1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الم
Alif-lam-meem
Hausa
A. L̃. M̃.
|
Ayah 30:2 الأية
غُلِبَتِ الرُّومُ
Ghulibati arroom
Hausa
An rinjãyi Rũmawa.
|
Ayah 30:3 الأية
فِي أَدْنَى الْأَرْضِ وَهُم مِّن بَعْدِ غَلَبِهِمْ سَيَغْلِبُونَ
Fee adna al-ardi wahum minbaAAdi ghalabihim sayaghliboon
Hausa
A cikin mafi kusantar ƙasarsu, kuma sũ, a bãyan rinjãyarsu, zã sn rinjãya.
|
Ayah 30:4 الأية
فِي بِضْعِ سِنِينَ ۗ لِلَّهِ الْأَمْرُ مِن قَبْلُ وَمِن بَعْدُ ۚ وَيَوْمَئِذٍ
يَفْرَحُ الْمُؤْمِنُونَ
Fee bidAAi sineena lillahial-amru min qablu wamin baAAdu wayawma-ithin
yafrahualmu/minoon
Hausa
A cikin'yan shẽkaru. Al'amari na Allah ne a gabãnin kõme da bãyansa, kuma a
rãnar nan mũminai zã su yi farin ciki.
|
Ayah 30:5 الأية
بِنَصْرِ اللهِ ۚ يَنصُرُ مَن يَشَاءُ ۖ وَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ
Binasri Allahi yansuruman yashao wahuwa alAAazeezu arraheem
Hausa
Da taimakon Allah Yanã taimakon wanda Yake so. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin
ƙai.
|
Ayah 30:6 الأية
وَعْدَ اللهِ ۖ لَا يُخْلِفُ اللهُ وَعْدَهُ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا
يَعْلَمُونَ
WaAAda Allahi la yukhlifu AllahuwaAAdahu walakinna akthara annasi layaAAlamoon
Hausa
Wa'adin Allah, Allah bã ya sãɓãwa ga wa'adinsa, kuma amma mafi yawan mutãne ba
su sani ba.
|
Ayah 30:7 الأية
يَعْلَمُونَ ظَاهِرًا مِّنَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَهُمْ عَنِ الْآخِرَةِ هُمْ
غَافِلُونَ
YaAAlamoona thahiranmina alhayati addunya wahum AAanial-akhirati hum ghafiloon
Hausa
Sunã sanin bayyanannar rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sũ shagalallu ne daga rãyuwar
Lãhira.
|
Ayah 30:8 الأية
أَوَلَمْ يَتَفَكَّرُوا فِي أَنفُسِهِم ۗ مَّا خَلَقَ اللهُ السَّمَاوَاتِ
وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَأَجَلٍ مُّسَمًّى ۗ وَإِنَّ
كَثِيرًا مِّنَ النَّاسِ بِلِقَاءِ رَبِّهِمْ لَكَافِرُونَ
Awa lam yatafakkaroo fee anfusihim makhalaqa Allahu assamawati wal-ardawama
baynahuma illa bilhaqqiwaajalin musamman wa-inna katheeran mina annasibiliqa-i
rabbihim lakafiroon
Hausa
Shin, ba su yi tunãni ba a cikin zukãtansu cẽwa Allah bai halitta sammai da ƙasa
ba da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da ajali ambatacce? Kuma lalle mãsu
yawa daga mutãne kãfirai ne ga gamuwa da Ubangijinsu?
|
Ayah 30:9 الأية
أَوَلَمْ يَسِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَيَنظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الَّذِينَ
مِن قَبْلِهِمْ ۚ كَانُوا أَشَدَّ مِنْهُمْ قُوَّةً وَأَثَارُوا الْأَرْضَ
وَعَمَرُوهَا أَكْثَرَ مِمَّا عَمَرُوهَا وَجَاءَتْهُمْ رُسُلُهُم بِالْبَيِّنَاتِ
ۖ فَمَا كَانَ اللهُ لِيَظْلِمَهُمْ وَلَٰكِن كَانُوا أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
Awa lam yaseeroo fee al-ardi fayanthurookayfa kana AAaqibatu allatheena min
qablihimkanoo ashadda minhum quwwatan waatharoo al-ardawaAAamarooha akthara
mimma AAamarooha wajaat-humrusuluhum bilbayyinati fama kana Allahuliyathlimahum
walakin kanoo anfusahumyathlimoon
Hausa
Shin, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã dõmin su gani yadda aƙibar waɗanda
ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafiya ƙarfi daga gare su kuma suka nõmi
ƙasa suka rãya ta fiye da yadda suka raya ta, kuma manzanninsu suka je musu da
hujjoji bayyanannu. Sabo da haka Allah ba Ya yiwuwa Ya zãlunce su, amma kansu
suka kasance sunã zãlunta.
