1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Sabbaha lillahi ma fee assamawatiwal-ardi wahuwa alAAazeezu alhakeem
Hausa
Abin da ke cikin sammai da ƙasa yă yi tasbĩhi ga Allah. Kuma Shĩ ne Mabuwăyi,
Mai hikima.
|
Ayah 57:2 الأية
لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ
شَيْءٍ قَدِيرٌ
Lahu mulku assamawatiwal-ardi yuhyee wayumeetu wahuwa AAalakulli shay-in qadeer
Hausa
Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa: Yană răyarwa kuma Yană kashẽwa, kuma Shĩ Mai
ikon yi ne a kan kőme.
|
Ayah 57:3 الأية
هُوَ الْأَوَّلُ وَالْآخِرُ وَالظَّاهِرُ وَالْبَاطِنُ ۖ وَهُوَ بِكُلِّ شَيْءٍ
عَلِيمٌ
Huwa al-awwalu wal-akhiru waththahiruwalbatinu wahuwa bikulli shay-in AAaleem
Hausa
Shĩ ne Na farko, Na ƙarshe, Bayyananne, Bőyayye, kuma Shĩ Masani ne ga dukkan
kőme.
|
Ayah 57:4 الأية
هُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ
اسْتَوَىٰ عَلَى الْعَرْشِ ۚ يَعْلَمُ مَا يَلِجُ فِي الْأَرْضِ وَمَا يَخْرُجُ
مِنْهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وَمَا يَعْرُجُ فِيهَا ۖ وَهُوَ مَعَكُمْ
أَيْنَ مَا كُنتُمْ ۚ وَاللهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ
Huwa allathee khalaqa assamawatiwal-arda fee sittati ayyamin thumma istawaAAala
alAAarshi yaAAlamu ma yaliju fee al-ardiwama yakhruju minha wama yanzilu mina
assama-iwama yaAAruju feeha wahuwa maAAakum ayna makuntum wallahu bima
taAAmaloona baseer
Hausa
Shĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin wasu kwănuka shida, sa'an nan Ya
daidaitu a kan Al'arshi, Yană sanin abin da ke shiga cikin ƙasa da abin da ke
fita daga gare ta, da abin da ke sauka daga sama da abin da ke hawa cikinta,
kuma Shĩ yană tareda ku duk inda kuka kasance. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da
kuke aikatăwa.
|
Ayah 57:5 الأية
لَّهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَإِلَى اللهِ تُرْجَعُ الْأُمُورُ
Lahu mulku assamawatiwal-ardi wa-ila Allahi turjaAAual-omoor
Hausa
Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma zuwa gare Shĩ (Allah) kawai ake mayar da
al'amura.
|
Ayah 57:6 الأية
يُولِجُ اللَّيْلَ فِي النَّهَارِ وَيُولِجُ النَّهَارَ فِي اللَّيْلِ ۚ وَهُوَ
عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ
Yooliju allayla fee annahariwayooliju annahara fee allayi wahuwa AAaleemun
bithatiassudoor
Hausa
Yană shigar da dare a cikin yini, kuma Yană shigar da yini a cikin dare, kuma
Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirăza.
|
Ayah 57:7 الأية
آمِنُوا بِاللهِ وَرَسُولِهِ وَأَنفِقُوا مِمَّا جَعَلَكُم مُّسْتَخْلَفِينَ
فِيهِ ۖ فَالَّذِينَ آمَنُوا مِنكُمْ وَأَنفَقُوا لَهُمْ أَجْرٌ كَبِيرٌ
Aminoo billahiwarasoolihi waanfiqoo mimma jaAAalakum mustakhlafeenafeehi
fallatheena amanoo minkum waanfaqoolahum ajrun kabeer
Hausa
Ku yi ĩmăni da Allah da ManzonSa, kuma ku ciyar daga abin da Allah Ya wakilta ku
a cikinsa (na dũkiya). To, waɗannan da suka yi ĩmăni daga cikinku, kuma suka
ciyar, sună da wani sakamako mai girma.
