1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
Ayah 36:2 الأية
وَالْقُرْآنِ الْحَكِيمِ
Walqur-ani alhakeem
Hausa
Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni Mai hikima.
|
Ayah 36:3 الأية
إِنَّكَ لَمِنَ الْمُرْسَلِينَ
Innaka lamina almursaleen
Hausa
Lalle kai, haƙĩƙa kanã cikinManzanni.
|
Ayah 36:4 الأية
عَلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
AAala siratin mustaqeem
Hausa
A kan hanya madaidaiciya.
|
Ayah 36:5 الأية
تَنزِيلَ الْعَزِيزِ الرَّحِيمِ
Tanzeela alAAazeezi arraheem
Hausa
(Allah Ya saukar da Al-kur'ãni) saukarwar Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
|
Ayah 36:6 الأية
لِتُنذِرَ قَوْمًا مَّا أُنذِرَ آبَاؤُهُمْ فَهُمْ غَافِلُونَ
Litunthira qawman ma onthiraabaohum fahum ghafiloon
Hausa
Dõmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutãne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabõda
haka sũmasu rafkana ne.
|
Ayah 36:7 الأية
لَقَدْ حَقَّ الْقَوْلُ عَلَىٰ أَكْثَرِهِمْ فَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ
Laqad haqqa alqawlu AAalaaktharihim fahum la yu/minoon
Hausa
Lalle, haƙĩƙa, kalma tã wajaba a kan mafi yawansu, dõmin sũ, bã zã su yi ĩmãni
ba.
|
Ayah 36:8 الأية
إِنَّا جَعَلْنَا فِي أَعْنَاقِهِمْ أَغْلَالًا فَهِيَ إِلَى الْأَذْقَانِ فَهُم
مُّقْمَحُونَ
Inna jaAAalna fee aAAnaqihimaghlalan fahiya ila al-athqani fahummuqmahoon
Hausa
Lalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyinsu, sa'an nan sũ (ƙuƙumman sun kai)
har zuwa ga haɓõɓinsu, sabõda haka, sũ banƙararru ne.
|
Ayah 36:9 الأية
وَجَعَلْنَا مِن بَيْنِ أَيْدِيهِمْ سَدًّا وَمِنْ خَلْفِهِمْ سَدًّا
فَأَغْشَيْنَاهُمْ فَهُمْ لَا يُبْصِرُونَ
WajaAAalna min bayni aydeehim saddanwamin khalfihim saddan faaghshaynahum fahum
la yubsiroon
Hausa
Kuma Muka sanya wata tõshiya a gaba gare su, da wata tõshiya a bãyansu, sabõda
haka Muka rufe su, sai suka zama bã su gani.
|
Ayah 36:10 الأية
وَسَوَاءٌ عَلَيْهِمْ أَأَنذَرْتَهُمْ أَمْ لَمْ تُنذِرْهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ
Wasawaon AAalayhim aanthartahumam lam tunthirhum la yu/minoon
Hausa
Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi
ba, sũ bã zã su yi ĩmãni ba.
|
Ayah 36:11 الأية
إِنَّمَا تُنذِرُ مَنِ اتَّبَعَ الذِّكْرَ وَخَشِيَ الرَّحْمَٰنَ بِالْغَيْبِ ۖ
فَبَشِّرْهُ بِمَغْفِرَةٍ وَأَجْرٍ كَرِيمٍ
Innama tunthiru mani ittabaAAaaththikra wakhashiya arrahmanabilghaybi
fabashshirhu bimaghfiratin waajrin kareem
Hausa
Kanã yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ãni ne, kuma ya ji tsõron mai rahama
a fake. To, ka yi masa bushãra da gãfara da wani sakamako na karimci.
|
Ayah 36:12 الأية
إِنَّا نَحْنُ نُحْيِي الْمَوْتَىٰ وَنَكْتُبُ مَا قَدَّمُوا وَآثَارَهُمْ ۚ
وَكُلَّ شَيْءٍ أَحْصَيْنَاهُ فِي إِمَامٍ مُّبِينٍ
Inna nahnu nuhyeealmawta wanaktubu ma qaddamoo waatharahumwakulla shay-in
ahsaynahu fee imamin mubeen
Hausa
Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da
gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani.
|
Ayah 36:13 الأية
وَاضْرِبْ لَهُم مَّثَلًا أَصْحَابَ الْقَرْيَةِ إِذْ جَاءَهَا الْمُرْسَلُونَ
Wadrib lahum mathalan as-habaalqaryati ith jaaha almursaloon
Hausa
Kuma ka buga musu misãli: Waɗansu ma'abũta alƙarya, a lõkacin da Manzanni suka
jẽ mata.