|
Ayah 30:10 الأية
ثُمَّ كَانَ عَاقِبَةَ الَّذِينَ أَسَاءُوا السُّوأَىٰ أَن كَذَّبُوا بِآيَاتِ
اللهِ وَكَانُوا بِهَا يَسْتَهْزِئُونَ
Thumma kana AAaqibata allatheenaasaoo assoo-a an kaththaboo bi-ayatiAllahi
wakanoo biha yastahzi-oon
Hausa
Sa'an nan ãƙibar waɗannan da suka aikata mũgun aiki ta kasance mafi muni, wãtau
sun ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma suka kasance sunã izgili da su.
|
Ayah 30:11 الأية
اللهُ يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ ثُمَّ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Allahu yabdao alkhalqa thummayuAAeeduhu thumma ilayhi turjaAAoon
Hausa
Allah ne ke fãra yin halitta, sa'an nan Ya sãke ta sa'an nan zuwa gare Shi ake
mayar da ku.
|
Ayah 30:12 الأية
وَيَوْمَ تَقُومُ السَّاعَةُ يُبْلِسُ الْمُجْرِمُونَ
Wayawma taqoomu assaAAatuyublisu almujrimoon
Hausa
Kuma a rãnar da sa'a ke tsayuwa, mãsu laifi zã su kãsa magana.
|
Ayah 30:13 الأية
وَلَمْ يَكُن لَّهُم مِّن شُرَكَائِهِمْ شُفَعَاءُ وَكَانُوا بِشُرَكَائِهِمْ
كَافِرِينَ
Walam yakun lahum min shuraka-ihimshufaAAao wakanoo bishuraka-ihim kafireen
Hausa
Kuma bã su da mãsu cẽto daga abũbuwan shirkinsu, kuma snn kasance mãsu
kãfircẽwadaga abũbuwan shirkinsu.
|
Ayah 30:14 الأية
وَيَوْمَ تَقُومُ السَّاعَةُ يَوْمَئِذٍ يَتَفَرَّقُونَ
Wayawma taqoomu assaAAatuyawma-ithin yatafarraqoon
Hausa
Kuma a rãnar da Sa'a ke tsayuwa, a rãnar nan mutãne ke farraba.
|
Ayah 30:15 الأية
فَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَهُمْ فِي رَوْضَةٍ
يُحْبَرُونَ
Faamma allatheena amanoowaAAamiloo assalihati fahum fee rawdatinyuhbaroon
Hausa
To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai to sũ anã
faranta musu rãyuka, a cikin wani lambu.
|
Ayah 30:16 الأية
وَأَمَّا الَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَلِقَاءِ الْآخِرَةِ
فَأُولَٰئِكَ فِي الْعَذَابِ مُحْضَرُونَ
Waamma allatheena kafaroo wakaththaboobi-ayatina waliqa-i al-akhiratifaola-ika
fee alAAathabi muhdaroon
Hausa
Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata, game da ãyõyinMu da kuma haɗuwa da
Rãnar Lãhira, to, waɗancan anã halartar da su a cikin azãba.
|
Ayah 30:17 الأية
فَسُبْحَانَ اللهِ حِينَ تُمْسُونَ وَحِينَ تُصْبِحُونَ
Fasubhana Allahi heenatumsoona waheena tusbihoon
Hausa
Sabõda haka tsarkakẽwa ta tabbata ga Allah a lõkacin da kuke shiga maraice, da
lõkacin da kuke shiga sãfiya.
|
Ayah 30:18 الأية
وَلَهُ الْحَمْدُ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَعَشِيًّا وَحِينَ تُظْهِرُونَ
Walahu alhamdu fee assamawatiwal-ardi waAAashiyyan waheena tuthhiroon
Hausa
Kuma Shĩ ne da gõdiya, a cikin sammai da ƙasã kuma da lõkacin yamma da lõkacin
zawãli.
|
Ayah 30:19 الأية
يُخْرِجُ الْحَيَّ مِنَ الْمَيِّتِ وَيُخْرِجُ الْمَيِّتَ مِنَ الْحَيِّ وَيُحْيِي
الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا ۚ وَكَذَٰلِكَ تُخْرَجُونَ
Yukhriju alhayya mina almayyitiwayukhriju almayyita mina alhayyi wayuhyee
al-ardabaAAda mawtiha wakathalika tukhrajoon
Hausa
Yanã fitar da mai rai daga matacce kuma Yanã fitar da matacce daga mai rai, kuma
Yanã rãyar da ƙasa a bãyan mutuwarta. Kuma haka ake fitar da ku.
