Prev  

12. Surah Yűsuf سورة يوسف

  Next  




1st Ayah  1  الأية ١الأولي
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الر ۚ تِلْكَ آيَاتُ الْكِتَابِ الْمُبِينِ
Alif-lam-ra tilka ayatualkitabi almubeen

Hausa
 
A. L̃. R. Waɗancan ăyoyin Littăfi mai bayyanăwa ne.

Ayah  12:2  الأية
إِنَّا أَنزَلْنَاهُ قُرْآنًا عَرَبِيًّا لَّعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ
Inna anzalnahu qur-ananAAarabiyyan laAAallakum taAAqiloon

Hausa
 
Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi, yană abin karantăwa na Lărabci; tsammăninkũ, kună hankalta.

Ayah  12:3  الأية
نَحْنُ نَقُصُّ عَلَيْكَ أَحْسَنَ الْقَصَصِ بِمَا أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ هَٰذَا الْقُرْآنَ وَإِن كُنتَ مِن قَبْلِهِ لَمِنَ الْغَافِلِينَ
Nahnu naqussu AAalayka ahsanaalqasasi bima awhayna ilayka hathaalqur-ana wa-in kunta min qablihi lamina alghafileen

Hausa
 
Mũ, Mună băyar da lăbări a gare ka, mafi kyăwon lăbări ga abin da Muka yi wahayin wannan Alƙur'ăni zuwa gare ka. Kuma lalle ne kă kasance a gabăninsa, haƙĩƙa,daga gafalallu.

Ayah  12:4  الأية
إِذْ قَالَ يُوسُفُ لِأَبِيهِ يَا أَبَتِ إِنِّي رَأَيْتُ أَحَدَ عَشَرَ كَوْكَبًا وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ رَأَيْتُهُمْ لِي سَاجِدِينَ
Ith qala yoosufu li-abeehi yaabati innee raaytu ahada AAashara kawkaban washshamsawalqamara raaytuhum lee sajideen

Hausa
 
A lőkacin da Yũsufu ya ce wa ubansa, "Yă băba! Lalle ne nĩ, nă ga taurări gőma shă ɗaya, da rănă da wată. Na gan su sună măsu sujada a gare ni."

Ayah  12:5  الأية
قَالَ يَا بُنَيَّ لَا تَقْصُصْ رُؤْيَاكَ عَلَىٰ إِخْوَتِكَ فَيَكِيدُوا لَكَ كَيْدًا ۖ إِنَّ الشَّيْطَانَ لِلْإِنسَانِ عَدُوٌّ مُّبِينٌ
Qala ya bunayya la taqsusru/yaka AAala ikhwatika fayakeedoo laka kaydan innaashshaytana lil-insani AAaduwwun mubeen

Hausa
 
Ya ce: "Ya ƙaramin ɗăna! Kada ka faɗi mafarkinka ga 'yan'uwanka, har su ƙulla maka wani kaidi. Lalle ne Shaidan ga mutum, haƙĩƙa, maƙiyi ne bayyanănne.

Ayah  12:6  الأية
وَكَذَٰلِكَ يَجْتَبِيكَ رَبُّكَ وَيُعَلِّمُكَ مِن تَأْوِيلِ الْأَحَادِيثِ وَيُتِمُّ نِعْمَتَهُ عَلَيْكَ وَعَلَىٰ آلِ يَعْقُوبَ كَمَا أَتَمَّهَا عَلَىٰ أَبَوَيْكَ مِن قَبْلُ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْحَاقَ ۚ إِنَّ رَبَّكَ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Wakathalika yajtabeeka rabbukawayuAAallimuka min ta/weeli al-ahadeethi wayutimmuniAAmatahu AAalayka waAAala ali yaAAqooba kamaatammaha AAala abawayka min qablu ibraheemawa-ishaqa inna rabbaka AAaleemun hakeem

Hausa
 
"Kuma kămar wancan ne, Ubangijinka Yake zăɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar lăbărai, kuma ya cika ni'imőminSa a kanka, kuma a kan gidan Yăƙũba kămar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabăni, Ibrăhĩm da Is'hăƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima."

Ayah  12:7  الأية
لَّقَدْ كَانَ فِي يُوسُفَ وَإِخْوَتِهِ آيَاتٌ لِّلسَّائِلِينَ
Laqad kana fee yoosufa wa-ikhwatihi ayatunlissa-ileen

Hausa
 
Lalle ne, haƙĩƙa, ăyőyi sun kasance ga Yũsufu da 'yan'uwansa dőmin măsu tambaya.

Ayah  12:8  الأية
إِذْ قَالُوا لَيُوسُفُ وَأَخُوهُ أَحَبُّ إِلَىٰ أَبِينَا مِنَّا وَنَحْنُ عُصْبَةٌ إِنَّ أَبَانَا لَفِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Ith qaloo layoosufu waakhoohu ahabbuila abeena minna wanahnu AAusbatuninna abana lafee dalalin mubeen

Hausa
 
A lőkacin da suka ce: lalle ne Yũsufu da ɗan'uwansa ne mafiya sőyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhăli kuwa mũ jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙĩƙa, yană cikin ɓata bayyananniya.

Ayah  12:9  الأية
اقْتُلُوا يُوسُفَ أَوِ اطْرَحُوهُ أَرْضًا يَخْلُ لَكُمْ وَجْهُ أَبِيكُمْ وَتَكُونُوا مِن بَعْدِهِ قَوْمًا صَالِحِينَ
Oqtuloo yoosufa awi itrahoohuardan yakhlu lakum wajhu abeekum watakoonoo min baAAdihiqawman saliheen

Hausa
 
Ku kashe Yũsufu, kő kuwa ku jẽfa shi a wata ƙasa, fuskar ubanku ta wőfinta sabőda ku, kuma ku kasance a băyansa mutăne sălihai.

Ayah  12:10  الأية
قَالَ قَائِلٌ مِّنْهُمْ لَا تَقْتُلُوا يُوسُفَ وَأَلْقُوهُ فِي غَيَابَتِ الْجُبِّ يَلْتَقِطْهُ بَعْضُ السَّيَّارَةِ إِن كُنتُمْ فَاعِلِينَ
Qala qa-ilun minhum lataqtuloo yoosufa waalqoohu fee ghayabati aljubbi yaltaqithubaAAdu assayyarati in kuntum faAAileen

Hausa
 
Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Kada ku kashe Yũsufu. Ku jẽfa shi a cikin duhun rĩjiya, wasu matafiya su tsince shi, idan kun kasance măsu aikatăwa ne."

Ayah  12:11  الأية
قَالُوا يَا أَبَانَا مَا لَكَ لَا تَأْمَنَّا عَلَىٰ يُوسُفَ وَإِنَّا لَهُ لَنَاصِحُونَ
Qaloo ya abana malaka la ta/manna AAala yoosufa wa-innalahu lanasihoon

Hausa
 
Suka ce: "Yă băbanmu! Mẽne ne a gare ka ba ka amince mana ba a kan Yũsufu, alhălikuwa lalle ne mũ, haƙăƙa măsu nashĩha muke a gare shi?"

Ayah  12:12  الأية
أَرْسِلْهُ مَعَنَا غَدًا يَرْتَعْ وَيَلْعَبْ وَإِنَّا لَهُ لَحَافِظُونَ
Arsilhu maAAana ghadan yartaAAwayalAAab wa-inna lahu lahafithoon

Hausa
 
"Ka bar shi tăre da mu a gőbe, ya ji dăɗi, kuma ya yi wăsa. Kuma lalle ne mu, a gare shi, măsu tsaro ne."

Ayah  12:13  الأية
قَالَ إِنِّي لَيَحْزُنُنِي أَن تَذْهَبُوا بِهِ وَأَخَافُ أَن يَأْكُلَهُ الذِّئْبُ وَأَنتُمْ عَنْهُ غَافِلُونَ
Qala innee layahzununee an thathhaboobihi waakhafu an ya/kulahu aththi/buwaantum AAanhu ghafiloon

Hausa
 
Ya ce: "Lalle ne ni, haƙăƙa yană ɓăta mini rai ku tafii da shi, Kuma ină tsőron kerkẽci ya cinye shi, alhăli ku kuwa kună măsu shagala daga gare shi."

Ayah  12:14  الأية
قَالُوا لَئِنْ أَكَلَهُ الذِّئْبُ وَنَحْنُ عُصْبَةٌ إِنَّا إِذًا لَّخَاسِرُونَ
Qaloo la-in akalahu aththi/buwanahnu AAusbatun inna ithan lakhasiroon

Hausa
 
Suka ce: "Haƙĩƙa idan kerkẽci ya cinye shi, alhăli kuwa mună dangin jũna, lalle ne mũ, a sa'an nan, hakĩka, mun zama măsu hasăra."

Ayah  12:15  الأية
فَلَمَّا ذَهَبُوا بِهِ وَأَجْمَعُوا أَن يَجْعَلُوهُ فِي غَيَابَتِ الْجُبِّ ۚ وَأَوْحَيْنَا إِلَيْهِ لَتُنَبِّئَنَّهُم بِأَمْرِهِمْ هَٰذَا وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
Falamma thahaboo bihiwaajmaAAoo an yajAAaloohu fee ghayabati aljubbi waawhaynailayhi latunabi-annahum bi-amrihim hatha wahum layashAAuroon

Hausa
 
To, a lőkacin da suka tafi da shi, kuma suka yi niyyar su sanya shi a cikin duhun rĩjiya, Muka yi wahayi zuwa gare shi, "Lalle ne, kană bă su lăbari game da wannan al'amari năsu, kuma sũ ba su sani ba."

Ayah  12:16  الأية
وَجَاءُوا أَبَاهُمْ عِشَاءً يَبْكُونَ
Wajaoo abahum AAishaanyabkoon

Hausa
 
Kuma suka je wa ubansu da dare sună kũka.

