1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
تَنزِيلُ الْكِتَابِ مِنَ اللهِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ
Tanzeelu alkitabi mina AllahialAAazeezi alhakeem
Hausa
Saukar da Littãfin daga Allah ne, Mabuwãyi, Mai hikima.
|
Ayah 39:2 الأية
إِنَّا أَنزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ فَاعْبُدِ اللهَ مُخْلِصًا
لَّهُ الدِّينَ
Inna anzalna ilayka alkitababilhaqqi faAAbudi Allaha mukhlisanlahu addeen
Hausa
Lalle Mũ Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka, da gaskiya. Sabõda haka, ka bauta
wa Allah kanã mai tsarkake addini a gare Shi.
|
Ayah 39:3 الأية
أَلَا لِلَّهِ الدِّينُ الْخَالِصُ ۚ وَالَّذِينَ اتَّخَذُوا مِن دُونِهِ
أَوْلِيَاءَ مَا نَعْبُدُهُمْ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَا إِلَى اللهِ زُلْفَىٰ إِنَّ
اللهَ يَحْكُمُ بَيْنَهُمْ فِي مَا هُمْ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ ۗ إِنَّ اللهَ لَا
يَهْدِي مَنْ هُوَ كَاذِبٌ كَفَّارٌ
Ala lillahi addeenualkhalisu wallatheena ittakhathoomin doonihi awliyaa ma
naAAbuduhum illaliyuqarriboona ila Allahi zulfa innaAllaha yahkumu baynahum fee
ma hum feehiyakhtalifoona inna Allaha la yahdee man huwa kathibunkaffar
Hausa
To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã
Shi ba, (sunã cẽwa) "Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga
Allah, kusantar daraja." Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka
zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya,
mai kãfirci.
|
Ayah 39:4 الأية
لَّوْ أَرَادَ اللهُ أَن يَتَّخِذَ وَلَدًا لَّاصْطَفَىٰ مِمَّا يَخْلُقُ مَا
يَشَاءُ ۚ سُبْحَانَهُ ۖ هُوَ اللهُ الْوَاحِدُ الْقَهَّارُ
Law arada Allahu an yattakhithawaladan lastafa mimma yakhluqu mayashao subhanahu
huwa Allahu alwahidualqahhar
Hausa
Dã Allah Yã yi nufin Ya riƙi ɗã, to, lalle sai Ya zãɓa daga abin da Yake
halittãwa abin da Yake so. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Shĩ ne Allah,
Makaɗaici, Mai tĩlastãwa.
|
Ayah 39:5 الأية
خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِالْحَقِّ ۖ يُكَوِّرُ اللَّيْلَ عَلَى
النَّهَارِ وَيُكَوِّرُ النَّهَارَ عَلَى اللَّيْلِ ۖ وَسَخَّرَ الشَّمْسَ
وَالْقَمَرَ ۖ كُلٌّ يَجْرِي لِأَجَلٍ مُّسَمًّى ۗ أَلَا هُوَ الْعَزِيزُ
الْغَفَّارُ
Khalaqa assamawati wal-ardabilhaqqi yukawwiru allayla AAala annahariwayukawwiru
annahara AAala allayliwasakhkhara ashshamsa walqamara kullun yajreeli-ajalin
musamman ala huwa alAAazeezu alghaffar
Hausa
Ya halitta sammai da ƙasã da gaskiya. Yanã shigar da dare a kan rãna, kuma Yanã
shigar da rãnã a kan dare kuma Yã hõre rãnã da watã, kõwannensu yanã gudãna zuwa
ga ajali ambatacce. To, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai gãfara.
|
Ayah 39:6 الأية
خَلَقَكُم مِّن نَّفْسٍ وَاحِدَةٍ ثُمَّ جَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَا وَأَنزَلَ لَكُم
مِّنَ الْأَنْعَامِ ثَمَانِيَةَ أَزْوَاجٍ ۚ يَخْلُقُكُمْ فِي بُطُونِ
أُمَّهَاتِكُمْ خَلْقًا مِّن بَعْدِ خَلْقٍ فِي ظُلُمَاتٍ ثَلَاثٍ ۚ ذَٰلِكُمُ
اللهُ رَبُّكُمْ لَهُ الْمُلْكُ ۖ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ۖ فَأَنَّىٰ
تُصْرَفُونَ
Khalaqakum min nafsin wahidatin thummajaAAala minha zawjaha waanzala lakum mina
al-anAAamithamaniyata azwajin yakhluqukum fee butooniommahatikum khalqan min
baAAdi khalqin fee thulumatinthalathin thalikumu Allahu rabbukum lahualmulku la
ilaha illa huwa faanna tusrafoon
Hausa
Yã halitta ku daga rai guda, sa'an nan Ya sanya ma'auranta daga gare shi. Kuma
ya saukar muku daga dabbõbin gida nau'i takwas Yanã halitta ku a cikin cikunnan
uwayenku, halitta a bãyan wata halitta, a cikin duffai uku. Wannan shĩ ne Allah
Ubangijinku. Mulki a gare shi yake. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake
karkatar da ku?
|
Ayah 39:7 الأية
إِن تَكْفُرُوا فَإِنَّ اللهَ غَنِيٌّ عَنكُمْ ۖ وَلَا يَرْضَىٰ لِعِبَادِهِ
الْكُفْرَ ۖ وَإِن تَشْكُرُوا يَرْضَهُ لَكُمْ ۗ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ
أُخْرَىٰ ۗ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُم مَّرْجِعُكُمْ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ
تَعْمَلُونَ ۚ إِنَّهُ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ
In takfuroo fa-inna Allaha ghaniyyunAAankum wala yarda liAAibadihi alkufra
wa-intashkuroo yardahu lakum wala taziru waziratunwizra okhra thumma ila
rabbikum marjiAAukumfayunabbi-okum bima kuntum taAAmaloona innahu AAaleemun
bithatiassudoor
Hausa
Idan kun kãfirta to, lalle Allah Wadãtacce ne daga barinku, kuma bã Shi yarda da
kãfirci ga bãyinSa, kuma idan kun gõde, Zai yarda da ita (gõdiyar) a gare ku,
kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani. Sa'an nan kuma
makõmarku zuwa ga Ubangijinku take, dõmin Ya bã ku lãbãri game da abin da kuka
kasance kunã aikatãwa. Lalle Shĩ, Masani ne ga abin da yake a ainihin zukata.