|
Ayah 30:20 الأية
وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَكُم مِّن تُرَابٍ ثُمَّ إِذَا أَنتُم بَشَرٌ
تَنتَشِرُونَ
Wamin ayatihi an khalaqakummin turabin thumma itha antum basharun tantashiroon
Hausa
Kuma akwai daga ãyõyinSa, Ya halitta ku daga turɓãya, sai gã ku kun zama mutum,
kunã wãtsuwa.
|
Ayah 30:21 الأية
وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِّتَسْكُنُوا
إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ
لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ
Wamin ayatihi an khalaqa lakummin anfusikum azwajan litaskunoo ilayha
wajaAAalabaynakum mawaddatan warahmatan inna fee thalika laayatinliqawmin
yatafakkaroon
Hausa
Kuma akwai daga ãyõyinsa, Ya halitta muku mãtan aure daga kanku, dõmin ku natsu
zuwa gare ta, kuma Ya sanya sõyayya da rahama a tsakãninku. Lalle a cikin wancan
akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin tunãni.
|
Ayah 30:22 الأية
وَمِنْ آيَاتِهِ خَلْقُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَاخْتِلَافُ أَلْسِنَتِكُمْ
وَأَلْوَانِكُمْ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّلْعَالِمِينَ
Wamin ayatihi khalqu assamawatiwal-ardi wakhtilafu alsinatikumwaalwanikum inna
fee thalika laayatinlilAAalimeen
Hausa
Kuma akwai daga ãyõyinSa halittar sammai da ƙasã da sãɓã, war harsunanku, da
launukanku. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mãsu ilmi.
|
Ayah 30:23 الأية
وَمِنْ آيَاتِهِ مَنَامُكُم بِاللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَابْتِغَاؤُكُم مِّن
فَضْلِهِ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَسْمَعُونَ
Wamin ayatihi manamukumbillayli wannahari wabtighaokummin fadlihi inna fee
thalika laayatinliqawmin yasmaAAoon
Hausa
Kuma akwai daga cikin ãyõyinSa, barcinku a cikin dare da rãna, da nẽmanku ga
falalarsa. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu saurãrãwa.
|
Ayah 30:24 الأية
وَمِنْ آيَاتِهِ يُرِيكُمُ الْبَرْقَ خَوْفًا وَطَمَعًا وَيُنَزِّلُ مِنَ
السَّمَاءِ مَاءً فَيُحْيِي بِهِ الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ
لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ
Wamin ayatihi yureekumualbarqa khawfan watamaAAan wayunazzilu mina assama-imaan
fayuhyee bihi al-arda baAAda mawtihainna fee thalika laayatin liqawminyaAAqiloon
Hausa
Kuma akwai daga cikin ãyõyinSa, Ya nũna muku walƙiya a kan tsõro da ɗammãni kuma
Ya dinga saukar da ruwa daga sama Sa'an nan Ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan
mutuwarta. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu hankaltawa.
|
Ayah 30:25 الأية
وَمِنْ آيَاتِهِ أَن تَقُومَ السَّمَاءُ وَالْأَرْضُ بِأَمْرِهِ ۚ ثُمَّ إِذَا
دَعَاكُمْ دَعْوَةً مِّنَ الْأَرْضِ إِذَا أَنتُمْ تَخْرُجُونَ
Wamin ayatihi an taqooma assamaowal-ardu bi-amrihi thumma itha daAAakumdaAAwatan
mina al-ardi itha antum takhrujoon
Hausa
Kuma akwai daga ãyõyinsa, tsayuwar sama da asƙã bisa umurninsa, sa'an nan idan
Ya kira ku, kira ɗaya, daga ƙasã, sai gã ku kunã fita.
|
Ayah 30:26 الأية
وَلَهُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ كُلٌّ لَّهُ قَانِتُونَ
Walahu man fee assamawatiwal-ardi kullun lahu qanitoon
Hausa
Kuma wanda ke cikin sammai da ƙasã Nãsa ne shi kaɗai. Dukansu mãsu tawãli'u ne a
gare Shi.
