ
Qala saawee ila jabalinyaAAsimunee mina alma-i qala la AAasimaalyawma min amri
Allahi illa man rahima wahalabaynahuma almawju fakana mina almughraqeen
Hausa
Ya ce: "Zan tattara zuwa ga wani dũtse ya tsare ni daga ruwan." (Nũhu) ya ce:
"Băbu mai tsarẽwa a yau daga umurnin Allah făce wanda Ya yi wa rahama." Sai
taguwar ruwa ta shămakace a tsakăninsu, sai ya kasance daga waɗanda aka nutsar.
|
Ayah 11:44 الأية
وَقِيلَ يَا أَرْضُ ابْلَعِي مَاءَكِ وَيَا سَمَاءُ أَقْلِعِي وَغِيضَ الْمَاءُ
وَقُضِيَ الْأَمْرُ وَاسْتَوَتْ عَلَى الْجُودِيِّ ۖ وَقِيلَ بُعْدًا لِّلْقَوْمِ
الظَّالِمِينَ
Waqeela ya ardu iblaAAee maakiwaya samao aqliAAee wagheeda almaowaqudiya al-amru
wastawat AAala aljoodiyyiwaqeela buAAdan lilqawmi aththalimeen
Hausa
Kuma aka ce: "Yă ƙasa! Ki haɗiye ruwanki, kuma yă sama! Ki kăme."Kuma aka faƙar
da ruwan kuma aka hukunta al'amarin, kuma Jirgin ya daidaita a kan Jũdiyyi, kuma
aka ce: "Nĩsa ya tabbata ga mutăne azzălumai."
|
Ayah 11:45 الأية
وَنَادَىٰ نُوحٌ رَّبَّهُ فَقَالَ رَبِّ إِنَّ ابْنِي مِنْ أَهْلِي وَإِنَّ
وَعْدَكَ الْحَقُّ وَأَنتَ أَحْكَمُ الْحَاكِمِينَ
Wanada noohun rabbahufaqala rabbi inna ibnee min ahlee wa-inna waAAdaka
alhaqquwaanta ahkamu alhakimeen
Hausa
Kuma Nũhu ya kira Ubangijinsa, sa'an nan ya ce: "Yă Ubangijina! Lalle ne ɗăna na
daga iyălĩna! Kuma haƙĩƙa wa'adinKa gaskiya ne, kuma Kai ne Mafi hukuncin măsu
yin hukunci."
|
Ayah 11:46 الأية
قَالَ يَا نُوحُ إِنَّهُ لَيْسَ مِنْ أَهْلِكَ ۖ إِنَّهُ عَمَلٌ غَيْرُ صَالِحٍ ۖ
فَلَا تَسْأَلْنِ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ ۖ إِنِّي أَعِظُكَ أَن تَكُونَ مِنَ
الْجَاهِلِينَ
Qala ya noohu innahulaysa min ahlika innahu AAamalun ghayru salihin falatas-alni
ma laysa laka bihi AAilmun innee aAAithukaan takoona mina aljahileen
Hausa
Ya ce: "Yă Nũhu! Lalle ne shi bă ya a ciki iyălanka, lalle ne shĩ, aiki ne wanda
ba na ƙwarai ba, sabőda haka kada ka tambaye Ni abin da bă ka da ilmi a kansa.
Haƙĩƙa, Nĩ Ină yi maka gargaɗi kada ka kasance daga jăhilai."
|
Ayah 11:47 الأية
قَالَ رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ
وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُن مِّنَ الْخَاسِرِينَ
Qala rabbi innee aAAoothu bikaan as-alaka ma laysa lee bihi AAilmun
wa-illataghfir lee watarhamnee akun mina alkhasireen
Hausa
Ya ce: "Yă Ubangijina! Lalle ne nĩ, ină nẽman tsari gare Ka da in tambaye Ka
abin da bă ni da wani ilmi a kansa. Idan ba Ka găfarta mini ba, kuma Ka yi mini
rahama, zan kasance daga măsu hasăra."
|
Ayah 11:48 الأية
قِيلَ يَا نُوحُ اهْبِطْ بِسَلَامٍ مِّنَّا وَبَرَكَاتٍ عَلَيْكَ وَعَلَىٰ أُمَمٍ
مِّمَّن مَّعَكَ ۚ وَأُمَمٌ سَنُمَتِّعُهُمْ ثُمَّ يَمَسُّهُم مِّنَّا عَذَابٌ
أَلِيمٌ
Qeela ya noohu ihbitbisalamin minna wabarakatin AAalayka waAAalaomamin mimman
maAAaka waomamun sanumattiAAuhum thumma yamassuhumminna AAathabun aleem
Hausa
Aka ce: "Ya Nũhu! Ka sauka da aminci da, a gare Mu da albarka a kanka, kuma
rahama ta tabbata a kan waɗansu al'ummőmi daga waɗanda suke tăre da kai. Da
waɗansu al'ummőmi da ză Mu jiyar da su dăɗi, sa'an nan kuma azăba mai raɗaɗi ta
shafe su daga gare Mu."
|
Ayah 11:49 الأية
تِلْكَ مِنْ أَنبَاءِ الْغَيْبِ نُوحِيهَا إِلَيْكَ ۖ مَا كُنتَ تَعْلَمُهَا أَنتَ
وَلَا قَوْمُكَ مِن قَبْلِ هَٰذَا ۖ فَاصْبِرْ ۖ إِنَّ الْعَاقِبَةَ لِلْمُتَّقِينَ
Tilka min anba-i alghaybi nooheehailayka ma kunta taAAlamuha anta wala
qawmukamin qabli hatha fasbir inna alAAaqibatalilmuttaqeen
Hausa
Waccan ƙissa tană daga lăbăran gaibi, Mună yin wahayinsu zuwa gare ka
(Muhammadu). Ba ka kasance kană sanin su ba, haka kuma mutănenka ba su sani ba
daga gabănin wannan. Sai ka yi haƙuri. Lalle ne ăƙiba tană ga măsu taƙawa,
|
Ayah 11:50 الأية
وَإِلَىٰ عَادٍ أَخَاهُمْ هُودًا ۚ قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللهَ مَا لَكُم
مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۖ إِنْ أَنتُمْ إِلَّا مُفْتَرُونَ
Wa-ila AAadin akhahumhoodan qala ya qawmi oAAbudoo Allaha malakum min ilahin
ghayruhu in antum illa muftaroon
Hausa
Kuma zuwa ga Ădăwa, (Mun aika) ɗan'uwansu Hũdu. Ya ce: "Yă kũ mutănena! Ku bauta
wa Allah. Ba ku da wani abin bautăwa făce Shi. Ba ku kasance ba făce kună măsu
ƙirƙirăwa.
|
Ayah 11:51 الأية
يَا قَوْمِ لَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ أَجْرًا ۖ إِنْ أَجْرِيَ إِلَّا عَلَى
الَّذِي فَطَرَنِي ۚ أَفَلَا تَعْقِلُونَ
Ya qawmi la as-alukum AAalayhiajran in ajriya illa AAala allathee fataraneeafala
taAAqiloon
Hausa
"Yă ku mutănena! Bă ni tambayar ku wata ijăra a kansa, ijărata ba ta zama ba,
făce ga wanda Ya ƙăga halittata. Shin fa, bă ku hankalta?"