|
Ayah 36:14 الأية
إِذْ أَرْسَلْنَا إِلَيْهِمُ اثْنَيْنِ فَكَذَّبُوهُمَا فَعَزَّزْنَا بِثَالِثٍ
فَقَالُوا إِنَّا إِلَيْكُم مُّرْسَلُونَ
Ith arsalna ilayhimu ithnaynifakaththaboohuma faAAazzazna bithalithinfaqaloo
inna ilaykum mursaloon
Hausa
A lõkacin da Muka aika (Manzannin) biyu zuwa gare su, sai suka ƙaryata su, sa'an
nan Muka ƙarfafa (su) da na uku, sai suka ce: "Lalle mũ, Manzanni ne zuwa gare
ku."
|
Ayah 36:15 الأية
قَالُوا مَا أَنتُمْ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُنَا وَمَا أَنزَلَ الرَّحْمَٰنُ مِن
شَيْءٍ إِنْ أَنتُمْ إِلَّا تَكْذِبُونَ
Qaloo ma antum illabasharun mithluna wama anzala arrahmanumin shay-in in antum
illa takthiboon
Hausa
Suka ce: "Kũ ba ku zamo bafãce mutãne ne kamarmu kuma Mai rahama bai saukar da
kõme ba, ba ku zamo ba fãce ƙarya kuke yi."
|
Ayah 36:16 الأية
قَالُوا رَبُّنَا يَعْلَمُ إِنَّا إِلَيْكُمْ لَمُرْسَلُونَ
Qaloo rabbuna yaAAlamu innailaykum lamursaloon
Hausa
Suka ce: "Ubangijinmu Yã sani, lalle mũ, haƙiƙa Manzanni nezuwa gare ku."
|
Ayah 36:17 الأية
وَمَا عَلَيْنَا إِلَّا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ
Wama AAalayna illaalbalaghu almubeen
Hausa
"Kuma bãbu abin da ke kanmu, fãce iyar da manzanci bayyananne."
|
Ayah 36:18 الأية
قَالُوا إِنَّا تَطَيَّرْنَا بِكُمْ ۖ لَئِن لَّمْ تَنتَهُوا لَنَرْجُمَنَّكُمْ
وَلَيَمَسَّنَّكُم مِّنَّا عَذَابٌ أَلِيمٌ
Qaloo inna tatayyarnabikum la-in lam tantahoo lanarjumannakum walayamassannakum
minnaAAathabun aleem
Hausa
Suka ce: "Lalle mũ munã shu'umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba, haƙĩƙa, zã
mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azãba mai raɗaɗi daga gare mu zã ta shãfe ku."
|
Ayah 36:19 الأية
قَالُوا طَائِرُكُم مَّعَكُمْ ۚ أَئِن ذُكِّرْتُم ۚ بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ
مُّسْرِفُونَ
Qaloo ta-irukum maAAakum a-in thukkirtumbal antum qawmun musrifoon
Hausa
Suka ce: "Shu'umcinku, yanã tãre da ku. Ashe, dõmin an tunãtar da ku? Ã'a, kũ
dai mutãne ne mãsu ƙẽtare haddi."
|
Ayah 36:20 الأية
وَجَاءَ مِنْ أَقْصَى الْمَدِينَةِ رَجُلٌ يَسْعَىٰ قَالَ يَا قَوْمِ اتَّبِعُوا
الْمُرْسَلِينَ
Wajaa min aqsa almadeenatirajulun yasAAa qala ya qawmi ittabiAAooalmursaleen
Hausa
Kuma wani mutum daga mafi nĩsan birnin ya je, yanã tafiya da gaggãwa, ya ce: "Ya
mutãnẽna! Ku bi Manzannin nan.
|
Ayah 36:21 الأية
اتَّبِعُوا مَن لَّا يَسْأَلُكُمْ أَجْرًا وَهُم مُّهْتَدُونَ
IttabiAAoo man la yas-alukum ajranwahum muhtadoon
Hausa
"Ku bi waɗanda bã su tambayar ku wata ijãra kuma sũ shiryayyu ne."
|
Ayah 36:22 الأية
وَمَا لِيَ لَا أَعْبُدُ الَّذِي فَطَرَنِي وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Wama liya la aAAbudu allatheefataranee wa-ilayhi turjaAAoon
Hausa
"Kuma mene ne a gare ni, bã zan bauta wa Wanda Ya ƙãga halittata ba, kuma zuwa
gare Shi ake mayar da ku?"
