1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
ص ۚ وَالْقُرْآنِ ذِي الذِّكْرِ
Sad walqur-ani theeaththikr
Hausa
Ṣ̃, Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni mai hukunce-hukunce.
|
Ayah 38:2 الأية
بَلِ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي عِزَّةٍ وَشِقَاقٍ
Bali allatheena kafaroo fee AAizzatinwashiqaq
Hausa
Ã'a, waɗanda suka kãfirta sunã cikin girman kai (ga rikon al'ãdunsu) da sãɓãni
(tsakãnin jũnansu).
|
Ayah 38:3 الأية
كَمْ أَهْلَكْنَا مِن قَبْلِهِم مِّن قَرْنٍ فَنَادَوا وَّلَاتَ حِينَ مَنَاصٍ
Kam ahlakna min qablihim min qarninfanadaw walata heena manas
Hausa
Da yawa Muka halakar da wani ƙarni, a gabãninsu, suka yi kira (nẽman cẽto), bãbu
lõkacin kuɓucewa.
|
Ayah 38:4 الأية
وَعَجِبُوا أَن جَاءَهُم مُّنذِرٌ مِّنْهُمْ ۖ وَقَالَ الْكَافِرُونَ هَٰذَا
سَاحِرٌ كَذَّابٌ
WaAAajiboo an jaahum munthirunminhum waqala alkafiroona hatha sahirunkaththab
Hausa
Kuma suka yi mãmãki dõmin Mai gargaɗi, daga cikinsu, ya je musu. Kuma kãfirai
sukace, "Wannan mai sihiri ne, maƙaryaci."
|
Ayah 38:5 الأية
أَجَعَلَ الْآلِهَةَ إِلَٰهًا وَاحِدًا ۖ إِنَّ هَٰذَا لَشَيْءٌ عُجَابٌ
AjaAAala al-alihata ilahan wahidaninna hatha lashay-on AAujab
Hausa
"Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu
ne mai ban mãmaki!"
|
Ayah 38:6 الأية
وَانطَلَقَ الْمَلَأُ مِنْهُمْ أَنِ امْشُوا وَاصْبِرُوا عَلَىٰ آلِهَتِكُمْ ۖ
إِنَّ هَٰذَا لَشَيْءٌ يُرَادُ
Wantalaqa almalao minhum aniimshoo wasbiroo AAala alihatikuminna hatha lashay-on
yurad
Hausa
Shũgabanni daga cikinsu, suka tafi (suka ce),"Ku yi tafiyarku, ku yi haƙuri a
kan abũbuwan bautawarku. Lalle wannan, haƙiƙa, wani abu ne ake nufi!"
|
Ayah 38:7 الأية
مَا سَمِعْنَا بِهَٰذَا فِي الْمِلَّةِ الْآخِرَةِ إِنْ هَٰذَا إِلَّا اخْتِلَاقٌ
Ma samiAAna bihatha feealmillati al-akhirati in hatha illa ikhtilaq
Hausa
"Ba mu taɓa ji ba, game da wannan a cikin addinin ƙarshe. Wannan bai zama ba
fãce ƙiren ƙarya."
|
Ayah 38:8 الأية
أَأُنزِلَ عَلَيْهِ الذِّكْرُ مِن بَيْنِنَا ۚ بَلْ هُمْ فِي شَكٍّ مِّن ذِكْرِي ۖ
بَل لَّمَّا يَذُوقُوا عَذَابِ
Aonzila AAalayhi aththikru minbaynina bal hum fee shakkin min thikree bal
lammayathooqoo AAathab
Hausa
"Shin, an saukar da Alƙur'ãni ne a kansa, a tsakãninmu (mũ kuma ba mu gani ba
)?" Ã'a, su dai sunã cikin shakka daga hukunciNa Ã'a, ba su i da ɗanɗanar azãba
ba.
|
Ayah 38:9 الأية
أَمْ عِندَهُمْ خَزَائِنُ رَحْمَةِ رَبِّكَ الْعَزِيزِ الْوَهَّابِ
Am AAindahum khaza-inu rahmatirabbika alAAazeezi alwahhab
Hausa
Ko kuma a wurinsu ne ake ajiye taskõkin rahamar Ubangijinka, Mabuwãyi, Mai yawan
kyauta?
|
Ayah 38:10 الأية
أَمْ لَهُم مُّلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ فَلْيَرْتَقُوا
فِي الْأَسْبَابِ
Am lahum mulku assamawatiwal-ardi wama baynahuma falyartaqoofee al-asbab
Hausa
Kõ kuma sũ ne da mallakar sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu? To sai su
hau a cikin sammai (dõmin, su hana saukar Alƙur'ãni ga Muhammadu).
|
Ayah 38:11 الأية
جُندٌ مَّا هُنَالِكَ مَهْزُومٌ مِّنَ الْأَحْزَابِ
Jundun ma hunalika mahzoomunmina al-ahzab
Hausa
Rundunõni ne abin da ke can, rusassu, na ƙungiyõyinsu.