|
Ayah 11:52 الأية
وَيَا قَوْمِ اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ ثُمَّ تُوبُوا إِلَيْهِ يُرْسِلِ السَّمَاءَ
عَلَيْكُم مِّدْرَارًا وَيَزِدْكُمْ قُوَّةً إِلَىٰ قُوَّتِكُمْ وَلَا تَتَوَلَّوْا
مُجْرِمِينَ
Waya qawmi istaghfiroo rabbakumthumma tooboo ilayhi yursili assamaa
AAalaykummidraran wayazidkum quwwatan ila quwwatikum walatatawallaw mujrimeen
Hausa
"Kuma, ya mutănena! Ku nẽmi Ubangijinku găfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare
Shi,zai saki sama a kanku, tană mai yawan zubar da ruwa, kuma Ya ƙăra muku wani
ƙarfi ga ƙarfinku. Kuma kada ku jũya kună măsu laifi."
|
Ayah 11:53 الأية
قَالُوا يَا هُودُ مَا جِئْتَنَا بِبَيِّنَةٍ وَمَا نَحْنُ بِتَارِكِي آلِهَتِنَا
عَن قَوْلِكَ وَمَا نَحْنُ لَكَ بِمُؤْمِنِينَ
Qaloo ya hoodu maji/tana bibayyinatin wama nahnu bitarikeealihatina AAan qawlika
wama nahnulaka bimu/mineen
Hausa
Suka ce: "Yă Hũdu! Ba ka zo mana da wata hujja bayyananna ba, kuma ba mu zama
măsu barin abũbuwan bautawarmu ba dőmin maganarka, kuma ba mu zama măsu yin
ĩmăni da kai ba."
|
Ayah 11:54 الأية
إِن نَّقُولُ إِلَّا اعْتَرَاكَ بَعْضُ آلِهَتِنَا بِسُوءٍ ۗ قَالَ إِنِّي أُشْهِدُ
اللهَ وَاشْهَدُوا أَنِّي بَرِيءٌ مِّمَّا تُشْرِكُونَ
In naqoolu illa iAAtaraka baAAdualihatina bisoo-in qala innee oshhidu
Allahawashhadoo annee baree-on mimma tushrikoon
Hausa
"Bă mu cẽwa, sai dai kurum sashen abũbuwan bautawarmu ya săme ka da cũtar
hauka." Yace: "Lalle ne nĩ, ină shaida waAllah, kuma ku yi shaidar cẽwa" lalle
ne nĩ mai barranta ne dagb abin da kuke yin shirki da shi."
|
Ayah 11:55 الأية
مِن دُونِهِ ۖ فَكِيدُونِي جَمِيعًا ثُمَّ لَا تُنظِرُونِ
Min doonihi fakeedoonee jameeAAan thumma latunthiroon
Hausa
"Baicin Allah: Sai ku yi mini kaidi gabă ɗaya, sa'an nan kuma kada ku yi mini
jinkiri."
|
Ayah 11:56 الأية
إِنِّي تَوَكَّلْتُ عَلَى اللهِ رَبِّي وَرَبِّكُم ۚ مَّا مِن دَابَّةٍ إِلَّا
هُوَ آخِذٌ بِنَاصِيَتِهَا ۚ إِنَّ رَبِّي عَلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Innee tawakkaltu AAala Allahirabbee warabbikum ma min dabbatin illa huwa
akhithunbinasiyatiha inna rabbee AAala siratinmustaqeem
Hausa
"Haƙĩƙa, ni na dőgara ga Allah, Ubangijĩna kuma Ubangijinku. Băbu wata dabba
făce Shi ne Mai riko ga kwarkwaɗarta. Haƙĩƙa, Ubangijĩna Yană (kan) tafarki
madaidaici."
|
Ayah 11:57 الأية
فَإِن تَوَلَّوْا فَقَدْ أَبْلَغْتُكُم مَّا أُرْسِلْتُ بِهِ إِلَيْكُمْ ۚ
وَيَسْتَخْلِفُ رَبِّي قَوْمًا غَيْرَكُمْ وَلَا تَضُرُّونَهُ شَيْئًا ۚ إِنَّ
رَبِّي عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ حَفِيظٌ
Fa-in tawallaw faqad ablaghtukum maorsiltu bihi ilaykum wayastakhlifu rabbee
qawman ghayrakum walatadurroonahu shay-an inna rabbee AAala kullishay-in hafeeth
Hausa
"To! Idan kun jũya, haƙĩƙa, nă iyar muku abin da aka aiko ni da shi zuwa gare
ku. Kuma Ubangijĩna Yană musanya waɗansu mutăne, waɗansunku su maye muku. Kuma
bă ku cũtar Sa da kőme. Lalle Ubangijina a kan dukkan kőme, Matsari ne."
|
Ayah 11:58 الأية
وَلَمَّا جَاءَ أَمْرُنَا نَجَّيْنَا هُودًا وَالَّذِينَ آمَنُوا مَعَهُ بِرَحْمَةٍ
مِّنَّا وَنَجَّيْنَاهُم مِّنْ عَذَابٍ غَلِيظٍ
Walamma jaa amrunanajjayna hoodan wallatheena amanoomaAAahu birahmatin minna
wanajjaynahum minAAathabin ghaleeth
Hausa
Kuma a lőkacin da umurninmu ya je, Muka kuɓutar da Hũdu da waɗanda suka yi ĩmăni
tăre da shi, sabődawata rahama daga gare Mu. Kuma Muka kuɓutr da su daga azăba
mai kauri.
|
Ayah 11:59 الأية
وَتِلْكَ عَادٌ ۖ جَحَدُوا بِآيَاتِ رَبِّهِمْ وَعَصَوْا رُسُلَهُ وَاتَّبَعُوا
أَمْرَ كُلِّ جَبَّارٍ عَنِيدٍ
Watilka AAadun jahadoo bi-ayatirabbihim waAAasaw rusulahu wattabaAAoo amra
kullijabbarin AAaneed
Hausa
Haka Ădăwa suka kasance, sun yi musun ăyőyin Ubangijinsu, kuma sun săɓa wa
ManzanninSa, kuma sun bi umurnin dukan mai girman kai, makangari.
|
Ayah 11:60 الأية
وَأُتْبِعُوا فِي هَٰذِهِ الدُّنْيَا لَعْنَةً وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ ۗ أَلَا إِنَّ
عَادًا كَفَرُوا رَبَّهُمْ ۗ أَلَا بُعْدًا لِّعَادٍ قَوْمِ هُودٍ
WaotbiAAoo fee hathihi addunyalaAAnatan wayawma alqiyamati ala inna
AAadankafaroo rabbahum ala buAAdan liAAadin qawmi hood
Hausa
Kuma an biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rănar Kiyăma. To! Lalle ne
Ădăwa sun kăfirta da Ubangijinsu. To, Nĩsa ya tabbata ga Ădăwa, mutănen Hũdu!
