1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
وَالنَّجْمِ إِذَا هَوَىٰ
Wannajmi itha hawa
Hausa
Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.
|
Ayah 53:2 الأية
مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمْ وَمَا غَوَىٰ
Ma dalla sahibukum wamaghawa
Hausa
Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.
|
Ayah 53:3 الأية
وَمَا يَنطِقُ عَنِ الْهَوَىٰ
Wama yantiqu AAani alhawa
Hausa
Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.
|
Ayah 53:4 الأية
إِنْ هُوَ إِلَّا وَحْيٌ يُوحَىٰ
In huwa illa wahyun yooha
Hausa
(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.
|
Ayah 53:5 الأية
عَلَّمَهُ شَدِيدُ الْقُوَىٰ
AAallamahu shadeedu alquwa
Hausa
(Malã'ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi.
|
Ayah 53:6 الأية
ذُو مِرَّةٍ فَاسْتَوَىٰ
Thoo mirratin fastawa
Hausa
Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.
|
Ayah 53:7 الأية
وَهُوَ بِالْأُفُقِ الْأَعْلَىٰ
Wahuwa bil-ofuqi al-aAAla
Hausa
Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi aukaka.
|
Ayah 53:8 الأية
ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّىٰ
Thumma dana fatadalla
Hausa
Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.
|
Ayah 53:9 الأية
فَكَانَ قَابَ قَوْسَيْنِ أَوْ أَدْنَىٰ
Fakana qaba qawsayni aw adna
Hausa
Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.
|
Ayah 53:10 الأية
فَأَوْحَىٰ إِلَىٰ عَبْدِهِ مَا أَوْحَىٰ
Faawha ila AAabdihi maawha
Hausa
Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa
).
|
Ayah 53:11 الأية
مَا كَذَبَ الْفُؤَادُ مَا رَأَىٰ
Ma kathaba alfu-adu maraa
Hausa
Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.
|
Ayah 53:12 الأية
أَفَتُمَارُونَهُ عَلَىٰ مَا يَرَىٰ
Afatumaroonahu AAala mayara
Hausa
Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?
|
Ayah 53:13 الأية
وَلَقَدْ رَآهُ نَزْلَةً أُخْرَىٰ
Walaqad raahu nazlatan okhra
Hausa
Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa .
|
Ayah 53:14 الأية
عِندَ سِدْرَةِ الْمُنتَهَىٰ
AAinda sidrati almuntaha
Hausa
A wurin da magaryar tuƙẽwa take.
|
Ayah 53:15 الأية
عِندَهَا جَنَّةُ الْمَأْوَىٰ
AAindaha jannatu alma/wa
Hausa
A inda taken, nan Aljannar makoma take.
|
Ayah 53:16 الأية
إِذْ يَغْشَى السِّدْرَةَ مَا يَغْشَىٰ
Ith yaghsha assidratama yaghsha
Hausa
Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.
|
Ayah 53:17 الأية
مَا زَاغَ الْبَصَرُ وَمَا طَغَىٰ
Ma zagha albasaru wamatagha
Hausa
Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.
|
Ayah 53:18 الأية
لَقَدْ رَأَىٰ مِنْ آيَاتِ رَبِّهِ الْكُبْرَىٰ
Laqad raa min ayatirabbihi alkubra
Hausa
Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma daga ãyõyin Ubangijinsa.
|
Ayah 53:19 الأية
أَفَرَأَيْتُمُ اللَّاتَ وَالْعُزَّىٰ
Afaraaytumu allata walAAuzza
Hausa
Shin, kun ga Lãta da uzza?
|
Ayah 53:20 الأية
وَمَنَاةَ الثَّالِثَةَ الْأُخْرَىٰ
Wamanata aththalithataal-okhra
Hausa
Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu?
|
Ayah 53:21 الأية
أَلَكُمُ الذَّكَرُ وَلَهُ الْأُنثَىٰ
Alakumu aththakaru walahual-ontha
Hausa
Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?
|
Ayah 53:22 الأية
تِلْكَ إِذًا قِسْمَةٌ ضِيزَىٰ
Tilka ithan qismatun deeza
Hausa
Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe.
|
Ayah 53:23 الأية
إِنْ هِيَ إِلَّا أَسْمَاءٌ سَمَّيْتُمُوهَا أَنتُمْ وَآبَاؤُكُم مَّا أَنزَلَ
اللهُ بِهَا مِن سُلْطَانٍ ۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا الظَّنَّ وَمَا تَهْوَى
الْأَنفُسُ ۖ وَلَقَدْ جَاءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ الْهُدَىٰ
In hiya illa asmaonsammaytumooha antum waabaokum maanzala Allahu biha min
sultanin inyattabiAAoona illa aththanna wamatahwa al-anfusu walaqad jaahum min
rabbihimu alhuda
Hausa
Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da
uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar
kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar ta daga wajen
Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton).
|
Ayah 53:24 الأية
أَمْ لِلْإِنسَانِ مَا تَمَنَّىٰ
Am lil-insani ma tamanna
Hausa
Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri?