|
Ayah 57:8 الأية
وَمَا لَكُمْ لَا تُؤْمِنُونَ بِاللهِ ۙ وَالرَّسُولُ يَدْعُوكُمْ لِتُؤْمِنُوا
بِرَبِّكُمْ وَقَدْ أَخَذَ مِيثَاقَكُمْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
Wama lakum la tu/minoona billahiwarrasoolu yadAAookum litu/minoo birabbikum
waqad akhathameethaqakum in kuntum mu/mineen
Hausa
kuma me ya same ku, bă ză ku yi ĩmăni ba da Allah, alhăli kuwa manzonSa na kiran
ku dőmin ku yi ĩmăni da Ubangijinku, kuma lalle Allah Ya karɓi alkawarinku (cẽwa
ză ku bauta Masa)? (Ku bauta Masa) idan kun kasance măsu ĩmăni.
|
Ayah 57:9 الأية
هُوَ الَّذِي يُنَزِّلُ عَلَىٰ عَبْدِهِ آيَاتٍ بَيِّنَاتٍ لِّيُخْرِجَكُم مِّنَ
الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ ۚ وَإِنَّ اللهَ بِكُمْ لَرَءُوفٌ رَّحِيمٌ
Huwa allathee yunazzilu AAalaAAabdihi ayatin bayyinatin liyukhrijakummina
aththulumati ila annooriwa-inna Allaha bikum laraoofun raheem
Hausa
Shĩ ne wanda ke sassaukar da ăyőyi bayyanannu ga BăwanSa, dőmin Ya fitar da ku
daga duffai zuwa ga haske, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai tausayi ne gare ku, Mai
jin ƙai.
|
Ayah 57:10 الأية
وَمَا لَكُمْ أَلَّا تُنفِقُوا فِي سَبِيلِ اللهِ وَلِلَّهِ مِيرَاثُ
السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ لَا يَسْتَوِي مِنكُم مَّنْ أَنفَقَ مِن قَبْلِ
الْفَتْحِ وَقَاتَلَ ۚ أُولَٰئِكَ أَعْظَمُ دَرَجَةً مِّنَ الَّذِينَ أَنفَقُوا مِن
بَعْدُ وَقَاتَلُوا ۚ وَكُلًّا وَعَدَ اللهُ الْحُسْنَىٰ ۚ وَاللهُ بِمَا
تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ
Wama lakum alla tunfiqoo feesabeeli Allahi walillahi meerathu assamawatiwal-ardi
la yastawee minkum man anfaqa minqabli alfathi waqatala ola-ika
aAAthamudarajatan mina allatheena anfaqoo min baAAdu waqataloowakullan waAAada
Allahu alhusna wallahubima taAAmaloona khabeer
Hausa
Kuma me ya săme ku, bă ză ku ciyar ba dőmin ɗaukaka kalmar Allah, alhăli kuwa
gădon sammai da ƙasă na Allah ne? Wanda ya ciyar a gabănin cin nasara, kuma ya
yi yăƙi daga cikinku, bă ya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). waɗancan ne
mafĩfĩta girman daraja bisa ga waɗanda suka ciyar daga băya kuma suka yi yăƙi.
Kuma dukansu Allah Ya yi musu wa'adi da (sakamako) mai kyau, kuma Allah Masani
ne ga abin da kuke aikatăwa.
|
Ayah 57:11 الأية
مَّن ذَا الَّذِي يُقْرِضُ اللهَ قَرْضًا حَسَنًا فَيُضَاعِفَهُ لَهُ وَلَهُ
أَجْرٌ كَرِيمٌ
Man tha allathee yuqriduAllaha qardan hasanan fayudaAAifahulahu walahu ajrun
kareem
Hausa
Wăne ne wanda zai ranta wa Allah rance mai kyau dőmin Allah Ya ninka masa shi (a
dũniya)kuma Yană da wani sakamako na karimci (a Lăhira)?