|
Ayah 38:12 الأية
كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ وَعَادٌ وَفِرْعَوْنُ ذُو الْأَوْتَادِ
Kaththabat qablahum qawmu noohinwaAAadun wafirAAawnu thoo al-awtad
Hausa
Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, da Ãdãwa da Fir'auna mai turãkun (da suka
kafe mulkinsa).
|
Ayah 38:13 الأية
وَثَمُودُ وَقَوْمُ لُوطٍ وَأَصْحَابُ الْأَيْكَةِ ۚ أُولَٰئِكَ الْأَحْزَابُ
Wathamoodu waqawmu lootin waas-habual-aykati ola-ika al-ahzab
Hausa
Da Samũdãwa da mutãnen Luɗu da ma'abũta ƙunci, waɗancan ne ƙungiyõyin.
|
Ayah 38:14 الأية
إِن كُلٌّ إِلَّا كَذَّبَ الرُّسُلَ فَحَقَّ عِقَابِ
In kullun illa kaththaba arrusulafahaqqa AAiqab
Hausa
Bãbu kõwa a cikinsu fãce ya ƙaryata Manzanni, sabõda haka azãbãTa ta wajaba.
|
Ayah 38:15 الأية
وَمَا يَنظُرُ هَٰؤُلَاءِ إِلَّا صَيْحَةً وَاحِدَةً مَّا لَهَا مِن فَوَاقٍ
Wama yanthuru haola-iilla sayhatan wahidatan ma lahamin fawaq
Hausa
Kuma waɗannan bã su jiran kõme fãce tsãwã guda, wadda bã ta da hani.
|
Ayah 38:16 الأية
وَقَالُوا رَبَّنَا عَجِّل لَّنَا قِطَّنَا قَبْلَ يَوْمِ الْحِسَابِ
Waqaloo rabbana AAajjil lanaqittana qabla yawmi alhisab
Hausa
Kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka gaggauta mana da rabonmu, a gabãnin rãnar
bincike."
|
Ayah 38:17 الأية
اصْبِرْ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَاذْكُرْ عَبْدَنَا دَاوُودَ ذَا الْأَيْدِ ۖ
إِنَّهُ أَوَّابٌ
Isbir AAala mayaqooloona wathkur AAabdana dawooda thaal-aydi innahu awwab
Hausa
Ka yi haƙuri bisa ga abin da suke faɗa (na izgili), kuma ka ambaci bãwanMu
Dãwũda ma'abũcin ƙarfin ibãda. Lalle, shi, mai mayar da al'amari ga Allah ne.
|
Ayah 38:18 الأية
إِنَّا سَخَّرْنَا الْجِبَالَ مَعَهُ يُسَبِّحْنَ بِالْعَشِيِّ وَالْإِشْرَاقِ
Inna sakhkharna aljibalamaAAahu yusabbihna bilAAashiyyi wal-ishraq
Hausa
Lalle Mũ, Mun hõre duwãtsu tãre da shi, sunã yin tasbĩhi maraice da fitõwar
rãnã.
|
Ayah 38:19 الأية
وَالطَّيْرَ مَحْشُورَةً ۖ كُلٌّ لَّهُ أَوَّابٌ
Wattayra mahshooratankullun lahu awwab
Hausa
Da tsuntsãye waɗanda ake tattarawa, kõwannensu mai kõmãwa ne a gare shi.
|
Ayah 38:20 الأية
وَشَدَدْنَا مُلْكَهُ وَآتَيْنَاهُ الْحِكْمَةَ وَفَصْلَ الْخِطَابِ
Washadadna mulkahu waataynahualhikmata wafasla alkhitab
Hausa
Kuma Muka ƙarfafa mulkinsa, kuma Muka bã shi hikima da rarrabẽwar magana.
|
Ayah 38:21 الأية
وَهَلْ أَتَاكَ نَبَأُ الْخَصْمِ إِذْ تَسَوَّرُوا الْمِحْرَابَ
Wahal ataka nabao alkhasmi ithtasawwaroo almihrab
Hausa
Kuma shin, lãbãrin mãsu husũma ya zo maka, a lõkacin da suka haura gãrun
masallaci?
