Prev  

16. Surah An-Nahl سورة النحل

  Next  




1st Ayah  1  الأية ١الأولي
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
أَتَىٰ أَمْرُ اللهِ فَلَا تَسْتَعْجِلُوهُ ۚ سُبْحَانَهُ وَتَعَالَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Ata amru Allahi falatastaAAjiloohu subhanahu wataAAala AAammayushrikoon

Hausa
 
Al'amarin Allah yă zo, sabőda haka kada ku nẽmi hanzartăwarsa. Tsarkin Allah ya tabbata, kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.

Ayah  16:2  الأية
يُنَزِّلُ الْمَلَائِكَةَ بِالرُّوحِ مِنْ أَمْرِهِ عَلَىٰ مَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ أَنْ أَنذِرُوا أَنَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا أَنَا فَاتَّقُونِ
Yunazzilu almala-ikata birroohimin amrihi AAala man yashao min AAibadihi ananthiroo annahu la ilaha illa anafattaqoon

Hausa
 
Yană sassaukar da mală'iku da Rũhi daga umurninSaa kan wanda Yake so daga băyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, băbu abin bautăwa făce Ni, sabőda haka ku bĩ Ni da taƙawa.

Ayah  16:3  الأية
خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِالْحَقِّ ۚ تَعَالَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Khalaqa assamawati wal-ardabilhaqqi taAAala AAammayushrikoon

Hausa
 
Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.

Ayah  16:4  الأية
خَلَقَ الْإِنسَانَ مِن نُّطْفَةٍ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٌ مُّبِينٌ
Khalaqa al-insana min nutfatinfa-itha huwa khaseemun mubeen

Hausa
 
Ya halicci mutum daga maniyyi, sai gă shi yană mai husũma bayyananniya.

Ayah  16:5  الأية
وَالْأَنْعَامَ خَلَقَهَا ۗ لَكُمْ فِيهَا دِفْءٌ وَمَنَافِعُ وَمِنْهَا تَأْكُلُونَ
Wal-anAAama khalaqahalakum feeha dif-on wamanafiAAu waminhata-kuloon

Hausa
 
Da dabbőbin ni'ima, Ya halicce su dőminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfănőni, kuma daga gare su kuke ci.

Ayah  16:6  الأية
وَلَكُمْ فِيهَا جَمَالٌ حِينَ تُرِيحُونَ وَحِينَ تَسْرَحُونَ
Walakum feeha jamalun heenatureehoona waheena tasrahoon

Hausa
 
Kuma kună da kyau a cikinsu a lőkacin da suke kőmőwa daga kĩwo da maraice da lőkacin da suke sakuwă.

Ayah  16:7  الأية
وَتَحْمِلُ أَثْقَالَكُمْ إِلَىٰ بَلَدٍ لَّمْ تَكُونُوا بَالِغِيهِ إِلَّا بِشِقِّ الْأَنفُسِ ۚ إِنَّ رَبَّكُمْ لَرَءُوفٌ رَّحِيمٌ
Watahmilu athqalakum ilabaladin lam takoonoo baligheehi illa bishiqqial-anfusi inna rabbakum laraoofun raheem

Hausa
 
Kuma sună ɗaukar kăyanku măsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance măsu isa gare shi ba, făce da tsananin wahalar răyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa, Mai tausayi, Maijin ƙai.

Ayah  16:8  الأية
وَالْخَيْلَ وَالْبِغَالَ وَالْحَمِيرَ لِتَرْكَبُوهَا وَزِينَةً ۚ وَيَخْلُقُ مَا لَا تَعْلَمُونَ
Walkhayla walbighalawalhameera litarkabooha wazeenatanwayakhluqu ma la taAAlamoon

Hausa
 
Kuma da dawăki da alfadarai da jăkuna, dőmin ku hau su, kuma da ƙawa. Kuma Yana halitta abin da ba ku sani ba.

Ayah  16:9  الأية
وَعَلَى اللهِ قَصْدُ السَّبِيلِ وَمِنْهَا جَائِرٌ ۚ وَلَوْ شَاءَ لَهَدَاكُمْ أَجْمَعِينَ
WaAAala Allahi qasdu assabeeliwaminha ja-irun walaw shaa lahadakumajmaAAeen

Hausa
 
Kuma ga Allah madaidaiciyar hanya take kuma daga gare ta akwai mai karkacẽwa. Kuma da Yă so, dă Ya shiryar da ku gabă ɗaya.

Ayah  16:10  الأية
هُوَ الَّذِي أَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً ۖ لَّكُم مِّنْهُ شَرَابٌ وَمِنْهُ شَجَرٌ فِيهِ تُسِيمُونَ
Huwa allathee anzala mina assama-imaan lakum minhu sharabun waminhu shajarun feehituseemoon

Hausa
 
Shĩ ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama dőminku, daga gare shi akwai abin sha, kuma daga gare shi ităce yake, a cikinsa kuke yin kĩwo.

Ayah  16:11  الأية
يُنبِتُ لَكُم بِهِ الزَّرْعَ وَالزَّيْتُونَ وَالنَّخِيلَ وَالْأَعْنَابَ وَمِن كُلِّ الثَّمَرَاتِ ۗ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ
Yunbitu lakum bihi azzarAAa wazzaytoonawannakheela wal-aAAnaba wamin kulli aththamaratiinna fee thalika laayatan liqawmin yatafakkaroon

Hausa
 
Yană tsirar da shũka game da shi, dőminku zaitũni da dabĩnai da inabai, kuma daga dukan 'yă'yan ităce. Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ăyă ga mutăne waɗanda suke yin tunăni.

Ayah  16:12  الأية
وَسَخَّرَ لَكُمُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ ۖ وَالنُّجُومُ مُسَخَّرَاتٌ بِأَمْرِهِ ۗ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ
Wasakhkhara lakumu allayla wannaharawashshamsa walqamara wannujoomumusakhkharatun bi-amrihi inna fee thalika laayatinliqawmin yaAAqiloon

Hausa
 
Kuma Ya hőrẽ muku dare da wuni da rănă da wată kuma taurări hőrarru ne da umurninSa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ăyőyi ga mutăne waɗanda suke hankalta.

Ayah  16:13  الأية
وَمَا ذَرَأَ لَكُمْ فِي الْأَرْضِ مُخْتَلِفًا أَلْوَانُهُ ۗ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً لِّقَوْمٍ يَذَّكَّرُونَ
Wama tharaa lakum fee al-ardimukhtalifan alwanuhu inna fee thalika laayatanliqawmin yaththakkaroon

Hausa
 
Kuma abin da Ya halitta muku a cikin ƙasa, yana mai săɓănin launukansa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ăyă ga mutăne waɗanda suke tunăwa.

Ayah  16:14  الأية
وَهُوَ الَّذِي سَخَّرَ الْبَحْرَ لِتَأْكُلُوا مِنْهُ لَحْمًا طَرِيًّا وَتَسْتَخْرِجُوا مِنْهُ حِلْيَةً تَلْبَسُونَهَا وَتَرَى الْفُلْكَ مَوَاخِرَ فِيهِ وَلِتَبْتَغُوا مِن فَضْلِهِ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Wahuwa allathee sakhkhara albahralita/kuloo minhu lahman tariyyan watastakhrijoominhu hilyatan talbasoonaha watara alfulkamawakhira feehi walitabtaghoo min fadlihiwalaAAallakum tashkuroon

Hausa
 
Kuma Shĩ ne Ya hőrẽ tẽku dőmin ku ci wani nama săbő daga gare shi, kuma kună fitarwa, daga gare shi, ƙawă wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirăge sună yankan ruwa a cikinsa kuma dőmin ku yi nẽman (fatauci) daga falalarSa. Kuma mai yiwuwa ne kuna gődẽwa.

Ayah  16:15  الأية
وَأَلْقَىٰ فِي الْأَرْضِ رَوَاسِيَ أَن تَمِيدَ بِكُمْ وَأَنْهَارًا وَسُبُلًا لَّعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ
Waalqa fee al-ardi rawasiyaan tameeda bikum waanharan wasubulan laAAallakum tahtadoon

Hausa
 
Kuma Ya jẽfa, a cikin ƙasa, tabbatattun duwatsu dőmin kada ta karkata da ku, da kőguna da hanyőyi, ɗammăninku kună shiryuwa.

Ayah  16:16  الأية
وَعَلَامَاتٍ ۚ وَبِالنَّجْمِ هُمْ يَهْتَدُونَ
WaAAalamatin wabinnajmihum yahtadoon

Hausa
 
Kuma da waɗansu alămőmi, kuma da taurări sună măsu nẽman shiryuwa (ga tafiyarsu ta fatauci).

Ayah  16:17  الأية
أَفَمَن يَخْلُقُ كَمَن لَّا يَخْلُقُ ۗ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Afaman yakhluqu kaman la yakhluquafala tathakkaroon

Hausa
 
Shin, wanda Yake yin halitta yană yin kama da wanda ba ya yin halitta? Shin fa, bă ku tunăwa?

Ayah  16:18  الأية
وَإِن تَعُدُّوا نِعْمَةَ اللهِ لَا تُحْصُوهَا ۗ إِنَّ اللهَ لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ
Wa-in taAAuddoo niAAmata Allahi latuhsooha inna Allaha laghafoorun raheem

Hausa
 
Kuma idan kun ƙidăya ni'imar Allah, bă ku iya lissafa ta. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai găfara ne, Mai jin ƙai.

Ayah  16:19  الأية
وَاللهُ يَعْلَمُ مَا تُسِرُّونَ وَمَا تُعْلِنُونَ
Wallahu yaAAlamu matusirroona wama tuAAlinoon

Hausa
 
Kuma Allah Yană sanin abin da kuke asirtăwa da abin da kuke bayyanăwa.

Ayah  16:20  الأية
وَالَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِ اللهِ لَا يَخْلُقُونَ شَيْئًا وَهُمْ يُخْلَقُونَ
Wallatheena yadAAoona mindooni Allahi la yakhluqoona shay-an wahumyukhlaqoon

Hausa
 
Kuma waɗanda suke kira, baicin Allah, ba su halicci kőme ba, kuma sũ ne ake halittawa.

Ayah  16:21  الأية
أَمْوَاتٌ غَيْرُ أَحْيَاءٍ ۖ وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ
Amwatun ghayru ahya-inwama yashAAuroona ayyana yubAAathoon

Hausa
 
Matattũ ne, bă su da rai, kuma ba su san a wane lőkaci ake tăyar da su ba.