|
Ayah 30:27 الأية
وَهُوَ الَّذِي يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ وَهُوَ أَهْوَنُ عَلَيْهِ ۚ
وَلَهُ الْمَثَلُ الْأَعْلَىٰ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ
الْحَكِيمُ
Wahuwa allathee yabdao alkhalqathumma yuAAeeduhu wahuwa ahwanu AAalayhi walahu
almathalu al-aAAlafee assamawati wal-ardiwahuwa alAAazeezu alhakeem
Hausa
Kuma Shĩ ne Wanda Ya fãra halitta, sa'an nan Ya sãke ta kuma sakẽwarta tã fi
sauƙi a gare shi. Kuma Yanã da misãli wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasã
kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
|
Ayah 30:28 الأية
ضَرَبَ لَكُم مَّثَلًا مِّنْ أَنفُسِكُمْ ۖ هَل لَّكُم مِّن مَّا مَلَكَتْ
أَيْمَانُكُم مِّن شُرَكَاءَ فِي مَا رَزَقْنَاكُمْ فَأَنتُمْ فِيهِ سَوَاءٌ
تَخَافُونَهُمْ كَخِيفَتِكُمْ أَنفُسَكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ الْآيَاتِ
لِقَوْمٍ يَعْقِلُونَ
Daraba lakum mathalan min anfusikumhal lakum mimma malakat aymanukum min
shurakaafee ma razaqnakum faantum feehi sawaon takhafoonahumkakheefatikum
anfusakum kathalika nufassilu al-ayatiliqawmin yaAAqiloon
Hausa
Ya bũga muku wani misãli daga kanku. Kõ kunã da abõkan tarẽwa, daga cikin bãyin
da hannãyenku na dãma suka mallaka, a cikin arzikinku, watau ku zama daidai a
ciki kunã tsõron su kamar tSõronku ga kanku? Haka dai Muke bayyana ãyõyi,
daki-daki, ga mutãne mãsu hankaltawa.
|
Ayah 30:29 الأية
بَلِ اتَّبَعَ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَهْوَاءَهُم بِغَيْرِ عِلْمٍ ۖ فَمَن يَهْدِي
مَنْ أَضَلَّ اللهُ ۖ وَمَا لَهُم مِّن نَّاصِرِينَ
Bali ittabaAAa allatheena thalamooahwaahum bighayri AAilmin faman yahdee man
adallaAllahu wama lahum min nasireen
Hausa
Ã'aha! waɗanda suka yi zã1unci sun bi son zũciyõyinsu, bã tãre da wani ilmi ba.
To wãne ne zai shiryar da wanda Allah Ya ɓatar, kuma bã su da waɗansu mataimaka?
|
Ayah 30:30 الأية
فَأَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفًا ۚ فِطْرَتَ اللهِ الَّتِي فَطَرَ النَّاسَ
عَلَيْهَا ۚ لَا تَبْدِيلَ لِخَلْقِ اللهِ ۚ ذَٰلِكَ الدِّينُ الْقَيِّمُ
وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
Faaqim wajhaka liddeeni haneefanfitrata Allahi allatee fatara annasaAAalayha la
tabdeela likhalqi Allahi thalikaaddeenu alqayyimu walakinna akthara annasila
yaAAlamoon
Hausa
Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini, kanã mai karkata zuwa ga gaskiya,
halittar Allah da Ya halitta mutãne a kanta. Bãbu musanyãwa ga halittar Allah,
wannan shĩ ne addini madaidaici kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
|
Ayah 30:31 الأية
مُنِيبِينَ إِلَيْهِ وَاتَّقُوهُ وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَلَا تَكُونُوا مِنَ
الْمُشْرِكِينَ
Muneebeena ilayhi wattaqoohuwaaqeemoo assalata wala takoonoomina almushrikeen
Hausa
Kunã mãsu mai da al'amari gare Shi, kuma ku bĩ Shi dataƙawa, kuma ku tsayar da
salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai.
|
Ayah 30:32 الأية
مِنَ الَّذِينَ فَرَّقُوا دِينَهُمْ وَكَانُوا شِيَعًا ۖ كُلُّ حِزْبٍ بِمَا
لَدَيْهِمْ فَرِحُونَ
Mina allatheena farraqoo deenahum wakanooshiyaAAan kullu hizbin bima ladayhim
farihoon
Hausa
Wãtau waɗanda suka rarrabe addininsu kuma suka kasance ƙungiya-ƙungiya, kõwace
ƙungiya tanã mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai.
|
Ayah 30:33 الأية
وَإِذَا مَسَّ النَّاسَ ضُرٌّ دَعَوْا رَبَّهُم مُّنِيبِينَ إِلَيْهِ ثُمَّ إِذَا
أَذَاقَهُم مِّنْهُ رَحْمَةً إِذَا فَرِيقٌ مِّنْهُم بِرَبِّهِمْ يُشْرِكُونَ
Wa-itha massa annasa durrundaAAaw rabbahum muneebeena ilayhi thumma itha
athaqahumminhu rahmatan itha fareequn minhum birabbihimyushrikoon
Hausa
Kuma idan cũta ta shãfi mutãne, sai su kirãyi Ubangijinsu, sunã mãsu mai da
al'amari gare Shi, sa'an nan idan Ya ɗanɗana musu wata rahama daga gare Shi, sai
gã wani ɓangare daga gare su sunã shirki da Ubangijinsu.