|
Ayah 39:8 الأية
وَإِذَا مَسَّ الْإِنسَانَ ضُرٌّ دَعَا رَبَّهُ مُنِيبًا إِلَيْهِ ثُمَّ إِذَا
خَوَّلَهُ نِعْمَةً مِّنْهُ نَسِيَ مَا كَانَ يَدْعُو إِلَيْهِ مِن قَبْلُ وَجَعَلَ
لِلَّهِ أَندَادًا لِّيُضِلَّ عَن سَبِيلِهِ ۚ قُلْ تَمَتَّعْ بِكُفْرِكَ قَلِيلًا
ۖ إِنَّكَ مِنْ أَصْحَابِ النَّارِ
Wa-itha massa al-insana durrundaAAa rabbahu muneeban ilayhi thumma
ithakhawwalahu niAAmatan minhu nasiya ma kana yadAAooilayhi min qablu wajaAAala
lillahi andadan liyudillaAAan sabeelihi qul tamattaAA bikufrika qaleelan innaka
min as-habiannar
Hausa
Kuma idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kira Ubangijinsa, yanã mai mai da
al'amari zuwa gare Shi, sa'an nan idan Ya jũyar da cũtar da ni'ima ta daga gare
Shi, sai ya manta da abin da ya kasance yanã kira zuwa gare shi a gabãnin haka,
kuma ya sanya wa Allah waɗansu abõkan tarẽwa dõmin ya ɓatar (da su) daga
hanyarSa. Ka ce (masa), "Ka ji dãɗi da kãfircinka, a ɗan lõkaci, lalle kai daga
'yan wutã ne."
|
Ayah 39:9 الأية
أَمَّنْ هُوَ قَانِتٌ آنَاءَ اللَّيْلِ سَاجِدًا وَقَائِمًا يَحْذَرُ الْآخِرَةَ
وَيَرْجُو رَحْمَةَ رَبِّهِ ۗ قُلْ هَلْ يَسْتَوِي الَّذِينَ يَعْلَمُونَ
وَالَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ ۗ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُولُو الْأَلْبَابِ
Amman huwa qanitun anaaallayli sajidan waqa-iman yahtharu al-akhiratawayarjoo
rahmata rabbihi qul hal yastawee allatheenayaAAlamoona wallatheena la
yaAAlamoonainnama yatathakkaru oloo al-albab
Hausa
Shin, wanda yake mai tawãli'u sã'õ'in dare, yanã mai sujada kuma yanã mai tsayi
ga salla, yanã tsõron Lãhira, kuma yanã fãtan rahamar Ubangijinsa, (yanã daidai
da waninsa?) Ka ce: "Ashe, waɗanda suka sani, sunã daidaita da waɗanda ba su
sani ba?" Mãsu hankali kawai ke yin tunãni.
|
Ayah 39:10 الأية
قُلْ يَا عِبَادِ الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا رَبَّكُمْ ۚ لِلَّذِينَ أَحْسَنُوا
فِي هَٰذِهِ الدُّنْيَا حَسَنَةٌ ۗ وَأَرْضُ اللهِ وَاسِعَةٌ ۗ إِنَّمَا يُوَفَّى
الصَّابِرُونَ أَجْرَهُم بِغَيْرِ حِسَابٍ
Qul ya AAibadi allatheenaamanoo ittaqoo rabbakum lillatheena ahsanoofee hathihi
addunya hasanatun waarduAllahi wasiAAatun innama yuwaffa assabiroonaajrahum
bighayri hisab
Hausa
Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ĩmãni!Ku bi Ubangijinku da
taƙawa. Waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya sunã da sakamako mai kyau,
kuma ƙasar Allah mai fãɗi ce. Mãsu haƙuri kawai ake cika wa ijãrarsu, bã da wani
lissãfi ba.
|
Ayah 39:11 الأية
قُلْ إِنِّي أُمِرْتُ أَنْ أَعْبُدَ اللهَ مُخْلِصًا لَّهُ الدِّينَ
Qul innee omirtu an aAAbuda Allahamukhlisan lahu addeen
Hausa
Ka ce: "Lalle nĩ, an umurce ni da in bauta wa Allah, inã tsarkake addini a gare
Shi.
|
Ayah 39:12 الأية
وَأُمِرْتُ لِأَنْ أَكُونَ أَوَّلَ الْمُسْلِمِينَ
Waomirtu li-an akoona awwala almuslimeen
Hausa
"Kuma an umurce ni da in kasance farkon mãsu miƙa wuya (ga umurnin Allah)."
|
Ayah 39:13 الأية
قُلْ إِنِّي أَخَافُ إِنْ عَصَيْتُ رَبِّي عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ
Qul innee akhafu in AAasayturabbee AAathaba yawmin AAatheem
Hausa
Ka ce: "Lalle nĩ inã tsõro, idan na sãɓã wa Ubangijĩna, ga azãbar yini mai
girma."
|
Ayah 39:14 الأية
قُلِ اللهَ أَعْبُدُ مُخْلِصًا لَّهُ دِينِي
Quli Allaha aAAbudu mukhlisanlahu deenee
Hausa
Ka ce: "Allah nake bautã wa, inã mai tsarkake addinĩna a gare Shi.
|
Ayah 39:15 الأية
فَاعْبُدُوا مَا شِئْتُم مِّن دُونِهِ ۗ قُلْ إِنَّ الْخَاسِرِينَ الَّذِينَ
خَسِرُوا أَنفُسَهُمْ وَأَهْلِيهِمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۗ أَلَا ذَٰلِكَ هُوَ
الْخُسْرَانُ الْمُبِينُ
FaAAbudoo ma shi/tum mindoonihi qul inna alkhasireena allatheena
khasirooanfusahum waahleehim yawma alqiyamati ala thalikahuwa alkhusranu
almubeen
Hausa
"To, ku bauta wa abin da kuke so, waninSa." Ka ce: "Lalle mãsu hasãra, sũ ne
waɗanda suka yi hasarar rãyukansu da iyãlansu, a Rãnar ¡iyãma. To, waccan fa,
ita ce hasãra bayyananna."
|
Ayah 39:16 الأية
لَهُم مِّن فَوْقِهِمْ ظُلَلٌ مِّنَ النَّارِ وَمِن تَحْتِهِمْ ظُلَلٌ ۚ ذَٰلِكَ
يُخَوِّفُ اللهُ بِهِ عِبَادَهُ ۚ يَا عِبَادِ فَاتَّقُونِ
Lahum min fawqihim thulalunmina annari wamin tahtihim thulalunthalika yukhawwifu
Allahu bihi AAibadahu yaAAibadi fattaqoon
Hausa
Sunã da waɗansu inuwõwi na wutã daga samansu, kuma daga ƙasansu akwai waɗansu
inuwõwi. Wancan Shĩ ne Allah ke tsõratar da bãyinSa da shi. Yã bãyĩNa! To, ku bĩ
Ni da taƙawa.
