1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
Ayah 45:2 الأية
تَنزِيلُ الْكِتَابِ مِنَ اللهِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ
Tanzeelu alkitabi mina AllahialAAazeezi alhakeem
Hausa
Saukar Littãfi daga Allah Mabuwãyi Mai hikima yake.
|
Ayah 45:3 الأية
إِنَّ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ لَآيَاتٍ لِّلْمُؤْمِنِينَ
Inna fee assamawati wal-ardilaayatin lilmu/mineen
Hausa
Lalle ne a cikin sammai da ƙasa akwai ãyõyi ga mãsu ĩmãni.
|
Ayah 45:4 الأية
وَفِي خَلْقِكُمْ وَمَا يَبُثُّ مِن دَابَّةٍ آيَاتٌ لِّقَوْمٍ يُوقِنُونَ
Wafee khalqikum wama yabuththu min dabbatinayatun liqawmin yooqinoon
Hausa
Kuma a cikin halittarku da abin da ke watsuwa na dabba akwai ãyõyi ga mutãne
mãsu yaƙĩni.
|
Ayah 45:5 الأية
وَاخْتِلَافِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَمَا أَنزَلَ اللهُ مِنَ السَّمَاءِ مِن
رِّزْقٍ فَأَحْيَا بِهِ الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا وَتَصْرِيفِ الرِّيَاحِ آيَاتٌ
لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ
Wakhtilafi allayli wannahariwama anzala Allahu mina assama-i minrizqin faahya
bihi al-arda baAAda mawtihawatasreefi arriyahi ayatunliqawmin yaAAqiloon
Hausa
Kuma da sãɓawar dare da yini da abin da Allah Ya saukar daga sama na arziki,
sa'an nan Ya rãyar da ƙasa game da shi a bãyan mutuwarta, da jũyawar iskõki,
akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali.
|
Ayah 45:6 الأية
تِلْكَ آيَاتُ اللهِ نَتْلُوهَا عَلَيْكَ بِالْحَقِّ ۖ فَبِأَيِّ حَدِيثٍ بَعْدَ
اللهِ وَآيَاتِهِ يُؤْمِنُونَ
Tilka ayatu Allahinatlooha AAalayka bilhaqqi fabi-ayyi hadeethinbaAAda Allahi
waayatihi yu/minoon
Hausa
Waɗancan ãyõyin Allah ne, Munã karanta su gare ka da gaskiya. To, da wane lãbãri
bãyan Allah da ãyõyinSa suke yin ĩmãni?
|
Ayah 45:7 الأية
وَيْلٌ لِّكُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ
Waylun likulli affakin atheem
Hausa
Bone ya tabbata ga dukan mai yawan ƙiren ƙarya, mai laifi.
|
Ayah 45:8 الأية
يَسْمَعُ آيَاتِ اللهِ تُتْلَىٰ عَلَيْهِ ثُمَّ يُصِرُّ مُسْتَكْبِرًا كَأَن
لَّمْ يَسْمَعْهَا ۖ فَبَشِّرْهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ
YasmaAAu ayati Allahitutla AAalayhi thumma yusirru mustakbiran kaan lamyasmaAAha
fabashshirhu biAAathabin aleem
Hausa
Yanã jin ãyõyin Allah anã karanta su a kansa, sa'an nan ya dõge yanã makãngari,
kamar bai jĩ su ba. To, ka yi masa bushara da azãba mai raɗaɗi.
|
Ayah 45:9 الأية
وَإِذَا عَلِمَ مِنْ آيَاتِنَا شَيْئًا اتَّخَذَهَا هُزُوًا ۚ أُولَٰئِكَ لَهُمْ
عَذَابٌ مُّهِينٌ
Wa-itha AAalima min ayatinashay-an ittakhathaha huzuwan ola-ika lahumAAathabun
muheen
Hausa
Kuma har idan ya san wani abu daga ãyõyinMu, sai ya rika su da izgili. Waɗancan
sunã da wata azãba mai wulãkantãwa (a dũniya).
|
Ayah 45:10 الأية
مِّن وَرَائِهِمْ جَهَنَّمُ ۖ وَلَا يُغْنِي عَنْهُم مَّا كَسَبُوا شَيْئًا وَلَا
مَا اتَّخَذُوا مِن دُونِ اللهِ أَوْلِيَاءَ ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Min wara-ihim jahannamu walayughnee AAanhum ma kasaboo shay-an wala
maittakhathoo min dooni Allahi awliyaa walahumAAathabun AAatheem
Hausa
Gaba gare su (a Lãhira) akwai Jahannama, kuma abin da suka sanã'anta bã ya
wadãtar da su daga kõme, kuma abũbuwan da suka riƙa majiɓinta, baicin Allah, bã
su wãdatar da su daga kõme. Kuma sunã da wata azãba mai girma.