Ayah  16:22  الأية
إِلَٰهُكُمْ إِلَٰهٌ وَاحِدٌ ۚ فَالَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ قُلُوبُهُم مُّنكِرَةٌ وَهُم مُّسْتَكْبِرُونَ
Ilahukum ilahun wahidunfallatheena la yu/minoona bil-akhiratiquloobuhum munkiratun wahum mustakbiroon

Hausa
 
Abin bautawarku, abin bautăwa ne guda, to, waɗanda ba su yin ĩmăni da Lăhira, zukătansu măsu musu ne, kuma su makangara ne.

Ayah  16:23  الأية
لَا جَرَمَ أَنَّ اللهَ يَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ ۚ إِنَّهُ لَا يُحِبُّ الْمُسْتَكْبِرِينَ
La jarama anna Allaha yaAAlamuma yusirroona wama yuAAlinoona innahu la yuhibbualmustakbireen

Hausa
 
Haƙĩƙa, lalle ne, Allah Yană sanin abin da suke asirtăwa da abin da suke bayyanăwa. Lalle ne Shi, bă Ya Son măsu girman kai.

Ayah  16:24  الأية
وَإِذَا قِيلَ لَهُم مَّاذَا أَنزَلَ رَبُّكُمْ ۙ قَالُوا أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ
Wa-itha qeela lahum mathaanzala rabbukum qaloo asateeru al-awwaleen

Hausa
 
Idan aka ce musu: "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Sai su ce: "Tătsũniyőyin mutănen farko."

Ayah  16:25  الأية
لِيَحْمِلُوا أَوْزَارَهُمْ كَامِلَةً يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۙ وَمِنْ أَوْزَارِ الَّذِينَ يُضِلُّونَهُم بِغَيْرِ عِلْمٍ ۗ أَلَا سَاءَ مَا يَزِرُونَ
Liyahmiloo awzarahum kamilatanyawma alqiyamati wamin awzari allatheena yudilloonahumbighayri AAilmin ala saa ma yaziroon

Hausa
 
Dőmin su ɗauki zunubansu cikakku a Rănar ˇiyăma, kuma daga zunuban waɗanda suke ɓatarwa bă da wani ilmi ba. To, abin da suke ɗauka na zunubi ya mũnana.

Ayah  16:26  الأية
قَدْ مَكَرَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَأَتَى اللهُ بُنْيَانَهُم مِّنَ الْقَوَاعِدِ فَخَرَّ عَلَيْهِمُ السَّقْفُ مِن فَوْقِهِمْ وَأَتَاهُمُ الْعَذَابُ مِنْ حَيْثُ لَا يَشْعُرُونَ
Qad makara allatheena min qablihimfaata Allahu bunyanahum mina alqawaAAidifakharra AAalayhimu assaqfu min fawqihim waatahumualAAathabu min haythu la yashAAuroon

Hausa
 
Lalle ne waɗanda suke a gabăninsu sun yi măkirci, sai Allah Ya je wa gininsu daga harsăshensa, sai rufi ya făɗa a kansu daga bisansu, kuma azăba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba.

Ayah  16:27  الأية
ثُمَّ يَوْمَ الْقِيَامَةِ يُخْزِيهِمْ وَيَقُولُ أَيْنَ شُرَكَائِيَ الَّذِينَ كُنتُمْ تُشَاقُّونَ فِيهِمْ ۚ قَالَ الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ إِنَّ الْخِزْيَ الْيَوْمَ وَالسُّوءَ عَلَى الْكَافِرِينَ
Thumma yawma alqiyamati yukhzeehimwayaqoolu ayna shuraka-iya allatheena kuntum tushaqqoonafeehim qala allatheena ootoo alAAilma inna alkhizyaalyawma wassoo-a AAala alkafireen

Hausa
 
Sa'an nan a Rănar ˇiyăma (Allah) Yană kunyată su, kuma Yană cẽwa: "Ină abőkan tărayyaTa, waɗanda kuka kasance kună găbă a cikin ɗaukaka sha'aninsu?" Waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Lalle ne wulăkanci a yau da cũta sun tabbata a kan kăfirai."

Ayah  16:28  الأية
الَّذِينَ تَتَوَفَّاهُمُ الْمَلَائِكَةُ ظَالِمِي أَنفُسِهِمْ ۖ فَأَلْقَوُا السَّلَمَ مَا كُنَّا نَعْمَلُ مِن سُوءٍ ۚ بَلَىٰ إِنَّ اللهَ عَلِيمٌ بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Allatheena tatawaffahumu almala-ikatuthalimee anfusihim faalqawoo assalamama kunna naAAmalu min soo-in bala inna AllahaAAaleemun bima kuntum taAAmaloon

Hausa
 
Waɗanda malăiku suke karɓar răyukansu sună măsu zăluntar kansu. Sai suka jẽfa nẽman sulhu (suka ce) "Ba mu kasance muna aikata wani mummũnan aiki ba." Kayya! Lalle Allah ne Masani ga abin da kuka kasance kună aikatăwa.

Ayah  16:29  الأية
فَادْخُلُوا أَبْوَابَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا ۖ فَلَبِئْسَ مَثْوَى الْمُتَكَبِّرِينَ
Fadkhuloo abwaba jahannama khalideenafeeha falabi/sa mathwa almutakabbireen

Hausa
 
Sai ku shiga ƙőfőfin Jahannama, kună madawwama a cikinta. Sa'an nan tir da mazaunin măsu girman kai.

Ayah  16:30  الأية
وَقِيلَ لِلَّذِينَ اتَّقَوْا مَاذَا أَنزَلَ رَبُّكُمْ ۚ قَالُوا خَيْرًا ۗ لِّلَّذِينَ أَحْسَنُوا فِي هَٰذِهِ الدُّنْيَا حَسَنَةٌ ۚ وَلَدَارُ الْآخِرَةِ خَيْرٌ ۚ وَلَنِعْمَ دَارُ الْمُتَّقِينَ
Waqeela lillatheena ittaqaw mathaanzala rabbukum qaloo khayran lillatheena ahsanoofee hathihi addunya hasanatun waladarual-akhirati khayrun walaniAAma daru almuttaqeen

Hausa
 
Kuma aka ce wa waɗanda suka yi taƙawa, "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Suka ce, "Alhẽri Ya saukar, ga waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya akwai wani abu mai kyau, kuma haƙĩƙa, Lăhira ce mafi alhẽri." Kuma haƙĩƙa, mădalla da gidan măsu taƙawa.

Ayah  16:31  الأية
جَنَّاتُ عَدْنٍ يَدْخُلُونَهَا تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ ۖ لَهُمْ فِيهَا مَا يَشَاءُونَ ۚ كَذَٰلِكَ يَجْزِي اللهُ الْمُتَّقِينَ
Jannatu AAadnin yadkhuloonahatajree min tahtiha al-anharu lahum feehama yashaoona kathalika yajzee Allahualmuttaqeen

Hausa
 
Gidăjen Aljannar zama sună shigarsu, ƙőramu sună gudăna daga ƙarƙashinsu, sună da abin da suke so a cikinsu. Kamar haka Allah ke săkă wa măsu taƙawa.

Ayah  16:32  الأية
الَّذِينَ تَتَوَفَّاهُمُ الْمَلَائِكَةُ طَيِّبِينَ ۙ يَقُولُونَ سَلَامٌ عَلَيْكُمُ ادْخُلُوا الْجَنَّةَ بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Allatheena tatawaffahumu almala-ikatutayyibeena yaqooloona salamun AAalaykumu odkhulooaljannata bima kuntum taAAmaloon

Hausa
 
Waɗanda mală'iku suke karɓar răyukansu sună măsu jin dăɗin rai, mală'ikun sună cẽwa. "Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna sabőda abin da kuka kasance kuna aikatăwa."

Ayah  16:33  الأية
هَلْ يَنظُرُونَ إِلَّا أَن تَأْتِيَهُمُ الْمَلَائِكَةُ أَوْ يَأْتِيَ أَمْرُ رَبِّكَ ۚ كَذَٰلِكَ فَعَلَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ وَمَا ظَلَمَهُمُ اللهُ وَلَٰكِن كَانُوا أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
Hal yanthuroona illa anta/tiyahumu almala-ikatu aw ya/tiya amru rabbika kathalikafaAAala allatheena min qablihim wama thalamahumuAllahu walakin kanoo anfusahum yathlimoon

Hausa
 
Shin sună jiran wani abu? Făce mală'iku su jẽ musu kő kuwa umurnin Ubangijinka. Kamar wancan ne waɗanda suke a gabăninsu, suka aikata. Kuma Allah bai zălunce su ba, kuma amma kansu suka kasance sună zălunta.

Ayah  16:34  الأية
فَأَصَابَهُمْ سَيِّئَاتُ مَا عَمِلُوا وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ
Faasabahum sayyi-atu maAAamiloo wahaqa bihim ma kanoo bihiyastahzi-oon

Hausa
 
Sai mũnănan abũbuwan da suka aikata ya săme su, kuma abin da suka kasance sună yi na izgili ya wajaba a kansu.

Ayah  16:35  الأية
وَقَالَ الَّذِينَ أَشْرَكُوا لَوْ شَاءَ اللهُ مَا عَبَدْنَا مِن دُونِهِ مِن شَيْءٍ نَّحْنُ وَلَا آبَاؤُنَا وَلَا حَرَّمْنَا مِن دُونِهِ مِن شَيْءٍ ۚ كَذَٰلِكَ فَعَلَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ فَهَلْ عَلَى الرُّسُلِ إِلَّا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ
Waqala allatheena ashrakoo lawshaa Allahu ma AAabadna min doonihimin shay-in nahnu wala abaonawala harramna min doonihi min shay-in kathalikafaAAala allatheena min qablihim fahal AAala arrusuliilla albalaghu almubeen

Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi shirki suka ce: "Dă Allah Yă so, dă bamu baută wa kőme ba, baicinSa, mũ ko ubannimmu kuma dă ba mu haramta kőme ba, baicin abin da Ya haramta." Kamar wancan ne waɗanda suke a gabăninsu suka aikata. To, shin, akwai wani abu a kan Manzanni, făce iyarwa bayyananniyă?

