Prev  

7. Surah Al-A'râf سورة الأعراف

  Next  




1st Ayah  1  الأية ١الأولي
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
المص
Alif-lam-meem-sad

Hausa
 
A. L̃. M̃. Ṣ̃.

Ayah  7:2  الأية
كِتَابٌ أُنزِلَ إِلَيْكَ فَلَا يَكُن فِي صَدْرِكَ حَرَجٌ مِّنْهُ لِتُنذِرَ بِهِ وَذِكْرَىٰ لِلْمُؤْمِنِينَ
Kitabun onzila ilayka falayakun fee sadrika harajun minhu litunthirabihi wathikra lilmu/mineen

Hausa
 
Littăfi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka daga gare shi, dőmin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunătarwa ne ga mũminai.

Ayah  7:3  الأية
اتَّبِعُوا مَا أُنزِلَ إِلَيْكُم مِّن رَّبِّكُمْ وَلَا تَتَّبِعُوا مِن دُونِهِ أَوْلِيَاءَ ۗ قَلِيلًا مَّا تَذَكَّرُونَ
IttabiAAoo ma onzila ilaykum minrabbikum wala tattabiAAoo min doonihi awliyaaqaleelan ma tathakkaroon

Hausa
 
Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunăwa.

Ayah  7:4  الأية
وَكَم مِّن قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَاهَا فَجَاءَهَا بَأْسُنَا بَيَاتًا أَوْ هُمْ قَائِلُونَ
Wakam min qaryatin ahlaknahafajaaha ba/suna bayatan aw hum qa-iloon

Hausa
 
Kuma da yawa wata alƙarya Muka halaka ta, sai azăbarMu ta jẽ mata da dare kő kuwa sună măsu ƙailũla.

Ayah  7:5  الأية
فَمَا كَانَ دَعْوَاهُمْ إِذْ جَاءَهُم بَأْسُنَا إِلَّا أَن قَالُوا إِنَّا كُنَّا ظَالِمِينَ
Fama kana daAAwahum ithjaahum ba/suna illa an qaloo innakunna thalimeen

Hausa
 
Sa'an nan băbu abin da yake da'awarsu, a lőkacin da azăbarMu ta jẽ musu, făce suka ce: "Lalle ne mũ muka kasance măsu zălunci,"

Ayah  7:6  الأية
فَلَنَسْأَلَنَّ الَّذِينَ أُرْسِلَ إِلَيْهِمْ وَلَنَسْأَلَنَّ الْمُرْسَلِينَ
Falanas-alanna allatheena orsilailayhim walanas-alanna almursaleen

Hausa
 
Sa'an nan lalle ne Mună tambayar waɗanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Mună tambayar Manzannin.

Ayah  7:7  الأية
فَلَنَقُصَّنَّ عَلَيْهِم بِعِلْمٍ ۖ وَمَا كُنَّا غَائِبِينَ
Falanaqussanna AAalayhim biAAilmin wamakunna gha-ibeen

Hausa
 
Sa'an nan haƙĩƙa Mună bă su lăbări da ilmi kuma ba Mu kasance măsu fakowa ba.

Ayah  7:8  الأية
وَالْوَزْنُ يَوْمَئِذٍ الْحَقُّ ۚ فَمَن ثَقُلَتْ مَوَازِينُهُ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ
Walwaznu yawma-ithini alhaqqufaman thaqulat mawazeenuhu faola-ika humu almuflihoon

Hausa
 
Kuma awo a rănar nan ne gaskiya. To, wanda sikẽlansasuka yi nauyi, to, waɗannan sũ ne măsu cin nasara.

Ayah  7:9  الأية
وَمَنْ خَفَّتْ مَوَازِينُهُ فَأُولَٰئِكَ الَّذِينَ خَسِرُوا أَنفُسَهُم بِمَا كَانُوا بِآيَاتِنَا يَظْلِمُونَ
Waman khaffat mawazeenuhu faola-ikaallatheena khasiroo anfusahum bima kanoo bi-ayatinayathlimoon

Hausa
 
Kuma wanda sikẽlansa suka yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu, sabőda abin da suka kasance, da ăyőyinMu, sună yi na zălunci.

Ayah  7:10  الأية
وَلَقَدْ مَكَّنَّاكُمْ فِي الْأَرْضِ وَجَعَلْنَا لَكُمْ فِيهَا مَعَايِشَ ۗ قَلِيلًا مَّا تَشْكُرُونَ
Walaqad makkannakum fee al-ardiwajaAAalna lakum feeha maAAayisha qaleelan matashkuroon

Hausa
 
Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarautar da ku, a cikin ƙasa, kuma Mun sanya muku abũbuwan răyuwa, a cikinta; kaɗan ƙwarai kuke gődẽwa.

Ayah  7:11  الأية
وَلَقَدْ خَلَقْنَاكُمْ ثُمَّ صَوَّرْنَاكُمْ ثُمَّ قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ لَمْ يَكُن مِّنَ السَّاجِدِينَ
Walaqad khalaqnakum thumma sawwarnakumthumma qulna lilmala-ikati osjudoo li-adamafasajadoo illa ibleesa lam yakun mina assajideen

Hausa
 
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halittă ku sa'an nan kuma Mun sũrantă ku, sa'an nan kumaMun ce wa mală'iku: "Ku yi sujada ga Ădam." Sai suka yi sujada făce Iblĩs, bai kasance daga măsuyin sujadar ba.

Ayah  7:12  الأية
قَالَ مَا مَنَعَكَ أَلَّا تَسْجُدَ إِذْ أَمَرْتُكَ ۖ قَالَ أَنَا خَيْرٌ مِّنْهُ خَلَقْتَنِي مِن نَّارٍ وَخَلَقْتَهُ مِن طِينٍ
Qala ma manaAAaka allatasjuda ith amartuka qala ana khayrun minhukhalaqtanee min narin wakhalaqtahu min teen

Hausa
 
Ya ce: "Mẽne ne ya hana ka, ba ka yi sujada ba, alőkacin da Na umurce ka?" Ya ce: "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare shi, Ka halitta ni daga wuta alhăli kuwa Kă halitta shi daga lăka."

Ayah  7:13  الأية
قَالَ فَاهْبِطْ مِنْهَا فَمَا يَكُونُ لَكَ أَن تَتَكَبَّرَ فِيهَا فَاخْرُجْ إِنَّكَ مِنَ الصَّاغِرِينَ
Qala fahbit minhafama yakoonu laka an tatakabbara feeha fakhrujinnaka mina assaghireen

Hausa
 
Ya ce: "To, ka sauka daga gare ta; dőmin bă, ya kasancẽwa a gare ka ga ka yi girman kai a cikinta. Sai ka fita. Lalle ne kană daga măsu ƙasƙanci."

Ayah  7:14  الأية
قَالَ أَنظِرْنِي إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ
Qala anthirnee ilayawmi yubAAathoon

Hausa
 
Ya ce: "Ka yi mini jinkiri zuwa ga rănar da ake tăyar da su."

Ayah  7:15  الأية
قَالَ إِنَّكَ مِنَ الْمُنظَرِينَ
Qala innaka mina almunthareen

Hausa
 
Ya ce: "Lalle ne, kană daga waɗanda aka yi wa jinkiri."

Ayah  7:16  الأية
قَالَ فَبِمَا أَغْوَيْتَنِي لَأَقْعُدَنَّ لَهُمْ صِرَاطَكَ الْمُسْتَقِيمَ
Qala fabima aghwaytaneelaaqAAudanna lahum sirataka almustaqeem

Hausa
 
Ya ce: "To ină rantsuwa da halakarwar da Ka yi mini, lalle ne, ină zaune musu tafarkinKa madaidaici."

Ayah  7:17  الأية
ثُمَّ لَآتِيَنَّهُم مِّن بَيْنِ أَيْدِيهِمْ وَمِنْ خَلْفِهِمْ وَعَنْ أَيْمَانِهِمْ وَعَن شَمَائِلِهِمْ ۖ وَلَا تَجِدُ أَكْثَرَهُمْ شَاكِرِينَ
Thumma laatiyannahum min bayniaydeehim wamin khalfihim waAAan aymanihim waAAan shama-ilihimwala tajidu aktharahum shakireen

Hausa
 
"Sa'an nan kuma haƙĩƙa, Ină je musu daga gaba gare su, kuma daga băya gare su, kuma daga jihőhin damansu da jihőhin hagunsu; Kuma bă ză ka sămi mafi yawansu măsu gődiya ba."

Ayah  7:18  الأية
قَالَ اخْرُجْ مِنْهَا مَذْءُومًا مَّدْحُورًا ۖ لَّمَن تَبِعَكَ مِنْهُمْ لَأَمْلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنكُمْ أَجْمَعِينَ
Qala okhruj minha mathoomanmadhooran laman tabiAAaka minhum laamlaanna jahannamaminkum ajmaAAeen

Hausa
 
Ya ce: "Ka fita daga gare ta kană abin zargi kőrarre. Lalle ne wanda ya bĩ ka daga gare su, haƙĩƙa, ză Ni cika jahannama daga gare ku, gabă ɗaya."

Ayah  7:19  الأية
وَيَا آدَمُ اسْكُنْ أَنتَ وَزَوْجُكَ الْجَنَّةَ فَكُلَا مِنْ حَيْثُ شِئْتُمَا وَلَا تَقْرَبَا هَٰذِهِ الشَّجَرَةَ فَتَكُونَا مِنَ الظَّالِمِينَ
Waya adamu oskun antawazawjuka aljannata fakula min haythu shi/tumawala taqraba hathihi ashshajaratafatakoona mina aththalimeen

Hausa
 
"Kuma ya Ădam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci wannan ităciya, har ku kasance daga azzălumai."

Ayah  7:20  الأية
فَوَسْوَسَ لَهُمَا الشَّيْطَانُ لِيُبْدِيَ لَهُمَا مَا وُورِيَ عَنْهُمَا مِن سَوْآتِهِمَا وَقَالَ مَا نَهَاكُمَا رَبُّكُمَا عَنْ هَٰذِهِ الشَّجَرَةِ إِلَّا أَن تَكُونَا مَلَكَيْنِ أَوْ تَكُونَا مِنَ الْخَالِدِينَ
Fawaswasa lahuma ashshaytanuliyubdiya lahuma ma wooriya AAanhuma minsaw-atihima waqala ma nahakumarabbukuma AAan hathihi ashshajarati illaan takoona malakayni aw takoona mina alkhalideen

Hausa
 
Sai Shaiɗan ya sanya musu waswăsi dőmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al'aurarsu, kuma ya ce: "Ubangijinku bai hană ku daga wannan ităciya ba făce dőmin kada ku kasance mală'iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama."

Ayah  7:21  الأية
وَقَاسَمَهُمَا إِنِّي لَكُمَا لَمِنَ النَّاصِحِينَ
Waqasamahuma innee lakumalamina annasiheen

Hausa
 
Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga măsu nasĩha ne.

Ayah  7:22  الأية
فَدَلَّاهُمَا بِغُرُورٍ ۚ فَلَمَّا ذَاقَا الشَّجَرَةَ بَدَتْ لَهُمَا سَوْآتُهُمَا وَطَفِقَا يَخْصِفَانِ عَلَيْهِمَا مِن وَرَقِ الْجَنَّةِ ۖ وَنَادَاهُمَا رَبُّهُمَا أَلَمْ أَنْهَكُمَا عَن تِلْكُمَا الشَّجَرَةِ وَأَقُل لَّكُمَا إِنَّ الشَّيْطَانَ لَكُمَا عَدُوٌّ مُّبِينٌ
Fadallahuma bighuroorin falammathaqa ashshajarata badat lahuma saw-atuhumawatafiqa yakhsifani AAalayhimamin waraqi aljannati wanadahuma rabbuhumaalam anhakuma AAan tilkuma ashshajaratiwaaqul lakuma inna ashshaytana lakumaAAaduwwun mubeen

Hausa
 
Sai ya saukar da su da rũɗi. Sa'an nan a lőkacin da suka ɗanɗani ităciyar, al'aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sună lĩƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: "Shin, Ban hană ku ba daga waccan ităciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne?"

Ayah  7:23  الأية
قَالَا رَبَّنَا ظَلَمْنَا أَنفُسَنَا وَإِن لَّمْ تَغْفِرْ لَنَا وَتَرْحَمْنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ
Qala rabbana thalamnaanfusana wa-in lam taghfir lana watarhamnalanakoonanna mina alkhasireen

Hausa
 
Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Mun zălunci kanmu. Kuma idan ba Ka găfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Mună kasancẽwa daga măsu hasăra."

Ayah  7:24  الأية
قَالَ اهْبِطُوا بَعْضُكُمْ لِبَعْضٍ عَدُوٌّ ۖ وَلَكُمْ فِي الْأَرْضِ مُسْتَقَرٌّ وَمَتَاعٌ إِلَىٰ حِينٍ
Qala ihbitoo baAAdukumlibaAAdin AAaduwwun walakum fee al-ardi mustaqarrunwamataAAun ila heen

Hausa
 
Ya ce: "Ku sauka, săshenku zuwa ga săshe yană maƙiyi, kuma kună da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin dăɗi zuwa ga wani lőkabi."

Ayah  7:25  الأية
قَالَ فِيهَا تَحْيَوْنَ وَفِيهَا تَمُوتُونَ وَمِنْهَا تُخْرَجُونَ
Qala feeha tahyawnawafeeha tamootoona waminha tukhrajoon

Hausa
 
Ya ce: "A cikinta kuke răyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku."

Ayah  7:26  الأية
يَا بَنِي آدَمَ قَدْ أَنزَلْنَا عَلَيْكُمْ لِبَاسًا يُوَارِي سَوْآتِكُمْ وَرِيشًا ۖ وَلِبَاسُ التَّقْوَىٰ ذَٰلِكَ خَيْرٌ ۚ ذَٰلِكَ مِنْ آيَاتِ اللهِ لَعَلَّهُمْ يَذَّكَّرُونَ
Ya banee adama qad anzalnaAAalaykum libasan yuwaree saw-atikumwareeshan walibasu attaqwa thalikakhayrun thalika min ayati AllahilaAAallahum yaththakkaroon

Hausa
 
Yă ɗiyan Ădam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa a kanku, tană rufe muku al'aurarku, kuma da ƙawă. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga ăyőyin Allah ne, tsammăninsu sună tunăwa!

Ayah  7:27  الأية
يَا بَنِي آدَمَ لَا يَفْتِنَنَّكُمُ الشَّيْطَانُ كَمَا أَخْرَجَ أَبَوَيْكُم مِّنَ الْجَنَّةِ يَنزِعُ عَنْهُمَا لِبَاسَهُمَا لِيُرِيَهُمَا سَوْآتِهِمَا ۗ إِنَّهُ يَرَاكُمْ هُوَ وَقَبِيلُهُ مِنْ حَيْثُ لَا تَرَوْنَهُمْ ۗ إِنَّا جَعَلْنَا الشَّيَاطِينَ أَوْلِيَاءَ لِلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ
Ya banee adama layaftinannakumu ashshaytanu kama akhrajaabawaykum mina aljannati yanziAAu AAanhuma libasahumaliyuriyahuma saw-atihima innahu yarakumhuwa waqabeeluhu min haythu la tarawnahum innajaAAalna ashshayateena awliyaa lillatheenala yu/minoon

Hausa
 
Yă ɗiyan Ădam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyăyenku, biyu daga Aljanna, yană fizge tufarsu daga gare su, dőmin ya nũna musu al'aurarsu. Lalle ne shĩ, yană ganin ku,shi da rundunarsa, daga inda bă ku ganin su. Lalle ne Mũ, Mun sanyaShaiɗan majiɓinci ga waɗanda bă su yin ĩmăni.

Ayah  7:28  الأية
وَإِذَا فَعَلُوا فَاحِشَةً قَالُوا وَجَدْنَا عَلَيْهَا آبَاءَنَا وَاللهُ أَمَرَنَا بِهَا ۗ قُلْ إِنَّ اللهَ لَا يَأْمُرُ بِالْفَحْشَاءِ ۖ أَتَقُولُونَ عَلَى اللهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ
Wa-itha faAAaloo fahishatan qaloowajadna AAalayha abaana wallahuamarana biha qul inna Allaha laya/muru bilfahsha-i ataqooloona AAalaAllahi ma la taAAlamoon

Hausa
 
Kuma idan suka aikata alfăsha su ce: "Mun sămi ubanninmu akanta." Kuma Allah ne Ya umurce mu da ita."Ka ce: "Lalle ne, Allah bă Ya umurni da alfăsha. Shin kună faɗar abin da bă ku da saninsa ga Allah?"

Ayah  7:29  الأية
قُلْ أَمَرَ رَبِّي بِالْقِسْطِ ۖ وَأَقِيمُوا وُجُوهَكُمْ عِندَ كُلِّ مَسْجِدٍ وَادْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ ۚ كَمَا بَدَأَكُمْ تَعُودُونَ
Qul amara rabbee bilqistiwaaqeemoo wujoohakum AAinda kulli masjidin wadAAoohumukhliseena lahu addeena kama badaakumtaAAoodoon

Hausa
 
Ka ce: "Ubangjina Yă yi umurni da ădalci; kuma ku tsayar da fuskőkinku a wurin kőwane masallăci, kuma ku rőƙẽ Shi, kună măsu tsarkake addini gare Shi. Kamar yadda Ya făra halittarku kuke kőmăwa."

