1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
ن ۚ وَالْقَلَمِ وَمَا يَسْطُرُونَ
Noon walqalami wama yasturoon
Hausa
Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa.
|
Ayah 68:2 الأية
مَا أَنتَ بِنِعْمَةِ رَبِّكَ بِمَجْنُونٍ
Ma anta biniAAmati rabbika bimajnoon
Hausa
Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba.
|
Ayah 68:3 الأية
وَإِنَّ لَكَ لَأَجْرًا غَيْرَ مَمْنُونٍ
Wa-inna laka laajran ghayra mamnoon
Hausa
Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa.
|
Ayah 68:4 الأية
وَإِنَّكَ لَعَلَىٰ خُلُقٍ عَظِيمٍ
Wa-innaka laAAala khuluqin AAatheem
Hausa
Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya.
|
Ayah 68:5 الأية
فَسَتُبْصِرُ وَيُبْصِرُونَ
Fasatubsiru wayubsiroon
Hausa
Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani.
|
Ayah 68:6 الأية
بِأَييِّكُمُ الْمَفْتُونُ
Bi-ayyikumu almaftoon
Hausa
Ga wanenku haukã take.
|
Ayah 68:7 الأية
إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِ وَهُوَ أَعْلَمُ
بِالْمُهْتَدِينَ
Inna rabbaka huwa aAAlamu biman dallaAAan sabeelihi wahuwa aAAlamu bilmuhtadeen
Hausa
Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne
Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
|
Ayah 68:8 الأية
فَلَا تُطِعِ الْمُكَذِّبِينَ
Fala tutiAAi almukaththibeen
Hausa
Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa.
|
Ayah 68:9 الأية
وَدُّوا لَوْ تُدْهِنُ فَيُدْهِنُونَ
Waddoo law tudhinu fayudhinoon
Hausa
Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta.
|
Ayah 68:10 الأية
وَلَا تُطِعْ كُلَّ حَلَّافٍ مَّهِينٍ
Wala tutiAA kulla hallafinmaheen
Hausa
Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce.
|
Ayah 68:11 الأية
هَمَّازٍ مَّشَّاءٍ بِنَمِيمٍ
Hammazin mashsha-in binameem
Hausa
Mai zunɗe, mai yãwo da gulma.
|
Ayah 68:12 الأية
مَّنَّاعٍ لِّلْخَيْرِ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ
MannaAAin lilkhayri muAAtadin atheem
Hausa
Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi.
|
Ayah 68:13 الأية
عُتُلٍّ بَعْدَ ذَٰلِكَ زَنِيمٍ
AAutullin baAAda thalika zaneem
Hausa
Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi ( bã ya son alhẽri).
|
Ayah 68:14 الأية
أَن كَانَ ذَا مَالٍ وَبَنِينَ
An kana tha malinwabaneen
Hausa
Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya.
|
Ayah 68:15 الأية
إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ آيَاتُنَا قَالَ أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ
Itha tutla AAalayhi ayatunaqala asateeru al-awwaleen
Hausa
Idan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne."
|
Ayah 68:16 الأية
سَنَسِمُهُ عَلَى الْخُرْطُومِ
Sanasimuhu AAala alkhurtoom
Hausa
Zã Mu yi masa alãma a kan hanci.
|
Ayah 68:17 الأية
إِنَّا بَلَوْنَاهُمْ كَمَا بَلَوْنَا أَصْحَابَ الْجَنَّةِ إِذْ أَقْسَمُوا
لَيَصْرِمُنَّهَا مُصْبِحِينَ
Inna balawnahum kamabalawna as-haba aljannati ith aqsamoolayasrimunnaha
musbiheen
Hausa
Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da
suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci.
|
Ayah 68:18 الأية
وَلَا يَسْتَثْنُونَ
Wala yastathnoon
Hausa
Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa.
|
Ayah 68:19 الأية
فَطَافَ عَلَيْهَا طَائِفٌ مِّن رَّبِّكَ وَهُمْ نَائِمُونَ
Fatafa AAalayha ta-ifunmin rabbika wahum na-imoon
Hausa
Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, ( ya ƙone ta,) alhãli sunã
barci.
|
Ayah 68:20 الأية
فَأَصْبَحَتْ كَالصَّرِيمِ
Faasbahat kassareem
Hausa
Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare.
|
Ayah 68:21 الأية
فَتَنَادَوْا مُصْبِحِينَ
Fatanadaw musbiheen
Hausa
Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci.