|
Ayah 45:11 الأية
هَٰذَا هُدًى ۖ وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِ رَبِّهِمْ لَهُمْ عَذَابٌ مِّن
رِّجْزٍ أَلِيمٌ
Hatha hudan wallatheenakafaroo bi-ayati rabbihim lahum AAathabunmin rijzin aleem
Hausa
Wannan (Alƙur'ãni) shi ne shiryuwa. Kuma waɗanda suka kãfirta game da ãyõyin
Ubangijinsu, sunã da wata azãba ta wulãkanci mai raɗaɗi.
|
Ayah 45:12 الأية
اللهُ الَّذِي سَخَّرَ لَكُمُ الْبَحْرَ لِتَجْرِيَ الْفُلْكُ فِيهِ بِأَمْرِهِ
وَلِتَبْتَغُوا مِن فَضْلِهِ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Allahu allathee sakhkharalakumu albahra litajriya alfulku feehi
bi-amrihiwalitabtaghoo min fadlihi walaAAallakum tashkuroon
Hausa
Allah ne wanda Ya hõre muku tẽku dõmin jirgi ya gudãna a cikinta da umurninSa,
kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, kuma tsammãninku zã ku gõde.
|
Ayah 45:13 الأية
وَسَخَّرَ لَكُم مَّا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا مِّنْهُ ۚ
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ
Wasakhkhara lakum ma fee assamawatiwama fee al-ardi jameeAAan minhu inna fee
thalikalaayatin liqawmin yatafakkaroon
Hausa
Kuma Ya hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasa, gabã
ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne
waɗanda ke yin tunãni.
|
Ayah 45:14 الأية
قُل لِّلَّذِينَ آمَنُوا يَغْفِرُوا لِلَّذِينَ لَا يَرْجُونَ أَيَّامَ اللهِ
لِيَجْزِيَ قَوْمًا بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ
Qul lillatheena amanooyaghfiroo lillatheena la yarjoona ayyama Allahiliyajziya
qawman bima kanoo yaksiboon
Hausa
Ka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, su yi gãfara ga waɗanda bã su fãtan rahama ga
kwãnukan Allah, dõmin (Allah) Ya sãka wa mutãne da abin da suka kasance sunã
aikatãwa.
|
Ayah 45:15 الأية
مَنْ عَمِلَ صَالِحًا فَلِنَفْسِهِ ۖ وَمَنْ أَسَاءَ فَعَلَيْهَا ۖ ثُمَّ إِلَىٰ
رَبِّكُمْ تُرْجَعُونَ
Man AAamila salihanfalinafsihi waman asaa faAAalayha thumma ilarabbikum
turjaAAoon
Hausa
Wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, dõmin kansã, kuma wanda ya mũnana aki, to, a
kansa. Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku.
|
Ayah 45:16 الأية
وَلَقَدْ آتَيْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ
وَرَزَقْنَاهُم مِّنَ الطَّيِّبَاتِ وَفَضَّلْنَاهُمْ عَلَى الْعَالَمِينَ
Walaqad atayna banee isra-eelaalkitaba walhukma wannubuwwatawarazaqnahum mina
attayyibati wafaddalnahumAAala alAAalameen
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai (wa Bãnĩ Isrã'ĩla Littãfi da hukunci da Annabci,
Kuma Mun azurta su daga abũbuwa mãsudãɗi, Kuma Mun fĩfta su a kan mutãnen dũniya
(a zãmaninsu).
|
Ayah 45:17 الأية
وَآتَيْنَاهُم بَيِّنَاتٍ مِّنَ الْأَمْرِ ۖ فَمَا اخْتَلَفُوا إِلَّا مِن بَعْدِ
مَا جَاءَهُمُ الْعِلْمُ بَغْيًا بَيْنَهُمْ ۚ إِنَّ رَبَّكَ يَقْضِي بَيْنَهُمْ
يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِيمَا كَانُوا فِيهِ يَخْتَلِفُونَ
Waataynahum bayyinatinmina al-amri fama ikhtalafoo illa min baAAdi majaahumu
alAAilmu baghyan baynahum inna rabbaka yaqdeebaynahum yawma alqiyamati feema
kanoo feehiyakhtalifoon
Hausa
Kuma Muka bã su hujjõji na umurni. Ba su sãɓa ba fãce bãyan ilmi ya jẽ musu,
sabõda zãlunci a tsakãninsu. Lalle ne, Ubangijinka zai yi hukunci a tsakãninsu,
a Rãnar ƙiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa (jũna).