|
Ayah 11:61 الأية
وَإِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَالِحًا ۚ قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللهَ مَا
لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۖ هُوَ أَنشَأَكُم مِّنَ الْأَرْضِ وَاسْتَعْمَرَكُمْ
فِيهَا فَاسْتَغْفِرُوهُ ثُمَّ تُوبُوا إِلَيْهِ ۚ إِنَّ رَبِّي قَرِيبٌ مُّجِيبٌ
Wa-ila thamooda akhahum salihanqala ya qawmi oAAbudoo Allaha malakum min ilahin
ghayruhu huwa anshaakum mina al-ardiwastaAAmarakum feeha fastaghfiroohu
thummatooboo ilayhi inna rabbee qareebun mujeeb
Hausa
Kuma zuwa ga Samũdăwa (an aika) ɗan'uwansu Sălihu. Ya ce: "Ya mutănena! Ku bauta
wa Allah. Bă ku da wani abin bautăwa făce Shi. Shĩ ne Ya ƙăga halittarku daga
ƙasa, kuma Ya sanya ku măsu yin kyarkyara a cikinta. Sai ku nẽme Shi găfara,
sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi. Lalle Ubangijina Makusanci ne Mai
karɓăwa."
|
Ayah 11:62 الأية
قَالُوا يَا صَالِحُ قَدْ كُنتَ فِينَا مَرْجُوًّا قَبْلَ هَٰذَا ۖ أَتَنْهَانَا
أَن نَّعْبُدَ مَا يَعْبُدُ آبَاؤُنَا وَإِنَّنَا لَفِي شَكٍّ مِّمَّا تَدْعُونَا
إِلَيْهِ مُرِيبٍ
Qaloo ya salihuqad kunta feena marjuwwan qabla hatha atanhanaan naAAbuda ma
yaAAbudu abaonawa-innana lafee shakkin mimma tadAAoonailayhi mureeb
Hausa
Suka ce: "Ya Sălihu! Haƙĩƙa, kă kasance a cikinmu, wanda ake fatan wani alhẽri
da shi a gabănin wannan. Shin kana hana mu bauta wa abin da ubanninmu suke bauta
wa? Kuma haƙĩƙa mũ, mună cikin shakka daga abin da kake kiran mu gare shi, mai
sanya kőkanto."
|
Ayah 11:63 الأية
قَالَ يَا قَوْمِ أَرَأَيْتُمْ إِن كُنتُ عَلَىٰ بَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّي وَآتَانِي
مِنْهُ رَحْمَةً فَمَن يَنصُرُنِي مِنَ اللهِ إِنْ عَصَيْتُهُ ۖ فَمَا
تَزِيدُونَنِي غَيْرَ تَخْسِيرٍ
Qala ya qawmi araaytum inkuntu AAala bayyinatin min rabbee waataneeminhu
rahmatan faman yansurunee mina Allahiin AAasaytuhu fama tazeedoonanee ghayra
takhseer
Hausa
Ya ce: "Ya mutănẽna! Kun gani? Idan na kasance a kan hujja bayyananna daga
Ubangijina, kuma Ya bă ni rahama daga gare Shi, to, wane ne zai taimake ni daga
Allah idan nă săɓa Masa? Sa'an nan bă ză ku ƙăre ni da kőme ba făce hasăra."
|
Ayah 11:64 الأية
وَيَا قَوْمِ هَٰذِهِ نَاقَةُ اللهِ لَكُمْ آيَةً فَذَرُوهَا تَأْكُلْ فِي أَرْضِ
اللهِ وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوءٍ فَيَأْخُذَكُمْ عَذَابٌ قَرِيبٌ
Waya qawmi hathihi naqatuAllahi lakum ayatan fatharooha ta/kulfee ardi Allahi
wala tamassoohabisoo-in faya/khuthakum AAathabun qareeb
Hausa
"Kuma ya mutănena! wannan răƙumar Allah ce, tană ăyă a gare ku. Sai ku bar ta ta
ci a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shăfe ta da wata cũta kar azăba makusanciya
ta kăma ku."
|
Ayah 11:65 الأية
فَعَقَرُوهَا فَقَالَ تَمَتَّعُوا فِي دَارِكُمْ ثَلَاثَةَ أَيَّامٍ ۖ ذَٰلِكَ
وَعْدٌ غَيْرُ مَكْذُوبٍ
FaAAaqarooha faqalatamattaAAoo fee darikum thalathata ayyamin thalikawaAAdun
ghayru makthoob
Hausa
Sai suka sőke ta. Sai ya ce: "Kuji dăɗi a cikin gidăjenku kwăna uku. Wannan
wa'adi ne bă abin ƙaryatăwa ba."
|
Ayah 11:66 الأية
فَلَمَّا جَاءَ أَمْرُنَا نَجَّيْنَا صَالِحًا وَالَّذِينَ آمَنُوا مَعَهُ
بِرَحْمَةٍ مِّنَّا وَمِنْ خِزْيِ يَوْمِئِذٍ ۗ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ الْقَوِيُّ
الْعَزِيزُ
Falamma jaa amrunanajjayna salihan wallatheena amanoomaAAahu birahmatin minna
wamin khizyi yawmi-ithininna rabbaka huwa alqawiyyu alAAazeez
Hausa
To, a lőkacin da umurninMu ya je, muka kuɓutar da Sălihu da waɗanda suka yi
ĩmăni tăre da shi, sabőda wata rahama daga gare Mu, kuma daga wulăkancin rănar
nan. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMai ƙarfi, Mabuwăyi.
|
Ayah 11:67 الأية
وَأَخَذَ الَّذِينَ ظَلَمُوا الصَّيْحَةُ فَأَصْبَحُوا فِي دِيَارِهِمْ جَاثِمِينَ
Waakhatha allatheena thalamooassayhatu faasbahoo fee diyarihimjathimeen
Hausa
Sai tsăwa ta kăma waɗanda suka yi zălunci, sai suka wăyi gari sună guggurfăne a
cikin gidăjensu.
|
Ayah 11:68 الأية
كَأَن لَّمْ يَغْنَوْا فِيهَا ۗ أَلَا إِنَّ ثَمُودَ كَفَرُوا رَبَّهُمْ ۗ أَلَا
بُعْدًا لِّثَمُودَ
Kaan lam yaghnaw feeha alainna thamooda kafaroo rabbahum ala buAAdan lithamood
Hausa
Kamar dai ba su zauna a cikinta ba. To! Lalle ne samũdăwa sun kăfirce wa
Ubangijinsu. To, Nĩsa ya tabbata ga Samũdăwa.