Ayah  7:30  الأية
فَرِيقًا هَدَىٰ وَفَرِيقًا حَقَّ عَلَيْهِمُ الضَّلَالَةُ ۗ إِنَّهُمُ اتَّخَذُوا الشَّيَاطِينَ أَوْلِيَاءَ مِن دُونِ اللهِ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُم مُّهْتَدُونَ
Fareeqan hada wafareeqan haqqaAAalayhimu addalalatu innahumu ittakhathooashshayateena awliyaa min dooni Allahiwayahsaboona annahum muhtadoon

Hausa
 
Wata ƙungiya (Allah) Yă shiryar, kuma wata ƙungiya ɓata tă wajaba a kansu; lalle ne sũ, sun riƙi shaiɗanu majiɓinta, baicin Allah, kuma sună zaton, lalle sũ, măsu shiryuwa ne.

Ayah  7:31  الأية
يَا بَنِي آدَمَ خُذُوا زِينَتَكُمْ عِندَ كُلِّ مَسْجِدٍ وَكُلُوا وَاشْرَبُوا وَلَا تُسْرِفُوا ۚ إِنَّهُ لَا يُحِبُّ الْمُسْرِفِينَ
Ya banee adama khuthoozeenatakum AAinda kulli masjidin wakuloo washraboo walatusrifoo innahu la yuhibbu almusrifeen

Hausa
 
Yă ɗiyan Ădam! Ku riƙi ƙawarku a wurin kőwane masallăci kuma ku ci, kuma ku sha; Kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ (Allah), bă Ya son măsu ɓarna.

Ayah  7:32  الأية
قُلْ مَنْ حَرَّمَ زِينَةَ اللهِ الَّتِي أَخْرَجَ لِعِبَادِهِ وَالطَّيِّبَاتِ مِنَ الرِّزْقِ ۚ قُلْ هِيَ لِلَّذِينَ آمَنُوا فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا خَالِصَةً يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۗ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ الْآيَاتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ
Qul man harrama zeenata Allahiallatee akhraja liAAibadihi wattayyibatimina arrizqi qul hiya lillatheena amanoofee alhayati addunya khalisatanyawma alqiyamati kathalika nufassilu al-ayatiliqawmin yaAAlamoon

Hausa
 
Ka ce: "Wăne ne ya haramta ƙawar Allah, wadda Ya fitar sabőda băyinSa, da măsu dăɗi daga abinci?" Ka ce: "Sũ, dőmin waɗanda suka yi ĩmani suke a cikin răyuwar dũniya, suna keɓantattu a Rănar Kiyăma. "Kamar wannan ne Muke bayyana ăyőyi, daki-daki, ga mutănen da suke sani.

Ayah  7:33  الأية
قُلْ إِنَّمَا حَرَّمَ رَبِّيَ الْفَوَاحِشَ مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَمَا بَطَنَ وَالْإِثْمَ وَالْبَغْيَ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَأَن تُشْرِكُوا بِاللهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِهِ سُلْطَانًا وَأَن تَقُولُوا عَلَى اللهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ
Qul innama harrama rabbiyaalfawahisha ma thahara minhawama batana wal-ithma walbaghyabighayri alhaqqi waan tushrikoo billahi malam yunazzil bihi sultanan waan taqooloo AAala Allahima la taAAlamoon

Hausa
 
Ka ce: "Abin sani kawai, Ubangijina Yă hana abũbuwanalfăsha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya ɓőyu, da zunubi da rarraba jama'a, bă da wani hakki ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalĩli ba gare shi, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba, ga Allah."

Ayah  7:34  الأية
وَلِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٌ ۖ فَإِذَا جَاءَ أَجَلُهُمْ لَا يَسْتَأْخِرُونَ سَاعَةً ۖ وَلَا يَسْتَقْدِمُونَ
Walikulli ommatin ajalun fa-itha jaaajaluhum la yasta/khiroona saAAatan walayastaqdimoon

Hausa
 
Kuma ga kőwace al'umma akwai ajali. Sa'an nan idan ajalinsu ya je, bă ză a yi musu jinkiri ba, sa'a guda, kuma bă ză su gabăce shi ba.

Ayah  7:35  الأية
يَا بَنِي آدَمَ إِمَّا يَأْتِيَنَّكُمْ رُسُلٌ مِّنكُمْ يَقُصُّونَ عَلَيْكُمْ آيَاتِي ۙ فَمَنِ اتَّقَىٰ وَأَصْلَحَ فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ
Ya banee adama immaya/tiyannakum rusulun minkum yaqussoona AAalaykum ayateefamani ittaqa waaslaha fala khawfunAAalayhim wala hum yahzanoon

Hausa
 
Yă ɗiyan Ădam! Ko dai wasu manzanni, daga cikinku, su jẽ muku, sună gaya muku ayőyiNato, wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, băbu tsoro a kansu, kuma bă su yin baƙin ciki.

Ayah  7:36  الأية
وَالَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَاسْتَكْبَرُوا عَنْهَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Wallatheena kaththaboobi-ayatina wastakbaroo AAanhaola-ika as-habu annari humfeeha khalidoon

Hausa
 
Kuma waɗanda suka ƙaryată game da ăyőyinMu, kuma suka yi girman kai daga gare su, waɗannan sũ ne abőkan wuta, sũ, a cikinta madawwama ne.

Ayah  7:37  الأية
فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَىٰ عَلَى اللهِ كَذِبًا أَوْ كَذَّبَ بِآيَاتِهِ ۚ أُولَٰئِكَ يَنَالُهُمْ نَصِيبُهُم مِّنَ الْكِتَابِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا جَاءَتْهُمْ رُسُلُنَا يَتَوَفَّوْنَهُمْ قَالُوا أَيْنَ مَا كُنتُمْ تَدْعُونَ مِن دُونِ اللهِ ۖ قَالُوا ضَلُّوا عَنَّا وَشَهِدُوا عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ أَنَّهُمْ كَانُوا كَافِرِينَ
Faman athlamu mimmani iftaraAAala Allahi kathiban aw kaththababi-ayatihi ola-ika yanaluhum naseebuhummina alkitabi hatta itha jaat-humrusuluna yatawaffawnahum qaloo ayna makuntum tadAAoona min dooni Allahi qaloo dallooAAanna washahidoo AAala anfusihim annahum kanookafireen

Hausa
 
To, wăne ne mafi zălunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kő kuwa ya ƙaryata game da ăyőyinSa? Waɗannan rabonsu daga Littăfi yană sămunsu, har a lőkacin da ManzanninMu suka je musu, sună karɓar răyukansu, su ce: "Ĩnă abin da kuka kasance kună kira, baicin Allah?" Su ce: "Sun ɓace daga gare mu, "Kuma su yi shaida a kansu cẽwa lalle sũ, sun kasance kăfirai."

Ayah  7:38  الأية
قَالَ ادْخُلُوا فِي أُمَمٍ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِكُم مِّنَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ فِي النَّارِ ۖ كُلَّمَا دَخَلَتْ أُمَّةٌ لَّعَنَتْ أُخْتَهَا ۖ حَتَّىٰ إِذَا ادَّارَكُوا فِيهَا جَمِيعًا قَالَتْ أُخْرَاهُمْ لِأُولَاهُمْ رَبَّنَا هَٰؤُلَاءِ أَضَلُّونَا فَآتِهِمْ عَذَابًا ضِعْفًا مِّنَ النَّارِ ۖ قَالَ لِكُلٍّ ضِعْفٌ وَلَٰكِن لَّا تَعْلَمُونَ
Qala odkhuloo fee omamin qad khalatmin qablikum mina aljinni wal-insi fee annarikullama dakhalat ommatun laAAanat okhtaha hattaitha iddarakoo feeha jameeAAan qalatokhrahum li-oolahum rabbana haola-iadalloona faatihim AAathaban diAAfanmina annari qala likullin diAAfunwalakin la taAAlamoon

Hausa
 
Ya ce: "Ku shiga a cikin al'ummai waɗanda, haƙĩƙa, sun shige daga gabăninku, daga aljannu da mutăne, a cikin Wuta. A kő da yaushe wata al'umma ta shiga sai ta la'ani 'yar'uwarta, har idan suka riski jũna, a cikinta, gabă ɗaya, ta ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu, sai Ka kăwo musu azăba ninki daga wuta." Ya ce: "Ga kőwane akwai ninki; kuma amma ba ku sani ba."

Ayah  7:39  الأية
وَقَالَتْ أُولَاهُمْ لِأُخْرَاهُمْ فَمَا كَانَ لَكُمْ عَلَيْنَا مِن فَضْلٍ فَذُوقُوا الْعَذَابَ بِمَا كُنتُمْ تَكْسِبُونَ
Waqalat oolahum li-okhrahumfama kana lakum AAalayna min fadlinfathooqoo alAAathaba bima kuntum taksiboon

Hausa
 
Kuma ta farkonsu ta ce wa ta ƙarshe: "To, bă ku da wata falala a kanmu, sai ku ɗanɗana azăba sabőda abin da kuka kasance kună tărăwa!"

Ayah  7:40  الأية
إِنَّ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَاسْتَكْبَرُوا عَنْهَا لَا تُفَتَّحُ لَهُمْ أَبْوَابُ السَّمَاءِ وَلَا يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ حَتَّىٰ يَلِجَ الْجَمَلُ فِي سَمِّ الْخِيَاطِ ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُجْرِمِينَ
Inna allatheena kaththaboo bi-ayatinawastakbaroo AAanha la tufattahulahum abwabu assama-i walayadkhuloona aljannata hatta yalija aljamalu feesammi alkhiyati wakathalika najzee almujrimeen

Hausa
 
Lalle ne waɗanda suka ƙaryată game da ăyőyinMu, kuma suka yi girman kai daga barinsu, bă ză a bubbuɗe musu kőfőfin sama ba, kuma bă su shiga Aljanna sai raƙumi ya shiga kafar allũra, kuma kamar wannan ne Muke săka wa măsu laifi.

Ayah  7:41  الأية
لَهُم مِّن جَهَنَّمَ مِهَادٌ وَمِن فَوْقِهِمْ غَوَاشٍ ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِي الظَّالِمِينَ
Lahum min jahannama mihadun waminfawqihim ghawashin wakathalika najzee aththalimeen

Hausa
 
Sună da wata shimfiɗa daga Jahannama kuma daga samansu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke săka wa azzălumai.

Ayah  7:42  الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَا نُكَلِّفُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Wallatheena amanoowaAAamiloo assalihati la nukallifunafsan illa wusAAaha ola-ika as-habualjannati hum feeha khalidoon

Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, bă Mu ƙallafa wa rai făce iyăwarsa, Waɗannan ne abőkan Aljanna, sũ, a cikinta, madawwma ne.

Ayah  7:43  الأية
وَنَزَعْنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنْ غِلٍّ تَجْرِي مِن تَحْتِهِمُ الْأَنْهَارُ ۖ وَقَالُوا الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي هَدَانَا لِهَٰذَا وَمَا كُنَّا لِنَهْتَدِيَ لَوْلَا أَنْ هَدَانَا اللهُ ۖ لَقَدْ جَاءَتْ رُسُلُ رَبِّنَا بِالْحَقِّ ۖ وَنُودُوا أَن تِلْكُمُ الْجَنَّةُ أُورِثْتُمُوهَا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
WanazaAAna ma fee sudoorihimmin ghillin tajree min tahtihimu al-anharu waqalooalhamdu lillahi allathee hadanalihatha wama kunna linahtadiya lawlaan hadana Allahu laqad jaat rusulurabbina bilhaqqi wanoodoo an tilkumualjannatu oorithtumooha bima kuntum taAAmaloon

Hausa
 
Kuma Muka fitar da abin da yake a cikin ƙirăzansu, daga ƙiyayya, ƙőramu sună gudăna daga ƙarƙashinsu, kuma suka ce: "Gődiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya shiryar da mu ga wannan. Kuma ba mu kasance mună iya shiryuwa ba, bă dőmin Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle ne haƙĩƙa, Manzannin Ubangjinmu, sun jẽ mana da gaskiya." Kuma aka kira su, cẽwa: "Waccan Aljlnna an gădar da ku ita, sabőda abin da kuka kasance kună aikatăwa."

Ayah  7:44  الأية
وَنَادَىٰ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ أَصْحَابَ النَّارِ أَن قَدْ وَجَدْنَا مَا وَعَدَنَا رَبُّنَا حَقًّا فَهَلْ وَجَدتُّم مَّا وَعَدَ رَبُّكُمْ حَقًّا ۖ قَالُوا نَعَمْ ۚ فَأَذَّنَ مُؤَذِّنٌ بَيْنَهُمْ أَن لَّعْنَةُ اللهِ عَلَى الظَّالِمِينَ
Wanada as-habualjannati as-haba annari an qadwajadna ma waAAadana rabbuna haqqanfahal wajadtum ma waAAada rabbukum haqqan qaloonaAAam faaththana mu-aththinun baynahum an laAAnatuAllahi AAala aththalimeen

Hausa
 
Kuma 'yan Aljanna suka kirăyi 'yan Wuta suka ce: "Lalle ne mun sămi abin da Ubangijinmu Ya yi mana wa'adi, gaskiya ne. To, shin, kun sămi abin da Ubangijinku Ya yi muku wa'adi, gaskiya?" Suka ce: "Na'am." Sai mai sanarwa ya yi yẽkuwa, cẽwa: "La'anar Allah ta tabbata a kan azzălumai."

Ayah  7:45  الأية
الَّذِينَ يَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللهِ وَيَبْغُونَهَا عِوَجًا وَهُم بِالْآخِرَةِ كَافِرُونَ
Allatheena yasuddoona AAansabeeli Allahi wayabghoonaha AAiwajan wahum bil-akhiratikafiroon

Hausa
 
"Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah, kuma sună nẽman ta ta zama karkatacciya,. kuma sũ, game da Lăhira, kăfirai ne."

Ayah  7:46  الأية
وَبَيْنَهُمَا حِجَابٌ ۚ وَعَلَى الْأَعْرَافِ رِجَالٌ يَعْرِفُونَ كُلًّا بِسِيمَاهُمْ ۚ وَنَادَوْا أَصْحَابَ الْجَنَّةِ أَن سَلَامٌ عَلَيْكُمْ ۚ لَمْ يَدْخُلُوهَا وَهُمْ يَطْمَعُونَ
Wabaynahuma hijabunwaAAala al-aAArafi rijalun yaAArifoonakullan biseemahum wanadaw as-habaaljannati an salamun AAalaykum lam yadkhuloohawahum yatmaAAoon

Hausa
 
Kuma a tsakăninsu akwai wani shămaki, kuma a kan A'arăf akwai wasu maza sună sanin kőwa da alămarsu; Kuma suka kirăyi abőkan Aljamia cẽwa: "Aminci ya tabbata a kanku: "Ba su shige ta ba, alhăli kuwa sũ, sună tsammăni.

Ayah  7:47  الأية
وَإِذَا صُرِفَتْ أَبْصَارُهُمْ تِلْقَاءَ أَصْحَابِ النَّارِ قَالُوا رَبَّنَا لَا تَجْعَلْنَا مَعَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ
Wa-itha surifat absaruhumtilqaa as-habi annari qaloorabbana la tajAAalna maAAa alqawmi aththalimeen

Hausa
 
Kuma idan an jũyar da gannansu wajen abőkan wuta, su ce: "Yă Ubangijinmu! Kada Ka sanyă mu tăre da mutăne azzălumai."

Ayah  7:48  الأية
وَنَادَىٰ أَصْحَابُ الْأَعْرَافِ رِجَالًا يَعْرِفُونَهُم بِسِيمَاهُمْ قَالُوا مَا أَغْنَىٰ عَنكُمْ جَمْعُكُمْ وَمَا كُنتُمْ تَسْتَكْبِرُونَ
Wanada as-habual-aAArafi rijalan yaAArifoonahum biseemahumqaloo ma aghna AAankum jamAAukum wamakuntum tastakbiroon

Hausa
 
Kuma abőkan A'araf suka kirăyi wasu maza, sună sanin su da alămarsu, suka ce: "Tărawar dũkiyarku da abin da kuka kasance kună yi na girman kai, bai wadătar ba daga barinku?"

Ayah  7:49  الأية
أَهَٰؤُلَاءِ الَّذِينَ أَقْسَمْتُمْ لَا يَنَالُهُمُ اللهُ بِرَحْمَةٍ ۚ ادْخُلُوا الْجَنَّةَ لَا خَوْفٌ عَلَيْكُمْ وَلَا أَنتُمْ تَحْزَنُونَ
Ahaola-i allatheenaaqsamtum la yanaluhumu Allahu birahmatinodkhuloo aljannata la khawfun AAalaykum wala antumtahzanoon

Hausa
 
"Shin, waɗannan ne waɗanda kuka yi rantsuwa, Allah bă zai săme su da rahama ba? Ku shiga Aljanna, băbu tsőro akanku, kuma ba ku zama kună baƙin ciki ba."

Ayah  7:50  الأية
وَنَادَىٰ أَصْحَابُ النَّارِ أَصْحَابَ الْجَنَّةِ أَنْ أَفِيضُوا عَلَيْنَا مِنَ الْمَاءِ أَوْ مِمَّا رَزَقَكُمُ اللهُ ۚ قَالُوا إِنَّ اللهَ حَرَّمَهُمَا عَلَى الْكَافِرِينَ
Wanada as-habu anarias-haba aljannati an afeedoo AAalaynamina alma-i aw mimma razaqakumu Allahu qalooinna Allaha harramahuma AAala alkafireen

Hausa
 
Kuma 'yan wuta suka kirăyi 'yan Aljanna cẽwa: "Ku zubo a kaumu daga ruwa kő kuwa daga abin da Allah Ya azurta ku." Su ce: "Lalle ne Allah Ya haramtă su a kan kăfirai."