|
Ayah 30:34 الأية
لِيَكْفُرُوا بِمَا آتَيْنَاهُمْ ۚ فَتَمَتَّعُوا فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ
Liyakfuroo bima ataynahumfatamattaAAoo fasawfa taAAlamoon
Hausa
Dõmin su kãfirta dl abin da Muka bã su. To ku ji dãɗi kaɗan Sa'an nan zã ku,
sani.
|
Ayah 30:35 الأية
أَمْ أَنزَلْنَا عَلَيْهِمْ سُلْطَانًا فَهُوَ يَتَكَلَّمُ بِمَا كَانُوا بِهِ
يُشْرِكُونَ
Am anzalna AAalayhim sultananfahuwa yatakallamu bima kanoo bihi yushrikoon
Hausa
Kõ Mun saukar da wani dalĩ li a gare su? Shi kuwa yanã magana da abin da suka
kasance sunã shirkin da shi?
|
Ayah 30:36 الأية
وَإِذَا أَذَقْنَا النَّاسَ رَحْمَةً فَرِحُوا بِهَا ۖ وَإِن تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌ
بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ إِذَا هُمْ يَقْنَطُونَ
Watha athaqna annasarahmatan farihoo biha wa-in tusibhumsayyi-atun bima qaddamat
aydeehim itha hum yaqnatoon
Hausa
Kuma idan Muka ɗanɗana wa mutãne wata rahama, sai su yi farin ciki da ita kuma
idan cũta ta sãme su, sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, sai gã su sunã
yanke ƙauna,
|
Ayah 30:37 الأية
أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّ اللهَ يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاءُ وَيَقْدِرُ ۚ
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Awa lam yaraw anna Allaha yabsutuarrizqa liman yashao wayaqdiru inna fee
thalikalaayatin liqawmin yu/minoon
Hausa
Shin, kuma ba su gani ba cẽwa Allah na shimfida arziki ga wanda Yake so kuma
Yanã ƙuntatãwa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin ĩmãni.
|
Ayah 30:38 الأية
فَآتِ ذَا الْقُرْبَىٰ حَقَّهُ وَالْمِسْكِينَ وَابْنَ السَّبِيلِ ۚ ذَٰلِكَ خَيْرٌ
لِّلَّذِينَ يُرِيدُونَ وَجْهَ اللهِ ۖ وَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ
Faati tha alqurba haqqahuwalmiskeena wabna assabeeli thalikakhayrun lillatheena
yureedoona wajha Allahi waola-ikahumu almuflihoon
Hausa
Sabõda haka ka bai wa zumu hakkinsa da miskĩnai da ɗan hanya, wannan shĩ ne
alhẽri ga waɗanda ke nufin yardar Allah kuma waɗancan sũ ne mãsu sãmun babban
rabo.
|
Ayah 30:39 الأية
وَمَا آتَيْتُم مِّن رِّبًا لِّيَرْبُوَ فِي أَمْوَالِ النَّاسِ فَلَا يَرْبُو
عِندَ اللهِ ۖ وَمَا آتَيْتُم مِّن زَكَاةٍ تُرِيدُونَ وَجْهَ اللهِ
فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُضْعِفُونَ
Wama ataytum min ribanliyarbuwa fee amwali annasi falayarboo AAinda Allahi wama
ataytum min zakatintureedoona wajha Allahi faola-ika humu almudAAifoon
Hausa
Kuma abin da kuka bãyar na riba dõmin ya ƙãru a cikin dũkiyar mutãne to, bã zai
ƙãru ba, a wurin Allah. Kuma abin da kuka bãyar na zakka, kanã nufin yardar
Allah to (mãsu yin haka) waɗancan sũ ne mãsu ninkãwa (ga dũkiyarsu).
|
Ayah 30:40 الأية
اللهُ الَّذِي خَلَقَكُمْ ثُمَّ رَزَقَكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يُحْيِيكُمْ
ۖ هَلْ مِن شُرَكَائِكُم مَّن يَفْعَلُ مِن ذَٰلِكُم مِّن شَيْءٍ ۚ سُبْحَانَهُ
وَتَعَالَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Allahu allathee khalaqakumthumma razaqakum thumma yumeetukum thumma yuhyeekum
halmin shuraka-ikum man yafAAalu min thalikum minshay-in subhanahu wataAAala
AAammayushrikoon
Hausa
Allah ne Wanda Ya halitta ku, sa'an nan Ya azurta ku, sa'an nan Ya matar da ku,
sa'an nan Ya rãyar da ku. Ashe, daga cikin abũbuwan shirkinku akwai wanda ke
aikata wani abu daga waɗannan ahũbuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Ya
ɗaukaka bisa ga abin da suke yi na shirki.