Ayah  12:17  الأية
قَالُوا يَا أَبَانَا إِنَّا ذَهَبْنَا نَسْتَبِقُ وَتَرَكْنَا يُوسُفَ عِندَ مَتَاعِنَا فَأَكَلَهُ الذِّئْبُ ۖ وَمَا أَنتَ بِمُؤْمِنٍ لَّنَا وَلَوْ كُنَّا صَادِقِينَ
Qaloo ya abanainna thahabna nastabiqu wataraknayoosufa AAinda mataAAina faakalahu aththi/buwama anta bimu/minin lana walaw kunna sadiqeen

Hausa
 
Suka ce: "Yă băbanmu! Lalle ne, mun tafi mună tsẽre, kuma muka bar Yusufu a wurin kăyanmu, sai kerkẽci ya cinye shi, kuma kai, bă mai amincẽwa da mu ba ne, kuma kő dă mun kasance măsu gaskiya!"_

Ayah  12:18  الأية
وَجَاءُوا عَلَىٰ قَمِيصِهِ بِدَمٍ كَذِبٍ ۚ قَالَ بَلْ سَوَّلَتْ لَكُمْ أَنفُسُكُمْ أَمْرًا ۖ فَصَبْرٌ جَمِيلٌ ۖ وَاللهُ الْمُسْتَعَانُ عَلَىٰ مَا تَصِفُونَ
Wajaoo AAala qameesihibidamin kathibin qala bal sawwalat lakum anfusukumamran fasabrun jameelun wallahu almustaAAanuAAala ma tasifoon

Hausa
 
Kuma suka je, a jikin rigarsa akwai wani jinin ƙarya. Ya ce: "Ă'a, zukatanku suka ƙawăta muku wani al'amari. Sai haƙuri mai kyau! Kuma Allah ne wanda ake nẽman taimako (a gunSa) a kan abin da kuke siffantăwa."

Ayah  12:19  الأية
وَجَاءَتْ سَيَّارَةٌ فَأَرْسَلُوا وَارِدَهُمْ فَأَدْلَىٰ دَلْوَهُ ۖ قَالَ يَا بُشْرَىٰ هَٰذَا غُلَامٌ ۚ وَأَسَرُّوهُ بِضَاعَةً ۚ وَاللهُ عَلِيمٌ بِمَا يَعْمَلُونَ
Wajaat sayyaratun faarsaloo waridahumfaadla dalwahu qala ya bushra hathaghulamun waasarroohu bidaAAatan wallahuAAaleemun bima yaAAmaloon

Hausa
 
Kuma wani ăyari ya je, sai suka aika mai nẽman musu rũwa, sai ya zura gugansa, ya ce: "Yă bushărata! Wannan yăro ne." Kuma suka ɓőye shi yană abin sayarwa. Kuma Allah ne Masani ga abin da suke aikatăwa.

Ayah  12:20  الأية
وَشَرَوْهُ بِثَمَنٍ بَخْسٍ دَرَاهِمَ مَعْدُودَةٍ وَكَانُوا فِيهِ مِنَ الزَّاهِدِينَ
Washarawhu bithamanin bakhsin darahimamaAAdoodatin wakanoo feehi mina azzahideen

Hausa
 
Kuma suka sayar da shi da 'yan kuɗi kaɗan, dirhamőmi ƙidăyayyu, Kuma sun kasance, a wurinsa, daga măsu isuwa da abu kaɗan.

Ayah  12:21  الأية
وَقَالَ الَّذِي اشْتَرَاهُ مِن مِّصْرَ لِامْرَأَتِهِ أَكْرِمِي مَثْوَاهُ عَسَىٰ أَن يَنفَعَنَا أَوْ نَتَّخِذَهُ وَلَدًا ۚ وَكَذَٰلِكَ مَكَّنَّا لِيُوسُفَ فِي الْأَرْضِ وَلِنُعَلِّمَهُ مِن تَأْوِيلِ الْأَحَادِيثِ ۚ وَاللهُ غَالِبٌ عَلَىٰ أَمْرِهِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
Waqala allathee ishtarahumin misra limraatihi akrimee mathwahu AAasaan yanfaAAana aw nattakhithahu waladan wakathalikamakkanna liyoosufa fee al-ardi walinuAAallimahu minta/weeli al-ahadeethi wallahu ghalibunAAala amrihi walakinna akthara annasila yaAAlamoon

Hausa
 
Kuma wanda ya saye shi daga Masar ya ce wa mătarsa, "Ki girmama mazauninsa, akwai tsammănin ya amfăne mu, kő kuwa mu riƙe shi ɗă."Kuma kamar wancan ne Muka tabbatar ga Yũsufu,a cikin ƙasa kuma dőmin Mu sanar da shi daia fassarar lũbũru, kuma Allah ne Marinjăyi a kan al'amarinSa, kuma amma mafi yawan mutăne ba su sani ba."

Ayah  12:22  الأية
وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُ آتَيْنَاهُ حُكْمًا وَعِلْمًا ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ
Walamma balagha ashuddahu ataynahuhukman waAAilman wakathalika najzee almuhsineen

Hausa
 
Kuma a lőkacin da ya isa mafi ƙarfinsa, Muka bă shi hukunci da ilmi. Kuma kamar wancan ne Muke săka wa măsu kyautatăwa.

Ayah  12:23  الأية
وَرَاوَدَتْهُ الَّتِي هُوَ فِي بَيْتِهَا عَن نَّفْسِهِ وَغَلَّقَتِ الْأَبْوَابَ وَقَالَتْ هَيْتَ لَكَ ۚ قَالَ مَعَاذَ اللهِ ۖ إِنَّهُ رَبِّي أَحْسَنَ مَثْوَايَ ۖ إِنَّهُ لَا يُفْلِحُ الظَّالِمُونَ
Warawadat-hu allatee huwa fee baytihaAAan nafsihi waghallaqati al-abwaba waqalat haytalaka qala maAAatha Allahi innahu rabbee ahsanamathwaya innahu la yuflihu aththalimoon

Hausa
 
Kuma wadda yake a cikin ɗăkinta, ta nẽme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙőfőfi, kuma ta ce, "Yă rage a gare ka!" ya ce: "Ina neman tsarin Allah! Lalle shĩne Ubangijina. Yă kyautata mazaunina. Lalle ne shĩ, măsu zălunci ba su cin nasara!"

Ayah  12:24  الأية
وَلَقَدْ هَمَّتْ بِهِ ۖ وَهَمَّ بِهَا لَوْلَا أَن رَّأَىٰ بُرْهَانَ رَبِّهِ ۚ كَذَٰلِكَ لِنَصْرِفَ عَنْهُ السُّوءَ وَالْفَحْشَاءَ ۚ إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُخْلَصِينَ
Walaqad hammat bihi wahamma biha lawlaan raa burhana rabbihi kathalika linasrifaAAanhu assoo-a walfahshaa innahumin AAibadina almukhlaseen

Hausa
 
Kuma lalle ne, tă himmantu da shi. Kuma yă himmantu da ita in bă dőmin ya ga dalĩlin Ubangijinsa ba. Kămar haka dai, dőmin Mu karkatar da mummũnan aiki da alfăsha daga gare shi. Lalle ne shi, daga băyinMu zaɓaɓɓu yake.

Ayah  12:25  الأية
وَاسْتَبَقَا الْبَابَ وَقَدَّتْ قَمِيصَهُ مِن دُبُرٍ وَأَلْفَيَا سَيِّدَهَا لَدَى الْبَابِ ۚ قَالَتْ مَا جَزَاءُ مَنْ أَرَادَ بِأَهْلِكَ سُوءًا إِلَّا أَن يُسْجَنَ أَوْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Wastabaqa albabawaqaddat qameesahu min duburin waalfaya sayyidahalada albabi qalat ma jazao manarada bi-ahlika soo-an illa an yusjana aw AAathabunaleem

Hausa
 
Kuma suka yi tsẽre zuwa ga ƙőfa. Sai ta tsăge rigarsa daga băya, kuma suka iske mijinta a wurin ƙőfar. Ta ce: "Mẽnene sakamakon wanda ya yi nufin cũta game da iyălinka? Făce a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azăba mai raɗaɗi."

Ayah  12:26  الأية
قَالَ هِيَ رَاوَدَتْنِي عَن نَّفْسِي ۚ وَشَهِدَ شَاهِدٌ مِّنْ أَهْلِهَا إِن كَانَ قَمِيصُهُ قُدَّ مِن قُبُلٍ فَصَدَقَتْ وَهُوَ مِنَ الْكَاذِبِينَ
Qala hiya rawadatnee AAannafsee washahida shahidun min ahliha in kanaqameesuhu qudda min qubulin fasadaqat wahuwa minaalkathibeen

Hausa
 
Ya ce: "Ita ce ta nẽme ni a kaina."Kuma wani mai shaida daga mutănenta ya băyar da shaida: "Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, tă yi gaskiya, kuma shĩ ne daga maƙaryata."

Ayah  12:27  الأية
وَإِن كَانَ قَمِيصُهُ قُدَّ مِن دُبُرٍ فَكَذَبَتْ وَهُوَ مِنَ الصَّادِقِينَ
Wa-in kana qameesuhu qudda minduburin fakathabat wahuwa mina assadiqeen

Hausa
 
"Kuma idan rigarsa ta kasance an tsăge ta daga băya, to, tă yi ƙarya, kuma shĩ ne daga măsu gaskiya."

Ayah  12:28  الأية
فَلَمَّا رَأَىٰ قَمِيصَهُ قُدَّ مِن دُبُرٍ قَالَ إِنَّهُ مِن كَيْدِكُنَّ ۖ إِنَّ كَيْدَكُنَّ عَظِيمٌ
Falamma raa qameesahuqudda min duburin qala innahu min kaydikunna innakaydakunna AAatheem

Hausa
 
Sa'an nan a lőkacin da ya ga rĩgarsa an tsăge ta daga băya, ya ce: "Lalle ne shi, daga kaidinku ne, mata! Lalle ne kaidinku mai girma ne!"

Ayah  12:29  الأية
يُوسُفُ أَعْرِضْ عَنْ هَٰذَا ۚ وَاسْتَغْفِرِي لِذَنبِكِ ۖ إِنَّكِ كُنتِ مِنَ الْخَاطِئِينَ
Yoosufu aAArid AAan hatha wastaghfireelithanbiki innaki kunti mina alkhati-een

Hausa
 
"Yusufu! Ka kau da kai daga wannan. Kuma ki nẽmi găfara dőmin laifinki. Lalle ne ke, kin kasance daga măsu kuskure."

Ayah  12:30  الأية
وَقَالَ نِسْوَةٌ فِي الْمَدِينَةِ امْرَأَتُ الْعَزِيزِ تُرَاوِدُ فَتَاهَا عَن نَّفْسِهِ ۖ قَدْ شَغَفَهَا حُبًّا ۖ إِنَّا لَنَرَاهَا فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Waqala niswatun fee almadeenatiimraatu alAAazeezi turawidu fataha AAannafsihi qad shaghafaha hubban inna lanarahafee dalalin mubeen

Hausa
 
Kuma waɗansu mătă a cikin Birnin suka ce: "Matar Azĩz tană nẽman hădiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yă rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Mună ganin taa cikin ɓata bayyanănna."