|
Ayah 36:23 الأية
أَأَتَّخِذُ مِن دُونِهِ آلِهَةً إِن يُرِدْنِ الرَّحْمَٰنُ بِضُرٍّ لَّا تُغْنِ
عَنِّي شَفَاعَتُهُمْ شَيْئًا وَلَا يُنقِذُونِ
Aattakhithu min doonihi alihatanin yuridni arrahmanu bidurrin la tughniAAannee
shafaAAatuhum shay-an wala yunqithoon
Hausa
"Shin, zan riƙi waninSa abũbuwan bautãwa? Idan Mai rahama Ya nufe ni da wata
cũta, to cẽtonsu bã ya amfanĩna da kõme, kuma bã za su iya tsãmar da ni bã."
|
Ayah 36:24 الأية
إِنِّي إِذًا لَّفِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Innee ithan lafee dalalinmubeen
Hausa
"Lalle nĩ, a lõkacin nan, tabbas, inã a cikin ɓata bayyananna."
|
Ayah 36:25 الأية
إِنِّي آمَنتُ بِرَبِّكُمْ فَاسْمَعُونِ
Innee amantu birabbikum fasmaAAoon
Hausa
"Lalle ni, nã yi ĩmãni da Ubangijinku, sabõda haka ku saurãre ni."
|
Ayah 36:26 الأية
قِيلَ ادْخُلِ الْجَنَّةَ ۖ قَالَ يَا لَيْتَ قَوْمِي يَعْلَمُونَ
Qeela odkhuli aljannata qala yalayta qawmee yaAAlamoon
Hausa
Aka ce (masa), "Ka shiga Aljanna." Ya ce, "Dã dai a ce mutãnẽna sunã iya sani."
|
Ayah 36:27 الأية
بِمَا غَفَرَ لِي رَبِّي وَجَعَلَنِي مِنَ الْمُكْرَمِينَ
Bima ghafara lee rabbee wajaAAalaneemina almukrameen
Hausa
"Game da gãfarar da Ubangijjĩna ya yi mini, kuma Ya sanya ni a cikin waɗanda aka
girmama."
|
Ayah 36:28 الأية
وَمَا أَنزَلْنَا عَلَىٰ قَوْمِهِ مِن بَعْدِهِ مِن جُندٍ مِّنَ السَّمَاءِ وَمَا
كُنَّا مُنزِلِينَ
Wama anzalna AAalaqawmihi min baAAdihi min jundin mina assama-i wamakunna
munzileen
Hausa
Kuma ba Mu saukar da waɗansu runduna ba daga sama a kan (halaka) mutãnensa, daga
bãyansa, kuma bã zã Mu kasance. Mãsu saukarwa ba.
|
Ayah 36:29 الأية
إِن كَانَتْ إِلَّا صَيْحَةً وَاحِدَةً فَإِذَا هُمْ خَامِدُونَ
In kanat illa sayhatanwahidatan fa-itha hum khamidoon
Hausa
Ba ta kasance ba face tsawa guda, sa'an nan sai gã su sõmammu.
|
Ayah 36:30 الأية
يَا حَسْرَةً عَلَى الْعِبَادِ ۚ مَا يَأْتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا كَانُوا بِهِ
يَسْتَهْزِئُونَ
Ya hasratan AAalaalAAibadi ma ya/teehim min rasoolin illa kanoobihi yastahzi-oon
Hausa
Yã nadãma a kan bãyĩNa! Wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu
yi masa izgili.
|
Ayah 36:31 الأية
أَلَمْ يَرَوْا كَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّنَ الْقُرُونِ أَنَّهُمْ إِلَيْهِمْ
لَا يَرْجِعُونَ
Alam yaraw kam ahlakna qablahum minaalqurooni annahum ilayhim la yarjiAAoon
Hausa
Ba su gani ba, da yawa Muka halakar da (mutãnen) ƙarnõni a gabãninsu kuma cẽwa
su bã zã su kõmo ba?
|
Ayah 36:32 الأية
وَإِن كُلٌّ لَّمَّا جَمِيعٌ لَّدَيْنَا مُحْضَرُونَ
Wa-in kullun lamma jameeAAun ladaynamuhdaroon
Hausa
Kuma lalle bãbu kõwa fãce waɗanda ake halartarwa ne a wurinMu.
|
Ayah 36:33 الأية
وَآيَةٌ لَّهُمُ الْأَرْضُ الْمَيْتَةُ أَحْيَيْنَاهَا وَأَخْرَجْنَا مِنْهَا
حَبًّا فَمِنْهُ يَأْكُلُونَ
Waayatun lahumu al-ardualmaytatu ahyaynaha waakhrajna minhahabban faminhu
ya/kuloon
Hausa
Kuma ãyã ce a gare su: ¡asã matacciya, Mu rãyar da ita, Mu fitar da ƙwãya daga
gare ta, sai gã shi daga gare ta suke ci.
