1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَجَعَلَ الظُّلُمَاتِ
وَالنُّورَ ۖ ثُمَّ الَّذِينَ كَفَرُوا بِرَبِّهِمْ يَعْدِلُونَ
Alhamdu lillahi allatheekhalaqa assamawati wal-ardawajaAAala aththulumati
wannoorathumma allatheena kafaroo birabbihim yaAAdiloon
Hausa
Gődiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halitta sammai da ƙasa, kuma Ya sanya duffai
da haske , sa'an nan kuma waɗanda suka kăfirta, da Ubangijinsu suke karkacewa.
|
Ayah 6:2 الأية
هُوَ الَّذِي خَلَقَكُم مِّن طِينٍ ثُمَّ قَضَىٰ أَجَلًا ۖ وَأَجَلٌ مُّسَمًّى
عِندَهُ ۖ ثُمَّ أَنتُمْ تَمْتَرُونَ
Huwa allathee khalaqakum min teeninthumma qada ajalan waajalun musamman AAindahu
thumma antumtamtaroon
Hausa
Shi ne wanda Ya halitta ku daga lăkă, sa'an nan kuma Ya yanka ajali alhăli wani
ajali ambatacce yană wurinSa. Sa'an nan kuma ku kună yin shakka.
|
Ayah 6:3 الأية
وَهُوَ اللهُ فِي السَّمَاوَاتِ وَفِي الْأَرْضِ ۖ يَعْلَمُ سِرَّكُمْ
وَجَهْرَكُمْ وَيَعْلَمُ مَا تَكْسِبُونَ
Wahuwa Allahu fee assamawatiwafee al-ardi yaAAlamu sirrakum wajahrakum
wayaAAlamu mataksiboon
Hausa
Kuma Shĩ ne Allah a cikin sammai, kuma a cikin ƙasa Yană sanin asĩrinku da
bayyanenku, kuma Yană sanin abin da kuke yi na tsirfa.
|
Ayah 6:4 الأية
وَمَا تَأْتِيهِم مِّنْ آيَةٍ مِّنْ آيَاتِ رَبِّهِمْ إِلَّا كَانُوا عَنْهَا
مُعْرِضِينَ
Wama ta/teehim min ayatin min ayatirabbihim illa kanoo AAanha muAArideen
Hausa
Kuma wata ăyă daga Ubangijinsu ba ză ta jẽ musu ba, făce su kasance, daga gare
ta, măsu bijirẽwa.
|
Ayah 6:5 الأية
فَقَدْ كَذَّبُوا بِالْحَقِّ لَمَّا جَاءَهُمْ ۖ فَسَوْفَ يَأْتِيهِمْ أَنبَاءُ مَا
كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ
Faqad kaththaboo bilhaqqilamma jaahum fasawfa ya/teehim anbao makanoo bihi
yastahzi-oon
Hausa
Sabőda haka, lalle sun ƙaryata (Manzo) game da gaskiya, a lőkacin da ta jẽ musu,
to lăbărun abin da suka kasance sună izgili da shi, ză su jẽ musu.
|
Ayah 6:6 الأية
أَلَمْ يَرَوْا كَمْ أَهْلَكْنَا مِن قَبْلِهِم مِّن قَرْنٍ مَّكَّنَّاهُمْ فِي
الْأَرْضِ مَا لَمْ نُمَكِّن لَّكُمْ وَأَرْسَلْنَا السَّمَاءَ عَلَيْهِم
مِّدْرَارًا وَجَعَلْنَا الْأَنْهَارَ تَجْرِي مِن تَحْتِهِمْ فَأَهْلَكْنَاهُم
بِذُنُوبِهِمْ وَأَنشَأْنَا مِن بَعْدِهِمْ قَرْنًا آخَرِينَ
Alam yaraw kam ahlakna min qablihimmin qarnin makkannahum fee al-ardi ma
lamnumakkin lakum waarsalna assamaa AAalayhimmidraran wajaAAalna al-anhara
tajree min tahtihimfaahlaknahum bithunoobihim waansha/na minbaAAdihim qarnan
akhareen
Hausa
Shin, ba su gani ba, da yawa Muka halakar da wani ƙarni daga gabăninsu, Mun
mallaka musu, a ckikin ƙasa, abin da ba Mu mallaka muku ba kuma Muka saki sama a
kansu tană ta zuba, kuma Muka sanya kőguna sună gudăna daga ƙarƙashinsu, sa'an
nan Muka halakă su sabőda zunubansu kuma Muka ƙăga halittar wani ƙarni na dabam
daga bayansu?
|
Ayah 6:7 الأية
وَلَوْ نَزَّلْنَا عَلَيْكَ كِتَابًا فِي قِرْطَاسٍ فَلَمَسُوهُ بِأَيْدِيهِمْ
لَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا إِنْ هَٰذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ
Walaw nazzalna AAalayka kitabanfee qirtasin falamasoohu bi-aydeehim laqala
allatheenakafaroo in hatha illa sihrun mubeen
Hausa
Kuma dă Mun sassaukar da wani littăfi, zuwa gare ka, a cikin takarda, sa'an nan
suka taɓa shi da hannuwansu, lalle dă waɗanda suka kăfirta sun ce: "Wannan bai
zama ba, face sihiri bayyananne."
|
Ayah 6:8 الأية
وَقَالُوا لَوْلَا أُنزِلَ عَلَيْهِ مَلَكٌ ۖ وَلَوْ أَنزَلْنَا مَلَكًا لَّقُضِيَ
الْأَمْرُ ثُمَّ لَا يُنظَرُونَ
Waqaloo lawla onzila AAalayhimalakun walaw anzalna malakan laqudiya
al-amruthumma la yuntharoon
Hausa
Suka ce: "Don me ba a saukar da wani mală'ika ba a gare shi?" to dă Mun saukar
da mală'ika haƙĩƙa dă an hukunta al'amarin sa'an nan kuma ba ză a yi musu
jinkiri ba.
|
Ayah 6:9 الأية
وَلَوْ جَعَلْنَاهُ مَلَكًا لَّجَعَلْنَاهُ رَجُلًا وَلَلَبَسْنَا عَلَيْهِم مَّا
يَلْبِسُونَ
Walaw jaAAalnahu malakan lajaAAalnahurajulan walalabasna AAalayhim ma yalbisoon
Hausa
Kuma dă Mun sanya mală'ika ya zama manzo lalle ne dă Mun mayar da shi mutum,
kuma dă Mun rikita musu abin da suke rikităwa.
|
Ayah 6:10 الأية
وَلَقَدِ اسْتُهْزِئَ بِرُسُلٍ مِّن قَبْلِكَ فَحَاقَ بِالَّذِينَ سَخِرُوا مِنْهُم
مَّا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ
Walaqadi istuhzi-a birusulin min qablika fahaqabillatheena sakhiroo minhum ma
kanoobihi yastahzi-oon
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da manzanni daga gabaninka, sai waɗanda suka
yi izgilin, abin da suka kasance sună izgili da shi ya făɗa musu.
|
Ayah 6:11 الأية
قُلْ سِيرُوا فِي الْأَرْضِ ثُمَّ انظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُكَذِّبِينَ
Qul seeroo fee al-ardi thumma onthurookayfa kana AAaqibatu almukaththibeen
Hausa
Ka ce: "Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan kuma ku dũba yadda ăƙibar măsu
ƙaryatăwa ta kasance."
|
Ayah 6:12 الأية
قُل لِّمَن مَّا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ قُل لِّلَّهِ ۚ كَتَبَ عَلَىٰ
نَفْسِهِ الرَّحْمَةَ ۚ لَيَجْمَعَنَّكُمْ إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ لَا رَيْبَ
فِيهِ ۚ الَّذِينَ خَسِرُوا أَنفُسَهُمْ فَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ
Qul liman ma fee assamawatiwal-ardi qul lillahi kataba AAalanafsihi arrahmata
layajmaAAannakum ilayawmi alqiyamati la rayba feehi allatheenakhasiroo anfusahum
fahum la yu/minoon
Hausa
Ka ce: "Na wăne ne abin da yake a cikin sammai da ƙasa?" Ka ce: "Na Allah ne."
Yă wajabta rahama ga kanSa. Lalle ne Yană tăra ku zuwa ga Rănar ˇiyăma, babu
shakka a gare Shi. Waɗanda suka yi hasărar răyukansu, to, sũ ba ză su yi ĩmani
ba."
|
Ayah 6:13 الأية
وَلَهُ مَا سَكَنَ فِي اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ ۚ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Walahu ma sakana fee allayli wannahariwahuwa assameeAAu alAAaleem
Hausa
"Kuma Shĩ ne da mallakar abin da ya yi kawaici a cikin dare da yini, kuma Shi ne
Mai ji, Masani."
|
Ayah 6:14 الأية
قُلْ أَغَيْرَ اللهِ أَتَّخِذُ وَلِيًّا فَاطِرِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ
وَهُوَ يُطْعِمُ وَلَا يُطْعَمُ ۗ قُلْ إِنِّي أُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ أَوَّلَ مَنْ
أَسْلَمَ ۖ وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ الْمُشْرِكِينَ
Qul aghayra Allahi attakhithuwaliyyan fatiri assamawati wal-ardiwahuwa yutAAimu
wala yutAAamu qul inneeomirtu an akoona awwala man aslama wala takoonanna
minaalmushrikeen
Hausa
Ka ce: "Shin, wanin Allah nike riƙo majiɓinci, (alhăli Allah ne ) Mai ƙăga
halittar sammai da ƙasa, kuma Shi, Yană ciyarwa, kuma ba a ciyar da Shi?" Ka ce:
"Lalle ne nĩ, an umurce ni da in kasance farkon wanda ya sallama, kuma kada
lalle ku kasance daga măsu shirki."
|
Ayah 6:15 الأية
قُلْ إِنِّي أَخَافُ إِنْ عَصَيْتُ رَبِّي عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ
Qul innee akhafu in AAasayturabbee AAathaba yawmin AAatheem
Hausa
Kace: "Lalle ne nĩ ină tsőron azăbar Yini Mai girma, idan nă săɓă wa
Ubangijina."
|
Ayah 6:16 الأية
مَّن يُصْرَفْ عَنْهُ يَوْمَئِذٍ فَقَدْ رَحِمَهُ ۚ وَذَٰلِكَ الْفَوْزُ الْمُبِينُ
Man yusraf AAanhu yawma-ithinfaqad rahimahu wathalika alfawzu almubeen
Hausa
"Wanda aka jũyar da shi daga gare shi, a wannan Rănar, to, lalle ne,( Allah) Yă
yi masa rahama, Kuma wannan ne tsĩra bayyananniya."
|
Ayah 6:17 الأية
وَإِن يَمْسَسْكَ اللهُ بِضُرٍّ فَلَا كَاشِفَ لَهُ إِلَّا هُوَ ۖ وَإِن
يَمْسَسْكَ بِخَيْرٍ فَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Wa-in yamsaska Allahu bidurrinfala kashifa lahu illa huwa wa-in
yamsaskabikhayrin fahuwa AAala kulli shay-in qadeer
Hausa
"Idan Allah Ya shăfe ka da wata cũta, to, babu mai kuranyẽwa gare ta, făce Shĩ,
kuma idanYa shăfe ka da wani alhẽri to shĩ ne, a kan kőme, Mai ĩkon yi."
|
Ayah 6:18 الأية
وَهُوَ الْقَاهِرُ فَوْقَ عِبَادِهِ ۚ وَهُوَ الْحَكِيمُ الْخَبِيرُ
Wahuwa alqahiru fawqa AAibadihiwahuwa alhakeemu alkhabeer
Hausa
"Kuma Shĩ ne mai Tanƙwasa a kan bayinSa, kuma Shi ne Mai hikima, Masani."