|
Ayah 38:22 الأية
إِذْ دَخَلُوا عَلَىٰ دَاوُودَ فَفَزِعَ مِنْهُمْ ۖ قَالُوا لَا تَخَفْ ۖ خَصْمَانِ
بَغَىٰ بَعْضُنَا عَلَىٰ بَعْضٍ فَاحْكُم بَيْنَنَا بِالْحَقِّ وَلَا تُشْطِطْ
وَاهْدِنَا إِلَىٰ سَوَاءِ الصِّرَاطِ
Ith dakhaloo AAala dawoodafafaziAAa minhum qaloo la takhaf khasmanibagha
baAAduna AAala baAAdinfahkum baynana bilhaqqi walatushtit wahdina ila
sawa-iassirat
Hausa
A lõkacin da suka shiga ga Dãwũda, sai ya firgita daga gare su. Suka ce: "Kada
kaji tsõro, masu husuma biyu ne; sãshenmu ya zãlunci sãshe. Sabõda haka, ka yi
hakunci a tsakãninmu da gaskiya. Kada ka ƙẽtare haddi kuma ka shiryar da mu
zuwa, ga tsakar hanya."
|
Ayah 38:23 الأية
إِنَّ هَٰذَا أَخِي لَهُ تِسْعٌ وَتِسْعُونَ نَعْجَةً وَلِيَ نَعْجَةٌ وَاحِدَةٌ
فَقَالَ أَكْفِلْنِيهَا وَعَزَّنِي فِي الْخِطَابِ
Inna hatha akhee lahu tisAAunwatisAAoona naAAjatan waliya naAAjatun wahidatun
faqalaakfilneeha waAAazzanee fee alkhitab
Hausa
"Lalle wannan dan'uwãna ne, yanã da tunkiya casa'in da tara, kuma inã da tunkiya
guda, sai ya ce: 'Ka lãmunce mini ita. Kuma ya buwãye ni ga magana."
|
Ayah 38:24 الأية
قَالَ لَقَدْ ظَلَمَكَ بِسُؤَالِ نَعْجَتِكَ إِلَىٰ نِعَاجِهِ ۖ وَإِنَّ كَثِيرًا
مِّنَ الْخُلَطَاءِ لَيَبْغِي بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا
وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَقَلِيلٌ مَّا هُمْ ۗ وَظَنَّ دَاوُودُ أَنَّمَا
فَتَنَّاهُ فَاسْتَغْفَرَ رَبَّهُ وَخَرَّ رَاكِعًا وَأَنَابَ ۩
Qala laqad thalamakabisu-ali naAAjatika ila niAAajihi wa-innakatheeran mina
alkhulata-i layabghee baAAduhum AAalabaAAdin illa allatheena amanoowaAAamiloo
assalihati waqaleelun mahum wathanna dawoodu annama fatannahufastaghfara rabbahu
wakharra rakiAAan waanab
Hausa
(Dãwũda) ya ce: "Lalle, haƙiƙa ya zãlunce ka game da tambayar tunkiyarka zuwa ga
tumakinsa. Kuma lalle ne mãsu yawa daga abõkan tarayya, haƙiƙa, sãshensu na
zambatar sãshe fãce waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai."
Kuma Dãwũda ya tabbata cẽwa Mun fitine shi ne, sabõda haka, ya nẽmi Ubangijinsa
gãfara,kuma ya fãɗi yanã mai sujada, kuma ya mayar da al'amari ga Allah.
|
Ayah 38:25 الأية
فَغَفَرْنَا لَهُ ذَٰلِكَ ۖ وَإِنَّ لَهُ عِندَنَا لَزُلْفَىٰ وَحُسْنَ مَآبٍ
Faghafarna lahu thalikawa-inna lahu AAindana lazulfa wahusna maab
Hausa
Sabõda haka Muka gãfarta masa wancan, kuma lalle yanã da wata kusantar daraja a
wurinMu, da kyaun makõma.
|
Ayah 38:26 الأية
يَا دَاوُودُ إِنَّا جَعَلْنَاكَ خَلِيفَةً فِي الْأَرْضِ فَاحْكُم بَيْنَ النَّاسِ
بِالْحَقِّ وَلَا تَتَّبِعِ الْهَوَىٰ فَيُضِلَّكَ عَن سَبِيلِ اللهِ ۚ إِنَّ
الَّذِينَ يَضِلُّونَ عَن سَبِيلِ اللهِ لَهُمْ عَذَابٌ شَدِيدٌ بِمَا نَسُوا
يَوْمَ الْحِسَابِ
Ya dawoodu inna jaAAalnakakhaleefatan fee al-ardi fahkum bayna annasibilhaqqi
wala tattabiAAi alhawa fayudillakaAAan sabeeli Allahi inna allatheena
yadilloonaAAan sabeeli Allahi lahum AAathabun shadeedun bimanasoo yawma alhisab
Hausa
Yã Dãwũda! Lalle Mũ Mun sanya ka Halĩfa a cikin ƙasã. To, ka yi hukunci tsakãnin
mutãne da gaskiya, kuma kada ka biye wa son zũciyar, har ya ɓatar dakai daga
hanyar Allah. Lalle waɗanda ke ɓacẽwa daga hanyar Allah sunã da wata azãba mai
tsanani dõmin abin da suka manta, a rãnar hisãbi
|
Ayah 38:27 الأية
وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاءَ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا بَاطِلًا ۚ ذَٰلِكَ
ظَنُّ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا مِنَ النَّارِ
Wama khalaqna assamaawal-arda wama baynahuma batilanthalika thannu allatheena
kafaroofawaylun lillatheena kafaroo mina annar
Hausa
Kuma ba Mu halitta sama da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu ba a kan ƙarya.