|
Ayah 36:34 الأية
وَجَعَلْنَا فِيهَا جَنَّاتٍ مِّن نَّخِيلٍ وَأَعْنَابٍ وَفَجَّرْنَا فِيهَا مِنَ
الْعُيُونِ
WajaAAalna feeha jannatinmin nakheelin waaAAnabin wafajjarna feehamina alAAuyoon
Hausa
Kuma Muka sanya, a cikinta (ƙasã), waɗansu gõnaki na dabĩno da inabõbi, kuma
Muka ɓuɓɓugar da ruwa daga marẽmari a cikinta.
|
Ayah 36:35 الأية
لِيَأْكُلُوا مِن ثَمَرِهِ وَمَا عَمِلَتْهُ أَيْدِيهِمْ ۖ أَفَلَا يَشْكُرُونَ
Liya/kuloo min thamarihi wamaAAamilat-hu aydeehim afala yashkuroon
Hausa
Dõmin su ci 'ya'yan itãcensa, alhãli kuwa hannãyensu ba su aikata shi ba. Shin,
to, bã zã su gõdẽ ba?
|
Ayah 36:36 الأية
سُبْحَانَ الَّذِي خَلَقَ الْأَزْوَاجَ كُلَّهَا مِمَّا تُنبِتُ الْأَرْضُ وَمِنْ
أَنفُسِهِمْ وَمِمَّا لَا يَعْلَمُونَ
Subhana allathee khalaqaal-azwaja kullaha mimma tunbitu al-arduwamin anfusihim
wamimma la yaAAlamoon
Hausa
Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya halitta nau'uka, namiji da mace, dukansu, daga
abin da ƙasã ke tsirarwa, kuma daga kansu, kuma daga abin da ba su sani ba.
|
Ayah 36:37 الأية
وَآيَةٌ لَّهُمُ اللَّيْلُ نَسْلَخُ مِنْهُ النَّهَارَ فَإِذَا هُم مُّظْلِمُونَ
Waayatun lahumu allaylu naslakhuminhu annahara fa-itha hum muthlimoon
Hausa
Kuma ãyã ce a gare su: Dare Muna feɗe rãna daga gare shi, sai gã su sunã mãsu
shiga duhu.
|
Ayah 36:38 الأية
وَالشَّمْسُ تَجْرِي لِمُسْتَقَرٍّ لَّهَا ۚ ذَٰلِكَ تَقْدِيرُ الْعَزِيزِ
الْعَلِيمِ
Washshamsu tajree limustaqarrin lahathalika taqdeeru alAAazeezi alAAaleem
Hausa
Kuma rãnã tanã gudãna zuwa ga wani matabbaci nãta. Wannan ƙaddarãwar Mabuwãyi
ne, Masani.
|
Ayah 36:39 الأية
وَالْقَمَرَ قَدَّرْنَاهُ مَنَازِلَ حَتَّىٰ عَادَ كَالْعُرْجُونِ الْقَدِيمِ
Walqamara qaddarnahu manazilahatta AAada kalAAurjooni alqadeem
Hausa
Kuma da watã Mun ƙaddara masa manzilõli, har ya kõma kamar tsumagiyar murlin
dabĩno wadda ta tsũfa.
|
Ayah 36:40 الأية
لَا الشَّمْسُ يَنبَغِي لَهَا أَن تُدْرِكَ الْقَمَرَ وَلَا اللَّيْلُ سَابِقُ
النَّهَارِ ۚ وَكُلٌّ فِي فَلَكٍ يَسْبَحُونَ
La ashshamsu yanbaghee lahaan tudrika alqamara wala allaylu sabiqu
annahariwakullun fee falakin yasbahoon
Hausa
Rãnã bã ya kamãta a gare ta, ta riski watã. Kuma dare bã ya kamãta a gare shi ya
zama mai tsẽre wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo.
|
Ayah 36:41 الأية
وَآيَةٌ لَّهُمْ أَنَّا حَمَلْنَا ذُرِّيَّتَهُمْ فِي الْفُلْكِ الْمَشْحُونِ
Waayatun lahum anna hamalnathurriyyatahum fee alfulki almashhoon
Hausa
Kuma ãyã ce a gare su. Lalle Mũ, Mun ɗauki zuriyarsu a cikin jirgin, wanda aka
yi wa lõdi.
|
Ayah 36:42 الأية
وَخَلَقْنَا لَهُم مِّن مِّثْلِهِ مَا يَرْكَبُونَ
Wakhalaqna lahum min mithlihi mayarkaboon
Hausa
Kuma Muka halitta musu, daga irinsa, abin da suke hawa.
