1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
سُورَةٌ أَنزَلْنَاهَا وَفَرَضْنَاهَا وَأَنزَلْنَا فِيهَا آيَاتٍ بَيِّنَاتٍ
لَّعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ
Sooratun anzalnaha wafaradnahawaanzalna feeha ayatin bayyinatinlaAAallakum
tathakkaroon
Hausa
(Wannan) sũra ce. Mun saukar da ita, kuma Mun wajabta ta, kuma Mun saukar da
ăyőyi bayyanannu a cikinta, dőmin ku riƙa tunăwa.
|
Ayah 24:2 الأية
الزَّانِيَةُ وَالزَّانِي فَاجْلِدُوا كُلَّ وَاحِدٍ مِّنْهُمَا مِائَةَ جَلْدَةٍ ۖ
وَلَا تَأْخُذْكُم بِهِمَا رَأْفَةٌ فِي دِينِ اللهِ إِن كُنتُمْ تُؤْمِنُونَ
بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ۖ وَلْيَشْهَدْ عَذَابَهُمَا طَائِفَةٌ مِّنَ
الْمُؤْمِنِينَ
Azzaniyatu wazzaneefajlidoo kulla wahidin minhuma mi-atajaldatin wala
ta/khuthkum bihima ra/fatunfee deeni Allahi in kuntum tu/minoona billahiwalyawmi
al-akhiri walyashhad AAathabahumata-ifatun mina almu/mineen
Hausa
Mazinăciya da mazinăci, to, ku yi bũlăla ga kőwane ɗaya daga gare su, bũlăla
ɗari. Kuma kada tausayi ya kăma ku game da su a cikin addinin Allah idan kun
kasance kună yin ĩmăni da Allah da Rănar Lăhira. Kuma wani yankin jama, a daga
mũminai, su halarci azăbarsu.
|
Ayah 24:3 الأية
الزَّانِي لَا يَنكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوْ مُشْرِكَةً وَالزَّانِيَةُ لَا
يَنكِحُهَا إِلَّا زَانٍ أَوْ مُشْرِكٌ ۚ وَحُرِّمَ ذَٰلِكَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ
Azzanee la yankihuilla zaniyatan aw mushrikatan wazzaniyatula yankihuha illa
zanin awmushrikun wahurrima thalika AAalaalmu/mineen
Hausa
Mazinăci bă ya aure făce da mazinăciya kő mushirika, kuma mazinăciya băbu mai
aurenta făce mazinăci kő mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan mũminai.
|
Ayah 24:4 الأية
وَالَّذِينَ يَرْمُونَ الْمُحْصَنَاتِ ثُمَّ لَمْ يَأْتُوا بِأَرْبَعَةِ شُهَدَاءَ
فَاجْلِدُوهُمْ ثَمَانِينَ جَلْدَةً وَلَا تَقْبَلُوا لَهُمْ شَهَادَةً أَبَدًا ۚ
وَأُولَٰئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ
Wallatheena yarmoona almuhsanatithumma lam ya/too bi-arbaAAati shuhadaa
fajlidoohumthamaneena jaldatan wala taqbaloo lahum shahadatanabadan waola-ika
humu alfasiqoon
Hausa
Kuma waɗanda ke jĩfar mătă masu kămun kai, sa'an nan kuma ba su jẽ da shaidu
huɗu ba to, ku yi musu bũlăla, bũlăla tamănin, kuma kada ku karɓi wata shaida
tăsu, har abada. Waɗancan su ne făsiƙai.
|
Ayah 24:5 الأية
إِلَّا الَّذِينَ تَابُوا مِن بَعْدِ ذَٰلِكَ وَأَصْلَحُوا فَإِنَّ اللهَ غَفُورٌ
رَّحِيمٌ
Illa allatheena taboomin baAAdi thalika waaslahoo fa-inna Allahaghafoorun raheem
Hausa
Făce waɗanda suka tũbadaga băyan wannan, kuma suka gyăru, to lalle ne Allah Mai
găfara ne, Mai jin ƙai.
|
Ayah 24:6 الأية
وَالَّذِينَ يَرْمُونَ أَزْوَاجَهُمْ وَلَمْ يَكُن لَّهُمْ شُهَدَاءُ إِلَّا
أَنفُسُهُمْ فَشَهَادَةُ أَحَدِهِمْ أَرْبَعُ شَهَادَاتٍ بِاللهِ ۙ إِنَّهُ
لَمِنَ الصَّادِقِينَ
Wallatheena yarmoona azwajahumwalam yakun lahum shuhadao illa anfusuhum
fashahadatuahadihim arbaAAu shahadatin billahiinnahu lamina assadiqeen
Hausa
Kuma waɗanda ke jĩfar mătan aurensu kuma waɗansu shaidu ba su kasance a gare su
ba, făce dai kansu, to, shaidar ɗayansu, shaida huɗu ce da Allah, 'Lalle shĩ,
haƙĩƙa, yană daga magasganta.'
|
Ayah 24:7 الأية
وَالْخَامِسَةُ أَنَّ لَعْنَتَ اللهِ عَلَيْهِ إِن كَانَ مِنَ الْكَاذِبِينَ
Walkhamisatu anna laAAnata AllahiAAalayhi in kana mina alkathibeen
Hausa
Kuma ta biyar cẽwa 'La'anar Allah ta tabbata a kansa, idan ya kasance daga
maƙaryata.'
|
Ayah 24:8 الأية
وَيَدْرَأُ عَنْهَا الْعَذَابَ أَن تَشْهَدَ أَرْبَعَ شَهَادَاتٍ بِاللهِ ۙ
إِنَّهُ لَمِنَ الْكَاذِبِينَ
Wayadrao AAanha alAAathaba antashhada arbaAAa shahadatin billahiinnahu lamina
alkathibeen
Hausa
Kuma yană tunkuɗe mata azăba ta yi shaida, shaida huɗu da Allah, 'Lalle shĩ
haƙĩƙa, yană daga maƙaryata.'
|
Ayah 24:9 الأية
وَالْخَامِسَةَ أَنَّ غَضَبَ اللهِ عَلَيْهَا إِن كَانَ مِنَ الصَّادِقِينَ
Walkhamisata anna ghadabaAllahi AAalayha in kana mina assadiqeen
Hausa
Kuma tă biyar cẽwa 'Hushin Allah ya tabbata a kanta idan ya kasance daga
magasganta.'
|
Ayah 24:10 الأية
وَلَوْلَا فَضْلُ اللهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ وَأَنَّ اللهَ تَوَّابٌ
حَكِيمٌ
Walawla fadlu AllahiAAalaykum warahmatuhu waanna Allaha tawwabunhakeem
Hausa
Kuma bă dőmin falalar Allah ba a kanku, da rahamarSa, kuma cẽwa Allah Mai karɓar
tũba ne, Mai hikima!
|
Ayah 24:11 الأية
إِنَّ الَّذِينَ جَاءُوا بِالْإِفْكِ عُصْبَةٌ مِّنكُمْ ۚ لَا تَحْسَبُوهُ شَرًّا
لَّكُم ۖ بَلْ هُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ ۚ لِكُلِّ امْرِئٍ مِّنْهُم مَّا اكْتَسَبَ مِنَ
الْإِثْمِ ۚ وَالَّذِي تَوَلَّىٰ كِبْرَهُ مِنْهُمْ لَهُ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Inna allatheena jaoo bil-ifkiAAusbatun minkum la tahsaboohu sharran lakumbal
huwa khayrun lakum likulli imri-in minhum ma iktasabamina al-ithmi wallathee
tawalla kibrahuminhum lahu AAathabun AAatheem
Hausa
Lalle ne waɗanda suka zo da ƙiren ƙarya waɗansu jama'a ne daga gare ku, kada ku
yi zatonsa sharri ne a gare ku. Ă'a, alhẽri ne gare ku. Kőwane mutum daga gare
su na da sakamakon abin da ya sană'anta na zunubi, kuma wanda ya jiɓinci
girmansa, daga gare su, yană da azăba mai girma.