Wannan shĩ ne zaton waɗanda suka kãfirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka
kãfirta daga wutã.
|
Ayah 38:28 الأية
أَمْ نَجْعَلُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ كَالْمُفْسِدِينَ فِي
الْأَرْضِ أَمْ نَجْعَلُ الْمُتَّقِينَ كَالْفُجَّارِ
Am najAAalu allatheena amanoowaAAamiloo assalihati kalmufsideenafee al-ardi am
najAAalu almuttaqeena kalfujjar
Hausa
Kõ zã Mu sanya waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai kamar
waɗanda suke mãsu barna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za Mu sanya masu bin Allah da
taƙawa kamar fãjirai makarkata?
|
Ayah 38:29 الأية
كِتَابٌ أَنزَلْنَاهُ إِلَيْكَ مُبَارَكٌ لِّيَدَّبَّرُوا آيَاتِهِ وَلِيَتَذَكَّرَ
أُولُو الْأَلْبَابِ
Kitabun anzalnahu ilayka mubarakunliyaddabbaroo ayatihi waliyatathakkara
olooal-albab
Hausa
(Wannan) Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yanã, mai albarka, dõmin su
lũra da ãyõyinsa, kuma don mãsu hankali su riƙa yin tunãni.
|
Ayah 38:30 الأية
وَوَهَبْنَا لِدَاوُودَ سُلَيْمَانَ ۚ نِعْمَ الْعَبْدُ ۖ إِنَّهُ أَوَّابٌ
Wawahabna lidawooda sulaymananiAAma alAAabdu innahu awwab
Hausa
Kuma Muka bai wa Dãwũda Sulaimãn. Mãdalla da bãwanMu, shi. Lalle shi (Sulaimãn)
mai mayar da al'amari ne ga Allah.
|
Ayah 38:31 الأية
إِذْ عُرِضَ عَلَيْهِ بِالْعَشِيِّ الصَّافِنَاتُ الْجِيَادُ
Ith AAurida AAalayhi bilAAashiyyiassafinatu aljiyad
Hausa
A lõkacin da aka gitta masa dawãki mãsu asali, a lõkacin maraice.
|
Ayah 38:32 الأية
فَقَالَ إِنِّي أَحْبَبْتُ حُبَّ الْخَيْرِ عَن ذِكْرِ رَبِّي حَتَّىٰ تَوَارَتْ
بِالْحِجَابِ
Faqala innee ahbabtu hubbaalkhayri AAan thikri rabbee hatta tawaratbilhijab
Hausa
Sai ya ce: "Lalle nĩ, na fĩfĩta son dũkiya daga tunãwar Ubangijina, har (rãnã)
ta faku da shãmaki!"
|
Ayah 38:33 الأية
رُدُّوهَا عَلَيَّ ۖ فَطَفِقَ مَسْحًا بِالسُّوقِ وَالْأَعْنَاقِ
Ruddooha AAalayya fatafiqa mashanbissooqi wal-aAAnaq
Hausa
"Ku mayar da su a gare ni." Sai ya shiga yankansu da takõbi ga ƙwabrukansu da
wuyõyinsu.
|
Ayah 38:34 الأية
وَلَقَدْ فَتَنَّا سُلَيْمَانَ وَأَلْقَيْنَا عَلَىٰ كُرْسِيِّهِ جَسَدًا ثُمَّ
أَنَابَ
Walaqad fatanna sulaymanawaalqayna AAala kursiyyihi jasadan thumma anab
Hausa
Kuma lalle haƙĩƙa, Mun fitini Sulaiman kuma Muka jẽfa wani jikin mutum a kan
karagarsa. Sa'an nan ya mayar da al'amari zuwa gare Mu.
|
Ayah 38:35 الأية
قَالَ رَبِّ اغْفِرْ لِي وَهَبْ لِي مُلْكًا لَّا يَنبَغِي لِأَحَدٍ مِّن بَعْدِي ۖ
إِنَّكَ أَنتَ الْوَهَّابُ
Qala rabbi ighfir lee wahab leemulkan la yanbaghee li-ahadin min baAAdee
innakaanta alwahhab
Hausa
Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta
da kõwa daga bãyãna. Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta.
|
Ayah 38:36 الأية
فَسَخَّرْنَا لَهُ الرِّيحَ تَجْرِي بِأَمْرِهِ رُخَاءً حَيْثُ أَصَابَ
Fasakhkharna lahu arreehatajree bi-amrihi rukhaan haythu asab
Hausa
Sabõda haka Muka hõre masa iska tanã gudu da umurninsa, tãna tãshi da sauƙi,
inda ya nufa.