Ayah  7:51  الأية
الَّذِينَ اتَّخَذُوا دِينَهُمْ لَهْوًا وَلَعِبًا وَغَرَّتْهُمُ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا ۚ فَالْيَوْمَ نَنسَاهُمْ كَمَا نَسُوا لِقَاءَ يَوْمِهِمْ هَٰذَا وَمَا كَانُوا بِآيَاتِنَا يَجْحَدُونَ
Allatheena ittakhathoodeenahum lahwan walaAAiban wagharrat-humu alhayatuaddunya falyawma nansahum kamanasoo liqaa yawmihim hatha wama kanoobi-ayatina yajhadoon

Hausa
 
"Waɗanda suka riƙi addininsu abin shagala da wăsa, kuma răyuwar dũniya ta rũɗe su." To, a yau Mună mantăwa da su, kamar yadda suka manta da haɗuwa da yininsu wannan, da kuma abin da suka kasance da ăyoyinMu sună musu.

Ayah  7:52  الأية
وَلَقَدْ جِئْنَاهُم بِكِتَابٍ فَصَّلْنَاهُ عَلَىٰ عِلْمٍ هُدًى وَرَحْمَةً لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Walaqad ji/nahum bikitabin fassalnahuAAala AAilmin hudan warahmatan liqawmin yu/minoon

Hausa
 
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun jẽ musu da Littăfi, Mun bayyana Shi, daki-daki, a kan ilmi, yană shiriya da rahama ga mutăne waɗanda suke yin ĩmani.

Ayah  7:53  الأية
هَلْ يَنظُرُونَ إِلَّا تَأْوِيلَهُ ۚ يَوْمَ يَأْتِي تَأْوِيلُهُ يَقُولُ الَّذِينَ نَسُوهُ مِن قَبْلُ قَدْ جَاءَتْ رُسُلُ رَبِّنَا بِالْحَقِّ فَهَل لَّنَا مِن شُفَعَاءَ فَيَشْفَعُوا لَنَا أَوْ نُرَدُّ فَنَعْمَلَ غَيْرَ الَّذِي كُنَّا نَعْمَلُ ۚ قَدْ خَسِرُوا أَنفُسَهُمْ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا يَفْتَرُونَ
Hal yanthuroona illata/weelahu yawma ya/tee ta/weeluhu yaqoolu allatheenanasoohu min qablu qad jaat rusulu rabbina bilhaqqifahal lana min shufaAAaa fayashfaAAoo lanaaw nuraddu fanaAAmala ghayra allathee kunnanaAAmalu qad khasiroo anfusahum wadalla AAanhum makanoo yaftaroon

Hausa
 
Shin, sună jira, făce fassararsa, a rănar da fassararsa take zuwa, waɗanda saka manta da Shi daga gabăni, sună cẽwa: "Lalle ne, Manzannin Ubangijin mu svun jẽ da gaskiya. To, shin, mună da wasu măsu cẽto, su yi cẽto gare mu, kő kuwa a mayar da mũ, har mu aikata wanin wanda muka kasance muna aikatăwa?" Lalle ne sun yi hasărar răyukansu, kuma abin da suka kasance sună ƙĩrƙirawa yă ɓace musu.

Ayah  7:54  الأية
إِنَّ رَبَّكُمُ اللهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَىٰ عَلَى الْعَرْشِ يُغْشِي اللَّيْلَ النَّهَارَ يَطْلُبُهُ حَثِيثًا وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ وَالنُّجُومَ مُسَخَّرَاتٍ بِأَمْرِهِ ۗ أَلَا لَهُ الْخَلْقُ وَالْأَمْرُ ۗ تَبَارَكَ اللهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ
Inna rabbakumu Allahu allatheekhalaqa assamawati wal-ardafee sittati ayyamin thumma istawa AAalaalAAarshi yughshee allayla annahara yatlubuhuhatheethan washshamsa walqamara wannujoomamusakhkharatin bi-amrihi ala lahu alkhalqu wal-amrutabaraka Allahu rabbu alAAalameen

Hausa
 
Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwănaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yană sanya dare ya rufa yini, yană nẽman sa da gaggawa, kuma rănă da wată da taurări hőrarru ne da umurninSa. To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tă bayyana!

Ayah  7:55  الأية
ادْعُوا رَبَّكُمْ تَضَرُّعًا وَخُفْيَةً ۚ إِنَّهُ لَا يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ
OdAAoo rabbakum tadarruAAanwakhufyatan innahu la yuhibbu almuAAtadeen

Hausa
 
Ku kirăyi Ubangijinku da ƙanƙan da kai, da kuma a ɓőye: lalle ne Shĩ, bă Yă son măsuwuce iyăka.

Ayah  7:56  الأية
وَلَا تُفْسِدُوا فِي الْأَرْضِ بَعْدَ إِصْلَاحِهَا وَادْعُوهُ خَوْفًا وَطَمَعًا ۚ إِنَّ رَحْمَتَ اللهِ قَرِيبٌ مِّنَ الْمُحْسِنِينَ
Wala tufsidoo fee al-ardibaAAda islahiha wadAAoohu khawfan watamaAAaninna rahmata Allahi qareebun mina almuhsineen

Hausa
 
Kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa a băyan gyaranta. Kuma ku kirăye shi sabőda tsőro da tsammăni; lalle ne rahamar Allah makusanciya ce daga măsu kyautatăwa.

Ayah  7:57  الأية
وَهُوَ الَّذِي يُرْسِلُ الرِّيَاحَ بُشْرًا بَيْنَ يَدَيْ رَحْمَتِهِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا أَقَلَّتْ سَحَابًا ثِقَالًا سُقْنَاهُ لِبَلَدٍ مَّيِّتٍ فَأَنزَلْنَا بِهِ الْمَاءَ فَأَخْرَجْنَا بِهِ مِن كُلِّ الثَّمَرَاتِ ۚ كَذَٰلِكَ نُخْرِجُ الْمَوْتَىٰ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ
Wahuwa allathee yursilu arriyahabushran bayna yaday rahmatihi hatta ithaaqallat sahaban thiqalan suqnahu libaladinmayyitin faanzalna bihi almaa faakhrajnabihi min kulli aththamarati kathalikanukhriju almawta laAAallakum tathakkaroon

Hausa
 
Kuma Shĩ ne wanda Yake aika iskőki, sună bishăra gaba ga rahamarSa, har idan sun ɗauki gizăgizai măsu nauyi, sai Mu kőra su ga wani gari matacce, sa'an nan Mu saukar da ruwa gare shi, sa'an nan Mu fitar, game da shi, daga dukkan 'ya'yan itĩce. Kamar wancan ne Muke fitar da matattu; tsammăninku, kună tunăni.

Ayah  7:58  الأية
وَالْبَلَدُ الطَّيِّبُ يَخْرُجُ نَبَاتُهُ بِإِذْنِ رَبِّهِ ۖ وَالَّذِي خَبُثَ لَا يَخْرُجُ إِلَّا نَكِدًا ۚ كَذَٰلِكَ نُصَرِّفُ الْآيَاتِ لِقَوْمٍ يَشْكُرُونَ
Walbaladu attayyibuyakhruju nabatuhu bi-ithni rabbihi wallatheekhabutha la yakhruju illa nakidan kathalikanusarrifu al-ayati liqawmin yashkuroon

Hausa
 
Kuma gari mai kyau, tsirinsa yană fita da iznin Ubangijinsa, kuma wanda ya mũnana, (tsirinsa) bă ya fita, făce da wahala; kamar wannan ne, Muka sarrafa ăyőyi dőmin mutăne waɗanda suke gődẽwa.

Ayah  7:59  الأية
لَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِ فَقَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ إِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ
Laqad arsalna noohan ilaqawmihi faqala ya qawmi oAAbudoo Allaha malakum min ilahin ghayruhu innee akhafu AAalaykumAAathaba yawmin AAatheem

Hausa
 
Lalle ne, haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutănẽnsa, sai ya ce: "Yă mutănẽna! Ku bauta waAllah! Bă ku da wani abin bautăwa waninSa. Lalle ne nĩ, ină yimuku tsőron azăbar wani Yini mai girma."

Ayah  7:60  الأية
قَالَ الْمَلَأُ مِن قَوْمِهِ إِنَّا لَنَرَاكَ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Qala almalao min qawmihi innalanaraka fee dalalin mubeen

Hausa
 
Mashawarta daga mutănensa suka ce: "Lalle ne mu, haƙĩƙa, Mună ganin ka a cikin ɓata bayyananniya."

Ayah  7:61  الأية
قَالَ يَا قَوْمِ لَيْسَ بِي ضَلَالَةٌ وَلَٰكِنِّي رَسُولٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ
Qala ya qawmi laysa bee dalalatunwalakinnee rasoolun min rabbi alAAalameen

Hausa
 
Ya ce: "Yă mutănena! Băbu ɓata guda gare ni, kuma amma nĩ Manzo ne daga ubangijin halittu !"

Ayah  7:62  الأية
أُبَلِّغُكُمْ رِسَالَاتِ رَبِّي وَأَنصَحُ لَكُمْ وَأَعْلَمُ مِنَ اللهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ
Oballighukum risalati rabbeewaansahu lakum waaAAlamu mina Allahi mala taAAlamoon

Hausa
 
"Ină iyar muku da săƙonnin Ubangijina; kuma ină yi muku nasĩha, kuma ină sani, daga Allah, abin da ba ku sani ba.

Ayah  7:63  الأية
أَوَعَجِبْتُمْ أَن جَاءَكُمْ ذِكْرٌ مِّن رَّبِّكُمْ عَلَىٰ رَجُلٍ مِّنكُمْ لِيُنذِرَكُمْ وَلِتَتَّقُوا وَلَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ
Awa AAajibtum an jaakum thikrunmin rabbikum AAala rajulin minkum liyunthirakumwalitattaqoo walaAAallakum turhamoon

Hausa
 
"Shin, kună mămăkin cẽwa ambato yă zo muku daga Ubangijinku a kan wani namiji, daga gare ku, dőmin ya yi muku gargaɗi, kuma dőmin ku yi taƙawa, kuma tsammăninku ană jin ƙanku?"

Ayah  7:64  الأية
فَكَذَّبُوهُ فَأَنجَيْنَاهُ وَالَّذِينَ مَعَهُ فِي الْفُلْكِ وَأَغْرَقْنَا الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمًا عَمِينَ
Fakaththaboohu faanjaynahu wallatheenamaAAahu fee alfulki waaghraqna allatheena kaththaboobi-ayatina innahum kanoo qawmanAAameen

Hausa
 
Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka tsĩrar da shi da waɗanda suke tăre da shi, a cikin jirgin; kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata shi game da ăyőyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance wasu mutăne ɗĩmautattu.

Ayah  7:65  الأية
وَإِلَىٰ عَادٍ أَخَاهُمْ هُودًا ۗ قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۚ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Wa-ila AAadin akhahumhoodan qala ya qawmi oAAbudoo Allaha malakum min ilahin ghayruhu afala tattaqoon

Hausa
 
Kuma zuwa ga Ădăwa, ɗan'uwansu Hudu, ya ce: "Ya mutănena! Ku baută wa Allah! Bă ku da wani abin baută wa, waninSa. Shin fa, bă ză ku yi taƙawa ba?"

Ayah  7:66  الأية
قَالَ الْمَلَأُ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن قَوْمِهِ إِنَّا لَنَرَاكَ فِي سَفَاهَةٍ وَإِنَّا لَنَظُنُّكَ مِنَ الْكَاذِبِينَ
Qala almalao allatheenakafaroo min qawmihi inna lanaraka fee safahatinwa-inna lanathunnuka mina alkathibeen

Hausa
 
Mashawarta waɗanda suka kăfirta daga mutănensa suka ce: "Lalle ne mũ, haƙĩƙka, Mună ganin ka a cikin wata wauta! Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, Mună zaton ka daga maƙaryata."

Ayah  7:67  الأية
قَالَ يَا قَوْمِ لَيْسَ بِي سَفَاهَةٌ وَلَٰكِنِّي رَسُولٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ
Qala ya qawmi laysa bee safahatunwalakinnee rasoolun min rabbi alAAalameen

Hausa
 
Ya ce: "Yă mutănena! Băbu wata wauta a gare ni, kuma amma nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu!"

Ayah  7:68  الأية
أُبَلِّغُكُمْ رِسَالَاتِ رَبِّي وَأَنَا لَكُمْ نَاصِحٌ أَمِينٌ
Oballighukum risalati rabbeewaana lakum nasihun ameen

Hausa
 
Ină iyar muku da săƙonnin Ubangijina, kuma nĩ, gare ku, mai nasĩha ne amintacce.

Ayah  7:69  الأية
أَوَعَجِبْتُمْ أَن جَاءَكُمْ ذِكْرٌ مِّن رَّبِّكُمْ عَلَىٰ رَجُلٍ مِّنكُمْ لِيُنذِرَكُمْ ۚ وَاذْكُرُوا إِذْ جَعَلَكُمْ خُلَفَاءَ مِن بَعْدِ قَوْمِ نُوحٍ وَزَادَكُمْ فِي الْخَلْقِ بَسْطَةً ۖ فَاذْكُرُوا آلَاءَ اللهِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Awa AAajibtum an jaakum thikrunmin rabbikum AAala rajulin minkum liyunthirakum wathkurooith jaAAalakum khulafaa min baAAdi qawmi noohinwazadakum fee alkhalqi bastatan fathkurooalaa Allahi laAAallakum tuflihoon

Hausa
 
"Shin, kuma kun yi mămăki cẽwa ambato daga Ubangijinku ya zo muku a kan wani namiji daga gare ku, dőmin ya yi muku gargaɗi? Kuma ku tună a lőkacin da Ya sanyă ku măsu mayẽwa daga băyan mutănen Nũhu, kuma Ya ƙăra muku zăti a cikin halitta. Sabőda haka ku tuna ni'imőmin Allah; tsammăninku kună cin nasara."

Ayah  7:70  الأية
قَالُوا أَجِئْتَنَا لِنَعْبُدَ اللهَ وَحْدَهُ وَنَذَرَ مَا كَانَ يَعْبُدُ آبَاؤُنَا ۖ فَأْتِنَا بِمَا تَعِدُنَا إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ
Qaloo aji/tana linaAAbuda Allahawahdahu wanathara ma kana yaAAbudu abaonafa/tina bima taAAiduna in kunta mina assadiqeen

Hausa
 
Suka ce: "Shin, kă zo mana ne dőmin mu bauta wa Allah Shi kaɗai, kuma mu bar abin da ubanninmu suka kasance sună bauta wa? To, ka ző mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi idan kă kasance daga măsu gaskiya."

Ayah  7:71  الأية
قَالَ قَدْ وَقَعَ عَلَيْكُم مِّن رَّبِّكُمْ رِجْسٌ وَغَضَبٌ ۖ أَتُجَادِلُونَنِي فِي أَسْمَاءٍ سَمَّيْتُمُوهَا أَنتُمْ وَآبَاؤُكُم مَّا نَزَّلَ اللهُ بِهَا مِن سُلْطَانٍ ۚ فَانتَظِرُوا إِنِّي مَعَكُم مِّنَ الْمُنتَظِرِينَ
Qala qad waqaAAa AAalaykum minrabbikum rijsun waghadabun atujadiloonanee fee asma-insammaytumooha antum waabaokum manazzala Allahu biha min sultanin fantathirooinnee maAAakum mina almuntathireen

Hausa
 
Ya ce: "Haƙĩƙa azăba da fushi sun auku a kanku daga Ubangijinku! Shin, kună jăyayya da ni a cikin wasu sunăye waɗanda kũ ne kuka yi musu sunăyen, kũ da ubanninku, Allah bai saukar da wani dalili ba a gare su? To, ku yi jira. Lalle ne ni, tăre da ku mai jira ne."

Ayah  7:72  الأية
فَأَنجَيْنَاهُ وَالَّذِينَ مَعَهُ بِرَحْمَةٍ مِّنَّا وَقَطَعْنَا دَابِرَ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا ۖ وَمَا كَانُوا مُؤْمِنِينَ
Faanjaynahu wallatheenamaAAahu birahmatin minna waqataAAna dabiraallatheena kaththaboo bi-ayatinawama kanoo mu/mineen

Hausa
 
To, sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da waɗanda suke tăre da shi sabőda wata rahama daga gare Mu, kuma Muka katse ƙarshen waɗanda suka ƙaryata game da ăyőyinMu, kuma ba su kasance mũminaiba.

Ayah  7:73  الأية
وَإِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَالِحًا ۗ قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۖ قَدْ جَاءَتْكُم بَيِّنَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ ۖ هَٰذِهِ نَاقَةُ اللهِ لَكُمْ آيَةً ۖ فَذَرُوهَا تَأْكُلْ فِي أَرْضِ اللهِ ۖ وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوءٍ فَيَأْخُذَكُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Wa-ila thamooda akhahum salihanqala ya qawmi oAAbudoo Allaha malakum min ilahin ghayruhu qad jaatkum bayyinatunmin rabbikum hathihi naqatu Allahi lakum ayatanfatharooha ta/kul fee ardi Allahi walatamassooha bisoo-in faya/khuthakum AAathabunaleem

Hausa
 
Kuma zuwa ga Samũdăwa ɗan'uwansu, Sălihu, ya ce: "Yă mutănena! Ku bauta wa Allah; bă ku da wani abin bauta wa wanninSa. Haƙĩƙa hujja bayyananniya tă zo muku daga Ubangijinku! wannan răƙumar Allah ce, a gare ku, wata ăyă ce. Sai ku bar ta ta ci, a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shăfe ta da wata cũta har azăba mai raɗaɗi ta kămă ku."