Ayah  16:36  الأية
وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَّسُولًا أَنِ اعْبُدُوا اللهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ ۖ فَمِنْهُم مَّنْ هَدَى اللهُ وَمِنْهُم مَّنْ حَقَّتْ عَلَيْهِ الضَّلَالَةُ ۚ فَسِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَانظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُكَذِّبِينَ
Walaqad baAAathna fee kulli ommatinrasoolan ani oAAbudoo Allaha wajtaniboo attaghootafaminhum man hada Allahu waminhum man haqqatAAalayhi addalalatu faseeroo fee al-ardifanthuroo kayfa kana AAaqibatualmukaththibeen

Hausa
 
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kőwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ¦ăgũtu." To, daga gare su akwai wanda Allah Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda ɓata ta wajaba a kansa. Sai ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda ăƙibar măsu ƙaryatăwa ta kasance.

Ayah  16:37  الأية
إِن تَحْرِصْ عَلَىٰ هُدَاهُمْ فَإِنَّ اللهَ لَا يَهْدِي مَن يُضِلُّ ۖ وَمَا لَهُم مِّن نَّاصِرِينَ
In tahris AAala hudahumfa-inna Allaha la yahdee man yudillu wamalahum min nasireen

Hausa
 
Idan ka yi kwaɗayi a kan shiryuwarsu, to, lalle ne, Allah bă Ya shiryar da wanda yake ɓatarwa, kuma bă su da waɗansu mataimaka.

Ayah  16:38  الأية
وَأَقْسَمُوا بِاللهِ جَهْدَ أَيْمَانِهِمْ ۙ لَا يَبْعَثُ اللهُ مَن يَمُوتُ ۚ بَلَىٰ وَعْدًا عَلَيْهِ حَقًّا وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
Waaqsamoo billahi jahda aymanihimla yabAAathu Allahu man yamootu bala waAAdanAAalayhi haqqan walakinna akthara annasila yaAAlamoon

Hausa
 
Kuma suka rantse da Allah iyăkar rantsuwarsu (cẽwa) Allah bă ya tăyar da wanda yake mutuwa! Na'am, Yană tăyarwa. Wa'adi ne (Allah) Ya yi a kanSa tabbatacce, kuma amma mafi yawan mutăne ba su sani ba.

Ayah  16:39  الأية
لِيُبَيِّنَ لَهُمُ الَّذِي يَخْتَلِفُونَ فِيهِ وَلِيَعْلَمَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَنَّهُمْ كَانُوا كَاذِبِينَ
Liyubayyina lahumu allatheeyakhtalifoona feehi waliyaAAlama allatheena kafarooannahum kanoo kathibeen

Hausa
 
Dőmin Ya bayyana musu abin da suke săɓă wa jũna a cikinsa, kuma dőmin waɗanda suka kăfirta su sani cẽwa lalle sũ ne suka kasance maƙaryată.

Ayah  16:40  الأية
إِنَّمَا قَوْلُنَا لِشَيْءٍ إِذَا أَرَدْنَاهُ أَن نَّقُولَ لَهُ كُن فَيَكُونُ
Innama qawluna lishay-inithaaradnahu an naqoola lahu kun fayakoon

Hausa
 
Abin sani kawai, MaganarMu ga wani abu idan Mun nufe shi, Mu ce masa, "Ka kasance; sai yană kasancẽwa.

Ayah  16:41  الأية
وَالَّذِينَ هَاجَرُوا فِي اللهِ مِن بَعْدِ مَا ظُلِمُوا لَنُبَوِّئَنَّهُمْ فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً ۖ وَلَأَجْرُ الْآخِرَةِ أَكْبَرُ ۚ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ
Wallatheena hajaroofee Allahi min baAAdi ma thulimoolanubawwi-annahum fee addunya hasanatanwalaajru al-akhirati akbaru law kanoo yaAAlamoon

Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin sha'anin Allah daga băyan an zălunce su, haƙĩƙa Mună zaunar da su a cikin dũniya da alhẽri kuma lalle lădar Lăhira ce mafi girmă, dă sun kasance sună sani.

Ayah  16:42  الأية
الَّذِينَ صَبَرُوا وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ
Allatheena sabaroo waAAalarabbihim yatawakkaloon

Hausa
 
Waɗanda suka yi haƙuri, kuma ga Ubangijinsu suke dőgara.

Ayah  16:43  الأية
وَمَا أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ إِلَّا رِجَالًا نُّوحِي إِلَيْهِمْ ۚ فَاسْأَلُوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِن كُنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ
Wama arsalna min qablika illarijalan noohee ilayhim fas-aloo ahla aththikriin kuntum la taAAlamoon

Hausa
 
Kuma ba Mu aika daga gabaninka ba, făce waɗansu mazăje Muna yin wahayi zuwa gare su. Sai ku tambayi mutănen Ambato idan kun kasance ba ku sani ba.

Ayah  16:44  الأية
بِالْبَيِّنَاتِ وَالزُّبُرِ ۗ وَأَنزَلْنَا إِلَيْكَ الذِّكْرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيْهِمْ وَلَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ
Bilbayyinati wazzuburiwaanzalna ilayka aththikra litubayyina linnasima nuzzila ilayhim walaAAallahum yatafakkaroon

Hausa
 
Da hujjőji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka, dőmin ka bayyana wa mutăne abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don ɗammăninsu su yi tunăni.

Ayah  16:45  الأية
أَفَأَمِنَ الَّذِينَ مَكَرُوا السَّيِّئَاتِ أَن يَخْسِفَ اللهُ بِهِمُ الْأَرْضَ أَوْ يَأْتِيَهُمُ الْعَذَابُ مِنْ حَيْثُ لَا يَشْعُرُونَ
Afaamina allatheena makaroo assayyi-atian yakhsifa Allahu bihimu al-arda aw ya/tiyahumualAAathabu min haythu la yashAAuroon

Hausa
 
Shin fa, waɗanda suka yi măkircin mũnănan ayyuka sun amince da Allah, bă zai shafe ƙasa da su ba ko kuwa azăba bă ză ta je musu daga inda ba su sani ba?

Ayah  16:46  الأية
أَوْ يَأْخُذَهُمْ فِي تَقَلُّبِهِمْ فَمَا هُم بِمُعْجِزِينَ
Aw ya/khuthahum fee taqallubihim famahum bimuAAjizeen

Hausa
 
Ko kuwa Ya kama su a cikin jujjuyawarsu? Sabőda haka ba su zama masu buwăya ba.

Ayah  16:47  الأية
أَوْ يَأْخُذَهُمْ عَلَىٰ تَخَوُّفٍ فَإِنَّ رَبَّكُمْ لَرَءُوفٌ رَّحِيمٌ
Aw ya/khuthahum AAalatakhawwufin fa-inna rabbakum laraoofun raheem

Hausa
 
Ko kuwa Ya kama su a kan naƙasa? To, lalle ne Ubangijinka haƙĩƙa Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.

Ayah  16:48  الأية
أَوَلَمْ يَرَوْا إِلَىٰ مَا خَلَقَ اللهُ مِن شَيْءٍ يَتَفَيَّأُ ظِلَالُهُ عَنِ الْيَمِينِ وَالشَّمَائِلِ سُجَّدًا لِّلَّهِ وَهُمْ دَاخِرُونَ
Awa lam yaraw ila ma khalaqaAllahu min shay-in yatafayyao thilaluhuAAani alyameeni washshama-ili sujjadan lillahiwahum dakhiroon

Hausa
 
Shin, ba su Iura ba da abin da Allah Ya halitta kő mene ne inuwőyinsu suna karkata daga dăma da wajăjen hagu, suna masu sujada ga Allah, alhăli suna masu ƙasƙantar da kai?

Ayah  16:49  الأية
وَلِلَّهِ يَسْجُدُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ مِن دَابَّةٍ وَالْمَلَائِكَةُ وَهُمْ لَا يَسْتَكْبِرُونَ
Walillahi yasjudu ma fee assamawatiwama fee al-ardi min dabbatin walmala-ikatuwahum la yastakbiroon

Hausa
 
Kuma ga Allah, abin da yake a cikin sammai da ƙasa na dabba da mala'iku, suke yin sujada, kuma bă su kangara.

Ayah  16:50  الأية
يَخَافُونَ رَبَّهُم مِّن فَوْقِهِمْ وَيَفْعَلُونَ مَا يُؤْمَرُونَ ۩
Yakhafoona rabbahum min fawqihimwayafAAaloona ma yu/maroon

Hausa
 
Suna tsőron Ubangijinsu daga bisansu, kuma suna aikata abin da ake umuruin su.

Ayah  16:51  الأية
وَقَالَ اللهُ لَا تَتَّخِذُوا إِلَٰهَيْنِ اثْنَيْنِ ۖ إِنَّمَا هُوَ إِلَٰهٌ وَاحِدٌ ۖ فَإِيَّايَ فَارْهَبُونِ
Waqala Allahu latattakhithoo ilahayni ithnayni innama huwailahun wahidun fa-iyyaya farhaboon

Hausa
 
Kuma Allah Ya ce: "Kada ku riƙi abũbuwan bautăwa biyu. Abin sani kawai, wanda ake bautăwa guda ne, sa'an nan sai kuji tsőroNa, Ni kawai."

Ayah  16:52  الأية
وَلَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَلَهُ الدِّينُ وَاصِبًا ۚ أَفَغَيْرَ اللهِ تَتَّقُونَ
Walahu ma fee assamawatiwal-ardi walahu addeenu wasibanafaghayra Allahi tattaqoon

Hausa
 
Kuma Yana da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, kuma Yana da addini wanda yake dawwamamme. Shin fa, wanin Allah kuke bĩ da taƙăwa?

Ayah  16:53  الأية
وَمَا بِكُم مِّن نِّعْمَةٍ فَمِنَ اللهِ ۖ ثُمَّ إِذَا مَسَّكُمُ الضُّرُّ فَإِلَيْهِ تَجْأَرُونَ
Wama bikum min niAAmatin famina Allahithumma itha massakumu addurru fa-ilayhitaj-aroon

Hausa
 
Kuma abin da yake a gare ku na ni'ima, to, daga Allah ne. Sa'an nan kuma idan cũta ta shăfeku, to, zuwa gare Shi kuke hargőwa.

Ayah  16:54  الأية
ثُمَّ إِذَا كَشَفَ الضُّرَّ عَنكُمْ إِذَا فَرِيقٌ مِّنكُم بِرَبِّهِمْ يُشْرِكُونَ
Thumma itha kashafa addurraAAankum itha fareequn minkum birabbihim yushrikoon

Hausa
 
sa'an nan idan Ya kuranye cũtar daga gare ku, sai gă wani ɓangare daga gare ku game da Ubangijinsu sună shirki.

