1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
قَدْ سَمِعَ اللهُ قَوْلَ الَّتِي تُجَادِلُكَ فِي زَوْجِهَا وَتَشْتَكِي إِلَى
اللهِ وَاللهُ يَسْمَعُ تَحَاوُرَكُمَا ۚ إِنَّ اللهَ سَمِيعٌ بَصِيرٌ
Qad samiAAa Allahu qawla allatee tujadilukafee zawjiha watashtakee ila Allahi
wallahuyasmaAAu tahawurakuma inna Allaha sameeAAunbaseer
Hausa
Lalle Alla Ya ji maganar wadda ke yi maka jăyayya game da mijinta, tană kai ƙăra
ga Allah, kuma Allah nă jin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani.
|
Ayah 58:2 الأية
الَّذِينَ يُظَاهِرُونَ مِنكُم مِّن نِّسَائِهِم مَّا هُنَّ أُمَّهَاتِهِمْ ۖ إِنْ
أُمَّهَاتُهُمْ إِلَّا اللَّائِي وَلَدْنَهُمْ ۚ وَإِنَّهُمْ لَيَقُولُونَ مُنكَرًا
مِّنَ الْقَوْلِ وَزُورًا ۚ وَإِنَّ اللهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٌ
Allatheena yuthahiroonaminkum min nisa-ihim ma hunna ommahatihim inommahatuhum
illa alla-ee waladnahumwa-innahum layaqooloona munkaran mina alqawli wazooran
wa-innaAllaha laAAafuwwun ghafoor
Hausa
Waɗanda ke yin zihări daga cikinku game da mătansu, sũmătan nan bă uwăyensu ba
ne, băbu uwayensu făce waɗanda suka haife su. Lalle sũ, sună faɗar abin ƙyămă na
magana da ƙarya, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai yăfẽwa ne, Mai găfara.
|
Ayah 58:3 الأية
وَالَّذِينَ يُظَاهِرُونَ مِن نِّسَائِهِمْ ثُمَّ يَعُودُونَ لِمَا قَالُوا
فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مِّن قَبْلِ أَن يَتَمَاسَّا ۚ ذَٰلِكُمْ تُوعَظُونَ بِهِ ۚ
وَاللهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ
Wallatheena yuthahiroonamin nisa-ihim thumma yaAAoodoona lima qaloofatahreeru
raqabatin min qabli an yatamassa thalikumtooAAathoona bihi wallahu
bimataAAmaloona khabeer
Hausa
Waɗanda ke yin zihări game da mătansu, sa'an nan su kőma wa abin da suka faɗa,
to, akwai 'yanta wuya a gabănin su shăfi jũna.Wannan ană yi muku wa'azi da shi.
Kuma Allah Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatăwa.
|
Ayah 58:4 الأية
فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ شَهْرَيْنِ مُتَتَابِعَيْنِ مِن قَبْلِ أَن
يَتَمَاسَّا ۖ فَمَن لَّمْ يَسْتَطِعْ فَإِطْعَامُ سِتِّينَ مِسْكِينًا ۚ ذَٰلِكَ
لِتُؤْمِنُوا بِاللهِ وَرَسُولِهِ ۚ وَتِلْكَ حُدُودُ اللهِ ۗ وَلِلْكَافِرِينَ
عَذَابٌ أَلِيمٌ
Faman lam yajid fasiyamushahrayni mutatabiAAayni min qabli an yatamassafaman lam
yastatiAA fa-itAAamu sitteenamiskeenan thalika litu/minoo billahiwarasoolihi
watilka hudoodu Allahi walilkafireenaAAathabun aleem
Hausa
To, wanda bai sămu ba, sai azumin wata biyu jẽre a gabănin su shăfi jũna, sa'an
nan wanda bai sămi ĩkon yi ba, to, sai ciyar da miskĩnai sittin. Wannan dőmin ku
yĩ ĩmăni da Allah da Manzonsa. Kuma waɗannan hukunce-hukunce haddődin Allah ne.