|
Ayah 36:43 الأية
وَإِن نَّشَأْ نُغْرِقْهُمْ فَلَا صَرِيخَ لَهُمْ وَلَا هُمْ يُنقَذُونَ
Wa-in nasha/ nughriqhum fala sareekhalahum wala hum yunqathoon
Hausa
Kuma idan Mun so, zã Mu nutsar da su, har bãbu kururuwar neman ãgaji, a gare su,
kuma ba su zama anã tsirar da su ba.
|
Ayah 36:44 الأية
إِلَّا رَحْمَةً مِّنَّا وَمَتَاعًا إِلَىٰ حِينٍ
Illa rahmatan minnawamataAAan ila heen
Hausa
Sai fa bisa ga wata rahama daga gare Mu, da jiyarwa dãɗi zuwa ga wani ɗan
lõkaci.
|
Ayah 36:45 الأية
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ اتَّقُوا مَا بَيْنَ أَيْدِيكُمْ وَمَا خَلْفَكُمْ
لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ
Wa-itha qeela lahumu ittaqoo mabayna aydeekum wama khalfakum laAAallakum
turhamoon
Hausa
Kuma idan aka ce musu, "Ku kãre abin da ke a gaba gare ku da abin da yake a
bãyanku, dõmin tsammãninku a ji tausayinku."
|
Ayah 36:46 الأية
وَمَا تَأْتِيهِم مِّنْ آيَةٍ مِّنْ آيَاتِ رَبِّهِمْ إِلَّا كَانُوا عَنْهَا
مُعْرِضِينَ
Wama ta/teehim min ayatin min ayatirabbihim illa kanoo AAanha muAArideen
Hausa
Kuma wata ãyã daga ãyõyin Ubangijinsu bã ta zuwa a gare su, sai sun kasance sunã
mãsu bijirẽwa daga gare ta.
|
Ayah 36:47 الأية
وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ أَنفِقُوا مِمَّا رَزَقَكُمُ اللهُ قَالَ الَّذِينَ
كَفَرُوا لِلَّذِينَ آمَنُوا أَنُطْعِمُ مَن لَّوْ يَشَاءُ اللهُ أَطْعَمَهُ إِنْ
أَنتُمْ إِلَّا فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Wa-itha qeela lahum anfiqoo mimmarazaqakumu Allahu qala allatheena
kafaroolillatheena amanoo anutAAimu man law yashaoAllahu atAAamahu in antum illa
fee dalalinmubeen
Hausa
Kuma idan aka ce musu, "Ku ciyar daga abin da Allah Ya azurta ku," sai waɗanda
suka kãfirta su ce ga waɗanda suka yi ĩmãni, "Ashe, zã mu ciyar da wanda idan
Allah Ya so Yanã ciyar da shi? Ba ku zama ba fãce a cikin ɓata bayyananniya."
|
Ayah 36:48 الأية
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا الْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Wayaqooloona mata hathaalwaAAdu in kuntum sadiqeen
Hausa
Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi yake (aukuwa) idan kun kasance mãsu
gaskiya?"
|
Ayah 36:49 الأية
مَا يَنظُرُونَ إِلَّا صَيْحَةً وَاحِدَةً تَأْخُذُهُمْ وَهُمْ يَخِصِّمُونَ
Ma yanthuroona illasayhatan wahidatan ta/khuthuhum wahumyakhissimoon
Hausa
Bã su jiran (kõme) fãce wata tsãwa guda, zã ta kãma su, alhãli kuwa sunã yin
husũma.
|
Ayah 36:50 الأية
فَلَا يَسْتَطِيعُونَ تَوْصِيَةً وَلَا إِلَىٰ أَهْلِهِمْ يَرْجِعُونَ
Fala yastateeAAoona tawsiyatanwala ila ahlihim yarjiAAoon
Hausa
Bã zã su iya yin wasiyya ba, kuma bã zã su iya kõmãwa zuwa ga iyãlansu ba.
|
Ayah 36:51 الأية
وَنُفِخَ فِي الصُّورِ فَإِذَا هُم مِّنَ الْأَجْدَاثِ إِلَىٰ رَبِّهِمْ يَنسِلُونَ
Wanufikha fee assoori fa-ithahum mina al-ajdathi ila rabbihim yansiloon
Hausa
Kuma aka yi bũsa a cikin ƙaho, to, sai gã su, daga kaburbura zuwa ga
Ubangijinsu, sunã ta gudu.
|
Ayah 36:52 الأية
قَالُوا يَا وَيْلَنَا مَن بَعَثَنَا مِن مَّرْقَدِنَا ۜ ۗ هَٰذَا مَا وَعَدَ
الرَّحْمَٰنُ وَصَدَقَ الْمُرْسَلُونَ
Qaloo ya waylana manbaAAathana min marqadina hatha mawaAAada arrahmanu
wasadaqaalmursaloon
Hausa
Suka ce: "Yã bonenmu! Wãne ne ya tãyar da mu daga barcinmu?" "Wannan shi ne abin
da Mai rahama ya yi wa'adi da shi, kuma Manzanni sun yi gaskiya."