Ayah  16:55  الأية
لِيَكْفُرُوا بِمَا آتَيْنَاهُمْ ۚ فَتَمَتَّعُوا ۖ فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ
Liyakfuroo bima ataynahumfatamattaAAoo fasawfa taAAlamoon

Hausa
 
Dőmin su kăfirta da abin da Muka bă su. To, ku ji dăɗi, sa'an nan da sannu ză ku sani.

Ayah  16:56  الأية
وَيَجْعَلُونَ لِمَا لَا يَعْلَمُونَ نَصِيبًا مِّمَّا رَزَقْنَاهُمْ ۗ تَاللهِ لَتُسْأَلُنَّ عَمَّا كُنتُمْ تَفْتَرُونَ
WayajAAaloona lima layaAAlamoona naseeban mimma razaqnahum tallahilatus-alunna AAamma kuntum taftaroon

Hausa
 
Kuma sună sanya rabő ga abin da ba su sani ba daga abin da Muka azurtă su. Ranstuwa da Allah! Lalle ne ză a tambaye ku daga abin da kuka kasance kună ƙirƙirăwa.

Ayah  16:57  الأية
وَيَجْعَلُونَ لِلَّهِ الْبَنَاتِ سُبْحَانَهُ ۙ وَلَهُم مَّا يَشْتَهُونَ
WayajAAaloona lillahi albanatisubhanahu walahum ma yashtahoon

Hausa
 
Kuma sună danganta 'ya'ya măta ga Allah. Tsarkinsa yă tabbata! Kuma sũ ne da abin da suke sha'awa.

Ayah  16:58  الأية
وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُم بِالْأُنثَىٰ ظَلَّ وَجْهُهُ مُسْوَدًّا وَهُوَ كَظِيمٌ
Wa-itha bushshira ahaduhum bilonthathalla wajhuhu muswaddan wahuwa katheem

Hausa
 
Kuma idan aka yi wa ɗayansu bushăra da mace sai fuskarsa ta wuni baƙa ƙirin, alhăli kuwa yană mai cike da baƙin ciki.

Ayah  16:59  الأية
يَتَوَارَىٰ مِنَ الْقَوْمِ مِن سُوءِ مَا بُشِّرَ بِهِ ۚ أَيُمْسِكُهُ عَلَىٰ هُونٍ أَمْ يَدُسُّهُ فِي التُّرَابِ ۗ أَلَا سَاءَ مَا يَحْكُمُونَ
Yatawara mina alqawmi minsoo-i ma bushshira bihi ayumsikuhu AAala hoonin amyadussuhu fee atturabi ala saa mayahkumoon

Hausa
 
Yană ɓőyẽwa daga mutăne dőmin mũnin abin da aka yimasa bushăra da shi. Shin, zai riƙe shi a kan wulăkanci kő zai turbuɗe shi a cikin turɓăya To, abin da suke hukuntăwa ya mũnana.

Ayah  16:60  الأية
لِلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ مَثَلُ السَّوْءِ ۖ وَلِلَّهِ الْمَثَلُ الْأَعْلَىٰ ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Lillatheena la yu/minoona bil-akhiratimathalu assaw-i walillahi almathalu al-aAAlawahuwa alAAazeezu alhakeem

Hausa
 
Ga waɗanda ba su yi ĩmăni da Lăhira ba akwai sifar cũta kuma ga Allah akwai sifa mafi ɗaukaka. Kuma shi ne Mabuwăyi, Mai hikima.

Ayah  16:61  الأية
وَلَوْ يُؤَاخِذُ اللهُ النَّاسَ بِظُلْمِهِم مَّا تَرَكَ عَلَيْهَا مِن دَابَّةٍ وَلَٰكِن يُؤَخِّرُهُمْ إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى ۖ فَإِذَا جَاءَ أَجَلُهُمْ لَا يَسْتَأْخِرُونَ سَاعَةً ۖ وَلَا يَسْتَقْدِمُونَ
Walaw yu-akhithu Allahuannasa bithulmihim ma tarakaAAalayha min dabbatin walakin yu-akhkhiruhumila ajalin musamman fa-itha jaa ajaluhum layasta/khiroona saAAatan wala yastaqdimoon

Hausa
 
Kuma dă Allah Yană kăma mutăne da zăluncinsu, dă bai bar wata dabba ba a kan ƙasa. Kuma amma Yană jinkirta musu zuwa ga ajali ambatacce. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, bă ză a yi musu jinkiri ba kő da sa'a guda, kuma bă ză su gabăta ba.

Ayah  16:62  الأية
وَيَجْعَلُونَ لِلَّهِ مَا يَكْرَهُونَ وَتَصِفُ أَلْسِنَتُهُمُ الْكَذِبَ أَنَّ لَهُمُ الْحُسْنَىٰ ۖ لَا جَرَمَ أَنَّ لَهُمُ النَّارَ وَأَنَّهُم مُّفْرَطُونَ
WayajAAaloona lillahi mayakrahoona watasifu alsinatuhumu alkathiba annalahumu alhusna la jarama anna lahumu annarawaannahum mufratoon

Hausa
 
Kuma sună sanyă wa Allah abin da suke ƙi, kuma harsunansu na siffanta ƙarya cẽwa lalle ne sună da abũbuwa măsu kyau. Băbu shakka lalle ne sună da wuta, kuma lalle sũ, waɗanda ake ƙyălẽwa ne (a cikinta) .

Ayah  16:63  الأية
تَاللهِ لَقَدْ أَرْسَلْنَا إِلَىٰ أُمَمٍ مِّن قَبْلِكَ فَزَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَهُوَ وَلِيُّهُمُ الْيَوْمَ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Tallahi laqad arsalnaila omamin min qablika fazayyana lahumu ashshaytanuaAAmalahum fahuwa waliyyuhumu alyawma walahum AAathabunaleem

Hausa
 
Rantsuwar Allah! Lalle ne haƙĩƙa Mun aika zuwa ga al'ummomi daga gabăninka, sai Shaiɗan ya ƙawăce musu ayyukansu, sabőda haka shĩ ne majiɓincinsu, a yau, kuma sună da azăba mai raɗaɗi.

Ayah  16:64  الأية
وَمَا أَنزَلْنَا عَلَيْكَ الْكِتَابَ إِلَّا لِتُبَيِّنَ لَهُمُ الَّذِي اخْتَلَفُوا فِيهِ ۙ وَهُدًى وَرَحْمَةً لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Wama anzalna AAalayka alkitabailla litubayyina lahumu allathee ikhtalafoo feehiwahudan warahmatan liqawmin yu/minoon

Hausa
 
Lalle ba Mu saukar da Littafi ba a kanka, făce dőmin ka bayyană musu abin da suka săɓă wa jũna a cikinsa, kuma dőmin shiriya da rahama ga mutăne waɗanda suke yin ĩmăni.

Ayah  16:65  الأية
وَاللهُ أَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَحْيَا بِهِ الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً لِّقَوْمٍ يَسْمَعُونَ
Wallahu anzala mina assama-imaan faahya bihi al-arda baAAdamawtiha inna fee thalika laayatan liqawminyasmaAAoon

Hausa
 
Kuma Allah Yă saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya răyar da ƙasa da shi a băyan mutuwarta. Lalle ne a cikin wannan haƙĩƙa akwai ăyă ga mutăne waɗanda suke saurăre.

Ayah  16:66  الأية
وَإِنَّ لَكُمْ فِي الْأَنْعَامِ لَعِبْرَةً ۖ نُّسْقِيكُم مِّمَّا فِي بُطُونِهِ مِن بَيْنِ فَرْثٍ وَدَمٍ لَّبَنًا خَالِصًا سَائِغًا لِّلشَّارِبِينَ
Wa-inna lakum fee al-anAAamilaAAibratan nusqeekum mimma fee butoonihi min baynifarthin wadamin labanan khalisan sa-ighan lishsharibeen

Hausa
 
Kuma lalle ne, kună da abin lũra a cikin dabbőbin ni'ima;Mună shăyar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakănin tukar tumbi da jini nőno tsantsan mai sauƙin haɗiya ga măsu shă.

Ayah  16:67  الأية
وَمِن ثَمَرَاتِ النَّخِيلِ وَالْأَعْنَابِ تَتَّخِذُونَ مِنْهُ سَكَرًا وَرِزْقًا حَسَنًا ۗ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ
Wamin thamarati annakheeli wal-aAAnabitattakhithoona minhu sakaran warizqan hasanan innafee thalika laayatan liqawmin yaAAqiloon

Hausa
 
Kuma daga 'ya'yan ităcen dabĩno da inabi. Kună sămudaga gare shi, abin măye da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ăyă ga mutăne waɗanda suke hankalta.

Ayah  16:68  الأية
وَأَوْحَىٰ رَبُّكَ إِلَى النَّحْلِ أَنِ اتَّخِذِي مِنَ الْجِبَالِ بُيُوتًا وَمِنَ الشَّجَرِ وَمِمَّا يَعْرِشُونَ
Waawha rabbuka ila annahliani ittakhithee mina aljibali buyootan wamina ashshajariwamimma yaAArishoon

Hausa
 
Kuma Ubangjinka Yă yi wahayi zuwa ga ƙudan zuma cẽwa: "Ki riƙi gidăje daga duwătsu, kuma daga ităce, kuma daga abin da suke ginăwa."

Ayah  16:69  الأية
ثُمَّ كُلِي مِن كُلِّ الثَّمَرَاتِ فَاسْلُكِي سُبُلَ رَبِّكِ ذُلُلًا ۚ يَخْرُجُ مِن بُطُونِهَا شَرَابٌ مُّخْتَلِفٌ أَلْوَانُهُ فِيهِ شِفَاءٌ لِّلنَّاسِ ۗ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ
Thumma kulee min kulli aththamaratifaslukee subula rabbiki thululan yakhruju min butoonihasharabun mukhtalifun alwanuhu feehi shifaonlinnasi inna fee thalika laayatanliqawmin yatafakkaroon

Hausa
 
"Sa'an nan ki ci daga dukan 'ya'yan ităce, sabőda haka ki shiga hanyőyin Ubangijinka, sună hőrarru." Wani abin shă yană fita daga cikunanta, mai săɓăwar launukansa a cikinsa akwai wata warkewa ga mutăne. Lalle ne, a cikin wannan, haƙĩƙa, akwaiăyőyi ga mutăne waɗanda suke yin tunăni.