Kuma kăfirai, sună da azăba mai raɗadi.
|
Ayah 58:5 الأية
إِنَّ الَّذِينَ يُحَادُّونَ اللهَ وَرَسُولَهُ كُبِتُوا كَمَا كُبِتَ الَّذِينَ
مِن قَبْلِهِمْ ۚ وَقَدْ أَنزَلْنَا آيَاتٍ بَيِّنَاتٍ ۚ وَلِلْكَافِرِينَ عَذَابٌ
مُّهِينٌ
Inna allatheena yuhaddoona Allahawarasoolahu kubitoo kama kubita allatheena
minqablihim waqad anzalna ayatin bayyinatinwalilkafireena AAathabun muheen
Hausa
Lalle waɗanda ke săɓă wa Allah da ManzonSa, an wulăkanta su kamar yadda aka
wulăkantar da waɗanda ke a gabăninsu, kuma lalle Mun saukar da ăyőyi bayyanannu,
kuma kăfirai nă da azăba mai wulăkantăwa.
|
Ayah 58:6 الأية
يَوْمَ يَبْعَثُهُمُ اللهُ جَمِيعًا فَيُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوا ۚ أَحْصَاهُ
اللهُ وَنَسُوهُ ۚ وَاللهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ
Yawma yabAAathuhumu Allahu jameeAAanfayunabbi-ohum bima AAamiloo ahsahu
Allahuwanasoohu wallahu AAala kulli shay-inshaheed
Hausa
Rănar da Allah zai tăyar da su gabă ɗaya, sa'an nan Ya bă su lăbări game da abin
da suka aikata, Allah Yă lissafa shi, alhăli kuwa sũ,sun manta da shi, kuma a
kan kőme Allah Halartacce ne.
|
Ayah 58:7 الأية
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللهَ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۖ
مَا يَكُونُ مِن نَّجْوَىٰ ثَلَاثَةٍ إِلَّا هُوَ رَابِعُهُمْ وَلَا خَمْسَةٍ
إِلَّا هُوَ سَادِسُهُمْ وَلَا أَدْنَىٰ مِن ذَٰلِكَ وَلَا أَكْثَرَ إِلَّا هُوَ
مَعَهُمْ أَيْنَ مَا كَانُوا ۖ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوا يَوْمَ
الْقِيَامَةِ ۚ إِنَّ اللهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ
Alam tara anna Allaha yaAAlamu mafee assamawati wama fee al-ardima yakoonu min
najwa thalathatin illahuwa rabiAAuhum wala khamsatin illa huwa sadisuhumwala
adna min thalika wala aktharailla huwa maAAahum ayna ma kanoo thummayunabbi-ohum
bima AAamiloo yawma alqiyamati innaAllaha bikulli shay-in AAaleem
Hausa
Ashe, ba ka ga cẽwa lalle Allah Yană sane da abin da yake a cikin sammai da abin
da ke cikin ƙasa ba? Wata gănăwa ta mutum uku bă ză ta kasance ba făce Allah Shĩ
ne na huɗu ɗinta, kuma băbu ta mutum biyar făce Shĩ ne na shida ɗinta, kuma babu
abin da ya kăsa wannan kuma babu abin da yake mafi yawa făce Shĩ Yană tăre da su
duk inda suka kasance, sa'an nan Ya bă su lăbări game da abin da suka aikata a
Rănar ˇiyăma. Lalle Allah Masani ne ga dukkan kőme.
|
Ayah 58:8 الأية
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ نُهُوا عَنِ النَّجْوَىٰ ثُمَّ يَعُودُونَ لِمَا
نُهُوا عَنْهُ وَيَتَنَاجَوْنَ بِالْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَمَعْصِيَتِ الرَّسُولِ
وَإِذَا جَاءُوكَ حَيَّوْكَ بِمَا لَمْ يُحَيِّكَ بِهِ اللهُ وَيَقُولُونَ فِي
أَنفُسِهِمْ لَوْلَا يُعَذِّبُنَا اللهُ بِمَا نَقُولُ ۚ حَسْبُهُمْ جَهَنَّمُ
يَصْلَوْنَهَا ۖ فَبِئْسَ الْمَصِيرُ
Alam tara ila allatheena nuhooAAani annajwa thumma yaAAoodoona lima nuhooAAanhu
wayatanajawna bil-ithmi walAAudwaniwamaAAsiyati arrasooli wa-itha jaookahayyawka
bima lam yuhayyika bihi Allahuwayaqooloona fee anfusihim lawla
yuAAaththibunaAllahu bima naqoolu hasbuhum jahannamu yaslawnahafabi/sa almaseer
Hausa
Ashe, ba ka ga waɗanda aka hane su ba daga ganăwar, sa'an nan sună kőmă wa abin
da aka hane su daga gare shi, kuma sună gănăwa game da zunubi da zălunci da săɓă
wa Manzon Allah, kuma idan sun zo maka sai su gasihe ka da abin da Allah bai
gaishe ka da shi ba, kuma sună cẽwa a cikin zukatansu: "Don me Allah ba Ya yi
mana azăba sabőda abin da muke faɗi?" Jahannama ita ce mai isarsu, ză su
shigeta. Sabőda haka makőmarsu ta mũnana.