|
Ayah 11:69 الأية
وَلَقَدْ جَاءَتْ رُسُلُنَا إِبْرَاهِيمَ بِالْبُشْرَىٰ قَالُوا سَلَامًا ۖ قَالَ
سَلَامٌ ۖ فَمَا لَبِثَ أَن جَاءَ بِعِجْلٍ حَنِيذٍ
Walaqad jaat rusuluna ibraheemabilbushra qaloo salaman qalasalamun fama labitha
an jaa biAAijlin haneeth
Hausa
Kuma haƙĩƙa, manzanninMu sun je wa Ibrăhim da bushăra suka ce: "Aminci." Ya ce:
"Aminci (ya tabbata a gare ku)." Sa'an nan bai yi jinkiri ba ya je da maraƙi
ƙawătacce.
|
Ayah 11:70 الأية
فَلَمَّا رَأَىٰ أَيْدِيَهُمْ لَا تَصِلُ إِلَيْهِ نَكِرَهُمْ وَأَوْجَسَ مِنْهُمْ
خِيفَةً ۚ قَالُوا لَا تَخَفْ إِنَّا أُرْسِلْنَا إِلَىٰ قَوْمِ لُوطٍ
Falamma raa aydiyahum latasilu ilayhi nakirahum waawjasa minhum kheefatan
qaloola takhaf inna orsilna ila qawmi loot
Hausa
Sa'an nan a lőkacin da ya ga hannayensu bă su săduwa zuwa gare shi (maraƙin),
sai ya yi ƙyămarsu, kuma ya ji tsőronsu. Suka ce, "Kada kaji tsőro lalle ne mũ,
an aiko mu ne zuwa ga mutănen Lũɗu"
|
Ayah 11:71 الأية
وَامْرَأَتُهُ قَائِمَةٌ فَضَحِكَتْ فَبَشَّرْنَاهَا بِإِسْحَاقَ وَمِن وَرَاءِ
إِسْحَاقَ يَعْقُوبَ
Wamraatuhu qa-imatun fadahikatfabashsharnaha bi-ishaqa wamin wara-iishaqa
yaAAqoob
Hausa
Kuma mătarsa tană tsaye . Ta yi dăriya. Sai Muka yi mata bushăra (da haihuwar)
Is'hăƙa, kuma a bayan Is'hăƙa, Yăƙũbu.
|
Ayah 11:72 الأية
قَالَتْ يَا وَيْلَتَىٰ أَأَلِدُ وَأَنَا عَجُوزٌ وَهَٰذَا بَعْلِي شَيْخًا ۖ إِنَّ
هَٰذَا لَشَيْءٌ عَجِيبٌ
Qalat ya waylata aaliduwaana AAajoozun wahatha baAAlee shaykhan inna
hathalashay-on AAajeeb
Hausa
Sai ta ce: "Yă kaitőna! Shin, zan haihu ne alhăli kuwa ină tsőhuwa, kuma ga
mijĩna tsőho ne? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mămăki."
|
Ayah 11:73 الأية
قَالُوا أَتَعْجَبِينَ مِنْ أَمْرِ اللهِ ۖ رَحْمَتُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ
عَلَيْكُمْ أَهْلَ الْبَيْتِ ۚ إِنَّهُ حَمِيدٌ مَّجِيدٌ
Qaloo ataAAjabeena min amri Allahirahmatu Allahi wabarakatuhu AAalaykum
ahlaalbayti innahu hameedun majeed
Hausa
Suka ce: "Shin kină mămaki ne daga al'amarin Allah? Rahamar Allah da albarkarSa
su tabbata a kanku, ya mutănen babban gida! Lalle ne Shĩ abin gődewa ne, Mai
girma."
|
Ayah 11:74 الأية
فَلَمَّا ذَهَبَ عَنْ إِبْرَاهِيمَ الرَّوْعُ وَجَاءَتْهُ الْبُشْرَىٰ يُجَادِلُنَا
فِي قَوْمِ لُوطٍ
Falamma thahaba AAan ibraheemaarrawAAu wajaat-hu albushra yujadilunafee qawmi
loot
Hausa
To, a lőkacin da firgita ta tafi daga Ibrăhĩm, kuma bushăra tă je masa, Yană mai
jayayya a gare Mu, sabőda mutănen Lũɗu!
|
Ayah 11:75 الأية
إِنَّ إِبْرَاهِيمَ لَحَلِيمٌ أَوَّاهٌ مُّنِيبٌ
Inna ibraheema lahaleemun awwahunmuneeb
Hausa
Lalle Ibrăhĩm, haƙĩƙa mai haƙuri ne, mai yawan addu'a, mai tawakkali.
|
Ayah 11:76 الأية
يَا إِبْرَاهِيمُ أَعْرِضْ عَنْ هَٰذَا ۖ إِنَّهُ قَدْ جَاءَ أَمْرُ رَبِّكَ ۖ
وَإِنَّهُمْ آتِيهِمْ عَذَابٌ غَيْرُ مَرْدُودٍ
Ya ibraheemu aAAridAAan hatha innahu qad jaa amru rabbika wa-innahum
ateehimAAathabun ghayru mardood
Hausa
Ya Ibrăhĩm! Ka bijira daga wannan. Lalle shi, haƙĩƙa, umurnin Ubangijinka ne ya
zo, kuma lalle ne sũ, abin da yake mai je musu azăba ce wadda bă a iya hanăwa.
|
Ayah 11:77 الأية
وَلَمَّا جَاءَتْ رُسُلُنَا لُوطًا سِيءَ بِهِمْ وَضَاقَ بِهِمْ ذَرْعًا وَقَالَ
هَٰذَا يَوْمٌ عَصِيبٌ
Walamma jaat rusulunalootan see-a bihim wadaqa bihim tharAAan waqalahatha yawmun
AAaseeb
Hausa
Kuma a lőkacin da manzanninMu suka je wa Lũɗu aka ɓăta masa rai game da su, ya,
ƙuntata rai sabőda su. Ya ce: "Wannan yini ne mai tsananin masĩfa."
|
Ayah 11:78 الأية
وَجَاءَهُ قَوْمُهُ يُهْرَعُونَ إِلَيْهِ وَمِن قَبْلُ كَانُوا يَعْمَلُونَ
السَّيِّئَاتِ ۚ قَالَ يَا قَوْمِ هَٰؤُلَاءِ بَنَاتِي هُنَّ أَطْهَرُ لَكُمْ ۖ
فَاتَّقُوا اللهَ وَلَا تُخْزُونِ فِي ضَيْفِي ۖ أَلَيْسَ مِنكُمْ رَجُلٌ
رَّشِيدٌ
Wajaahu qawmuhu yuhraAAoona ilayhiwamin qablu kanoo yaAAmaloona assayyi-ati
qalaya qawmi haola-i banatee hunna atharulakum fattaqoo Allaha wala tukhzooni
fee dayfeealaysa minkum rajulun rasheed
Hausa
Kuma mutănensa suka je masa sună gaggăwa zuwa gare shi, kuma a gabăni, sun
kasance sună aikatăwar mũnănan ayyuka. Ya ce: "Yă mutănẽna! waɗannan, 'yă'yă na
sũ ne mafiya tsarki a gare ku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku wulăkantă
ni a cikin băƙĩna. Shin, băbu wani namiji shiryayye daga gare ku?"