Ayah  16:70  الأية
وَاللهُ خَلَقَكُمْ ثُمَّ يَتَوَفَّاكُمْ ۚ وَمِنكُم مَّن يُرَدُّ إِلَىٰ أَرْذَلِ الْعُمُرِ لِكَيْ لَا يَعْلَمَ بَعْدَ عِلْمٍ شَيْئًا ۚ إِنَّ اللهَ عَلِيمٌ قَدِيرٌ
Wallahu khalaqakum thummayatawaffakum waminkum man yuraddu ila arthalialAAumuri likay la yaAAlama baAAda AAilmin shay-an innaAllaha AAaleemun qadeer

Hausa
 
Kuma Allah ne Ya halicce ku, sa'an nan Yană karɓar răyukanku, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwă zuwa ga mafi ƙasƙncin răyuwa, dőmin kada ya san kőme a băyan dă ya zama mai ilmi. Lalle Allah ne Masani Mai ĩkon yi.

Ayah  16:71  الأية
وَاللهُ فَضَّلَ بَعْضَكُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ فِي الرِّزْقِ ۚ فَمَا الَّذِينَ فُضِّلُوا بِرَادِّي رِزْقِهِمْ عَلَىٰ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَهُمْ فِيهِ سَوَاءٌ ۚ أَفَبِنِعْمَةِ اللهِ يَجْحَدُونَ
Wallahu faddala baAAdakumAAala baAAdin fee arrizqi fama allatheenafuddiloo biraddee rizqihim AAala mamalakat aymanuhum fahum feehi sawaon afabiniAAmatiAllahi yajhadoon

Hausa
 
Kuma Allah Ya fifita săshenku a kan săshe a arziki. Sa'an nan waɗanda aka fĩfĩta ba su zama măsu mayar da arzikinsu a kan abin da hannăyensu na dăma suka mallaka ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni'imar Allah suke musu?

Ayah  16:72  الأية
وَاللهُ جَعَلَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا وَجَعَلَ لَكُم مِّنْ أَزْوَاجِكُم بَنِينَ وَحَفَدَةً وَرَزَقَكُم مِّنَ الطَّيِّبَاتِ ۚ أَفَبِالْبَاطِلِ يُؤْمِنُونَ وَبِنِعْمَتِ اللهِ هُمْ يَكْفُرُونَ
Wallahu jaAAala lakum minanfusikum azwajan wajaAAala lakum min azwajikumbaneena wahafadatan warazaqakum mina attayyibatiafabilbatili yu/minoona wabiniAAmati Allahihum yakfuroon

Hausa
 
Kuma Allah Yă sanya muku mătan aure daga kăwunanku, kuma Ya sanya muku daga mătan aurenku ɗiyă da jĩkőki, kuma Ya arzũta ku daga abũbuwa măsu dăɗi. Shin fa, da ƙarya suke yin ĩmăni, kuma da ni'imar Allah sũ, suke kăfirta?

Ayah  16:73  الأية
وَيَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللهِ مَا لَا يَمْلِكُ لَهُمْ رِزْقًا مِّنَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ شَيْئًا وَلَا يَسْتَطِيعُونَ
WayaAAbudoona min dooni Allahi mala yamliku lahum rizqan mina assamawatiwal-ardi shay-an wala yastateeAAoon

Hausa
 
Kuma sună baută wa, baicin Allah, abin da yake bă ya mallakar wani arziki dőminsu, daga sammai da ƙasa game da kőme, kuma bă su iyawa (ga aikata kőme) .

Ayah  16:74  الأية
فَلَا تَضْرِبُوا لِلَّهِ الْأَمْثَالَ ۚ إِنَّ اللهَ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ
Fala tadriboo lillahial-amthala inna Allaha yaAAlamu waantum lataAAlamoon

Hausa
 
Sa'an nan kada ku băyar da waɗansu misălai ga Allah. Lalle ne Allah Yană sani, kuma kũ, ba ku sani ba.

Ayah  16:75  الأية
ضَرَبَ اللهُ مَثَلًا عَبْدًا مَّمْلُوكًا لَّا يَقْدِرُ عَلَىٰ شَيْءٍ وَمَن رَّزَقْنَاهُ مِنَّا رِزْقًا حَسَنًا فَهُوَ يُنفِقُ مِنْهُ سِرًّا وَجَهْرًا ۖ هَلْ يَسْتَوُونَ ۚ الْحَمْدُ لِلَّهِ ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Daraba Allahu mathalan AAabdanmamlookan la yaqdiru AAala shay-in waman razaqnahuminna rizqan hasanan fahuwa yunfiqu minhu sirranwajahran hal yastawoona alhamdu lillahi balaktharuhum la yaAAlamoon

Hausa
 
Allah Yă buga wani misali da wani băwa wanda bă ya iya sămun ĩko a kan yin kőme, da (wani băwa) wanda Muka azurtă shi daga gare Mu da arziki mai kyau. Sa'an nan shĩ yană ciyarwa daga arzikin, a asirce da bayyane. Shin sună daidaita? Gődiya ta tabbata ga Allah. Ă'a mafi yawansu ba su sani ba.

Ayah  16:76  الأية
وَضَرَبَ اللهُ مَثَلًا رَّجُلَيْنِ أَحَدُهُمَا أَبْكَمُ لَا يَقْدِرُ عَلَىٰ شَيْءٍ وَهُوَ كَلٌّ عَلَىٰ مَوْلَاهُ أَيْنَمَا يُوَجِّههُّ لَا يَأْتِ بِخَيْرٍ ۖ هَلْ يَسْتَوِي هُوَ وَمَن يَأْمُرُ بِالْعَدْلِ ۙ وَهُوَ عَلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Wadaraba Allahu mathalanrajulayni ahaduhuma abkamu la yaqdiru AAalashay-in wahuwa kallun AAala mawlahu aynamayuwajjihhu la ya/ti bikhayrin hal yastawee huwa wamanya/muru bilAAadli wahuwa AAala siratinmustaqeem

Hausa
 
Kuma Allah Ya buga wani misăli, maza biyu, ɗayansu bẽbe ne, ba ya iya sămun ikon yin kőme, kuma shi nauyi ne a kan mai mallakarsa, inda duk ya fuskantar da shi, bă ya zuwa da wani alhẽri. Shin, yană daidaita, shi da (namiji na biyu) wanda yake umurni da a yi ădalci kuma yană a kan tafarki madaidaici?

Ayah  16:77  الأية
وَلِلَّهِ غَيْبُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَمَا أَمْرُ السَّاعَةِ إِلَّا كَلَمْحِ الْبَصَرِ أَوْ هُوَ أَقْرَبُ ۚ إِنَّ اللهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Walillahi ghaybu assamawatiwal-ardi wama amru assaAAatiilla kalamhi albasari aw huwa aqrabu innaAllaha AAala kulli shay-in qadeer

Hausa
 
Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake, kuma al'amarin Să'a bai zama ba făce kamar walƙăwar gani, kő kuwa shĩ ne mafi kusa! Lalle Allah a kan dukan kőme Mai ikon yi ne.

Ayah  16:78  الأية
وَاللهُ أَخْرَجَكُم مِّن بُطُونِ أُمَّهَاتِكُمْ لَا تَعْلَمُونَ شَيْئًا وَجَعَلَ لَكُمُ السَّمْعَ وَالْأَبْصَارَ وَالْأَفْئِدَةَ ۙ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Wallahu akhrajakum min butooniommahatikum la taAAlamoona shay-an wajaAAala lakumuassamAAa wal-absara wal-af-idatalaAAallakum tashkuroon

Hausa
 
Kuma Allah ne Ya fitar da ku daga cikunan iyăyenku, ba da kună sanin kőme ba, kuma Ya sanya muku ji da gannai da zukăta, tsammăninku ză ku gőde.

Ayah  16:79  الأية
أَلَمْ يَرَوْا إِلَى الطَّيْرِ مُسَخَّرَاتٍ فِي جَوِّ السَّمَاءِ مَا يُمْسِكُهُنَّ إِلَّا اللهُ ۗ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Alam yaraw ila attayrimusakhkharatin fee jawwi assama-i mayumsikuhunna illa Allahu inna fee thalika laayatinliqawmin yu/minoon

Hausa
 
Shin ba su ga tsuntsăye ba sună hőrarru cikin sararin sama băbu abin da yake riƙe su făce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ăyőyi ga mutăne waɗanda suke yin ĩmăni.

Ayah  16:80  الأية
وَاللهُ جَعَلَ لَكُم مِّن بُيُوتِكُمْ سَكَنًا وَجَعَلَ لَكُم مِّن جُلُودِ الْأَنْعَامِ بُيُوتًا تَسْتَخِفُّونَهَا يَوْمَ ظَعْنِكُمْ وَيَوْمَ إِقَامَتِكُمْ ۙ وَمِنْ أَصْوَافِهَا وَأَوْبَارِهَا وَأَشْعَارِهَا أَثَاثًا وَمَتَاعًا إِلَىٰ حِينٍ
Wallahu jaAAala lakum minbuyootikum sakanan wajaAAala lakum min juloodi al-anAAamibuyootan tastakhiffoonaha yawma thaAAnikumwayawma iqamatikum wamin aswafihawaawbariha waashAAariha athathanwamataAAan ila heen

Hausa
 
Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku daga fatun dabbőbin ni'ima wasu gidăje kună ɗaukar su da sauƙi a rănar tafiyarku da rănar zamanku, kuma daga sũfinsu da găshinsu da gẽzarsu (Allah) Ya sanya muku kăyan ɗăki da na jin dăɗi zuwa ga wani lőƙaci.

Ayah  16:81  الأية
وَاللهُ جَعَلَ لَكُم مِّمَّا خَلَقَ ظِلَالًا وَجَعَلَ لَكُم مِّنَ الْجِبَالِ أَكْنَانًا وَجَعَلَ لَكُمْ سَرَابِيلَ تَقِيكُمُ الْحَرَّ وَسَرَابِيلَ تَقِيكُم بَأْسَكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ يُتِمُّ نِعْمَتَهُ عَلَيْكُمْ لَعَلَّكُمْ تُسْلِمُونَ
Wallahu jaAAala lakum mimmakhalaqa thilalan wajaAAala lakum mina aljibaliaknanan wajaAAala lakum sarabeela taqeekumu alharrawasarabeela taqeekum ba/sakum kathalika yutimmuniAAmatahu AAalaykum laAAallakum tuslimoon

Hausa
 
Kuma Allah ne Ya sanyă muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanyă muku ɗăkuna daga duwătsu, kuma Ya sanyă muku waɗansu riguna sună tsare muku zăfi, da waɗansu rĩguna sună tsare muku makăminku. Kamar wancan ne (Allah) Yake cika ni'imarSa a kanku, tsammănin ku, kuna sallamawa.