|
Ayah 58:9 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا تَنَاجَيْتُمْ فَلَا تَتَنَاجَوْا
بِالْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَمَعْصِيَتِ الرَّسُولِ وَتَنَاجَوْا بِالْبِرِّ
وَالتَّقْوَىٰ ۖ وَاتَّقُوا اللهَ الَّذِي إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ
Ya ayyuha allatheena amanooitha tanajaytum fala tatanajaw bil-ithmiwalAAudwani
wamaAAsiyati arrasooliwatanajaw bilbirri wattaqwa wattaqooAllaha allathee ilayhi
tuhsharoon
Hausa
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! Idan za ku yi gănăwa, to, kada ku găna game da
zunubi da zălunci da săɓă wa Manzon Allah, kuma ku yi gănăwa game da alhẽri da
taƙawa. Ku bi Allah da taƙawa wanda ză a tattara ku zuwa gare, shi.
|
Ayah 58:10 الأية
إِنَّمَا النَّجْوَىٰ مِنَ الشَّيْطَانِ لِيَحْزُنَ الَّذِينَ آمَنُوا وَلَيْسَ
بِضَارِّهِمْ شَيْئًا إِلَّا بِإِذْنِ اللهِ ۚ وَعَلَى اللهِ فَلْيَتَوَكَّلِ
الْمُؤْمِنُونَ
Innama annajwa mina ashshaytaniliyahzuna allatheena amanoo walaysa
bidarrihimshay-an illa bi-ithni Allahi waAAalaAllahi falyatawakkali almu/minoon
Hausa
Gănăwar daga Shaiɗan take kawai dőmin ya mũnană wa waɗanda suka yi ĩmăni, alhăli
kuwa bă zai iya cũtar su da kőme ba făce da iznin Allah. Kuma sai mũminai su
dogara ga Allah.
|
Ayah 58:11 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا قِيلَ لَكُمْ تَفَسَّحُوا فِي الْمَجَالِسِ
فَافْسَحُوا يَفْسَحِ اللهُ لَكُمْ ۖ وَإِذَا قِيلَ انشُزُوا فَانشُزُوا يَرْفَعِ
اللهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنكُمْ وَالَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ دَرَجَاتٍ ۚ
وَاللهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ
Ya ayyuha allatheena amanooitha qeela lakum tafassahoo fee almajalisifafsahoo
yafsahi Allahu lakum wa-ithaqeela onshuzoo fanshuzoo yarfaAAi Allahu
allatheenaamanoo minkum wallatheena ootoo alAAilmadarajatin wallahu bima
taAAmaloonakhabeer
Hausa
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! Idan an ce muka, "Ku yalwată a cikin majalisai,"
to, ku yalwată, sai Allah Ya yalwată muku, kuma idan an ce muku, "Ku tăshi" to,
ku tăshi. Allah nă ɗaukaka waɗanda suka yi ĩmăni daga cikinku da waɗanda aka bai
wa ilim wasu darajőji măsu yawa, kuma, Allah Mai ƙididdigewa ne ga dukan kőme.
|
Ayah 58:12 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نَاجَيْتُمُ الرَّسُولَ فَقَدِّمُوا بَيْنَ
يَدَيْ نَجْوَاكُمْ صَدَقَةً ۚ ذَٰلِكَ خَيْرٌ لَّكُمْ وَأَطْهَرُ ۚ فَإِن لَّمْ
تَجِدُوا فَإِنَّ اللهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Ya ayyuha allatheena amanooitha najaytumu arrasoola faqaddimoo baynayaday
najwakum sadaqatan thalika khayrunlakum waatharu fa-in lam tajidoo fa-inna
Allahaghafoorun raheem
Hausa
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! Idan ză ku gănăwa da Manzon Allah, to, ku gabătar
da 'yar sadaka a gabănin gănăwarku, wannan ne mafi alhẽri a gare ku, kuma mafi
tsarki. Sai idan ba ku sămi (abin sadakar ba), to, lalle, Allah, Mai găfara ne,
Mai jin ƙai.