|
Ayah 11:79 الأية
قَالُوا لَقَدْ عَلِمْتَ مَا لَنَا فِي بَنَاتِكَ مِنْ حَقٍّ وَإِنَّكَ لَتَعْلَمُ
مَا نُرِيدُ
Qaloo laqad AAalimta ma lanafee banatika min haqqin wa-innaka lataAAlamu
manureed
Hausa
Suka ce: "Lalle, haƙĩƙa kă sani, bă mu da wani hakki a cikin 'ya'yanka, kuma
lalle kai haƙĩƙa, kană sane da abin da muke nufi."
|
Ayah 11:80 الأية
قَالَ لَوْ أَنَّ لِي بِكُمْ قُوَّةً أَوْ آوِي إِلَىٰ رُكْنٍ شَدِيدٍ
Qala law anna lee bikum quwwatan aw aweeila ruknin shadeed
Hausa
Ya ce: "Dă dai ină da wani ƙarfi game da ku, kő kuwa ină da gőyon băya daga wani
rukuni mai ƙarfi?"
|
Ayah 11:81 الأية
قَالُوا يَا لُوطُ إِنَّا رُسُلُ رَبِّكَ لَن يَصِلُوا إِلَيْكَ ۖ فَأَسْرِ
بِأَهْلِكَ بِقِطْعٍ مِّنَ اللَّيْلِ وَلَا يَلْتَفِتْ مِنكُمْ أَحَدٌ إِلَّا
امْرَأَتَكَ ۖ إِنَّهُ مُصِيبُهَا مَا أَصَابَهُمْ ۚ إِنَّ مَوْعِدَهُمُ الصُّبْحُ
ۚ أَلَيْسَ الصُّبْحُ بِقَرِيبٍ
Qaloo ya lootu innarusulu rabbika lan yasiloo ilayka faasri bi-ahlika
biqitAAinmina allayli wala yaltafit minkum ahadun illaimraataka innahu museebuha
ma asabahuminna mawAAidahumu assubhu alaysa assubhubiqareeb
Hausa
(Manzannin) Suka ce: "Yă Lũɗu! Lalle mũ, manzannin Ubangijinka ne. Bă ză su iya
săduwa zuwa gare ka ba. Sai ka yi tafiyarka a wani yankin dare da iyălinka, kuma
kada wani daga gare ku ya waiwaya făce mătarka. Lalle ne abin da ya same su mai
sămunta ne. Lalle wa'adinsu lőkacin săfiya ne. Shin lőkacin săfiya bă kusa ba
ne?"
|
Ayah 11:82 الأية
فَلَمَّا جَاءَ أَمْرُنَا جَعَلْنَا عَالِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهَا
حِجَارَةً مِّن سِجِّيلٍ مَّنضُودٍ
Falamma jaa amrunajaAAalna AAaliyaha safilahawaamtarna AAalayha hijaratanmin
sijjeelin mandood
Hausa
Sa'an nan a lőkacin da umurninMu ya je, Muka sanya na samanta ya zama na
ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwătsu a kanta (ƙasar Lũɗu) daga taɓocũrarre.
|
Ayah 11:83 الأية
مُّسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَ ۖ وَمَا هِيَ مِنَ الظَّالِمِينَ بِبَعِيدٍ
Musawwamatan AAinda rabbika wama hiyamina aththalimeena bibaAAeed
Hausa
Alamtacce a wurin Ubangijinka. Kuma ita (ƙasar Lũɗu)ba ta zama mai nĩsa ba daga
azzălumai (kuraishăwa).
|
Ayah 11:84 الأية
وَإِلَىٰ مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْبًا ۚ قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللهَ مَا
لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۖ وَلَا تَنقُصُوا الْمِكْيَالَ وَالْمِيزَانَ ۚ
إِنِّي أَرَاكُم بِخَيْرٍ وَإِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ مُّحِيطٍ
Wa-ila madyana akhahumshuAAayban qala ya qawmi oAAbudoo Allaha malakum min
ilahin ghayruhu wala tanqusooalmikyala walmeezana innee arakumbikhayrin wa-innee
akhafu AAalaykum AAathaba yawminmuheet
Hausa
Kuma zuwa ga Madyana (Mun aika) ɗan'uwansu Shu'aibu. Ya ce: "Ya Mutănena! Ku
bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautăwa făce shi kuma kada ku rage mũdu da
sikẽli. Lalle nĩ, ină ganin ku da wadăta. Kuma lalle ină ji muku tsőron azăbar
yini mai kẽwayẽwa."
|
Ayah 11:85 الأية
وَيَا قَوْمِ أَوْفُوا الْمِكْيَالَ وَالْمِيزَانَ بِالْقِسْطِ ۖ وَلَا تَبْخَسُوا
النَّاسَ أَشْيَاءَهُمْ وَلَا تَعْثَوْا فِي الْأَرْضِ مُفْسِدِينَ
Waya qawmi awfoo almikyala walmeezanabilqisti wala tabkhasoo annasaashyaahum
wala taAAthaw fee al-ardimufsideen
Hausa
"Ya mutănẽna! Ku cika mũdu da sikẽli da ădalci, kuma kada ku naƙasta wa mutăne
kăyansu, kuma kada ku yi ɓarnă a cikin ƙasa kună măsu fasădi."
|
Ayah 11:86 الأية
بَقِيَّتُ اللهِ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ ۚ وَمَا أَنَا عَلَيْكُم
بِحَفِيظٍ
Baqiyyatu Allahi khayrun lakum inkuntum mu/mineena wama ana AAalaykum bihafeeth
Hausa
"Falalar Allah mai wanzuwa ita ce mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance
muminai, kuma ni bă mai tsaro ne a kanku ba."
|
Ayah 11:87 الأية
قَالُوا يَا شُعَيْبُ أَصَلَاتُكَ تَأْمُرُكَ أَن نَّتْرُكَ مَا يَعْبُدُ آبَاؤُنَا
أَوْ أَن نَّفْعَلَ فِي أَمْوَالِنَا مَا نَشَاءُ ۖ إِنَّكَ لَأَنتَ الْحَلِيمُ
الرَّشِيدُ
Qaloo ya shuAAaybu asalatukata/muruka an natruka ma yaAAbudu abaonaaw an
nafAAala fee amwalina ma nashaoinnaka laanta alhaleemu arrasheed
Hausa
Suka ce: "Yă Shu'aibu! Shin sallarka ce take umurtar ka ga mu bar abin da
ubanninmu suke bautăwa, kő kuwa mu bar aikata abin da muke so a cikin
dũkiyőyinmu? Lalle, haƙĩƙa kai ne mai haƙuri shiryayye!"