|
Ayah 39:17 الأية
وَالَّذِينَ اجْتَنَبُوا الطَّاغُوتَ أَن يَعْبُدُوهَا وَأَنَابُوا إِلَى اللهِ
لَهُمُ الْبُشْرَىٰ ۚ فَبَشِّرْ عِبَادِ
Wallatheena ijtanaboo attaghootaan yaAAbudooha waanaboo ila Allahilahumu
albushra fabashshir AAibad
Hausa
Kuma waɗanda suka nĩsanci Shaiɗannu ga bauta musu, kuma suka mai da al'amari ga
Allah, sunã da bushãra. To, ka bãyar da bushãra ga bãyiNa.
|
Ayah 39:18 الأية
الَّذِينَ يَسْتَمِعُونَ الْقَوْلَ فَيَتَّبِعُونَ أَحْسَنَهُ ۚ أُولَٰئِكَ
الَّذِينَ هَدَاهُمُ اللهُ ۖ وَأُولَٰئِكَ هُمْ أُولُو الْأَلْبَابِ
Allatheena yastamiAAoona alqawlafayattabiAAoona ahsanahu ola-ika
allatheenahadahumu Allahu waola-ika hum oloo al-albab
Hausa
Waɗanda ke sauraren magana, sa'an nan su bi mafi kyaunta. waɗancan sũ ne Allah
Ya shiryar da su, kuma waɗancan su ne mãsu hankali,
|
Ayah 39:19 الأية
أَفَمَنْ حَقَّ عَلَيْهِ كَلِمَةُ الْعَذَابِ أَفَأَنتَ تُنقِذُ مَن فِي النَّارِ
Afaman haqqa AAalayhi kalimatu alAAathabiafaanta tunqithu man fee annar
Hausa
Shin fa, wanda kalmar azãba ta wajaba a kansa? Shin fa, kanã iya tsãmar da wanda
ke a cikin wutã?
|
Ayah 39:20 الأية
لَٰكِنِ الَّذِينَ اتَّقَوْا رَبَّهُمْ لَهُمْ غُرَفٌ مِّن فَوْقِهَا غُرَفٌ
مَّبْنِيَّةٌ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ ۖ وَعْدَ اللهِ ۖ لَا يُخْلِفُ
اللهُ الْمِيعَادَ
Lakini allatheena ittaqawrabbahum lahum ghurafun min fawqiha ghurafun
mabniyyatuntajree min tahtiha al-anharu waAAda Allahila yukhlifu Allahu
almeeAAad
Hausa
Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa, sunã da bẽnãye, daga samansu akwai
waɗansu bẽnãye ginannu, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Alkawarin Allah.
Allah bã Ya sãɓã wa alkawarinSa.
|
Ayah 39:21 الأية
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللهَ أَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَسَلَكَهُ يَنَابِيعَ
فِي الْأَرْضِ ثُمَّ يُخْرِجُ بِهِ زَرْعًا مُّخْتَلِفًا أَلْوَانُهُ ثُمَّ يَهِيجُ
فَتَرَاهُ مُصْفَرًّا ثُمَّ يَجْعَلُهُ حُطَامًا ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَذِكْرَىٰ
لِأُولِي الْأَلْبَابِ
Alam tara anna Allaha anzala mina assama-imaan fasalakahu yanabeeAAa fee
al-ardithumma yukhriju bihi zarAAan mukhtalifan alwanuhu thummayaheeju fatarahu
musfarran thumma yajAAaluhu hutamaninna fee thalika lathikra li-olee al-albab
Hausa
Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Yã
gudãnar da shi yanã marẽmari a cikin ƙasã sa'an nan Yã fitar da shũka game da
shi, launukan shũkar mãsu sãɓãnin jũna sa'annan shũkar ta ƙeƙashe har ka gan ta
fatsifatsi, sa'an nan Allah Ya sanya ta dandaƙaƙƙiya? Lalle ne ga wancan akwai
tunãtarwa ga mãsu hankali (ga iyãwar gudãnar da ruwa a cikin gidãjen Aljanna).
|
Ayah 39:22 الأية
أَفَمَن شَرَحَ اللهُ صَدْرَهُ لِلْإِسْلَامِ فَهُوَ عَلَىٰ نُورٍ مِّن رَّبِّهِ
ۚ فَوَيْلٌ لِّلْقَاسِيَةِ قُلُوبُهُم مِّن ذِكْرِ اللهِ ۚ أُولَٰئِكَ فِي
ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Afaman sharaha Allahu sadrahulil-islami fahuwa AAala noorin min rabbihi
fawaylunlilqasiyati quloobuhum min thikri Allahi ola-ikafee dalalin mubeen
Hausa
Shin fa, wanda Allah Ya buɗa ƙirjinsa, dõmin Musulunci sa'an nan shi yanã a kan
haske daga Ubangijinsa, (zai zama kamar waninsa)? To, bone yã tabbata ga
maƙeƙasa zukãtansu daga ambaton Allah. Waɗancan sunã a cikin wata ɓata
bayyananna.
|
Ayah 39:23 الأية
اللهُ نَزَّلَ أَحْسَنَ الْحَدِيثِ كِتَابًا مُّتَشَابِهًا مَّثَانِيَ
تَقْشَعِرُّ مِنْهُ جُلُودُ الَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُمْ ثُمَّ تَلِينُ
جُلُودُهُمْ وَقُلُوبُهُمْ إِلَىٰ ذِكْرِ اللهِ ۚ ذَٰلِكَ هُدَى اللهِ يَهْدِي
بِهِ مَن يَشَاءُ ۚ وَمَن يُضْلِلِ اللهُ فَمَا لَهُ مِنْ هَادٍ
Allahu nazzala ahsana alhadeethikitaban mutashabihan mathaniya taqshaAAirruminhu
juloodu allatheena yakhshawna rabbahum thummataleenu julooduhum waquloobuhum ila
thikri Allahithalika huda Allahi yahdee bihi man yashaowaman yudlili Allahu fama
lahu min had
Hausa
Allah Ya sassaukar da mafi kyaun lãbãri, Littãfi mai kama da jũna, wanda ake
konkoma karãtunsa fãtun waɗanda ke tsõron Ubangijinsu, sunã tãƙura sabõda Shi,
sa'an nan fãtunsu da zukãtansu su yi laushi zuwa ga ambaton Allah. Waccan ita ce
shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Ya so game da ita. Kuma wanda Allah Ya
ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa.