Ayah  12:31  الأية
فَلَمَّا سَمِعَتْ بِمَكْرِهِنَّ أَرْسَلَتْ إِلَيْهِنَّ وَأَعْتَدَتْ لَهُنَّ مُتَّكَأً وَآتَتْ كُلَّ وَاحِدَةٍ مِّنْهُنَّ سِكِّينًا وَقَالَتِ اخْرُجْ عَلَيْهِنَّ ۖ فَلَمَّا رَأَيْنَهُ أَكْبَرْنَهُ وَقَطَّعْنَ أَيْدِيَهُنَّ وَقُلْنَ حَاشَ لِلَّهِ مَا هَٰذَا بَشَرًا إِنْ هَٰذَا إِلَّا مَلَكٌ كَرِيمٌ
Falamma samiAAat bimakrihinna arsalatilayhinna waaAAtadat lahunna muttakaan waatat kulla wahidatinminhunna sikkeenan waqalati okhruj AAalayhinna falammaraaynahu akbarnahu waqattaAAna aydiyahunna waqulna hashalillahi ma hatha basharan in hathailla malakun kareem

Hausa
 
Sa'an nan a lőkacin da ta ji lăbări game da măkircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dőgara wajen cinsa, kuma ta bai wa kőwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: "Ka fito a kansu." To, a lőkacin da, suka gan shi, suka girmamă shi, kuma suka yanyanke hannăyensu, kuma suka ce: "Tsarki yană ga Allah! Wannan bă mutum ba ne! Wannan bai zama ba făce Mală'ika ne mai daraja!"

Ayah  12:32  الأية
قَالَتْ فَذَٰلِكُنَّ الَّذِي لُمْتُنَّنِي فِيهِ ۖ وَلَقَدْ رَاوَدتُّهُ عَن نَّفْسِهِ فَاسْتَعْصَمَ ۖ وَلَئِن لَّمْ يَفْعَلْ مَا آمُرُهُ لَيُسْجَنَنَّ وَلَيَكُونًا مِّنَ الصَّاغِرِينَ
Qalat fathalikunna allatheelumtunnanee feehi walaqad rawadtuhu AAan nafsihi fastAAsamawala-in lam yafAAal ma amuruhu layusjanannawalayakoonan mina assaghireen

Hausa
 
Ta ce: "To wannan ne fa wanda kuka, zarge ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙẽƙa na nẽme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma nĩ ină rantsuwa, idan bai aikata abin da nake umurnin sa ba, haƙẽƙa ană ɗaure shi. Haƙĩƙa, yană kasan, cewa daga ƙasƙantattu."

Ayah  12:33  الأية
قَالَ رَبِّ السِّجْنُ أَحَبُّ إِلَيَّ مِمَّا يَدْعُونَنِي إِلَيْهِ ۖ وَإِلَّا تَصْرِفْ عَنِّي كَيْدَهُنَّ أَصْبُ إِلَيْهِنَّ وَأَكُن مِّنَ الْجَاهِلِينَ
Qala rabbi assijnu ahabbuilayya mimma yadAAoonanee ilayhi wa-illa tasrifAAannee kaydahunna asbu ilayhinna waakun mina aljahileen

Hausa
 
Ya ce: "Yă Ubangijina! Kurkuku ne mafi sőyuwa a gare ni daga abin da suke kiră na zuwa gare shi. Kuma idan ba Ka karkatar da kaidinsu daga gare ni ba, zan karkata zuwa gare su, kuma in kasance daga jăhilai."

Ayah  12:34  الأية
فَاسْتَجَابَ لَهُ رَبُّهُ فَصَرَفَ عَنْهُ كَيْدَهُنَّ ۚ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Fastajaba lahu rabbuhu fasarafaAAanhu kaydahunna innahu huwa assameeAAu alAAaleem

Hausa
 
Sai Ubangijinsa Ya karɓa masa sabőda haka Ya karkatar da kaidinsu daga gare shi. Lalle Shĩ ne Mai jĩ, Masani.

Ayah  12:35  الأية
ثُمَّ بَدَا لَهُم مِّن بَعْدِ مَا رَأَوُا الْآيَاتِ لَيَسْجُنُنَّهُ حَتَّىٰ حِينٍ
Thumma bada lahum min baAAdi maraawoo al-ayati layasjununnahu hatta heen

Hausa
 
Sa'an nan kuma ya bayyana a gare su a băyan sun ga alămőmin, lalle ne dai su ɗaure shi har zuwa wani lőkaci.

Ayah  12:36  الأية
وَدَخَلَ مَعَهُ السِّجْنَ فَتَيَانِ ۖ قَالَ أَحَدُهُمَا إِنِّي أَرَانِي أَعْصِرُ خَمْرًا ۖ وَقَالَ الْآخَرُ إِنِّي أَرَانِي أَحْمِلُ فَوْقَ رَأْسِي خُبْزًا تَأْكُلُ الطَّيْرُ مِنْهُ ۖ نَبِّئْنَا بِتَأْوِيلِهِ ۖ إِنَّا نَرَاكَ مِنَ الْمُحْسِنِينَ
Wadakhala maAAahu assijna fatayaniqala ahaduhuma innee aranee aAAsirukhamran waqala al-akharu innee aranee ahmilufawqa ra/see khubzan ta/kulu attayru minhu nabbi/nabita/weelihi inna naraka mina almuhsineen

Hausa
 
Kuma waɗansu samări biyu suka shiga kurkuku tăre da shi. ¦ayansu ya ce: "Lalle ne nĩ, nă yi mafarkin gă ni ină mătsar giya." Kuma ɗayan ya ce: "Lalle ne nĩ, nă yi Mafarkin gă ni ină ɗauke da waina a bisa kaina, tsuntsăye sună ci daga gare ta. Ka bă mu lăbări game da fassararsu. Lalle ne mũ, Mună ganin ka daga măsu kyautatăwa."

Ayah  12:37  الأية
قَالَ لَا يَأْتِيكُمَا طَعَامٌ تُرْزَقَانِهِ إِلَّا نَبَّأْتُكُمَا بِتَأْوِيلِهِ قَبْلَ أَن يَأْتِيَكُمَا ۚ ذَٰلِكُمَا مِمَّا عَلَّمَنِي رَبِّي ۚ إِنِّي تَرَكْتُ مِلَّةَ قَوْمٍ لَّا يُؤْمِنُونَ بِاللهِ وَهُم بِالْآخِرَةِ هُمْ كَافِرُونَ
Qala la ya/teekuma taAAamunturzaqanihi illa nabba/tukuma bita/weelihiqabla an ya/tiyakuma thalikuma mimmaAAallamanee rabbee innee taraktu millata qawmin layu/minoona billahi wahum bil-akhiratihum kafiroon

Hausa
 
Ya ce: "Wani abinci bă zai zo muku ba wanda ake azurtă ku da shi făce nă bă ku lăbărin fassararsa , kăfin ya zo muku. Wannan kuwa yană daga abin da Ubangijĩna Ya sanar da ni. Lalle ne nĩ nă bar addinin mutăne waɗanda ba su yi ĩmăni da Allah ba, kuma game da lăhira, sũ kăfirai ne."

Ayah  12:38  الأية
وَاتَّبَعْتُ مِلَّةَ آبَائِي إِبْرَاهِيمَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ ۚ مَا كَانَ لَنَا أَن نُّشْرِكَ بِاللهِ مِن شَيْءٍ ۚ ذَٰلِكَ مِن فَضْلِ اللهِ عَلَيْنَا وَعَلَى النَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَشْكُرُونَ
WattabaAAtu millata aba-eeibraheema wa-ishaqa wayaAAqooba ma kanalana an nushrika billahi min shay-in thalikamin fadli Allahi AAalayna waAAala annasiwalakinna akthara annasi layashkuroon

Hausa
 
"Kuma na bi addinin iyayẽna, Ibrăhĩm da Is'hăka da Yăƙũba. Bă ya yiwuwa a gare mu mu yi shirka da Allah da kőme. Wannan yana daga falalar Allah a kanmu da mutăne, amma mafi yawan mutăne bă su gődewa."

Ayah  12:39  الأية
يَا صَاحِبَيِ السِّجْنِ أَأَرْبَابٌ مُّتَفَرِّقُونَ خَيْرٌ أَمِ اللهُ الْوَاحِدُ الْقَهَّارُ
Ya sahibayi assijniaarbabun mutafarriqoona khayrun ami Allahu alwahidualqahhar

Hausa
 
"Yă abőkaina biyu na kurkuku! Shin iyăyen giji dabam-dabam ne mafiya alhẽri kő kuwa Allah Makaɗaici Mai tanƙwasăwa?"

Ayah  12:40  الأية
مَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِهِ إِلَّا أَسْمَاءً سَمَّيْتُمُوهَا أَنتُمْ وَآبَاؤُكُم مَّا أَنزَلَ اللهُ بِهَا مِن سُلْطَانٍ ۚ إِنِ الْحُكْمُ إِلَّا لِلَّهِ ۚ أَمَرَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ ۚ ذَٰلِكَ الدِّينُ الْقَيِّمُ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
Ma taAAbudoona min doonihi illaasmaan sammaytumooha antum waabaokumma anzala Allahu biha min sultaninini alhukmu illa lillahi amara allataAAbudoo illa iyyahu thalika addeenualqayyimu walakinna akthara annasi layaAAlamoon

Hausa
 
"Ba ku bauta wa kőme, baicinSa, făce waɗansu sũnăye waɗanda kuka ambace su, kũ da ubanninku.Allah bai saukar da wani dalĩli ba game da su. Băbu hukunci făce na Allah. Ya yi umurnin kada ku bauta wa kőwa făce Shi. Wancan ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutăne ba su sani ba."

Ayah  12:41  الأية
يَا صَاحِبَيِ السِّجْنِ أَمَّا أَحَدُكُمَا فَيَسْقِي رَبَّهُ خَمْرًا ۖ وَأَمَّا الْآخَرُ فَيُصْلَبُ فَتَأْكُلُ الطَّيْرُ مِن رَّأْسِهِ ۚ قُضِيَ الْأَمْرُ الَّذِي فِيهِ تَسْتَفْتِيَانِ
Ya sahibayi assijniamma ahadukuma fayasqee rabbahu khamranwaamma al-akharu fayuslabu fata/kulu attayrumin ra/sihi qudiya al-amru allathee feehi tastaftiyan

Hausa
 
"Yă abőkaina biyu, na kurkuku! Amma ɗayanku, to, zai shăyar da uban gidansa giya, kuma gudan, to, ză a tsĩrẽ shi, sa'an nan tsuntsăye su ci daga kansa. An hukunta al'amarin, wanda a cikinsa kuke yin fatawa."