|
Ayah 38:37 الأية
وَالشَّيَاطِينَ كُلَّ بَنَّاءٍ وَغَوَّاصٍ
Washshayateena kulla banna-inwaghawwas
Hausa
Da shaiɗanu dukan mai gini, da mai nutsa (a cikin kõguna.)
|
Ayah 38:38 الأية
وَآخَرِينَ مُقَرَّنِينَ فِي الْأَصْفَادِ
Waakhareena muqarraneena fee al-asfad
Hausa
Waɗansu, ɗaɗɗaure a cikin marũruwa.
|
Ayah 38:39 الأية
هَٰذَا عَطَاؤُنَا فَامْنُنْ أَوْ أَمْسِكْ بِغَيْرِ حِسَابٍ
Hatha AAataona famnunaw amsik bighayri hisab
Hausa
Wannan kyautarMu ce. Sai ka yi kyauta ga wanda kake so, ko kuma ka riƙe, bãbu
wani bincike.
|
Ayah 38:40 الأية
وَإِنَّ لَهُ عِندَنَا لَزُلْفَىٰ وَحُسْنَ مَآبٍ
Wa-inna lahu AAindana lazulfawahusna maab
Hausa
Kuma lalle, haƙĩƙa yanã da kusantar daraja a wurinMu da kyaun makõma.
|
Ayah 38:41 الأية
وَاذْكُرْ عَبْدَنَا أَيُّوبَ إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُ أَنِّي مَسَّنِيَ الشَّيْطَانُ
بِنُصْبٍ وَعَذَابٍ
Wathkur AAabdanaayyooba ith nada rabbahu annee massaniya ashshaytanubinusbin
waAAathab
Hausa
Kuma ka ambaci bãwanMu Ayyũba a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle
nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba."
|
Ayah 38:42 الأية
ارْكُضْ بِرِجْلِكَ ۖ هَٰذَا مُغْتَسَلٌ بَارِدٌ وَشَرَابٌ
Orkud birijlika hathamughtasalun baridun washarab
Hausa
Ka shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin shã.
|
Ayah 38:43 الأية
وَوَهَبْنَا لَهُ أَهْلَهُ وَمِثْلَهُم مَّعَهُمْ رَحْمَةً مِّنَّا وَذِكْرَىٰ
لِأُولِي الْأَلْبَابِ
Wawahabna lahu ahlahu wamithlahummaAAahum rahmatan minna wathikrali-olee
al-albab
Hausa
Kuma Muka bã shi iyalansa da kwatankwacinsu tãre da su sabõda rahama daga gare
Mu, da tunãtarwa ga mãsu hankali.
|
Ayah 38:44 الأية
وَخُذْ بِيَدِكَ ضِغْثًا فَاضْرِب بِّهِ وَلَا تَحْنَثْ ۗ إِنَّا وَجَدْنَاهُ
صَابِرًا ۚ نِّعْمَ الْعَبْدُ ۖ إِنَّهُ أَوَّابٌ
Wakhuth biyadika dighthan fadribbihi wala tahnath inna wajadnahu sabiranniAAma
alAAabdu innahu awwab
Hausa
Kuma ka riƙi wata ƙulla da hannunka, ka yi dũka da ita kuma kada ka karya
rantsuwarka. Lalle Mũ, Mun sãme shi mai haƙuri. Madalla da bãwa, shĩ Lalle shĩ
mai mayar da al'amari ga Allah ne.
|
Ayah 38:45 الأية
وَاذْكُرْ عِبَادَنَا إِبْرَاهِيمَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ أُولِي الْأَيْدِي
وَالْأَبْصَارِ
Wathkur AAibadanaibraheema wa-ishaqa wayaAAqooba olee al-aydee wal-absar
Hausa
Kuma ka ambaci bãyinMu: Ibrahĩm da ls'hãƙa da Ya'aƙũba, ma'abũta ƙarfin (ɗaukar
umurninMu) da basĩra.
|
Ayah 38:46 الأية
إِنَّا أَخْلَصْنَاهُم بِخَالِصَةٍ ذِكْرَى الدَّارِ
Inna akhlasnahum bikhalisatinthikra addar
Hausa
Lalle Mũ, Mun keɓance su game da wata, tsattsarkar aba: Hukunce-hukuncen gidan
dũniya (mai tunãtar da su Lãhira).
|
Ayah 38:47 الأية
وَإِنَّهُمْ عِندَنَا لَمِنَ الْمُصْطَفَيْنَ الْأَخْيَارِ
Wa-innahum AAindana lamina almustafaynaal-akhyar
Hausa
Kuma lalle sũ a wurinMu, tabbas, sunã daga zãɓaɓɓu, mafĩfĩta.