|
Ayah 39:24 الأية
أَفَمَن يَتَّقِي بِوَجْهِهِ سُوءَ الْعَذَابِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۚ وَقِيلَ
لِلظَّالِمِينَ ذُوقُوا مَا كُنتُمْ تَكْسِبُونَ
Afaman yattaqee biwajhihi soo-a alAAathabiyawma alqiyamati waqeela
liththalimeenathooqoo ma kuntum taksiboon
Hausa
Shin fa, wanda ke kãre mũguwar azãba da fuskarsa (yanã zama kamar waninsa) a
Rãnar ƙiyãma? Kuma a ce wa azzãlumai, "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã
aikatãwa."
|
Ayah 39:25 الأية
كَذَّبَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَأَتَاهُمُ الْعَذَابُ مِنْ حَيْثُ لَا
يَشْعُرُونَ
Kaththaba allatheena minqablihim faatahumu alAAathabu min haythu layashAAuroon
Hausa
Waɗanda ke a gabãninsu, sun ƙaryata, sai azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani
ba.
|
Ayah 39:26 الأية
فَأَذَاقَهُمُ اللهُ الْخِزْيَ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۖ وَلَعَذَابُ
الْآخِرَةِ أَكْبَرُ ۚ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ
Faathaqahumu Allahu alkhizyafee alhayati addunya walaAAathabual-akhirati akbaru
law kanoo yaAAlamoon
Hausa
Sai Allah Ya ɗanɗana musu azãbar wulãkanci a cikin rãyuwar dũniya, kuma lalle
azãbar Lãhira ita ce mafi girma, dã sun kasance sunã da sani.
|
Ayah 39:27 الأية
وَلَقَدْ ضَرَبْنَا لِلنَّاسِ فِي هَٰذَا الْقُرْآنِ مِن كُلِّ مَثَلٍ لَّعَلَّهُمْ
يَتَذَكَّرُونَ
Walaqad darabna linnasifee hatha alqur-ani min kulli mathalin
laAAallahumyatathakkaroon
Hausa
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun buga wa mutãne a, cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane
misãli, ɗammãninsu su yi tunãni.
|
Ayah 39:28 الأية
قُرْآنًا عَرَبِيًّا غَيْرَ ذِي عِوَجٍ لَّعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ
Qur-anan AAarabiyyan ghayra theeAAiwajin laAAallahum yattaqoon
Hausa
Abin karantãwa ne na Lãrabci, ba mai wata karkata ba, ɗammãninsu, su yi taƙawa.
|
Ayah 39:29 الأية
ضَرَبَ اللهُ مَثَلًا رَّجُلًا فِيهِ شُرَكَاءُ مُتَشَاكِسُونَ وَرَجُلًا سَلَمًا
لِّرَجُلٍ هَلْ يَسْتَوِيَانِ مَثَلًا ۚ الْحَمْدُ لِلَّهِ ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا
يَعْلَمُونَ
Daraba Allahu mathalan rajulanfeehi shurakao mutashakisoona warajulan
salamanlirajulin hal yastawiyani mathalan alhamdu lillahibal aktharuhum la
yaAAlamoon
Hausa
Allah Yã buga misãli; wani mutum (bãwa) a cikinsa akwai mãsu tarayya, mãsu mũgun
hãlin jãyayya, da wani mutum (bãwa) dukansa ga wani mutum. Shin, zã su daidaita
ga misãli? Gõdiya ta tabbata ga Allah (a kan bayãni). Ã'a, mafi yawan mutãne ba
su sani ba.
|
Ayah 39:30 الأية
إِنَّكَ مَيِّتٌ وَإِنَّهُم مَّيِّتُونَ
Innaka mayyitun wa-innahum mayyitoon
Hausa
Lalle kai mai mutuwa ne, kuma su mã lalle mãsu mutuwa ne.
|
Ayah 39:31 الأية
ثُمَّ إِنَّكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ عِندَ رَبِّكُمْ تَخْتَصِمُونَ
Thumma innakum yawma alqiyamatiAAinda rabbikum takhtasimoon
Hausa
Sa'an nan, lalle kũ, a Rãnar ¡iyãma, a wurin Ubangijinku, zã ku yi ta yin
husũma.
|
Ayah 39:32 الأية
فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن كَذَبَ عَلَى اللهِ وَكَذَّبَ بِالصِّدْقِ إِذْ جَاءَهُ ۚ
أَلَيْسَ فِي جَهَنَّمَ مَثْوًى لِّلْكَافِرِينَ
Faman athlamu mimman kathabaAAala Allahi wakaththaba bissidqiith jaahu alaysa
fee jahannama mathwan lilkafireen
Hausa
To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya yi ƙarya ga Allah, kuma ya ƙaryata
gaskiya a lõkacin da ta jẽ masa? Shin bãbu mazauni a cikin Jahannama ga kãfirai?
|
Ayah 39:33 الأية
وَالَّذِي جَاءَ بِالصِّدْقِ وَصَدَّقَ بِهِ ۙ أُولَٰئِكَ هُمُ الْمُتَّقُونَ
Wallathee jaa bissidqiwasaddaqa bihi ola-ika humu almuttaqoon
Hausa
Kuma wanda ya zo da gaskiya, kuma ya gaskata a game da ita, waɗancan sũ ne mãsu
taƙawa.
|
Ayah 39:34 الأية
لَهُم مَّا يَشَاءُونَ عِندَ رَبِّهِمْ ۚ ذَٰلِكَ جَزَاءُ الْمُحْسِنِينَ
Lahum ma yashaoona AAindarabbihim thalika jazao almuhsineen
Hausa
Sunã da abin da suke so wajen Ubangijinsu. Wancan shĩ ne sakamakon mãsu
kyautatãwa.
|
Ayah 39:35 الأية
لِيُكَفِّرَ اللهُ عَنْهُمْ أَسْوَأَ الَّذِي عَمِلُوا وَيَجْزِيَهُمْ أَجْرَهُم
بِأَحْسَنِ الَّذِي كَانُوا يَعْمَلُونَ
Liyukaffira Allahu AAanhum aswaa allatheeAAamiloo wayajziyahum ajrahum bi-ahsani
allathee kanooyaAAmaloon
Hausa
Dõmin Allah Ya kankare musu mafi mũnin abin da suka aikata, kuma Ya sãkã musu
ijãrarsu da mafi kyaun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
|
Ayah 39:36 الأية
أَلَيْسَ اللهُ بِكَافٍ عَبْدَهُ ۖ وَيُخَوِّفُونَكَ بِالَّذِينَ مِن دُونِهِ ۚ
وَمَن يُضْلِلِ اللهُ فَمَا لَهُ مِنْ هَادٍ
Alaysa Allahu bikafin AAabdahuwayukhawwifoonaka billatheena min doonihi waman
yudliliAllahu fama lahu min had
Hausa
Ashe Allah bai zama Mai isa ga BãwanSa ba? Kuma sunã tsõratar da kai ga waɗanda
suke waninSa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to, bã, shi da mai shiryarwa.