|
Ayah 11:88 الأية
قَالَ يَا قَوْمِ أَرَأَيْتُمْ إِن كُنتُ عَلَىٰ بَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّي
وَرَزَقَنِي مِنْهُ رِزْقًا حَسَنًا ۚ وَمَا أُرِيدُ أَنْ أُخَالِفَكُمْ إِلَىٰ مَا
أَنْهَاكُمْ عَنْهُ ۚ إِنْ أُرِيدُ إِلَّا الْإِصْلَاحَ مَا اسْتَطَعْتُ ۚ وَمَا
تَوْفِيقِي إِلَّا بِاللهِ ۚ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَإِلَيْهِ أُنِيبُ
Qala ya qawmi araaytum inkuntu AAala bayyinatin min rabbee warazaqanee minhu
rizqanhasanan wama oreedu an okhalifakum ilama anhakum AAanhu in oreedu illa
al-islahama istataAAtu wama tawfeeqee illa billahiAAalayhi tawakkaltu wa-ilayhi
oneeb
Hausa
Ya ce: "Ya mutănena! Kun gani idan no kasance a kan hujja bayyananniya daga
Ubangijina, kuma Ya azurta nĩ da arzikimai kyăwo daga gare Shi? Kuma bă ni nufin
in săɓa muku zuwa ga abin da nake hana ku daga gare shi. Bă ni nufin kőme făce
gyără, gwargwadon da na sămi dăma. Kuma muwăfaƙăta ba ta zama ba făce daga
Allah. A gare shi na dőgara, kuma zuwa gare Shi na wakkala."
|
Ayah 11:89 الأية
وَيَا قَوْمِ لَا يَجْرِمَنَّكُمْ شِقَاقِي أَن يُصِيبَكُم مِّثْلُ مَا أَصَابَ
قَوْمَ نُوحٍ أَوْ قَوْمَ هُودٍ أَوْ قَوْمَ صَالِحٍ ۚ وَمَا قَوْمُ لُوطٍ مِّنكُم
بِبَعِيدٍ
Waya qawmi la yajrimannakumshiqaqee an yuseebakum mithlu ma asabaqawma noohin aw
qawma hoodin aw qawma salihinwama qawmu lootin minkum bibaAAeed
Hausa
"Kuma ya mutănena! Kada săɓa mini ya ɗauke ku ga misălin abin da ya sămi mutănen
Nũhu kő kuwa mutănen Hũdu kő kuwa mutănen Sălihu ya săme ku. Mutănen Lũɗu ba su
zama a wuri mai nĩsa ba daga gare ku."
|
Ayah 11:90 الأية
وَاسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ ثُمَّ تُوبُوا إِلَيْهِ ۚ إِنَّ رَبِّي رَحِيمٌ وَدُودٌ
Wastaghfiroo rabbakum thumma toobooilayhi inna rabbee raheemun wadood
Hausa
"Kuma ku nẽmi Ubangijinku găfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare shi. Lalle
Ubangijĩna Mai Jin ƙai ne, Mai nũna sőyayya."
|
Ayah 11:91 الأية
قَالُوا يَا شُعَيْبُ مَا نَفْقَهُ كَثِيرًا مِّمَّا تَقُولُ وَإِنَّا لَنَرَاكَ
فِينَا ضَعِيفًا ۖ وَلَوْلَا رَهْطُكَ لَرَجَمْنَاكَ ۖ وَمَا أَنتَ عَلَيْنَا
بِعَزِيزٍ
Qaloo ya shuAAaybu manafqahu katheeran mimma taqoolu wa-inna lanarakafeena
daAAeefan walawla rahtukalarajamnaka wama anta AAalayna biAAazeez
Hausa
Suka ce: "Yă Shu'aibu! Bă mu fahimta da yawa daga abin da kake faɗi, kuma mună
ganin ka mai rauni a cikinmu. Kuma bă dőmin jama'arka ba dă mun jẽfe ka, sabőda
ba ka zama mai daraja a gunmu ba."
|
Ayah 11:92 الأية
قَالَ يَا قَوْمِ أَرَهْطِي أَعَزُّ عَلَيْكُم مِّنَ اللهِ وَاتَّخَذْتُمُوهُ
وَرَاءَكُمْ ظِهْرِيًّا ۖ إِنَّ رَبِّي بِمَا تَعْمَلُونَ مُحِيطٌ
Qala ya qawmi arahteeaAAazzu AAalaykum mina Allahi wattakhathtumoohuwaraakum
thihriyyan inna rabbee bimataAAmaloona muheet
Hausa
Ya ce: "Ya mutănena! Ashe, jama'ăta ce mafi daraja a gare ku daga Allah, kuma
kun riƙẽ Shi a băyanku abin jẽfarwa? Lallene Ubangijĩna Mai kẽwayẽwa nega abin
da kuke aikatăwa."
|
Ayah 11:93 الأية
وَيَا قَوْمِ اعْمَلُوا عَلَىٰ مَكَانَتِكُمْ إِنِّي عَامِلٌ ۖ سَوْفَ تَعْلَمُونَ
مَن يَأْتِيهِ عَذَابٌ يُخْزِيهِ وَمَنْ هُوَ كَاذِبٌ ۖ وَارْتَقِبُوا إِنِّي
مَعَكُمْ رَقِيبٌ
Waya qawmi iAAmaloo AAala makanatikuminnee AAamilun sawfa taAAlamoona man
ya/teehi AAathabunyukhzeehi waman huwa kathibun wartaqiboo innemaAAakum raqeeb
Hausa
"Kuma ya mutănena! Ku yi aiki a kan hălinku. Lalle nĩmai aiki ne. Da sannu ză ku
san wăne ne azăba ză ta zo masa, ta wulakanta shi, kuma wăne ne maƙaryaci. Kuma
ku yi jiran dăko, lalle ni mai dăko ne tăre da ku."
|
Ayah 11:94 الأية
وَلَمَّا جَاءَ أَمْرُنَا نَجَّيْنَا شُعَيْبًا وَالَّذِينَ آمَنُوا مَعَهُ
بِرَحْمَةٍ مِّنَّا وَأَخَذَتِ الَّذِينَ ظَلَمُوا الصَّيْحَةُ فَأَصْبَحُوا فِي
دِيَارِهِمْ جَاثِمِينَ
Walamma jaa amrunanajjayna shuAAayban wallatheena amanoomaAAahu birahmatin minna
waakhathati allatheenathalamoo assayhatu faasbahoofee diyarihim jathimeen
Hausa
Kuma a lőkacin da umurninMu yă je, Muka kuɓutar da Shu'aibu da waɗanda suka yi
ĩmăni tăre da shi, sabőda wata rahama daga gare, Mu. Kuma tsăwa ta kama waɗanda
suka yi zălunci. Sai suka wăyi gari guggurfăne a cikin gidăjensu.
|
Ayah 11:95 الأية
كَأَن لَّمْ يَغْنَوْا فِيهَا ۗ أَلَا بُعْدًا لِّمَدْيَنَ كَمَا بَعِدَتْ ثَمُودُ
Kaan lam yaghnaw feeha alabuAAdan limadyana kama baAAidat thamood
Hausa
Kamar ba su zaună ba a cikinsu. To, halaka ta tabbata ga Madyana kamar yadda
Samũdăwa suka halaka.