Ayah  7:74  الأية
وَاذْكُرُوا إِذْ جَعَلَكُمْ خُلَفَاءَ مِن بَعْدِ عَادٍ وَبَوَّأَكُمْ فِي الْأَرْضِ تَتَّخِذُونَ مِن سُهُولِهَا قُصُورًا وَتَنْحِتُونَ الْجِبَالَ بُيُوتًا ۖ فَاذْكُرُوا آلَاءَ اللهِ وَلَا تَعْثَوْا فِي الْأَرْضِ مُفْسِدِينَ
Wathkuroo ithjaAAalakum khulafaa min baAAdi AAadin wabawwaakumfee al-ardi tattakhithoona min suhooliha qusooranwatanhitoona aljibala buyootan fathkurooalaa Allahi wala taAAthaw fee al-ardimufsideen

Hausa
 
"Kuma ku tuna a lőkacin da Ya sanyă ku mamaya daga băyan Ădăwa kuma Ya zaunar da ku a cikin ƙasa, kună riƙon manyan gidăje daga tuddanta, kuma kună sassaƙar ɗăkuna daga duwătsu; sabőda haka ku tuna ni'imőmin Allah, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa kuna măsu fasădi."

Ayah  7:75  الأية
قَالَ الْمَلَأُ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا مِن قَوْمِهِ لِلَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا لِمَنْ آمَنَ مِنْهُمْ أَتَعْلَمُونَ أَنَّ صَالِحًا مُّرْسَلٌ مِّن رَّبِّهِ ۚ قَالُوا إِنَّا بِمَا أُرْسِلَ بِهِ مُؤْمِنُونَ
Qala almalao allatheenaistakbaroo min qawmihi lillatheena istudAAifooliman amana minhum ataAAlamoona anna salihanmursalun min rabbihi qaloo inna bima orsilabihi mu/minoon

Hausa
 
Mashawarta waɗanda suka yi girman kai daga mutanensa suka ce ga waɗanda aka raunanar, ga waɗanda suka yi ĩmăni daga gare su: "Shin, kună sanin cẽwaSălihu manzo ne daga Ubangijinsa?" Suka ce: "Lalle ne mũ, da abin daaka aiko shi, măsu ĩmăni ne."

Ayah  7:76  الأية
قَالَ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا إِنَّا بِالَّذِي آمَنتُم بِهِ كَافِرُونَ
Qala allatheena istakbaroo innabillathee amantum bihi kafiroon

Hausa
 
Waɗanda suka yi girman kai suka ce: "Lalle ne mu, ga abin da kuka yi ĩmăni da shi kăfirai ne."

Ayah  7:77  الأية
فَعَقَرُوا النَّاقَةَ وَعَتَوْا عَنْ أَمْرِ رَبِّهِمْ وَقَالُوا يَا صَالِحُ ائْتِنَا بِمَا تَعِدُنَا إِن كُنتَ مِنَ الْمُرْسَلِينَ
FaAAaqaroo annaqata waAAatawAAan amri rabbihim waqaloo ya salihui/tina bima taAAiduna in kunta minaalmursaleen

Hausa
 
Sai suka sőke răƙumar, kuma suka kangare daga barin umurnin Ubangijinsu, kuma suka ce: "Yă Sălihu! Ka ző mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi, idan kă kasance daga manzanni !"

Ayah  7:78  الأية
فَأَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ
Faakhathat-humu arrajfatu faasbahoofee darihim jathimeen

Hausa
 
Sai tsăwa ta kămă su, sabőda haka suka wăyi gari a cikin gidansu guggurfăne!

Ayah  7:79  الأية
فَتَوَلَّىٰ عَنْهُمْ وَقَالَ يَا قَوْمِ لَقَدْ أَبْلَغْتُكُمْ رِسَالَةَ رَبِّي وَنَصَحْتُ لَكُمْ وَلَٰكِن لَّا تُحِبُّونَ النَّاصِحِينَ
Fatawalla AAanhum waqala yaqawmi laqad ablaghtukum risalata rabbee wanasahtulakum walakin la tuhibboona annasiheen

Hausa
 
Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Ya mutănena! Lalle ne, haƙĩƙa, nă iyar muku damanzancin Ubangijina. Kuma nă yi muku nasĩha kuma amma bă ku son măsu nasĩha!"

Ayah  7:80  الأية
وَلُوطًا إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ أَتَأْتُونَ الْفَاحِشَةَ مَا سَبَقَكُم بِهَا مِنْ أَحَدٍ مِّنَ الْعَالَمِينَ
Walootan ith qalaliqawmihi ata/toona alfahishata ma sabaqakum bihamin ahadin mina alAAalameen

Hausa
 
Da Lũɗu, a lőkacin daya ce wa mutănensa: "Shin, kună jẽ wa alfăsha, băbu kőwa da ya gabăce ku da ita daga halittu?"

Ayah  7:81  الأية
إِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الرِّجَالَ شَهْوَةً مِّن دُونِ النِّسَاءِ ۚ بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ مُّسْرِفُونَ
Innakum lata/toona arrijalashahwatan min dooni annisa-i bal antum qawmunmusrifoon

Hausa
 
"Lalle ne ku, haƙĩƙa kună jẽ wa maza da sha'awa, baicin mata; Ă'a, kũ mutăne ne maɓarnata."

Ayah  7:82  الأية
وَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ إِلَّا أَن قَالُوا أَخْرِجُوهُم مِّن قَرْيَتِكُمْ ۖ إِنَّهُمْ أُنَاسٌ يَتَطَهَّرُونَ
Wama kana jawabaqawmihi illa an qaloo akhrijoohum min qaryatikuminnahum onasun yatatahharoon

Hausa
 
Kuma băbu abin da ya kasance jawăbin mutănensa, făce ɗai suka ce: "Ku fitar da su daga alƙaryarku: lalle ne sũ, wasumutăne ne măsu da'awar tsarki!"

Ayah  7:83  الأية
فَأَنجَيْنَاهُ وَأَهْلَهُ إِلَّا امْرَأَتَهُ كَانَتْ مِنَ الْغَابِرِينَ
Faanjaynahu waahlahu illaimraatahu kanat mina alghabireen

Hausa
 
Sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da iyălansa, făce matarsa, ta kasance daga măsu wanzuwa.

Ayah  7:84  الأية
وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِم مَّطَرًا ۖ فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُجْرِمِينَ
Waamtarna AAalayhim mataranfanthur kayfa kana AAaqibatualmujrimeen

Hausa
 
Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa; Sai ka dũba yadda ăƙibar măsu laifi ta kasance!

Ayah  7:85  الأية
وَإِلَىٰ مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْبًا ۗ قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۖ قَدْ جَاءَتْكُم بَيِّنَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ ۖ فَأَوْفُوا الْكَيْلَ وَالْمِيزَانَ وَلَا تَبْخَسُوا النَّاسَ أَشْيَاءَهُمْ وَلَا تُفْسِدُوا فِي الْأَرْضِ بَعْدَ إِصْلَاحِهَا ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
Wa-ila madyana akhahumshuAAayban qala ya qawmi oAAbudoo Allaha malakum min ilahin ghayruhu qad jaatkum bayyinatunmin rabbikum faawfoo alkayla walmeezana walatabkhasoo annasa ashyaahum walatufsidoo fee al-ardi baAAda islahiha thalikumkhayrun lakum in kuntum mu/mineen

Hausa
 
Kuma zuwa Madayana ɗan'uwansu Shu'aibu, ya ce: "Ya mutănena! Ku bauta wa Allah; bă ku da wani abin bauta wa waninSa. Lalle ne, wata hujja bayyananniya daga Ubangijinku tă ző muku! Sai ku cika mũdu da sikeli kumakada ku nakasa wa mutăne kăyansu, kuma kada ku yi fasădi a cikin ƙasa a băyan gyaranta. Wannan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance mũminai."

Ayah  7:86  الأية
وَلَا تَقْعُدُوا بِكُلِّ صِرَاطٍ تُوعِدُونَ وَتَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللهِ مَنْ آمَنَ بِهِ وَتَبْغُونَهَا عِوَجًا ۚ وَاذْكُرُوا إِذْ كُنتُمْ قَلِيلًا فَكَثَّرَكُمْ ۖ وَانظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُفْسِدِينَ
Wala taqAAudoo bikulli siratintooAAidoona watasuddoona AAan sabeeli Allahi man amanabihi watabghoonaha AAiwajan wathkuroo ithkuntum qaleelan fakaththarakum wanthurookayfa kana AAaqibatu almufsideen

Hausa
 
"Kuma kada ku zauna ga kőwane tafarki kună ƙyacẽwa, kuma kună kangẽwa, daga hanyar Allah, ga wanda ya yi ĩmăni da shi, kuma kună nẽman ta ta zama karkatacciya, kuma ku tuna, a lőkacin da kuka kasance kaɗan, sai Ya yawaita ku, kuma ku dũba yadda ăƙibar măsu fasădi ta kasance:"

Ayah  7:87  الأية
وَإِن كَانَ طَائِفَةٌ مِّنكُمْ آمَنُوا بِالَّذِي أُرْسِلْتُ بِهِ وَطَائِفَةٌ لَّمْ يُؤْمِنُوا فَاصْبِرُوا حَتَّىٰ يَحْكُمَ اللهُ بَيْنَنَا ۚ وَهُوَ خَيْرُ الْحَاكِمِينَ
Wa-in kana ta-ifatun minkum amanoobillathee orsiltu bihi wata-ifatun lamyu/minoo fasbiroo hatta yahkumaAllahu baynana wahuwa khayru alhakimeen

Hausa
 
"Kuma idan wata ƙungiya daga gare ku ta kasance ta yi ĩmăni da abin da aka aiko ni da shi, kuma wata ƙungiya ba ta yi ĩmăni ba, to, ku yi haƙuri, har Allah Ya yi hukunci a tsakăninmu; kuma Shi ne Mafi alhẽrin măsu hukunci."

Ayah  7:88  الأية
قَالَ الْمَلَأُ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا مِن قَوْمِهِ لَنُخْرِجَنَّكَ يَا شُعَيْبُ وَالَّذِينَ آمَنُوا مَعَكَ مِن قَرْيَتِنَا أَوْ لَتَعُودُنَّ فِي مِلَّتِنَا ۚ قَالَ أَوَلَوْ كُنَّا كَارِهِينَ
Qala almalao allatheenaistakbaroo min qawmihi lanukhrijannaka ya shuAAaybu wallatheenaamanoo maAAaka min qaryatina aw lataAAoodunna feemillatina qala awa law kunna kariheen

Hausa
 
Mashawarta waɗanda suka kangare daga mutănensa, suka ce: "Lalle ne, Mună fitar da kai, Yă Shu'aibu, kai da waɗanda suka yi Ĩmăni tăre da kai, daga alƙaryarmu; kő kuwa lalle ku kőmo a cikin addininmu." Ya ce: "Ashe! Kuma kő dă mun kasance măsu ƙĩ?"

Ayah  7:89  الأية
قَدِ افْتَرَيْنَا عَلَى اللهِ كَذِبًا إِنْ عُدْنَا فِي مِلَّتِكُم بَعْدَ إِذْ نَجَّانَا اللهُ مِنْهَا ۚ وَمَا يَكُونُ لَنَا أَن نَّعُودَ فِيهَا إِلَّا أَن يَشَاءَ اللهُ رَبُّنَا ۚ وَسِعَ رَبُّنَا كُلَّ شَيْءٍ عِلْمًا ۚ عَلَى اللهِ تَوَكَّلْنَا ۚ رَبَّنَا افْتَحْ بَيْنَنَا وَبَيْنَ قَوْمِنَا بِالْحَقِّ وَأَنتَ خَيْرُ الْفَاتِحِينَ
Qadi iftarayna AAala Allahikathiban in AAudna fee millatikum baAAda ithnajjana Allahu minha wamayakoonu lana an naAAooda feeha illa an yashaaAllahu rabbuna wasiAAa rabbuna kulla shay-inAAilman AAala Allahi tawakkalna rabbanaiftah baynana wabayna qawmina bilhaqqiwaanta khayru alfatiheen

Hausa
 
"Lalle ne mun ƙirƙira ƙarya ga Allah idan mun kőma a cikin addininku a băyan lőkacin da Allah ya tsĩrar da mu daga gare shi, kuma bă ya kasancewa a gare mu, mu kőma a cikinsa, făce idan Al1ah, Ubangijinmu Ya so. Ubangijinmu Yă yalwaci dukan kőme ga ilmi. Ga Allah muka dőgara. Yă Ubangijinmu! Ka yi hukunci a tsakăninmu da tsakanin mutănenmu da gaskiya, kuma Kai ne Mafi alhẽrin măsu hukunci."

Ayah  7:90  الأية
وَقَالَ الْمَلَأُ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن قَوْمِهِ لَئِنِ اتَّبَعْتُمْ شُعَيْبًا إِنَّكُمْ إِذًا لَّخَاسِرُونَ
Waqala almalao allatheenakafaroo min qawmihi la-ini ittabaAAtum shuAAayban innakum ithanlakhasiroon

Hausa
 
Kuma mashawarta waɗanda suka kăfirta daga mutănensa, suka ce: "Lalle ne, idan kun bi Shu'aibu haƙĩƙa kũ, a lőkacin nan, măsu hasăra ne."

Ayah  7:91  الأية
فَأَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ
Faakhathat-humu arrajfatu faasbahoofee darihim jathimeen

Hausa
 
Sai tsăwa ta kăma su, sabőda haka suka wăyi gari, a cikin gidansu, sună guggurfăne.

Ayah  7:92  الأية
الَّذِينَ كَذَّبُوا شُعَيْبًا كَأَن لَّمْ يَغْنَوْا فِيهَا ۚ الَّذِينَ كَذَّبُوا شُعَيْبًا كَانُوا هُمُ الْخَاسِرِينَ
Allatheena kaththabooshuAAayban kaan lam yaghnaw feeha allatheena kaththabooshuAAayban kanoo humu alkhasireen

Hausa
 
Waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu kamar ba su zauna ba a cikinta, waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu, sun kasance sũ nemăsu hasăra!

Ayah  7:93  الأية
فَتَوَلَّىٰ عَنْهُمْ وَقَالَ يَا قَوْمِ لَقَدْ أَبْلَغْتُكُمْ رِسَالَاتِ رَبِّي وَنَصَحْتُ لَكُمْ ۖ فَكَيْفَ آسَىٰ عَلَىٰ قَوْمٍ كَافِرِينَ
Fatawalla AAanhum waqala yaqawmi laqad ablaghtukum risalati rabbee wanasahtulakum fakayfa asa AAala qawmin kafireen

Hausa
 
Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Yă mutănena! Haƙĩƙa, nă iyar muku da săƙonnin Ubangijina, kuma nă yi muku nasĩha! To, yăya zan yi baƙin ciki a kan mutăne kăfirai?"

Ayah  7:94  الأية
وَمَا أَرْسَلْنَا فِي قَرْيَةٍ مِّن نَّبِيٍّ إِلَّا أَخَذْنَا أَهْلَهَا بِالْبَأْسَاءِ وَالضَّرَّاءِ لَعَلَّهُمْ يَضَّرَّعُونَ
Wama arsalna fee qaryatin minnabiyyin illa akhathna ahlaha bilba/sa-iwaddarra-i laAAallahum yaddarraAAoon

Hausa
 
Kuma ba Mu aika wani Annabi a cikin wata alƙarya ba, făce Mun kăma mutănenta da azăba da cũta, tsammăninsu sună yin ƙasƙantar da kai.

Ayah  7:95  الأية
ثُمَّ بَدَّلْنَا مَكَانَ السَّيِّئَةِ الْحَسَنَةَ حَتَّىٰ عَفَوا وَّقَالُوا قَدْ مَسَّ آبَاءَنَا الضَّرَّاءُ وَالسَّرَّاءُ فَأَخَذْنَاهُم بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
Thumma baddalna makana assayyi-atialhasanata hatta AAafaw waqaloo qadmassa abaana addarraowassarrao faakhathnahum baghtatanwahum la yashAAuroon

Hausa
 
Sa'an nan kuma Muka musanya mai kyau a matsayin mummũna, har su yi yawa, kuma su ce: "Cũta da azăba sun shăfi ubanninmu." ( sai su kőma wa kăfirci). Sai Mu kămă su kwatsam! alhăli kuwa sũ, bă su sansancẽwa."

Ayah  7:96  الأية
وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْقُرَىٰ آمَنُوا وَاتَّقَوْا لَفَتَحْنَا عَلَيْهِم بَرَكَاتٍ مِّنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ وَلَٰكِن كَذَّبُوا فَأَخَذْنَاهُم بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ
Walaw anna ahla alqura amanoowattaqaw lafatahna AAalayhim barakatinmina assama-i wal-ardi walakinkaththaboo faakhathnahum bima kanooyaksiboon

Hausa
 
Kuma dă lalle mutănen alƙaryu sun yi ĩmăni kuma suka yi taƙawa dă haƙĩƙa Mun bũɗe albarkőki a kansu daga sama da ƙasa, kuma amma sun ƙaryata, don haka Muka kăma su da abin da suka kasance sună tărăwa.

Ayah  7:97  الأية
أَفَأَمِنَ أَهْلُ الْقُرَىٰ أَن يَأْتِيَهُم بَأْسُنَا بَيَاتًا وَهُمْ نَائِمُونَ
Afaamina ahlu alqura an ya/tiyahumba/suna bayatan wahum na-imoon

Hausa
 
Shin, mutănen alƙaryu sun amince wa azăbar Mu ta jẽ musu da dare, alhăli kuwa sună barci?