|
Ayah 39:37 الأية
وَمَن يَهْدِ اللهُ فَمَا لَهُ مِن مُّضِلٍّ ۗ أَلَيْسَ اللهُ بِعَزِيزٍ ذِي
انتِقَامٍ
Waman yahdi Allahu fama lahumin mudillin alaysa Allahu biAAazeezin theeintiqam
Hausa
Kuma wanda Allah Ya shiryar, to, bã shi da mai ɓatarwa. Ashe, Allah bai zama
Mabuwãyi ba, Mai azãbar rãmuwa?
|
Ayah 39:38 الأية
وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ لَيَقُولُنَّ اللهُ
ۚ قُلْ أَفَرَأَيْتُم مَّا تَدْعُونَ مِن دُونِ اللهِ إِنْ أَرَادَنِيَ اللهُ
بِضُرٍّ هَلْ هُنَّ كَاشِفَاتُ ضُرِّهِ أَوْ أَرَادَنِي بِرَحْمَةٍ هَلْ هُنَّ
مُمْسِكَاتُ رَحْمَتِهِ ۚ قُلْ حَسْبِيَ اللهُ ۖ عَلَيْهِ يَتَوَكَّلُ
الْمُتَوَكِّلُونَ
Wala-in saaltahum man khalaqa assamawatiwal-arda layaqoolunna Allahu qul
afaraaytumma tadAAoona min dooni Allahi in aradaniyaAllahu bidurrin hal hunna
kashifatu durrihiaw aradanee birahmatin hal hunna mumsikaturahmatihi qul hasbiya
Allahu AAalayhiyatawakkalu almutawakkiloon
Hausa
Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wane ne ya halitta sammai da ƙasã?" Haƙĩƙa, zã
su ce, "Allah ne." Ka ce: "Ashe, to, kun gani abin da kuke kira, waɗanda suke
wanin Allah ne, idan Allah Ya nufe ni da wata cũta, shin sũ abũbuwan nan mãsu
kuranye, cutarsa ne? Kõ kuma Ya nufe ni da wata rahama, shin, su abũbuwan nan
mãsu kãme rahamarSa ne?" Ka ce: "Mai isata Allah ne, gare Shi mãsu tawakkali ke
dõgara."
|
Ayah 39:39 الأية
قُلْ يَا قَوْمِ اعْمَلُوا عَلَىٰ مَكَانَتِكُمْ إِنِّي عَامِلٌ ۖ فَسَوْفَ
تَعْلَمُونَ
Qul ya qawmi iAAmaloo AAalamakanatikum innee AAamilun fasawfa taAAlamoon
Hausa
Ka ce: "Yã mutãnena! Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle nĩ, inã aiki a kan hãlĩna.
Sa'an nan zã ku sani."
|
Ayah 39:40 الأية
مَن يَأْتِيهِ عَذَابٌ يُخْزِيهِ وَيَحِلُّ عَلَيْهِ عَذَابٌ مُّقِيمٌ
Man ya/teehi AAathabun yukhzeehi wayahilluAAalayhi AAathabun muqeem
Hausa
"Wanda azãba ta je masa, zã ta wulãkanta shi, kuma wata azãba mai dawwama za ta
sauka a kansa."
|
Ayah 39:41 الأية
إِنَّا أَنزَلْنَا عَلَيْكَ الْكِتَابَ لِلنَّاسِ بِالْحَقِّ ۖ فَمَنِ اهْتَدَىٰ
فَلِنَفْسِهِ ۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيْهَا ۖ وَمَا أَنتَ عَلَيْهِم
بِوَكِيلٍ
Inna anzalna AAalayka alkitabalinnasi bilhaqqi famani ihtadafalinafsihi waman
dalla fa-innama yadilluAAalayha wama anta AAalayhim biwakeel
Hausa
Lalle Mũ Mun saukar da littãfi a gare ka dõmin mutãne da gaskiya. Sa'an nan
wanda ya nẽmi shiriya, to, dõmin kansa, kuma wanda ya ɓace, to, yanã ɓacẽwa ne a
kanta. Kuma ba ka zama wakĩli a kansu ba.
|
Ayah 39:42 الأية
اللهُ يَتَوَفَّى الْأَنفُسَ حِينَ مَوْتِهَا وَالَّتِي لَمْ تَمُتْ فِي
مَنَامِهَا ۖ فَيُمْسِكُ الَّتِي قَضَىٰ عَلَيْهَا الْمَوْتَ وَيُرْسِلُ
الْأُخْرَىٰ إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ
يَتَفَكَّرُونَ
Allahu yatawaffa al-anfusa heenamawtiha wallatee lam tamut fee manamihafayumsiku
allatee qada AAalayha almawta wayursilual-okhra ila ajalin musamman inna fee
thalikalaayatin liqawmin yatafakkaroon
Hausa
Allah ne ke karɓar rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a
cikin barcinsu. Sa'an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki
gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga
mutãne waɗanda ke yin tunãni.
|
Ayah 39:43 الأية
أَمِ اتَّخَذُوا مِن دُونِ اللهِ شُفَعَاءَ ۚ قُلْ أَوَلَوْ كَانُوا لَا
يَمْلِكُونَ شَيْئًا وَلَا يَعْقِلُونَ
Ami ittakhathoo min dooni AllahishufaAAaa qul awa law kanoo la yamlikoonashay-an
wala yaAAqiloon
Hausa
Kõ kuma sun riƙi mãsu cẽto ne, waɗansun Allah? Ka ce: "Shin, kuma kõ dã sun
kasance bã su da mallakar kõme, kuma bã su hankalta?"
|
Ayah 39:44 الأية
قُل لِّلَّهِ الشَّفَاعَةُ جَمِيعًا ۖ لَّهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ
ثُمَّ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Qul lillahi ashshafaAAatujameeAAan lahu mulku assamawati wal-ardithumma ilayhi
turjaAAoon
Hausa
Ka ce: "Cẽto gabã ɗaya ga Allah yake. Mulkin sammai da ƙasã Nãsa ne. Sa'an nan
zuwa gare Shi ake mayar da ku."
|
Ayah 39:45 الأية
وَإِذَا ذُكِرَ اللهُ وَحْدَهُ اشْمَأَزَّتْ قُلُوبُ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ
بِالْآخِرَةِ ۖ وَإِذَا ذُكِرَ الَّذِينَ مِن دُونِهِ إِذَا هُمْ يَسْتَبْشِرُونَ
Wa-itha thukira Allahuwahdahu ishmaazzat quloobu allatheena layu/minoona
bil-akhirati wa-itha thukiraallatheena min doonihi itha hum yastabshiroon
Hausa
Kuma idan aka ambaci Allah Shi kaɗai zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni ba da
Lãhira, su yi ƙiyãma, kuma idan an ambaci waɗanda suke kiran, wasunSa, sai gãsu
sunã yin bushãrar farin ciki.
|
Ayah 39:46 الأية
قُلِ اللهُمَّ فَاطِرَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ عَالِمَ الْغَيْبِ
وَالشَّهَادَةِ أَنتَ تَحْكُمُ بَيْنَ عِبَادِكَ فِي مَا كَانُوا فِيهِ
يَخْتَلِفُونَ
Quli allahumma fatira assamawatiwal-ardi AAalima alghaybi washshahadatianta
tahkumu bayna AAibadika fee ma kanoofeehi yakhtalifoon
Hausa
Ka ce: "Ya Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasã, Masanin gaibi da bayyane!