|
Ayah 38:48 الأية
وَاذْكُرْ إِسْمَاعِيلَ وَالْيَسَعَ وَذَا الْكِفْلِ ۖ وَكُلٌّ مِّنَ الْأَخْيَارِ
Wathkur ismaAAeelawa-ilyasaAAa watha alkifli wakullun mina al-akhyar
Hausa
Kuma ka ambaci Isma'ĩla da llyãs da Zulkifli, kuma dukansu sunã daga zãɓaɓɓu.
|
Ayah 38:49 الأية
هَٰذَا ذِكْرٌ ۚ وَإِنَّ لِلْمُتَّقِينَ لَحُسْنَ مَآبٍ
Hatha thikrun wa-innalilmuttaqeena lahusna maab
Hausa
Wannan tunãtarwa ce, kuma lalle mãsu bin Allah da taƙawa, sunã da kyakkyawar
makõma.
|
Ayah 38:50 الأية
جَنَّاتِ عَدْنٍ مُّفَتَّحَةً لَّهُمُ الْأَبْوَابُ
Jannati AAadnin mufattahatanlahumu al-abwab
Hausa
Gidãjen Aljannar zama , alhãli kuwa tanã abar buɗe wa kõfõfi sabõda su.
|
Ayah 38:51 الأية
مُتَّكِئِينَ فِيهَا يَدْعُونَ فِيهَا بِفَاكِهَةٍ كَثِيرَةٍ وَشَرَابٍ
Muttaki-eena feeha yadAAoona feehabifakihatin katheeratin washarab
Hausa
Sunã gingincire a cikinsu, sunã kira a cikinsu, ga 'ya'yan itãcen marmari mãsu
yawa, da abin shã.
|
Ayah 38:52 الأية
وَعِندَهُمْ قَاصِرَاتُ الطَّرْفِ أَتْرَابٌ
WaAAindahum qasiratu attarfiatrab
Hausa
Kuma a wurinsu akwai mãtan aure mãsu gajarta ganinsu ga mazansu, tsãrar jũna.
|
Ayah 38:53 الأية
هَٰذَا مَا تُوعَدُونَ لِيَوْمِ الْحِسَابِ
Hatha ma tooAAadoona liyawmialhisab
Hausa
Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi ga rãnar hisãbi.
|
Ayah 38:54 الأية
إِنَّ هَٰذَا لَرِزْقُنَا مَا لَهُ مِن نَّفَادٍ
Inna hatha larizquna malahu min nafad
Hausa
Lalle wannan, haƙĩƙa, azurtarwarMu ce, bã ta ƙãrẽwa.
|
Ayah 38:55 الأية
هَٰذَا ۚ وَإِنَّ لِلطَّاغِينَ لَشَرَّ مَآبٍ
Hatha wa-inna littagheenalasharra maab
Hausa
Wannan shĩ ne kuma lalle makangara, haƙĩƙa, sunã da mafi sharrin makõma.
|
Ayah 38:56 الأية
جَهَنَّمَ يَصْلَوْنَهَا فَبِئْسَ الْمِهَادُ
Jahannama yaslawnaha fabi/saalmihad
Hausa
Jahannama, sunã shigarta. To, shimfiɗar tã mũnana, ita.
|
Ayah 38:57 الأية
هَٰذَا فَلْيَذُوقُوهُ حَمِيمٌ وَغَسَّاقٌ
Hatha falyathooqoohu hameemunwaghassaq
Hausa
Wannan shĩ ne! To, su ɗanɗane shi: ruwan zãfi ne da ruɓaɓɓen jini.
|
Ayah 38:58 الأية
وَآخَرُ مِن شَكْلِهِ أَزْوَاجٌ
Waakharu min shaklihi azwaj
Hausa
Da wani daga siffarsa nau'i-nau'i.
|
Ayah 38:59 الأية
هَٰذَا فَوْجٌ مُّقْتَحِمٌ مَّعَكُمْ ۖ لَا مَرْحَبًا بِهِمْ ۚ إِنَّهُمْ صَالُو
النَّارِ
Hatha fawjun muqtahimunmaAAakum la marhaban bihim innahum saloo annar
Hausa
Wannan wani yanki ne mai kũtsawa tãre da ku, bãbu marãba a gare su, lalle sũ,
mãsu shiga Wutã ne.
|
Ayah 38:60 الأية
قَالُوا بَلْ أَنتُمْ لَا مَرْحَبًا بِكُمْ ۖ أَنتُمْ قَدَّمْتُمُوهُ لَنَا ۖ
فَبِئْسَ الْقَرَارُ
Qaloo bal antum la marhabanbikum antum qaddamtumoohu lana fabi/sa alqarar
Hausa
Suka ce: "Ã'a, ku ne bãbu marãba a gare ku, kũ ne kuka gabãtar da shi a gare
mu." To, matabbatar tã mũnana (ita wutar).