|
Ayah 24:12 الأية
لَّوْلَا إِذْ سَمِعْتُمُوهُ ظَنَّ الْمُؤْمِنُونَ وَالْمُؤْمِنَاتُ بِأَنفُسِهِمْ
خَيْرًا وَقَالُوا هَٰذَا إِفْكٌ مُّبِينٌ
Lawla ith samiAAtumoohu thannaalmu/minoona walmu/minatu bi-anfusihim khayran
waqaloohatha ifkun mubeen
Hausa
Don me a lőkacin da kuka ji shi mũminai maza da mũminai măta ba su yi zaton
alhẽri game da kansu ba kuma su ce: "Wannan ƙiren ƙarya ne bayyananne?"
|
Ayah 24:13 الأية
لَّوْلَا جَاءُوا عَلَيْهِ بِأَرْبَعَةِ شُهَدَاءَ ۚ فَإِذْ لَمْ يَأْتُوا
بِالشُّهَدَاءِ فَأُولَٰئِكَ عِندَ اللهِ هُمُ الْكَاذِبُونَ
Lawla jaoo AAalayhibi-arbaAAati shuhadaa fa-ith lam ya/too
bishshuhada-ifaola-ika AAinda Allahi humu alkathiboon
Hausa
Don me ba su zo da shaidu huɗu a kansa ba? To idan ba su kăwo shaidun nan ba to,
waɗannan, a wurin Allah, sũ ne maƙaryata.
|
Ayah 24:14 الأية
وَلَوْلَا فَضْلُ اللهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ
لَمَسَّكُمْ فِي مَا أَفَضْتُمْ فِيهِ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Walawla fadlu AllahiAAalaykum warahmatuhu fee addunya wal-akhiratilamassakum fee
ma afadtum feehi AAathabunAAatheem
Hausa
Kuma bă dőmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa a cikin dũniya da Lăhira.
Lalle ne,dă azăba mai girma ta shăfe ku a cikin abin da kuka kũtsa da magana a
cikinsa.
|
Ayah 24:15 الأية
إِذْ تَلَقَّوْنَهُ بِأَلْسِنَتِكُمْ وَتَقُولُونَ بِأَفْوَاهِكُم مَّا لَيْسَ
لَكُم بِهِ عِلْمٌ وَتَحْسَبُونَهُ هَيِّنًا وَهُوَ عِندَ اللهِ عَظِيمٌ
Ith talaqqawnahu bi-alsinatikumwataqooloona bi-afwahikum ma laysa lakum
bihiAAilmun watahsaboonahu hayyinan wahuwa AAinda AllahiAAatheem
Hausa
A lőkacin da kuke marăbarsa da harsunanku kuma kună cẽwa da bakunanku abin da bă
ku da wani ilmi game da shi, kuma kună zaton sa mai sauƙi alhăli kuwa, shi a
wurin Allah, babba ne.
|
Ayah 24:16 الأية
وَلَوْلَا إِذْ سَمِعْتُمُوهُ قُلْتُم مَّا يَكُونُ لَنَا أَن نَّتَكَلَّمَ
بِهَٰذَا سُبْحَانَكَ هَٰذَا بُهْتَانٌ عَظِيمٌ
Walawla ith samiAAtumoohuqultum ma yakoonu lana an natakallama bihathasubhanaka
hatha buhtanun AAatheem
Hausa
Kuma don me a lőkacin da kuka ji shi, ba ku ce ba, "Bă ya yiwuwa a gare mu, mu
yi magana a game da wannan. Tsarki ya tabbata a gare Ka, wannan ƙiren ƙarya ne
mai girma"?
|
Ayah 24:17 الأية
يَعِظُكُمُ اللهُ أَن تَعُودُوا لِمِثْلِهِ أَبَدًا إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
YaAAithukumu Allahu antaAAoodoo limithlihi abadan in kuntum mu/mineen
Hausa
Allah Yană yi muku wa'azi, kada ku kőma ga irinsa, har abada, idan kun kasance
mũminai.
|
Ayah 24:18 الأية
وَيُبَيِّنُ اللهُ لَكُمُ الْآيَاتِ ۚ وَاللهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Wayubayyinu Allahu lakumu al-ayatiwallahu AAaleemun hakeem
Hausa
Kuma Allah Yană bayyana muku ăyőyinSa, kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
|
Ayah 24:19 الأية
إِنَّ الَّذِينَ يُحِبُّونَ أَن تَشِيعَ الْفَاحِشَةُ فِي الَّذِينَ آمَنُوا لَهُمْ
عَذَابٌ أَلِيمٌ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ ۚ وَاللهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا
تَعْلَمُونَ
Inna allatheena yuhibboona antasheeAAa alfahishatu fee allatheena amanoolahum
AAathabun aleemun fee addunya wal-akhiratiwallahu yaAAlamu waantum la taAAlamoon
Hausa
Lalle ne waɗanda ke son alfăsha ta wătsu ga waɗanda suka yi ĩmăni sună da azăba
mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lăhira. KumaAllah, Shi ne Ya sani, alhăli kuwa, kũ
ba ku sani ba.
|
Ayah 24:20 الأية
وَلَوْلَا فَضْلُ اللهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ وَأَنَّ اللهَ رَءُوفٌ
رَّحِيمٌ
Walawla fadlu AllahiAAalaykum warahmatuhu waanna Allaha raoofun raheem
Hausa
Kuma bă dőmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa. Kuma lalle ne Allah Mai
tausayi ne, Mai jin ƙai!
|
Ayah 24:21 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّبِعُوا خُطُوَاتِ الشَّيْطَانِ ۚ وَمَن
يَتَّبِعْ خُطُوَاتِ الشَّيْطَانِ فَإِنَّهُ يَأْمُرُ بِالْفَحْشَاءِ وَالْمُنكَرِ
ۚ وَلَوْلَا فَضْلُ اللهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ مَا زَكَىٰ مِنكُم مِّنْ
أَحَدٍ أَبَدًا وَلَٰكِنَّ اللهَ يُزَكِّي مَن يَشَاءُ ۗ وَاللهُ سَمِيعٌ
عَلِيمٌ
Ya ayyuha allatheena amanoola tattabiAAoo khutuwati ashshaytaniwaman yattabiAA
khutuwati ashshaytanifa-innahu ya/muru bilfahsha-i walmunkariwalawla fadlu
Allahi AAalaykum warahmatuhuma zaka minkum min ahadin abadan walakinnaAllaha
yuzakkee man yashao wallahusameeAAun AAaleem
Hausa
Ya ku waɗanda suka yi ĩmăni, kada ku bi hanyőyin Shaiɗan. Kuma wanda ke bin
hanyőyin Shaiɗan, to, lalle ne shi, yană umurni da yin alfăsha da abin da ba a
sani ba, kuma bă dőmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa, băbu wani mutum
daga gare ku da zai tsarkaka har abada, kuma amma Allah Yană tsarkake wanda Yake
so kuma Allah Mai ji ne, Masani.
|
Ayah 24:22 الأية
وَلَا يَأْتَلِ أُولُو الْفَضْلِ مِنكُمْ وَالسَّعَةِ أَن يُؤْتُوا أُولِي
الْقُرْبَىٰ وَالْمَسَاكِينَ وَالْمُهَاجِرِينَ فِي سَبِيلِ اللهِ ۖ وَلْيَعْفُوا
وَلْيَصْفَحُوا ۗ أَلَا تُحِبُّونَ أَن يَغْفِرَ اللهُ لَكُمْ ۗ وَاللهُ
غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Wala ya/tali oloo alfadliminkum wassaAAati an yu/too olee alqurba
walmasakeenawalmuhajireena fee sabeeli AllahiwalyaAAfoo walyasfahoo ala
tuhibboonaan yaghfira Allahu lakum wallahu ghafoorunraheem
Hausa
Kuma kada ma'abũta falala daga gare ku da mawadăta su rantse ga rashin su băyar
da alhẽri ga ma'abũta zumunta da miskĩnai da muhăjirai, a cikin hanyar Allah.