|
Ayah 36:53 الأية
إِن كَانَتْ إِلَّا صَيْحَةً وَاحِدَةً فَإِذَا هُمْ جَمِيعٌ لَّدَيْنَا
مُحْضَرُونَ
In kanat illa sayhatanwahidatan fa-itha hum jameeAAun ladayna muhdaroon
Hausa
Ba ta kasance ba fãce wata tsãwa ce guda, sai gã su duka, sunã abin halartarwa a
gare Mu.
|
Ayah 36:54 الأية
فَالْيَوْمَ لَا تُظْلَمُ نَفْسٌ شَيْئًا وَلَا تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنتُمْ
تَعْمَلُونَ
Falyawma la tuthlamunafsun shay-an wala tujzawna illa ma kuntumtaAAmaloon
Hausa
To, a yau, bã zã a zãlunci wani rai da kõme ba. Kuma bã zã a sãkã muku ba fãce
da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
|
Ayah 36:55 الأية
إِنَّ أَصْحَابَ الْجَنَّةِ الْيَوْمَ فِي شُغُلٍ فَاكِهُونَ
Inna as-haba aljannati alyawmafee shughulin fakihoon
Hausa
Lalle, 'yan Aljanna, a yau, sunã cikin shagali, sunã mãsu nishãɗi.
|
Ayah 36:56 الأية
هُمْ وَأَزْوَاجُهُمْ فِي ظِلَالٍ عَلَى الْأَرَائِكِ مُتَّكِئُونَ
Hum waazwajuhum fee thilalinAAala al-ara-iki muttaki-oon
Hausa
Sũ da mãtan aurensu sunã cikin inuwõwi, a kan karagai, sunã mãsu gincira.
|
Ayah 36:57 الأية
لَهُمْ فِيهَا فَاكِهَةٌ وَلَهُم مَّا يَدَّعُونَ
Lahum feeha fakihatun walahumma yaddaAAoon
Hausa
Sunã da, 'ya'yan itãcen marmari a cikinta kuma sunã sãmun abin da suke kiran a
kãwo.
|
Ayah 36:58 الأية
سَلَامٌ قَوْلًا مِّن رَّبٍّ رَّحِيمٍ
Salamun qawlan min rabbin raheem
Hausa
"Aminci," da magana, daga Ubangiji Mai jin ƙai.
|
Ayah 36:59 الأية
وَامْتَازُوا الْيَوْمَ أَيُّهَا الْمُجْرِمُونَ
Wamtazoo alyawma ayyuhaalmujrimoon
Hausa
"Ku rarrabe dabam, a yau, yã kũ mãsu laifi!"
|
Ayah 36:60 الأية
أَلَمْ أَعْهَدْ إِلَيْكُمْ يَا بَنِي آدَمَ أَن لَّا تَعْبُدُوا الشَّيْطَانَ ۖ
إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُّبِينٌ
Alam aAAhad ilaykum ya banee adamaan la taAAbudoo ashshaytana innahu
lakumAAaduwwun mubeen
Hausa
"Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, yã ɗiyan Ãdamu? Cẽwa kada ku bauta wa
Shaiɗan, lalle shĩ, maƙiyi ne a gareku bayyananne?"
|
Ayah 36:61 الأية
وَأَنِ اعْبُدُونِي ۚ هَٰذَا صِرَاطٌ مُّسْتَقِيمٌ
Waani oAAbudoonee hatha siratunmustaqeem
Hausa
"Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya."
|
Ayah 36:62 الأية
وَلَقَدْ أَضَلَّ مِنكُمْ جِبِلًّا كَثِيرًا ۖ أَفَلَمْ تَكُونُوا تَعْقِلُونَ
Walaqad adalla minkum jibillankatheeran afalam takoonoo taAAqiloon
Hausa
"Kuma lalle haƙĩƙa, (Shaiɗan) yã ɓatar da jama'a mãsu yawa daga gare ku. Ashe to
ba ku kasance kunã yin hankali ba?"
|
Ayah 36:63 الأية
هَٰذِهِ جَهَنَّمُ الَّتِي كُنتُمْ تُوعَدُونَ
Hathihi jahannamu allatee kuntumtooAAadoon
Hausa
"Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance anã yi muku wa'adi da ita."
|
Ayah 36:64 الأية
اصْلَوْهَا الْيَوْمَ بِمَا كُنتُمْ تَكْفُرُونَ
Islawha alyawma bimakuntum takfuroon
Hausa
"Ku shigẽ ta a yau, sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci."