|
Ayah 30:41 الأية
ظَهَرَ الْفَسَادُ فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ بِمَا كَسَبَتْ أَيْدِي النَّاسِ
لِيُذِيقَهُم بَعْضَ الَّذِي عَمِلُوا لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ
Thahara alfasadu feealbarri walbahri bima kasabat aydee annasiliyutheeqahum
baAAda allathee AAamiloolaAAallahum yarjiAAoon
Hausa
¥arnã tã bayyana a cikin ƙasa da tẽku, sabõda abin da hannãyen mutãne suka
aikata. Dõmin Allah Ya ɗanɗana musu sãshin abin da suka aikata, ɗammãninsu zã su
kõmo.
|
Ayah 30:42 الأية
قُلْ سِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَانظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الَّذِينَ مِن
قَبْلُ ۚ كَانَ أَكْثَرُهُم مُّشْرِكِينَ
Qul seeroo fee al-ardi fanthurookayfa kana AAaqibatu allatheena min qablu
kanaaktharuhum mushrikeen
Hausa
Ka ce: "Ku tafi a cikin ƙasã sa'an nan ku dũbi yadda ãƙibar waɗanda suka kasance
a gabãninku ta kasance. Mafi yawansu sun kasance mãsu yin shirki."
|
Ayah 30:43 الأية
فَأَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ الْقَيِّمِ مِن قَبْلِ أَن يَأْتِيَ يَوْمٌ لَّا
مَرَدَّ لَهُ مِنَ اللهِ ۖ يَوْمَئِذٍ يَصَّدَّعُونَ
Faaqim wajhaka liddeeni alqayyimimin qabli an ya/tiya yawmun la maradda lahu
mina Allahiyawma-ithin yassaddaAAoon
Hausa
Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini madaidaici a gabãnin wani yini ya
zo, bãbu makawa gare Shi daga Allah, a rãnar nan mutãne sunã tsãgẽwa (su rabu
biyu).
|
Ayah 30:44 الأية
مَن كَفَرَ فَعَلَيْهِ كُفْرُهُ ۖ وَمَنْ عَمِلَ صَالِحًا فَلِأَنفُسِهِمْ
يَمْهَدُونَ
Man kafara faAAalayhi kufruhu waman AAamila salihanfali-anfusihim yamhadoon
Hausa
Wanda ya kãfirta,to,kãfircinsa na kansa, kuma wanda ya aikata aikin ƙwarai, to,
sabõda kansu suke yin shimfiɗa.
|
Ayah 30:45 الأية
لِيَجْزِيَ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ مِن فَضْلِهِ ۚ إِنَّهُ لَا
يُحِبُّ الْكَافِرِينَ
Liyajziya allatheena amanoowaAAamiloo assalihati min fadlihiinnahu la yuhibbu
alkafireen
Hausa
Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga
falalarSa. Lalle Allah bã Ya son kafirai.
|
Ayah 30:46 الأية
وَمِنْ آيَاتِهِ أَن يُرْسِلَ الرِّيَاحَ مُبَشِّرَاتٍ وَلِيُذِيقَكُم مِّن
رَّحْمَتِهِ وَلِتَجْرِيَ الْفُلْكُ بِأَمْرِهِ وَلِتَبْتَغُوا مِن فَضْلِهِ
وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Wamin ayatihi an yursila arriyahamubashshiratin waliyutheeqakum min
rahmatihiwalitajriya alfulku bi-amrihi walitabtaghoo min fadlihiwalaAAallakum
tashkuroon
Hausa
Kuma akwai daga ãyõyinSa, ya aika iskõki mãsu bãyar da bushãra kuma dõmin Ya
ɗanɗana muku daga rahamarSa, kuma dõmin jirãgen ruwa su gudãna da umurninSa,
kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, fãtanku zã ku gode.
|
Ayah 30:47 الأية
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ رُسُلًا إِلَىٰ قَوْمِهِمْ فَجَاءُوهُم
بِالْبَيِّنَاتِ فَانتَقَمْنَا مِنَ الَّذِينَ أَجْرَمُوا ۖ وَكَانَ حَقًّا
عَلَيْنَا نَصْرُ الْمُؤْمِنِينَ
Walaqad arsalna min qablika rusulanila qawmihim fajaoohum bilbayyinatifantaqamna
mina allatheena ajramoo wakanahaqqan AAalayna nasru almu/mineen
Hausa
Kuma lalle Mun aiki waɗansu Manzanni a gabãninka, zuwa ga mutãnensu sai suka je
musu da hujjõji, bayyanannu, sa'an nan Muka azabtar da waɗanda suka yi laifi,
kuma ya kasance tabbatacce taimakon mũminai wajibi ne a kan mu.