Kuma su yăfe, kuma su kau da kai. shin, bă ku son Allah Ya găfarta muku, alhăli
Allah Mai găfara ne, Mai jin ƙai?
|
Ayah 24:23 الأية
إِنَّ الَّذِينَ يَرْمُونَ الْمُحْصَنَاتِ الْغَافِلَاتِ الْمُؤْمِنَاتِ لُعِنُوا
فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Inna allatheena yarmoona almuhsanatialghafilati almu/minati luAAinoo fee
addunyawal-akhirati walahum AAathabun AAatheem
Hausa
Lalle ne waɗannan da suke jĩfar mătă măsu kămun kai găfilai mũminai, an la'ane
su, a cikin dũniya da Lăhira, kuma sunăda azăba mai girma.
|
Ayah 24:24 الأية
يَوْمَ تَشْهَدُ عَلَيْهِمْ أَلْسِنَتُهُمْ وَأَيْدِيهِمْ وَأَرْجُلُهُم بِمَا
كَانُوا يَعْمَلُونَ
Yawma tashhadu AAalayhim alsinatuhumwaaydeehim waarjuluhum bima kanoo yaAAmaloon
Hausa
A rănar da harsunansu da hannăyensu, da ƙafăfunsu suke băyar da shaida a kansu,
game da abin da suka kasance sună aikatăwa.
|
Ayah 24:25 الأية
يَوْمَئِذٍ يُوَفِّيهِمُ اللهُ دِينَهُمُ الْحَقَّ وَيَعْلَمُونَ أَنَّ اللهَ
هُوَ الْحَقُّ الْمُبِينُ
Yawma-ithin yuwaffeehimu Allahudeenahumu alhaqqa wayaAAlamoona anna Allaha huwa
alhaqqualmubeen
Hausa
a rănar dl Allah Yake cika musu sakamakonsu tabbatacce kuma sună sanin (cẽwa)
lalle Allah, Shi ne Gaskiya bayyananna.
|
Ayah 24:26 الأية
الْخَبِيثَاتُ لِلْخَبِيثِينَ وَالْخَبِيثُونَ لِلْخَبِيثَاتِ ۖ وَالطَّيِّبَاتُ
لِلطَّيِّبِينَ وَالطَّيِّبُونَ لِلطَّيِّبَاتِ ۚ أُولَٰئِكَ مُبَرَّءُونَ مِمَّا
يَقُولُونَ ۖ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَرِزْقٌ كَرِيمٌ
Alkhabeethatu lilkhabeetheena walkhabeethoonalilkhabeethati wattayyibatu
littayyibeenawattayyiboona littayyibatiola-ika mubarraoona mimma yaqooloona
lahummaghfiratun warizqun kareem
Hausa
Miyăgun mătă dőmin miyagun maza suke, kuma miyăgun maza dőmin miyăgun mătă suke
kuma tsarkăkan mătă dőmin tsarkăkan maza suke kuma tsarkăkan maza dőmin
tsarkăkan mătă suke. waɗancan sũ ne waɗanda ake barrantăwa daga abin da (măsu
ƙazafi) suke faɗa kuma sună da găfara da arziki na karimci.
|
Ayah 24:27 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَدْخُلُوا بُيُوتًا غَيْرَ بُيُوتِكُمْ
حَتَّىٰ تَسْتَأْنِسُوا وَتُسَلِّمُوا عَلَىٰ أَهْلِهَا ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ
لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ
Ya ayyuha allatheena amanoola tadkhuloo buyootan ghayra buyootikum
hattatasta/nisoo watusallimoo AAala ahliha thalikumkhayrun lakum laAAallakum
tathakkaroon
Hausa
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku shiga gidăje waɗanda bă gidăjenku ba sai
kun sămi izni, kuma kun yi sallama a kan ma'abũtansu. Wannan ne mafi alhẽri gare
ku, tsammaninku, ză ku tuna.
|
Ayah 24:28 الأية
فَإِن لَّمْ تَجِدُوا فِيهَا أَحَدًا فَلَا تَدْخُلُوهَا حَتَّىٰ يُؤْذَنَ لَكُمْ ۖ
وَإِن قِيلَ لَكُمُ ارْجِعُوا فَارْجِعُوا ۖ هُوَ أَزْكَىٰ لَكُمْ ۚ وَاللهُ
بِمَا تَعْمَلُونَ عَلِيمٌ
Fa-in lam tajidoo feeha ahadanfala tadkhulooha hatta yu/thanalakum wa-in qeela
lakumu irjiAAoo farjiAAoo huwa azkalakum wallahu bima taAAmaloona AAaleem
Hausa
To, idan ba ku sămi kőwa a cikinsu ba, to, kada ku shige su, sai an yi muku
izni. Kuma idan an ce muku, "Ku kőma." Sai ku kőma, shi ne mafi tsarkaka a gare
ku. Kuma Allah game da abin da kuke aikatăwa, Masani ne.
|
Ayah 24:29 الأية
لَّيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَن تَدْخُلُوا بُيُوتًا غَيْرَ مَسْكُونَةٍ فِيهَا
مَتَاعٌ لَّكُمْ ۚ وَاللهُ يَعْلَمُ مَا تُبْدُونَ وَمَا تَكْتُمُونَ
Laysa AAalaykum junahun an tadkhuloobuyootan ghayra maskoonatin feeha mataAAun
lakum wallahuyaAAlamu ma tubdoona wama taktumoon
Hausa
Băbu laifi a kanku, ga ku shiga gidăje waɗanda bă zaunannu ba, a cikinsu akwai
waɗansu kăya năku. Kuma Allah Yană sanin abin da kuke nũnăwa, da abin dakuke
ɓăyẽwa.
|
Ayah 24:30 الأية
قُل لِّلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ۚ
ذَٰلِكَ أَزْكَىٰ لَهُمْ ۗ إِنَّ اللهَ خَبِيرٌ بِمَا يَصْنَعُونَ
Qul lilmu/mineena yaghuddoo min absarihumwayahfathoo furoojahum thalika
azkalahum inna Allaha khabeerun bima yasnaAAoon
Hausa
Ka ce wa mũminai maza su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjőjinsu. wannan
shĩ ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da
suke sană'antăwa.