|
Ayah 6:19 الأية
قُلْ أَيُّ شَيْءٍ أَكْبَرُ شَهَادَةً ۖ قُلِ اللهُ ۖ شَهِيدٌ بَيْنِي
وَبَيْنَكُمْ ۚ وَأُوحِيَ إِلَيَّ هَٰذَا الْقُرْآنُ لِأُنذِرَكُم بِهِ وَمَن
بَلَغَ ۚ أَئِنَّكُمْ لَتَشْهَدُونَ أَنَّ مَعَ اللهِ آلِهَةً أُخْرَىٰ ۚ قُل
لَّا أَشْهَدُ ۚ قُلْ إِنَّمَا هُوَ إِلَٰهٌ وَاحِدٌ وَإِنَّنِي بَرِيءٌ مِّمَّا
تُشْرِكُونَ
Qul ayyu shay-in akbaru shahadatanquli Allahu shaheedun baynee wabaynakum
waoohiyailayya hatha alqur-anu li-onthirakum bihiwaman balagha a-innakum
latashhadoona anna maAAa Allahi alihatanokhra qul la ashhadu qul innama huwa
ilahunwahidun wa-innanee baree-on mimma tushrikoon
Hausa
Ka ce: "Wane abu ne mafi girma ga shaida?" Ka ce: "Allah ne shaida a tsakănina
da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ăni dőmin in yi muku gargaɗi da
shi, da wanda lăbări ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙĩƙa,kună shaidar
cẽwa, lalle ne tăre da Allah akwai wasu abũbuwan bautawa?" Ka ce: "Bă zan yi
shaidar ( haka) ba." Ka ce: "Abin sani, Shi ne Abin bautăwa Guda kumă lalle ne
nĩ barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirki."
|
Ayah 6:20 الأية
الَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ يَعْرِفُونَهُ كَمَا يَعْرِفُونَ أَبْنَاءَهُمُ
ۘ الَّذِينَ خَسِرُوا أَنفُسَهُمْ فَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ
Allatheena ataynahumualkitaba yaAArifoonahu kama yaAArifoona abnaahumallatheena
khasiroo anfusahum fahum la yu/minoon
Hausa
Waɗanda Muka bă su Littăfi sună sanin sa kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Waɗanda
suka yi hasărar răyukansu, to, sũ bă su yin ĩmăni.
|
Ayah 6:21 الأية
وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَىٰ عَلَى اللهِ كَذِبًا أَوْ كَذَّبَ بِآيَاتِهِ
ۗ إِنَّهُ لَا يُفْلِحُ الظَّالِمُونَ
Waman athlamu mimmani iftaraAAala Allahi kathiban aw kaththababi-ayatihi innahu
la yuflihu aththalimoon
Hausa
Wăne ne mafi zălunci daga wanda yake ƙirƙira karya ga Allah, kő kuwa ya ƙaryata
game da ăyőyinsa? Lalle ne shĩ, azzalumai bă ză su ci nasara ba.
|
Ayah 6:22 الأية
وَيَوْمَ نَحْشُرُهُمْ جَمِيعًا ثُمَّ نَقُولُ لِلَّذِينَ أَشْرَكُوا أَيْنَ
شُرَكَاؤُكُمُ الَّذِينَ كُنتُمْ تَزْعُمُونَ
Wayawma nahshuruhum jameeAAan thummanaqoolu lillatheena ashrakoo ayna
shurakaokumu allatheenakuntum tazAAumoon
Hausa
Kuma rănar da Muka tăra su gabă ɗaya, sa'an nan Mu ce wa waɗanda suka yi shirki:
"Ină abőkan tărayyarku waɗanda kuka kasance kună riyăwa?"
|
Ayah 6:23 الأية
ثُمَّ لَمْ تَكُن فِتْنَتُهُمْ إِلَّا أَن قَالُوا وَاللهِ رَبِّنَا مَا كُنَّا
مُشْرِكِينَ
Thumma lam takun fitnatuhum illa an qaloowallahi rabbina ma kunnamushrikeen
Hausa
Sa'an nan kuma fitinarsu ba ta kasance ba, făce dőmin sun ce: "Mună rantsuwa da
Allah Ubangijinmu, ba mu kasance măsu yin shirki ba."
|
Ayah 6:24 الأية
انظُرْ كَيْفَ كَذَبُوا عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ ۚ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا
يَفْتَرُونَ
Onthur kayfa kathabooAAala anfusihim wadalla AAanhum ma kanooyaftaroon
Hausa
Ka dũba yadda suka ƙaryata kansu! Kuma abin da suka kasance sună ƙirƙira
ƙaryarsa, ya ɓace daga gare su.
|
Ayah 6:25 الأية
وَمِنْهُم مَّن يَسْتَمِعُ إِلَيْكَ ۖ وَجَعَلْنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ أَكِنَّةً
أَن يَفْقَهُوهُ وَفِي آذَانِهِمْ وَقْرًا ۚ وَإِن يَرَوْا كُلَّ آيَةٍ لَّا
يُؤْمِنُوا بِهَا ۚ حَتَّىٰ إِذَا جَاءُوكَ يُجَادِلُونَكَ يَقُولُ الَّذِينَ
كَفَرُوا إِنْ هَٰذَا إِلَّا أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ
Waminhum man yastamiAAu ilayka wajaAAalnaAAala quloobihim akinnatan an
yafqahoohu wafee athanihimwaqran wa-in yaraw kulla ayatin la yu/minoo bihahatta
itha jaooka yujadiloonakayaqoolu allatheena kafaroo in hatha illa
asateerual-awwaleen
Hausa
Kuma daga cikinsu akwai wanda yake saurăre gare ka. Kuma Mun sanya abũbuwan rufi
a kan zukătansu dőmin kada su fahimcẽ shi kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya)
wani nauyi. Kuma idan sun ga kőwace ăyă bă ză su yi ĩmăni da ita ba har idan
sunjẽ maka sună jăyayya da kai, waɗanda suka kăfirta sună cẽwa: "Wannan bai zama
ba făce tătsũniyőyin mutănen farko."
|
Ayah 6:26 الأية
وَهُمْ يَنْهَوْنَ عَنْهُ وَيَنْأَوْنَ عَنْهُ ۖ وَإِن يُهْلِكُونَ إِلَّا
أَنفُسَهُمْ وَمَا يَشْعُرُونَ
Wahum yanhawna AAanhu wayan-awna AAanhuwa-in yuhlikoona illa anfusahum wama
yashAAuroon
Hausa
Kuma sună hanăwa daga gare shi, kuma sună nĩsanta daga gare shi, kuma bă su
halakarwa, făce kansu, kuma bă su sansancẽwa.
|
Ayah 6:27 الأية
وَلَوْ تَرَىٰ إِذْ وُقِفُوا عَلَى النَّارِ فَقَالُوا يَا لَيْتَنَا نُرَدُّ وَلَا
نُكَذِّبَ بِآيَاتِ رَبِّنَا وَنَكُونَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ
Walaw tara ith wuqifoo AAalaannari faqaloo ya laytananuraddu wala nukaththiba
bi-ayatirabbina wanakoona mina almu/mineen
Hausa
Kuma dă kană gani, a lőkacin da aka tsayar da su a kan wuta, sai suka ce: "Yă
kaitőnmu! Dă ana mayar da mu, kuma bă ză mu ƙaryata ba daga ăyőyin Ubangijinmu,
kuma ză mu kasance Daga mũminai."
|
Ayah 6:28 الأية
بَلْ بَدَا لَهُم مَّا كَانُوا يُخْفُونَ مِن قَبْلُ ۖ وَلَوْ رُدُّوا لَعَادُوا
لِمَا نُهُوا عَنْهُ وَإِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ
Bal bada lahum ma kanooyukhfoona min qablu walaw ruddoo laAAadoo limanuhoo
AAanhu wa-innahum lakathiboon
Hausa
Ă'aha, abin da suka kasance suna ɓőyẽwa, daga gabăni, ya bayyana a gare su. Kuma
dă an mayar da su, lalle dă sun kőma ga abin da aka hana su daga barinsa. Kuma
lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
|
Ayah 6:29 الأية
وَقَالُوا إِنْ هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا الدُّنْيَا وَمَا نَحْنُ بِمَبْعُوثِينَ
Waqaloo in hiya illa hayatunaaddunya wama nahnu bimabAAootheen
Hausa
Kuma suka ce: "Ba ta zama ba, făce rayuwarmu ta duniya, kuma ba mu zama waɗanda
ake tăyarwa ba."
|
Ayah 6:30 الأية
وَلَوْ تَرَىٰ إِذْ وُقِفُوا عَلَىٰ رَبِّهِمْ ۚ قَالَ أَلَيْسَ هَٰذَا بِالْحَقِّ
ۚ قَالُوا بَلَىٰ وَرَبِّنَا ۚ قَالَ فَذُوقُوا الْعَذَابَ بِمَا كُنتُمْ
تَكْفُرُونَ
Walaw tara ith wuqifoo AAalarabbihim qala alaysa hatha bilhaqqiqaloo bala
warabbina qala fathooqooalAAathaba bima kuntum takfuroon
Hausa
Kuma dă kana gani, a lőkacin da aka tsayar da su ga UbangiJinsu, Ya ce: "Ashe
wannan bai zama gaskiya ba?" Suka ce: "Nă'am, muna rantsuwa da Ubangijinmu!" Ya
ce: "To ku ɗanɗani azaba sabőda abin da kuka kasance kuna yi na kăfirci."
|
Ayah 6:31 الأية
قَدْ خَسِرَ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِلِقَاءِ اللهِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا جَاءَتْهُمُ
السَّاعَةُ بَغْتَةً قَالُوا يَا حَسْرَتَنَا عَلَىٰ مَا فَرَّطْنَا فِيهَا وَهُمْ
يَحْمِلُونَ أَوْزَارَهُمْ عَلَىٰ ظُهُورِهِمْ ۚ أَلَا سَاءَ مَا يَزِرُونَ
Qad khasira allatheena kaththaboobiliqa-i Allahi hatta itha jaat-humuassaAAatu
baghtatan qaloo ya hasratanaAAala ma farratna feeha wahumyahmiloona awzarahum
AAala thuhoorihimala saa ma yaziroon
Hausa
Lalle ne waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasara, har idan
Sa'a ta je musu kwatsam, sai su ce: "Yă nadămarmu a kan abin da muka yi sakaci a
cikinta!" Alhăli kuwa su suna ɗaukar kayansu masu nauyi a kan bayayyakinsu. To,
abin da suke ɗauka yă mũnana.
|
Ayah 6:32 الأية
وَمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلَّا لَعِبٌ وَلَهْوٌ ۖ وَلَلدَّارُ الْآخِرَةُ
خَيْرٌ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَ ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَ
Wama alhayatu addunyailla laAAibun walahwun waladdaru al-akhiratikhayrun
lillatheena yattaqoona afala taAAqiloon
Hausa
Kuma răyuwar dũniya ba ta zama ba, făce wăsa da shagala, kuma lalle ne, Lăhira
ce mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa. Shin, ba za ku yi hankali ba?
|
Ayah 6:33 الأية
قَدْ نَعْلَمُ إِنَّهُ لَيَحْزُنُكَ الَّذِي يَقُولُونَ ۖ فَإِنَّهُمْ لَا
يُكَذِّبُونَكَ وَلَٰكِنَّ الظَّالِمِينَ بِآيَاتِ اللهِ يَجْحَدُونَ
Qad naAAlamu innahu layahzunuka allatheeyaqooloona fa-innahum la
yukaththiboonaka walakinnaaththalimeena bi-ayatiAllahi yajhadoon
Hausa
Lalle ne Muna sani cewa haƙĩƙa, abin da suke faɗa yana ɓăta maka rai. To, lalle
ne su, bă su ƙaryata ka (a cikin zukatansu ) kuma amma azzălumai da ăyőyin Allah
suke musu.
|
Ayah 6:34 الأية
وَلَقَدْ كُذِّبَتْ رُسُلٌ مِّن قَبْلِكَ فَصَبَرُوا عَلَىٰ مَا كُذِّبُوا
وَأُوذُوا حَتَّىٰ أَتَاهُمْ نَصْرُنَا ۚ وَلَا مُبَدِّلَ لِكَلِمَاتِ اللهِ ۚ
وَلَقَدْ جَاءَكَ مِن نَّبَإِ الْمُرْسَلِينَ
Walaqad kuththibat rusulun minqablika fasabaroo AAala ma kuththiboowaoothoo
hatta atahum nasrunawala mubaddila likalimati Allahi walaqad jaakamin naba-i
almursaleen
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an ƙaryata manzanni daga gabăninka, sai suka yi haƙuri a
kan abin da aka ƙaryata su, kuma aka cũtar da su, har taimakonMu ya je musu,
kuma babu mai musanyăwa ga kalmőmin Allah. Kuma lalle ne (abin da yake natsar da
kai) ya zo maka daga lăbărin (annabăwan) farko.