|
Ayah 68:22 الأية
أَنِ اغْدُوا عَلَىٰ حَرْثِكُمْ إِن كُنتُمْ صَارِمِينَ
Ani ighdoo AAala harthikum inkuntum sarimeen
Hausa
Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa.
|
Ayah 68:23 الأية
فَانطَلَقُوا وَهُمْ يَتَخَافَتُونَ
Fantalaqoo wahum yatakhafatoon
Hausa
Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa).
|
Ayah 68:24 الأية
أَن لَّا يَدْخُلَنَّهَا الْيَوْمَ عَلَيْكُم مِّسْكِينٌ
An la yadkhulannaha alyawmaAAalaykum miskeen
Hausa
"Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!"
|
Ayah 68:25 الأية
وَغَدَوْا عَلَىٰ حَرْدٍ قَادِرِينَ
Waghadaw AAala hardin qadireen
Hausa
Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu.
|
Ayah 68:26 الأية
فَلَمَّا رَأَوْهَا قَالُوا إِنَّا لَضَالُّونَ
Falamma raawha qalooinna ladalloon
Hausa
Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!"
|
Ayah 68:27 الأية
بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ
Bal nahnu mahroomoon
Hausa
"Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne."
|
Ayah 68:28 الأية
قَالَ أَوْسَطُهُمْ أَلَمْ أَقُل لَّكُمْ لَوْلَا تُسَبِّحُونَ
Qala awsatuhum alam aqul lakumlawla tusabbihoon
Hausa
Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?"
|
Ayah 68:29 الأية
قَالُوا سُبْحَانَ رَبِّنَا إِنَّا كُنَّا ظَالِمِينَ
Qaloo subhana rabbinainna kunna thalimeen
Hausa
Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai."
|
Ayah 68:30 الأية
فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَلَاوَمُونَ
Faaqbala baAAduhum AAala baAAdinyatalawamoon
Hausa
Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu.
|
Ayah 68:31 الأية
قَالُوا يَا وَيْلَنَا إِنَّا كُنَّا طَاغِينَ
Qaloo ya waylana innakunna tagheen
Hausa
Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka."
|
Ayah 68:32 الأية
عَسَىٰ رَبُّنَا أَن يُبْدِلَنَا خَيْرًا مِّنْهَا إِنَّا إِلَىٰ رَبِّنَا
رَاغِبُونَ
AAasa rabbuna an yubdilanakhayran minha inna ila rabbina raghiboon
Hausa
"Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ
(ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne."
|
Ayah 68:33 الأية
كَذَٰلِكَ الْعَذَابُ ۖ وَلَعَذَابُ الْآخِرَةِ أَكْبَرُ ۚ لَوْ كَانُوا
يَعْلَمُونَ
Kathalika alAAathabu walaAAathabual-akhirati akbaru law kanoo yaAAlamoon
Hausa
Haka dai azãbar take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance
zã su iya gãnẽwã.
|
Ayah 68:34 الأية
إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ عِندَ رَبِّهِمْ جَنَّاتِ النَّعِيمِ
Inna lilmuttaqeena AAinda rabbihim jannatiannaAAeem
Hausa
Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima.
|
Ayah 68:35 الأية
أَفَنَجْعَلُ الْمُسْلِمِينَ كَالْمُجْرِمِينَ
AfanajAAalu almuslimeena kalmujrimeen
Hausa
Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi?
|
Ayah 68:36 الأية
مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ
Ma lakum kayfa tahkumoon
Hausa
Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)?
|
Ayah 68:37 الأية
أَمْ لَكُمْ كِتَابٌ فِيهِ تَدْرُسُونَ
Am lakum kitabun feehi tadrusoon
Hausa
Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa?
|
Ayah 68:38 الأية
إِنَّ لَكُمْ فِيهِ لَمَا تَخَيَّرُونَ
Inna lakum feehi lama takhayyaroon
Hausa
Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa?
|
Ayah 68:39 الأية
أَمْ لَكُمْ أَيْمَانٌ عَلَيْنَا بَالِغَةٌ إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ ۙ إِنَّ
لَكُمْ لَمَا تَحْكُمُونَ
Am lakum aymanun AAalayna balighatunila yawmi alqiyamati inna lakum lama
tahkumoon
Hausa
Kõ kunã ( riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kanMu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma,
cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku?