Ayah  12:42  الأية
وَقَالَ لِلَّذِي ظَنَّ أَنَّهُ نَاجٍ مِّنْهُمَا اذْكُرْنِي عِندَ رَبِّكَ فَأَنسَاهُ الشَّيْطَانُ ذِكْرَ رَبِّهِ فَلَبِثَ فِي السِّجْنِ بِضْعَ سِنِينَ
Waqala lillathee thannaannahu najin minhuma othkurnee AAindarabbika faansahu ashshaytanu thikrarabbihi falabitha fee assijni bidAAa sineen

Hausa
 
Kuma ya ce da wanda ya tabbatar da cẽwa shi mai kuɓuta ne daga gare su, "Ka ambacẽ ni a wurin uban gidanka." Sai Shaiɗan ya mantar da shi tunăwar Ubangijinsa, sabőda haka ya zauna a cikin kurkuku 'yan shekaru.

Ayah  12:43  الأية
وَقَالَ الْمَلِكُ إِنِّي أَرَىٰ سَبْعَ بَقَرَاتٍ سِمَانٍ يَأْكُلُهُنَّ سَبْعٌ عِجَافٌ وَسَبْعَ سُنبُلَاتٍ خُضْرٍ وَأُخَرَ يَابِسَاتٍ ۖ يَا أَيُّهَا الْمَلَأُ أَفْتُونِي فِي رُؤْيَايَ إِن كُنتُمْ لِلرُّؤْيَا تَعْبُرُونَ
Waqala almaliku innee arasabAAa baqaratin simanin ya/kuluhunna sabAAun AAijafunwasabAAa sunbulatin khudrin waokhara yabisatinya ayyuha almalao aftoonee fee ru/yaya inkuntum lirru/ya taAAburoon

Hausa
 
Kuma sarki ya ce: "Lalle ne, nă yi mafarki; nă ga shănu bakwai măsu ƙiba, waɗansu bakwai rămammu, sună cin su, da zangarku bakwai kőre-kőre da waɗansu ƙeƙasassu. Yă kũ jama'a! Ku yi mini fatawa a cikin mafarkĩna, idan kun kasance ga mafarki kună fassarawa."

Ayah  12:44  الأية
قَالُوا أَضْغَاثُ أَحْلَامٍ ۖ وَمَا نَحْنُ بِتَأْوِيلِ الْأَحْلَامِ بِعَالِمِينَ
Qaloo adghathu ahlaminwama nahnu bita/weeli al-ahlami biAAalimeen

Hausa
 
Suka ce: "Yăye-yăyen mafarki ne, kuma ba mu zamo masana ga fassarar yăye-yăyen mafarki ba."

Ayah  12:45  الأية
وَقَالَ الَّذِي نَجَا مِنْهُمَا وَادَّكَرَ بَعْدَ أُمَّةٍ أَنَا أُنَبِّئُكُم بِتَأْوِيلِهِ فَأَرْسِلُونِ
Waqala allathee najaminhuma waddakara baAAda ommatin anaonabbi-okum bita/weelihi faarsiloon

Hausa
 
Kuma wannan da ya kuɓuta daga cikinsu ya ce: a băyan yă yi tunăni a lőkaci mai tsawo, "Nĩ, ină bă ku lăbări game da fassararsa. Sai ku aike ni."

Ayah  12:46  الأية
يُوسُفُ أَيُّهَا الصِّدِّيقُ أَفْتِنَا فِي سَبْعِ بَقَرَاتٍ سِمَانٍ يَأْكُلُهُنَّ سَبْعٌ عِجَافٌ وَسَبْعِ سُنبُلَاتٍ خُضْرٍ وَأُخَرَ يَابِسَاتٍ لَّعَلِّي أَرْجِعُ إِلَى النَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَعْلَمُونَ
Yoosufu ayyuha assiddeequaftina fee sabAAi baqaratin simaninya/kuluhunna sabAAun AAijafun wasabAAi sunbulatinkhudrin waokhara yabisatin laAAallee arjiAAuila annasi laAAallahum yaAAlamoon

Hausa
 
"Yă Yũsufu! Yă kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shănu bakwai măsu ƙiba, waɗansu bakwai rămammu sună cin su, da zangarku bakwai kőrăye da waɗansu ƙẽƙasassu, tsammănĩna in kőma ga mutăne, tsammăninsu ză su sani."

Ayah  12:47  الأية
قَالَ تَزْرَعُونَ سَبْعَ سِنِينَ دَأَبًا فَمَا حَصَدتُّمْ فَذَرُوهُ فِي سُنبُلِهِ إِلَّا قَلِيلًا مِّمَّا تَأْكُلُونَ
Qala tazraAAoona sabAAa sineenadaaban fama hasadtum fatharoohu feesunbulihi illa qaleelan mimma ta/kuloon

Hausa
 
Ya ce: "Kună shũka, shẽkara bakwai tutur, sa'an nan abin da kuka girbe, sai ku bar shi, a cikin zanganniyarsa, sai kaɗan daga abin da kuke ci."

Ayah  12:48  الأية
ثُمَّ يَأْتِي مِن بَعْدِ ذَٰلِكَ سَبْعٌ شِدَادٌ يَأْكُلْنَ مَا قَدَّمْتُمْ لَهُنَّ إِلَّا قَلِيلًا مِّمَّا تُحْصِنُونَ
Thumma ya/tee min baAAdi thalikasabAAun shidadun ya/kulna ma qaddamtum lahunna illaqaleelan mimma tuhsinoon

Hausa
 
"Sa'an nan kuma waɗansu bakwai măsu tsanani su zo daga hăyan wancan, su cinye abin da kuka gabătar dőminsu, făce kaɗan daga abin da kuke ădanăwa."

Ayah  12:49  الأية
ثُمَّ يَأْتِي مِن بَعْدِ ذَٰلِكَ عَامٌ فِيهِ يُغَاثُ النَّاسُ وَفِيهِ يَعْصِرُونَ
Thumma ya/tee min baAAdi thalika AAamunfeehi yughathu annasu wafeehi yaAAsiroon

Hausa
 
"Sa'an nan kuma wata shẽkara ta zo daga băyan wancan, a cikinta ake yi wa mutăne ruwa mai albarka, kuma a cikinta suke mătsar abin sha."

Ayah  12:50  الأية
وَقَالَ الْمَلِكُ ائْتُونِي بِهِ ۖ فَلَمَّا جَاءَهُ الرَّسُولُ قَالَ ارْجِعْ إِلَىٰ رَبِّكَ فَاسْأَلْهُ مَا بَالُ النِّسْوَةِ اللَّاتِي قَطَّعْنَ أَيْدِيَهُنَّ ۚ إِنَّ رَبِّي بِكَيْدِهِنَّ عَلِيمٌ
Waqala almaliku i/toonee bihi falammajaahu arrasoolu qala irjiAA ilarabbika fas-alhu ma balu anniswatiallatee qattaAAna aydiyahunna inna rabbeebikaydihinna AAaleem

Hausa
 
Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi." To, a lőkacin da manzo ya je masa (Yũsufu), ya ce: "Ka kőma zuwa ga uban gidanka, sa' an nan ka tambaye shi; Mẽnene hălin mătăyen nan waɗanda suka yanyanke hannăyensu? Lalle ne Ubangijĩna ne Masani game da kaidinsu."

Ayah  12:51  الأية
قَالَ مَا خَطْبُكُنَّ إِذْ رَاوَدتُّنَّ يُوسُفَ عَن نَّفْسِهِ ۚ قُلْنَ حَاشَ لِلَّهِ مَا عَلِمْنَا عَلَيْهِ مِن سُوءٍ ۚ قَالَتِ امْرَأَتُ الْعَزِيزِ الْآنَ حَصْحَصَ الْحَقُّ أَنَا رَاوَدتُّهُ عَن نَّفْسِهِ وَإِنَّهُ لَمِنَ الصَّادِقِينَ
Qala ma khatbukunna ithrawadtunna yoosufa AAan nafsihi qulna hasha lillahima AAalimna AAalayhi min soo-in qalatiimraatu alAAazeezi al-ana hashasa alhaqquana rawadtuhu AAan nafsihi wa-innahu lamina assadiqeen

Hausa
 
Ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinku, a lőkacin da kaka nẽmi Yũsufu daga kansa?" Suka ce: "Tsarki ga Allah yake! Ba mu san wani mummũnan aiki a kansaba." Mătar Azĩz ta ce: "Yanzu fagaskiya ta bayyana. Nĩ ce nă nẽme shi daga kansa. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, yană daga măsu gaskiya.

Ayah  12:52  الأية
ذَٰلِكَ لِيَعْلَمَ أَنِّي لَمْ أَخُنْهُ بِالْغَيْبِ وَأَنَّ اللهَ لَا يَهْدِي كَيْدَ الْخَائِنِينَ
Thalika liyaAAlama annee lam akhunhubilghaybi waanna Allaha la yahdee kaydaalkha-ineen

Hausa
 
"Wancan ne, dőmin ya san cẽwa lalle ne ni ban yaudareshi ba a ɓőye, kuma lalle Allah bă Ya shiryar da kaidin mayaudara."

Ayah  12:53  الأية
وَمَا أُبَرِّئُ نَفْسِي ۚ إِنَّ النَّفْسَ لَأَمَّارَةٌ بِالسُّوءِ إِلَّا مَا رَحِمَ رَبِّي ۚ إِنَّ رَبِّي غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Wama obarri-o nafsee inna annafsalaammaratun bissoo-i illa ma rahimarabbee inna rabbee ghafoorun raheem

Hausa
 
"Kuma bă ni kuɓutar da kaina. Lalle ne rai, haƙĩƙa, mai yawan umurni ne da mummũnan aiki, făce abin da Ubangjina Ya yi na; rahama. Lalle Ubangjina Mai găfara ne, Mai jin ƙai."

Ayah  12:54  الأية
وَقَالَ الْمَلِكُ ائْتُونِي بِهِ أَسْتَخْلِصْهُ لِنَفْسِي ۖ فَلَمَّا كَلَّمَهُ قَالَ إِنَّكَ الْيَوْمَ لَدَيْنَا مَكِينٌ أَمِينٌ
Waqala almaliku i/toonee bihiastakhlishu linafsee falamma kallamahu qalainnaka alyawma ladayna makeenun ameen

Hausa
 
Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi in kẽɓe shi ga kaina." To, a lőkacin da Yũsufu ya yi masa magana sai ya ce: "Lalle ne kai a yau, a gunmu, mai daraja ne, amintacce."