|
Ayah 57:12 الأية
يَوْمَ تَرَى الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ يَسْعَىٰ نُورُهُم بَيْنَ
أَيْدِيهِمْ وَبِأَيْمَانِهِم بُشْرَاكُمُ الْيَوْمَ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِن
تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
Yawma tara almu/mineena walmu/minatiyasAAa nooruhum bayna aydeehim
wabi-aymanihim bushrakumualyawma jannatun tajree min tahtiha al-anharukhalideena
feeha thalika huwa alfawzu alAAatheem
Hausa
Rănar da ză ka ga mũminai maza da mũminai mătă haskensu nă tafiya a gaba gare
su, da kuma dăma gare su. (Ană ce musu) "Bushărarku a yau, ita ce gidajen
Aljanna." Ruwa na gudăna daga ƙarƙashinsu sună măsu dawwama a cikinsu. Wannan,
shĩ ne babban rabo mai girma.
|
Ayah 57:13 الأية
يَوْمَ يَقُولُ الْمُنَافِقُونَ وَالْمُنَافِقَاتُ لِلَّذِينَ آمَنُوا انظُرُونَا
نَقْتَبِسْ مِن نُّورِكُمْ قِيلَ ارْجِعُوا وَرَاءَكُمْ فَالْتَمِسُوا نُورًا
فَضُرِبَ بَيْنَهُم بِسُورٍ لَّهُ بَابٌ بَاطِنُهُ فِيهِ الرَّحْمَةُ وَظَاهِرُهُ
مِن قِبَلِهِ الْعَذَابُ
Yawma yaqoolu almunafiqoona walmunafiqatulillatheena amanoo onthuroonanaqtabis
min noorikum qeela irjiAAoo waraakum faltamisoonooran faduriba baynahum bisoorin
lahu babun batinuhufeehi arrahmatu wathahiruhumin qibalihi alAAathab
Hausa
Rănar da munafikai maza da munăfikai mătă ke cẽwa waɗanda suka yi ĩmăni: "Ku
dũbẽ mu, mu yi makămashi daga haskenku!" A ce (musu): "Ku kőma a băyanku, dőmin
ku nẽmo wani haske." Sai a danne a tsakăninsu da wani găru yană da wani ƙyaure,
a cikinsa nan rahama take, kuma a băyansa daga wajensa azaba take.
|
Ayah 57:14 الأية
يُنَادُونَهُمْ أَلَمْ نَكُن مَّعَكُمْ ۖ قَالُوا بَلَىٰ وَلَٰكِنَّكُمْ فَتَنتُمْ
أَنفُسَكُمْ وَتَرَبَّصْتُمْ وَارْتَبْتُمْ وَغَرَّتْكُمُ الْأَمَانِيُّ حَتَّىٰ
جَاءَ أَمْرُ اللهِ وَغَرَّكُم بِاللهِ الْغَرُورُ
Yunadoonahum alam nakun maAAakum qaloobala walakinnakum fatantum anfusakum
watarabbastumwartabtum wagharratkumu al-amaniyyu hattajaa amru Allahi
wagharrakum billahialgharoor
Hausa
Sună kiran su, "Ashe, bă tăre muke da ku ba?" Su ce: "Ĩ, amma kũ, kun fitini
kanku, kuma kun yi jiran wata masĩfa, kuma kunyi shakka, kuma waɗansu
gũrace-gũrace sun rũɗe ku, har umurnin Allah ya jẽ muku, kumamarũɗi ya rũɗe ku
game da Allah."