|
Ayah 24:31 الأية
وَقُل لِّلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ
وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا ۖ وَلْيَضْرِبْنَ
بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّ ۖ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا
لِبُعُولَتِهِنَّ أَوْ آبَائِهِنَّ أَوْ آبَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ أَبْنَائِهِنَّ
أَوْ أَبْنَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي إِخْوَانِهِنَّ أَوْ
بَنِي أَخَوَاتِهِنَّ أَوْ نِسَائِهِنَّ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُنَّ أَوِ
التَّابِعِينَ غَيْرِ أُولِي الْإِرْبَةِ مِنَ الرِّجَالِ أَوِ الطِّفْلِ الَّذِينَ
لَمْ يَظْهَرُوا عَلَىٰ عَوْرَاتِ النِّسَاءِ ۖ وَلَا يَضْرِبْنَ بِأَرْجُلِهِنَّ
لِيُعْلَمَ مَا يُخْفِينَ مِن زِينَتِهِنَّ ۚ وَتُوبُوا إِلَى اللهِ جَمِيعًا
أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Waqul lilmu/minati yaghdudnamin absarihinna wayahfathnafuroojahunna wala
yubdeena zeenatahunna illa mathahara minha walyadribnabikhumurihinna AAala
juyoobihinna wala yubdeenazeenatahunna illa libuAAoolatihinna aw aba-ihinnaaw
aba-i buAAoolatihinna aw abna-ihinna awabna-i buAAoolatihinna aw ikhwanihinna aw
baneeikhwanihinna aw banee akhawatihinna aw nisa-ihinnaaw ma malakat aymanuhunna
awi attabiAAeenaghayri olee al-irbati mina arrijali awi attifliallatheena lam
yathharoo AAala AAawratiannisa-i wala yadribnabi-arjulihinna liyuAAlama ma
yukhfeena min zeenatihinnawatooboo ila Allahi jameeAAan ayyuhaalmu/minoona
laAAallakum tuflihoon
Hausa
Kuma ka ce wa mũminai măta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjőjinsu
kuma kada su bayyana ƙawarsu făce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dőka
da mayăfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu făce ga mazansu ko
ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko
ɗiyan 'yan'uwansu mătă, kő mătan ƙungiyarsu, ko abin da hannăyensu na dăma suka
mallaka, ko mabiya wasun măsu bukătar măta daga maza, kő jărirai waɗanda. bă su
tsinkăya a kan al'aurar mătă. Kuma kada su yi dũka da ƙafăfunsu dőmin a san abin
da suke ɓőyẽwa daga ƙawarsu.Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabă ɗaya, yă ku mũminai!
Tsammăninku, ku sămi babban rabo.
|
Ayah 24:32 الأية
وَأَنكِحُوا الْأَيَامَىٰ مِنكُمْ وَالصَّالِحِينَ مِنْ عِبَادِكُمْ وَإِمَائِكُمْ
ۚ إِن يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللهُ مِن فَضْلِهِ ۗ وَاللهُ وَاسِعٌ
عَلِيمٌ
Waankihoo al-ayamaminkum wassaliheena min AAibadikumwa-ima-ikum in yakoonoo
fuqaraa yughnihimu Allahumin fadlihi wallahu wasiAAun AAaleem
Hausa
Kuma ku aurar da gwaurăye daga gare ku, da sălihai daga băyinku, da kuyanginku.
Idan sun kasance matalauta Allah zai wadătar da su daga falalarSa. Kuma Allah
Mawadăci ne, Masani.
|
Ayah 24:33 الأية
وَلْيَسْتَعْفِفِ الَّذِينَ لَا يَجِدُونَ نِكَاحًا حَتَّىٰ يُغْنِيَهُمُ اللهُ
مِن فَضْلِهِ ۗ وَالَّذِينَ يَبْتَغُونَ الْكِتَابَ مِمَّا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ
فَكَاتِبُوهُمْ إِنْ عَلِمْتُمْ فِيهِمْ خَيْرًا ۖ وَآتُوهُم مِّن مَّالِ اللهِ
الَّذِي آتَاكُمْ ۚ وَلَا تُكْرِهُوا فَتَيَاتِكُمْ عَلَى الْبِغَاءِ إِنْ أَرَدْنَ
تَحَصُّنًا لِّتَبْتَغُوا عَرَضَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۚ وَمَن يُكْرِههُّنَّ
فَإِنَّ اللهَ مِن بَعْدِ إِكْرَاهِهِنَّ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
WalyastaAAfifi allatheena layajidoona nikahan hatta yughniyahumu Allahumin
fadlihi wallatheena yabtaghoona alkitabamimma malakat aymanukum fakatiboohum
inAAalimtum feehim khayran waatoohum min mali Allahiallathee atakum wala
tukrihoo fatayatikumAAala albigha-i in aradna tahassunanlitabtaghoo AAarada
alhayati addunyawaman yukrihhunna fa-inna Allaha min baAAdi ikrahihinnaghafoorun
raheem
Hausa
Kuma waɗannan da ba su sămi aure ba su kăme kansu har Allah Ya wadătar da su
daga, falalarsa. Kuma waɗanda ke nẽman fansa daga abin da hannuwanku na dăma
suka mallaka, to, ku ɗaura musu fansă idan kun san akwai wani alhẽri a cikinsu
kuma ku bă su wani abu daga dũkiyar Allah wannan da Ya bă ku. Kuma kada ku
tĩlasta kuyanginku a kan yin zina, idan sun yi nufin tsaron kansu, dőmin ku nẽmi
răyuwar dũniya, kuma wanda ya tĩlasta su to, lalle Allah, a băyan tĩlasta su,
Mai găfara ne, Mai jin ƙai.
|
Ayah 24:34 الأية
وَلَقَدْ أَنزَلْنَا إِلَيْكُمْ آيَاتٍ مُّبَيِّنَاتٍ وَمَثَلًا مِّنَ الَّذِينَ
خَلَوْا مِن قَبْلِكُمْ وَمَوْعِظَةً لِّلْمُتَّقِينَ
Walaqad anzalna ilaykum ayatinmubayyinatin wamathalan mina allatheena khalaw
minqablikum wamawAAithatan lilmuttaqeen
Hausa
Kuma lalle ne Mun saukar zuwa gare ku, ăyőyi măsu bayyanăwa, da misăli daga
waɗanda suka shige daga gabăninku, da wa'azi ga măsu taƙawa.
|
Ayah 24:35 الأية
اللهُ نُورُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ مَثَلُ نُورِهِ كَمِشْكَاةٍ فِيهَا
مِصْبَاحٌ ۖ الْمِصْبَاحُ فِي زُجَاجَةٍ ۖ الزُّجَاجَةُ كَأَنَّهَا كَوْكَبٌ
دُرِّيٌّ يُوقَدُ مِن شَجَرَةٍ مُّبَارَكَةٍ زَيْتُونَةٍ لَّا شَرْقِيَّةٍ وَلَا
غَرْبِيَّةٍ يَكَادُ زَيْتُهَا يُضِيءُ وَلَوْ لَمْ تَمْسَسْهُ نَارٌ ۚ نُّورٌ
عَلَىٰ نُورٍ ۗ يَهْدِي اللهُ لِنُورِهِ مَن يَشَاءُ ۚ وَيَضْرِبُ اللهُ
الْأَمْثَالَ لِلنَّاسِ ۗ وَاللهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ
Allahu nooru assamawatiwal-ardi mathalu noorihi kamishkatin feehamisbahun
almisbahu fee zujajatinazzujajatu kaannaha kawkabun durriyyunyooqadu min
shajaratin mubarakatin zaytoonatin lasharqiyyatin wala gharbiyyatin yakadu
zaytuhayudee-o walaw lam tamsas-hu narun noorun AAalanoorin yahdee Allahu
linoorihi man yashao wayadribuAllahu al-amthala linnasi wallahubikulli shay-in
AAaleem
Hausa
Allah ne Hasken sammai da ƙasa, misălin HaskenSa, kamar tăgă, a cikinta akwai
fitila, fitilar a cikin ƙarau, ƙarau ɗin kamar shi taurăro ne mai tsananin
haske, ană kunna shi daga wata ităciya mai albarka, ta zaitũni, bă bagabashiya
ba kuma bă bayammaciya ba, manta na kusa ya yi haske, kuma kő wuta ba ta shăfe
shi ba, haske a kan haske, Allah na shiryar da wanda Yake so zuwa ga HaskenSa.