|
Ayah 36:65 الأية
الْيَوْمَ نَخْتِمُ عَلَىٰ أَفْوَاهِهِمْ وَتُكَلِّمُنَا أَيْدِيهِمْ وَتَشْهَدُ
أَرْجُلُهُم بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ
Alyawma nakhtimu AAala afwahihimwatukallimuna aydeehim watashhadu arjuluhum bima
kanooyaksiboon
Hausa
A yau, Munã sanya hãtimin rufi a kan bãkunansu, kuma hannãyensu su yi Mana
magana, kuma ƙafãfunsu su yi shaidu da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
|
Ayah 36:66 الأية
وَلَوْ نَشَاءُ لَطَمَسْنَا عَلَىٰ أَعْيُنِهِمْ فَاسْتَبَقُوا الصِّرَاطَ
فَأَنَّىٰ يُبْصِرُونَ
Walaw nashao latamasnaAAala aAAyunihim fastabaqoo assiratafaanna yubsiroon
Hausa
Dã Mun so, dã Mun shãfe gani daga idãnunsu, sai su yi tsẽre ga hanya, to, yaya
zã su yi gani?
|
Ayah 36:67 الأية
وَلَوْ نَشَاءُ لَمَسَخْنَاهُمْ عَلَىٰ مَكَانَتِهِمْ فَمَا اسْتَطَاعُوا مُضِيًّا
وَلَا يَرْجِعُونَ
Walaw nashao lamasakhnahumAAala makanatihim fama istataAAoo mudiyyanwala
yarjiAAoon
Hausa
Kuma da Mun so, da Mun juyar da halittarsu a kan halinsu, saboda haka ba zã su
iya shuɗewa ba, kuma ba zã su komo ba.
|
Ayah 36:68 الأية
وَمَن نُّعَمِّرْهُ نُنَكِّسْهُ فِي الْخَلْقِ ۖ أَفَلَا يَعْقِلُونَ
Waman nuAAammirhu nunakkis-hu fee alkhalqiafala yaAAqiloon
Hausa
Kuma wanda Muka rãya shi, Manã sunkuyar da shi ga halittarsa. Ashe, bã su
hankalta?
|
Ayah 36:69 الأية
وَمَا عَلَّمْنَاهُ الشِّعْرَ وَمَا يَنبَغِي لَهُ ۚ إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ
وَقُرْآنٌ مُّبِينٌ
Wama AAallamnahu ashshiAArawama yanbaghee lahu in huwa illa thikrunwaqur-anun
mubeen
Hausa
Ba Mu sanar da shi (Annabi) wãkã ba, kuma wãkã ba ta kamãta da shi (Annabi) ba.
Shi (Al-ƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ce, da abin karãtu bayyananne.
|
Ayah 36:70 الأية
لِّيُنذِرَ مَن كَانَ حَيًّا وَيَحِقَّ الْقَوْلُ عَلَى الْكَافِرِينَ
Liyunthira man kana hayyanwayahiqqa alqawlu AAala alkafireen
Hausa
Dõmin ya yi gargaɗi ga wanda ya kasance mai rai, kuma magana ta wajaba a kan
kãfirai.
|
Ayah 36:71 الأية
أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّا خَلَقْنَا لَهُم مِّمَّا عَمِلَتْ أَيْدِينَا أَنْعَامًا
فَهُمْ لَهَا مَالِكُونَ
Awa lam yaraw anna khalaqnalahum mimma AAamilat aydeena anAAaman fahumlaha
malikoon
Hausa
Shin, ba su gani ba (cẽwa) lalle Mun halitta musu dabbõbi daga abin da
HannayenMu suka aikata, sai sunã mallakar su?
|
Ayah 36:72 الأية
وَذَلَّلْنَاهَا لَهُمْ فَمِنْهَا رَكُوبُهُمْ وَمِنْهَا يَأْكُلُونَ
Wathallalnaha lahumfaminha rakoobuhum waminha ya/kuloon
Hausa
Kuma Muka hõre su, sabõda su, sabõda haka daga gare su abin hawansu yake, kuma
daga gare su suke ci.
|
Ayah 36:73 الأية
وَلَهُمْ فِيهَا مَنَافِعُ وَمَشَارِبُ ۖ أَفَلَا يَشْكُرُونَ
Walahum feeha manafiAAu wamasharibuafala yashkuroon
Hausa
Kuma sunã da waɗansu amfãnõni a cikinsu, da abũbuwan shã. Ashe fa, bã zã; su
gõdẽ ba?
|
Ayah 36:74 الأية
وَاتَّخَذُوا مِن دُونِ اللهِ آلِهَةً لَّعَلَّهُمْ يُنصَرُونَ
Wattakhathoo min dooni Allahialihatan laAAallahum yunsaroon
Hausa
Kuma suka riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa wanin Allah, ɗammãninsu zã su taimake
su.