|
Ayah 38:61 الأية
قَالُوا رَبَّنَا مَن قَدَّمَ لَنَا هَٰذَا فَزِدْهُ عَذَابًا ضِعْفًا فِي النَّارِ
Qaloo rabbana man qaddama lanahatha fazidhu AAathaban diAAfan fee annar
Hausa
Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Wanda ya gabãtar da wannan a gare mu, to, Ka ƙãra masa
azãba, ninki, a cikin wutã."
|
Ayah 38:62 الأية
وَقَالُوا مَا لَنَا لَا نَرَىٰ رِجَالًا كُنَّا نَعُدُّهُم مِّنَ الْأَشْرَارِ
Waqaloo ma lana lanara rijalan kunna naAAudduhum mina al-ashrar
Hausa
Kuma suka ce: "Mẽ ya sãme mu, bã mu ganin waɗansu mazãje, mun kasance munã
ƙidãya su daga asharãrai?"
|
Ayah 38:63 الأية
أَتَّخَذْنَاهُمْ سِخْرِيًّا أَمْ زَاغَتْ عَنْهُمُ الْأَبْصَارُ
Attakhathnahum sikhriyyan am zaghatAAanhumu al-absar
Hausa
"Shin, mun riƙe su abin izgili ne kõ idãnunmu sun karkata daga gare su ne?"
|
Ayah 38:64 الأية
إِنَّ ذَٰلِكَ لَحَقٌّ تَخَاصُمُ أَهْلِ النَّارِ
Inna thalika lahaqqun takhasumuahli annar
Hausa
Lalle wannan, haƙĩƙa, gaskiya ne, husũmar mutãnen wutã.
|
Ayah 38:65 الأية
قُلْ إِنَّمَا أَنَا مُنذِرٌ ۖ وَمَا مِنْ إِلَٰهٍ إِلَّا اللهُ الْوَاحِدُ
الْقَهَّارُ
Qul innama ana munthirunwama min ilahin illa Allahu alwahidualqahhar
Hausa
Ka ce: "Nĩ mai gargaɗikawai ne, kuma babu wani abin bautawa sai Allah,
Makaɗaici, Mai tilastawa."
|
Ayah 38:66 الأية
رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا الْعَزِيزُ الْغَفَّارُ
Rabbu assamawati wal-ardiwama baynahuma alAAazeezu alghaffar
Hausa
"Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu Mabuwãyi, Mai gãfara."
|
Ayah 38:67 الأية
قُلْ هُوَ نَبَأٌ عَظِيمٌ
Qul huwa nabaon AAatheem
Hausa
Ka ce: "Shĩ (Alkur'ãni) babban lãbãri ne mai girma".
|
Ayah 38:68 الأية
أَنتُمْ عَنْهُ مُعْرِضُونَ
Antum AAanhu muAAridoon
Hausa
"Kũ, mãsu bijirẽwa ne daga gare shi!"
|
Ayah 38:69 الأية
مَا كَانَ لِيَ مِنْ عِلْمٍ بِالْمَلَإِ الْأَعْلَىٰ إِذْ يَخْتَصِمُونَ
Ma kana liya min AAilmin bilmala-ial-aAAla ith yakhtasimoon
Hausa
"Wani ilmi bai kasance a gare ni ba game da jama'a (malã'iku) mafi ɗaukaka a
lõkacin da suke yin husũma."
|
Ayah 38:70 الأية
إِن يُوحَىٰ إِلَيَّ إِلَّا أَنَّمَا أَنَا نَذِيرٌ مُّبِينٌ
In yooha ilayya illa annamaana natheerun mubeen
Hausa
"Ba a yi mini wahayin kõme ba face cẽwa ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa."
|
Ayah 38:71 الأية
إِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلَائِكَةِ إِنِّي خَالِقٌ بَشَرًا مِّن طِينٍ
Ith qala rabbuka lilmala-ikatiinnee khaliqun basharan min teen
Hausa
A lõkacin da Ubangijinka Ya ce wa malã'iku, "Lalle Nĩ Mai halitta mutum ne daga
lãkã.
|
Ayah 38:72 الأية
فَإِذَا سَوَّيْتُهُ وَنَفَخْتُ فِيهِ مِن رُّوحِي فَقَعُوا لَهُ سَاجِدِينَ
Fa-itha sawwaytuhu wanafakhtu feehimin roohee faqaAAoo lahu sajideen
Hausa
"Sa'an nan idan Nã daidaita shi, kuma Na hũra (wani abu) daga RuhĩNa a cikinsa
to ku fãɗi kunã mãsu sujada a gare; shi."
|
Ayah 38:73 الأية
فَسَجَدَ الْمَلَائِكَةُ كُلُّهُمْ أَجْمَعُونَ
Fasajada almala-ikatu kulluhumajmaAAoon
Hausa
Sai malã'ikun suka yi sujada dukansu, gabã ɗaya.