Ayah  7:98  الأية
أَوَأَمِنَ أَهْلُ الْقُرَىٰ أَن يَأْتِيَهُم بَأْسُنَا ضُحًى وَهُمْ يَلْعَبُونَ
Awa amina ahlu alqura an ya/tiyahumba/suna duhan wahum yalAAaboon

Hausa
 
Kő kuwa mutănen alƙaryu sun amince wa azăbarMu ta jẽ musu da hantsi, alhăli kuwa sună wăsa?

Ayah  7:99  الأية
أَفَأَمِنُوا مَكْرَ اللهِ ۚ فَلَا يَأْمَنُ مَكْرَ اللهِ إِلَّا الْقَوْمُ الْخَاسِرُونَ
Afaaminoo makra Allahi falaya/manu makra Allahi illa alqawmu alkhasiroon

Hausa
 
Shin fa, sun amince wa makarun Allah? To, băbu mai amince wa makarun Allah făce mutăne măsu hasăra!

Ayah  7:100  الأية
أَوَلَمْ يَهْدِ لِلَّذِينَ يَرِثُونَ الْأَرْضَ مِن بَعْدِ أَهْلِهَا أَن لَّوْ نَشَاءُ أَصَبْنَاهُم بِذُنُوبِهِمْ ۚ وَنَطْبَعُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لَا يَسْمَعُونَ
Awa lam yahdi lillatheena yarithoonaal-arda min baAAdi ahliha an law nashao asabnahumbithunoobihim wanatbaAAu AAala quloobihimfahum la yasmaAAoon

Hausa
 
Shin, kuma bai shiryar da waɗanda suke gădon ƙasa ba daga băyan mutănenta cẽwa da Mună so, dă Mun săme su da zunubansu, kuma Mu rufe a kan zukătansu, sai su zama bă su ji?

Ayah  7:101  الأية
تِلْكَ الْقُرَىٰ نَقُصُّ عَلَيْكَ مِنْ أَنبَائِهَا ۚ وَلَقَدْ جَاءَتْهُمْ رُسُلُهُم بِالْبَيِّنَاتِ فَمَا كَانُوا لِيُؤْمِنُوا بِمَا كَذَّبُوا مِن قَبْلُ ۚ كَذَٰلِكَ يَطْبَعُ اللهُ عَلَىٰ قُلُوبِ الْكَافِرِينَ
Tilka alqura naqussu AAalaykamin anba-iha walaqad jaat-hum rusuluhum bilbayyinatifama kanoo liyu/minoo bima kaththaboomin qablu kathalika yatbaAAu Allahu AAalaquloobi alkafireen

Hausa
 
Waɗancan alƙaryu Mună gaya maka daga lăbăransu, kuma lalle ne, haƙĩƙa manzanninMu sun jẽ musu da hujjőji bayyanannnu; to, ba su kasance sună yin ĩmănida abin da suka ƙaryata daga gabăni ba. Kamar wancan ne Allah Yake rufẽwa a kan zukătan kăfirai.

Ayah  7:102  الأية
وَمَا وَجَدْنَا لِأَكْثَرِهِم مِّنْ عَهْدٍ ۖ وَإِن وَجَدْنَا أَكْثَرَهُمْ لَفَاسِقِينَ
Wama wajadna li-aktharihimmin AAahdin wa-in wajadna aktharahum lafasiqeen

Hausa
 
Kuma ba Mu sămi wani alkawari ba ga mafi yawansu, kuma lalle ne, Mun sămi mafi yawansu, haƙĩƙa, făsiƙai.

Ayah  7:103  الأية
ثُمَّ بَعَثْنَا مِن بَعْدِهِم مُّوسَىٰ بِآيَاتِنَا إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِ فَظَلَمُوا بِهَا ۖ فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُفْسِدِينَ
Thumma baAAathna min baAAdihim moosabi-ayatina ila firAAawna wamala-ihifathalamoo biha fanuthurkayfa kana AAaqibatu almufsideen

Hausa
 
Sa'an nan kuma Mun aika Musa, daga băyansu, da ăyőyinMu zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka yi zălunci game da su. To, dũbi yadda ăƙibar maɓarnata take.

Ayah  7:104  الأية
وَقَالَ مُوسَىٰ يَا فِرْعَوْنُ إِنِّي رَسُولٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ
Waqala moosa yafirAAawnu innee rasoolun min rabbi alAAalameen

Hausa
 
Kuma Musa ya ce: "Ya Fir'auna! Lalle ne nĩ, manzo ne daga Ubangijin halittu."

Ayah  7:105  الأية
حَقِيقٌ عَلَىٰ أَن لَّا أَقُولَ عَلَى اللهِ إِلَّا الْحَقَّ ۚ قَدْ جِئْتُكُم بِبَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ فَأَرْسِلْ مَعِيَ بَنِي إِسْرَائِيلَ
Haqeequn AAala an laaqoola AAala Allahi illa alhaqqa qadji/tukum bibayyinatin min rabbikum faarsil maAAiya banee isra-eel

Hausa
 
"Tabbatacce ne a kan kada in faɗi kőme ga Allah făce gaskiya. Lalle ne, nă zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku; Sai ka saki Banĩ Isră'ila tăreda ni."

Ayah  7:106  الأية
قَالَ إِن كُنتَ جِئْتَ بِآيَةٍ فَأْتِ بِهَا إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ
Qala in kunta ji/ta bi-ayatinfa/ti biha in kunta mina assadiqeen

Hausa
 
Ya ce: "Idan kă kasance kă zo da wata ăyă, to, ka kăwő ta, idan kă kasance daga măsu gaskiya."

Ayah  7:107  الأية
فَأَلْقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعْبَانٌ مُّبِينٌ
Faalqa AAasahu fa-ithahiya thuAAbanun mubeen

Hausa
 
Sai ya jẽfa sandarsa, sai gă ta kumurci bayyananne!

Ayah  7:108  الأية
وَنَزَعَ يَدَهُ فَإِذَا هِيَ بَيْضَاءُ لِلنَّاظِرِينَ
WanazaAAa yadahu fa-itha hiya baydaolinnathireen

Hausa
 
Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga măsu dũbi!

Ayah  7:109  الأية
قَالَ الْمَلَأُ مِن قَوْمِ فِرْعَوْنَ إِنَّ هَٰذَا لَسَاحِرٌ عَلِيمٌ
Qala almalao min qawmi firAAawnainna hatha lasahirun AAaleem

Hausa
 
Mashăwarta daga mutănen Fir'auna suka ce: "Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, matsafi ne mai ilmi."

Ayah  7:110  الأية
يُرِيدُ أَن يُخْرِجَكُم مِّنْ أَرْضِكُمْ ۖ فَمَاذَا تَأْمُرُونَ
Yureedu an yukhrijakum min ardikumfamatha ta/muroon

Hausa
 
" Yană son ya fitar da ku daga ƙasarku: To, mẽne ne kuke shawartawa?"

Ayah  7:111  الأية
قَالُوا أَرْجِهْ وَأَخَاهُ وَأَرْسِلْ فِي الْمَدَائِنِ حَاشِرِينَ
Qaloo arjih waakhahu waarsilfee almada-ini hashireen

Hausa
 
Suka ce: "Ka jinkirtar da shĩ, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika da măsu gayyar mutăne a cikin garũruwa.

Ayah  7:112  الأية
يَأْتُوكَ بِكُلِّ سَاحِرٍ عَلِيمٍ
Ya/tooka bikulli sahirin AAaleem

Hausa
 
"Su ző maka da duka matsafi, mai ilmi."

Ayah  7:113  الأية
وَجَاءَ السَّحَرَةُ فِرْعَوْنَ قَالُوا إِنَّ لَنَا لَأَجْرًا إِن كُنَّا نَحْنُ الْغَالِبِينَ
Wajaa assaharatufirAAawna qaloo inna lana laajran in kunnanahnu alghalibeen

Hausa
 
Kuma matsafa suka jẽ wa fir'aună suka ce: "Lalle ne, shin, Mună da ijăra, idan mun kasance mũ ne marinjaya?"

Ayah  7:114  الأية
قَالَ نَعَمْ وَإِنَّكُمْ لَمِنَ الْمُقَرَّبِينَ
Qala naAAam wa-innakum laminaalmuqarrabeen

Hausa
 
Ya ce: "Na, am kuma lalle ne kună a cikin makusanta."

Ayah  7:115  الأية
قَالُوا يَا مُوسَىٰ إِمَّا أَن تُلْقِيَ وَإِمَّا أَن نَّكُونَ نَحْنُ الْمُلْقِينَ
Qaloo ya moosa immaan tulqiya wa-imma an nakoona nahnu almulqeen

Hausa
 
Suka ce: "Ya Mũsă! Kő dai ka jẽfa, kő kuwa mu kasance, mũ ne, măsu jẽfăwa?"

Ayah  7:116  الأية
قَالَ أَلْقُوا ۖ فَلَمَّا أَلْقَوْا سَحَرُوا أَعْيُنَ النَّاسِ وَاسْتَرْهَبُوهُمْ وَجَاءُوا بِسِحْرٍ عَظِيمٍ
Qala alqoo falamma alqaw saharooaAAyuna annasi wastarhaboohum wajaoobisihrin AAatheem

Hausa
 
Ya ce: "Ku jẽfa." To a 1őkacin da suka jẽfa, suka sihirce idănun mutăne kuma suka tsőratar da su; Kuma suka jẽ da tsafi mai girma."

Ayah  7:117  الأية
وَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ مُوسَىٰ أَنْ أَلْقِ عَصَاكَ ۖ فَإِذَا هِيَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ
Waawhayna ila moosaan alqi AAasaka fa-itha hiya talqafu maya/fikoon

Hausa
 
Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsă cẽwa: "Ka jẽfa sandarka." Sai gă ta tană lăƙumar abin da suke ƙarya da shi!

Ayah  7:118  الأية
فَوَقَعَ الْحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
FawaqaAAa alhaqqu wabatala makanoo yaAAmaloon

Hausa
 
Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatăwa ya ɓăci.

Ayah  7:119  الأية
فَغُلِبُوا هُنَالِكَ وَانقَلَبُوا صَاغِرِينَ
Faghuliboo hunalika wanqalaboosaghireen

Hausa
 
Sai aka rinjăye su a can, kuma suka jũya sună ƙasƙantattu.

Ayah  7:120  الأية
وَأُلْقِيَ السَّحَرَةُ سَاجِدِينَ
Waolqiya assaharatu sajideen

Hausa
 
Kuma aka jẽfar da matsafan, sună măsu sujada.

Ayah  7:121  الأية
قَالُوا آمَنَّا بِرَبِّ الْعَالَمِينَ
Qaloo amanna birabbialAAalameen

Hausa
 
Suka ce: "Mun yi ĩmăni da Ubangijin halittu."

Ayah  7:122  الأية
رَبِّ مُوسَىٰ وَهَارُونَ
Rabbi moosa waharoon

Hausa
 
"Ubangijin Mũsă da Harũna."

Ayah  7:123  الأية
قَالَ فِرْعَوْنُ آمَنتُم بِهِ قَبْلَ أَنْ آذَنَ لَكُمْ ۖ إِنَّ هَٰذَا لَمَكْرٌ مَّكَرْتُمُوهُ فِي الْمَدِينَةِ لِتُخْرِجُوا مِنْهَا أَهْلَهَا ۖ فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ
Qala firAAawnu amantum bihiqabla an athana lakum inna hatha lamakrunmakartumoohu fee almadeenati litukhrijoo minha ahlahafasawfa taAAlamoon

Hausa
 
Fir'auna ya ce: "Ashe, kun yi ĩmăni da shi a gabănin inyi izni a gare ku? Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, măkirci ne kuka măkirta a cikin birni, dőmin ku fitar da mutănensa daga gare shi; To, da sannu ză ku sani."

Ayah  7:124  الأية
لَأُقَطِّعَنَّ أَيْدِيَكُمْ وَأَرْجُلَكُم مِّنْ خِلَافٍ ثُمَّ لَأُصَلِّبَنَّكُمْ أَجْمَعِينَ
LaoqatiAAanna aydiyakum waarjulakummin khilafin thumma laosallibannakum ajmaAAeen

Hausa
 
"Lalle ne, ină karkătse hannăyenku da ƙafăfunku daga săɓăni, sa'an nan kuma, haƙĩƙa, ină tsĩre, ku gabă ɗaya."

Ayah  7:125  الأية
قَالُوا إِنَّا إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ
Qaloo inna ila rabbinamunqaliboon

Hausa
 
Suka ce: "Lalle ne mu, zuwa ga Ubangijinmu, măsu jũyăwa ne."

Ayah  7:126  الأية
وَمَا تَنقِمُ مِنَّا إِلَّا أَنْ آمَنَّا بِآيَاتِ رَبِّنَا لَمَّا جَاءَتْنَا ۚ رَبَّنَا أَفْرِغْ عَلَيْنَا صَبْرًا وَتَوَفَّنَا مُسْلِمِينَ
Wama tanqimu minna illaan amanna bi-ayati rabbinalamma jaatna rabbana afrigh AAalaynasabran watawaffana muslimeen

Hausa
 
"Kuma bă ka zargin kőme daga gare mu făce dőmin mun yi ĩmăni da ăyőyin Ubangijinmu a lőkacin da suka ző mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu, kuma Ka cika mana mună Musulmai! "

Ayah  7:127  الأية
وَقَالَ الْمَلَأُ مِن قَوْمِ فِرْعَوْنَ أَتَذَرُ مُوسَىٰ وَقَوْمَهُ لِيُفْسِدُوا فِي الْأَرْضِ وَيَذَرَكَ وَآلِهَتَكَ ۚ قَالَ سَنُقَتِّلُ أَبْنَاءَهُمْ وَنَسْتَحْيِي نِسَاءَهُمْ وَإِنَّا فَوْقَهُمْ قَاهِرُونَ
Waqala almalao min qawmi firAAawnaatatharu moosa waqawmahu liyufsidoo fee al-ardiwayatharaka waalihataka qala sanuqattilu abnaahumwanastahyee nisaahum wa-inna fawqahum qahiroon

Hausa
 
Kuma mashawarta daga mutănen Fir'auna suka ce: "Shin, ză ka bar Mũsă da mutănensa dőmin su yi ɓarna a cikin ƙasa, kuma ya bar ka, kai da gumăkanka?" Ya ce: "Ză mu yayyanka ɗiyansu maza kuma mu răya mătansu; kuma lalle ne mũ, a bisa gare su, marinjăya ne."

Ayah  7:128  الأية
قَالَ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِ اسْتَعِينُوا بِاللهِ وَاصْبِرُوا ۖ إِنَّ الْأَرْضَ لِلَّهِ يُورِثُهَا مَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ ۖ وَالْعَاقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ
Qala moosa liqawmihiistaAAeenoo billahi wasbiroo innaal-arda lillahi yoorithuha man yashaomin AAibadihi walAAaqibatu lilmuttaqeen

Hausa
 
Mũsă ya ce wa mutănensa: "Ku nẽmi taimako da Allah, kuma ku yi haƙuri; Lalle ne ƙasa ta Allah ce, Yăna gădar da ita ga wanda Yake so daga băyinSa, kuma ăƙiba ta măsu taƙawa ce."

Ayah  7:129  الأية
قَالُوا أُوذِينَا مِن قَبْلِ أَن تَأْتِيَنَا وَمِن بَعْدِ مَا جِئْتَنَا ۚ قَالَ عَسَىٰ رَبُّكُمْ أَن يُهْلِكَ عَدُوَّكُمْ وَيَسْتَخْلِفَكُمْ فِي الْأَرْضِ فَيَنظُرَ كَيْفَ تَعْمَلُونَ
Qaloo ootheena minqabli an ta/tiyana wamin baAAdi ma ji/tana qalaAAasa rabbukum an yuhlika AAaduwwakum wayastakhlifakum feeal-ardi fayanthura kayfa taAAmaloon

Hausa
 
Suka ce: "An cũtar da mu daga gabănin ka ző mana, kuma daga băyan da kă ző mana." Ya ce: "Akwai tsammănin Ubangijinku, Ya halaka maƙiyanku, kuma Ya sanya ku, ku maye a cikin ƙasa, sa'an nan Ya dũba yadda kuke aikatăwa."

Ayah  7:130  الأية
وَلَقَدْ أَخَذْنَا آلَ فِرْعَوْنَ بِالسِّنِينَ وَنَقْصٍ مِّنَ الثَّمَرَاتِ لَعَلَّهُمْ يَذَّكَّرُونَ
Walaqad akhathna alafirAAawna bissineena wanaqsin mina aththamaratilaAAallahum yaththakkaroon

Hausa
 
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun kăma mutănen Fir'auna da tsananin shẽkaru (fari) da nakasa daga 'ya'yan ităce; Tsammăninsu sună tunăwa.

Ayah  7:131  الأية
فَإِذَا جَاءَتْهُمُ الْحَسَنَةُ قَالُوا لَنَا هَٰذِهِ ۖ وَإِن تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌ يَطَّيَّرُوا بِمُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُ ۗ أَلَا إِنَّمَا طَائِرُهُمْ عِندَ اللهِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Fa-itha jaat-humu alhasanatuqaloo lana hathihi wa-in tusibhumsayyi-atun yattayyaroo bimoosa waman maAAahu alainnama ta-iruhum AAinda Allahi walakinnaaktharahum la yaAAlamoon

Hausa
 
Sa'an nan idan wani alhẽri ya jẽ musu, sai su ce: "Masĩfa ta săme su, sai su yi shu'umci da Mũsă da wanda yake tăre da shi, To, shu'umcinsu a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawansu bă su sani!"