|
Ayah 6:35 الأية
وَإِن كَانَ كَبُرَ عَلَيْكَ إِعْرَاضُهُمْ فَإِنِ اسْتَطَعْتَ أَن تَبْتَغِيَ
نَفَقًا فِي الْأَرْضِ أَوْ سُلَّمًا فِي السَّمَاءِ فَتَأْتِيَهُم بِآيَةٍ ۚ
وَلَوْ شَاءَ اللهُ لَجَمَعَهُمْ عَلَى الْهُدَىٰ ۚ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ
الْجَاهِلِينَ
Wa-in kana kabura AAalayka iAAraduhumfa-ini istataAAta an tabtaghiya nafaqan fee
al-ardiaw sullaman fee assama-i fata/tiyahum bi-ayatinwalaw shaa Allahu
lajamaAAahum AAala alhudafala takoonanna mina aljahileen
Hausa
Kuma idan yă kasance cewa finjirewarsu tă yi nauyi a gare ka, to, idan kana
iyăwa, ka nemi wani ɓullő a cikin ƙasa, kő kuwa wani tsăni a cikin sama dőmin ka
zo musu da wata ăyă, ( sai ka yi). Kuma dă Allah Yă so haƙĩƙa dă Yătăra su a kan
shiriya. Sabőda haka, kada lalle ka kasance daga jăhilai.
|
Ayah 6:36 الأية
إِنَّمَا يَسْتَجِيبُ الَّذِينَ يَسْمَعُونَ ۘ وَالْمَوْتَىٰ يَبْعَثُهُمُ اللهُ
ثُمَّ إِلَيْهِ يُرْجَعُونَ
Innama yastajeebu allatheenayasmaAAoona walmawta yabAAathuhumu Allahuthumma
ilayhi yurjaAAoon
Hausa
Abin sani kawai, waɗanda suke saurare ne suke karɓăwa, kuma matattu Allah Yake
tăyar da su, Sa'an nan kuma zuwa gare Shi ake mayar da su.
|
Ayah 6:37 الأية
وَقَالُوا لَوْلَا نُزِّلَ عَلَيْهِ آيَةٌ مِّن رَّبِّهِ ۚ قُلْ إِنَّ اللهَ
قَادِرٌ عَلَىٰ أَن يُنَزِّلَ آيَةً وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Waqaloo lawla nuzzila AAalayhiayatun min rabbihi qul inna Allaha qadirunAAala an
yunazzila ayatan walakinnaaktharahum la yaAAlamoon
Hausa
Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da ăyă ba, a kansa, daga Ubangjinsa?" Ka ce:
"Lalle ne Allah Mai ĩko ne a kan Yasaukar da ăyă, kuma amma mafi yawansu, ba su
sani ba."
|
Ayah 6:38 الأية
وَمَا مِن دَابَّةٍ فِي الْأَرْضِ وَلَا طَائِرٍ يَطِيرُ بِجَنَاحَيْهِ إِلَّا
أُمَمٌ أَمْثَالُكُم ۚ مَّا فَرَّطْنَا فِي الْكِتَابِ مِن شَيْءٍ ۚ ثُمَّ إِلَىٰ
رَبِّهِمْ يُحْشَرُونَ
Wama min dabbatin fee al-ardiwala ta-irin yateeru bijanahayhi illaomamun
amthalukum ma farratna feealkitabi min shay-in thumma ila rabbihim yuhsharoon
Hausa
Kuma băbu wata dabba a cikin ƙasa kuma băbu wani tsuntsu wanda yake tashi da
fukafukinsa făce al'umma ne misălanku. Ba Mu yi sakacin barin kőme ba a cikin
Littăfi, sa'an nan kuma zuwa ga Ubangjinsu ake tăra su.
|
Ayah 6:39 الأية
وَالَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا صُمٌّ وَبُكْمٌ فِي الظُّلُمَاتِ ۗ مَن يَشَإِ
اللهُ يُضْلِلْهُ وَمَن يَشَأْ يَجْعَلْهُ عَلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Wallatheena kaththaboobi-ayatina summun wabukmun fee aththulumatiman yasha-i
Allahu yudlilhu waman yasha/ yajAAalhuAAala siratin mustaqeem
Hausa
Kuma waɗanda suka ƙaryata gameda ăyőyinMu, kurăme ne kuma bebăye, acikin duffai.
Wanda Allah Ya so Yană ɓatar da shi, kuma wanda Ya so zai sanya shi a kan hanya
madaidaiciya.
|
Ayah 6:40 الأية
قُلْ أَرَأَيْتَكُمْ إِنْ أَتَاكُمْ عَذَابُ اللهِ أَوْ أَتَتْكُمُ السَّاعَةُ
أَغَيْرَ اللهِ تَدْعُونَ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Qul araaytakum in atakum AAathabuAllahi aw atatkumu assaAAatu aghayra
AllahitadAAoona in kuntum sadiqeen
Hausa
Ka ce: "Shĩn, kun gan ku, idan azăbar Allah ta zo muku, kő Să'ar Tashin Kiyăma
ta zo muku, shin wanin Allah kuke kira, idan dai kun kasance măsu gaskiya?"
|
Ayah 6:41 الأية
بَلْ إِيَّاهُ تَدْعُونَ فَيَكْشِفُ مَا تَدْعُونَ إِلَيْهِ إِن شَاءَ وَتَنسَوْنَ
مَا تُشْرِكُونَ
Bal iyyahu tadAAoona fayakshifu matadAAoona ilayhi in shaa watansawna ma
tushrikoon
Hausa
"Ă'a, Shĩ dai kuke kira sai Ya kuranye abin da kuke kira zuwa gare Shi, idan Ya
so, kuma kună mantăwar abin da kuke yin shirkin tăre da shi."
|
Ayah 6:42 الأية
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا إِلَىٰ أُمَمٍ مِّن قَبْلِكَ فَأَخَذْنَاهُم بِالْبَأْسَاءِ
وَالضَّرَّاءِ لَعَلَّهُمْ يَتَضَرَّعُونَ
Walaqad arsalna ila omamin minqablika faakhathnahum bilba/sa-i
waddarra-ilaAAallahum yatadarraAAoon
Hausa
Kuma lalle Mun aika zuwa ga al'ummai daga gabăninka, sai Muka kămă su da tsanani
da cũta, tsammăninsu ză su ƙanƙan da kai,
|
Ayah 6:43 الأية
فَلَوْلَا إِذْ جَاءَهُم بَأْسُنَا تَضَرَّعُوا وَلَٰكِن قَسَتْ قُلُوبُهُمْ
وَزَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Falawla ith jaahumba/suna tadarraAAoo walakin qasat quloobuhumwazayyana lahumu
ashshaytanu ma kanooyaAAmaloon
Hausa
To, don me, a lőkacin da tsananinMu ya jẽ musu ba su yi tawălu'i ba? Kuma amma
zukatansu sun ƙẽƙashe kuma shaiɗan yă ƙawăta musu abin da suka kasance sună
aikatăwa.
|
Ayah 6:44 الأية
فَلَمَّا نَسُوا مَا ذُكِّرُوا بِهِ فَتَحْنَا عَلَيْهِمْ أَبْوَابَ كُلِّ شَيْءٍ
حَتَّىٰ إِذَا فَرِحُوا بِمَا أُوتُوا أَخَذْنَاهُم بَغْتَةً فَإِذَا هُم
مُّبْلِسُونَ
Falamma nasoo ma thukkiroobihi fatahna AAalayhim abwaba kulli shay-in hattaitha
farihoo bima ootoo akhathnahumbaghtatan fa-itha hum mublisoon
Hausa
Sa'an nan kuma alőkacin da suka manta da abin da aka tunătar da su da shi, sai
Muka bũɗe, a kansu, ƙőfőfin dukkan kőme, har a lőkacin da suka yi farin ciki da
abin da aka ba su, Muka kămă su, kwatsam, sai gă su sun yi tsuru tsuru.
|
Ayah 6:45 الأية
فَقُطِعَ دَابِرُ الْقَوْمِ الَّذِينَ ظَلَمُوا ۚ وَالْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ
الْعَالَمِينَ
FaqutiAAa dabiru alqawmi allatheenathalamoo walhamdu lillahirabbi alAAalameen
Hausa
Sai aka katse ƙarshen mutănen, waɗanda suka yi zălunci. Kuma gődiya tă tabbata
ga Allah Ubangijin tălikai.
|
Ayah 6:46 الأية
قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِنْ أَخَذَ اللهُ سَمْعَكُمْ وَأَبْصَارَكُمْ وَخَتَمَ عَلَىٰ
قُلُوبِكُم مَّنْ إِلَٰهٌ غَيْرُ اللهِ يَأْتِيكُم بِهِ ۗ انظُرْ كَيْفَ
نُصَرِّفُ الْآيَاتِ ثُمَّ هُمْ يَصْدِفُونَ
Qul araaytum in akhatha AllahusamAAakum waabsarakum wakhatama AAala
quloobikumman ilahun ghayru Allahi ya/teekum bihi onthurkayfa nusarrifu al-ayati
thumma hum yasdifoon
Hausa
Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya riƙe jinku, da gannanku, kuma Ya sanya
hătimi a kan zukătanku, wane abin bauttăwa ne, wanin Allah, zai jẽ muku da shi?"
Ka dũba yadda Muke sarrafaăyőyi, Sa'an nan kuma sũ, sună finjirẽwa.
|
Ayah 6:47 الأية
قُلْ أَرَأَيْتَكُمْ إِنْ أَتَاكُمْ عَذَابُ اللهِ بَغْتَةً أَوْ جَهْرَةً هَلْ
يُهْلَكُ إِلَّا الْقَوْمُ الظَّالِمُونَ
Qul araaytakum in atakum AAathabuAllahi baghtatan aw jahratan hal yuhlaku
illaalqawmu aththalimoon
Hausa
Ka ce: "Shin, kun gan ku, idan azăbar Allah ta jẽ muku, kwatsam, kő kuwa
bayyane, shin, ană halakăwa, făce dai mutăne azzălumai?"
|
Ayah 6:48 الأية
وَمَا نُرْسِلُ الْمُرْسَلِينَ إِلَّا مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ ۖ فَمَنْ آمَنَ
وَأَصْلَحَ فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ
Wama nursilu almursaleena illamubashshireena wamunthireena faman amana
waaslahafala khawfun AAalayhim wala hum yahzanoon
Hausa
Kuma bă Mu aikăwa da manzănni făce măsu bayar da bushăra, kuma măsu gargaɗi. To,
wanda ya yi ĩmăni kuma yagyăra aiki, to, babu tsőro a kansu, kuma ba su yin
baƙin ciki.
|
Ayah 6:49 الأية
وَالَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا يَمَسُّهُمُ الْعَذَابُ بِمَا كَانُوا
يَفْسُقُونَ
Wallatheena kaththaboobi-ayatina yamassuhumu alAAathabu bimakanoo yafsuqoon
Hausa
Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ăyőyinMu, azăba tană shăfar su sabőda abin da
suka kasance sună yi na făsiƙanci.