Kuma Allah na buga misălai ga mutăne, kuma Allah game da dukan kőme, Masani ne.
|
Ayah 24:36 الأية
فِي بُيُوتٍ أَذِنَ اللهُ أَن تُرْفَعَ وَيُذْكَرَ فِيهَا اسْمُهُ يُسَبِّحُ لَهُ
فِيهَا بِالْغُدُوِّ وَالْآصَالِ
Fee buyootin athina Allahu anturfaAAa wayuthkara feeha ismuhu yusabbihulahu
feeha bilghuduwwi wal-asal
Hausa
A cikin waɗansu gidăje waɗanda Allah Yă yi umurnin a ɗaukaka kuma a ambaci
sũnansa a cikinsu, sună yin tasbĩhi a gare Shi a cikinsu, săfe da maraice.
|
Ayah 24:37 الأية
رِجَالٌ لَّا تُلْهِيهِمْ تِجَارَةٌ وَلَا بَيْعٌ عَن ذِكْرِ اللهِ وَإِقَامِ
الصَّلَاةِ وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ ۙ يَخَافُونَ يَوْمًا تَتَقَلَّبُ فِيهِ
الْقُلُوبُ وَالْأَبْصَارُ
Rijalun la tulheehim tijaratunwala bayAAun AAan thikri Allahi wa-iqamiassalati
wa-eeta-i azzakatiyakhafoona yawman tataqallabu feehi alquloobu wal-absar
Hausa
Waɗansu maza, waɗanda wani fatauci bă ya shagaltar da su, kuma sayarwa bă ta
shagaltar da su daga ambaton Allah, da tsai da salla da băyar da zakka, sună
tsőron wani yini wanda zukăta sună bibbirkita a cikinsa, da gannai.
|
Ayah 24:38 الأية
لِيَجْزِيَهُمُ اللهُ أَحْسَنَ مَا عَمِلُوا وَيَزِيدَهُم مِّن فَضْلِهِ ۗ
وَاللهُ يَرْزُقُ مَن يَشَاءُ بِغَيْرِ حِسَابٍ
Liyajziyahumu Allahu ahsana maAAamiloo wayazeedahum min fadlihi wallahuyarzuqu
man yashao bighayri hisab
Hausa
Dőmin Allah Ya săka musu da mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Ya ƙăra musu
daga falalarsa. Kuma Allah Yană azurta wanda Yake so, bă da lissafi ba.
|
Ayah 24:39 الأية
وَالَّذِينَ كَفَرُوا أَعْمَالُهُمْ كَسَرَابٍ بِقِيعَةٍ يَحْسَبُهُ الظَّمْآنُ
مَاءً حَتَّىٰ إِذَا جَاءَهُ لَمْ يَجِدْهُ شَيْئًا وَوَجَدَ اللهَ عِندَهُ
فَوَفَّاهُ حِسَابَهُ ۗ وَاللهُ سَرِيعُ الْحِسَابِ
Wallatheena kafaroo aAAmaluhumkasarabin biqeeAAatin yahsabuhu aththam-anumaan
hatta itha jaahu lamyajidhu shay-an wawajada Allaha AAindahu fawaffahu
hisabahuwallahu sareeAAu alhisab
Hausa
Kuma waɗanda suka ƙăfirta ayyukansu sună kamar ƙawalwalniyă ga faƙo, mai
ƙishirwa yană zaton sa ruwa, har idan ya jẽ masa bai iske shi kőme ba, kuma ya
sămi Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisăbinsa. Kuma Allah Mai gaggăwar
sakamako ne.
|
Ayah 24:40 الأية
أَوْ كَظُلُمَاتٍ فِي بَحْرٍ لُّجِّيٍّ يَغْشَاهُ مَوْجٌ مِّن فَوْقِهِ مَوْجٌ مِّن
فَوْقِهِ سَحَابٌ ۚ ظُلُمَاتٌ بَعْضُهَا فَوْقَ بَعْضٍ إِذَا أَخْرَجَ يَدَهُ لَمْ
يَكَدْ يَرَاهَا ۗ وَمَن لَّمْ يَجْعَلِ اللهُ لَهُ نُورًا فَمَا لَهُ مِن نُّورٍ
Aw kathulumatin fee bahrinlujjiyyin yaghshahu mawjun min fawqihi mawjun min
fawqihisahabun thulumatun baAAduhafawqa baAAdin itha akhraja yadahu lam yakad
yarahawaman lam yajAAali Allahu lahu nooran fama lahu minnoor
Hausa
Kő kuwa kamar duffai a cikin tẽku mai zurfi, tăguwar ruwa tană rufe da shi, daga
bisansa akwai wata tăguwa, daga bisansa akwai wani girgije, duffai săshensu a
bisa săshe, idan ya fitar da tăfinsa ba ya kusa ya gan shi. Kuma wanda Allah bai
sanya masa haske ba, to, bă ya da wani haske.
|
Ayah 24:41 الأية
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللهَ يُسَبِّحُ لَهُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ
وَالطَّيْرُ صَافَّاتٍ ۖ كُلٌّ قَدْ عَلِمَ صَلَاتَهُ وَتَسْبِيحَهُ ۗ وَاللهُ
عَلِيمٌ بِمَا يَفْعَلُونَ
Alam tara anna Allaha yusabbihulahu man fee assamawati wal-ardiwattayru saffatin
kullun qadAAalima salatahu watasbeehahu wallahuAAaleemun bima yafAAaloon
Hausa
Shin, ba ka gani ba (cẽwa) lalle ne Allah, Wanda yake a cikin sammai da ƙasa
sună yi Masa tasbĩhi, kuma tsuntsaye sună măsu sanwa, kőwane lalle ya san
sallarsa da tasbĩhinsa kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatăwa?
|
Ayah 24:42 الأية
وَلِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ وَإِلَى اللهِ الْمَصِيرُ
Walillahi mulku assamawatiwal-ardi wa-ila Allahi almaseer
Hausa
Mulkin sammai da ƙasa ga Allah kawai yake, kuma zuwa ga Allah makőma take.
|
Ayah 24:43 الأية
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللهَ يُزْجِي سَحَابًا ثُمَّ يُؤَلِّفُ بَيْنَهُ ثُمَّ
يَجْعَلُهُ رُكَامًا فَتَرَى الْوَدْقَ يَخْرُجُ مِنْ خِلَالِهِ وَيُنَزِّلُ مِنَ
السَّمَاءِ مِن جِبَالٍ فِيهَا مِن بَرَدٍ فَيُصِيبُ بِهِ مَن يَشَاءُ وَيَصْرِفُهُ
عَن مَّن يَشَاءُ ۖ يَكَادُ سَنَا بَرْقِهِ يَذْهَبُ بِالْأَبْصَارِ
Alam tara anna Allaha yuzjee sahabanthumma yu-allifu baynahu thumma yajAAaluhu
rukaman fataraalwadqa yakhruju min khilalihi wayunazzilu mina assama-imin
jibalin feeha min baradin fayuseebu bihiman yashao wayasrifuhu AAan man yashao
yakadusana barqihi yathhabu bil-absar
Hausa
Ashe, ba ka ganĩ ba, lalle ne Allah Yană kőra girgije, sa'an nan kuma Ya haɗa a
tsakăninsa sa'an nan kuma Ya sanya shi mai hauhawar jũna? Sai ka ga ruwa yană
fita daga tsattsakinsa, kuma Ya saukar daga waɗansu duwătsu a cikinsa na ƙanƙară
daga sama, sai ya sămu wanda Yake so da shi, kuma Ya karkatar da shi daga barin
wanda Yake so. Hasken walƙiyarsa Yană kusa ya tafi da gannai.