Ayah  12:55  الأية
قَالَ اجْعَلْنِي عَلَىٰ خَزَائِنِ الْأَرْضِ ۖ إِنِّي حَفِيظٌ عَلِيمٌ
Qala ijAAalnee AAala khaza-inial-ardi innee hafeethun AAaleem

Hausa
 
Ya ce: "Ka sanya ni a kan taskőkin ƙasa. Lalle ne nĩ, mai tsarẽwa ne, kuma masani."

Ayah  12:56  الأية
وَكَذَٰلِكَ مَكَّنَّا لِيُوسُفَ فِي الْأَرْضِ يَتَبَوَّأُ مِنْهَا حَيْثُ يَشَاءُ ۚ نُصِيبُ بِرَحْمَتِنَا مَن نَّشَاءُ ۖ وَلَا نُضِيعُ أَجْرَ الْمُحْسِنِينَ
Wakathalika makanna liyoosufafee al-ardi yatabawwao minha haythu yashaonuseebu birahmatina man nashao walanudeeAAu ajra almuhsineen

Hausa
 
Kuma kamar wancan ne Muka băyar da ĩko ga Yũsufu a cikin ƙasa yană sauka a inda duk yake so. Mună sămun wanda Muke so da rahamar Mu, kuma bă Mu tőzartar da lădar măsu kyautatawa.

Ayah  12:57  الأية
وَلَأَجْرُ الْآخِرَةِ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ آمَنُوا وَكَانُوا يَتَّقُونَ
Walaajru al-akhirati khayrun lillatheenaamanoo wakanoo yattaqoon

Hausa
 
Kuma lalle lădar Lăhira ce mafi alhẽri ga waɗandasuka yi ĩmăni, kuma suka kasance măsu taƙawa.

Ayah  12:58  الأية
وَجَاءَ إِخْوَةُ يُوسُفَ فَدَخَلُوا عَلَيْهِ فَعَرَفَهُمْ وَهُمْ لَهُ مُنكِرُونَ
Wajaa ikhwatu yoosufa fadakhalooAAalayhi faAAarafahum wahum lahu munkiroon

Hausa
 
Kuma 'yan'uwan Yũsufu suka jẽ, sa'an nan suka shiga a gare shi, sai ya găne su, alhăli kuwa su, sună măsu musunsa.

Ayah  12:59  الأية
وَلَمَّا جَهَّزَهُم بِجَهَازِهِمْ قَالَ ائْتُونِي بِأَخٍ لَّكُم مِّنْ أَبِيكُمْ ۚ أَلَا تَرَوْنَ أَنِّي أُوفِي الْكَيْلَ وَأَنَا خَيْرُ الْمُنزِلِينَ
Walamma jahhazahum bijahazihimqala i/toonee bi-akhin lakum min abeekum alatarawna annee oofee alkayla waana khayru almunzileen

Hausa
 
Kuma a lőkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, ya ce: "Ku zo mini da wani ɗan'uwa năku daga ubanku. Ba ku gani ba cẽwa lalle ne nĩ, ină cika ma'auni, kuma nĩ ne mafi alhẽrin măsu saukarwa?"

Ayah  12:60  الأية
فَإِن لَّمْ تَأْتُونِي بِهِ فَلَا كَيْلَ لَكُمْ عِندِي وَلَا تَقْرَبُونِ
Fa-in lam ta/toonee bihi fala kaylalakum AAindee wala taqraboon

Hausa
 
"Sa'an nan idan ba ku zo mini da shĩ ba, to, băbu awoa gare ku a wurĩna, kuma kada ku,kasance ni."

Ayah  12:61  الأية
قَالُوا سَنُرَاوِدُ عَنْهُ أَبَاهُ وَإِنَّا لَفَاعِلُونَ
Qaloo sanurawidu AAanhu abahuwa-inna lafaAAiloon

Hausa
 
Suka ce: "Ză mu nẽme shi daga ubansa. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, măsu aikatăwa ne."

Ayah  12:62  الأية
وَقَالَ لِفِتْيَانِهِ اجْعَلُوا بِضَاعَتَهُمْ فِي رِحَالِهِمْ لَعَلَّهُمْ يَعْرِفُونَهَا إِذَا انقَلَبُوا إِلَىٰ أَهْلِهِمْ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ
Waqala lifityanihi ijAAaloo bidaAAatahumfee rihalihim laAAallahum yaAArifoonaha ithainqalaboo ila ahlihim laAAallahum yarjiAAoon

Hausa
 
Kuma ya ce wa yaransa, "Ku sanya hajjarsu a cikin kăyansu, tsammăninsu sună găne ta idan sun jũya zuwa ga mutănensu, tsammă ninsu, ză su kőmo."

Ayah  12:63  الأية
فَلَمَّا رَجَعُوا إِلَىٰ أَبِيهِمْ قَالُوا يَا أَبَانَا مُنِعَ مِنَّا الْكَيْلُ فَأَرْسِلْ مَعَنَا أَخَانَا نَكْتَلْ وَإِنَّا لَهُ لَحَافِظُونَ
Falamma rajaAAoo ila abeehim qalooya abana muniAAa minna alkaylufaarsil maAAana akhana naktal wa-innalahu lahafithoon

Hausa
 
To, a lőkacin da suka kőma zuwa ga ubansu, suka ce: "Yă băbanmu! An hana mu awo sai ka aika ɗan'uwanmu tăre da mu. Ză mu yi awo. Kuma lalle ne, haƙĩƙa mũ, măsu lũra da Shi ne."

Ayah  12:64  الأية
قَالَ هَلْ آمَنُكُمْ عَلَيْهِ إِلَّا كَمَا أَمِنتُكُمْ عَلَىٰ أَخِيهِ مِن قَبْلُ ۖ فَاللهُ خَيْرٌ حَافِظًا ۖ وَهُوَ أَرْحَمُ الرَّاحِمِينَ
Qala hal amanukum AAalayhi illakama amintukum AAala akheehi min qablu fallahukhayrun hafithan wahuwa arhamu arrahimeen

Hausa
 
Ya ce: "Ashe, ză ni amince muku a kansa? Făce dai kamar yadda na amince muku a kan ɗan'uwansa daga gabăni, sai dai Allah ne Mafĩfĩcin măsu tsari, kuma Shĩ ne Mafi rahamar măsu rahama."

Ayah  12:65  الأية
وَلَمَّا فَتَحُوا مَتَاعَهُمْ وَجَدُوا بِضَاعَتَهُمْ رُدَّتْ إِلَيْهِمْ ۖ قَالُوا يَا أَبَانَا مَا نَبْغِي ۖ هَٰذِهِ بِضَاعَتُنَا رُدَّتْ إِلَيْنَا ۖ وَنَمِيرُ أَهْلَنَا وَنَحْفَظُ أَخَانَا وَنَزْدَادُ كَيْلَ بَعِيرٍ ۖ ذَٰلِكَ كَيْلٌ يَسِيرٌ
Walamma fatahoo mataAAahumwajadoo bidaAAatahum ruddat ilayhim qaloo yaabana ma nabghee hathihi bidaAAatunaruddat ilayna wanameeru ahlana wanahfathuakhana wanazdadu kayla baAAeerin thalikakaylun yaseer

Hausa
 
Kuma a lőkacin da suka bũɗe kăyansu, suka sămi hajjarsu an mayar musu da ita, suka ce: "Yă băbanmu! Ba mu zălunci! Wannan hajjarmu ce an mayar mana da ita, kuma mu nẽmo wa iyalinmu abinci, kuma mu kiyăye ɗan'uwanmu, kuma mu ƙăra awon kăyan răƙumi guda, wancan awo ne mai sauki."

Ayah  12:66  الأية
قَالَ لَنْ أُرْسِلَهُ مَعَكُمْ حَتَّىٰ تُؤْتُونِ مَوْثِقًا مِّنَ اللهِ لَتَأْتُنَّنِي بِهِ إِلَّا أَن يُحَاطَ بِكُمْ ۖ فَلَمَّا آتَوْهُ مَوْثِقَهُمْ قَالَ اللهُ عَلَىٰ مَا نَقُولُ وَكِيلٌ
Qala lan orsilahu maAAakum hattatu/tooni mawthiqan mina Allahi lata/tunnanee bihi illaan yuhata bikum falamma atawhu mawthiqahum qalaAllahu AAala ma naqoolu wakeel

Hausa
 
Ya ce: "Bă zan sake shi tăre da kũ ba, sai kun kawo mini alkawarinku baga Allah, haƙĩƙa, kună dawo mini da shi, sai fa idan an kẽwaye ku." To, a, lőkacinda suka yi măsa alkawari, ya ce: "Allah ne wakĩli a kan abin da muke faɗa."

Ayah  12:67  الأية
وَقَالَ يَا بَنِيَّ لَا تَدْخُلُوا مِن بَابٍ وَاحِدٍ وَادْخُلُوا مِنْ أَبْوَابٍ مُّتَفَرِّقَةٍ ۖ وَمَا أُغْنِي عَنكُم مِّنَ اللهِ مِن شَيْءٍ ۖ إِنِ الْحُكْمُ إِلَّا لِلَّهِ ۖ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ ۖ وَعَلَيْهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُتَوَكِّلُونَ
Waqala ya baniyya latadkhuloo min babin wahidin wadkhuloo minabwabin mutafarriqatin wama oghnee AAankum mina Allahimin shay-in ini alhukmu illa lillahiAAalayhi tawakkaltu waAAalayhi falyatawakkali almutawakkiloon

Hausa
 
Kuma ya ce: "Yă ɗiyana! Kada ku shiga ta ƙőfa guda, ku shiga ta ƙőfőfi dabam-dabam, kuma bă na wadătar muku kőme daga Allah. Băbu hukunci făce daga Allah, a gare Shi na dőgara, kuma a gare Shi măsu dőgara sai su dőgara."

Ayah  12:68  الأية
وَلَمَّا دَخَلُوا مِنْ حَيْثُ أَمَرَهُمْ أَبُوهُم مَّا كَانَ يُغْنِي عَنْهُم مِّنَ اللهِ مِن شَيْءٍ إِلَّا حَاجَةً فِي نَفْسِ يَعْقُوبَ قَضَاهَا ۚ وَإِنَّهُ لَذُو عِلْمٍ لِّمَا عَلَّمْنَاهُ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
Walamma dakhaloo min haythuamarahum aboohum ma kana yughnee AAanhum mina Allahimin shay-in illa hajatan fee nafsi yaAAqooba qadahawa-innahu lathoo AAilmin lima AAallamnahuwalakinna akthara annasi layaAAlamoon

Hausa
 
Kuma a lőkacin da suka shiga daga inda ubansu ya umurce su wani abu bai kasance yană wadătarwa ga barinsu daga Allah ba făce wata bukata ce a ran Yăƙũbu,ya bayyana ta. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, ma'abũcin wani ilmi ne ga abin da Muka sanar da shi, kuma mafi yawan mutăne ba su sani ba.