|
Ayah 53:25 الأية
فَلِلَّهِ الْآخِرَةُ وَالْأُولَىٰ
Falillahi al-akhiratu wal-oola
Hausa
To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi
kuskure).
|
Ayah 53:26 الأية
وَكَم مِّن مَّلَكٍ فِي السَّمَاوَاتِ لَا تُغْنِي شَفَاعَتُهُمْ شَيْئًا إِلَّا
مِن بَعْدِ أَن يَأْذَنَ اللهُ لِمَن يَشَاءُ وَيَرْضَىٰ
Wakam min malakin fee assamawatila tughnee shafaAAatuhum shay-an illa minbaAAdi
an ya/thana Allahu liman yashao wayarda
Hausa
Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan
Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.
|
Ayah 53:27 الأية
إِنَّ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ لَيُسَمُّونَ الْمَلَائِكَةَ
تَسْمِيَةَ الْأُنثَىٰ
Inna allatheena la yu/minoonabil-akhirati layusammoona almala-ikatatasmiyata
al-ontha
Hausa
Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan
mace.
|
Ayah 53:28 الأية
وَمَا لَهُم بِهِ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا الظَّنَّ ۖ وَإِنَّ
الظَّنَّ لَا يُغْنِي مِنَ الْحَقِّ شَيْئًا
Wama lahum bihi min AAilmin inyattabiAAoona illa aththanna wa-innaaththanna la
yughnee mina alhaqqishay-a
Hausa
Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle
zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya.
|
Ayah 53:29 الأية
فَأَعْرِضْ عَن مَّن تَوَلَّىٰ عَن ذِكْرِنَا وَلَمْ يُرِدْ إِلَّا الْحَيَاةَ
الدُّنْيَا
FaaAArid AAan man tawalla AAanthikrina walam yurid illa alhayataaddunya
Hausa
Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambatonMu kuma bai yi
nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya).
|
Ayah 53:30 الأية
ذَٰلِكَ مَبْلَغُهُم مِّنَ الْعِلْمِ ۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ
عَن سَبِيلِهِ وَهُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ اهْتَدَىٰ
Thalika mablaghuhum mina alAAilmiinna rabbaka huwa aAAlamu biman dalla AAan
sabeelihiwahuwa aAAlamu bimani ihtada
Hausa
Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka
Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya
nẽmi shiriya.
|
Ayah 53:31 الأية
وَلِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ لِيَجْزِيَ الَّذِينَ
أَسَاءُوا بِمَا عَمِلُوا وَيَجْزِيَ الَّذِينَ أَحْسَنُوا بِالْحُسْنَى
Walillahi ma fee assamawatiwama fee al-ardi liyajziya allatheena asaoobima
AAamiloo wayajziya allatheena ahsanoobilhusna
Hausa
Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne,
dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa
waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau.
|
Ayah 53:32 الأية
الَّذِينَ يَجْتَنِبُونَ كَبَائِرَ الْإِثْمِ وَالْفَوَاحِشَ إِلَّا اللَّمَمَ ۚ
إِنَّ رَبَّكَ وَاسِعُ الْمَغْفِرَةِ ۚ هُوَ أَعْلَمُ بِكُمْ إِذْ أَنشَأَكُم مِّنَ
الْأَرْضِ وَإِذْ أَنتُمْ أَجِنَّةٌ فِي بُطُونِ أُمَّهَاتِكُمْ ۖ فَلَا تُزَكُّوا
أَنفُسَكُمْ ۖ هُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ اتَّقَىٰ
Allatheena yajtaniboona kaba-iraal-ithmi walfawahisha illa allamama innarabbaka
wasiAAu almaghfirati huwa aAAlamu bikum ithanshaakum mina al-ardi wa-ith antum
ajinnatun feebutooni ommahatikum fala tuzakkoo anfusakumhuwa aAAlamu bimani
ittaqa
Hausa
Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka,
lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare
ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a
cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake kanku, Shĩ ne Mafi sani
ga wanda ya yi taƙawa.
|
Ayah 53:33 الأية
أَفَرَأَيْتَ الَّذِي تَوَلَّىٰ
Afaraayta allathee tawalla
Hausa
Shin, ka ga wannan da ya jũya baya?
|
Ayah 53:34 الأية
وَأَعْطَىٰ قَلِيلًا وَأَكْدَىٰ
WaaAAta qaleelan waakda
Hausa
Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa?
|
Ayah 53:35 الأية
أَعِندَهُ عِلْمُ الْغَيْبِ فَهُوَ يَرَىٰ
aAAindahu AAilmu alghaybi fahuwa yara
Hausa
Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin?
|
Ayah 53:36 الأية
أَمْ لَمْ يُنَبَّأْ بِمَا فِي صُحُفِ مُوسَىٰ
Am lam yunabba/ bima fee suhufimoosa
Hausa
Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã?
|
Ayah 53:37 الأية
وَإِبْرَاهِيمَ الَّذِي وَفَّىٰ
Wa-ibraheema allathee waffa
Hausa
Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari?