|
Ayah 57:15 الأية
فَالْيَوْمَ لَا يُؤْخَذُ مِنكُمْ فِدْيَةٌ وَلَا مِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ
مَأْوَاكُمُ النَّارُ ۖ هِيَ مَوْلَاكُمْ ۖ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ
Falyawma la yu/khathuminkum fidyatun wala mina allatheena kafaroo
ma/wakumuannaru hiya mawlakum wabi/sa almaseer
Hausa
"To, a yau bă ză a karɓi fansa daga gare ku ba. Kuma bă ză a karɓa daga waɗanda
suka kăfirta ba. Makőmarku wută ce, ita ce mai dacẽwa da ku, kuma makőmarku ɗin
nan tă mũnana."
|
Ayah 57:16 الأية
أَلَمْ يَأْنِ لِلَّذِينَ آمَنُوا أَن تَخْشَعَ قُلُوبُهُمْ لِذِكْرِ اللهِ وَمَا
نَزَلَ مِنَ الْحَقِّ وَلَا يَكُونُوا كَالَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِن قَبْلُ
فَطَالَ عَلَيْهِمُ الْأَمَدُ فَقَسَتْ قُلُوبُهُمْ ۖ وَكَثِيرٌ مِّنْهُمْ
فَاسِقُونَ
Alam ya/ni lillatheena amanooan takhshaAAa quloobuhum lithikri Allahi wamanazala
mina alhaqqi wala yakoonoo kallatheenaootoo alkitaba min qablu fatala AAalayhimu
al-amadufaqasat quloobuhum wakatheerun minhum fasiqoon
Hausa
Shin, lőkaci bai yi ba ga wa ɗanda suka yi ĩmănĩ zukătansu su yi tawălu'i ga
ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya? Kada su kasance kamar waɗanda
aka bai wa littăfi a gabănin haka, sai zămani ya yi tsawo a kansu, sabőda haka
zukătansu suka ƙẽƙashe, kuma masu yawa daga cikinsu făsiƙai ne.
|
Ayah 57:17 الأية
اعْلَمُوا أَنَّ اللهَ يُحْيِي الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا ۚ قَدْ بَيَّنَّا
لَكُمُ الْآيَاتِ لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ
IAAlamoo anna Allaha yuhyeeal-arda baAAda mawtiha qad bayyanna lakumual-ayati
laAAallakum taAAqiloon
Hausa
Ku sani cẽwa Allah Yană răyar da ƙasă a băyan mutuwarta. Lalle Mun bayyanamuku
ăyőyi da fatan ză ku yi hankali.
|
Ayah 57:18 الأية
إِنَّ الْمُصَّدِّقِينَ وَالْمُصَّدِّقَاتِ وَأَقْرَضُوا اللهَ قَرْضًا حَسَنًا
يُضَاعَفُ لَهُمْ وَلَهُمْ أَجْرٌ كَرِيمٌ
Inna almussaddiqeena walmussaddiqatiwaaqradoo Allaha qardan hasanan
yudaAAafulahum walahum ajrun kareem
Hausa
Lalle măsu gaskatăwa maza da măsu gaskatăwa mătă, kuma suka ranta wa Allah rance
mai kyau, ană riɓanya musu, kuma suna da wani sakamako na karimci.
|
Ayah 57:19 الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا بِاللهِ وَرُسُلِهِ أُولَٰئِكَ هُمُ الصِّدِّيقُونَ ۖ
وَالشُّهَدَاءُ عِندَ رَبِّهِمْ لَهُمْ أَجْرُهُمْ وَنُورُهُمْ ۖ وَالَّذِينَ
كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ
Wallatheena amanoo billahiwarusulihi ola-ika humu assiddeeqoona
washshuhadaoAAinda rabbihim lahum ajruhum wanooruhum wallatheenakafaroo
wakaththaboo bi-ayatina ola-ikaas-habu aljaheem
Hausa
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni da Allah da MazanninSa waɗannan sũ ne kamălar
gaskatăwa kuma su ne măsu shahăda awurin Ubangjinsu. sună da sakamakonsu da
haskensu. waɗanda suka kafirta kuma suka ƙaryata game da ăyőyinMu, waɗannan su
ne'yan Jahĩm.