|
Ayah 6:50 الأية
قُل لَّا أَقُولُ لَكُمْ عِندِي خَزَائِنُ اللهِ وَلَا أَعْلَمُ الْغَيْبَ وَلَا
أَقُولُ لَكُمْ إِنِّي مَلَكٌ ۖ إِنْ أَتَّبِعُ إِلَّا مَا يُوحَىٰ إِلَيَّ ۚ قُلْ
هَلْ يَسْتَوِي الْأَعْمَىٰ وَالْبَصِيرُ ۚ أَفَلَا تَتَفَكَّرُونَ
Qul la aqoolu lakum AAindee khaza-inuAllahi wala aAAlamu alghayba wala
aqoolulakum innee malakun in attabiAAu illa ma yoohailayya qul hal yastawee
al-aAAma walbaseeruafala tatafakkaroon
Hausa
Ka ce: "Ba zan ce muku, a wurina akwai taskőkin Allah ba. Kuma ba ni sanin
gaibi, kuma ba ni gaya muku cẽwa ni mală'ika ne. Ba ni bi, făce abin da ake yiwo
wahayi zuwa gare ni." Ka ce: "Shin, makăho da mai gani sună daidaita? Shin fa,
ba ku yin tunăni?"
|
Ayah 6:51 الأية
وَأَنذِرْ بِهِ الَّذِينَ يَخَافُونَ أَن يُحْشَرُوا إِلَىٰ رَبِّهِمْ ۙ لَيْسَ
لَهُم مِّن دُونِهِ وَلِيٌّ وَلَا شَفِيعٌ لَّعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ
Waanthir bihi allatheena yakhafoonaan yuhsharoo ila rabbihim laysa lahum min
doonihiwaliyyun wala shafeeAAun laAAallahum yattaqoon
Hausa
Kuma ka yi gargaɗi da shi ga waɗanda suke jin tsőron a tăra su zuwa ga
Ubangijinsu, ba su da wani masőyi baicinSa, kuma babu mai cẽto, tsammăninsu,
sună yin taƙawa.
|
Ayah 6:52 الأية
وَلَا تَطْرُدِ الَّذِينَ يَدْعُونَ رَبَّهُم بِالْغَدَاةِ وَالْعَشِيِّ يُرِيدُونَ
وَجْهَهُ ۖ مَا عَلَيْكَ مِنْ حِسَابِهِم مِّن شَيْءٍ وَمَا مِنْ حِسَابِكَ
عَلَيْهِم مِّن شَيْءٍ فَتَطْرُدَهُمْ فَتَكُونَ مِنَ الظَّالِمِينَ
Wala tatrudi allatheenayadAAoona rabbahum bilghadati walAAashiyyiyureedoona
wajhahu ma AAalayka min hisabihimmin shay-in wama min hisabika AAalayhim
minshay-in fatatrudahum fatakoona mina aththalimeen
Hausa
Kuma kada ka kőri waɗanda suke kiran Ubangijinsu săfe da maraice, sună nufin
yardarSa, babu wani abu daga hisăbinsu a kanka, kuma babu wani abu daga
hisăbinka a kansu, har ka kőre su ka kasance daga azzălumai.
|
Ayah 6:53 الأية
وَكَذَٰلِكَ فَتَنَّا بَعْضَهُم بِبَعْضٍ لِّيَقُولُوا أَهَٰؤُلَاءِ مَنَّ اللهُ
عَلَيْهِم مِّن بَيْنِنَا ۗ أَلَيْسَ اللهُ بِأَعْلَمَ بِالشَّاكِرِينَ
Wakathalika fatanna baAAdahumbibaAAdin liyaqooloo ahaola-i manna AllahuAAalayhim
min baynina alaysa Allahu bi-aAAlama bishshakireen
Hausa
Kuma kamar wannan ne, Muka fitini săshensu da săshe, dőmin su ce: "Shin waɗannan
ne Allah Ya yi falala a kansu daga tsakăninmu?" Shin, Allah bai zama Mafi sani
ba ga măsu gődiya?
|
Ayah 6:54 الأية
وَإِذَا جَاءَكَ الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِآيَاتِنَا فَقُلْ سَلَامٌ عَلَيْكُمْ ۖ
كَتَبَ رَبُّكُمْ عَلَىٰ نَفْسِهِ الرَّحْمَةَ ۖ أَنَّهُ مَنْ عَمِلَ مِنكُمْ
سُوءًا بِجَهَالَةٍ ثُمَّ تَابَ مِن بَعْدِهِ وَأَصْلَحَ فَأَنَّهُ غَفُورٌ
رَّحِيمٌ
Wa-itha jaaka allatheenayu/minoona bi-ayatina faqul salamunAAalaykum kataba
rabbukum AAala nafsihi arrahmataannahu man AAamila minkum soo-an bijahalatin
thumma tabamin baAAdihi waaslaha faannahu ghafoorun raheem
Hausa
Kuma idan waɗanda suke yin ĩmăni da ăyőyinMu suka jẽ maka, sai ka ce: "Aminci ya
tabbata a gareku; Ubangjinku Ya wajabta rahama ga kanSa, cẽwa lalle ne wanda ya
aikata aibi da jăhilci daga cikinku, sa'an nan kuma ya tũba daga băyansa, kuma
ya gyăra, to, lalle Shi, Mai găfara ne, Mai jin ƙai."
|
Ayah 6:55 الأية
وَكَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ الْآيَاتِ وَلِتَسْتَبِينَ سَبِيلُ الْمُجْرِمِينَ
Wakathalika nufassilu al-ayatiwalitastabeena sabeelu almujrimeen
Hausa
Kuma kamar wannan ne Muke bayyana ăyőyi, daki-daki, kuma dőmin hanyar măsu laifi
ta bayyana.
|
Ayah 6:56 الأية
قُلْ إِنِّي نُهِيتُ أَنْ أَعْبُدَ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِ اللهِ ۚ قُل
لَّا أَتَّبِعُ أَهْوَاءَكُمْ ۙ قَدْ ضَلَلْتُ إِذًا وَمَا أَنَا مِنَ
الْمُهْتَدِينَ
Qul innee nuheetu an aAAbuda allatheenatadAAoona min dooni Allahi qul la
attabiAAu ahwaakumqad dalaltu ithan wama ana minaalmuhtadeen
Hausa
Ka ce: "Lalle ne ni, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira daga baicin
Allah." Ka cc: "Ba ni bin son zũciyőyinku, (dőmin in nă yi haka) lalle ne, nă
ɓace. A sa'an nan, kuma ban zama daga shiryayyu ba."
|
Ayah 6:57 الأية
قُلْ إِنِّي عَلَىٰ بَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّي وَكَذَّبْتُم بِهِ ۚ مَا عِندِي مَا
تَسْتَعْجِلُونَ بِهِ ۚ إِنِ الْحُكْمُ إِلَّا لِلَّهِ ۖ يَقُصُّ الْحَقَّ ۖ وَهُوَ
خَيْرُ الْفَاصِلِينَ
Qul innee AAala bayyinatin min rabbeewakaththabtum bihi ma AAindee
matastaAAjiloona bihi ini alhukmu illa lillahiyaqussu alhaqqa wahuwa khayru
alfasileen
Hausa
Ka ce: "Lalle ne ină kan hujja daga Ubangjina, kuma kun ƙaryata (ni) game da
Shi; abin da kuke nẽman gaugăwarsa, bă ya wurina, hukunci kuwa bai zama ba făce,
ga Allah, Yană băyar da lăbărin gaskiya, kuma shĩ ne mafi alhẽrin măsu
rarrabẽwa."
|
Ayah 6:58 الأية
قُل لَّوْ أَنَّ عِندِي مَا تَسْتَعْجِلُونَ بِهِ لَقُضِيَ الْأَمْرُ بَيْنِي
وَبَيْنَكُمْ ۗ وَاللهُ أَعْلَمُ بِالظَّالِمِينَ
Qul law anna AAindee matastaAAjiloona bihi laqudiya al-amru baynee wabaynakum
wallahuaAAlamu biththalimeen
Hausa
Ka ce: "Lalle ne, dă a wurina akwai abin da kuke nẽman gaugăwa da shi, haƙĩƙa dă
an hukunta al'amarin, a tsakănina da tsakăninku, kuma Allah Shĩ ne Mafi sani ga
azzũlumai."
|
Ayah 6:59 الأية
وَعِندَهُ مَفَاتِحُ الْغَيْبِ لَا يَعْلَمُهَا إِلَّا هُوَ ۚ وَيَعْلَمُ مَا فِي
الْبَرِّ وَالْبَحْرِ ۚ وَمَا تَسْقُطُ مِن وَرَقَةٍ إِلَّا يَعْلَمُهَا وَلَا
حَبَّةٍ فِي ظُلُمَاتِ الْأَرْضِ وَلَا رَطْبٍ وَلَا يَابِسٍ إِلَّا فِي كِتَابٍ
مُّبِينٍ
WaAAindahu mafatihu alghaybi layaAAlamuha illa huwa wayaAAlamu ma feealbarri
walbahri wama tasqutu minwaraqatin illa yaAAlamuha wala habbatinfee thulumati
al-ardi wala ratbinwala yabisin illa fee kitabin mubeen
Hausa
Kuma a wurinSa mabũdan gaibi suke, babu wanda yake sanin su făce Shi, kuma Yană
sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya făɗuwa, făce Yă san
shi, kuma băbu wata ƙwăya a cikin duffan ƙasă, kuma babu ɗanye, kuma babu
ƙẽƙasasshe, făce yană a cikin wani Littăfi mai bayyanăwa.
|
Ayah 6:60 الأية
وَهُوَ الَّذِي يَتَوَفَّاكُم بِاللَّيْلِ وَيَعْلَمُ مَا جَرَحْتُم بِالنَّهَارِ
ثُمَّ يَبْعَثُكُمْ فِيهِ لِيُقْضَىٰ أَجَلٌ مُّسَمًّى ۖ ثُمَّ إِلَيْهِ
مَرْجِعُكُمْ ثُمَّ يُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Wahuwa allathee yatawaffakumbillayli wayaAAlamu ma jarahtum binnaharithumma
yabAAathukum feehi liyuqda ajalun musamman thummailayhi marjiAAukum thumma
yunabbi-okum bima kuntumtaAAmaloon
Hausa
Kuma Shĩ ne wanda Yake karɓar răyukanku da dare, kuma Yană sanin abin da kuka
yăga da răna, sa'an nan Yană tăyar da ku a cikinsa, dőmin a hukunta ajali
ambatacce sa'an nan kuma zuwa gare shi makőmarku take, sa'an nan kuma Ya ba ku
lăbari da abin da kuka kasance kună aikatăwa.
|
Ayah 6:61 الأية
وَهُوَ الْقَاهِرُ فَوْقَ عِبَادِهِ ۖ وَيُرْسِلُ عَلَيْكُمْ حَفَظَةً حَتَّىٰ
إِذَا جَاءَ أَحَدَكُمُ الْمَوْتُ تَوَفَّتْهُ رُسُلُنَا وَهُمْ لَا يُفَرِّطُونَ
Wahuwa alqahiru fawqa AAibadihiwayursilu AAalaykum hafathatan hattaitha jaa
ahadakumu almawtu tawaffat-hurusuluna wahum la yufarritoon
Hausa
Kuma Shĩ ne Mai rinjăya bisa ga băyinSa, kuma Yană aikan măsu tsaro a kanku, har
idan mutuwa ta jẽ wa ɗayanku, sai manzanninMu su karɓi ransa alhăli su ba su yin
sakaci.
|
Ayah 6:62 الأية
ثُمَّ رُدُّوا إِلَى اللهِ مَوْلَاهُمُ الْحَقِّ ۚ أَلَا لَهُ الْحُكْمُ وَهُوَ
أَسْرَعُ الْحَاسِبِينَ
Thumma ruddoo ila Allahi mawlahumualhaqqi ala lahu alhukmu wahuwa asraAAu
alhasibeen
Hausa
Sa'an nan kuma a mayar da su zuwa ga Allah Ubangjinsu na gaskiya. To! A gare shi
hukunci yake, kuma Shi ne Mafi gaugăwar măsu bincike.