Kai ne ke yin hukunci a tsakãnin bãyinKa a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa
wa jũna a cikinsa."
|
Ayah 39:47 الأية
وَلَوْ أَنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا مَا فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا وَمِثْلَهُ مَعَهُ
لَافْتَدَوْا بِهِ مِن سُوءِ الْعَذَابِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۚ وَبَدَا لَهُم مِّنَ
اللهِ مَا لَمْ يَكُونُوا يَحْتَسِبُونَ
Walaw anna lillatheena thalamooma fee al-ardi jameeAAan wamithlahu maAAahu
laftadawbihi min soo-i alAAathabi yawma alqiyamati wabadalahum mina Allahi ma
lam yakoonoo yahtasiboon
Hausa
Kuma dã waɗanda suka yi zãlunci sunã da abin da ke cikin ƙasã gaba ɗaya, da
misãlinsa a tãre da shi lalle dã sun yi fansa da shi daga mummunar azãba, a
Rãnar ¡iyãma. Kuma abin da ba su kasance sunã zato ba, daga Allah, ya bayyana a
gare su.
|
Ayah 39:48 الأية
وَبَدَا لَهُمْ سَيِّئَاتُ مَا كَسَبُوا وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا بِهِ
يَسْتَهْزِئُونَ
Wabada lahum sayyi-atu makasaboo wahaqa bihim ma kanoo bihiyastahzi-oon
Hausa
Mũnãnan ayyuka da suka aikata, suka bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance
sunã yi, na izgili, ya wajaba a kansu.
|
Ayah 39:49 الأية
فَإِذَا مَسَّ الْإِنسَانَ ضُرٌّ دَعَانَا ثُمَّ إِذَا خَوَّلْنَاهُ نِعْمَةً
مِّنَّا قَالَ إِنَّمَا أُوتِيتُهُ عَلَىٰ عِلْمٍ ۚ بَلْ هِيَ فِتْنَةٌ وَلَٰكِنَّ
أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Fa-itha massa al-insana durrundaAAana thumma itha khawwalnahuniAAmatan minna
qala innama ooteetuhu AAalaAAilmin bal hiya fitnatun walakinna aktharahum
layaAAlamoon
Hausa
To, idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, sa'an nan idan Muka canza
masa ita, ya sãmi ni'ima daga gare Mu, sai ya ce: "An bã ni ita ne a kan wani
ilmi nãwa kawai." Ã'a ita wannan (magana) fitina ce, kuma amma mafi yawansu ba
su sani ba.
|
Ayah 39:50 الأية
قَدْ قَالَهَا الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَمَا أَغْنَىٰ عَنْهُم مَّا كَانُوا
يَكْسِبُونَ
Qad qalaha allatheenamin qablihim fama aghna AAanhum ma kanooyaksiboon
Hausa
Lalle waɗanda ke a gabãninsu, sun faɗe ta, sabõda haka abin da suka kasance sunã
aikatãwa bai wadãtar da su da kõme ba.
|
Ayah 39:51 الأية
فَأَصَابَهُمْ سَيِّئَاتُ مَا كَسَبُوا ۚ وَالَّذِينَ ظَلَمُوا مِنْ هَٰؤُلَاءِ
سَيُصِيبُهُمْ سَيِّئَاتُ مَا كَسَبُوا وَمَا هُم بِمُعْجِزِينَ
Faasabahum sayyi-atu makasaboo wallatheena thalamoo min haola-isayuseebuhum
sayyi-atu ma kasaboo wamahum bimuAAjizeen
Hausa
Sai (sakamakon) mũnãnan abin da suka aikata ya same su. Kuma waɗanda suka yi
zãlunci daga waɗannan, (sakamakon) munãnan abin da suka aikata zai sãme su, kuma
ba su zama mabuwãya ba.
|
Ayah 39:52 الأية
أَوَلَمْ يَعْلَمُوا أَنَّ اللهَ يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاءُ وَيَقْدِرُ ۚ
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Awa lam yaAAlamoo anna Allaha yabsutuarrizqa liman yashao wayaqdiru inna fee
thalikalaayatin liqawmin yu/minoon
Hausa
Ashe kuma ba su sani ba cẽwa Allah, na shimfiɗa arziƙi ga wanda Yake so, kuma
Yanã ƙuƙuntawa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin ĩmãni.
|
Ayah 39:53 الأية
قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِن
رَّحْمَةِ اللهِ ۚ إِنَّ اللهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ
الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
Qul ya AAibadiya allatheenaasrafoo AAala anfusihim la taqnatoo min rahmatiAllahi
inna Allaha yaghfiru aththunoobajameeAAan innahu huwa alghafooru arraheem
Hausa
Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi barna a kan rãyukansu! Kada ku
yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle
Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."
|
Ayah 39:54 الأية
وَأَنِيبُوا إِلَىٰ رَبِّكُمْ وَأَسْلِمُوا لَهُ مِن قَبْلِ أَن يَأْتِيَكُمُ
الْعَذَابُ ثُمَّ لَا تُنصَرُونَ
Waaneeboo ila rabbikum waaslimoo lahumin qabli an ya/tiyakumu alAAathabu thumma
la tunsaroon
Hausa
"Kuma ku mayar da al'amari zuwa ga Ubangijinku, kuma ku sallama Masa, a gabãnin
azãba ta zo muku, sa'an nan kuwa bã zã a taimake ku ba."
|
Ayah 39:55 الأية
وَاتَّبِعُوا أَحْسَنَ مَا أُنزِلَ إِلَيْكُم مِّن رَّبِّكُم مِّن قَبْلِ أَن
يَأْتِيَكُمُ الْعَذَابُ بَغْتَةً وَأَنتُمْ لَا تَشْعُرُونَ
WattabiAAoo ahsana maonzila ilaykum min rabbikum min qabli an ya/tiyakumu
alAAathabubaghtatan waantum la tashAAuroon
Hausa
"Kuma ku bi mafi kyaun abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, a
gabãnin azãba ta zo muku, bisa auke, kuma kũ ba ku sani ba."