|
Ayah 58:13 الأية
أَأَشْفَقْتُمْ أَن تُقَدِّمُوا بَيْنَ يَدَيْ نَجْوَاكُمْ صَدَقَاتٍ ۚ فَإِذْ لَمْ
تَفْعَلُوا وَتَابَ اللهُ عَلَيْكُمْ فَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ
وَأَطِيعُوا اللهَ وَرَسُولَهُ ۚ وَاللهُ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ
Aashfaqtum an tuqaddimoo bayna yaday najwakumsadaqatin fa-ith lam tafAAaloo
watabaAllahu AAalaykum faaqeemoo assalatawaatoo azzakata waateeAAoo
Allahawarasoolahu wallahu khabeerun bimataAAmaloon
Hausa
Ashe, kun ji tsőron ku gabătar da sadakőki a gabănin gănăwarku? To, idan ba ku
aikata ba, kuma Allah Ya kőmo da ku zuwa ga sauƙi, sai ku tsai da salla, kuma ku
băyar da zakka, kuma ku yi ɗă'ă ga Allah da ManzonSa. Kuma Allah ne Mai
ƙididdigewa ga abin da kuke aikatăwa.
|
Ayah 58:14 الأية
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ تَوَلَّوْا قَوْمًا غَضِبَ اللهُ عَلَيْهِم مَّا هُم
مِّنكُمْ وَلَا مِنْهُمْ وَيَحْلِفُونَ عَلَى الْكَذِبِ وَهُمْ يَعْلَمُونَ
Alam tara ila allatheenatawallaw qawman ghadiba Allahu AAalayhim mahum minkum
wala minhum wayahlifoona AAalaalkathibi wahum yaAAlamoon
Hausa
Ashe, baka ga waɗanda suka jiɓinci waɗansu mutăne da Allah Ya yi hushi a kansu
ba, bă su cikinku, kuma bă su a cikinsu kuma sună rantsuwa a kan ƙarya, alhăli
kuwa sună sane?
|
Ayah 58:15 الأية
أَعَدَّ اللهُ لَهُمْ عَذَابًا شَدِيدًا ۖ إِنَّهُمْ سَاءَ مَا كَانُوا
يَعْمَلُونَ
aAAadda Allahu lahum AAathabanshadeedan innahum saa ma kanoo yaAAmaloon
Hausa
Allah Ya yi musu tattalin azăba mai tsanani. Lalle sũ abin da suka kasance sună
aikatăwa ya mũnana.
|
Ayah 58:16 الأية
اتَّخَذُوا أَيْمَانَهُمْ جُنَّةً فَصَدُّوا عَن سَبِيلِ اللهِ فَلَهُمْ عَذَابٌ
مُّهِينٌ
Ittakhathoo aymanahum junnatanfasaddoo AAan sabeeli Allahi falahum
AAathabunmuheen
Hausa
Sun riƙi rantsuwőwinsu garkuwa, sabőda haka suka kange (mũminai) daga jihădin
ɗaukaka tafarkin Allah. To, sună da azăba mai wulăkantăwa.
|
Ayah 58:17 الأية
لَّن تُغْنِيَ عَنْهُمْ أَمْوَالُهُمْ وَلَا أَوْلَادُهُم مِّنَ اللهِ شَيْئًا ۚ
أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Lan tughniya AAanhum amwaluhum walaawladuhum mina Allahi shay-an ola-ika
as-habuannari hum feeha khalidoon
Hausa
Dũkiyőyinsu ba su wadătar musu kőme ba daga Allah, haka kuma ɗiyansu. Waɗannan
'yan wută ne. Sũ, măsu dawwama ne a cikinta.
|
Ayah 58:18 الأية
يَوْمَ يَبْعَثُهُمُ اللهُ جَمِيعًا فَيَحْلِفُونَ لَهُ كَمَا يَحْلِفُونَ لَكُمْ
ۖ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُمْ عَلَىٰ شَيْءٍ ۚ أَلَا إِنَّهُمْ هُمُ الْكَاذِبُونَ
Yawma yabAAathuhumu Allahu jameeAAanfayahlifoona lahu kama yahlifoona lakum
wayahsaboonaannahum AAala shay-in ala innahum humu alkathiboon
Hausa
Rănar da Allah ke tăyar da su gabă ɗaya, sai su yi Masa rantsuwa kamar yadda
suke yi muku rantsuwa (a nan dũniya) kuma sună zaton cẽwa sũ a kan wani abu
suke! To, lalle sũ, sũ ne maƙaryata.