|
Ayah 6:63 الأية
قُلْ مَن يُنَجِّيكُم مِّن ظُلُمَاتِ الْبَرِّ وَالْبَحْرِ تَدْعُونَهُ تَضَرُّعًا
وَخُفْيَةً لَّئِنْ أَنجَانَا مِنْ هَٰذِهِ لَنَكُونَنَّ مِنَ الشَّاكِرِينَ
Qul man yunajjeekum min thulumatialbarri walbahri tadAAoonahu
tadarruAAanwakhufyatan la-in anjana min hathihilanakoonanna mina ashshakireen
Hausa
Ka ce: "Wane ne Yake tsĩrar da ku daga duhũhuwan tududa ruwa, kună kiran Sa bisa
ga ƙanƙan da kai Kuma a ɓőye: 'Lalle ne idan Ka tsĩrar da mu daga wannan
(masĩfa), haƙĩƙa, muna kasancẽwa daga măsu gődiya?'"
|
Ayah 6:64 الأية
قُلِ اللهُ يُنَجِّيكُم مِّنْهَا وَمِن كُلِّ كَرْبٍ ثُمَّ أَنتُمْ تُشْرِكُونَ
Quli Allahu yunajjeekum minhawamin kulli karbin thumma antum tushrikoon
Hausa
Ka ce: "Allah ne Yake tsĩrar da ku daga gare ta, kuma daga dukan baƙin ciki
sa'an nan kuma ku, kună yin shirki!"
|
Ayah 6:65 الأية
قُلْ هُوَ الْقَادِرُ عَلَىٰ أَن يَبْعَثَ عَلَيْكُمْ عَذَابًا مِّن فَوْقِكُمْ
أَوْ مِن تَحْتِ أَرْجُلِكُمْ أَوْ يَلْبِسَكُمْ شِيَعًا وَيُذِيقَ بَعْضَكُم
بَأْسَ بَعْضٍ ۗ انظُرْ كَيْفَ نُصَرِّفُ الْآيَاتِ لَعَلَّهُمْ يَفْقَهُونَ
Qul huwa alqadiru AAala anyabAAatha AAalaykum AAathaban min fawqikum aw min
tahtiarjulikum aw yalbisakum shiyaAAan wayutheeqa baAAdakumba/sa baAAdin onthur
kayfa nusarrifual-ayati laAAallahum yafqahoon
Hausa
Ka ce: "Shĩ ne Mai ĩko a kan Ya aika da wata azăba a kanku daga bisanku, kő kuwa
daga ƙarƙashin ƙafăfunku, kő kuwa Ya gauraya ku ƙungiyőyi, kuma Ya ɗanɗană wa
săshenku masĩfar săshe." "Ka dũba yadda Muke sarrafa ăyőyi, tsammăninsu sună
fahimta!"
|
Ayah 6:66 الأية
وَكَذَّبَ بِهِ قَوْمُكَ وَهُوَ الْحَقُّ ۚ قُل لَّسْتُ عَلَيْكُم بِوَكِيلٍ
Wakaththaba bihi qawmuka wahuwa alhaqququl lastu AAalaykum biwakeel
Hausa
Kuma mutănenka sun ƙaryata (ka) game da Shi, alhăli kuwa Shi ne gaskiya. Ka ce:
"Nĩban zama wakĩli a kanku ba."
|
Ayah 6:67 الأية
لِّكُلِّ نَبَإٍ مُّسْتَقَرٌّ ۚ وَسَوْفَ تَعْلَمُونَ
Likulli naba-in mustaqarrun wasawfataAAlamoon
Hausa
"Akwai matabbata ga dukan lăbări, kuma ză ku sani."
|
Ayah 6:68 الأية
وَإِذَا رَأَيْتَ الَّذِينَ يَخُوضُونَ فِي آيَاتِنَا فَأَعْرِضْ عَنْهُمْ حَتَّىٰ
يَخُوضُوا فِي حَدِيثٍ غَيْرِهِ ۚ وَإِمَّا يُنسِيَنَّكَ الشَّيْطَانُ فَلَا
تَقْعُدْ بَعْدَ الذِّكْرَىٰ مَعَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ
Wa-itha raayta allatheenayakhoodoona fee ayatina faaAAridAAanhum hatta yakhoodoo
fee hadeethinghayrihi wa-imma yunsiyannaka ashshaytanufala taqAAud baAAda
aththikra maAAaalqawmi aththalimeen
Hausa
Kuma idan kă ga waɗanda suke kũtsawa a cikin ăyőyinMu, to, ka bijire daga gare
su, sai sun kũtsa a cikin wani lăbări waninsa. Kuma imma dai shaiɗan lalle ya
mantar da kai, to, kada ka zauna a bayan tunăwa tăre da mutăne azzălumai.
|
Ayah 6:69 الأية
وَمَا عَلَى الَّذِينَ يَتَّقُونَ مِنْ حِسَابِهِم مِّن شَيْءٍ وَلَٰكِن ذِكْرَىٰ
لَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ
Wama AAala allatheenayattaqoona min hisabihim min shay-in walakinthikra
laAAallahum yattaqoon
Hausa
Kuma babu wani abu daga hisăbinsu (măsu kutsăwa a cikin ayőyin Allah (a kan măsu
taƙawa amma akwai tunătarwa (a kansu), tsămmăninsu (măsu kutsawar) ză su yi
taƙawa.
|
Ayah 6:70 الأية
وَذَرِ الَّذِينَ اتَّخَذُوا دِينَهُمْ لَعِبًا وَلَهْوًا وَغَرَّتْهُمُ الْحَيَاةُ
الدُّنْيَا ۚ وَذَكِّرْ بِهِ أَن تُبْسَلَ نَفْسٌ بِمَا كَسَبَتْ لَيْسَ لَهَا مِن
دُونِ اللهِ وَلِيٌّ وَلَا شَفِيعٌ وَإِن تَعْدِلْ كُلَّ عَدْلٍ لَّا يُؤْخَذْ
مِنْهَا ۗ أُولَٰئِكَ الَّذِينَ أُبْسِلُوا بِمَا كَسَبُوا ۖ لَهُمْ شَرَابٌ مِّنْ
حَمِيمٍ وَعَذَابٌ أَلِيمٌ بِمَا كَانُوا يَكْفُرُونَ
Wathari allatheena ittakhathoodeenahum laAAiban walahwan wagharrat-humu
alhayatuaddunya wathakkir bihi an tubsala nafsunbima kasabat laysa laha min
dooni Allahiwaliyyun wala shafeeAAun wa-in taAAdil kulla AAadlin layu/khath
minha ola-ika allatheenaobsiloo bima kasaboo lahum sharabun min
hameeminwaAAathabun aleemun bima kanoo yakfuroon
Hausa
Kuma ka bar waɗanda suka riƙi addĩninsu abin wăsa da wargi alhăli răyuwar dũniya
tă rũɗe su, kuma ka tunătar game da shi (Alƙur'ăni): Kada a jẽfa raia cikin
halaka sabőda abin da ya tsirfanta; ba shi da wani majiɓinci baicin Allah, kuma
babu wani mai cẽto; kuma, kő ya daidaita dukan fansa, ba ză a karɓa ba daga gare
shi. Waɗancan ne aka yanke wa tsammăni sabőda abin da suka tsirfanta; sună da
wani abin shă daga ruwan zăfi, da wata azăba mai raɗaɗi, sabőda abin da suka
kasance sună yi na kăfirci.
|
Ayah 6:71 الأية
قُلْ أَنَدْعُو مِن دُونِ اللهِ مَا لَا يَنفَعُنَا وَلَا يَضُرُّنَا وَنُرَدُّ
عَلَىٰ أَعْقَابِنَا بَعْدَ إِذْ هَدَانَا اللهُ كَالَّذِي اسْتَهْوَتْهُ
الشَّيَاطِينُ فِي الْأَرْضِ حَيْرَانَ لَهُ أَصْحَابٌ يَدْعُونَهُ إِلَى الْهُدَى
ائْتِنَا ۗ قُلْ إِنَّ هُدَى اللهِ هُوَ الْهُدَىٰ ۖ وَأُمِرْنَا لِنُسْلِمَ
لِرَبِّ الْعَالَمِينَ
Qul anadAAoo min dooni Allahi mala yanfaAAuna wala yadurrunawanuraddu AAala
aAAqabina baAAda ithhadana Allahu kallathee istahwat-huashshayateenu fee al-ardi
hayranalahu as-habun yadAAoonahu ila alhudai/tina qul inna huda Allahi huwa
alhudawaomirna linuslima lirabbi alAAalameen
Hausa
Ka ce: "Shin, ză mu yi kiran abin da bă ya amfăninmu, baicin Allah, kuma bă ya
cũtar damu, kuma a mayar da mu a kan dugăduganmu, a bayan Allah Yă shiryar da mu
kamar wanda shaiɗănu suka kăyar da shi a cikin ƙasa, yană mai ɗĩmuwa, yană da
abőkaisună kiran sa zuwa ga shiriya, 'Ka zo mana'" Kace: "Lalle ne, shiriyar
Allah ita ce shiriya. Kuma an umurce mu, mu sallama wa Ubangijin tălikai."
|
Ayah 6:72 الأية
وَأَنْ أَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَاتَّقُوهُ ۚ وَهُوَ الَّذِي إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ
Waan aqeemoo assalatawattaqoohu wahuwa allathee ilayhi tuhsharoon
Hausa
"Kuma (an ce mana): Ku tsai da salla kuma ku bĩ shi (Allah) da taƙawa kuma Shi
ne wanda Yake zuwa gare Shi ake tăra ku."
|
Ayah 6:73 الأية
وَهُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِالْحَقِّ ۖ وَيَوْمَ يَقُولُ
كُن فَيَكُونُ ۚ قَوْلُهُ الْحَقُّ ۚ وَلَهُ الْمُلْكُ يَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّورِ
ۚ عَالِمُ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ ۚ وَهُوَ الْحَكِيمُ الْخَبِيرُ
Wahuwa allathee khalaqa assamawatiwal-arda bilhaqqi wayawma yaqoolukun fayakoonu
qawluhu alhaqqu walahu almulku yawmayunfakhu fee assoori AAalimu alghaybi
washshahadatiwahuwa alhakeemu alkhabeer
Hausa
Kuma Shĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa da mulkinSa, kuma a Rănar da Yake
cẽwa: "Ka kasance," sai abu ya yi ta kasancẽwa. MaganarSa ce gaskiya, kuma gare
Shi mulki yake a Rănar da ake bũsa a cikin ƙaho. Masanin fake da bayyane ne,
Kuma Shi ne Mai hikima Masani.
|
Ayah 6:74 الأية
وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ لِأَبِيهِ آزَرَ أَتَتَّخِذُ أَصْنَامًا آلِهَةً ۖ
إِنِّي أَرَاكَ وَقَوْمَكَ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Wa-ith qala ibraheemuli-abeehi azara atattakhithu asnaman alihataninnee araka
waqawmaka fee dalalin mubeen
Hausa
Kuma a lőkacin da Ibrăhĩma ya ce wa ubansa Ăzara: "Shin, kană riƙon gumăka
abũbuwan bautăwa? Lalle nĩ, ină ganin ka kai damută- nenka, a cikin ɓata
bayyananniya."
|
Ayah 6:75 الأية
وَكَذَٰلِكَ نُرِي إِبْرَاهِيمَ مَلَكُوتَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَلِيَكُونَ
مِنَ الْمُوقِنِينَ
Wakathalika nuree ibraheemamalakoota assamawati wal-ardiwaliyakoona mina
almooqineen
Hausa
Kuma kamar wancan ne, Muke nũna wa Ibrăhĩma mulkin sammai da ƙasa, kuma dőmin ya
kasance daga măsu yaƙĩni.
|
Ayah 6:76 الأية
فَلَمَّا جَنَّ عَلَيْهِ اللَّيْلُ رَأَىٰ كَوْكَبًا ۖ قَالَ هَٰذَا رَبِّي ۖ
فَلَمَّا أَفَلَ قَالَ لَا أُحِبُّ الْآفِلِينَ
Falamma janna AAalayhi allaylu raakawkaban qala hatha rabbee falamma afala
qalala ohibbu al-afileen
Hausa
To, a lőkacin da dare ya rufe a kansa, ya ga wani taurăro, ya ce: "Wannan ne,
ubangijina?" Sa'an nan a lőkacin da ya faɗi, ya ce: "Ba ni son măsu făɗuwa."