|
Ayah 45:18 الأية
ثُمَّ جَعَلْنَاكَ عَلَىٰ شَرِيعَةٍ مِّنَ الْأَمْرِ فَاتَّبِعْهَا وَلَا تَتَّبِعْ
أَهْوَاءَ الَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ
Thumma jaAAalnaka AAalashareeAAatin mina al-amri fattabiAAha walatattabiAA ahwaa
allatheena la yaAAlamoon
Hausa
Sa'an nan Muka sanya ka a kan wata sharĩ'a ta al'amarin.Sai ka bĩ ta, Kuma kada
kã bi son zũciyõyin waɗannan daba su sani ba.
|
Ayah 45:19 الأية
إِنَّهُمْ لَن يُغْنُوا عَنكَ مِنَ اللهِ شَيْئًا ۚ وَإِنَّ الظَّالِمِينَ
بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ ۖ وَاللهُ وَلِيُّ الْمُتَّقِينَ
Innahum lan yughnoo AAanka mina Allahishay-an wa-inna aththalimeena
baAAduhumawliyao baAAdin wallahu waliyyualmuttaqeen
Hausa
Lalle ne sũ, bã zã su wadãtar da kai da kõme ba daga Allah. Kuma lalle ne
azzãlumai sãshensu majiɓintan sãshe ne. Kuma Allah ne Majiɓincin mãsu taƙawa.
|
Ayah 45:20 الأية
هَٰذَا بَصَائِرُ لِلنَّاسِ وَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِّقَوْمٍ يُوقِنُونَ
Hatha basa-iru linnasiwahudan warahmatun liqawmin yooqinoon
Hausa
wannan (Alkur'ãni) hukunce-hukuncen natsuwa ne ga mutãne, da shiryuwa, da
rahama, ga mutãne waɗanda ke da yaƙĩni.
|
Ayah 45:21 الأية
أَمْ حَسِبَ الَّذِينَ اجْتَرَحُوا السَّيِّئَاتِ أَن نَّجْعَلَهُمْ كَالَّذِينَ
آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ سَوَاءً مَّحْيَاهُمْ وَمَمَاتُهُمْ ۚ سَاءَ مَا
يَحْكُمُونَ
Am hasiba allatheena ijtarahooassayyi-ati an najAAalahum kallatheenaamanoo
waAAamiloo assalihati sawaanmahyahum wamamatuhum saa ma yahkumoon
Hausa
Kõ waɗanda suka yãgi miyãgun ayyuka sunã zaton Mu sanyã su kamar waɗanda suka yi
ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, su zama daidai ga rãyuwarsu da
mutuwarsu? Abin da suke hukuntãwa yã mũnanã!
|
Ayah 45:22 الأية
وَخَلَقَ اللهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِالْحَقِّ وَلِتُجْزَىٰ كُلُّ نَفْسٍ
بِمَا كَسَبَتْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ
Wakhalaqa Allahu assamawatiwal-arda bilhaqqi walitujzakullu nafsin bima kasabat
wahum la yuthlamoon
Hausa
Alhãli kuwa Allah ne Ya halitta sammai da ƙasã sabõda gaskiya, Kuma dõmin a sãka
wa kõwane rai da abin da ya sanã'anta, kuma su, bã zã a zãlunce su ba.
|
Ayah 45:23 الأية
أَفَرَأَيْتَ مَنِ اتَّخَذَ إِلَٰهَهُ هَوَاهُ وَأَضَلَّهُ اللهُ عَلَىٰ عِلْمٍ
وَخَتَمَ عَلَىٰ سَمْعِهِ وَقَلْبِهِ وَجَعَلَ عَلَىٰ بَصَرِهِ غِشَاوَةً فَمَن
يَهْدِيهِ مِن بَعْدِ اللهِ ۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Afaraayta mani ittakhatha ilahahuhawahu waadallahu Allahu AAalaAAilmin wakhatama
AAala samAAihi waqalbihi wajaAAala AAalabasarihi ghishawatan faman yahdeehi min
baAAdi Allahiafala tathakkaroon
Hausa
Shin, kã ga wanda ya riƙi son zũciyarsa sĩh ne abin bautawarsa, kuma Allah Ya
ɓatar da shi a kan wani ilmi, Kuma Ya sa hatini a kan jinsa, da zũciyarsa, kuma
Ya sa wata yãnã ã kan ganinsa? To, wãne ne zai shiryar da shi bãyan Allah? Shin
to, bã zã ku yi tunãni ba?