|
Ayah 30:48 الأية
اللهُ الَّذِي يُرْسِلُ الرِّيَاحَ فَتُثِيرُ سَحَابًا فَيَبْسُطُهُ فِي
السَّمَاءِ كَيْفَ يَشَاءُ وَيَجْعَلُهُ كِسَفًا فَتَرَى الْوَدْقَ يَخْرُجُ مِنْ
خِلَالِهِ ۖ فَإِذَا أَصَابَ بِهِ مَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ إِذَا هُمْ
يَسْتَبْشِرُونَ
Allahu allathee yursilu arriyahafatutheeru sahaban fayabsutuhu fee assama-ikayfa
yashao wayajAAaluhu kisafan fatara alwadqayakhruju min khilalihi fa-itha asaba
bihiman yashao min AAibadihi itha humyastabshiroon
Hausa
Allah ne Wanda ke aika iskõki, sai su mõtsar da girgije, sa'an nan Ya shimfiɗa
shi a cikin sama yadda Yake so, kuma Ya sanya shi wani ɓaɓɓake, sa'an nan ka ga
ruwa na fita daga tsakãninsa. Sa'an nan idan Allah Ya sãmi waɗanda Ya so daga
bãyinsa, Sai gã su suna bushãra da shi.
|
Ayah 30:49 الأية
وَإِن كَانُوا مِن قَبْلِ أَن يُنَزَّلَ عَلَيْهِم مِّن قَبْلِهِ لَمُبْلِسِينَ
Wa-in kanoo min qabli an yunazzalaAAalayhim min qablihi lamubliseen
Hausa
Kuma kõ da sun kasance a gabãnin a saukar da shi a kansu, kusa-kusa, sunã baƙin
ciki hai bã su iya magana.
|
Ayah 30:50 الأية
فَانظُرْ إِلَىٰ آثَارِ رَحْمَتِ اللهِ كَيْفَ يُحْيِي الْأَرْضَ بَعْدَ
مَوْتِهَا ۚ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمُحْيِي الْمَوْتَىٰ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ
قَدِيرٌ
Fanthur ila atharirahmati Allahi kayfa yuhyee al-ardabaAAda mawtiha inna thalika
lamuhyee almawtawahuwa AAala kulli shay-in qadeer
Hausa
Sai ka dũbi alãmõmin rahamar Allah yadda Yake rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta.
Lalle wannan (Mai wannan aiki), tabbas, Mai rãyar da halitta ne, kuma Shi Mai
ikon yi ne a kan kõme.
|
Ayah 30:51 الأية
وَلَئِنْ أَرْسَلْنَا رِيحًا فَرَأَوْهُ مُصْفَرًّا لَّظَلُّوا مِن بَعْدِهِ
يَكْفُرُونَ
Wala-in arsalna reehanfaraawhu musfarran lathalloo min baAAdihiyakfuroon
Hausa
Kuma lalle idan Mun aika wata iska, suka ganta fatsifatsi, lalle zã su yini a
bãyansa sunã kãfirta.
|
Ayah 30:52 الأية
فَإِنَّكَ لَا تُسْمِعُ الْمَوْتَىٰ وَلَا تُسْمِعُ الصُّمَّ الدُّعَاءَ إِذَا
وَلَّوْا مُدْبِرِينَ
Fa-innaka la tusmiAAu almawtawala tusmiAAu assumma adduAAaaitha wallaw mudbireen
Hausa
Sabõda haka, kai, bã ka jiyar da matattu kira, kuma bã ka jiyar da kurãme kira
idan sun jũya bãya sunã gudu.
|
Ayah 30:53 الأية
وَمَا أَنتَ بِهَادِ الْعُمْيِ عَن ضَلَالَتِهِمْ ۖ إِن تُسْمِعُ إِلَّا مَن
يُؤْمِنُ بِآيَاتِنَا فَهُم مُّسْلِمُونَ
Wama anta bihadi alAAumyi AAandalalatihim in tusmiAAu illa man yu/minu
bi-ayatinafahum muslimoon
Hausa
Kuma ba ka zamo mai shiryar da makãfi ba daga ɓatarsu, bã ka jiyarwa fãce wanda
ke yin ĩmãni da ãyõyinMu, watau sũ ne mãsu mĩƙa wuya, su sallama.