|
Ayah 57:20 الأية
اعْلَمُوا أَنَّمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا لَعِبٌ وَلَهْوٌ وَزِينَةٌ وَتَفَاخُرٌ
بَيْنَكُمْ وَتَكَاثُرٌ فِي الْأَمْوَالِ وَالْأَوْلَادِ ۖ كَمَثَلِ غَيْثٍ
أَعْجَبَ الْكُفَّارَ نَبَاتُهُ ثُمَّ يَهِيجُ فَتَرَاهُ مُصْفَرًّا ثُمَّ يَكُونُ
حُطَامًا ۖ وَفِي الْآخِرَةِ عَذَابٌ شَدِيدٌ وَمَغْفِرَةٌ مِّنَ اللهِ
وَرِضْوَانٌ ۚ وَمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلَّا مَتَاعُ الْغُرُورِ
IAAlamoo annama alhayatuaddunya laAAibun walahwun wazeenatun
watafakhurunbaynakum watakathurun fee al-amwali wal-awladikamathali ghaythin
aAAjaba alkuffara nabatuhuthumma yaheeju fatarahu musfarran thumma yakoonu
hutamanwafee al-akhirati AAathabun shadeedun wamaghfiratunmina Allahi waridwanun
wama alhayatuaddunya illa mataAAu alghuroor
Hausa
Ku sani cẽwa răyuwar dũniya wăsă ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a
tsakăninku da găsar wadăta ta dũkiya da ɗiya, kamar misălin shũka wadda
yabanyarta ta băyar da sha'awa ga manőma, sa'an nan ta ƙẽƙashe, har ka ganta tă
zama rawaya sa'an nan ta kőma rauno. Kuma, alămra akwai azăba mai tsanani da
găfara daga Allah da yarda. Kuma răyuwar dũniya ba ta zama ba făce ɗan jin dăɗin
rũɗi kawai.
|
Ayah 57:21 الأية
سَابِقُوا إِلَىٰ مَغْفِرَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا كَعَرْضِ
السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ أُعِدَّتْ لِلَّذِينَ آمَنُوا بِاللهِ وَرُسُلِهِ ۚ
ذَٰلِكَ فَضْلُ اللهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَاءُ ۚ وَاللهُ ذُو الْفَضْلِ
الْعَظِيمِ
Sabiqoo ila maghfiratin minrabbikum wajannatin AAarduha kaAAardi
assama-iwal-ardi oAAiddat lillatheena amanoobillahi warusulihi thalika fadlu
Allahiyu/teehi man yashao wallahu thooalfadli alAAatheem
Hausa
Ku yi tsẽre zuwa ga (nẽman) găfara daga Ubangjinku, da Aljanna făɗinta kamar
făɗin samă da ƙasă ne, an yi tattalinta dőmin waɗanda suka yi ĩmăni da Allah da
ManzanninSa. Wannan falalar Allah ce, Yană băyar da ita ga wanda Ya so. Kuma
Allah Mai falala ne Mai girma.
|
Ayah 57:22 الأية
مَا أَصَابَ مِن مُّصِيبَةٍ فِي الْأَرْضِ وَلَا فِي أَنفُسِكُمْ إِلَّا فِي
كِتَابٍ مِّن قَبْلِ أَن نَّبْرَأَهَا ۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى اللهِ يَسِيرٌ
Ma asaba min museebatinfee al-ardi wala fee anfusikum illa fee kitabinmin qabli
an nabraaha inna thalika AAala Allahiyaseer
Hausa
Wata masifa bă ză ta auku ba a cikin ƙasă kő a cikin rayukanku făce tană a cikin
littăfi a gabănin Mu halitta ta. Lalle wannan, ga Allah, mai sauƙi ne.