Ayah  7:132  الأية
وَقَالُوا مَهْمَا تَأْتِنَا بِهِ مِنْ آيَةٍ لِّتَسْحَرَنَا بِهَا فَمَا نَحْنُ لَكَ بِمُؤْمِنِينَ
Waqaloo mahma ta/tinabihi min ayatin litasharana biha famanahnu laka bimu/mineen

Hausa
 
Kuma suka ce: "Kő me ka ző mana da shi daga ăyă, dőmin ka sihirce mu da ita, to, baza mu zama, sabőda kai, măsu ĩmăni ba."

Ayah  7:133  الأية
فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمُ الطُّوفَانَ وَالْجَرَادَ وَالْقُمَّلَ وَالضَّفَادِعَ وَالدَّمَ آيَاتٍ مُّفَصَّلَاتٍ فَاسْتَكْبَرُوا وَكَانُوا قَوْمًا مُّجْرِمِينَ
Faarsalna AAalayhimu attoofanawaljarada walqummala waddafadiAAawaddama ayatin mufassalatinfastakbaroo wakanoo qawman mujrimeen

Hausa
 
Sai Muka aika a kansu da cikőwa, da făra, da ƙwarƙwata da kwăɗi, da jini; ăyőyi abũbuwan rarrabẽwa; Sai suka kangare, kuma suka kasance mutăne măsu laifi.

Ayah  7:134  الأية
وَلَمَّا وَقَعَ عَلَيْهِمُ الرِّجْزُ قَالُوا يَا مُوسَى ادْعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِندَكَ ۖ لَئِن كَشَفْتَ عَنَّا الرِّجْزَ لَنُؤْمِنَنَّ لَكَ وَلَنُرْسِلَنَّ مَعَكَ بَنِي إِسْرَائِيلَ
Walamma waqaAAa AAalayhimu arrijzuqaloo ya moosa odAAu lana rabbaka bimaAAahida AAindaka la-in kashafta AAanna arrijzalanu/minanna laka walanursilanna maAAaka banee isra-eel

Hausa
 
Kuma a lőkacin da masĩfa ta auku a kansu, sukan ce: "Yă Mũsă! Ka rőƙa mana Ubangijinka, sabőda abin da Ya yi alkwari a wurinka, lalle ne idan ka kau da azăbar daga barinmu, haƙĩƙa Mună ĩmăni sabőda kai, kuma mună sakin Banĩ Isră'ila tĩre da kai."

Ayah  7:135  الأية
فَلَمَّا كَشَفْنَا عَنْهُمُ الرِّجْزَ إِلَىٰ أَجَلٍ هُم بَالِغُوهُ إِذَا هُمْ يَنكُثُونَ
Falamma kashafna AAanhumu arrijzaila ajalin hum balighoohu itha humyankuthoon

Hausa
 
To, a lőkacin da Muka kuranye azăba daga barinsu zuwa a wani ajali wanda suke măsu iske shi ne, sai gă su sună warwarẽwa!

Ayah  7:136  الأية
فَانتَقَمْنَا مِنْهُمْ فَأَغْرَقْنَاهُمْ فِي الْيَمِّ بِأَنَّهُمْ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَكَانُوا عَنْهَا غَافِلِينَ
Fantaqamna minhum faaghraqnahumfee alyammi bi-annahum kaththaboo bi-ayatinawakanoo AAanha ghafileen

Hausa
 
Sai Muka yi azăbar rămuwa, daga gare su, sabőda haka Muka nutsar da su a cikin tẽku, dőmin lalle ne sũ, sun ƙaryata game da ăyőyinMu, kuma sun kasance daga barinsu, găfilai.

Ayah  7:137  الأية
وَأَوْرَثْنَا الْقَوْمَ الَّذِينَ كَانُوا يُسْتَضْعَفُونَ مَشَارِقَ الْأَرْضِ وَمَغَارِبَهَا الَّتِي بَارَكْنَا فِيهَا ۖ وَتَمَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ الْحُسْنَىٰ عَلَىٰ بَنِي إِسْرَائِيلَ بِمَا صَبَرُوا ۖ وَدَمَّرْنَا مَا كَانَ يَصْنَعُ فِرْعَوْنُ وَقَوْمُهُ وَمَا كَانُوا يَعْرِشُونَ
Waawrathna alqawma allatheenakanoo yustadAAafoona mashariqa al-ardiwamagharibaha allatee barakna feehawatammat kalimatu rabbika alhusna AAalabanee isra-eela bima sabaroo wadammarnama kana yasnaAAu firAAawnu waqawmuhu wamakanoo yaAArishoon

Hausa
 
Kuma Muka gădar da mutănen, waɗanda sun kasance ană raunana su, a gabacin ƙasa da yammacinta, wadda Muka sanya albarka a cikinta, kuma kalmar Ubangijinka mai kyau ta cika a kan Banĩ Isră'ĩla, sabőda abin dasuka yi na haƙuri. Kuma Muka murtsuke abin da Fir'auna da mutănensa suka kasance sună sană'antawa, da abin da suka kasance sună shimfiɗăwa.

Ayah  7:138  الأية
وَجَاوَزْنَا بِبَنِي إِسْرَائِيلَ الْبَحْرَ فَأَتَوْا عَلَىٰ قَوْمٍ يَعْكُفُونَ عَلَىٰ أَصْنَامٍ لَّهُمْ ۚ قَالُوا يَا مُوسَى اجْعَل لَّنَا إِلَٰهًا كَمَا لَهُمْ آلِهَةٌ ۚ قَالَ إِنَّكُمْ قَوْمٌ تَجْهَلُونَ
Wajawazna bibanee isra-eelaalbahra faataw AAala qawmin yaAAkufoona AAalaasnamin lahum qaloo ya moosaijAAal lana ilahan kama lahum alihatunqala innakum qawmun tajhaloon

Hausa
 
Kuma Muka ƙẽtarar da Banĩ Isra'ila ga tẽku, sai suka jẽ a kan wasu mutăne waɗanda sună lizimta da ibăda a kan wasu gumăka, năsu suka ce: "Yă Mũsă! Ka sanya mana wani abin bautawa kamar yadda suke da abũbuwan bautăwa " Ya ce: "Lalle ne kũ, mutăne ne kună jahilta."

Ayah  7:139  الأية
إِنَّ هَٰؤُلَاءِ مُتَبَّرٌ مَّا هُمْ فِيهِ وَبَاطِلٌ مَّا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Inna haola-i mutabbarun mahum feehi wabatilun ma kanoo yaAAmaloon

Hausa
 
"Lalle ne waɗannan, abin da suke a cikinsa halakakke ne, kuma abin da suka kasance sună aikătawa ƙarya ne."

Ayah  7:140  الأية
قَالَ أَغَيْرَ اللهِ أَبْغِيكُمْ إِلَٰهًا وَهُوَ فَضَّلَكُمْ عَلَى الْعَالَمِينَ
Qala aghayra Allahi abgheekumilahan wahuwa faddalakum AAala alAAalameen

Hausa
 
Ya ce: "Shin, wanin Allah nike nẽma muku ya zama abin bautăwa, alhăli kuwa Shĩ (Allah) Ya fĩfĩta ku a kan halittu?"

Ayah  7:141  الأية
وَإِذْ أَنجَيْنَاكُم مِّنْ آلِ فِرْعَوْنَ يَسُومُونَكُمْ سُوءَ الْعَذَابِ ۖ يُقَتِّلُونَ أَبْنَاءَكُمْ وَيَسْتَحْيُونَ نِسَاءَكُمْ ۚ وَفِي ذَٰلِكُم بَلَاءٌ مِّن رَّبِّكُمْ عَظِيمٌ
Wa-ith anjaynakum min alifirAAawna yasoomoonakum soo-a alAAathabi yuqattiloona abnaakumwayastahyoona nisaakum wafee thalikum balaonmin rabbikum AAatheem

Hausa
 
Kuma a lőkacin da Muka tsĩrar da ku daga mutănen Fir'auna, sună tayă muku mugunyar azăba. sună karkashe ɗiyanku maza, kuma sună răyar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabăwa daga Ubangijinku, Mai girma.

Ayah  7:142  الأية
وَوَاعَدْنَا مُوسَىٰ ثَلَاثِينَ لَيْلَةً وَأَتْمَمْنَاهَا بِعَشْرٍ فَتَمَّ مِيقَاتُ رَبِّهِ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً ۚ وَقَالَ مُوسَىٰ لِأَخِيهِ هَارُونَ اخْلُفْنِي فِي قَوْمِي وَأَصْلِحْ وَلَا تَتَّبِعْ سَبِيلَ الْمُفْسِدِينَ
WawaAAadna moosa thalatheenalaylatan waatmamnaha biAAashrin fatamma meeqaturabbihi arbaAAeena laylatan waqala moosa li-akheehiharoona okhlufnee fee qawmee waaslih walatattabiAA sabeela almufsideen

Hausa
 
Kuma Muka yi wa'adi ga Mũsă da dare talătin kuma Muka cikă su da gőma, sai miƙatin Ubangijinsa ya cika dare arba'in. Kuma Mũsă ya ce wa ɗan'uwansa, Hărũna: "Ka maye mini a cikin mutănena, kuma ka gyăra, kuma kada ka bi hanyar măsu fasădi." Kuma a lőkacin da Mũsă ya jẽ ga mĩkatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Mũsă ya ce: "Yă Ubangijina! Ka nũna mini in yi dũbi zuwa gare Ka!" Ya ce: "Bă ză ka gan Ni ba, kuma amma ka dũba zuwa ga dũtse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, ză ka gan Ni." Sa'an nan a lőkacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dũtsen, Ya sanyă shi niƙaƙƙe. Kuma Mũsă ya făɗi sőmamme. To, a lőkacin da ya farka, ya ce: "TsarkinKa ya tabbata! Nă tũba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon mũminai."

Ayah  7:143  الأية
وَلَمَّا جَاءَ مُوسَىٰ لِمِيقَاتِنَا وَكَلَّمَهُ رَبُّهُ قَالَ رَبِّ أَرِنِي أَنظُرْ إِلَيْكَ ۚ قَالَ لَن تَرَانِي وَلَٰكِنِ انظُرْ إِلَى الْجَبَلِ فَإِنِ اسْتَقَرَّ مَكَانَهُ فَسَوْفَ تَرَانِي ۚ فَلَمَّا تَجَلَّىٰ رَبُّهُ لِلْجَبَلِ جَعَلَهُ دَكًّا وَخَرَّ مُوسَىٰ صَعِقًا ۚ فَلَمَّا أَفَاقَ قَالَ سُبْحَانَكَ تُبْتُ إِلَيْكَ وَأَنَا أَوَّلُ الْمُؤْمِنِينَ
Walamma jaa moosalimeeqatina wakallamahu rabbuhu qala rabbiarinee anthur ilayka qala lan taraneewalakini onthur ila aljabali fa-iniistaqarra makanahu fasawfa taranee falammatajalla rabbuhu liljabali jaAAalahu dakkan wakharra moosasaAAiqan falamma afaqa qala subhanakatubtu ilayka waana awwalu almu/mineen

Hausa
 
Kuma a lőkacin da Mũsă ya jẽ ga mĩkatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Mũsă ya ce: "Yă Ubangijina! Ka nũna mini in yi dũbi zuwa gare Ka!" Ya ce: "Bă ză ka gan Ni ba, kuma amma ka dũba zuwa ga dũtse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, ză ka gan Ni." Sa'an nan a lőkacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dũtsen, Ya sanyă shi niƙaƙƙe. Kuma Mũsă ya făɗi sőmamme. To, a lőkacin da ya farka, ya ce: "TsarkinKa ya tabbata! Nă tũba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon mũminai."

Ayah  7:144  الأية
قَالَ يَا مُوسَىٰ إِنِّي اصْطَفَيْتُكَ عَلَى النَّاسِ بِرِسَالَاتِي وَبِكَلَامِي فَخُذْ مَا آتَيْتُكَ وَكُن مِّنَ الشَّاكِرِينَ
Qala ya moosa innee istafaytukaAAala annasi birisalateewabikalamee fakhuth ma ataytuka wakunmina ashshakireen

Hausa
 
Ya ce: "Ya Mũsă! Lalle ne Nĩ, Nă zăɓe ka bisa ga mutăne da manzanciNa, kuma da maganăTa. Sabőda haka ka riƙi abin da Nă bă ka, kuma ka kasance daga măsu gődiya."

Ayah  7:145  الأية
وَكَتَبْنَا لَهُ فِي الْأَلْوَاحِ مِن كُلِّ شَيْءٍ مَّوْعِظَةً وَتَفْصِيلًا لِّكُلِّ شَيْءٍ فَخُذْهَا بِقُوَّةٍ وَأْمُرْ قَوْمَكَ يَأْخُذُوا بِأَحْسَنِهَا ۚ سَأُرِيكُمْ دَارَ الْفَاسِقِينَ
Wakatabna lahu fee al-alwahimin kulli shay-in mawAAithatan watafseelanlikulli shay-in fakhuthha biquwwatin wa/mur qawmakaya/khuthoo bi-ahsaniha saoreekum daraalfasiqeen

Hausa
 
Kuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kőwane abu, wa'azi da rarrabẽwa ga dukan kőwane abu: "Sai ka riƙe su da ƙarfi, kuma ka umurci mutănenka, su yi riƙo ga abin da yake mafi kyawunsu; ză Ni nũna muku gidan făsiƙai."

Ayah  7:146  الأية
سَأَصْرِفُ عَنْ آيَاتِيَ الَّذِينَ يَتَكَبَّرُونَ فِي الْأَرْضِ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَإِن يَرَوْا كُلَّ آيَةٍ لَّا يُؤْمِنُوا بِهَا وَإِن يَرَوْا سَبِيلَ الرُّشْدِ لَا يَتَّخِذُوهُ سَبِيلًا وَإِن يَرَوْا سَبِيلَ الْغَيِّ يَتَّخِذُوهُ سَبِيلًا ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَكَانُوا عَنْهَا غَافِلِينَ
Saasrifu AAan ayatiyaallatheena yatakabbaroona fee al-ardi bighayri alhaqqiwa-in yaraw kulla ayatin la yu/minoo bihawa-in yaraw sabeela arrushdi la yattakhithoohusabeelan wa-in yaraw sabeela alghayyi yattakhithoohusabeelan thalika bi-annahum kaththaboo bi-ayatinawakanoo AAanha ghafileen

Hausa
 
Ză Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, bă da wani hakki ba, daga ăyőyiNa. Kuma idan sun ga dukan ăyă, bă ză su yi ĩmăni da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, bă ză su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, dőmin lalle ne su, sun ƙaryata da ăyőyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu găfilai.

Ayah  7:147  الأية
وَالَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَلِقَاءِ الْآخِرَةِ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ ۚ هَلْ يُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Wallatheena kaththaboobi-ayatina waliqa-i al-akhiratihabitat aAAmaluhum hal yujzawna illama kanoo yaAAmaloon

Hausa
 
Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ăyőyinMu da gamuwa da Lăhira, ayyukansu sun ɓăci. Shin, ana saka musu, făce da abin da suka kasance suna aikatăwa?

Ayah  7:148  الأية
وَاتَّخَذَ قَوْمُ مُوسَىٰ مِن بَعْدِهِ مِنْ حُلِيِّهِمْ عِجْلًا جَسَدًا لَّهُ خُوَارٌ ۚ أَلَمْ يَرَوْا أَنَّهُ لَا يُكَلِّمُهُمْ وَلَا يَهْدِيهِمْ سَبِيلًا ۘ اتَّخَذُوهُ وَكَانُوا ظَالِمِينَ
Wattakhatha qawmu moosamin baAAdihi min huliyyihim AAijlan jasadan lahu khuwarunalam yaraw annahu la yukallimuhum wala yahdeehimsabeelan ittakhathoohu wakanoo thalimeen

Hausa
 
Kuma mutănen Mũsă suka riƙi maraƙi, jikin mutăne, yană rũri, daga băyan tafiyarsa, daga kăyan ƙawarsu. Shin, ba su ganĩ ba, cẽwa lalle ne shi, bă ya yi musu magana, kuma bă ya shiryar da su ga hanya, sun riƙa shi, kuma sun kasance măsu zălunci.

Ayah  7:149  الأية
وَلَمَّا سُقِطَ فِي أَيْدِيهِمْ وَرَأَوْا أَنَّهُمْ قَدْ ضَلُّوا قَالُوا لَئِن لَّمْ يَرْحَمْنَا رَبُّنَا وَيَغْفِرْ لَنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ
Walamma suqita fee aydeehimwaraaw annahum qad dalloo qaloo la-in lam yarhamnarabbuna wayaghfir lana lanakoonanna mina alkhasireen

Hausa
 
Kuma a lőkacin da suka yi nadăma, kuma suka ga cẽwalalle ne sũ haƙĩƙa sun ɓace, suka ce: "Haƙĩƙa, idan UbangijinMu bai yi mana rahama ba, kuma Ya găfarta mana, lalle ne mună kasancẽwa daga măsu hasăra."