|
Ayah 30:54 الأية
اللهُ الَّذِي خَلَقَكُم مِّن ضَعْفٍ ثُمَّ جَعَلَ مِن بَعْدِ ضَعْفٍ قُوَّةً
ثُمَّ جَعَلَ مِن بَعْدِ قُوَّةٍ ضَعْفًا وَشَيْبَةً ۚ يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ ۖ
وَهُوَ الْعَلِيمُ الْقَدِيرُ
Allahu allathee khalaqakum mindaAAfin thumma jaAAala min baAAdi daAAfin
quwwatanthumma jaAAala min baAAdi quwwatin daAAfan washaybatanyakhluqu ma yashao
wahuwa alAAaleemu alqadeer
Hausa
Allah ne Ya halitta ku daga rauni, sa'an nan Ya sanya wani ƙarfi a bayan wani
rauni, sa'an nan Ya sanya wani rauni da furfura a bãyan wani ƙarfi, Allah na
halitta abin da Ya so, kuma Shĩ ne Mai ilmi, Mai ĩkon yi,
|
Ayah 30:55 الأية
وَيَوْمَ تَقُومُ السَّاعَةُ يُقْسِمُ الْمُجْرِمُونَ مَا لَبِثُوا غَيْرَ سَاعَةٍ
ۚ كَذَٰلِكَ كَانُوا يُؤْفَكُونَ
Wayawma taqoomu assaAAatuyuqsimu almujrimoona ma labithoo ghayra saAAatin
kathalikakanoo yu/fakoon
Hausa
Kuma a rãnar da Sa'a ke tsayuwa, mãsu laifi na rantsuwã: Ba su zauna a cikin
kabari ba fãce sã'a guda. Kamar haka suka kasance anã karkatar da su.
|
Ayah 30:56 الأية
وَقَالَ الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ وَالْإِيمَانَ لَقَدْ لَبِثْتُمْ فِي كِتَابِ
اللهِ إِلَىٰ يَوْمِ الْبَعْثِ ۖ فَهَٰذَا يَوْمُ الْبَعْثِ وَلَٰكِنَّكُمْ
كُنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ
Waqala allatheena ootooalAAilma wal-eemana laqad labithtum fee kitabiAllahi ila
yawmi albaAAthi fahatha yawmualbaAAthi walakinnakum kuntum la taAAlamoon
Hausa
Kuma waɗanda aka bai wa ilmi da ĩmãni suka ce: "Lalle, haƙĩƙa kun zauna a cikin
Littãfin Allah, har zuwa rãnar tãyarwa, to, kuma wannan ita ce rãnar tãyarwar,
kuma amma kũ, kun kasance ba ku sani ba."
|
Ayah 30:57 الأية
فَيَوْمَئِذٍ لَّا يَنفَعُ الَّذِينَ ظَلَمُوا مَعْذِرَتُهُمْ وَلَا هُمْ
يُسْتَعْتَبُونَ
Fayawma-ithin la yanfaAAu allatheenathalamoo maAAthiratuhum wala
humyustaAAtaboon
Hausa
To, a rãnar da uzurin waɗanda suka yi zãlunci bã ya amfaninsu, kuma bã a neman
yardarsu.
|
Ayah 30:58 الأية
وَلَقَدْ ضَرَبْنَا لِلنَّاسِ فِي هَٰذَا الْقُرْآنِ مِن كُلِّ مَثَلٍ ۚ وَلَئِن
جِئْتَهُم بِآيَةٍ لَّيَقُولَنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا إِنْ أَنتُمْ إِلَّا
مُبْطِلُونَ
Walaqad darabna linnasifee hatha alqur-ani min kulli mathalin wala-inji/tahum
bi-ayatin layaqoolanna allatheena kafarooin antum illa mubtiloon
Hausa
Kuma lalle tabbas Mun buga kõwane irin misãli ga mutãne a cikin wannan
Alƙur'ãni, kuma lalle idan kã je musu da kõwace ãyã, lalle, waɗanda suka kãfirta
zã su ce "Kũ, bã kõme kuke ba fãce mãsu barua."
|
Ayah 30:59 الأية
كَذَٰلِكَ يَطْبَعُ اللهُ عَلَىٰ قُلُوبِ الَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ
Kathalika yatbaAAu AllahuAAala quloobi allatheena la yaAAlamoon
Hausa
Kamar haka Allah Yake shãfe haske a kan zukãtan waɗanda ba su sani ba.
|
Ayah 30:60 الأية
فَاصْبِرْ إِنَّ وَعْدَ اللهِ حَقٌّ ۖ وَلَا يَسْتَخِفَّنَّكَ الَّذِينَ لَا
يُوقِنُونَ
Fasbir inna waAAda Allahihaqqun wala yastakhiffannaka allatheena layooqinoon
Hausa
Sabõda haka ka yi haƙuri lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma kada waɗanda bã su
da yaƙĩni su sassabce maka hankali.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|