|
Ayah 6:77 الأية
فَلَمَّا رَأَى الْقَمَرَ بَازِغًا قَالَ هَٰذَا رَبِّي ۖ فَلَمَّا أَفَلَ قَالَ
لَئِن لَّمْ يَهْدِنِي رَبِّي لَأَكُونَنَّ مِنَ الْقَوْمِ الضَّالِّينَ
Falamma raa alqamara bazighanqala hatha rabbee falamma afala qalala-in lam
yahdinee rabbee laakoonanna mina alqawmi addalleen
Hausa
Sa'an nan a lőkacin da ya ga wată yană mai bayyana, ya ce: "Wannan ne
Ubangijina?" Sa'an nan a lőkacin da ya făɗi, ya ce: "Lalle ne idan Ubangijina
bai shiryar da ni ba, haƙĩƙa, ină kasancẽwa daga mutăne ɓatattu."
|
Ayah 6:78 الأية
فَلَمَّا رَأَى الشَّمْسَ بَازِغَةً قَالَ هَٰذَا رَبِّي هَٰذَا أَكْبَرُ ۖ
فَلَمَّا أَفَلَتْ قَالَ يَا قَوْمِ إِنِّي بَرِيءٌ مِّمَّا تُشْرِكُونَ
Falamma raa ashshamsabazighatan qala hatha rabbee hathaakbaru falamma afalat
qala ya qawmi inneebaree-on mimma tushrikoon
Hausa
Sa'an nan a lőkacin da ya ga rănă tană bayyana, ya ce: "Wannan shĩ ne
Ubangijina, wannan ne mafi girma?" Sa'an nan a lőkacin da ta făɗi, ya ce: "Ya
mutănena! Lalle ne ni barrantacce nake daga abin da kuke yi na shirki."
|
Ayah 6:79 الأية
إِنِّي وَجَّهْتُ وَجْهِيَ لِلَّذِي فَطَرَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ حَنِيفًا ۖ
وَمَا أَنَا مِنَ الْمُشْرِكِينَ
Innee wajjahtu wajhiya lillathee fataraassamawati wal-arda haneefanwama ana mina
almushrikeen
Hausa
"Lalle ne nĩ, na fuskantar da fuskata ga wanda, Ya ƙăga halittar sammai da ƙasa,
ină mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bă ni cikin măsu shirki."
|
Ayah 6:80 الأية
وَحَاجَّهُ قَوْمُهُ ۚ قَالَ أَتُحَاجُّونِّي فِي اللهِ وَقَدْ هَدَانِ ۚ وَلَا
أَخَافُ مَا تُشْرِكُونَ بِهِ إِلَّا أَن يَشَاءَ رَبِّي شَيْئًا ۗ وَسِعَ رَبِّي
كُلَّ شَيْءٍ عِلْمًا ۗ أَفَلَا تَتَذَكَّرُونَ
Wahajjahu qawmuhu qala atuhajjoonneefee Allahi waqad hadani wala akhafu
matushrikoona bihi illa an yashaa rabbee shay-anwasiAAa rabbee kulla shay-in
AAilman afala tatathakkaroon
Hausa
Kuma mutănensa suka yi musu da shi. Ya ce: "Shin kună musu da ni a cikin
sha'anin Allah, alhăli kuwa Yă shiryai da ni? Kuma bă ni tsőron abin da kuke yin
shirki da shi, făce idan Ubangijina Yă so wani abu. Ubangijina Ya yalwaci dukkan
kőme da ilmi. Shin, ba ză ku yi tunăni ba?"
|
Ayah 6:81 الأية
وَكَيْفَ أَخَافُ مَا أَشْرَكْتُمْ وَلَا تَخَافُونَ أَنَّكُمْ أَشْرَكْتُم
بِاللهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِهِ عَلَيْكُمْ سُلْطَانًا ۚ فَأَيُّ الْفَرِيقَيْنِ
أَحَقُّ بِالْأَمْنِ ۖ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Wakayfa akhafu ma ashraktumwala takhafoona annakum ashraktum billahima lam
yunazzil bihi AAalaykum sultanan faayyualfareeqayni ahaqqu bil-amni in kuntum
taAAlamoon
Hausa
"Kuma yăyă nake jin tsőron abin da kuka yi shirki da shi, kuma ba ku tsőron cẽwa
lalle ne kũ, kun yi shirki da Allah, abin da (Allah) bai saukar da wata hujja ba
game da shi? To, wane ɓangare daga săshen biyu ne mafi cancanta da aminci, idan
kun kasance kună sani?"
|
Ayah 6:82 الأية
الَّذِينَ آمَنُوا وَلَمْ يَلْبِسُوا إِيمَانَهُم بِظُلْمٍ أُولَٰئِكَ لَهُمُ
الْأَمْنُ وَهُم مُّهْتَدُونَ
Allatheena amanoo walamyalbisoo eemanahum bithulmin ola-ikalahumu al-amnu wahum
muhtadoon
Hausa
"Waɗanda suka yi ĩmăni, kuma ba su gauraya ĩmăninsu da zălunci ba, waɗannan sună
da aminci, kuma sũ ne shiryayyu."
|
Ayah 6:83 الأية
وَتِلْكَ حُجَّتُنَا آتَيْنَاهَا إِبْرَاهِيمَ عَلَىٰ قَوْمِهِ ۚ نَرْفَعُ
دَرَجَاتٍ مَّن نَّشَاءُ ۗ إِنَّ رَبَّكَ حَكِيمٌ عَلِيمٌ
Watilka hujjatuna ataynahaibraheema AAala qawmihi narfaAAu darajatinman nashao
inna rabbaka hakeemun AAaleem
Hausa
Kuma waccan ita ce hujjarMu, Mun bayăr da ita ga Ibrăhĩma a kan mutănensa. Mună
ɗaukaka wanda Muka so da darajőji. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani.
|
Ayah 6:84 الأية
وَوَهَبْنَا لَهُ إِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ ۚ كُلًّا هَدَيْنَا ۚ وَنُوحًا هَدَيْنَا
مِن قَبْلُ ۖ وَمِن ذُرِّيَّتِهِ دَاوُودَ وَسُلَيْمَانَ وَأَيُّوبَ وَيُوسُفَ
وَمُوسَىٰ وَهَارُونَ ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ
Wawahabna lahu ishaqawayaAAqooba kullan hadayna wanoohan hadaynamin qablu wamin
thurriyyatihi dawooda wasulaymanawaayyooba wayoosufa wamoosa waharoona
wakathalikanajzee almuhsineen
Hausa
Kuma Muka bă shi Is'hăƙa da Yăƙubu, dukansu Mun shiryar, kuma Nũhu Mun shiryar
da shi a gabăni, kuma daga zuriyarsa akwai Dăwũda da Sulaimănu da Ayyũba, da
Yũsufu da Mũsă da Hărũna, kuma kamar wancan ne Muke săka wa măsu kyautatăwa.
|
Ayah 6:85 الأية
وَزَكَرِيَّا وَيَحْيَىٰ وَعِيسَىٰ وَإِلْيَاسَ ۖ كُلٌّ مِّنَ الصَّالِحِينَ
Wazakariyya wayahyawaAAeesa walyasa kullun mina assaliheen
Hausa
Da Zakariyya da Yahaya da Isa da Ilyasu dukansu daga sălihai suke.
|
Ayah 6:86 الأية
وَإِسْمَاعِيلَ وَالْيَسَعَ وَيُونُسَ وَلُوطًا ۚ وَكُلًّا فَضَّلْنَا عَلَى
الْعَالَمِينَ
Wa-ismaAAeela walyasaAAawayoonusa walootan wakullan faddalna AAalaalAAalameen
Hausa
Da Ismă'la da Ilyasa, a da Yũnusa da Luɗu, kuma dukansu Mun fĩfĩtă su a kan
tălikai.
|
Ayah 6:87 الأية
وَمِنْ آبَائِهِمْ وَذُرِّيَّاتِهِمْ وَإِخْوَانِهِمْ ۖ وَاجْتَبَيْنَاهُمْ
وَهَدَيْنَاهُمْ إِلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Wamin aba-ihim wathurriyyatihimwa-ikhwanihim wajtabaynahum wahadaynahumila
siratin mustaqeem
Hausa
Kuma daga ubanninsu, da zũriyarsu, da 'yan'uwansu, kuma Muka zăɓe su, kuma Muka
shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.
|
Ayah 6:88 الأية
ذَٰلِكَ هُدَى اللهِ يَهْدِي بِهِ مَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ ۚ وَلَوْ
أَشْرَكُوا لَحَبِطَ عَنْهُم مَّا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Thalika huda Allahiyahdee bihi man yashao min AAibadihi walaw ashrakoolahabita
AAanhum ma kanoo yaAAmaloon
Hausa
Wancan ne shiryarwar Allah, Yană shiryar da wanda Yake so daga bayinSa. Kuma dă
sun yi shirki dă haƙĩƙa abin da suka kasance sună ,aikatăwa yă lălăce.
|
Ayah 6:89 الأية
أُولَٰئِكَ الَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ ۚ فَإِن
يَكْفُرْ بِهَا هَٰؤُلَاءِ فَقَدْ وَكَّلْنَا بِهَا قَوْمًا لَّيْسُوا بِهَا
بِكَافِرِينَ
Ola-ika allatheena ataynahumualkitaba walhukma wannubuwwatafa-in yakfur biha
haola-i faqad wakkalnabiha qawman laysoo biha bikafireen
Hausa
Waɗancan ne waɗanda Muka bai wa Littăfi da hukunci da Annabci. To idan waɗannan
(mutăne ) sun kăfirta da ita, to, haƙĩƙa, Mun wakkala wasu mutăne gare ta, ba su
zama game da ita kăfirai ba.
|
Ayah 6:90 الأية
أُولَٰئِكَ الَّذِينَ هَدَى اللهُ ۖ فَبِهُدَاهُمُ اقْتَدِهْ ۗ قُل لَّا
أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ أَجْرًا ۖ إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرَىٰ لِلْعَالَمِينَ
Ola-ika allatheena hadaAllahu fabihudahumu iqtadih qul la as-alukumAAalayhi
ajran in huwa illa thikra lilAAalameen
Hausa
Waɗancan ne Allah Ya shiryar, sabőda haka ka yi kőyi da shiryarsu. Ka ce: "Ba ni
tambayar ku wata ijăra. Shĩ (Alƙur'ăni) bai zama ba făce tunătarwa ga tălikai."
|
Ayah 6:91 الأية
وَمَا قَدَرُوا اللهَ حَقَّ قَدْرِهِ إِذْ قَالُوا مَا أَنزَلَ اللهُ عَلَىٰ
بَشَرٍ مِّن شَيْءٍ ۗ قُلْ مَنْ أَنزَلَ الْكِتَابَ الَّذِي جَاءَ بِهِ مُوسَىٰ
نُورًا وَهُدًى لِّلنَّاسِ ۖ تَجْعَلُونَهُ قَرَاطِيسَ تُبْدُونَهَا وَتُخْفُونَ
كَثِيرًا ۖ وَعُلِّمْتُم مَّا لَمْ تَعْلَمُوا أَنتُمْ وَلَا آبَاؤُكُمْ ۖ قُلِ
اللهُ ۖ ثُمَّ ذَرْهُمْ فِي خَوْضِهِمْ يَلْعَبُونَ
Wama qadaroo Allaha haqqaqadrihi ith qaloo ma anzala AllahuAAala basharin min
shay-in qul man anzala alkitabaallathee jaa bihi moosa nooran wahudan
linnasitajAAaloonahu qarateesa tubdoonaha watukhfoonakatheeran waAAullimtum ma
lam taAAlamoo antum wala abaokumquli Allahu thumma tharhum fee
khawdihimyalAAaboon
Hausa
Kuma ba su ƙaddara Allah a kan hakkin ƙaddara shi ba, a lőkacin da suka ce:
"Allah bai saukar da kőme ba ga wani mutum." Ka ce: "Wăne ne ya saukar da
Littăfi wanda Mũsă ya zo da shi, yană haske da shiriya ga mutăne, kună sanya shi
takardu, kũna bayyana su, kuma kună ɓőye mai yawa, kuma an sanar da ku abin da
ba ku sani ba, ku da ubanninku?" Ka ce: "Allah," sa'an nan ka bar su a cikin
sharhőliyarsu sună wăsă.