|
Ayah 11:96 الأية
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مُوسَىٰ بِآيَاتِنَا وَسُلْطَانٍ مُّبِينٍ
Walaqad arsalna moosa bi-ayatinawasultanin mubeen
Hausa
Kuma haƙĩƙa Mun aiki Mũsă da ăyőyinMu, da dalĩli bayyananne.
|
Ayah 11:97 الأية
إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِ فَاتَّبَعُوا أَمْرَ فِرْعَوْنَ ۖ وَمَا أَمْرُ
فِرْعَوْنَ بِرَشِيدٍ
Ila firAAawna wamala-ihi fattabaAAooamra firAAawna wama amru firAAawna birasheed
Hausa
Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa. Sai suka bi umurnin Fir'auna, amma al'amarin
Fir'auna bai zama shiryayye ba.
|
Ayah 11:98 الأية
يَقْدُمُ قَوْمَهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فَأَوْرَدَهُمُ النَّارَ ۖ وَبِئْسَ
الْوِرْدُ الْمَوْرُودُ
Yaqdumu qawmahu yawma alqiyamatifaawradahumu annara wabi/sa alwirdu almawrood
Hausa
Yană shũgabantar mutănensa a Rănar Kiyăma, har ya tuzgar da su a wuta. Kuma tir
da irin tuzgăwarsu.
|
Ayah 11:99 الأية
وَأُتْبِعُوا فِي هَٰذِهِ لَعْنَةً وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ ۚ بِئْسَ الرِّفْدُ
الْمَرْفُودُ
WaotbiAAoo fee hathihi laAAnatanwayawma alqiyamati bi/sa arrifdu almarfood
Hausa
Kuma aka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rănar Kiyăma. Tir da
kyautar da ake yi musu.
|
Ayah 11:100 الأية
ذَٰلِكَ مِنْ أَنبَاءِ الْقُرَىٰ نَقُصُّهُ عَلَيْكَ ۖ مِنْهَا قَائِمٌ وَحَصِيدٌ
Thalika min anba-i alquranaqussuhu AAalayka minha qa-imun wahaseed
Hausa
Wancan Yană daga lăbăran alƙaryőyi. Mună bă ka lăbărinsu, daga gare su akwai
wanda ke tsaye da kuma girbabbe.
|
Ayah 11:101 الأية
وَمَا ظَلَمْنَاهُمْ وَلَٰكِن ظَلَمُوا أَنفُسَهُمْ ۖ فَمَا أَغْنَتْ عَنْهُمْ
آلِهَتُهُمُ الَّتِي يَدْعُونَ مِن دُونِ اللهِ مِن شَيْءٍ لَّمَّا جَاءَ أَمْرُ
رَبِّكَ ۖ وَمَا زَادُوهُمْ غَيْرَ تَتْبِيبٍ
Wama thalamnahumwalakin thalamoo anfusahum famaaghnat AAanhum alihatuhumu
allatee yadAAoona min dooni Allahimin shay-in lamma jaa amru rabbika wama
zadoohumghayra tatbeeb
Hausa
Kuma ba Mu zălunce su ba, amma sun zălunci kansu sa'an nan abũbuwan bautawarsu
waɗanda suke kiran su, baicin Allah, ba su wadătar musu kőme ba a lőkacin da
umurnin Ubangijinka ya je, kuma (gumăkan) ba su ƙăra musu wani abu ba făce
hasăra.
|
Ayah 11:102 الأية
وَكَذَٰلِكَ أَخْذُ رَبِّكَ إِذَا أَخَذَ الْقُرَىٰ وَهِيَ ظَالِمَةٌ ۚ إِنَّ
أَخْذَهُ أَلِيمٌ شَدِيدٌ
Wakathalika akhthu rabbika ithaakhatha alqura wahiya thalimatuninna akhthahu
aleemun shadeed
Hausa
Kuma kamar wancan ne kămun Ubangijinka, idan Ya kăma alƙaryőyi alhăli kuwa sună
măsu zălunci. Lalle kamũnSa mai raɗaɗi ne, mai tsanani.
|
Ayah 11:103 الأية
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً لِّمَنْ خَافَ عَذَابَ الْآخِرَةِ ۚ ذَٰلِكَ يَوْمٌ
مَّجْمُوعٌ لَّهُ النَّاسُ وَذَٰلِكَ يَوْمٌ مَّشْهُودٌ
Inna fee thalika laayatanliman khafa AAathaba al-akhirati thalikayawmun
majmooAAun lahu annasu wathalikayawmun mashhoodun
Hausa
Lalle ne a cikin wancan akwai ăyă ga wanda ya ji tsőron azăbar Lăhira. Wancan
yini ne wanda ake tăra mutăne a cikinsa kuma wancan yini ne abin halarta.
|
Ayah 11:104 الأية
وَمَا نُؤَخِّرُهُ إِلَّا لِأَجَلٍ مَّعْدُودٍ
Wama nu-akhkhiruhu illali-ajalin maAAdood
Hausa
Ba Mu jinkirtă shi ba făce dőmin ajali ƙidăyayye.
|
Ayah 11:105 الأية
يَوْمَ يَأْتِ لَا تَكَلَّمُ نَفْسٌ إِلَّا بِإِذْنِهِ ۚ فَمِنْهُمْ شَقِيٌّ
وَسَعِيدٌ
Yawma ya/ti la takallamu nafsun illabi-ithnihi faminhum shaqiyyun wasaAAeed
Hausa
Rănar da za ta zo wani rai ba ya iya magana făce da izninSa. Sa'an nan daga
cikinsu akwai shaƙiyyi da mai arziki.
|
Ayah 11:106 الأية
فَأَمَّا الَّذِينَ شَقُوا فَفِي النَّارِ لَهُمْ فِيهَا زَفِيرٌ وَشَهِيقٌ
Faamma allatheena shaqoofafee annari lahum feeha zafeerun washaheeq
Hausa
To, amma waɗanda suka yi shaƙăwa, to, sună a cikin wuta. Sună măsu ƙăra da shẽka
acikinta.
|
Ayah 11:107 الأية
خَالِدِينَ فِيهَا مَا دَامَتِ السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ إِلَّا مَا شَاءَ رَبُّكَ
ۚ إِنَّ رَبَّكَ فَعَّالٌ لِّمَا يُرِيدُ
Khalideena feeha ma damatiassamawatu wal-ardu illama shaa rabbuka inna rabbaka
faAAAAalun limayureed
Hausa
Suna madawwama a cikinta matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, făce abin da
Ubangijinka Ya so. Lalle Ubangijinka Mai aikatăwa ne ga abin da Yake nufi.
|
Ayah 11:108 الأية
وَأَمَّا الَّذِينَ سُعِدُوا فَفِي الْجَنَّةِ خَالِدِينَ فِيهَا مَا دَامَتِ
السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ إِلَّا مَا شَاءَ رَبُّكَ ۖ عَطَاءً غَيْرَ مَجْذُوذٍ
Waamma allatheena suAAidoofafee aljannati khalideena feeha ma damatiassamawatu
wal-ardu illama shaa rabbuka AAataan ghayra majthooth
Hausa
Amma waɗanda suka yi arziki to, sună a cikin Aljanna sună madawwama ,a cikinta,
matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, făce abin da Ubangijinka Ya so. Kyauta wadda
bă ta yankẽwa.