|
Ayah 24:44 الأية
يُقَلِّبُ اللهُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبْرَةً
لِّأُولِي الْأَبْصَارِ
Yuqallibu Allahu allayla wannaharainna fee thalika laAAibratan li-olee al-absar
Hausa
Allah Yană jũyar da dare da yini. Lalle ne a cikin wannan akwai abin kula ga
ma'abũta gannai.
|
Ayah 24:45 الأية
وَاللهُ خَلَقَ كُلَّ دَابَّةٍ مِّن مَّاءٍ ۖ فَمِنْهُم مَّن يَمْشِي عَلَىٰ
بَطْنِهِ وَمِنْهُم مَّن يَمْشِي عَلَىٰ رِجْلَيْنِ وَمِنْهُم مَّن يَمْشِي عَلَىٰ
أَرْبَعٍ ۚ يَخْلُقُ اللهُ مَا يَشَاءُ ۚ إِنَّ اللهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ
قَدِيرٌ
Wallahu khalaqa kulla dabbatinmin ma-in faminhum man yamshee AAala
batnihiwaminhum man yamshee AAala rijlayni waminhum man yamsheeAAala arbaAAin
yakhluqu Allahu ma yashaoinna Allaha AAala kulli shay-in qadeer
Hausa
Kuma Allah ne Ya halitta kőwace dabba daga ruwa. To, daga cikinsu akwai waɗanda
ke tafiya a kan cikinsu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan ƙafăfu
biyu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya akan huɗu. Allah Yăna halitta
abin da Yake so, lalle Allah, a kan kőwane abu, Mai ĩkon yi ne.
|
Ayah 24:46 الأية
لَّقَدْ أَنزَلْنَا آيَاتٍ مُّبَيِّنَاتٍ ۚ وَاللهُ يَهْدِي مَن يَشَاءُ إِلَىٰ
صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Laqad anzalna ayatinmubayyinatin wallahu yahdee man yashaoila siratin mustaqeem
Hausa
Lalle ne haƙĩƙa Mun saukar da ăyőyi, măsu bayyanăwa. Kuma Allah Yană shiryar da
wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya.
|
Ayah 24:47 الأية
وَيَقُولُونَ آمَنَّا بِاللهِ وَبِالرَّسُولِ وَأَطَعْنَا ثُمَّ يَتَوَلَّىٰ
فَرِيقٌ مِّنْهُم مِّن بَعْدِ ذَٰلِكَ ۚ وَمَا أُولَٰئِكَ بِالْمُؤْمِنِينَ
Wayaqooloona amanna billahiwabirrasooli waataAAna thumma yatawallafareequn
minhum min baAAdi thalika wama ola-ikabilmu/mineen
Hausa
Kuma sună cẽwa, "Mun yi ĩmăni da Allah da kuma Manzo, kuma mun yi ɗă'ă." Sa'an
nan kuma wata ƙungiya daga gare su,su jũya daga băyan wancan. Kuma waɗancan ba
mũminai ba ne.
|
Ayah 24:48 الأية
وَإِذَا دُعُوا إِلَى اللهِ وَرَسُولِهِ لِيَحْكُمَ بَيْنَهُمْ إِذَا فَرِيقٌ
مِّنْهُم مُّعْرِضُونَ
Wa-itha duAAoo ila Allahiwarasoolihi liyahkuma baynahum itha fareequn
minhummuAAridoon
Hausa
Kuma idan aka kiră su zuwa ga Allah da ManzonSa, dőmin Ya yi hukunci a
tsakăninsu, sai gă wata ƙnngiya daga gare su sună măsu bijirewa.
|
Ayah 24:49 الأية
وَإِن يَكُن لَّهُمُ الْحَقُّ يَأْتُوا إِلَيْهِ مُذْعِنِينَ
Wa-in yakun lahumu alhaqqu ya/tooilayhi muthAAineen
Hausa
Kuma idan hakki ya kasance a gare su, ză su jẽ zuwa gare shi, snnă măsu mĩƙa
wuya.
|
Ayah 24:50 الأية
أَفِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ أَمِ ارْتَابُوا أَمْ يَخَافُونَ أَن يَحِيفَ اللهُ
عَلَيْهِمْ وَرَسُولُهُ ۚ بَلْ أُولَٰئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ
Afee quloobihim maradun ami irtabooam yakhafoona an yaheefa Allahu
AAalayhimwarasooluhu bal ola-ika humu aththalimoon
Hausa
Shin, a cikin zukătansu akwai cũta ne, ko kuwa sună tsőron Allah Ya yi zălunci a
kansu da ManzonSa? Ă'a, waɗancan sũ ne azzălumai.
|
Ayah 24:51 الأية
إِنَّمَا كَانَ قَوْلَ الْمُؤْمِنِينَ إِذَا دُعُوا إِلَى اللهِ وَرَسُولِهِ
لِيَحْكُمَ بَيْنَهُمْ أَن يَقُولُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا ۚ وَأُولَٰئِكَ هُمُ
الْمُفْلِحُونَ
Innama kana qawla almu/mineenaitha duAAoo ila Allahi warasoolihi
liyahkumabaynahum an yaqooloo samiAAna waataAAna waola-ikahumu almuflihoon
Hausa
Maganar mũminai, idan aka kira su zuwa ga Allah da ManzonSa dőmin Ya yi hukunci
a tsakăninsu takan kasance kawai su ce "Mun ji, kuma mun yi ɗă'ă, Kuma waɗannan
sũ ne măsu cin nasara."
|
Ayah 24:52 الأية
وَمَن يُطِعِ اللهَ وَرَسُولَهُ وَيَخْشَ اللهَ وَيَتَّقْهِ فَأُولَٰئِكَ هُمُ
الْفَائِزُونَ
Waman yutiAAi Allahawarasoolahu wayakhsha Allaha wayattaqhi faola-ikahumu
alfa-izoon
Hausa
Kuma wanda ya yi ɗă'ă ga Allah da ManzonSa, kuma ya ji tsőron Allah, ya kuma bĩ
Shi da taƙawa to waɗannan sũ ne măsu babban rabo.
|
Ayah 24:53 الأية
وَأَقْسَمُوا بِاللهِ جَهْدَ أَيْمَانِهِمْ لَئِنْ أَمَرْتَهُمْ لَيَخْرُجُنَّ ۖ
قُل لَّا تُقْسِمُوا ۖ طَاعَةٌ مَّعْرُوفَةٌ ۚ إِنَّ اللهَ خَبِيرٌ بِمَا
تَعْمَلُونَ
Waaqsamoo billahi jahda aymanihimla-in amartahum layakhrujunna qul la tuqsimoo
taAAatunmaAAroofatun inna Allaha khabeerun bima taAAmaloon
Hausa
Kuma suka rantse da Allah iyăkar rantsuwarsu, 'Lalle ne idan ka umurce su haƙĩƙa
sună fita.' Ka ce, "Kada ku rantse, ɗă'ă sananna ce! Lalle ne, Allah Mai
ƙididdigewă ne ga abin da kuke aikatăwă."