Ayah  12:69  الأية
وَلَمَّا دَخَلُوا عَلَىٰ يُوسُفَ آوَىٰ إِلَيْهِ أَخَاهُ ۖ قَالَ إِنِّي أَنَا أَخُوكَ فَلَا تَبْتَئِسْ بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Walamma dakhaloo AAala yoosufaawa ilayhi akhahu qala innee anaakhooka fala tabta-is bima kanoo yaAAmaloon

Hausa
 
Kuma a lőkacin da suka shiga wajen Yũsufu, ya tattara ɗan'uwansa zuwa gare shi, ya ce: "Lalle nĩ ne ɗan'uwanka, sabőda haka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sună aikatăwa."

Ayah  12:70  الأية
فَلَمَّا جَهَّزَهُم بِجَهَازِهِمْ جَعَلَ السِّقَايَةَ فِي رَحْلِ أَخِيهِ ثُمَّ أَذَّنَ مُؤَذِّنٌ أَيَّتُهَا الْعِيرُ إِنَّكُمْ لَسَارِقُونَ
Falamma jahhazahum bijahazihimjaAAala assiqayata fee rahli akheehi thummaaththana mu-aththinun ayyatuha alAAeeruinnakum lasariqoon

Hausa
 
Sa'an nan a lőkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, sai ya sanya ma'auni a cikin kăyan ɗan'uwansa sa'an nan kuma mai yẽkuwa ya yi yẽkuwa," Yă kũ ăyari! lalle ne, haƙĩƙa kũ ɓarăyi ne."

Ayah  12:71  الأية
قَالُوا وَأَقْبَلُوا عَلَيْهِم مَّاذَا تَفْقِدُونَ
Qaloo waaqbaloo AAalayhim mathatafqidoon

Hausa
 
Suka ce: kuma suka fuskanta zuwa gare su: "Mẽne ne kuke nẽma?"

Ayah  12:72  الأية
قَالُوا نَفْقِدُ صُوَاعَ الْمَلِكِ وَلِمَن جَاءَ بِهِ حِمْلُ بَعِيرٍ وَأَنَا بِهِ زَعِيمٌ
Qaloo nafqidu suwaAAaalmaliki waliman jaa bihi himlu baAAeerin waanabihi zaAAeem

Hausa
 
Suka ce: "Mună nẽman ma'aunin sarki. Kuma wanda ya zo da shi, yană da kăyan răkumi ɗaya, kuma ni ne lămuni game da shi."

Ayah  12:73  الأية
قَالُوا تَاللهِ لَقَدْ عَلِمْتُم مَّا جِئْنَا لِنُفْسِدَ فِي الْأَرْضِ وَمَا كُنَّا سَارِقِينَ
Qaloo tallahi laqadAAalimtum ma ji/na linufsida fee al-ardi wamakunna sariqeen

Hausa
 
Suka ce: "Tallahi! Lalle ne, haƙĩƙa, kun sani, ba mu zodon mu yi ɓarna a cikin ƙasa ba, kuma ba mu kasance ɓarăyi ba."

Ayah  12:74  الأية
قَالُوا فَمَا جَزَاؤُهُ إِن كُنتُمْ كَاذِبِينَ
Qaloo fama jazaohu inkuntum kathibeen

Hausa
 
Suka ce: "To mẽne ne sakamakonsa idan, kun kasance maƙaryata?"

Ayah  12:75  الأية
قَالُوا جَزَاؤُهُ مَن وُجِدَ فِي رَحْلِهِ فَهُوَ جَزَاؤُهُ ۚ كَذَٰلِكَ نَجْزِي الظَّالِمِينَ
Qaloo jazaohu man wujida feerahlihi fahuwa jazaohu kathalika najzee aththalimeen

Hausa
 
Suka ce: "Sakamakonsa, wanda aka same shi a cikin kăyansa, to, shi ne sakamakonsa, kamar wancan ne muke săka wa azzălumai."

Ayah  12:76  الأية
فَبَدَأَ بِأَوْعِيَتِهِمْ قَبْلَ وِعَاءِ أَخِيهِ ثُمَّ اسْتَخْرَجَهَا مِن وِعَاءِ أَخِيهِ ۚ كَذَٰلِكَ كِدْنَا لِيُوسُفَ ۖ مَا كَانَ لِيَأْخُذَ أَخَاهُ فِي دِينِ الْمَلِكِ إِلَّا أَن يَشَاءَ اللهُ ۚ نَرْفَعُ دَرَجَاتٍ مَّن نَّشَاءُ ۗ وَفَوْقَ كُلِّ ذِي عِلْمٍ عَلِيمٌ
Fabadaa bi-awAAiyatihim qabla wiAAa-iakheehi thumma istakhrajaha min wiAAa-i akheehi kathalikakidna liyoosufa ma kana liya/khuthaakhahu fee deeni almaliki illa an yashaa AllahunarfaAAu darajatin man nashao wafawqa kulli theeAAilmin AAaleem

Hausa
 
To, sai ya făra (bincike) da jikunansu a gabănin jakar ɗan'uwansa. Sa'an nan ya fitar da ita daga jakar ɗan'uwansa. Kamar wancan muka shirya wa Yũsufu. Bai kasance ya kăma ɗan'uwansa a cikin addinin (dőkőkin) sarki ba, făce idan Allah Ya so. Mună ɗaukaka darajőji ga wanda Muka so, kuma a saman kőwane ma'abũcin ilmi akwai wani masani.

Ayah  12:77  الأية
قَالُوا إِن يَسْرِقْ فَقَدْ سَرَقَ أَخٌ لَّهُ مِن قَبْلُ ۚ فَأَسَرَّهَا يُوسُفُ فِي نَفْسِهِ وَلَمْ يُبْدِهَا لَهُمْ ۚ قَالَ أَنتُمْ شَرٌّ مَّكَانًا ۖ وَاللهُ أَعْلَمُ بِمَا تَصِفُونَ
Qaloo in yasriq faqad saraqa akhunlahu min qablu faasarraha yoosufu fee nafsihi walam yubdihalahum qala antum sharrun makanan wallahuaAAlamu bima tasifoon

Hausa
 
Suka ce: "Idan ya yi săta, to, lalle ne wani ɗan'uwansa yă taɓa yin săta a gabăninsa." Sai Yũsufu ya bőye ta a cikin ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce: "Kũ ne mafi sharri ga wuri. Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffantăwa."

Ayah  12:78  الأية
قَالُوا يَا أَيُّهَا الْعَزِيزُ إِنَّ لَهُ أَبًا شَيْخًا كَبِيرًا فَخُذْ أَحَدَنَا مَكَانَهُ ۖ إِنَّا نَرَاكَ مِنَ الْمُحْسِنِينَ
Qaloo ya ayyuhaalAAazeezu inna lahu aban shaykhan kabeeran fakhuth ahadanamakanahu inna naraka mina almuhsineen

Hausa
 
Suka ce: "Yă kai Azĩzu! Lalle ne yană da wani ubă, tsoho mai daraja, sabőda haka ka kăma ɗayanmu amatsayinsa.Lalle ne mũ, muna ganin ka daga măsu kyautatăwa."

Ayah  12:79  الأية
قَالَ مَعَاذَ اللهِ أَن نَّأْخُذَ إِلَّا مَن وَجَدْنَا مَتَاعَنَا عِندَهُ إِنَّا إِذًا لَّظَالِمُونَ
Qala maAAatha Allahi anna/khutha illa man wajadna mataAAanaAAindahu inna ithan lathalimoon

Hausa
 
Ya ce: "Allah Ya tsare mu daga mu kăma wani făce wanda muka sămi kăyanmu a wurinsa. Lalle ne mũ, a lőkacin nan,haƙĩƙa, azzălumai ne."

Ayah  12:80  الأية
فَلَمَّا اسْتَيْأَسُوا مِنْهُ خَلَصُوا نَجِيًّا ۖ قَالَ كَبِيرُهُمْ أَلَمْ تَعْلَمُوا أَنَّ أَبَاكُمْ قَدْ أَخَذَ عَلَيْكُم مَّوْثِقًا مِّنَ اللهِ وَمِن قَبْلُ مَا فَرَّطتُمْ فِي يُوسُفَ ۖ فَلَنْ أَبْرَحَ الْأَرْضَ حَتَّىٰ يَأْذَنَ لِي أَبِي أَوْ يَحْكُمَ اللهُ لِي ۖ وَهُوَ خَيْرُ الْحَاكِمِينَ
Falamma istay-asoo minhu khalasoonajiyyan qala kabeeruhum alam taAAlamoo anna abakumqad akhatha AAalaykum mawthiqan mina Allahi waminqablu ma farrattum fee yoosufa falan abrahaal-arda hatta ya/thana lee abee aw yahkumaAllahu lee wahuwa khayru alhakimeen

Hausa
 
Sabőda haka, a lőkacin da suka yanke tsammăni daga gare shi, sai suka fita sună măsu gănăwa. Babbansu ya ce: "Shin, ba ku sani ba cẽwa lalle ne ubanku yariƙi alkawari daga Allah a kanku, kuma daga gabanin haka akwai abin da kuka yi na sakaci game da Yũsufu? Sabőda haka, bă zan gushe daga ƙasar nan ba făce ubana yă yi mini izni, kő kuwa Allah Ya yi hukunci a gare ni, kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mahukunta."

Ayah  12:81  الأية
ارْجِعُوا إِلَىٰ أَبِيكُمْ فَقُولُوا يَا أَبَانَا إِنَّ ابْنَكَ سَرَقَ وَمَا شَهِدْنَا إِلَّا بِمَا عَلِمْنَا وَمَا كُنَّا لِلْغَيْبِ حَافِظِينَ
IrjiAAoo ila abeekum faqooloo yaabana inna ibnaka saraqa wama shahidnailla bima AAalimna wama kunnalilghaybi hafitheen

Hausa
 
"Ku kőma zuwa ga ubanku, ku gaya masa: Yă băbanmu, lalle ne ɗanka yă yi săta, kuma ba mu yi shaida ba făce da abin da muka sani, kuma ba mu kasance mun san gaibu ba."