|
Ayah 45:24 الأية
وَقَالُوا مَا هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا الدُّنْيَا نَمُوتُ وَنَحْيَا وَمَا
يُهْلِكُنَا إِلَّا الدَّهْرُ ۚ وَمَا لَهُم بِذَٰلِكَ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِنْ هُمْ
إِلَّا يَظُنُّونَ
Waqaloo ma hiya illa hayatunaaddunya namootu wanahya wamayuhlikuna illa addahru
wama lahum bithalikamin AAilmin in hum illa yathunnoon
Hausa
Kuma suka ce: "Bãbu kõme fãce rãyuwarmu ta dũniya; munã mutuwa kuma munã rãyuwa
(da haihuwa) kuma bãbu abin da ke halaka mu sai zãmani." Alhãli kuwa (ko da suke
faɗar maganar) bã su da wani ilmi game da wannan, bã su bin kõme face zato.
|
Ayah 45:25 الأية
وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا بَيِّنَاتٍ مَّا كَانَ حُجَّتَهُمْ إِلَّا
أَن قَالُوا ائْتُوا بِآبَائِنَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Wa-itha tutla AAalayhim ayatunabayyinatin ma kana hujjatahum illaan qaloo i/too
bi-aba-ina in kuntum sadiqeen
Hausa
Kuma idan anã karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu, bãbu abin da ya kasance
hujjarsu fãce suka ce: "Ku zo mana da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."
|
Ayah 45:26 الأية
قُلِ اللهُ يُحْيِيكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يَجْمَعُكُمْ إِلَىٰ يَوْمِ
الْقِيَامَةِ لَا رَيْبَ فِيهِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
Quli Allahu yuhyeekum thummayumeetukum thumma yajmaAAukum ila yawmi alqiyamatila
rayba feehi walakinna akthara annasila yaAAlamoon
Hausa
Ka ce: "Allah ne ke rãyar da ku kuma Shĩ ne ke matarda ku, sa'an nan Ya tãra ku
zuwa ga Rãnar ¡iyãma, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne ba su
sani ba."
|
Ayah 45:27 الأية
وَلِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَيَوْمَ تَقُومُ السَّاعَةُ
يَوْمَئِذٍ يَخْسَرُ الْمُبْطِلُونَ
Walillahi mulku assamawatiwal-ardi wayawma taqoomu assaAAatuyawma-ithin yakhsaru
almubtiloon
Hausa
"Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne, Shĩ kaɗai. Kuma rãnar da Sa'a ke
tsayuwa, a rãnar nan mãsu ɓãtãwã (ga hujjõjin Allah dõmin su ki bin sharĩ'arSa)
zã su yi hasãra."
|
Ayah 45:28 الأية
وَتَرَىٰ كُلَّ أُمَّةٍ جَاثِيَةً ۚ كُلُّ أُمَّةٍ تُدْعَىٰ إِلَىٰ كِتَابِهَا
الْيَوْمَ تُجْزَوْنَ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Watara kulla ommatin jathiyatankullu ommatin tudAAa ila kitabihaalyawma tujzawna
ma kuntum taAAmaloon
Hausa
Kuma zã ka ga kõwace al'umma tanã gurfãne, kõwace al'umma anã kiran ta zuwa ga
littãfinta. ( A ce musu) "A yau anã sãka muku da abin da kuka kasance kunã
aikatãwa."
|
Ayah 45:29 الأية
هَٰذَا كِتَابُنَا يَنطِقُ عَلَيْكُم بِالْحَقِّ ۚ إِنَّا كُنَّا نَسْتَنسِخُ مَا
كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Hatha kitabuna yantiquAAalaykum bilhaqqi inna kunnanastansikhu ma kuntum
taAAmaloon
Hausa
"Wannan littãfinMu ne yanã yin magana a kanku da gas, kiya. Lalle Mũ, Mun
kasanceMuna sauya rubũtun tamkar abin dakuka kasance kunã aikãtãwa."
|
Ayah 45:30 الأية
فَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَيُدْخِلُهُمْ رَبُّهُمْ فِي
رَحْمَتِهِ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْمُبِينُ
Faamma allatheena amanoowaAAamiloo assalihati fayudkhiluhumrabbuhum fee
rahmatihi thalika huwa alfawzualmubeen
Hausa
To, amma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, to, Ubangijinsu
zai sanya su a cikin rahamarsa. Wannan shĩ ne babban rabo bayyananne.