|
Ayah 68:40 الأية
سَلْهُمْ أَيُّهُم بِذَٰلِكَ زَعِيمٌ
Salhum ayyuhum bithalika zaAAeem
Hausa
Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)?
|
Ayah 68:41 الأية
أَمْ لَهُمْ شُرَكَاءُ فَلْيَأْتُوا بِشُرَكَائِهِمْ إِن كَانُوا صَادِقِينَ
Am lahum shurakao falya/too bishuraka-ihimin kanoo sadiqeen
Hausa
Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu,
idan sun kasance mãsu gaskiya.
|
Ayah 68:42 الأية
يَوْمَ يُكْشَفُ عَن سَاقٍ وَيُدْعَوْنَ إِلَى السُّجُودِ فَلَا يَسْتَطِيعُونَ
Yawma yukshafu AAan saqin wayudAAawnaila assujoodi fala yastateeAAoon
Hausa
Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujũda, sai bã zã su
iyãwa ba.
|
Ayah 68:43 الأية
خَاشِعَةً أَبْصَارُهُمْ تَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ ۖ وَقَدْ كَانُوا يُدْعَوْنَ إِلَى
السُّجُودِ وَهُمْ سَالِمُونَ
KhashiAAatan absaruhumtarhaquhum thillatun waqad kanoo yudAAawna ilaassujoodi
wahum salimoon
Hausa
Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance
anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi).
|
Ayah 68:44 الأية
فَذَرْنِي وَمَن يُكَذِّبُ بِهَٰذَا الْحَدِيثِ ۖ سَنَسْتَدْرِجُهُم مِّنْ حَيْثُ
لَا يَعْلَمُونَ
Fatharnee waman yukaththibubihatha alhadeethi sanastadrijuhum min haythula
yaAAlamoon
Hausa
Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu
istidrãji daga inda ba su sani ba.
|
Ayah 68:45 الأية
وَأُمْلِي لَهُمْ ۚ إِنَّ كَيْدِي مَتِينٌ
Waomlee lahum inna kaydee mateen
Hausa
Ina jinkirtã musu, lalle kaidiNa mai ƙarfi ne.
|
Ayah 68:46 الأية
أَمْ تَسْأَلُهُمْ أَجْرًا فَهُم مِّن مَّغْرَمٍ مُّثْقَلُونَ
Am tas-aluhum ajran fahum min maghraminmuthqaloon
Hausa
Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin
an nauyaya musu?
|
Ayah 68:47 الأية
أَمْ عِندَهُمُ الْغَيْبُ فَهُمْ يَكْتُبُونَ
Am AAindahumu alghaybu fahum yaktuboon
Hausa
Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga
gare shi) ne?
|
Ayah 68:48 الأية
فَاصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ وَلَا تَكُن كَصَاحِبِ الْحُوتِ إِذْ نَادَىٰ وَهُوَ
مَكْظُومٌ
Fasbir lihukmi rabbikawala takun kasahibi alhooti ith nadawahuwa makthoom
Hausa
Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin
kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi.
|
Ayah 68:49 الأية
لَّوْلَا أَن تَدَارَكَهُ نِعْمَةٌ مِّن رَّبِّهِ لَنُبِذَ بِالْعَرَاءِ وَهُوَ
مَذْمُومٌ
Lawla an tadarakahu niAAmatunmin rabbihi lanubitha bilAAara-i wahuwa mathmoom
Hausa
Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi
a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi.
|
Ayah 68:50 الأية
فَاجْتَبَاهُ رَبُّهُ فَجَعَلَهُ مِنَ الصَّالِحِينَ
Fajtabahu rabbuhu fajaAAalahumina assaliheen
Hausa
Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki.
|
Ayah 68:51 الأية
وَإِن يَكَادُ الَّذِينَ كَفَرُوا لَيُزْلِقُونَكَ بِأَبْصَارِهِمْ لَمَّا سَمِعُوا
الذِّكْرَ وَيَقُولُونَ إِنَّهُ لَمَجْنُونٌ
Wa-in yakadu allatheenakafaroo layuzliqoonaka bi-absarihim lamma
samiAAooaththikra wayaqooloona innahu lamajnoon
Hausa
Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da
kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã
cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne!"
|
Ayah 68:52 الأية
وَمَا هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَالَمِينَ
Wama huwa illa thikrunlilAAalameen
Hausa
Shi ( Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|