|
Ayah 53:38 الأية
أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَىٰ
Alla taziru waziratun wizraokhra
Hausa
Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani.
|
Ayah 53:39 الأية
وَأَن لَّيْسَ لِلْإِنسَانِ إِلَّا مَا سَعَىٰ
Waan laysa lil-insani illa masaAAa
Hausa
Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata.
|
Ayah 53:40 الأية
وَأَنَّ سَعْيَهُ سَوْفَ يُرَىٰ
Waanna saAAyahu sawfa yura
Hausa
Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi.
|
Ayah 53:41 الأية
ثُمَّ يُجْزَاهُ الْجَزَاءَ الْأَوْفَىٰ
Thumma yujzahu aljazaa al-awfa
Hausa
Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?
|
Ayah 53:42 الأية
وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ الْمُنتَهَىٰ
Waanna ila rabbika almuntaha
Hausa
Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take?
|
Ayah 53:43 الأية
وَأَنَّهُ هُوَ أَضْحَكَ وَأَبْكَىٰ
Waannahu huwa adhaka waabka
Hausa
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka.
|
Ayah 53:44 الأية
وَأَنَّهُ هُوَ أَمَاتَ وَأَحْيَا
Waannahu huwa amata waahya
Hausa
Kuma lalle, Shĩ , Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar.
|
Ayah 53:45 الأية
وَأَنَّهُ خَلَقَ الزَّوْجَيْنِ الذَّكَرَ وَالْأُنثَىٰ
Waannahu khalaqa azzawjayni aththakarawal-ontha
Hausa
Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.
|
Ayah 53:46 الأية
مِن نُّطْفَةٍ إِذَا تُمْنَىٰ
Min nutfatin itha tumna
Hausa
Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.
|
Ayah 53:47 الأية
وَأَنَّ عَلَيْهِ النَّشْأَةَ الْأُخْرَىٰ
Waanna AAalayhi annash-ata al-okhra
Hausa
Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.
|
Ayah 53:48 الأية
وَأَنَّهُ هُوَ أَغْنَىٰ وَأَقْنَىٰ
Waannahu huwa aghna waaqna
Hausa
Kuma lalle, Shĩ , Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.
|
Ayah 53:49 الأية
وَأَنَّهُ هُوَ رَبُّ الشِّعْرَىٰ
Waannahu huwa rabbu ashshiAAra
Hausa
Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira .
|
Ayah 53:50 الأية
وَأَنَّهُ أَهْلَكَ عَادًا الْأُولَىٰ
Waannahu ahlaka AAadan al-oola
Hausa
Kuma lalle, Shĩ , Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko.
|
Ayah 53:51 الأية
وَثَمُودَ فَمَا أَبْقَىٰ
Wathamooda fama abqa
Hausa
Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.
|
Ayah 53:52 الأية
وَقَوْمَ نُوحٍ مِّن قَبْلُ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا هُمْ أَظْلَمَ وَأَطْغَىٰ
Waqawma noohin min qablu innahum kanoohum athlama waatgha
Hausa
Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi
girman kai.
|
Ayah 53:53 الأية
وَالْمُؤْتَفِكَةَ أَهْوَىٰ
Walmu/tafikata ahwa
Hausa
Da waɗanda aka birkice ƙasarsu, Ya kãyar da su.
|
Ayah 53:54 الأية
فَغَشَّاهَا مَا غَشَّىٰ
Faghashshaha ma ghashsha
Hausa
Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.
|
Ayah 53:55 الأية
فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰ
Fabi-ayyi ala-i rabbika tatamara
Hausa
To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake yin shakka?
|
Ayah 53:56 الأية
هَٰذَا نَذِيرٌ مِّنَ النُّذُرِ الْأُولَىٰ
Hatha natheerun mina annuthurial-oola
Hausa
wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.
|
Ayah 53:57 الأية
أَزِفَتِ الْآزِفَةُ
Azifati al-azifat
Hausa
Makusanciya fa, tã yi kusa.
|
Ayah 53:58 الأية
لَيْسَ لَهَا مِن دُونِ اللهِ كَاشِفَةٌ
Laysa laha min dooni Allahi kashifat
Hausa
Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.
|
Ayah 53:59 الأية
أَفَمِنْ هَٰذَا الْحَدِيثِ تَعْجَبُونَ
Afamin hatha alhadeethitaAAjaboon
Hausa
Shin, kuma daga wannan lãbãri kuke mãmãki?
|
Ayah 53:60 الأية
وَتَضْحَكُونَ وَلَا تَبْكُونَ
Watadhakoona wala tabkoon
Hausa
Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?
|
Ayah 53:61 الأية
وَأَنتُمْ سَامِدُونَ
Waantum samidoon
Hausa
Alhãli kunã mãsu wãsã?
|
Ayah 53:62 الأية
فَاسْجُدُوا لِلَّهِ وَاعْبُدُوا ۩
Fasjudoo lillahi waAAbudoo
Hausa
To, ku yi tawãli'u ga Allah, kuma ku bauta (masa).
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|