Ayah  7:150  الأية
وَلَمَّا رَجَعَ مُوسَىٰ إِلَىٰ قَوْمِهِ غَضْبَانَ أَسِفًا قَالَ بِئْسَمَا خَلَفْتُمُونِي مِن بَعْدِي ۖ أَعَجِلْتُمْ أَمْرَ رَبِّكُمْ ۖ وَأَلْقَى الْأَلْوَاحَ وَأَخَذَ بِرَأْسِ أَخِيهِ يَجُرُّهُ إِلَيْهِ ۚ قَالَ ابْنَ أُمَّ إِنَّ الْقَوْمَ اسْتَضْعَفُونِي وَكَادُوا يَقْتُلُونَنِي فَلَا تُشْمِتْ بِيَ الْأَعْدَاءَ وَلَا تَجْعَلْنِي مَعَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ
Walamma rajaAAa moosa ilaqawmihi ghadbana asifan qala bi/samakhalaftumoonee min baAAdee aAAajiltum amra rabbikum waalqa al-alwahawaakhatha bira/si akheehi yajurruhu ilayhi qalaibna omma inna alqawma istadAAafoonee wakadooyaqtuloonanee fala tushmit biya al-aAAdaa walatajAAalnee maAAa alqawmi aththalimeen

Hausa
 
Kuma a lőkacin da Mũsă ya kőma zuwa ga mutănensa, yană mai fushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Tir da abin da kuka yi mini wakilci, a băyană! Shin, kun nẽmi gaggawar umurnin Ubangijinku ne?" Kuma ya jefar da Allunan, kuma ya yi riƙo ga kan ɗan'uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Ya ce: "Yă ɗan'uwata! Lalle ne mutănen, sun ɗauke ni mai rauni, kuma sun yi kusa su kashe ni, sabőda haka kada ka dărantar da maƙiya game da ni, kuma kada ka sanya ni tăre da mutăne azzălumai."

Ayah  7:151  الأية
قَالَ رَبِّ اغْفِرْ لِي وَلِأَخِي وَأَدْخِلْنَا فِي رَحْمَتِكَ ۖ وَأَنتَ أَرْحَمُ الرَّاحِمِينَ
Qala rabbi ighfir lee wali-akheewaadkhilna fee rahmatika waanta arhamu arrahimeen

Hausa
 
Ya ce: "Yă Ubangijina! Ka găfarta mini, nĩ da ɗan'uwana, kuma Ka shigar da mu a cikin rahamarKa, alhăli kuwa Kai ne Mafi rahamar măsu rahama!"

Ayah  7:152  الأية
إِنَّ الَّذِينَ اتَّخَذُوا الْعِجْلَ سَيَنَالُهُمْ غَضَبٌ مِّن رَّبِّهِمْ وَذِلَّةٌ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُفْتَرِينَ
Inna allatheena ittakhathooalAAijla sayanaluhum ghadabun min rabbihim wathillatunfee alhayati addunya wakathalikanajzee almuftareen

Hausa
 
Lalle ne waɗanda suka riƙi maraƙin, wani fushi daga Ubangijinsu da wani walăkanci a cikin răyuwar dũniya, ză su săme su: Kuma kamar wancan ne Muke săka wa măsu ƙirƙira ƙarya.

Ayah  7:153  الأية
وَالَّذِينَ عَمِلُوا السَّيِّئَاتِ ثُمَّ تَابُوا مِن بَعْدِهَا وَآمَنُوا إِنَّ رَبَّكَ مِن بَعْدِهَا لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ
Wallatheena AAamiloo assayyi-atithumma taboo min baAAdiha waamanoo innarabbaka min baAAdiha laghafoorun raheem

Hausa
 
Kuma waɗanda suka aikata miyăgun ayyuka, sa'an nan suka tũba daga băyansu kuma sukayi ĩmăni, lalle ne Ubangijinka daga băyansu, haƙĩƙa, Mai găfarane, Mai jin ƙai.

Ayah  7:154  الأية
وَلَمَّا سَكَتَ عَن مُّوسَى الْغَضَبُ أَخَذَ الْأَلْوَاحَ ۖ وَفِي نُسْخَتِهَا هُدًى وَرَحْمَةٌ لِّلَّذِينَ هُمْ لِرَبِّهِمْ يَرْهَبُونَ
Walamma sakata AAan moosaalghadabu akhatha al-alwaha wafee nuskhatihahudan warahmatun lillatheena hum lirabbihimyarhaboon

Hausa
 
Kuma a lőkacin da fushin ya kwanta daga barin Mũsă, sai ya riƙi Allunan, kuma a cikin kwafensu akwai shiriya da rahama ga waɗanda suke sũ, ga Ubangijinsu, măsu jin tsőro ne.

Ayah  7:155  الأية
وَاخْتَارَ مُوسَىٰ قَوْمَهُ سَبْعِينَ رَجُلًا لِّمِيقَاتِنَا ۖ فَلَمَّا أَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ قَالَ رَبِّ لَوْ شِئْتَ أَهْلَكْتَهُم مِّن قَبْلُ وَإِيَّايَ ۖ أَتُهْلِكُنَا بِمَا فَعَلَ السُّفَهَاءُ مِنَّا ۖ إِنْ هِيَ إِلَّا فِتْنَتُكَ تُضِلُّ بِهَا مَن تَشَاءُ وَتَهْدِي مَن تَشَاءُ ۖ أَنتَ وَلِيُّنَا فَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا ۖ وَأَنتَ خَيْرُ الْغَافِرِينَ
Wakhtara moosaqawmahu sabAAeena rajulan limeeqatina falammaakhathat-humu arrajfatu qala rabbi lawshi/ta ahlaktahum min qablu wa-iyyaya atuhlikunabima faAAala assufahao minna in hiyailla fitnatuka tudillu biha man tashaowatahdee man tashao anta waliyyuna faghfirlana warhamna waanta khayru alghafireen

Hausa
 
Kuma Mũsă ya zăɓi mutănensa, namiji saba'in dőmin miƙătinMu. To, a lőkacin da tsăwa ta kăma su, ya ce: "Yă Ubangijina! Dă Kă so, dă Kă halakar da su daga gabăni, sũ da ni. Shin ză Kahalaka mu, sabőda abin da wăwăyen daga gare mu suka aikata? Ba ta zama ba făce fitinarKa Kană ɓatarwa, da ita, wanda Kake so kuma kană shiryarwa da ita, wanda Kake so; Kai ne Majiɓincinmu. Sai Ka găfarta mana; kuma Ka yi mana rahama, alhăli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin măsu găfara."

Ayah  7:156  الأية
وَاكْتُبْ لَنَا فِي هَٰذِهِ الدُّنْيَا حَسَنَةً وَفِي الْآخِرَةِ إِنَّا هُدْنَا إِلَيْكَ ۚ قَالَ عَذَابِي أُصِيبُ بِهِ مَنْ أَشَاءُ ۖ وَرَحْمَتِي وَسِعَتْ كُلَّ شَيْءٍ ۚ فَسَأَكْتُبُهَا لِلَّذِينَ يَتَّقُونَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَالَّذِينَ هُم بِآيَاتِنَا يُؤْمِنُونَ
Waktub lana fee hathihiaddunya hasanatan wafee al-akhiratiinna hudna ilayka qala AAathabee oseebubihi man ashao warahmatee wasiAAat kulla shay-infasaaktubuha lillatheena yattaqoona wayu/toona azzakatawallatheena hum bi-ayatinayu/minoon

Hausa
 
"Kuma Ka rubũta mana alhẽri a cikin wannan dũniya, kuma a cikin Lăhira. Lalle ne mũ,mun tũba zuwa gare Ka." Ya ce: "AzăbaTa Ină sămu, da ita, wanda Nike so, kuma rahamaTa, ta yalwaci dukan kőme. Sa'an nan ză Ni rubũta ta ga waɗanda suke yin taƙawa, kuma sună băyar da zakka, da waɗanda suke, game da ăyőyinMu mũminai ne."

Ayah  7:157  الأية
الَّذِينَ يَتَّبِعُونَ الرَّسُولَ النَّبِيَّ الْأُمِّيَّ الَّذِي يَجِدُونَهُ مَكْتُوبًا عِندَهُمْ فِي التَّوْرَاةِ وَالْإِنجِيلِ يَأْمُرُهُم بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَاهُمْ عَنِ الْمُنكَرِ وَيُحِلُّ لَهُمُ الطَّيِّبَاتِ وَيُحَرِّمُ عَلَيْهِمُ الْخَبَائِثَ وَيَضَعُ عَنْهُمْ إِصْرَهُمْ وَالْأَغْلَالَ الَّتِي كَانَتْ عَلَيْهِمْ ۚ فَالَّذِينَ آمَنُوا بِهِ وَعَزَّرُوهُ وَنَصَرُوهُ وَاتَّبَعُوا النُّورَ الَّذِي أُنزِلَ مَعَهُ ۙ أُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ
Allatheena yattabiAAoona arrasoolaannabiyya al-ommiyya allathee yajidoonahumaktooban AAindahum fee attawrati wal-injeeliya/muruhum bilmaAAroofi wayanhahum AAani almunkariwayuhillu lahumu attayyibati wayuharrimuAAalayhimu alkhaba-itha wayadaAAu AAanhum israhumwal-aghlala allatee kanat AAalayhim fallatheenaamanoo bihi waAAazzaroohu wanasaroohu wattabaAAooannoora allathee onzila maAAahu ola-ikahumu almuflihoon

Hausa
 
"Waɗanda suke sună bin Manzo, Annabi, Ummiyyi wanda suke sămun sa rubũce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla.

Ayah  7:158  الأية
قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنِّي رَسُولُ اللهِ إِلَيْكُمْ جَمِيعًا الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ فَآمِنُوا بِاللهِ وَرَسُولِهِ النَّبِيِّ الْأُمِّيِّ الَّذِي يُؤْمِنُ بِاللهِ وَكَلِمَاتِهِ وَاتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ
Qul ya ayyuha annasuinnee rasoolu Allahi ilaykum jameeAAan allatheelahu mulku assamawati wal-ardila ilaha illa huwa yuhyee wayumeetufaaminoo billahi warasoolihi annabiyyial-ommiyyi allathee yu/minu billahi wakalimatihiwattabiAAoohu laAAallakum tahtadoon

Hausa
 
Ka ce: "Yă kũ mutăne! Lalle ne nĩ manzon Allah nezuwa gare ku, gabă ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Băbu wani abin bautawa făce Shi, Yană răyarwa, kuma Yană matarwa, sai ku yi ĩmăni daAllah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmăni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammăninku, kună shiryuwa."

Ayah  7:159  الأية
وَمِن قَوْمِ مُوسَىٰ أُمَّةٌ يَهْدُونَ بِالْحَقِّ وَبِهِ يَعْدِلُونَ
Wamin qawmi moosa ommatun yahdoonabilhaqqi wabihi yaAAdiloon

Hausa
 
Kuma daga mutănen Mũsă akwai al'umma, sună shiryarwa da gaskiya, kuma da ita suke yin ădalci.

Ayah  7:160  الأية
وَقَطَّعْنَاهُمُ اثْنَتَيْ عَشْرَةَ أَسْبَاطًا أُمَمًا ۚ وَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ مُوسَىٰ إِذِ اسْتَسْقَاهُ قَوْمُهُ أَنِ اضْرِب بِّعَصَاكَ الْحَجَرَ ۖ فَانبَجَسَتْ مِنْهُ اثْنَتَا عَشْرَةَ عَيْنًا ۖ قَدْ عَلِمَ كُلُّ أُنَاسٍ مَّشْرَبَهُمْ ۚ وَظَلَّلْنَا عَلَيْهِمُ الْغَمَامَ وَأَنزَلْنَا عَلَيْهِمُ الْمَنَّ وَالسَّلْوَىٰ ۖ كُلُوا مِن طَيِّبَاتِ مَا رَزَقْنَاكُمْ ۚ وَمَا ظَلَمُونَا وَلَٰكِن كَانُوا أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
WaqattaAAnahumu ithnatayAAashrata asbatan omaman waawhayna ilamoosa ithi istasqahu qawmuhu ani idribbiAAasaka alhajara fanbajasat minhu ithnataAAashrata AAaynan qad AAalima kullu onasin mashrabahum wathallalnaAAalayhimu alghamama waanzalna AAalayhimu almannawassalwa kuloo min tayyibati marazaqnakum wama thalamoona walakinkanoo anfusahum yathlimoon

Hausa
 
Kuma Muka yayyanka su sibɗi gőma shă biyu, al'ummai. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsă a lőkacin da mutănensasuka nẽme shi, ga shăyarwa, cẽwa: "Ka dőki dũtsen da sandarka."Sai marmaro gőma shă biyu suka ɓuɓɓuga daga gare shi: Lalle ne kőwaɗanne mutăne sun san mashăyarsu. Kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kansu."Ku ci daga măsu dăɗin abin da Muka azurta ku."Kuma ba su zăluncẽ Mu ba; kuma amma răyukansu suke zălunta.

Ayah  7:161  الأية
وَإِذْ قِيلَ لَهُمُ اسْكُنُوا هَٰذِهِ الْقَرْيَةَ وَكُلُوا مِنْهَا حَيْثُ شِئْتُمْ وَقُولُوا حِطَّةٌ وَادْخُلُوا الْبَابَ سُجَّدًا نَّغْفِرْ لَكُمْ خَطِيئَاتِكُمْ ۚ سَنَزِيدُ الْمُحْسِنِينَ
Wa-ith qeela lahumu oskunoo hathihialqaryata wakuloo minha haythu shi/tum waqooloo hittatunwadkhuloo albaba sujjadan naghfir lakum khatee-atikumsanazeedu almuhsineen

Hausa
 
Kuma a lőkacin da aka ce masu: "Ku zauna ga wannan alƙarya, kuma ku ci daga gare ta, inda kuka so, kuma ku ce: 'Saryarwa,' kuma ku shiga kőfa kuna măsu sujada; Mu găfarta muku laifuffukanku, kuma ză Mu ɗăra wa măsu kyautatăwa."

Ayah  7:162  الأية
فَبَدَّلَ الَّذِينَ ظَلَمُوا مِنْهُمْ قَوْلًا غَيْرَ الَّذِي قِيلَ لَهُمْ فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ رِجْزًا مِّنَ السَّمَاءِ بِمَا كَانُوا يَظْلِمُونَ
Fabaddala allatheena thalamoominhum qawlan ghayra allathee qeela lahum faarsalnaAAalayhim rijzan mina assama-i bima kanooyathlimoon

Hausa
 
Sai waɗanda suka yi zălunci daga gare su, suka musanya magana watar wadda aka ce musu, sai Muka aika azăba a kansu, daga sama, sabőda abin da suka kasance sună yi na zălunci.

Ayah  7:163  الأية
وَاسْأَلْهُمْ عَنِ الْقَرْيَةِ الَّتِي كَانَتْ حَاضِرَةَ الْبَحْرِ إِذْ يَعْدُونَ فِي السَّبْتِ إِذْ تَأْتِيهِمْ حِيتَانُهُمْ يَوْمَ سَبْتِهِمْ شُرَّعًا وَيَوْمَ لَا يَسْبِتُونَ ۙ لَا تَأْتِيهِمْ ۚ كَذَٰلِكَ نَبْلُوهُم بِمَا كَانُوا يَفْسُقُونَ
Was-alhum AAani alqaryati allatee kanathadirata albahri ith yaAAdoona fee assabtiith ta/teehim heetanuhum yawma sabtihimshurraAAan wayawma la yasbitoona la ta/teehim kathalikanabloohum bima kanoo yafsuqoon

Hausa
 
Kuma ka tambaye su daga alƙarya wadda ta kasance kusa ga tẽku, a lőkacin da suke ƙẽtare haddi a cikin Asabar, a lőkacin da kĩfăyensu, suke je musu a rănar Asabar ɗinsu jẽre. Kuma a rănar da ba su yi Asabar ba, bă su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance sună yi na făsiƙanci.

Ayah  7:164  الأية
وَإِذْ قَالَتْ أُمَّةٌ مِّنْهُمْ لِمَ تَعِظُونَ قَوْمًا ۙ اللهُ مُهْلِكُهُمْ أَوْ مُعَذِّبُهُمْ عَذَابًا شَدِيدًا ۖ قَالُوا مَعْذِرَةً إِلَىٰ رَبِّكُمْ وَلَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ
Wa-ith qalat ommatun minhumlima taAAithoona qawman Allahu muhlikuhum awmuAAaththibuhum AAathaban shadeedan qaloomaAAthiratan ila rabbikum walaAAallahum yattaqoon

Hausa
 
Kuma a lőkacin da wata al'umma daga gare su ta ce: "Don me kuke yin wa'azi ga mutăne waɗanda Allah Yake Mai halaka su kő kuwa Mai yi musu azăba, azăba mai tsanani?" Suka ce: "Dőmin nẽman hanzari zuwa ga Ubangijinku, kuma tsammăninsu, sună yin taƙawa."

Ayah  7:165  الأية
فَلَمَّا نَسُوا مَا ذُكِّرُوا بِهِ أَنجَيْنَا الَّذِينَ يَنْهَوْنَ عَنِ السُّوءِ وَأَخَذْنَا الَّذِينَ ظَلَمُوا بِعَذَابٍ بَئِيسٍ بِمَا كَانُوا يَفْسُقُونَ
Falamma nasoo ma thukkiroobihi anjayna allatheena yanhawna AAani assoo-iwaakhathna allatheena thalamoobiAAathabin ba-eesin bima kanoo yafsuqoon

Hausa
 
To, a lőkacin da suka manta da abin da aka tunătar da su da shi, Mun tsĩrar da waɗanda suke hani daga cũta, kuma Muka kăma waɗanda suka yi zălunci, da azăba mai tsanani dőmin abin da suka kasance sună yi, na fasiƙanci.