Ayah  16:82  الأية
فَإِن تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا عَلَيْكَ الْبَلَاغُ الْمُبِينُ
Fa-in tawallaw fa-innama AAalaykaalbalaghu almubeen

Hausa
 
To, idan sun jũya, to, abin da ya wajaba a kanka, shi ne iyarwă kawai, bayyananniyă.

Ayah  16:83  الأية
يَعْرِفُونَ نِعْمَتَ اللهِ ثُمَّ يُنكِرُونَهَا وَأَكْثَرُهُمُ الْكَافِرُونَ
YaAArifoona niAAmata Allahi thummayunkiroonaha waaktharuhumu alkafiroon

Hausa
 
Suna sanin ni'imar Allah, sa'an nan kuma sună musunta, kuma mafi yawansu kăfirai ne.

Ayah  16:84  الأية
وَيَوْمَ نَبْعَثُ مِن كُلِّ أُمَّةٍ شَهِيدًا ثُمَّ لَا يُؤْذَنُ لِلَّذِينَ كَفَرُوا وَلَا هُمْ يُسْتَعْتَبُونَ
Wayawma nabAAathu min kulli ommatinshaheedan thumma la yu/thanu lillatheenakafaroo wala hum yustaAAtaboon

Hausa
 
Kuma a rănar da Muke tăyar da mai shaida daga kőwace al'umma, sa'an nan kuma bă ză a yi izni ba ga waɗanda suka kăfirta, kuma ba su zama ana nẽman kőmawarsu ba.

Ayah  16:85  الأية
وَإِذَا رَأَى الَّذِينَ ظَلَمُوا الْعَذَابَ فَلَا يُخَفَّفُ عَنْهُمْ وَلَا هُمْ يُنظَرُونَ
Wa-itha raa allatheena thalamooalAAathaba fala yukhaffafu AAanhum wala humyuntharoon

Hausa
 
Kuma idan waɗanda suka yi zălunci suka ga azăba, sa'an nan bă za a saukake ta daga gare su ba, kuma bă su zama ană yi musu jinkiri ba.

Ayah  16:86  الأية
وَإِذَا رَأَى الَّذِينَ أَشْرَكُوا شُرَكَاءَهُمْ قَالُوا رَبَّنَا هَٰؤُلَاءِ شُرَكَاؤُنَا الَّذِينَ كُنَّا نَدْعُو مِن دُونِكَ ۖ فَأَلْقَوْا إِلَيْهِمُ الْقَوْلَ إِنَّكُمْ لَكَاذِبُونَ
Wa-itha raa allatheenaashrakoo shurakaahum qaloo rabbana haola-ishurakaona allatheena kunna nadAAoomin doonika faalqaw ilayhimu alqawla innakum lakathiboon

Hausa
 
Kuma idan waɗanda suka yi shirka suka ga abũbuwan shirkarsu sai su ce: "Yă Ubangijinmu! Waɗannan ne abũbuwanshirkarmu waɗanda muka kasance mună kira baicinKa". Sai su jẽfamagana zuwa gare su, "Lalle ne ku, haƙĩƙa, maƙaryata ne."

Ayah  16:87  الأية
وَأَلْقَوْا إِلَى اللهِ يَوْمَئِذٍ السَّلَمَ ۖ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا يَفْتَرُونَ
Waalqaw ila Allahi yawma-ithinassalama wadalla AAanhum ma kanooyaftaroon

Hausa
 
Kuma su shiga nẽman sulhu zuwa ga Allah a rănar nan, kuma abin da suka kasance sună ƙirƙirăwa ya ɓace daga gare su.

Ayah  16:88  الأية
الَّذِينَ كَفَرُوا وَصَدُّوا عَن سَبِيلِ اللهِ زِدْنَاهُمْ عَذَابًا فَوْقَ الْعَذَابِ بِمَا كَانُوا يُفْسِدُونَ
Allatheena kafaroo wasaddooAAan sabeeli Allahi zidnahum AAathaban fawqaalAAathabi bima kanoo yufsidoon

Hausa
 
Waɗanda suka kăfirta kuma suka kange daga hanyar, Allah, Mun ƙăra musu wata azăba bisa ga azăbar, sabőda abin da suka kasance sună yi na fasădi.

Ayah  16:89  الأية
وَيَوْمَ نَبْعَثُ فِي كُلِّ أُمَّةٍ شَهِيدًا عَلَيْهِم مِّنْ أَنفُسِهِمْ ۖ وَجِئْنَا بِكَ شَهِيدًا عَلَىٰ هَٰؤُلَاءِ ۚ وَنَزَّلْنَا عَلَيْكَ الْكِتَابَ تِبْيَانًا لِّكُلِّ شَيْءٍ وَهُدًى وَرَحْمَةً وَبُشْرَىٰ لِلْمُسْلِمِينَ
Wayawma nabAAathu fee kulli ommatinshaheedan AAalayhim min anfusihim waji/na bika shaheedanAAala haola-i wanazzalna AAalaykaalkitaba tibyanan likulli shay-in wahudan warahmatanwabushra lilmuslimeen

Hausa
 
Kuma a rănar da Muke tăyar da shaidu a cikin kőwace al'umma a kansu daga kăwunansu, kuma Muka zo da kai kană mai băyar da shaida a kan waɗannan, kuma Mun saussaukar da Littăli a kanka dőmin yin băyani ga dukkan kőme da shiriya da rahama da bushăra ga măsu mĩƙa wuya (Musulmi).

Ayah  16:90  الأية
إِنَّ اللهَ يَأْمُرُ بِالْعَدْلِ وَالْإِحْسَانِ وَإِيتَاءِ ذِي الْقُرْبَىٰ وَيَنْهَىٰ عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنكَرِ وَالْبَغْيِ ۚ يَعِظُكُمْ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ
Inna Allaha ya/muru bilAAadliwal-ihsani wa-eeta-i theealqurba wayanha AAani alfahsha-i walmunkariwalbaghyi yaAAithukum laAAallakum tathakkaroon

Hausa
 
Lalle Allah nă yin umurni da ădalci da kyautatăwa, da bai wa ma'abũcin zumunta, kuma yană hani ga alfăsha da abin da aka ƙi da rarrabe jama'a. Yană yi muku gargaɗi, ɗammănin ku, kună tunăwa.

Ayah  16:91  الأية
وَأَوْفُوا بِعَهْدِ اللهِ إِذَا عَاهَدتُّمْ وَلَا تَنقُضُوا الْأَيْمَانَ بَعْدَ تَوْكِيدِهَا وَقَدْ جَعَلْتُمُ اللهَ عَلَيْكُمْ كَفِيلًا ۚ إِنَّ اللهَ يَعْلَمُ مَا تَفْعَلُونَ
Waawfoo biAAahdi Allahi ithaAAahadtum wala tanqudoo al-aymanabaAAda tawkeediha waqad jaAAaltumu Allaha AAalaykumkafeelan inna Allaha yaAAlamu ma tafAAaloon

Hausa
 
Kuma ku cika da alkăwarin Allah idan kun yi alkawari, kuma kada ku warware rantsuwőyinku a băyan ƙarfafa su, alhăli kuma haƙĩƙa kun sanya Allah Mai lămuncẽwa a kanku. Kuma lalle Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatăwa.

Ayah  16:92  الأية
وَلَا تَكُونُوا كَالَّتِي نَقَضَتْ غَزْلَهَا مِن بَعْدِ قُوَّةٍ أَنكَاثًا تَتَّخِذُونَ أَيْمَانَكُمْ دَخَلًا بَيْنَكُمْ أَن تَكُونَ أُمَّةٌ هِيَ أَرْبَىٰ مِنْ أُمَّةٍ ۚ إِنَّمَا يَبْلُوكُمُ اللهُ بِهِ ۚ وَلَيُبَيِّنَنَّ لَكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مَا كُنتُمْ فِيهِ تَخْتَلِفُونَ
Wala takoonoo kallatee naqadatghazlaha min baAAdi quwwatin ankathan tattakhithoonaaymanakum dakhalan baynakum an takoona ommatun hiya arbamin ommatin innama yablookumu Allahu bihiwalayubayyinanna lakum yawma alqiyamati ma kuntumfeehi takhtalifoon

Hausa
 
Kuma kada ku kasance kamar wadda ta warware zarenta a băyan tukka, ya zama warwararku, kună riƙon rantsuwőyinku dőmin yaudara a tsakăninku, dőmin kasancẽwar wata al'umma tăfi rĩba daga wata al'umma! Abin sani kawai Allah Yană jarrabar ku da shi, kuma lalle ne yană bayyana muku a Rănar ˇiyăma, abin da kuka kasance, a cikinsa, kună săɓă wajũna.

Ayah  16:93  الأية
وَلَوْ شَاءَ اللهُ لَجَعَلَكُمْ أُمَّةً وَاحِدَةً وَلَٰكِن يُضِلُّ مَن يَشَاءُ وَيَهْدِي مَن يَشَاءُ ۚ وَلَتُسْأَلُنَّ عَمَّا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Walaw shaa Allahu lajaAAalakumommatan wahidatan walakin yudillu man yashaowayahdee man yashao walatus-alunna AAamma kuntumtaAAmaloon

Hausa
 
Kuma dă Allah Ya so, haƙĩ ƙa, dă Ya sanya ku al'umma gudă, kuma Yană ɓatar da wanda Ya so. kuma Yană shiryar da wanda Ya so. Lalle ne ană tambayarku abin da kuka kasance kună aikatăwa.

Ayah  16:94  الأية
وَلَا تَتَّخِذُوا أَيْمَانَكُمْ دَخَلًا بَيْنَكُمْ فَتَزِلَّ قَدَمٌ بَعْدَ ثُبُوتِهَا وَتَذُوقُوا السُّوءَ بِمَا صَدَدتُّمْ عَن سَبِيلِ اللهِ ۖ وَلَكُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Wala tattakhithoo aymanakumdakhalan baynakum fatazilla qadamun baAAda thubootiha watathooqooassoo-a bima sadadtum AAan sabeeli Allahiwalakum AAathabun AAatheem

Hausa
 
Kada ku riƙi rantsuwőyinku dőmin yaudara a tsakăninku, har ƙafa ta yi sulɓi a băyan tabbatarta, kuma ku ɗanɗani azăba sabőda abin da kuka kange daga hanyar Allah. Kuma kună da wata azăba mai girma.