|
Ayah 24:54 الأية
قُلْ أَطِيعُوا اللهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ ۖ فَإِن تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا
عَلَيْهِ مَا حُمِّلَ وَعَلَيْكُم مَّا حُمِّلْتُمْ ۖ وَإِن تُطِيعُوهُ تَهْتَدُوا
ۚ وَمَا عَلَى الرَّسُولِ إِلَّا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ
Qul ateeAAoo Allaha waateeAAooarrasoola fa-in tawallaw fa-innama AAalayhi
mahummila waAAalaykum ma hummiltum wa-in tuteeAAoohutahtadoo wama AAala
arrasooli illaalbalaghu almubeen
Hausa
Ka ce: "Ku yi ɗă'ă ga Allah kuma ku yi ɗă'ă ga Manzo. To, idan kun jũya, to, a
kansa akwai abin da aka aza masa kawai, kuma a kanku akwai abin da aka aza muku
kawai, Kuma idan kun yi masa ɗă'ă za ku shiryu. Kuma băbu abin da yake a kan
Manzo făce iyarwa bayyananna."
|
Ayah 24:55 الأية
وَعَدَ اللهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنكُمْ وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ
لَيَسْتَخْلِفَنَّهُمْ فِي الْأَرْضِ كَمَا اسْتَخْلَفَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ
وَلَيُمَكِّنَنَّ لَهُمْ دِينَهُمُ الَّذِي ارْتَضَىٰ لَهُمْ وَلَيُبَدِّلَنَّهُم
مِّن بَعْدِ خَوْفِهِمْ أَمْنًا ۚ يَعْبُدُونَنِي لَا يُشْرِكُونَ بِي شَيْئًا ۚ
وَمَن كَفَرَ بَعْدَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ
WaAAada Allahu allatheena amanoominkum waAAamiloo assalihatilayastakhlifannahum
fee al-ardi kama istakhlafaallatheena min qablihim walayumakkinanna lahum
deenahumuallathee irtada lahum walayubaddilannahum minbaAAdi khawfihim amnan
yaAAbudoonanee la yushrikoona beeshay-an waman kafara baAAda thalika faola-ika
humualfasiqoon
Hausa
Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmăni daga gare. Ku, kuma suka aikata
ayyukan ƙwarai, lalle zai shugabantar da su a cikin ƙasa kamar yadda Ya
shugabantar da waɗanda suke daga gabăninsu, kuma lalle ne zai tabbatar musu da
addininsu wanda Ya yardar musu, kuma lalle ne Yană musanya musu daga băyan
tsőronsu da aminci, sună bauta Mini bă su haɗa kőme da Nĩ. Kuma wanda ya kăfirta
a băyan wannan, to, waɗancan, su ne făsiƙai.
|
Ayah 24:56 الأية
وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ لَعَلَّكُمْ
تُرْحَمُونَ
Waaqeemoo assalata waatooazzakata waateeAAoo arrasoolalaAAallakum turhamoon
Hausa
Kuma ku tsayar da salla, kuma ku băyar da zakka, kuma ku yi ɗă'ă ga Manzo,
tsammăninku a yi muku rahama.
|
Ayah 24:57 الأية
لَا تَحْسَبَنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا مُعْجِزِينَ فِي الْأَرْضِ ۚ وَمَأْوَاهُمُ
النَّارُ ۖ وَلَبِئْسَ الْمَصِيرُ
La tahsabanna allatheenakafaroo muAAjizeena fee al-ardi wama/wahumu
annaruwalabi/sa almaseer
Hausa
Kada lalle ka yi zaton waɗanda suka kăfirta ză su buwăya a cikin ƙasa, kuma
makőmarsu wuta ce, kuma lalle ne makomar tă mũnana.
|
Ayah 24:58 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لِيَسْتَأْذِنكُمُ الَّذِينَ مَلَكَتْ
أَيْمَانُكُمْ وَالَّذِينَ لَمْ يَبْلُغُوا الْحُلُمَ مِنكُمْ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ ۚ
مِّن قَبْلِ صَلَاةِ الْفَجْرِ وَحِينَ تَضَعُونَ ثِيَابَكُم مِّنَ الظَّهِيرَةِ
وَمِن بَعْدِ صَلَاةِ الْعِشَاءِ ۚ ثَلَاثُ عَوْرَاتٍ لَّكُمْ ۚ لَيْسَ عَلَيْكُمْ
وَلَا عَلَيْهِمْ جُنَاحٌ بَعْدَهُنَّ ۚ طَوَّافُونَ عَلَيْكُم بَعْضُكُمْ عَلَىٰ
بَعْضٍ ۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ اللهُ لَكُمُ الْآيَاتِ ۗ وَاللهُ عَلِيمٌ
حَكِيمٌ
Ya ayyuha allatheena amanooliyasta/thinkumu allatheena malakat
aymanukumwallatheena lam yablughoo alhuluma minkumthalatha marratin min qabli
salatialfajri waheena tadaAAoona thiyabakum mina aththaheeratiwamin baAAdi
salati alAAisha-i thalathuAAawratin lakum laysa AAalaykum wala AAalayhim
junahunbaAAdahunna tawwafoona AAalaykum baAAdukumAAala baAAdin kathalika
yubayyinu Allahulakumu al-ayati wallahu AAaleemun hakeem
Hausa
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Waɗannan da hannuwanku na dăma suka mallaka da
waɗanda ba su isa mafarki ba daga cikinku, su nẽmi izni sau uku; daga gabănin
sallar alfijir da lőkacin da kuke ajiye tufăfinku sabőda zăfin rănă, kuma daga
băyan sallar ishă'i. Sũ ne al'aurőri uku a gare ku. Băbu laifi a kanku kuma băbu
a kansu a băyansu. Sũ măsu kẽwaya ne a kanku săshenku a kan săshe. Kamar wannan
ne Allah Yake bayyana ăyőyinSa a gare ku. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
|
Ayah 24:59 الأية
وَإِذَا بَلَغَ الْأَطْفَالُ مِنكُمُ الْحُلُمَ فَلْيَسْتَأْذِنُوا كَمَا
اسْتَأْذَنَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ اللهُ لَكُمْ
آيَاتِهِ ۗ وَاللهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Wa-itha balagha al-atfaluminkumu alhuluma falyasta/thinoo kama
ista/thanaallatheena min qablihim kathalika yubayyinu Allahulakum ayatihi
wallahu AAaleemun hakeem
Hausa
Kuma idan yăra daga cikinku suka isa mafarki to su nẽmi izni, kamar yadda
waɗanda suke a gabăninsu suka nẽmi iznin. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana
ăyőyinSa a gare ku, kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
|
Ayah 24:60 الأية
وَالْقَوَاعِدُ مِنَ النِّسَاءِ اللَّاتِي لَا يَرْجُونَ نِكَاحًا فَلَيْسَ
عَلَيْهِنَّ جُنَاحٌ أَن يَضَعْنَ ثِيَابَهُنَّ غَيْرَ مُتَبَرِّجَاتٍ بِزِينَةٍ ۖ
وَأَن يَسْتَعْفِفْنَ خَيْرٌ لَّهُنَّ ۗ وَاللهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
WalqawaAAidu mina annisa-iallatee la yarjoona nikahan falaysaAAalayhinna junahun
an yadaAAna thiyabahunnaghayra mutabarrijatin bizeenatin waan yastaAAfifna
khayrunlahunna wallahu sameeAAun AAaleem
Hausa
Kuma tsőfaffi daga mătă, waɗanda bă su fatan wani aure to, băbu laifi a kansu su
ajiye tufăfinsu, bă sună măsu fitar da ƙawa ba, kuma su tsare mutuncinsu shĩ ne
mafi alhẽri a gare su. Kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.