Ayah  12:82  الأية
وَاسْأَلِ الْقَرْيَةَ الَّتِي كُنَّا فِيهَا وَالْعِيرَ الَّتِي أَقْبَلْنَا فِيهَا ۖ وَإِنَّا لَصَادِقُونَ
Was-ali alqaryata allatee kunnafeeha walAAeera allatee aqbalna feehawa-inna lasadiqoon

Hausa
 
"Kuma ka tambayi alƙarya wadda muka kasance a cikinta da ăyari wanda muka gabăto acikinsa, kuma lalle ne haƙĩƙa, mũ măsu gaskiya ne."

Ayah  12:83  الأية
قَالَ بَلْ سَوَّلَتْ لَكُمْ أَنفُسُكُمْ أَمْرًا ۖ فَصَبْرٌ جَمِيلٌ ۖ عَسَى اللهُ أَن يَأْتِيَنِي بِهِمْ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْعَلِيمُ الْحَكِيمُ
Qala bal sawwalat lakum anfusukumamran fasabrun jameelun AAasa Allahu anya/tiyanee bihim jameeAAan innahu huwa alAAaleemu alhakeem

Hausa
 
Ya ce: "Ă'a, zukatanku sun ƙawăta wani al'amari a gare ku. Sai haƙuri mai kyăwo, akwai tsammănin Allah Ya zo mini da su gabă ɗaya ( Yũsufu da 'yan'uwansa). Lalle ne Shĩ ne Masani, Mai hikima."

Ayah  12:84  الأية
وَتَوَلَّىٰ عَنْهُمْ وَقَالَ يَا أَسَفَىٰ عَلَىٰ يُوسُفَ وَابْيَضَّتْ عَيْنَاهُ مِنَ الْحُزْنِ فَهُوَ كَظِيمٌ
Watawalla AAanhum waqala yaasafa AAala yoosufa wabyaddat AAaynahumina alhuzni fahuwa katheem

Hausa
 
Kuma ya jũya daga gare su, kuma ya ce: "Yă baƙin cikina a kan Yũsufu!" Kuma idănunsa suka yi fari sabőda huznu sa'an nan yană ta haɗẽwar haushi.

Ayah  12:85  الأية
قَالُوا تَاللهِ تَفْتَأُ تَذْكُرُ يُوسُفَ حَتَّىٰ تَكُونَ حَرَضًا أَوْ تَكُونَ مِنَ الْهَالِكِينَ
Qaloo tallahi taftaotathkuru yoosufa hatta takoona haradanaw takoona mina alhalikeen

Hausa
 
Suka ce: "Tallahi! Bă ză ka gushe ba, kană ambaton Yũsufu, har ka kasance Mai rauni ƙwarai, kő kuwa ka kasance daga măsu halaka."

Ayah  12:86  الأية
قَالَ إِنَّمَا أَشْكُو بَثِّي وَحُزْنِي إِلَى اللهِ وَأَعْلَمُ مِنَ اللهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ
Qala innama ashkoo baththee wahuzneeila Allahi waaAAlamu mina Allahi ma lataAAlamoon

Hausa
 
Ya ce: "Abin sani kawai, ină kai ƙarar baƙin cikĩna da sunőna zuwa ga Allah, kuma na san abin da ba ku sani ba daga Allah."

Ayah  12:87  الأية
يَا بَنِيَّ اذْهَبُوا فَتَحَسَّسُوا مِن يُوسُفَ وَأَخِيهِ وَلَا تَيْأَسُوا مِن رَّوْحِ اللهِ ۖ إِنَّهُ لَا يَيْأَسُ مِن رَّوْحِ اللهِ إِلَّا الْقَوْمُ الْكَافِرُونَ
Ya baniyya ithhaboo fatahassasoomin yoosufa waakheehi wala tay-asoo min rawhi Allahiinnahu la yay-asu min rawhi Allahi illaalqawmu alkafiroon

Hausa
 
"Yă ɗiyăna! Sai ku tafi ku nẽmo lăbărin Yũsufu da ɗan'uwansa. Kada ku yanke tsammăni daga rahamar Allah. Lalle ne, băbu Mai yanke tsammăni daga rahamar Allah făce mutăne kăfirai."

Ayah  12:88  الأية
فَلَمَّا دَخَلُوا عَلَيْهِ قَالُوا يَا أَيُّهَا الْعَزِيزُ مَسَّنَا وَأَهْلَنَا الضُّرُّ وَجِئْنَا بِبِضَاعَةٍ مُّزْجَاةٍ فَأَوْفِ لَنَا الْكَيْلَ وَتَصَدَّقْ عَلَيْنَا ۖ إِنَّ اللهَ يَجْزِي الْمُتَصَدِّقِينَ
Falamma dakhaloo AAalayhi qalooya ayyuha alAAazeezu massana waahlanaaddurru waji/na bibidaAAatin muzjatinfaawfi lana alkayla watasaddaq AAalayna innaAllaha yajzee almutasaddiqeen

Hausa
 
Sa'an nan a lőkacin da suka shiga gare shi suka ce: "Yă kai Azĩzu! Cũta ta shăfe mu, mũ da iyălinmu, kuma mun zo da wata hăja maras kuma. Sai ka cika mana ma'auni, kuma ka yi sadaka a gare mu. Lalle ne Allah Yană săka wa măsu yin sadaka. "

Ayah  12:89  الأية
قَالَ هَلْ عَلِمْتُم مَّا فَعَلْتُم بِيُوسُفَ وَأَخِيهِ إِذْ أَنتُمْ جَاهِلُونَ
Qala hal AAalimtum mafaAAaltum biyoosufa waakheehi ith antum jahiloon

Hausa
 
Ya ce: "Shin, kan san abin da kuka aikata ga Yũsufu da ɗan'uwansa a lőkacin da kuke jăhilai?"

Ayah  12:90  الأية
قَالُوا أَإِنَّكَ لَأَنتَ يُوسُفُ ۖ قَالَ أَنَا يُوسُفُ وَهَٰذَا أَخِي ۖ قَدْ مَنَّ اللهُ عَلَيْنَا ۖ إِنَّهُ مَن يَتَّقِ وَيَصْبِرْ فَإِنَّ اللهَ لَا يُضِيعُ أَجْرَ الْمُحْسِنِينَ
Qaloo a-innaka laanta yoosufa qalaana yoosufu wahatha akhee qad manna AllahuAAalayna innahu man yattaqi wayasbir fa-inna Allahala yudeeAAu ajra almuhsineen

Hausa
 
Saka ce: "Shin kő, lalle ne, kai ne Yũsufu?" Ya ce: "Nĩ ne Yũsufu, kuma wamian shĩ ne ɗan'uwăna. Hƙĩƙa Allah Yă yi falala a gare mu. Lalle ne, shi wanda ya bi Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, Lalle ne Allah bă Ya tőzarta lădar măsu kyautatăwa."

Ayah  12:91  الأية
قَالُوا تَاللهِ لَقَدْ آثَرَكَ اللهُ عَلَيْنَا وَإِن كُنَّا لَخَاطِئِينَ
Qaloo tallahi laqad atharakaAllahu AAalayna wa-in kunna lakhati-een

Hausa
 
Suka ce: "Tallahi! Lalle ne haƙĩƙa, Allah Yă zăɓe ka akannmu, kuma lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, măsu kuskure."

Ayah  12:92  الأية
قَالَ لَا تَثْرِيبَ عَلَيْكُمُ الْيَوْمَ ۖ يَغْفِرُ اللهُ لَكُمْ ۖ وَهُوَ أَرْحَمُ الرَّاحِمِينَ
Qala la tathreeba AAalaykumualyawma yaghfiru Allahu lakum wahuwa arhamu arrahimeen

Hausa
 
Ya ce: "Băbu zargi akanku a yau, Allah Yană găfartă muku, kuma Shĩ ne Mafi rahamar măsu rahama."

Ayah  12:93  الأية
اذْهَبُوا بِقَمِيصِي هَٰذَا فَأَلْقُوهُ عَلَىٰ وَجْهِ أَبِي يَأْتِ بَصِيرًا وَأْتُونِي بِأَهْلِكُمْ أَجْمَعِينَ
Ithhaboo biqameesee hathafaalqoohu AAala wajhi abee ya/ti baseeran wa/tooneebi-ahlikum ajmaAAeen

Hausa
 
"Ku tafi da rĩgăta wannan, sa'an nan ku jẽfa ta a kan fuskar mahaifina, zai kőma mai gani. Kuma ku zo mini da iyălinku băki ɗaya."

Ayah  12:94  الأية
وَلَمَّا فَصَلَتِ الْعِيرُ قَالَ أَبُوهُمْ إِنِّي لَأَجِدُ رِيحَ يُوسُفَ ۖ لَوْلَا أَن تُفَنِّدُونِ
Walamma fasalati alAAeeru qalaaboohum innee laajidu reeha yoosufa lawla antufannidoon

Hausa
 
Kuma, a lőkacin da ăyari ya bar (Masar) ubansa ya ce: "Lalle ne nĩ ină shăƙar iskar Yũsufu, bă dőmin kană ƙaryata ni ba."

Ayah  12:95  الأية
قَالُوا تَاللهِ إِنَّكَ لَفِي ضَلَالِكَ الْقَدِيمِ
Qaloo tallahi innakalafee dalalika alqadeem

Hausa
 
Suka ce: "Tallahi lalle ne, kai, haƙĩƙa, kană a cikin ɓatarka daɗaɗɗa."

Ayah  12:96  الأية
فَلَمَّا أَن جَاءَ الْبَشِيرُ أَلْقَاهُ عَلَىٰ وَجْهِهِ فَارْتَدَّ بَصِيرًا ۖ قَالَ أَلَمْ أَقُل لَّكُمْ إِنِّي أَعْلَمُ مِنَ اللهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ
Falamma an jaa albasheeru alqahuAAala wajhihi fartadda baseeran qalaalam aqul lakum innee aAAlamu mina Allahi ma lataAAlamoon

Hausa
 
Sa'an nan a lőkacin da mai băyar da bushăra ya je, sai ya jẽfa ta a kan fuskarsa, sai ya kőma mai gani. Ya ce: "Shin, ban gaya muku ba, lalle ne, ni ină sanin abin da ba ku sani ba, daga Allah?"

Ayah  12:97  الأية
قَالُوا يَا أَبَانَا اسْتَغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا إِنَّا كُنَّا خَاطِئِينَ
Qaloo ya abanaistaghfir lana thunoobana inna kunnakhati-een

Hausa
 
Suka ce: "Yă ubanmu! ka nẽma mana găfara ga zunubanmu, lalle ne mũ, mun kasance măsu kuskure."