|
Ayah 38:74 الأية
إِلَّا إِبْلِيسَ اسْتَكْبَرَ وَكَانَ مِنَ الْكَافِرِينَ
Illa ibleesa istakbara wakanamina alkafireen
Hausa
Fãce Iblis, ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai.
|
Ayah 38:75 الأية
قَالَ يَا إِبْلِيسُ مَا مَنَعَكَ أَن تَسْجُدَ لِمَا خَلَقْتُ بِيَدَيَّ ۖ
أَسْتَكْبَرْتَ أَمْ كُنتَ مِنَ الْعَالِينَ
Qala ya ibleesu mamanaAAaka an tasjuda lima khalaqtu biyadayya astakbarta
amkunta mina alAAaleen
Hausa
(Allah) Ya ce, "Yã Ibilis! Mẽ ya hana ka, ka yi sujada ga abin da Nã halitta da
HannayeNa biyu? Shin, kã yi girman kai ne, kõ kuwa kã kasance daga maɗaukaka
ne?"
|
Ayah 38:76 الأية
قَالَ أَنَا خَيْرٌ مِّنْهُ ۖ خَلَقْتَنِي مِن نَّارٍ وَخَلَقْتَهُ مِن طِينٍ
Qala ana khayrun minhukhalaqtanee min narin wakhalaqtahu min teen
Hausa
Ya ce, "Nĩ, mafifici ne daga gare shi: Kã halitta ni daga wutã, kuma Kã halitta
shi daga lãkã."
|
Ayah 38:77 الأية
قَالَ فَاخْرُجْ مِنْهَا فَإِنَّكَ رَجِيمٌ
Qala fakhruj minhafa-innaka rajeem
Hausa
Ya ce, "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai la'ananne ne."
|
Ayah 38:78 الأية
وَإِنَّ عَلَيْكَ لَعْنَتِي إِلَىٰ يَوْمِ الدِّينِ
Wa-inna AAalayka laAAnatee ila yawmiaddeen
Hausa
"Kuma lalle a kanka akwai la'anaTa har zuwa rãnar sakamako."
|
Ayah 38:79 الأية
قَالَ رَبِّ فَأَنظِرْنِي إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ
Qala rabbi faanthirneeila yawmi yubAAathoon
Hausa
Ya ce, "Ya Ubangijina! To, Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su."
|
Ayah 38:80 الأية
قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ الْمُنظَرِينَ
Qala fa-innaka mina almunthareen
Hausa
Ya ce, "To, lalle kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri,
|
Ayah 38:81 الأية
إِلَىٰ يَوْمِ الْوَقْتِ الْمَعْلُومِ
Ila yawmi alwaqti almaAAloom
Hausa
"Zuwa ga yinin lõkaci sananne."
|
Ayah 38:82 الأية
قَالَ فَبِعِزَّتِكَ لَأُغْوِيَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ
Qala fabiAAizzatika laoghwiyannahumajmaAAeen
Hausa
Ya ce, "To, inã rantsuwa da buwãyarKa, lalle, inã ɓatar da su gabã ɗaya.
|
Ayah 38:83 الأية
إِلَّا عِبَادَكَ مِنْهُمُ الْمُخْلَصِينَ
Illa AAibadaka minhumualmukhlaseen
Hausa
"Fãce bãyinKa tsarkakakku daga gare su."
|
Ayah 38:84 الأية
قَالَ فَالْحَقُّ وَالْحَقَّ أَقُولُ
Qala falhaqqu walhaqqaaqool
Hausa
(Allah) Ya ce, "To, (wannan magana ita ce) gaskiya. Kuma gaskiya Nake faɗa."
|
Ayah 38:85 الأية
لَأَمْلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنكَ وَمِمَّن تَبِعَكَ مِنْهُمْ أَجْمَعِينَ
Laamlaanna jahannama minka wamimmantabiAAaka minhum ajmaAAeen
Hausa
"Lalle zã Ni cika Jahannama daga gare ka, kuma daga wanda ya bĩ ka daga gare su,
gabã ɗaya"
|
Ayah 38:86 الأية
قُلْ مَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ وَمَا أَنَا مِنَ الْمُتَكَلِّفِينَ
Qul ma as-alukum AAalayhi min ajrinwama ana mina almutakallifeen
Hausa
Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra, a kansa kuma bã ni daga mãsu ƙãƙalen
faɗarsa."
|
Ayah 38:87 الأية
إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَالَمِينَ
In huwa illa thikrun lilAAalameen
Hausa
"Shĩ (Alkur'ãn) bai zama ba fãce ambato ne ga dukan halitta."
|
Ayah 38:88 الأية
وَلَتَعْلَمُنَّ نَبَأَهُ بَعْدَ حِينٍ
WalataAAlamunna nabaahu baAAda heen
Hausa
"Kuma lalle zã ku san babban lãbãrinsa a bayan ɗan lõkaci."
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|