|
Ayah 24:61 الأية
لَّيْسَ عَلَى الْأَعْمَىٰ حَرَجٌ وَلَا عَلَى الْأَعْرَجِ حَرَجٌ وَلَا عَلَى
الْمَرِيضِ حَرَجٌ وَلَا عَلَىٰ أَنفُسِكُمْ أَن تَأْكُلُوا مِن بُيُوتِكُمْ أَوْ
بُيُوتِ آبَائِكُمْ أَوْ بُيُوتِ أُمَّهَاتِكُمْ أَوْ بُيُوتِ إِخْوَانِكُمْ أَوْ
بُيُوتِ أَخَوَاتِكُمْ أَوْ بُيُوتِ أَعْمَامِكُمْ أَوْ بُيُوتِ عَمَّاتِكُمْ أَوْ
بُيُوتِ أَخْوَالِكُمْ أَوْ بُيُوتِ خَالَاتِكُمْ أَوْ مَا مَلَكْتُم مَّفَاتِحَهُ
أَوْ صَدِيقِكُمْ ۚ لَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَن تَأْكُلُوا جَمِيعًا أَوْ
أَشْتَاتًا ۚ فَإِذَا دَخَلْتُم بُيُوتًا فَسَلِّمُوا عَلَىٰ أَنفُسِكُمْ تَحِيَّةً
مِّنْ عِندِ اللهِ مُبَارَكَةً طَيِّبَةً ۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ اللهُ لَكُمُ
الْآيَاتِ لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ
Laysa AAala al-aAAma harajunwala AAala al-aAAraji harajun walaAAala almareedi
harajun wala AAalaanfusikum an ta/kuloo min buyootikum aw buyooti aba-ikumaw
buyooti ommahatikum aw buyooti ikhwanikum awbuyooti akhawatikum aw buyooti
aAAmamikum awbuyooti AAammatikum aw buyooti akhwalikum awbuyooti khalatikum aw
ma malaktum mafatihahuaw sadeeqikum laysa AAalaykum junahun an ta/kuloojameeAAan
aw ashtatan fa-itha dakhaltum buyootanfasallimoo AAala anfusikum tahiyyatan min
AAindiAllahi mubarakatan tayyibatan kathalikayubayyinu Allahu lakumu al-ayati
laAAallakumtaAAqiloon
Hausa
Băbu laifi a kan makăho, kuma băbu laifi a kan gurgu, kuma băbu laifi a kan
majiyyaci, kuma băbu laifi a kan kőwanenku, ga ku ci (abinci) daga gidăjenku, kő
daga gidăjen ubanninku, kő daga gidăjen uwăyenku, kő daga gidăjen 'yan'uwanku
mază, kő daga gidăjen 'yan'uwanku mătă, kő daga gidăjen baffanninku, kő daga
gidăjen gwaggwanninku, kő daga gidăjen kăwunnanku, kő daga gidăjen innőninku kő
abin da kuka mallaki mabũɗansa kő abőkinku băbu laifi a gare ku ku ci gabă ɗaya,
kő dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidăje, ku yi sallama a kan kăwunanku,
gaisuwă ta daga wurin Allah mai albarka, mai dăɗi. Kamar wancan ne Allah Yake
bayyana muku ăyőyinSa, tsammăninku ku yi hankali.
|
Ayah 24:62 الأية
إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ الَّذِينَ آمَنُوا بِاللهِ وَرَسُولِهِ وَإِذَا كَانُوا
مَعَهُ عَلَىٰ أَمْرٍ جَامِعٍ لَّمْ يَذْهَبُوا حَتَّىٰ يَسْتَأْذِنُوهُ ۚ إِنَّ
الَّذِينَ يَسْتَأْذِنُونَكَ أُولَٰئِكَ الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِاللهِ
وَرَسُولِهِ ۚ فَإِذَا اسْتَأْذَنُوكَ لِبَعْضِ شَأْنِهِمْ فَأْذَن لِّمَن شِئْتَ
مِنْهُمْ وَاسْتَغْفِرْ لَهُمُ اللهَ ۚ إِنَّ اللهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Innama almu/minoona allatheenaamanoo billahi warasoolihi wa-itha kanoomaAAahu
AAala amrin jamiAAin lam yathhaboo hattayasta/thinoohu inna allatheena
yasta/thinoonakaola-ika allatheena yu/minoona billahiwarasoolihi fa-itha
ista/thanooka libaAAdisha/nihim fa/than liman shi/ta minhum wastaghfirlahumu
Allaha inna Allaha ghafoorun raheem
Hausa
Waɗanda ke mũminai sősai, su ne waɗanda suka yi ĩmăni da Allah da ManzonSa, kuma
idan sun kasance tăre da shi, a kan wani al'amari na aikin gayya, bă su tafiya
sai sun nẽme shi izni. Lalle ne, waɗanda suke biɗar ka izni waɗancan sũ ne suke
yin ĩmăni da Allah da ManzonSa. To, idan sun nẽme ka izni sabőda wani
sha'aninsu, to, ka yi izni ga wanda ka so daga gare su, kuma ka nẽmă musu găfara
daga Allah. Lalle Allah Mai găfara ne, Mai jin ƙai .
|
Ayah 24:63 الأية
لَّا تَجْعَلُوا دُعَاءَ الرَّسُولِ بَيْنَكُمْ كَدُعَاءِ بَعْضِكُم بَعْضًا ۚ قَدْ
يَعْلَمُ اللهُ الَّذِينَ يَتَسَلَّلُونَ مِنكُمْ لِوَاذًا ۚ فَلْيَحْذَرِ
الَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنْ أَمْرِهِ أَن تُصِيبَهُمْ فِتْنَةٌ أَوْ يُصِيبَهُمْ
عَذَابٌ أَلِيمٌ
La tajAAaloo duAAaa arrasoolibaynakum kaduAAa-i baAAdikum baAAdan qadyaAAlamu
Allahu allatheena yatasallaloona minkumliwathan falyahthari allatheena
yukhalifoonaAAan amrihi an tuseebahum fitnatun aw yuseebahumAAathabun aleem
Hausa
Kada ku sanya kiran Manzo a tsakăninku kamar kiran săshenku ga săshe. Lalle ne
Allah Yană sanin waɗanda ke sancẽwa daga cikinku da saɗăɗe. To, waɗanda suke
săɓăwa daga umurninSa, su yi saunar wata fitina ta săme su, kő kuwa wata azăba
mai raɗăɗi ta săme su.
|
Ayah 24:64 الأية
أَلَا إِنَّ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ قَدْ يَعْلَمُ مَا
أَنتُمْ عَلَيْهِ وَيَوْمَ يُرْجَعُونَ إِلَيْهِ فَيُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوا ۗ
وَاللهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ
Ala inna lillahi ma feeassamawati wal-ardi qadyaAAlamu ma antum AAalayhi wayawma
yurjaAAoona ilayhifayunabbi-ohum bima AAamiloo wallahubikulli shay-in AAaleem
Hausa
To! Lalle Allah ne Yake da mulkin abin da ke a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙa,
Yană sanin abin da kuke a kansa kuma a rănar da ake mayar da su zuwa gare shi,
sai Yană bă su lăbări game da abin da suka aikata. Kuma Allah, ga dukkan kőme,
Masani ne.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|