|
Ayah 57:23 الأية
لِّكَيْلَا تَأْسَوْا عَلَىٰ مَا فَاتَكُمْ وَلَا تَفْرَحُوا بِمَا آتَاكُمْ ۗ
وَاللهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ مُخْتَالٍ فَخُورٍ
Likayla ta/saw AAala mafatakum wala tafrahoo bima atakumwallahu la yuhibbu kulla
mukhtalinfakhoor
Hausa
Dőmin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi mumar
alfahari da abin da Ya bă ku. Kuma Allah bă Ya son dukkan mai tăƙama, mai
alfahari.
|
Ayah 57:24 الأية
الَّذِينَ يَبْخَلُونَ وَيَأْمُرُونَ النَّاسَ بِالْبُخْلِ ۗ وَمَن يَتَوَلَّ
فَإِنَّ اللهَ هُوَ الْغَنِيُّ الْحَمِيدُ
Allatheena yabkhaloona waya/muroona annasabilbukhli waman yatawalla fa-inna
Allaha huwaalghaniyyu alhameed
Hausa
Watau, waɗanda ke yin rőwa, kuma sună umumin mutăne da yin rőwa. Kuma wanda ya
jũya băya, to, lalle Allah, Shĩ ne kaɗai Mawadăci, Gődadde.
|
Ayah 57:25 الأية
لَقَدْ أَرْسَلْنَا رُسُلَنَا بِالْبَيِّنَاتِ وَأَنزَلْنَا مَعَهُمُ الْكِتَابَ
وَالْمِيزَانَ لِيَقُومَ النَّاسُ بِالْقِسْطِ ۖ وَأَنزَلْنَا الْحَدِيدَ فِيهِ
بَأْسٌ شَدِيدٌ وَمَنَافِعُ لِلنَّاسِ وَلِيَعْلَمَ اللهُ مَن يَنصُرُهُ
وَرُسُلَهُ بِالْغَيْبِ ۚ إِنَّ اللهَ قَوِيٌّ عَزِيزٌ
Laqad arsalna rusulana bilbayyinatiwaanzalna maAAahumu alkitaba
walmeezanaliyaqooma annasu bilqisti waanzalnaalhadeeda feehi ba/sun shadeedun
wamanafiAAu linnasiwaliyaAAlama Allahu man yansuruhu warusulahu bilghaybiinna
Allaha qawiyyun AAazeez
Hausa
Haƙĩƙa, lalle Mun aiko ManzanninMu da hujjőji bayyanannu, kuma Muka saukar da
Littăfi da sikẽli tăre da su dőmin mutăne su tsayu da ădalci, kuma Mun saukar da
baƙin ƙarfe, a cikinsa akwai cutarwa mai tsanani da amfăni ga mutăne, kuma dőmin
Allah Ya san mai taimakonSa da ManzanninSa a fake. Lalle ne Allah Mai ƙarfi ne,
Mabuwăyi.
|
Ayah 57:26 الأية
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا وَإِبْرَاهِيمَ وَجَعَلْنَا فِي ذُرِّيَّتِهِمَا
النُّبُوَّةَ وَالْكِتَابَ ۖ فَمِنْهُم مُّهْتَدٍ ۖ وَكَثِيرٌ مِّنْهُمْ فَاسِقُونَ
Walaqad arsalna noohan wa-ibraheemawajaAAalna fee thurriyyatihima
annubuwwatawalkitaba faminhum muhtadin wakatheerun minhum fasiqoon
Hausa
Kuma haƙĩƙa, lalle, Mun aiki Nũhu da Ibrahĩm, kuma Muka sanya Annabci da Littĩfi
a cikin zuriyarsu; daga cikinsu akwai mai nẽman shiryuwa, kuma măsu yawa daga
cikinsu fasiƙai ne.