|
Ayah 36:75 الأية
لَا يَسْتَطِيعُونَ نَصْرَهُمْ وَهُمْ لَهُمْ جُندٌ مُّحْضَرُونَ
La yastateeAAoona nasrahumwahum lahum jundun muhdaroon
Hausa
Bã zã su iya taimakonsu ba, alhãli kuwa sũ runduna ce wadda ake halartarwa (a
cikin wutã).
|
Ayah 36:76 الأية
فَلَا يَحْزُنكَ قَوْلُهُمْ ۘ إِنَّا نَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ
Fala yahzunka qawluhum innanaAAlamu ma yusirroona wama yuAAlinoon
Hausa
Sabõda haka, kada maganarsu ta ɓãta maka rai. Lalle Mũ, Munã sanin abin da suke
asirtãwa da abin da suke bayyanãwa.
|
Ayah 36:77 الأية
أَوَلَمْ يَرَ الْإِنسَانُ أَنَّا خَلَقْنَاهُ مِن نُّطْفَةٍ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٌ
مُّبِينٌ
Awa lam yara al-insanu annakhalaqnahu min nutfatin fa-itha huwa khaseemunmubeen
Hausa
Ashe, kuma mutum bai ga (cẽwa) lalle Mũ, Mun halitta shi daga maniyyi ba, sai gã
shi mai yawan husũma, mai bayyanãwar husũmar.
|
Ayah 36:78 الأية
وَضَرَبَ لَنَا مَثَلًا وَنَسِيَ خَلْقَهُ ۖ قَالَ مَن يُحْيِي الْعِظَامَ وَهِيَ
رَمِيمٌ
Wadaraba lana mathalanwanasiya khalqahu qala man yuhyee alAAithamawahiya rameem
Hausa
Kuma ya buga Mana wani misãli, kuma ya manta da halittarsa, ya ce: "Wãne ne ke
rãyar da ƙasũsuwa alhãli kuwa sunã rududdugaggu?"
|
Ayah 36:79 الأية
قُلْ يُحْيِيهَا الَّذِي أَنشَأَهَا أَوَّلَ مَرَّةٍ ۖ وَهُوَ بِكُلِّ خَلْقٍ
عَلِيمٌ
Qul yuhyeeha allatheeanshaaha awwala marratin wahuwa bikulli khalqin AAaleem
Hausa
Ka ce: "Wanda ya ƙãga halittarsu a farkon lõkaci Shĩ ke rãyar da su, kuma Shi,
game da kõwace halitta, Mai ilmi ne."
|
Ayah 36:80 الأية
الَّذِي جَعَلَ لَكُم مِّنَ الشَّجَرِ الْأَخْضَرِ نَارًا فَإِذَا أَنتُم مِّنْهُ
تُوقِدُونَ
Allathee jaAAala lakum mina ashshajarial-akhdari naran fa-itha antum
minhutooqidoon
Hausa
"Wanda ya sanya muku wutã daga itãce kõre, sai gã ku kunã kunnãwa daga gare
shi."
|
Ayah 36:81 الأية
أَوَلَيْسَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِقَادِرٍ عَلَىٰ أَن
يَخْلُقَ مِثْلَهُم ۚ بَلَىٰ وَهُوَ الْخَلَّاقُ الْعَلِيمُ
Awa laysa allathee khalaqa assamawatiwal-arda biqadirin AAala an
yakhluqamithlahum bala wahuwa alkhallaqu alAAaleem
Hausa
"Shin, kuma Wanda Ya halitta sammai da ƙasã bai zama Mai ĩkon yi ba ga Ya
halitta kwatankwacinsu? Na'am, zai iya! Kuma Shĩ Mai yawan halittãwa ne,Mai
ilmi."
|
Ayah 36:82 الأية
إِنَّمَا أَمْرُهُ إِذَا أَرَادَ شَيْئًا أَن يَقُولَ لَهُ كُن فَيَكُونُ
Innama amruhu itha aradashay-an an yaqoola lahu kun fayakoon
Hausa
UmurninSa idan Yã yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, "Ka kasance," sai yana
kasancewa (kamar yadda Yake nufi).
|
Ayah 36:83 الأية
فَسُبْحَانَ الَّذِي بِيَدِهِ مَلَكُوتُ كُلِّ شَيْءٍ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Fasubhana allathee biyadihimalakootu kulli shay-in wa-ilayhi turjaAAoon
Hausa
Sabõda haka, tsarki yã tabbata ga Wanda mallakar kõwane abu take ga HannãyenSa,
kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|