|
Ayah 11:109 الأية
فَلَا تَكُ فِي مِرْيَةٍ مِّمَّا يَعْبُدُ هَٰؤُلَاءِ ۚ مَا يَعْبُدُونَ إِلَّا
كَمَا يَعْبُدُ آبَاؤُهُم مِّن قَبْلُ ۚ وَإِنَّا لَمُوَفُّوهُمْ نَصِيبَهُمْ
غَيْرَ مَنقُوصٍ
Fala taku fee miryatin mimmayaAAbudu haola-i ma yaAAbudoona illakama yaAAbudu
abaohum min qablu wa-innalamuwaffoohum naseebahum ghayra manqoos
Hausa
Sabőda haka kada ka kasance a cikin shakka daga abin da waɗannan suke bautawa.
Bă su wata ibăda făce kamar yadda ubanninsu ke aikatăwa a gabani. Kuma haƙĩƙa
Mũ, Măsu cika musu rabon su ne, bă tăre da nakasăwa ba.
|
Ayah 11:110 الأية
وَلَقَدْ آتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ فَاخْتُلِفَ فِيهِ ۚ وَلَوْلَا كَلِمَةٌ
سَبَقَتْ مِن رَّبِّكَ لَقُضِيَ بَيْنَهُمْ ۚ وَإِنَّهُمْ لَفِي شَكٍّ مِّنْهُ
مُرِيبٍ
Walaqad atayna moosaalkitaba fakhtulifa feehi walawla kalimatunsabaqat min
rabbika laqudiya baynahum wa-innahum lafeeshakkin minhu mureeb
Hausa
Kuma haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsă littăfi, sai aka săɓă wa jũna a cikinsa. Kuma bă
dőmin wata kalma wadda ta gabăta daga Ubangijinka ba, haƙĩƙa, dă an yi hukunci a
tsakăninsu. Kuma haƙĩƙa, sună a cikin wata shakka, game da shi, mai sanya
kőkanto.
|
Ayah 11:111 الأية
وَإِنَّ كُلًّا لَّمَّا لَيُوَفِّيَنَّهُمْ رَبُّكَ أَعْمَالَهُمْ ۚ إِنَّهُ بِمَا
يَعْمَلُونَ خَبِيرٌ
Wa-inna kullan lammalayuwaffiyannahum rabbuka aAAmalahum innahu bimayaAAmaloona
khabeer
Hausa
Kuma lalle, haƙĩƙa, Ubangijinka Mai cika wa kőwa (sakamakon) ayyukansa ne. Lalle
Shĩ, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke aikatăwa.
|
Ayah 11:112 الأية
فَاسْتَقِمْ كَمَا أُمِرْتَ وَمَن تَابَ مَعَكَ وَلَا تَطْغَوْا ۚ إِنَّهُ بِمَا
تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ
Fastaqim kama omirta waman tabamaAAaka wala tatghaw innahu bima
taAAmaloonabaseer
Hausa
Sai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kai da waɗanda suka tũba tăre da kai
kună bă măsu ƙẽtara haddi ba. Lalle shĩ, Mai gani ne ga abin da kuke aikatăwa.
|
Ayah 11:113 الأية
وَلَا تَرْكَنُوا إِلَى الَّذِينَ ظَلَمُوا فَتَمَسَّكُمُ النَّارُ وَمَا لَكُم
مِّن دُونِ اللهِ مِنْ أَوْلِيَاءَ ثُمَّ لَا تُنصَرُونَ
Wala tarkanoo ila allatheenathalamoo fatamassakumu annaru wamalakum min dooni
Allahi min awliyaa thumma latunsaroon
Hausa
Kada ku karkata zuwa ga waɗanda suka yi zălunci har wuta ta shăfe ku. Kuma bă ku
da waɗansu majiɓinta baicin Allah, sa'an nan kuma bă ză a taimake ku ba.
|
Ayah 11:114 الأية
وَأَقِمِ الصَّلَاةَ طَرَفَيِ النَّهَارِ وَزُلَفًا مِّنَ اللَّيْلِ ۚ إِنَّ
الْحَسَنَاتِ يُذْهِبْنَ السَّيِّئَاتِ ۚ ذَٰلِكَ ذِكْرَىٰ لِلذَّاكِرِينَ
Waaqimi assalata tarafayiannahari wazulafan mina allayli inna
alhasanatiyuthhibna assayyi-ati thalika thikraliththakireen
Hausa
Kuma ka tsai da salla a gẽfe guda biyu na yini da wani yanki daga dare. Lalle ne
ayyukan ƙwarai sună kőre mũnănan ayyuka. wancan ne tunătarwa ga măsu tunăwa.
|
Ayah 11:115 الأية
وَاصْبِرْ فَإِنَّ اللهَ لَا يُضِيعُ أَجْرَ الْمُحْسِنِينَ
Wasbir fa-inna Allahala yudeeAAu ajra almuhsineen
Hausa
Kuma ka yi haƙuri. Allah bă Ya tőzartar da lădar măsu kyautatăwa.
|
Ayah 11:116 الأية
فَلَوْلَا كَانَ مِنَ الْقُرُونِ مِن قَبْلِكُمْ أُولُو بَقِيَّةٍ يَنْهَوْنَ عَنِ
الْفَسَادِ فِي الْأَرْضِ إِلَّا قَلِيلًا مِّمَّنْ أَنجَيْنَا مِنْهُمْ ۗ
وَاتَّبَعَ الَّذِينَ ظَلَمُوا مَا أُتْرِفُوا فِيهِ وَكَانُوا مُجْرِمِينَ
Falawla kana mina alquroonimin qablikum oloo baqiyyatin yanhawna AAani alfasadi
feeal-ardi illa qaleelan mimman anjayna minhumwattabaAAa allatheena thalamoo
maotrifoo feehi wakanoo mujrimeen
Hausa
To, don me măsu hankali ba su kasance daga mutănen ƙarnőnin da suke a gabăninku
ba, sună hani daga ɓarna a cikin ƙasa? făce kaɗan daga wanda Muka kuɓutar daga
gare su (sun yi hanin). Kuma waɗanda suka yi zălunci suka bin abin da aka
ni'imtar da su a cikinsa, suka kasance măsu laifi.
|
Ayah 11:117 الأية
وَمَا كَانَ رَبُّكَ لِيُهْلِكَ الْقُرَىٰ بِظُلْمٍ وَأَهْلُهَا مُصْلِحُونَ
Wama kana rabbuka liyuhlikaalqura bithulmin waahluha muslihoon
Hausa
Kuma Ubangijinka bai kasance Yană halakar da alƙaryu sabőda wani zălunci ba,
alhăli mutănensu sună măsu gyărăwa.
|
|