Ayah  16:95  الأية
وَلَا تَشْتَرُوا بِعَهْدِ اللهِ ثَمَنًا قَلِيلًا ۚ إِنَّمَا عِندَ اللهِ هُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Wala tashtaroo biAAahdi Allahithamanan qaleelan innama AAinda Allahi huwa khayrunlakum in kuntum taAAlamoon

Hausa
 
Kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da alkawarin Allah. Lalle ne abin da yake a wurin Allah shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kună sani.

Ayah  16:96  الأية
مَا عِندَكُمْ يَنفَدُ ۖ وَمَا عِندَ اللهِ بَاقٍ ۗ وَلَنَجْزِيَنَّ الَّذِينَ صَبَرُوا أَجْرَهُم بِأَحْسَنِ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Ma AAindakum yanfadu wamaAAinda Allahi baqin walanajziyanna allatheenasabaroo ajrahum bi-ahsani ma kanooyaAAmaloon

Hausa
 
Abin da yake a wurinku yană ƙărẽwa, kuma abin da yake a wurin Allah ne mai wanzuwă. Kuma lalle ne, Mună săka wa waɗanda suka yi haƙuri da lădarsu da mafi kyăwun abin da suka kasance sună aikatăwa.

Ayah  16:97  الأية
مَنْ عَمِلَ صَالِحًا مِّن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَنُحْيِيَنَّهُ حَيَاةً طَيِّبَةً ۖ وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَجْرَهُم بِأَحْسَنِ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Man AAamila salihan min thakarinaw ontha wahuwa mu/minun falanuhyiyannahu hayatantayyibatan walanajziyannahum ajrahum bi-ahsani makanoo yaAAmaloon

Hausa
 
Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kő kuwa mace, alhăli yană mũmini, to, haƙĩƙa Mună răyar da shi, răyuwa mai dăɗi. Kuma haƙĩƙa Mună săkă musu lădarsu da mafi kyăwun abin da suka kasance sună aikatăwa.

Ayah  16:98  الأية
فَإِذَا قَرَأْتَ الْقُرْآنَ فَاسْتَعِذْ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ
Fa-itha qara/ta alqur-ana fastaAAithbillahi mina ashshaytani arrajeem

Hausa
 
Sa'an nan idan ka karantă Alƙur'ăni, sai ka nẽmi tsari ga Allah daga shaiɗan jẽfaffe.

Ayah  16:99  الأية
إِنَّهُ لَيْسَ لَهُ سُلْطَانٌ عَلَى الَّذِينَ آمَنُوا وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ
Innahu laysa lahu sultanun AAalaallatheena amanoo waAAala rabbihimyatawakkaloon

Hausa
 
Lalle ne shi, bă shi da wani ƙarfi a kan waɗanda suka yi ĩmăni, kuma sună dőgara ga Ubangijinsu.

Ayah  16:100  الأية
إِنَّمَا سُلْطَانُهُ عَلَى الَّذِينَ يَتَوَلَّوْنَهُ وَالَّذِينَ هُم بِهِ مُشْرِكُونَ
Innama sultanuhu AAalaallatheena yatawallawnahu wallatheena humbihi mushrikoon

Hausa
 
Abin sani kawai ƙarfinsa yană a kan waɗanda suke jiɓintar sa, kuma waɗanda suke sũ, game da shi, măsu shirki ne.

Ayah  16:101  الأية
وَإِذَا بَدَّلْنَا آيَةً مَّكَانَ آيَةٍ ۙ وَاللهُ أَعْلَمُ بِمَا يُنَزِّلُ قَالُوا إِنَّمَا أَنتَ مُفْتَرٍ ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Wa-itha baddalna ayatanmakana ayatin wallahu aAAlamu bimayunazzilu qaloo innama anta muftarin bal aktharuhumla yaAAlamoon

Hausa
 
Kuma idan Muka musanya wata ăyă a matsayin wata ăyă, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da Yake saukarwa sai su ce: "Abin sani kawai, kai, aƙirƙiri ne." Ă'a, mafi yawansu bă swa sani.

Ayah  16:102  الأية
قُلْ نَزَّلَهُ رُوحُ الْقُدُسِ مِن رَّبِّكَ بِالْحَقِّ لِيُثَبِّتَ الَّذِينَ آمَنُوا وَهُدًى وَبُشْرَىٰ لِلْمُسْلِمِينَ
Qul nazzalahu roohu alqudusi minrabbika bilhaqqi liyuthabbita allatheena amanoowahudan wabushra lilmuslimeen

Hausa
 
Ka ce: "Rũhul ˇudusi ne ya sassaukar da shi, daga Ubangijinka da gaskiya, dőmin ya tabbatar da waɗanda suka yi ĩmăni, kuma(dőmin) shiriya da bushăra ga Musulmi."

Ayah  16:103  الأية
وَلَقَدْ نَعْلَمُ أَنَّهُمْ يَقُولُونَ إِنَّمَا يُعَلِّمُهُ بَشَرٌ ۗ لِّسَانُ الَّذِي يُلْحِدُونَ إِلَيْهِ أَعْجَمِيٌّ وَهَٰذَا لِسَانٌ عَرَبِيٌّ مُّبِينٌ
Walaqad naAAlamu annahum yaqooloona innamayuAAallimuhu basharun lisanu allathee yulhidoonailayhi aAAjamiyyun wahatha lisanun AAarabiyyunmubeen

Hausa
 
Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mună sanin (cẽwa) lalle ne sũ, sună cẽwa, "Abin sani kawai wani mutum ne yake karantar da shi." Harshen wanda suke karkatai da maganar zuwa gare shi, Ba'ajame ne, kuma wannan (Alƙur'ăni) harshe ne Balărabe bayyananne.

Ayah  16:104  الأية
إِنَّ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِآيَاتِ اللهِ لَا يَهْدِيهِمُ اللهُ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Inna allatheena la yu/minoonabi-ayati Allahi la yahdeehimu Allahuwalahum AAathabun aleem

Hausa
 
Lalle ne waɗanda bă su yin ĩmăni da ăyőyin Allah, Allahbă zai shiryar da su ba, kuma sună da azăba mai raɗaɗi.

Ayah  16:105  الأية
إِنَّمَا يَفْتَرِي الْكَذِبَ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِآيَاتِ اللهِ ۖ وَأُولَٰئِكَ هُمُ الْكَاذِبُونَ
Innama yaftaree alkathibaallatheena la yu/minoona bi-ayati Allahiwaola-ika humu alkathiboon

Hausa
 
Abin sani kawai waɗanda bă su yin ĩmăni da ăyőyin Allah, sũ ne suke ƙirƙira ƙarya. Kuma waɗannan sũ ne maƙaryata.

Ayah  16:106  الأية
مَن كَفَرَ بِاللهِ مِن بَعْدِ إِيمَانِهِ إِلَّا مَنْ أُكْرِهَ وَقَلْبُهُ مُطْمَئِنٌّ بِالْإِيمَانِ وَلَٰكِن مَّن شَرَحَ بِالْكُفْرِ صَدْرًا فَعَلَيْهِمْ غَضَبٌ مِّنَ اللهِ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Man kafara billahi minbaAAdi eemanihi illa man okriha waqalbuhu mutma-innunbil-eemani walakin man sharaha bilkufrisadran faAAalayhim ghadabun mina Allahiwalahum AAathabun AAatheem

Hausa
 
Wanda ya kăfirta da Allah daga băyan ĩmăninsa, făce wanda aka tĩlasta alhăli kuwa zũciyarsa tană natse da ĩmăni kuma wanda ya yi farin ciki da kăfirci, to, akwai fushi a kansa daga Allah, kuma sună da wata azăba mai girma.

Ayah  16:107  الأية
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ اسْتَحَبُّوا الْحَيَاةَ الدُّنْيَا عَلَى الْآخِرَةِ وَأَنَّ اللهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْكَافِرِينَ
Thalika bi-annahumu istahabbooalhayata addunya AAala al-akhiratiwaanna Allaha la yahdee alqawma alkafireen

Hausa
 
Waɗancan ne kăfirai dőmin sun fĩfĩta son dũniya a kan Lăhira, kuma lalle ne Allah bă Ya shiryar da mutăne kăfirai.

Ayah  16:108  الأية
أُولَٰئِكَ الَّذِينَ طَبَعَ اللهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ وَسَمْعِهِمْ وَأَبْصَارِهِمْ ۖ وَأُولَٰئِكَ هُمُ الْغَافِلُونَ
Ola-ika allatheena tabaAAaAllahu AAala quloobihim wasamAAihim waabsarihimwaola-ika humu alghafiloon

Hausa
 
Waɗancan ne waɗanda Allah Ya bice hasken zukătansu da jinsu da gannansu. Kuma waɗancan sũ ne gafalallu.

Ayah  16:109  الأية
لَا جَرَمَ أَنَّهُمْ فِي الْآخِرَةِ هُمُ الْخَاسِرُونَ
La jarama annahum fee al-akhiratihumu alkhasiroon

Hausa
 
Băbu shakka lalle ne a Lăhira sũ ne măsu hasăra.

Ayah  16:110  الأية
ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ هَاجَرُوا مِن بَعْدِ مَا فُتِنُوا ثُمَّ جَاهَدُوا وَصَبَرُوا إِنَّ رَبَّكَ مِن بَعْدِهَا لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ
Thumma inna rabbaka lillatheena hajaroomin baAAdi ma futinoo thumma jahadoo wasabarooinna rabbaka min baAAdiha laghafoorun raheem

Hausa
 
Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka yi hijiră daga băyan an fitine su, sa'an nan kuma suka yi jihădi, kuma suka yi haƙuri, lalle ne Ubangijinka, daga băyanta haƙĩƙa Mai găfara ne, Mai jin ƙai.

Ayah  16:111  الأية
يَوْمَ تَأْتِي كُلُّ نَفْسٍ تُجَادِلُ عَن نَّفْسِهَا وَتُوَفَّىٰ كُلُّ نَفْسٍ مَّا عَمِلَتْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ
Yawma ta/tee kullu nafsin tujadiluAAan nafsiha watuwaffa kullu nafsin maAAamilat wahum la yuthlamoon

Hausa
 
A rănar da kőwane rai zai je yană jăyayyar tunkuɗẽwa daga kansa, kuma a cika wa kőwane rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma sũ bă ză a zălunce su ba.