|
Ayah 45:31 الأية
وَأَمَّا الَّذِينَ كَفَرُوا أَفَلَمْ تَكُنْ آيَاتِي تُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ
فَاسْتَكْبَرْتُمْ وَكُنتُمْ قَوْمًا مُّجْرِمِينَ
Waamma allatheena kafarooafalam takun ayatee tutla AAalaykum
fastakbartumwakuntum qawman mujrimeen
Hausa
Kuma amma waɗanda suka kãfirtã (Allah zai ce musu): "Shin, ãyõyĩNã ba su kasance
anã karãnta su ã kanku ba sai kuka kangare, Kuma kuka kasance mutãne mãsu
laifi?"
|
Ayah 45:32 الأية
وَإِذَا قِيلَ إِنَّ وَعْدَ اللهِ حَقٌّ وَالسَّاعَةُ لَا رَيْبَ فِيهَا قُلْتُم
مَّا نَدْرِي مَا السَّاعَةُ إِن نَّظُنُّ إِلَّا ظَنًّا وَمَا نَحْنُ
بِمُسْتَيْقِنِينَ
Wa-itha qeela inna waAAda Allahihaqqun wassaAAatu la rayba feehaqultum ma nadree
ma assaAAatu in nathunnuilla thannan wama nahnubimustayqineen
Hausa
"Kuma idan aka ce, lalle wa'ãdin Allah gaskiya ne, kuma Sa'a, bãbu shakka a
cikinta sai kuka ce, 'Ba mu san abin da ake cẽwa Sa'a ba, bã mu zãto (game da
ita) fãce zato mai rauni, Kuma ba mu zama mãsu yaƙni ba."'
|
Ayah 45:33 الأية
وَبَدَا لَهُمْ سَيِّئَاتُ مَا عَمِلُوا وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا بِهِ
يَسْتَهْزِئُونَ
Wabada lahum sayyi-atu maAAamiloo wahaqa bihim ma kanoo bihiyastahzi-oon
Hausa
Kuma mũnanan abin da suka aikata ya bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance
sunã yi na izgili ya wajaba a kansu.
|
Ayah 45:34 الأية
وَقِيلَ الْيَوْمَ نَنسَاكُمْ كَمَا نَسِيتُمْ لِقَاءَ يَوْمِكُمْ هَٰذَا
وَمَأْوَاكُمُ النَّارُ وَمَا لَكُم مِّن نَّاصِرِينَ
Waqeela alyawma nansakum kamanaseetum liqaa yawmikum hatha wama/wakumu
annaruwama lakum min nasireen
Hausa
Kuma aka ce: "A yau zã Mu manta da ku, kamar yadda kuka manta da gamuwa da
yininku wannan. Kuma mãkõmarku wutã ce, Kuma bã ku da waɗansu mãsu taimako.
|
Ayah 45:35 الأية
ذَٰلِكُم بِأَنَّكُمُ اتَّخَذْتُمْ آيَاتِ اللهِ هُزُوًا وَغَرَّتْكُمُ
الْحَيَاةُ الدُّنْيَا ۚ فَالْيَوْمَ لَا يُخْرَجُونَ مِنْهَا وَلَا هُمْ
يُسْتَعْتَبُونَ
Thalikum bi-annakumu ittakhathtumayati Allahi huzuwan wagharratkumu
alhayatuaddunya falyawma la yukhrajoonaminha wala hum yustaAAtaboon
Hausa
"Wancan dõmin lalle kũ, kun riƙi ãyõyin Allah da izgili, Kuma rãyuwar dũniya ta
rũɗe ku. To, a yau bã zã su fita daga gare ta ba, Kuma bã zã su zama waɗanda ake
nẽman yardarsu ba."
|
Ayah 45:36 الأية
فَلِلَّهِ الْحَمْدُ رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَرَبِّ الْأَرْضِ رَبِّ الْعَالَمِينَ
Falillahi alhamdu rabbi assamawatiwarabbi al-ardi rabbi alAAalameen
Hausa
Sabõda haka, gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin sammai, kuma Ubangijin ƙasã,
Ubangijin halittu.
|
Ayah 45:37 الأية
وَلَهُ الْكِبْرِيَاءُ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ وَهُوَ الْعَزِيزُ
الْحَكِيمُ
Walahu alkibriyao fee assamawatiwal-ardi wahuwa alAAazeezu alhakeem
Hausa
Kuma gare Shi girma yake, a cikin sammai da ƙasã, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai
Hikima.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|