|
Ayah 58:19 الأية
اسْتَحْوَذَ عَلَيْهِمُ الشَّيْطَانُ فَأَنسَاهُمْ ذِكْرَ اللهِ ۚ أُولَٰئِكَ
حِزْبُ الشَّيْطَانِ ۚ أَلَا إِنَّ حِزْبَ الشَّيْطَانِ هُمُ الْخَاسِرُونَ
Istahwatha AAalayhimu ashshaytanufaansahum thikra Allahi ola-ika
hizbuashshaytani ala inna hizba ashshaytanihumu alkhasiroon
Hausa
Shaiɗan ya rinjaya a kansu, sai ya mantar da su ambaton Allah, waɗannan ƙungiyar
Shaiɗan ne. To, lalle ƙungiyar Shaiɗan, sũ ne măsu hasăra.
|
Ayah 58:20 الأية
إِنَّ الَّذِينَ يُحَادُّونَ اللهَ وَرَسُولَهُ أُولَٰئِكَ فِي الْأَذَلِّينَ
Inna allatheena yuhaddoona Allahawarasoolahu ola-ika fee al-athalleen
Hausa
Lalle, waɗanda ke săɓă wa Allah da ManzonSa waɗannan sună a cikin (mutăne) mafi
ƙasƙanci.
|
Ayah 58:21 الأية
كَتَبَ اللهُ لَأَغْلِبَنَّ أَنَا وَرُسُلِي ۚ إِنَّ اللهَ قَوِيٌّ عَزِيزٌ
Kataba Allahu laaghlibanna anawarusulee inna Allaha qawiyyun AAazeez
Hausa
Allah Ya rubũta cẽwa," Lalle zan rinjăya, Nĩ da ManzanniNa." Lalle Allah Mai
ƙarfi ne, Mabuwăyi.
|
Ayah 58:22 الأية
لَّا تَجِدُ قَوْمًا يُؤْمِنُونَ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ يُوَادُّونَ مَنْ
حَادَّ اللهَ وَرَسُولَهُ وَلَوْ كَانُوا آبَاءَهُمْ أَوْ أَبْنَاءَهُمْ أَوْ
إِخْوَانَهُمْ أَوْ عَشِيرَتَهُمْ ۚ أُولَٰئِكَ كَتَبَ فِي قُلُوبِهِمُ الْإِيمَانَ
وَأَيَّدَهُم بِرُوحٍ مِّنْهُ ۖ وَيُدْخِلُهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا
الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ رَضِيَ اللهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ ۚ
أُولَٰئِكَ حِزْبُ اللهِ ۚ أَلَا إِنَّ حِزْبَ اللهِ هُمُ الْمُفْلِحُونَ
La tajidu qawman yu/minoona billahiwalyawmi al-akhiri yuwaddoona man haddaAllaha
warasoolahu walaw kanoo abaahumaw abnaahum aw ikhwanahum aw AAasheeratahum
ola-ikakataba fee quloobihimu al-eemana waayyadahum biroohinminhu wayudkhiluhum
jannatin tajree min tahtihaal-anharu khalideena feeha radiya AllahuAAanhum
waradoo AAanhu ola-ika hizbu Allahiala inna hizba Allahi humu almuflihoon
Hausa
Bă ză ka sămi mutăne măsu yin ĩmăni da Allah da RănarLăhira sună sőyayya da
wanda ya săɓă wa Allah da ManzonSa ba, kő dă sun kasance ubanninsu ne, kő
ɗiyansu kő 'yan'uwansu, ko danginsu. waɗannan Allah Yă rubuta ĩmăni a cikin
zukătansu, kuma Yă ƙarfafa su da wani rũhi daga gare Shi, kuma zai shigar da su
a gidăjen Aljanna, ƙoramu na gudăna ƙarƙashinsu sună măsu dawwama a cikinsu.
Allah Yă yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Waɗannan ƙungiyar Allah ne. To,
lalle ƙungiyar Allah sũ ne măsu babban rabo.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|