Ayah  16:112  الأية
وَضَرَبَ اللهُ مَثَلًا قَرْيَةً كَانَتْ آمِنَةً مُّطْمَئِنَّةً يَأْتِيهَا رِزْقُهَا رَغَدًا مِّن كُلِّ مَكَانٍ فَكَفَرَتْ بِأَنْعُمِ اللهِ فَأَذَاقَهَا اللهُ لِبَاسَ الْجُوعِ وَالْخَوْفِ بِمَا كَانُوا يَصْنَعُونَ
Wadaraba Allahu mathalanqaryatan kanat aminatan mutma-innatanya/teeha rizquha raghadan min kulli makaninfakafarat bi-anAAumi Allahi faathaqaha Allahulibasa aljooAAi walkhawfi bima kanooyasnaAAoon

Hausa
 
Kuma Allah Ya buga misăli, wata alƙarya ta kasance amintacciyă, natsattsiyă, arzikinta yană je mata a wadăce daga kőwane wuri sai ta kăfirta da ni'imőmin Allah, sabőda haka Allah ya ɗanɗana mata tufăfin yunwa da tsőro, sabőda abin da suka kasance sună sană'antăwa.

Ayah  16:113  الأية
وَلَقَدْ جَاءَهُمْ رَسُولٌ مِّنْهُمْ فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمُ الْعَذَابُ وَهُمْ ظَالِمُونَ
Walaqad jaahum rasoolun minhum fakaththaboohufaakhathahumu alAAathabu wahum thalimoon

Hausa
 
Kuma lalle ne haƙĩƙa wani Manzo daga gare su, ya jẽmusu, sai suka ƙaryata shi, sabőda haka azăba ta kăma su, alhăli kuwa sũ ne măsu zălunci.

Ayah  16:114  الأية
فَكُلُوا مِمَّا رَزَقَكُمُ اللهُ حَلَالًا طَيِّبًا وَاشْكُرُوا نِعْمَتَ اللهِ إِن كُنتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ
Fakuloo mimma razaqakumu Allahuhalalan tayyiban washkuroo niAAmataAllahi in kuntum iyyahu taAAbudoon

Hausa
 
Sa'an nan ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku da shi, halas, kuma mai dăɗi, kuma ku gőde wa ni'imar Allah idan kun kasance shi kuke bautăwa.

Ayah  16:115  الأية
إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيْكُمُ الْمَيْتَةَ وَالدَّمَ وَلَحْمَ الْخِنزِيرِ وَمَا أُهِلَّ لِغَيْرِ اللهِ بِهِ ۖ فَمَنِ اضْطُرَّ غَيْرَ بَاغٍ وَلَا عَادٍ فَإِنَّ اللهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Innama harrama AAalaykumualmaytata waddama walahma alkhinzeeri wamaohilla lighayri Allahi bihi famani idturra ghayra baghinwala AAadin fa-inna Allaha ghafoorun raheem

Hausa
 
Abin sani kawai (Allah) Ya haramta muku mussai da jini da năman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan jama'a kuma baicin mai zălunci, to, lalle Allah ne Mai găfara, Mai jin ƙai.

Ayah  16:116  الأية
وَلَا تَقُولُوا لِمَا تَصِفُ أَلْسِنَتُكُمُ الْكَذِبَ هَٰذَا حَلَالٌ وَهَٰذَا حَرَامٌ لِّتَفْتَرُوا عَلَى اللهِ الْكَذِبَ ۚ إِنَّ الَّذِينَ يَفْتَرُونَ عَلَى اللهِ الْكَذِبَ لَا يُفْلِحُونَ
Wala taqooloo lima tasifualsinatukumu alkathiba hatha halalunwahatha haramun litaftaroo AAala Allahialkathiba inna allatheena yaftaroona AAalaAllahi alkathiba la yuflihoon

Hausa
 
Kuma kada ku ce, dőmin abin da harsunanku suke siffantawa da ƙarya, "Wannan halas ne, kuma wannan harămun ne." Dőmin ku ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne, waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah bă ză su ci nasara ba.

Ayah  16:117  الأية
مَتَاعٌ قَلِيلٌ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
MataAAun qaleelun walahum AAathabunaleem

Hausa
 
Jin dăɗi ne kaɗan. Kuma sună da wata azăba mai raɗaɗi.

Ayah  16:118  الأية
وَعَلَى الَّذِينَ هَادُوا حَرَّمْنَا مَا قَصَصْنَا عَلَيْكَ مِن قَبْلُ ۖ وَمَا ظَلَمْنَاهُمْ وَلَٰكِن كَانُوا أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
WaAAala allatheena hadooharramna ma qasasnaAAalayka min qablu wama thalamnahumwalakin kanoo anfusahum yathlimoon

Hausa
 
Kuma kan waɗanda suka tũba (Yăhũdu) Mun haramta abin da Muka băyar da lăbari a gare ka daga gabăni, kuma ba Mu zălunce su ba, amma sun kasance kansu suke zălunta.

Ayah  16:119  الأية
ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ عَمِلُوا السُّوءَ بِجَهَالَةٍ ثُمَّ تَابُوا مِن بَعْدِ ذَٰلِكَ وَأَصْلَحُوا إِنَّ رَبَّكَ مِن بَعْدِهَا لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ
Thumma inna rabbaka lillatheenaAAamiloo assoo-a bijahalatin thumma taboomin baAAdi thalika waaslahoo inna rabbakamin baAAdiha laghafoorun raheem

Hausa
 
Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki da jăhilci, sa'an nan suka tũba daga băyan wancan, kuma suka gyăra, lalle ne Ubangijinka, daga băyanta haƙĩƙa Mai găfara ne, Mai jin ƙai.

Ayah  16:120  الأية
إِنَّ إِبْرَاهِيمَ كَانَ أُمَّةً قَانِتًا لِّلَّهِ حَنِيفًا وَلَمْ يَكُ مِنَ الْمُشْرِكِينَ
Inna ibraheema kana ommatan qanitanlillahi haneefan walam yaku mina almushrikeen

Hausa
 
Lalle ne Ibrăhĩm ya kasance shũgaba, mai ƙasƙantar da kai ga Allah, mai karkată zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga măsu shirki ba.

Ayah  16:121  الأية
شَاكِرًا لِّأَنْعُمِهِ ۚ اجْتَبَاهُ وَهَدَاهُ إِلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Shakiran li-anAAumihi ijtabahuwahadahu ila siratin mustaqeem

Hausa
 
Mai gődiya ga ni'imominSa (Allah), Ya zăɓe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici.

Ayah  16:122  الأية
وَآتَيْنَاهُ فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً ۖ وَإِنَّهُ فِي الْآخِرَةِ لَمِنَ الصَّالِحِينَ
Waataynahu fee addunyahasanatan wa-innahu fee al-akhirati lamina assaliheen

Hausa
 
Kuma Muka ba shi alhẽri a cikin dũniya, Kuma lalle shĩ, a Lăhira, yană daga sălihai.

Ayah  16:123  الأية
ثُمَّ أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ أَنِ اتَّبِعْ مِلَّةَ إِبْرَاهِيمَ حَنِيفًا ۖ وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ
Thumma awhayna ilayka aniittabiAA millata ibraheema haneefan wama kanamina almushrikeen

Hausa
 
Sa'an nan kuma Muka yi wahayi zuwa gare ka (cẽwa), "Ka bi aƙĩdar Ibrahĩm, mai karkată zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga măsu shirki ba.'

Ayah  16:124  الأية
إِنَّمَا جُعِلَ السَّبْتُ عَلَى الَّذِينَ اخْتَلَفُوا فِيهِ ۚ وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَحْكُمُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِيمَا كَانُوا فِيهِ يَخْتَلِفُونَ
Innama juAAila assabtu AAalaallatheena ikhtalafoo feehi wa-inna rabbaka layahkumubaynahum yawma alqiyamati feema kanoo feehiyakhtalifoon

Hausa
 
Abin sani kawai, an sanya Asabar a kan waɗanda suka săɓă wajũna a cikin sha'aninsa. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa,Yană yin hukunci a tsakaninsu a Rănar ˇiyăma a cikin abin da suka kasance a cikinsa sună săɓă wa jũnă.

Ayah  16:125  الأية
ادْعُ إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِالْحِكْمَةِ وَالْمَوْعِظَةِ الْحَسَنَةِ ۖ وَجَادِلْهُم بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ ۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِ ۖ وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ
OdAAu ila sabeeli rabbika bilhikmatiwalmawAAithati alhasanati wajadilhumbillatee hiya ahsanu inna rabbaka huwa aAAlamubiman dalla AAan sabeelihi wahuwa aAAlamu bilmuhtadeen

Hausa
 
Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyau kuma ka yi jăyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓăce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga măsu shiryuwa.

Ayah  16:126  الأية
وَإِنْ عَاقَبْتُمْ فَعَاقِبُوا بِمِثْلِ مَا عُوقِبْتُم بِهِ ۖ وَلَئِن صَبَرْتُمْ لَهُوَ خَيْرٌ لِّلصَّابِرِينَ
Wa-in AAaqabtum faAAaqiboobimithli ma AAooqibtum bihi wala-in sabartum lahuwakhayrun lissabireen

Hausa
 
Kuma idan kuka săka wa uƙũba to ku săka wa uƙũba da misălin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhẽri ga măsu haƙuri.

Ayah  16:127  الأية
وَاصْبِرْ وَمَا صَبْرُكَ إِلَّا بِاللهِ ۚ وَلَا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَلَا تَكُ فِي ضَيْقٍ مِّمَّا يَمْكُرُونَ
Wasbir wama sabrukailla billahi wala tahzanAAalayhim wala taku fee dayqin mimmayamkuroon

Hausa
 
Kuma ka yi haƙuri, kuma haƙurinka bă zai zama ba făce dőmin Allah, kuma kada ka yi baƙin ciki sabo da su, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke yi na măkirci.

Ayah  16:128  الأية
إِنَّ اللهَ مَعَ الَّذِينَ اتَّقَوا وَّالَّذِينَ هُم مُّحْسِنُونَ
Inna Allaha maAAa allatheenaittaqaw wallatheena hum muhsinoon

Hausa
 
Lalle Allah Yană tăre da waɗanda suka yi taƙawa da waɗanda suke sũ măsu kyautatăwa ne. 





© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us