|
Ayah 6:92 الأية
وَهَٰذَا كِتَابٌ أَنزَلْنَاهُ مُبَارَكٌ مُّصَدِّقُ الَّذِي بَيْنَ يَدَيْهِ
وَلِتُنذِرَ أُمَّ الْقُرَىٰ وَمَنْ حَوْلَهَا ۚ وَالَّذِينَ يُؤْمِنُونَ
بِالْآخِرَةِ يُؤْمِنُونَ بِهِ ۖ وَهُمْ عَلَىٰ صَلَاتِهِمْ يُحَافِظُونَ
Wahatha kitabun anzalnahumubarakun musaddiqu allathee bayna yadayhiwalitunthira
omma alqura waman hawlahawallatheena yu/minoona bil-akhiratiyu/minoona bihi
wahum AAala salatihim yuhafithoon
Hausa
Kuma wannan Littăfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, mai gaskata wanda
yake a gabansa ne, kuma dőmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda
yake gefenta. Kuma waɗanda suke yin ĩmăni da Lăhira sună ĩmăni da shi
(Alƙur'ăni), kuma sũ, a kan sallarsu, sună tsarẽwa.
|
Ayah 6:93 الأية
وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَىٰ عَلَى اللهِ كَذِبًا أَوْ قَالَ أُوحِيَ
إِلَيَّ وَلَمْ يُوحَ إِلَيْهِ شَيْءٌ وَمَن قَالَ سَأُنزِلُ مِثْلَ مَا أَنزَلَ
اللهُ ۗ وَلَوْ تَرَىٰ إِذِ الظَّالِمُونَ فِي غَمَرَاتِ الْمَوْتِ
وَالْمَلَائِكَةُ بَاسِطُو أَيْدِيهِمْ أَخْرِجُوا أَنفُسَكُمُ ۖ الْيَوْمَ
تُجْزَوْنَ عَذَابَ الْهُونِ بِمَا كُنتُمْ تَقُولُونَ عَلَى اللهِ غَيْرَ
الْحَقِّ وَكُنتُمْ عَنْ آيَاتِهِ تَسْتَكْبِرُونَ
Waman athlamu mimmani iftaraAAala Allahi kathiban aw qala oohiyailayya walam
yooha ilayhi shay-on waman qalasaonzilu mithla ma anzala Allahu walaw taraithi
aththalimoona fee ghamaratialmawti walmala-ikatu basitooaydeehim akhrijoo
anfusakumu alyawma tujzawna AAathabaalhooni bima kuntum taqooloona AAala
Allahighayra alhaqqi wakuntum AAan ayatihitastakbiroon
Hausa
Kuma wăne ne mafi zălunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kő kuwa ya ce:
"An yi wahayi zuwa gare ni," alhăli kuwa ba a yi wahayin kőme ba zuwa gare shi,
da wanda ya ce: "zan saukar da misălin abin da Allah Ya saukar?" Kuma dă kă
gani, a lőkacin da azzălumai suke cikin măyen mutuwa, kuma mală'iku sună măsu
shimfiɗa hannuwansu, (sună ce musu) "Ku fitar da kanku; a yau ană săka muku da
azăbar wulăƙanci sabőda abin da kuka kasance kună faɗa, wanin gaskiya, ga Allah
kuma kun kasance daga ăyőyinSa kună yin girman kai."
|
Ayah 6:94 الأية
وَلَقَدْ جِئْتُمُونَا فُرَادَىٰ كَمَا خَلَقْنَاكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍ وَتَرَكْتُم
مَّا خَوَّلْنَاكُمْ وَرَاءَ ظُهُورِكُمْ ۖ وَمَا نَرَىٰ مَعَكُمْ شُفَعَاءَكُمُ
الَّذِينَ زَعَمْتُمْ أَنَّهُمْ فِيكُمْ شُرَكَاءُ ۚ لَقَد تَّقَطَّعَ بَيْنَكُمْ
وَضَلَّ عَنكُم مَّا كُنتُمْ تَزْعُمُونَ
Walaqad ji/tumoona furadakama khalaqnakum awwala marratin wataraktum
makhawwalnakum waraa thuhoorikum wamanara maAAakum shufaAAaakumu
allatheenazaAAamtum annahum feekum shurakao laqad taqattaAAabaynakum wadalla
AAankum ma kuntum tazAAumoon
Hausa
Kuma lalle ne haƙĩƙa, kun zo Mana ɗai ɗai, kamar yadda Muka halittă ku a farkon
lőkaci. Kuma kun bar abin da Muka mallaka muku a bayan bayayyakinku, kuma ba Mu
gani a tăre da kũ ba, macẽtanku waɗanda kuka riya cẽwa lalle ne sũ, a cikinku
măsu tărayya ne. Lalle ne, hăƙĩƙa,kőme yă yanyanke a tsakăninku, kuma abin da
kuka kasance kună riyăwa ya ɓace daga gare ku.
|
Ayah 6:95 الأية
إِنَّ اللهَ فَالِقُ الْحَبِّ وَالنَّوَىٰ ۖ يُخْرِجُ الْحَيَّ مِنَ الْمَيِّتِ
وَمُخْرِجُ الْمَيِّتِ مِنَ الْحَيِّ ۚ ذَٰلِكُمُ اللهُ ۖ فَأَنَّىٰ تُؤْفَكُونَ
Inna Allaha faliqu alhabbiwannawa yukhriju alhayya mina almayyitiwamukhriju
almayyiti mina alhayyi thalikumu Allahufaanna tu/fakoon
Hausa
Lalle ne, Allah ne Mai tsăgewar ƙwăyar hatsi da kwalfar gurtsu. Yană fitar da
mai rai daga mamaci, kuma (Shi) Mai fitar da mamaci ne daga mai rai, wannan ne
Allah. To, yăya ake karkatar da ku?
|
Ayah 6:96 الأية
فَالِقُ الْإِصْبَاحِ وَجَعَلَ اللَّيْلَ سَكَنًا وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ
حُسْبَانًا ۚ ذَٰلِكَ تَقْدِيرُ الْعَزِيزِ الْعَلِيمِ
Faliqu al-isbahiwajaAAala allayla sakanan washshamsa walqamara husbananthalika
taqdeeru alAAazeezi alAAaleem
Hausa
Mai tsăgẽwar săfiya, kuma Ya sanya dare mai natsuwa, kuma da răna da wată a bisa
lissăfi. vwannan ne ƙaddarăwar Mabuwăyi Masani.
|
Ayah 6:97 الأية
وَهُوَ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ النُّجُومَ لِتَهْتَدُوا بِهَا فِي ظُلُمَاتِ
الْبَرِّ وَالْبَحْرِ ۗ قَدْ فَصَّلْنَا الْآيَاتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ
Wahuwa allathee jaAAala lakumu annujoomalitahtadoo biha fee thulumati
albarriwalbahri qad fassalna al-ayatiliqawmin yaAAlamoon
Hausa
Kuma Shi ne Ya sanya muku taurări dőmin ku shiryu da su a cikin duffan tudu da
ruwa. Lalle ne Mun bayyana ăyőyi daki-daki, ga mutăne waɗanda suke sani.
|
Ayah 6:98 الأية
وَهُوَ الَّذِي أَنشَأَكُم مِّن نَّفْسٍ وَاحِدَةٍ فَمُسْتَقَرٌّ وَمُسْتَوْدَعٌ ۗ
قَدْ فَصَّلْنَا الْآيَاتِ لِقَوْمٍ يَفْقَهُونَ
Wahuwa allathee anshaakum min nafsinwahidatin famustaqarrun wamustawdaAAun qad
fassalnaal-ayati liqawmin yafqahoon
Hausa
Kuma Shi ne Ya ƙăga halittarku daga rai guda, sa'an nan da mai tabbata da wanda
ake ajẽwa. Lalle ne Mun bayyană ăyőyi daki-daki, ga mutăne waɗanda suke fahimta.
|
Ayah 6:99 الأية
وَهُوَ الَّذِي أَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَخْرَجْنَا بِهِ نَبَاتَ كُلِّ
شَيْءٍ فَأَخْرَجْنَا مِنْهُ خَضِرًا نُّخْرِجُ مِنْهُ حَبًّا مُّتَرَاكِبًا وَمِنَ
النَّخْلِ مِن طَلْعِهَا قِنْوَانٌ دَانِيَةٌ وَجَنَّاتٍ مِّنْ أَعْنَابٍ
وَالزَّيْتُونَ وَالرُّمَّانَ مُشْتَبِهًا وَغَيْرَ مُتَشَابِهٍ ۗ انظُرُوا إِلَىٰ
ثَمَرِهِ إِذَا أَثْمَرَ وَيَنْعِهِ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكُمْ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ
يُؤْمِنُونَ
Wahuwa allathee anzala mina assama-imaan faakhrajna bihi nabata kulli
shay-infaakhrajna minhu khadiran nukhriju minhu habbanmutarakiban wamina
annakhli min talAAihaqinwanun daniyatun wajannatin min aAAnabinwazzaytoona
warrummana mushtabihanwaghayra mutashabihin onthuroo ilathamarihi itha athmara
wayanAAihi inna fee thalikumlaayatin liqawmin yu/minoon
Hausa
Kuma Shi ne Ya saukar da ruwa daga sama, Muka fitar da tsiron dukkan kőme game
dă shi, sa'an nan Muka fitar da kőre daga gare shi, Muna fitar da kwăya
ɗamfararriya daga gare shi (kőren), kuma daga dabĩno daga hirtsinta akwai
dumbuje-dumbuje makusanta, kuma (Muka fitar) da gőnaki na inabőbi da zăitũni da
rummăni, măsu kamă da jũna da wasun măsu kama da jũna. Ku dũba zuwa 'ya'yan
ităcensa, idan ya yi 'ya'yan, da nunarsa. Lalle ne a cikin wannan akwai ăyőyi ga
waɗanda suke yin ĩmăni.
|
Ayah 6:100 الأية
وَجَعَلُوا لِلَّهِ شُرَكَاءَ الْجِنَّ وَخَلَقَهُمْ ۖ وَخَرَقُوا لَهُ بَنِينَ
وَبَنَاتٍ بِغَيْرِ عِلْمٍ ۚ سُبْحَانَهُ وَتَعَالَىٰ عَمَّا يَصِفُونَ
WajaAAaloo lillahi shurakaaaljinna wakhalaqahum wakharaqoo lahu baneena
wabanatinbighayri AAilmin subhanahu wataAAala AAammayasifoon
Hausa
Kuma suka sanya wa Allah abőkan tărayya, aljannu, alhăli kuwa (Shi) Ya halitta
su. Kuma sun ƙirƙira masa ɗiya da 'yă'ya, bă da ilmi ba. TsarkinSa yă tabbata!
Kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke sifantăwa.
|
Ayah 6:101 الأية
بَدِيعُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ أَنَّىٰ يَكُونُ لَهُ وَلَدٌ وَلَمْ تَكُن
لَّهُ صَاحِبَةٌ ۖ وَخَلَقَ كُلَّ شَيْءٍ ۖ وَهُوَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ
BadeeAAu assamawatiwal-ardi anna yakoonu lahu waladun walamtakun lahu sahibatun
wakhalaqa kulla shay-in wahuwabikulli shay-in AAaleem
Hausa
Mafarin halittar sammai da ƙasa. Yăya ɗă zai zama a gare Shi alhăli kuwa măta ba
ta kasance ba, a gare Shi, kuma Ya halitta dukkan, kőme, kuma Shĩ, game da dukan
kőme, Masani ne?
|
Ayah 6:102 الأية
ذَٰلِكُمُ اللهُ رَبُّكُمْ ۖ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ۖ خَالِقُ كُلِّ شَيْءٍ
فَاعْبُدُوهُ ۚ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ وَكِيلٌ
Thalikumu Allahu rabbukum lailaha illa huwa khaliqu kulli shay-in
faAAbudoohuwahuwa AAala kulli shay-in wakeel
Hausa
Wancan ne Allah Ubangijinku. Băbu wani abin bautăwa făce Shĩ, Mahaliccin dukan
kőme. Sabőda haka ku bauta Masa kuma Shi ne wakĩli a kan dukan, kőme.
|
Ayah 6:103 الأية
لَّا تُدْرِكُهُ الْأَبْصَارُ وَهُوَ يُدْرِكُ الْأَبْصَارَ ۖ وَهُوَ اللَّطِيفُ
الْخَبِيرُ
La tudrikuhu al-absaru wahuwayudriku al-absara wahuwa allateefu alkhabeer
Hausa
Gannai bă su iya riskuwarSa, kuma Shĩ Yană riskuwar gannai, kuma Shĩ ne Mai
tausasăwa,Masani.
|
Ayah 6:104 الأية
قَدْ جَاءَكُم بَصَائِرُ مِن رَّبِّكُمْ ۖ فَمَنْ أَبْصَرَ فَلِنَفْسِهِ ۖ وَمَنْ
عَمِيَ فَعَلَيْهَا ۚ وَمَا أَنَا عَلَيْكُم بِحَفِيظٍ
Qad jaakum basa-iru minrabbikum faman absara falinafsihi waman AAamiya
faAAalayhawama ana AAalaykum bihafeeth
Hausa
Lalle ne abũbuwan lũra sun je muku daga Ubangijinku, to, wanda ya kula, to,
dőmin kansa, kuma wanda ya makanta, to, laifi yană a kansa, kuma nĩ, a kanku, bă
mai tsaro ba ne.
|
Ayah 6:105 الأية
وَكَذَٰلِكَ نُصَرِّفُ الْآيَاتِ وَلِيَقُولُوا دَرَسْتَ وَلِنُبَيِّنَهُ لِقَوْمٍ
يَعْلَمُونَ
Wakathalika nusarrifu al-ayatiwaliyaqooloo darasta walinubayyinahu liqawmin
yaAAlamoon
Hausa
Kamar wannan ne Muke sarrafa ăyőyi, kuma dőmin su ce: "Kă karanta!" Kuma dőmin
Mu bayyana shi ga mutăne waɗanda sună sani.
|
Ayah 6:106 الأية
اتَّبِعْ مَا أُوحِيَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ ۖ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ۖ
وَأَعْرِضْ عَنِ الْمُشْرِكِينَ
IttabiAA ma oohiya ilayka minrabbika la ilaha illa huwa waaAAridAAani
almushrikeen
Hausa
Ka bi abin da aka yi wahayi zuwa gare ka daga Ubangijinka; babu wani abin
bautăwa făce Shi, kuma ka bijire daga măsu shirki.
|
Ayah 6:107 الأية
وَلَوْ شَاءَ اللهُ مَا أَشْرَكُوا ۗ وَمَا جَعَلْنَاكَ عَلَيْهِمْ حَفِيظًا ۖ
وَمَا أَنتَ عَلَيْهِم بِوَكِيلٍ
Walaw shaa Allahu maashrakoo wama jaAAalnaka AAalayhim hafeethanwama anta
AAalayhim biwakeel
Hausa
Kuma dă Allah Yă so, dă ba su yi shirki ba, kuma ba Mu, sanya ka mai tsaro a
kansu ba, kuma ba kai ne wakĩli a kansu ba.
|
Ayah 6:108 الأية
وَلَا تَسُبُّوا الَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِ اللهِ فَيَسُبُّوا اللهَ
عَدْوًا بِغَيْرِ عِلْمٍ ۗ كَذَٰلِكَ زَيَّنَّا لِكُلِّ أُمَّةٍ عَمَلَهُمْ ثُمَّ
إِلَىٰ رَبِّهِم مَّرْجِعُهُمْ فَيُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Wala tasubboo allatheenayadAAoona min dooni Allahi fayasubboo AllahaAAadwan
bighayri AAilmin kathalika zayyanna likulliommatin AAamalahum thumma ila
rabbihim marjiAAuhumfayunabbi-ohum bima kanoo yaAAmaloon
Hausa
Kuma kada ku zăgi waɗanda suke kira, baicin Allah, har su zăgi Allah bisa
zălunci, ba, da ilmi ba. Kamar wannan ne Muka ƙawăta ga kőwace al'umma aikinsu,
sa'an nan zuwa ga Ubangijinsu makőmarsu take, sa'an nan Ya ba su lăbari da abin
da suka kasance sună aikatăwa.
|
Ayah 6:109 الأية
وَأَقْسَمُوا بِاللهِ جَهْدَ أَيْمَانِهِمْ لَئِن جَاءَتْهُمْ آيَةٌ
لَّيُؤْمِنُنَّ بِهَا ۚ قُلْ إِنَّمَا الْآيَاتُ عِندَ اللهِ ۖ وَمَا
يُشْعِرُكُمْ أَنَّهَا إِذَا جَاءَتْ لَا يُؤْمِنُونَ
Waaqsamoo billahi jahda aymanihimla-in jaat-hum ayatun layu/minunna biha
qulinnama al-ayatu AAinda Allahi wamayushAAirukum annaha itha jaat layu/minoon
Hausa
Kuma suka yi rantsuwa da Allah iyakar rantsuwőyinsu (cẽwa) lalle ne idan wata
ăyă ta jẽmusu, haƙĩƙa, sună yin ĩmăni da ita. Ka ce: "Abin sani kawai, ăyőyi a
wurin Allah suke. Kuma mẽne nezai sanya ku ku sansance cẽwa,lalle ne su, idan
ăyőyin sun je, ba ză su yi ĩmăni ba?"
|
Ayah 6:110 الأية
وَنُقَلِّبُ أَفْئِدَتَهُمْ وَأَبْصَارَهُمْ كَمَا لَمْ يُؤْمِنُوا بِهِ أَوَّلَ
مَرَّةٍ وَنَذَرُهُمْ فِي طُغْيَانِهِمْ يَعْمَهُونَ
Wanuqallibu af-idatahum waabsarahumkama lam yu/minoo bihi awwala marratin
wanatharuhumfee tughyanihim yaAAmahoon
Hausa
Kuma Mună jujjũya zukătansu da ganansu, kamar yadda ba su yi ĩmăni da shi ba a
farkon lőkaci kuma Mună barin su a cikin kũtsăwarsu, sună ɗĩmuwa.
|
Ayah 6:111 الأية
وَلَوْ أَنَّنَا نَزَّلْنَا إِلَيْهِمُ الْمَلَائِكَةَ وَكَلَّمَهُمُ الْمَوْتَىٰ
وَحَشَرْنَا عَلَيْهِمْ كُلَّ شَيْءٍ قُبُلًا مَّا كَانُوا لِيُؤْمِنُوا إِلَّا أَن
يَشَاءَ اللهُ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ يَجْهَلُونَ
Walaw annana nazzalnailayhimu almala-ikata wakallamahumu almawta
wahasharnaAAalayhim kulla shay-in qubulan ma kanoo liyu/minooilla an yashaa
Allahu walakinnaaktharahum yajhaloon
Hausa
Kuma dă a ce, lalle Mũ Mun saukar da Mală'iku zuwa gare su, kuma matattu suka yi
musu magana, kuma Muka tăra dukkan kőme a kansu, gungu-gungu, ba su kasance sună
iya yin ĩmăni ba, sai fa idan Allah Yă so, Kuma amma mafi yawansu sună jăhiltar
haka.
|
Ayah 6:112 الأية
وَكَذَٰلِكَ جَعَلْنَا لِكُلِّ نَبِيٍّ عَدُوًّا شَيَاطِينَ الْإِنسِ وَالْجِنِّ
يُوحِي بَعْضُهُمْ إِلَىٰ بَعْضٍ زُخْرُفَ الْقَوْلِ غُرُورًا ۚ وَلَوْ شَاءَ
رَبُّكَ مَا فَعَلُوهُ ۖ فَذَرْهُمْ وَمَا يَفْتَرُونَ
Wakathalika jaAAalna likullinabiyyin AAaduwwan shayateena al-insi waljinni
yooheebaAAduhum ila baAAdin zukhrufa alqawlighurooran walaw shaa rabbuka ma
faAAaloohu fatharhumwama yaftaroon
Hausa
Kuma kamar wancan ne Muka sanya wa kőwane Annabi maƙiyi; shaiɗănun mutăne da
aljannu, săshensu yană yin ishăra zuwa săshe da ƙawătaccen zance bisa ga rũɗi.
Kuma dă Ubangijinka Yă so, dă ba su aikată shi ba, don haka ka bar su da abin
da, suke ƙirƙirăwa.
|
Ayah 6:113 الأية
وَلِتَصْغَىٰ إِلَيْهِ أَفْئِدَةُ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ
وَلِيَرْضَوْهُ وَلِيَقْتَرِفُوا مَا هُم مُّقْتَرِفُونَ
Walitasgha ilayhi af-idatuallatheena la yu/minoona bil-akhiratiwaliyardawhu
waliyaqtarifoo ma hum muqtarifoon
Hausa
Kuma dőmin zukătan waɗanda ba su yi ĩmăni da Lăhira ba su karkata saurărẽ zuwa
gareshi, kuma dőmin su yarda da shi, kuma dőmin su kamfaci abin da suke măsu
kamfata.
|
Ayah 6:114 الأية
أَفَغَيْرَ اللهِ أَبْتَغِي حَكَمًا وَهُوَ الَّذِي أَنزَلَ إِلَيْكُمُ
الْكِتَابَ مُفَصَّلًا ۚ وَالَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ يَعْلَمُونَ أَنَّهُ
مُنَزَّلٌ مِّن رَّبِّكَ بِالْحَقِّ ۖ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ الْمُمْتَرِينَ
Afaghayra Allahi abtaghee hakamanwahuwa allathee anzala ilaykumu alkitaba
mufassalanwallatheena ataynahumu alkitabayaAAlamoona annahu munazzalun min
rabbika bilhaqqifala takoonanna mina almumtareen
Hausa
Shin fa, wanin Allah nake nẽma ya zama mai hukunci, alhăli kuwa Shĩ ne wanda Ya
saukar muku da Littăfi abin rabẽwadaki-daki? Kuma waɗanda Muka bai wa Littăfi
sună sanin cẽwa lalleshi (Alƙur'ăni) abin saukarwa ne daga Ubangijinka, da
gaskiya? Sabőda haka kada ku kasance daga măsu shakka.
|
Ayah 6:115 الأية
وَتَمَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ صِدْقًا وَعَدْلًا ۚ لَّا مُبَدِّلَ لِكَلِمَاتِهِ ۚ
وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Watammat kalimatu rabbika sidqanwaAAadlan la mubaddila likalimatihi wahuwa
assameeAAualAAaleem
Hausa
Kuma kalmar Ubangijinka tă cika, tană gaskiya da ădalci. Babu mai musanyăwa ga
kalmőminSa, kuma Shi ne Maiji, Masani.
|
Ayah 6:116 الأية
وَإِن تُطِعْ أَكْثَرَ مَن فِي الْأَرْضِ يُضِلُّوكَ عَن سَبِيلِ اللهِ ۚ إِن
يَتَّبِعُونَ إِلَّا الظَّنَّ وَإِنْ هُمْ إِلَّا يَخْرُصُونَ
Wa-in tutiAA akthara man fee al-ardiyudillooka AAan sabeeli Allahi in
yattabiAAoona illaaththanna wa-in hum illa yakhrusoon
Hausa
Kuma idan ka bi mafiya yawan waɗanda suke a cikin ƙasa da ɗă'a sună ɓatar da kai
daga hanyar Allah. Ba su bin kőme sai făce ƙaddari-faɗi suke yi.
|
Ayah 6:117 الأية
إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ مَن يَضِلُّ عَن سَبِيلِهِ ۖ وَهُوَ أَعْلَمُ
بِالْمُهْتَدِينَ
Inna rabbaka huwa aAAlamu man yadilluAAan sabeelihi wahuwa aAAlamu bilmuhtadeen
Hausa
Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga wanda yake ɓacẽwa daga hanyarsa kuma
Shi ne mafi sani ga masu shiryuwa.
|
|