|
Ayah 39:56 الأية
أَن تَقُولَ نَفْسٌ يَا حَسْرَتَا عَلَىٰ مَا فَرَّطتُ فِي جَنبِ اللهِ وَإِن
كُنتُ لَمِنَ السَّاخِرِينَ
An taqoola nafsun ya hasrataAAala ma farrattu fee janbi Allahiwa-in kuntu lamina
assakhireen
Hausa
"Kada wani rai ya ce: 'Yã nadãmãta a kan abin da na yi sakaci a cikin sãshen
Allah' kuma lalle na kasance, haƙĩƙa, daga mãsu izgili!"'
|
Ayah 39:57 الأية
أَوْ تَقُولَ لَوْ أَنَّ اللهَ هَدَانِي لَكُنتُ مِنَ الْمُتَّقِينَ
Aw taqoola law anna Allaha hadaneelakuntu mina almuttaqeen
Hausa
"Ko kuma (kada) ya ce: 'Da Allah Ya shiryar da ni, dã na kasance daga mãsu
taƙawa.'"
|
Ayah 39:58 الأية
أَوْ تَقُولَ حِينَ تَرَى الْعَذَابَ لَوْ أَنَّ لِي كَرَّةً فَأَكُونَ مِنَ
الْمُحْسِنِينَ
Aw taqoola heena tara alAAathabalaw anna lee karratan faakoona mina almuhsineen
Hausa
"Ko kuma (kada (ya ce: a lõkacin da yake ganin azãba, 'Dã lalle a ce inã da wata
kõmawa (zuwa dũniya) dõmin in kasance daga mãsu kyautatãwa.'"
|
Ayah 39:59 الأية
بَلَىٰ قَدْ جَاءَتْكَ آيَاتِي فَكَذَّبْتَ بِهَا وَاسْتَكْبَرْتَ وَكُنتَ مِنَ
الْكَافِرِينَ
Bala qad jaatka ayateefakaththabta biha wastakbarta wakunta minaalkafireen
Hausa
"Na'am! Lalle ne ãyõyiNa sun jẽ maka, sai ka ƙaryata a game da su, kuma ka yi
girman kai, kuma ka kasance daga kãfirai."
|
Ayah 39:60 الأية
وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ تَرَى الَّذِينَ كَذَبُوا عَلَى اللهِ وُجُوهُهُم
مُّسْوَدَّةٌ ۚ أَلَيْسَ فِي جَهَنَّمَ مَثْوًى لِّلْمُتَكَبِّرِينَ
Wayawma alqiyamati tara allatheenakathaboo AAala Allahi wujoohuhum
muswaddatunalaysa fee jahannama mathwan lilmutakabbireen
Hausa
Kuma a Rãnar ¡iyãma kanã ganin waɗanda suka yi ƙarya ga Allah fuskõkinsu sunã
mãsu yin baƙi. Ashe bãbu mazauni a cikin Jahannama ga mãsu girman kai?
|
Ayah 39:61 الأية
وَيُنَجِّي اللهُ الَّذِينَ اتَّقَوْا بِمَفَازَتِهِمْ لَا يَمَسُّهُمُ السُّوءُ
وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ
Wayunajjee Allahu allatheenaittaqaw bimafazatihim la yamassuhumu assoo-owala hum
yahzanoon
Hausa
Kuma Allah na tsĩrar da waɗanda suka yi taƙawa a game da wurin sãmun babban
rabonsu, cũta bã zã tashãfe su ba, kuma ba su zama sunã baƙin ciki ba.
|
Ayah 39:62 الأية
اللهُ خَالِقُ كُلِّ شَيْءٍ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ وَكِيلٌ
Allahu khaliqu kulli shay-inwahuwa AAala kulli shay-in wakeel
Hausa
Allah ne Mai halitta dukan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme.
|
Ayah 39:63 الأية
لَّهُ مَقَالِيدُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۗ وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِ
اللهِ أُولَٰئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ
Lahu maqaleedu assamawatiwal-ardi wallatheena kafaroo bi-ayatiAllahi ola-ika
humu alkhasiroon
Hausa
Shĩ ke da mabũɗan sammai da ƙasã. Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah,
waɗannan sũ nemãsu hasãra.
|
Ayah 39:64 الأية
قُلْ أَفَغَيْرَ اللهِ تَأْمُرُونِّي أَعْبُدُ أَيُّهَا الْجَاهِلُونَ
Qul afaghayra Allahi ta/muroonneeaAAbudu ayyuha aljahiloon
Hausa
Ka ce: "Shin, wanin Allah kuke umurni na da in bauta wa? Yã ku jãhilai!"
|
Ayah 39:65 الأية
وَلَقَدْ أُوحِيَ إِلَيْكَ وَإِلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكَ لَئِنْ أَشْرَكْتَ
لَيَحْبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ
Walaqad oohiya ilayka wa-ilaallatheena min qablika la-in ashrakta
layahbatannaAAamaluka walatakoonanna mina alkhasireen
Hausa
Kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka, "Lalle
idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu
hasãra."
|
Ayah 39:66 الأية
بَلِ اللهَ فَاعْبُدْ وَكُن مِّنَ الشَّاكِرِينَ
Bali Allaha faAAbud wakunmina ashshakireen
Hausa
Ã'aha! Ka bauta wa Allah kaɗai, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya.
|
Ayah 39:67 الأية
وَمَا قَدَرُوا اللهَ حَقَّ قَدْرِهِ وَالْأَرْضُ جَمِيعًا قَبْضَتُهُ يَوْمَ
الْقِيَامَةِ وَالسَّمَاوَاتُ مَطْوِيَّاتٌ بِيَمِينِهِ ۚ سُبْحَانَهُ وَتَعَالَىٰ
عَمَّا يُشْرِكُونَ
Wama qadaroo Allaha haqqaqadrihi wal-ardu jameeAAan qabdatuhu yawmaalqiyamati
wassamawatu matwiyyatunbiyameenihi subhanahu wataAAala AAammayushrikoon
Hausa
Kuma ba su ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin ĩkon yinsa ba: ¡asã duka damƙarSa ce, a
Rãnar ¡iyãma, kuma sammai abũbuwan naɗewa ne ga dãmanSa. Tsarki ya tabbata a
gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga barin abin da suke shirki da shi.