|
Ayah 57:27 الأية
ثُمَّ قَفَّيْنَا عَلَىٰ آثَارِهِم بِرُسُلِنَا وَقَفَّيْنَا بِعِيسَى ابْنِ
مَرْيَمَ وَآتَيْنَاهُ الْإِنجِيلَ وَجَعَلْنَا فِي قُلُوبِ الَّذِينَ اتَّبَعُوهُ
رَأْفَةً وَرَحْمَةً وَرَهْبَانِيَّةً ابْتَدَعُوهَا مَا كَتَبْنَاهَا عَلَيْهِمْ
إِلَّا ابْتِغَاءَ رِضْوَانِ اللهِ فَمَا رَعَوْهَا حَقَّ رِعَايَتِهَا ۖ
فَآتَيْنَا الَّذِينَ آمَنُوا مِنْهُمْ أَجْرَهُمْ ۖ وَكَثِيرٌ مِّنْهُمْ
فَاسِقُونَ
Thumma qaffayna AAala atharihimbirusulina waqaffayna biAAeesa ibni
maryamawaataynahu al-injeela wajaAAalna fee quloobiallatheena ittabaAAoohu
ra/fatan warahmatan warahbaniyyatanibtadaAAooha ma katabnaha AAalayhimilla
ibtighaa ridwani Allahifama raAAawha haqqa riAAayatihafaatayna allatheena amanoo
minhumajrahum wakatheerun minhum fasiqoon
Hausa
Sa'an nan Muka biyar a băyansu da ManzanninMu; kuma Muka biyar da ĩsă ɗan
Maryama, kuma Muka ba shi Linjila kuma Muka sanya tausayi da rahama a cikin
zukătan waɗanda suka bĩ shi, da ruhbănanci wanda suka ƙăga, shi, ba Mu rubũta
shi ba a kansu, făce dai (Mun rubũta musu nẽman yardar Allah, sa'an nan ba su
tsare shi haƙƙin tsarẽwarsa ba, sabőda haka Muka bai wa waɗanda suka yi ĩmăni
daga cikinsu sakamakonsu kuma măsu yawa daga cikinsu făsiƙai ne.
|
Ayah 57:28 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللهَ وَآمِنُوا بِرَسُولِهِ يُؤْتِكُمْ
كِفْلَيْنِ مِن رَّحْمَتِهِ وَيَجْعَل لَّكُمْ نُورًا تَمْشُونَ بِهِ وَيَغْفِرْ
لَكُمْ ۚ وَاللهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Ya ayyuha allatheena amanooittaqoo Allaha waaminoo birasoolihi yu/tikumkiflayni
min rahmatihi wayajAAal lakum nooran tamshoonabihi wayaghfir lakum wallahu
ghafoorun raheem
Hausa
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! Ku bi Allah da taƙawa, ku yi ĩmăni da ManzonSa Ya
bă ku rabo biyu daga rahamarSa, kuma Ya sanya muku wani haske wanda kuke yin
tafiya da shi, kuma Ya găfarta muku. Kuma Allah Mai găfara ne, Mai rahama.
|
Ayah 57:29 الأية
لِّئَلَّا يَعْلَمَ أَهْلُ الْكِتَابِ أَلَّا يَقْدِرُونَ عَلَىٰ شَيْءٍ مِّن
فَضْلِ اللهِ ۙ وَأَنَّ الْفَضْلَ بِيَدِ اللهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَاءُ ۚ
وَاللهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ
Li-alla yaAAlama ahlu alkitabialla yaqdiroona AAala shay-in min fadli
Allahiwaanna alfadla biyadi Allahi yu/teehi man yashaowallahu thoo alfadli
alAAatheem
Hausa
Dőmin kada mutănen Littăfi su san cẽwa lalle bă su da ikon yi ga kőme na falalar
Allah, kuma ita falalar ga hannun Allah kawai take, Yană băyar da ita ga wanda
Ya so (wannan jăhilci yă hana su ĩmani). Kuma Al1ah Mai falala ne mai girma.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|