Ayah  12:98  الأية
قَالَ سَوْفَ أَسْتَغْفِرُ لَكُمْ رَبِّي ۖ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
Qala sawfa astaghfiru lakum rabbeeinnahu huwa alghafooru arraheem

Hausa
 
Ya ce: "Da sannu ză ni nẽma muku găfara daga Ubangijina. Shi ne Mai găfara, Mai jin ƙai."

Ayah  12:99  الأية
فَلَمَّا دَخَلُوا عَلَىٰ يُوسُفَ آوَىٰ إِلَيْهِ أَبَوَيْهِ وَقَالَ ادْخُلُوا مِصْرَ إِن شَاءَ اللهُ آمِنِينَ
Falamma dakhaloo AAala yoosufaawa ilayhi abawayhi waqala odkhuloo misrain shaa Allahu amineen

Hausa
 
Sa'an nan a lőkacin da suka shiga gun Yũsufu, yă tattara mahaifansa biyu a gare shi, kuma ya ce: "Ku shiga Masar in Allah Ya so, kuna amintattu."

Ayah  12:100  الأية
وَرَفَعَ أَبَوَيْهِ عَلَى الْعَرْشِ وَخَرُّوا لَهُ سُجَّدًا ۖ وَقَالَ يَا أَبَتِ هَٰذَا تَأْوِيلُ رُؤْيَايَ مِن قَبْلُ قَدْ جَعَلَهَا رَبِّي حَقًّا ۖ وَقَدْ أَحْسَنَ بِي إِذْ أَخْرَجَنِي مِنَ السِّجْنِ وَجَاءَ بِكُم مِّنَ الْبَدْوِ مِن بَعْدِ أَن نَّزَغَ الشَّيْطَانُ بَيْنِي وَبَيْنَ إِخْوَتِي ۚ إِنَّ رَبِّي لَطِيفٌ لِّمَا يَشَاءُ ۚ إِنَّهُ هُوَ الْعَلِيمُ الْحَكِيمُ
WarafaAAa abawayhi AAala alAAarshiwakharroo lahu sujjadan waqala ya abati hathata/weelu ru/yaya min qablu qad jaAAalaha rabbee haqqanwaqad ahsana bee ith akhrajanee mina assijniwajaa bikum mina albadwi min baAAdi an nazagha ashshaytanubaynee wabayna ikhwatee inna rabbee lateefun limayashao innahu huwa alAAaleemu alhakeem

Hausa
 
Kuma ya ɗaukaka iyăyensa biyu a kan karaga, sa'an nan suka făɗi a gare shi, suna măsu sujada. Kuma ya ce: "Ya băbăna! Wannan ita ce fassarar mafarkin nan năwa. Lalle ne Ubangijina Ya sanya shi ya tabbata sősai, kuma lalle ne Ya kyautata game da ni a lőkacin da Ya fitar da ni daga kurkuku. Kuma Ya zo da ku daga ƙauye, a băyan Shaiɗan yă yi fisgar ɓarna a tsakănĩna da tsakănin 'yan'uwana, Lalle ne Ubangijina Mai tausasawa ne ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ,Shĩ ne Masani, Mai hikima."

Ayah  12:101  الأية
رَبِّ قَدْ آتَيْتَنِي مِنَ الْمُلْكِ وَعَلَّمْتَنِي مِن تَأْوِيلِ الْأَحَادِيثِ ۚ فَاطِرَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ أَنتَ وَلِيِّي فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ ۖ تَوَفَّنِي مُسْلِمًا وَأَلْحِقْنِي بِالصَّالِحِينَ
Rabbi qad ataytanee mina almulkiwaAAallamtanee min ta/weeli al-ahadeethi fatira assamawatiwal-ardi anta waliyyee fee addunyawal-akhirati tawaffanee musliman waalhiqneebissaliheen

Hausa
 
"Yă Ubangijina lalle ne Kă bă ni daga mulki, kuma Kă sanar da ni daga fassarar lăbaru. Ya Mahaliccin sammai da ƙasa! Kai ne Majiɓincĩna a dũniya da Lăhira Ka karɓi raina ină Musulmi, kuma Ka riskar da ni ga sălihai."

Ayah  12:102  الأية
ذَٰلِكَ مِنْ أَنبَاءِ الْغَيْبِ نُوحِيهِ إِلَيْكَ ۖ وَمَا كُنتَ لَدَيْهِمْ إِذْ أَجْمَعُوا أَمْرَهُمْ وَهُمْ يَمْكُرُونَ
Thalika min anba-i alghaybinooheehi ilayka wama kunta ladayhim ithajmaAAoo amrahum wahum yamkuroon

Hausa
 
Wannan daga lăbarun gaibi ne, Mună yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lőkacin da suke yin niyyar zartar da al'amarinsu, alhăli sună yin măkirci.

Ayah  12:103  الأية
وَمَا أَكْثَرُ النَّاسِ وَلَوْ حَرَصْتَ بِمُؤْمِنِينَ
Wama aktharu annasiwalaw harasta bimu/mineen

Hausa
 
Kuma mafi yawan mutăne ba su zama măsu ĩmăni ba,kő da kă yi kwaɗayin haka.

Ayah  12:104  الأية
وَمَا تَسْأَلُهُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۚ إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَالَمِينَ
Wama tas-aluhum AAalayhi min ajrinin huwa illa thikrun lilAAalameen

Hausa
 
Kuma bă ka tambayar su wata lădă a kansa. Shĩ bai zama ba făce ambato dőmin halittu.

Ayah  12:105  الأية
وَكَأَيِّن مِّنْ آيَةٍ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ يَمُرُّونَ عَلَيْهَا وَهُمْ عَنْهَا مُعْرِضُونَ
Wakaayyin min ayatin fee assamawatiwal-ardi yamurroona AAalayha wahum AAanhamuAAridoon

Hausa
 
Kuma da yawa, wata ăyă a cikin sammai da ƙasa sună shũɗẽwa a kanta kuma sũ, sună bijirẽwa daga gare ta.

Ayah  12:106  الأية
وَمَا يُؤْمِنُ أَكْثَرُهُم بِاللهِ إِلَّا وَهُم مُّشْرِكُونَ
Wama yu/minu aktharuhum billahiilla wahum mushrikoon

Hausa
 
Kuma mafi yawansu ba su yin ĩmăni da Allah făce kuma sună măsu shirki.

Ayah  12:107  الأية
أَفَأَمِنُوا أَن تَأْتِيَهُمْ غَاشِيَةٌ مِّنْ عَذَابِ اللهِ أَوْ تَأْتِيَهُمُ السَّاعَةُ بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
Afaaminoo an ta/tiyahum ghashiyatunmin AAathabi Allahi aw ta/tiyahumu assaAAatubaghtatan wahum la yashAAuroon

Hausa
 
Shin fa, sun amince cẽwa wata masĩfa daga azăbar Allah ta zo musu ko kuwa Tăshin ˇiyăma ta zo musu kwatsam, alhăli sũ ba su sani ba?

Ayah  12:108  الأية
قُلْ هَٰذِهِ سَبِيلِي أَدْعُو إِلَى اللهِ ۚ عَلَىٰ بَصِيرَةٍ أَنَا وَمَنِ اتَّبَعَنِي ۖ وَسُبْحَانَ اللهِ وَمَا أَنَا مِنَ الْمُشْرِكِينَ
Qul hathihi sabeelee adAAoo ilaAllahi AAala baseeratin ana wamaniittabaAAanee wasubhana Allahi wama anamina almushrikeen

Hausa
 
Ka ce: "Wannan ce hanyăta ; ină kira zuwa ga Allah a kan basĩra, nĩ da waɗanda suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga măsu shirki ba."

Ayah  12:109  الأية
وَمَا أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ إِلَّا رِجَالًا نُّوحِي إِلَيْهِم مِّنْ أَهْلِ الْقُرَىٰ ۗ أَفَلَمْ يَسِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَيَنظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۗ وَلَدَارُ الْآخِرَةِ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ اتَّقَوْا ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَ
Wama arsalna min qablika illarijalan noohee ilayhim min ahli alquraafalam yaseeroo fee al-ardi fayanthurookayfa kana AAaqibatu allatheena min qablihimwaladaru al-akhirati khayrun lillatheenaittaqaw afala taAAqiloon

Hausa
 
Kuma ba Mu aika ba a gabăninka făce mazăje, Mună wahayi zuwa gare su, daga mutănen ƙauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasa ba, dőmin su dũbayadda ăƙibar waɗanda suka kasance daga gabăninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lăhira shĩ ne mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa? Shin fa, bă ku hankalta?

Ayah  12:110  الأية
حَتَّىٰ إِذَا اسْتَيْأَسَ الرُّسُلُ وَظَنُّوا أَنَّهُمْ قَدْ كُذِبُوا جَاءَهُمْ نَصْرُنَا فَنُجِّيَ مَن نَّشَاءُ ۖ وَلَا يُرَدُّ بَأْسُنَا عَنِ الْقَوْمِ الْمُجْرِمِينَ
Hatta itha istay-asa arrusuluwathannoo annahum qad kuthiboo jaahumnasruna fanujjiya man nashao walayuraddu ba/suna AAani alqawmi almujrimeen

Hausa
 
Har a lőkacin da Manzanni suka yanke tsammăni, kuma suka yi zaton cẽwa an jingina suga ƙarya, sai taimakonMu ya je masu, Sa'an nan Mu tsẽrar da wanda Muke so, kuma bă a mayar da azăbarMu daga mutăne măsu laifi.

Ayah  12:111  الأية
لَقَدْ كَانَ فِي قَصَصِهِمْ عِبْرَةٌ لِّأُولِي الْأَلْبَابِ ۗ مَا كَانَ حَدِيثًا يُفْتَرَىٰ وَلَٰكِن تَصْدِيقَ الَّذِي بَيْنَ يَدَيْهِ وَتَفْصِيلَ كُلِّ شَيْءٍ وَهُدًى وَرَحْمَةً لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Laqad kana fee qasasihimAAibratun li-olee al-albabi ma kana hadeethanyuftara walakin tasdeeqa allatheebayna yadayhi watafseela kulli shay-in wahudan warahmatanliqawmin yu/minoon

Hausa
 
Lalle ne haƙĩƙa abin kula yă kasance a cikin ƙissoshinsu ga masu hankali. Bai kasance wani ƙirƙiran lăbări ba kuma amma shi gaskatăwa ne ga, abin da yake a gaba gare shi, da rarrabẽwar dukan abũbuwa, da shiriya da rahama ga mutăne waɗanda suka yi ĩmăni.





© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us