|
Ayah 39:68 الأية
وَنُفِخَ فِي الصُّورِ فَصَعِقَ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَمَن فِي الْأَرْضِ إِلَّا
مَن شَاءَ اللهُ ۖ ثُمَّ نُفِخَ فِيهِ أُخْرَىٰ فَإِذَا هُمْ قِيَامٌ يَنظُرُونَ
Wanufikha fee assoori fasaAAiqaman fee assamawati waman fee al-ardiilla man shaa
Allahu thumma nufikha feehiokhra fa-itha hum qiyamun yanthuroon
Hausa
Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasã suka sũma sai
wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa'an nan aka hũra a cikinsa, wata hũrãwa,
sai gã su tsaitsaye, sunã kallo.
|
Ayah 39:69 الأية
وَأَشْرَقَتِ الْأَرْضُ بِنُورِ رَبِّهَا وَوُضِعَ الْكِتَابُ وَجِيءَ
بِالنَّبِيِّينَ وَالشُّهَدَاءِ وَقُضِيَ بَيْنَهُم بِالْحَقِّ وَهُمْ لَا
يُظْلَمُونَ
Waashraqati al-ardu binoori rabbihawawudiAAa alkitabu wajee-a
binnabiyyeenawashshuhada-i waqudiya baynahum bilhaqqiwahum la yuthlamoon
Hausa
Kuma ƙasã ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littãfi, kuma aka zo
da Annabãwa da mãsu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakãninsu, da gaskiya, alhãli
kuwa, sũ, bã zã a zãlunce su ba.
|
Ayah 39:70 الأية
وَوُفِّيَتْ كُلُّ نَفْسٍ مَّا عَمِلَتْ وَهُوَ أَعْلَمُ بِمَا يَفْعَلُونَ
Wawuffiyat kullu nafsin ma AAamilatwahuwa aAAlamu bima yafAAaloon
Hausa
Kuma aka cika wa kõwane rai abin da ya aikata. Kuma (Allah) Shĩ ne Mafi sani
game da abin da suke aikatãwa.
|
Ayah 39:71 الأية
وَسِيقَ الَّذِينَ كَفَرُوا إِلَىٰ جَهَنَّمَ زُمَرًا ۖ حَتَّىٰ إِذَا جَاءُوهَا
فُتِحَتْ أَبْوَابُهَا وَقَالَ لَهُمْ خَزَنَتُهَا أَلَمْ يَأْتِكُمْ رُسُلٌ
مِّنكُمْ يَتْلُونَ عَلَيْكُمْ آيَاتِ رَبِّكُمْ وَيُنذِرُونَكُمْ لِقَاءَ
يَوْمِكُمْ هَٰذَا ۚ قَالُوا بَلَىٰ وَلَٰكِنْ حَقَّتْ كَلِمَةُ الْعَذَابِ عَلَى
الْكَافِرِينَ
Waseeqa allatheena kafaroo ilajahannama zumaran hatta itha jaoohafutihat
abwabuha waqala lahumkhazanatuha alam ya/tikum rusulun minkum yatloonaAAalaykum
ayati rabbikum wayunthiroonakumliqaa yawmikum hatha qaloo bala walakinhaqqat
kalimatu alAAathabi AAala alkafireen
Hausa
Kuma aka kõra waɗanda suka kãfirta zuwa Jahannama, jama'a-jama'a har a lõkacin
da suka je mata, sai aka buɗe ƙõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Ashe,
waɗansu Manzanni, daga cikinku ba su je muku ba, sunã karanta ãyõyin Ubangijinku
a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin gamuwa da yininku wannan?" Suka ce, "Na'am,
"kuma amma kalmar azãba ita ce ta wajaba a kan kãfirai!"
|
Ayah 39:72 الأية
قِيلَ ادْخُلُوا أَبْوَابَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا ۖ فَبِئْسَ مَثْوَى
الْمُتَكَبِّرِينَ
Qeela odkhuloo abwaba jahannama khalideenafeeha fabi/sa mathwa almutakabbireen
Hausa
Aka ce, "Ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kaunã madawwama a cikinta. Sa'an nan
mazaunin makangara yã munana."
|
Ayah 39:73 الأية
وَسِيقَ الَّذِينَ اتَّقَوْا رَبَّهُمْ إِلَى الْجَنَّةِ زُمَرًا ۖ حَتَّىٰ إِذَا
جَاءُوهَا وَفُتِحَتْ أَبْوَابُهَا وَقَالَ لَهُمْ خَزَنَتُهَا سَلَامٌ عَلَيْكُمْ
طِبْتُمْ فَادْخُلُوهَا خَالِدِينَ
Waseeqa allatheena ittaqaw rabbahumila aljannati zumaran hatta itha
jaoohawafutihat abwabuha waqala lahumkhazanatuha salamun AAalaykum tibtum
fadkhuloohakhalideen
Hausa
Kuma aka kõra waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa zuwa Aljanna jama'a-jama'a
har a lõkacin da suka jẽ mata, alhãli kuwa an buɗe kõfõfinta, kuma matsaranta
suka ce musu, "Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji dãɗi, sabõda haka ku shige
ta, kunã madawwama( a cikinta)."
|
Ayah 39:74 الأية
وَقَالُوا الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي صَدَقَنَا وَعْدَهُ وَأَوْرَثَنَا الْأَرْضَ
نَتَبَوَّأُ مِنَ الْجَنَّةِ حَيْثُ نَشَاءُ ۖ فَنِعْمَ أَجْرُ الْعَامِلِينَ
Waqaloo alhamdu lillahiallathee sadaqana waAAdahu waawrathanaal-arda natabawwao
mina aljannati haythu nashaofaniAAma ajru alAAamileen
Hausa
Kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya yi mana gaskiya ga wa'adinSa,
kuma Ya gãdar da mu ƙasã, munã zama a cikin Aljanna a inda muke so." To, madalla
da ijãrar ma'aikata.
|
Ayah 39:75 الأية
وَتَرَى الْمَلَائِكَةَ حَافِّينَ مِنْ حَوْلِ الْعَرْشِ يُسَبِّحُونَ بِحَمْدِ
رَبِّهِمْ ۖ وَقُضِيَ بَيْنَهُم بِالْحَقِّ وَقِيلَ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ
الْعَالَمِينَ
Watara almala-ikata haffeenamin hawli alAAarshi yusabbihoona bihamdirabbihim
waqudiya baynahum bilhaqqi waqeelaalhamdu lillahi rabbi alAAalameen
Hausa
Kuma kanã ganin malã'iku sunã mãsu tsayãwa da haƙƙoƙin da aka ɗõra musu daga
kẽwayen Al'arshi, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu. Kuma aka yi hukunci
a tsakãninsu da gaskiya. Kuma aka ce, "Gõdiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin
halittu."
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|