Ayah  7:166  الأية
فَلَمَّا عَتَوْا عَن مَّا نُهُوا عَنْهُ قُلْنَا لَهُمْ كُونُوا قِرَدَةً خَاسِئِينَ
Falamma AAataw AAan ma nuhooAAanhu qulna lahum koonoo qiradatan khasi-een

Hausa
 
Sa'an nan a lőkacin da suka yi girman kai daga barin abin da aka hana su daga gare shi, Muka ce musu: "Ku kasance birai ƙasƙantattu."

Ayah  7:167  الأية
وَإِذْ تَأَذَّنَ رَبُّكَ لَيَبْعَثَنَّ عَلَيْهِمْ إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ مَن يَسُومُهُمْ سُوءَ الْعَذَابِ ۗ إِنَّ رَبَّكَ لَسَرِيعُ الْعِقَابِ ۖ وَإِنَّهُ لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ
Wa-ith taaththana rabbukalayabAAathanna AAalayhim ila yawmi alqiyamati manyasoomuhum soo-a alAAathabi inna rabbaka lasareeAAu alAAiqabiwa-innahu laghafoorun raheem

Hausa
 
Kuma a lőkacin da Ubangijinku Ya sanar, lalle ne, ză Ya aika a kansu (Yahũd), zuwa, Rănarˇiyăma, wanda zai ɗanɗana musu mummunar azăba, lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai gaggawar uƙũba ne, kuma shĩ haƙĩƙa, Mai găfara ne, Mai jin ƙai.

Ayah  7:168  الأية
وَقَطَّعْنَاهُمْ فِي الْأَرْضِ أُمَمًا ۖ مِّنْهُمُ الصَّالِحُونَ وَمِنْهُمْ دُونَ ذَٰلِكَ ۖ وَبَلَوْنَاهُم بِالْحَسَنَاتِ وَالسَّيِّئَاتِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ
WaqattaAAnahum fee al-ardiomaman minhumu assalihoona waminhum doona thalikawabalawnahum bilhasanati wassayyi-atilaAAallahum yarjiAAoon

Hausa
 
Kuma Muka yayyanka su, a cikin ƙasa, al'ummőmi, daga gare su akwai sălihai, kuma daga gare su akwai wanda bă haka ba. Muka jarrabe su da abũbuwan alhẽri da na musĩfa; Tsammăninsu, sună kőmőwa.

Ayah  7:169  الأية
فَخَلَفَ مِن بَعْدِهِمْ خَلْفٌ وَرِثُوا الْكِتَابَ يَأْخُذُونَ عَرَضَ هَٰذَا الْأَدْنَىٰ وَيَقُولُونَ سَيُغْفَرُ لَنَا وَإِن يَأْتِهِمْ عَرَضٌ مِّثْلُهُ يَأْخُذُوهُ ۚ أَلَمْ يُؤْخَذْ عَلَيْهِم مِّيثَاقُ الْكِتَابِ أَن لَّا يَقُولُوا عَلَى اللهِ إِلَّا الْحَقَّ وَدَرَسُوا مَا فِيهِ ۗ وَالدَّارُ الْآخِرَةُ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَ ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَ
Fakhalafa min baAAdihim khalfun warithooalkitaba ya/khuthoona AAarada hathaal-adna wayaqooloona sayughfaru lana wa-in ya/tihimAAaradun mithluhu ya/khuthoohu alam yu/khathAAalayhim meethaqu alkitabi an la yaqoolooAAala Allahi illa alhaqqa wadarasoo mafeehi waddaru al-akhiratu khayrun lillatheenayattaqoona afala taAAqiloon

Hausa
 
Sai wasu' yan băya suka maye daga băyansu, sun gaji Littăfin, sună karɓar sifar wannan ƙasƙantacciya, sună cẽwa: "Ză a găfarta mana. "Iadan kuma wata sifa irinta ta zo, za su karɓe ta. Shin, ba a karɓi alkawarin Littăfi ba a kansu cẽwa kada su faɗa ga Allah, făce gaskiya, alhăli kuwa sun karanta abin da yake a cikinsa, kuma Gidan Lăhira ne mafi alhẽriga wanda ya yi taƙawa? Shin, bă ză ku hankalta ba?

Ayah  7:170  الأية
وَالَّذِينَ يُمَسِّكُونَ بِالْكِتَابِ وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجْرَ الْمُصْلِحِينَ
Wallatheena yumassikoona bilkitabiwaaqamoo assalata inna lanudeeAAu ajra almusliheen

Hausa
 
Kuma waɗanda suke riƙẽwa da laittăfi kuma suka tsayar da salla, lalle ne Mũ, bă Mu tőzarta lădar măsu gyărăwa.

Ayah  7:171  الأية
وَإِذْ نَتَقْنَا الْجَبَلَ فَوْقَهُمْ كَأَنَّهُ ظُلَّةٌ وَظَنُّوا أَنَّهُ وَاقِعٌ بِهِمْ خُذُوا مَا آتَيْنَاكُم بِقُوَّةٍ وَاذْكُرُوا مَا فِيهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ
Wa-ith nataqna aljabalafawqahum kaannahu thullatun wathannooannahu waqiAAun bihim khuthoo ma ataynakumbiquwwatin wathkuroo ma feehi laAAallakumtattaqoon

Hausa
 
Kuma a lőkacin da muka ɗaukaka dũtse sama da su, kumar dai shi girgije ne, kuma suka haƙƙaƙe, lalle ne shĩ, mai făɗuwa ne a gare su, (aka ce): "Ku karɓi abin da Muka kăwo muku da ƙarfi, kuma ku tuna abin da yake a cikinsa, tsammăninku kună yin taƙawa."

Ayah  7:172  الأية
وَإِذْ أَخَذَ رَبُّكَ مِن بَنِي آدَمَ مِن ظُهُورِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَأَشْهَدَهُمْ عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ أَلَسْتُ بِرَبِّكُمْ ۖ قَالُوا بَلَىٰ ۛ شَهِدْنَا ۛ أَن تَقُولُوا يَوْمَ الْقِيَامَةِ إِنَّا كُنَّا عَنْ هَٰذَا غَافِلِينَ
Wa-ith akhatha rabbuka minbanee adama min thuhoorihim thurriyyatahumwaashhadahum AAala anfusihim alastu birabbikum qaloobala shahidna an taqooloo yawma alqiyamatiinna kunna AAan hatha ghafileen

Hausa
 
Kuma a lőkacin da Ubangijinka Ya karɓi (alkawari) daga ɗiyan Ădam, daga băyayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan răyukansu, (Ya ce): "Shin, bă Nĩ ne Ubangijinku ba?" Suka ce: "Na'am! Mun yi shaida!" (ya ce): "Kada ku ce a Rănar Kiyăma: Lalle ne mũ, daga wannan, gafalallu ne."

Ayah  7:173  الأية
أَوْ تَقُولُوا إِنَّمَا أَشْرَكَ آبَاؤُنَا مِن قَبْلُ وَكُنَّا ذُرِّيَّةً مِّن بَعْدِهِمْ ۖ أَفَتُهْلِكُنَا بِمَا فَعَلَ الْمُبْطِلُونَ
Aw taqooloo innama ashraka abaonamin qablu wakunna thurriyyatan min baAAdihimafatuhlikuna bima faAAala almubtiloon

Hausa
 
Kő kuwa ku ce: "Abin sani kawai, ubanninmu suka yi shirki daga farko, kuma mũ, mun kasance zũriya daga băyansu. Shin fa,Kană halaka mu, sabőda abin da măsu ɓătăwa suka aikata?"

Ayah  7:174  الأية
وَكَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ الْآيَاتِ وَلَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ
Wakathalika nufassilu al-ayatiwalaAAallahum yarjiAAoon

Hausa
 
Kuma kamar haka Muke rarrabe ăyőyi, daki-daki; tsammăninsu, sună kőmőwa.

Ayah  7:175  الأية
وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ الَّذِي آتَيْنَاهُ آيَاتِنَا فَانسَلَخَ مِنْهَا فَأَتْبَعَهُ الشَّيْطَانُ فَكَانَ مِنَ الْغَاوِينَ
Watlu AAalayhim nabaa allatheeataynahu ayatina fansalakhaminha faatbaAAahu ashshaytanu fakanamina alghaween

Hausa
 
Ka karanta a kansu lăbărin wanda Muka kăwo masa ăyőyinMu, sai ya săɓule daga gare su, sai shaidan ya bi shi, sai ya kasance a cikin halakakku.

Ayah  7:176  الأية
وَلَوْ شِئْنَا لَرَفَعْنَاهُ بِهَا وَلَٰكِنَّهُ أَخْلَدَ إِلَى الْأَرْضِ وَاتَّبَعَ هَوَاهُ ۚ فَمَثَلُهُ كَمَثَلِ الْكَلْبِ إِن تَحْمِلْ عَلَيْهِ يَلْهَثْ أَوْ تَتْرُكْهُ يَلْهَث ۚ ذَّٰلِكَ مَثَلُ الْقَوْمِ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا ۚ فَاقْصُصِ الْقَصَصَ لَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ
Walaw shi/na larafaAAnahu bihawalakinnahu akhlada ila al-ardi wattabaAAahawahu famathaluhu kamathali alkalbi in tahmilAAalayhi yalhath aw tatruk-hu yalhath thalika mathalualqawmi allatheena kaththaboo bi-ayatinafaqsusi alqasasa laAAallahumyatafakkaroon

Hausa
 
Kuma dă Mun so, da Mun ɗaukakă shi da su, kuma amma shĩ, ya nẽmi dawwama a cikin ƙasa, kuma ya bi son zũciyarsa. To, misălinsa kamar misălin kare ne, idan ka yi ɗauki a kansa ya yi lallage, kő kuwa ka bar shi sai ya yi lallage, wannan ne misălin mutăne waɗanda suka ƙaryata game da ăyőyinMu: Ka jẽranta karătun lăbărun; tsammăninsu sună tunăni.

Ayah  7:177  الأية
سَاءَ مَثَلًا الْقَوْمُ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَأَنفُسَهُمْ كَانُوا يَظْلِمُونَ
Saa mathalan alqawmu allatheenakaththaboo bi-ayatina waanfusahum kanooyathlimoon

Hausa
 
Tir da zama misăli, mutănen da suka ƙaryata game da ăyőyinMu, kuma kansu suka kasance sună zălunta.

Ayah  7:178  الأية
مَن يَهْدِ اللهُ فَهُوَ الْمُهْتَدِي ۖ وَمَن يُضْلِلْ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ
Man yahdi Allahu fahuwa almuhtadeewaman yudlil faola-ika humu alkhasiroon

Hausa
 
Wanda Allah Ya shiryar, to, shĩ ne Mai shiryuwa, kuma wanda Ya ɓatar, to, waɗannan sũ ne măsu hasăra.

Ayah  7:179  الأية
وَلَقَدْ ذَرَأْنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيرًا مِّنَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ ۖ لَهُمْ قُلُوبٌ لَّا يَفْقَهُونَ بِهَا وَلَهُمْ أَعْيُنٌ لَّا يُبْصِرُونَ بِهَا وَلَهُمْ آذَانٌ لَّا يَسْمَعُونَ بِهَا ۚ أُولَٰئِكَ كَالْأَنْعَامِ بَلْ هُمْ أَضَلُّ ۚ أُولَٰئِكَ هُمُ الْغَافِلُونَ
Walaqad thara/na lijahannamakatheeran mina aljinni wal-insi lahum quloobun layafqahoona biha walahum aAAyunun la yubsiroonabiha walahum athanun la yasmaAAoona bihaola-ika kal-anAAami bal hum adalluola-ika humu alghafiloon

Hausa
 
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sabőda Jahannama, măsu yawa daga aljannu da mutăne, sună da zukăta, ba su fahimta da su, kuma sună da idănu, bă su gani da su, kuma sună da kunnuwa, ba su ji da su; waɗancan kamar bisăshe suke. Ă'a, sũ ne mafi ɓacẽwa; Waɗancan sũ ne gafalallu.

Ayah  7:180  الأية
وَلِلَّهِ الْأَسْمَاءُ الْحُسْنَىٰ فَادْعُوهُ بِهَا ۖ وَذَرُوا الَّذِينَ يُلْحِدُونَ فِي أَسْمَائِهِ ۚ سَيُجْزَوْنَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Walillahi al-asmao alhusnafadAAoohu biha watharoo allatheenayulhidoona fee asma-ihi sayujzawna ma kanooyaAAmaloon

Hausa
 
Kuma Allah Yană da sũnăye măsu kyau. Sai ku rőƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhădi a cikin sũnăyenSa:ză a săka musu abin da suka kasance sună aikatăwa.

Ayah  7:181  الأية
وَمِمَّنْ خَلَقْنَا أُمَّةٌ يَهْدُونَ بِالْحَقِّ وَبِهِ يَعْدِلُونَ
Wamimman khalaqna ommatun yahdoonabilhaqqi wabihi yaAAdiloon

Hausa
 
Kuma daga waɗanda Muka halitta akwai wata al'umma, sună shiryarwa da gaskiya, kuma,da ita suke yin ădalci.

Ayah  7:182  الأية
وَالَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا سَنَسْتَدْرِجُهُم مِّنْ حَيْثُ لَا يَعْلَمُونَ
Wallatheena kaththaboobi-ayatina sanastadrijuhum min haythula yaAAlamoon

Hausa
 
Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ăyőyinMu, ză Mu yi musu istidrăji daga inda ba su sani ba.

Ayah  7:183  الأية
وَأُمْلِي لَهُمْ ۚ إِنَّ كَيْدِي مَتِينٌ
Waomlee lahum inna kaydee mateen

Hausa
 
Kuma Ină yi musu jinkiri, lalle ne kaidĩNa, mai ƙarfi ne.

Ayah  7:184  الأية
أَوَلَمْ يَتَفَكَّرُوا ۗ مَا بِصَاحِبِهِم مِّن جِنَّةٍ ۚ إِنْ هُوَ إِلَّا نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Awa lam yatafakkaroo ma bisahibihimmin jinnatin in huwa illa natheerun mubeen

Hausa
 
Shin, ba su yi tunĩni ba, cẽwa băbu wata hauka ga ma'abucinsu? shĩ bai zama ba făce mai gargaɗi mai bayyanăwa.

Ayah  7:185  الأية
أَوَلَمْ يَنظُرُوا فِي مَلَكُوتِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا خَلَقَ اللهُ مِن شَيْءٍ وَأَنْ عَسَىٰ أَن يَكُونَ قَدِ اقْتَرَبَ أَجَلُهُمْ ۖ فَبِأَيِّ حَدِيثٍ بَعْدَهُ يُؤْمِنُونَ
Awalam yanthuroo feemalakooti assamawati wal-ardiwama khalaqa Allahu min shay-in waan AAasaan yakoona qadi iqtaraba ajaluhum fabi-ayyi hadeethinbaAAdahu yu/minoon

Hausa
 
Shin, ba su yi dũbi ba a cikin mulkin sammai da ƙasa, da kuma abin da Allah Ya halitta daga kőme, kuma akwai tsammăni kasancewar ajalinsu, haƙĩƙa, ya kusanta? To,da wane lăbări a băyansa suke yin ĩmăni?

Ayah  7:186  الأية
مَن يُضْلِلِ اللهُ فَلَا هَادِيَ لَهُ ۚ وَيَذَرُهُمْ فِي طُغْيَانِهِمْ يَعْمَهُونَ
Man yudlili Allahu falahadiya lahu wayatharuhum fee tughyanihimyaAAmahoon

Hausa
 
Wanda Allah Ya ɓatar to băbu mai shiryarwa a gare shi: kuma Yană barin su, a cikin ɓatarsu sună ɗimuwa.

Ayah  7:187  الأية
يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا ۖ قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِندَ رَبِّي ۖ لَا يُجَلِّيهَا لِوَقْتِهَا إِلَّا هُوَ ۚ ثَقُلَتْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ لَا تَأْتِيكُمْ إِلَّا بَغْتَةً ۗ يَسْأَلُونَكَ كَأَنَّكَ حَفِيٌّ عَنْهَا ۖ قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِندَ اللهِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
Yas-aloonaka AAani assaAAatiayyana mursaha qul innama AAilmuhaAAinda rabbee la yujalleeha liwaqtiha illahuwa thaqulat fee assamawati wal-ardila ta/teekum illa baghtatan yas-aloonaka kaannaka hafiyyunAAanha qul innama AAilmuha AAinda Allahiwalakinna akthara annasi layaAAlamoon

Hausa
 
Sună tambayar ka daga Sa'a, a yaushe tabbatarta take? Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Băbu mai bayyana ta ga lőkacinta făce shĩ Tă yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Bă ză ta zo muku ba făce kwatsam." sună tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawan mutăne bă su sani."

Ayah  7:188  الأية
قُل لَّا أَمْلِكُ لِنَفْسِي نَفْعًا وَلَا ضَرًّا إِلَّا مَا شَاءَ اللهُ ۚ وَلَوْ كُنتُ أَعْلَمُ الْغَيْبَ لَاسْتَكْثَرْتُ مِنَ الْخَيْرِ وَمَا مَسَّنِيَ السُّوءُ ۚ إِنْ أَنَا إِلَّا نَذِيرٌ وَبَشِيرٌ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Qul la amliku linafsee nafAAan waladarran illa ma shaa Allahuwalaw kuntu aAAlamu alghayba lastakthartu mina alkhayriwama massaniya assoo-o in ana illanatheerun wabasheerun liqawmin yu/minoon

Hausa
 
Ka ce: "Bă ni mallaka wa raina wani amfăni, kuma haka ban tunkuɗe wata cũta, făceabin da Allah Ya so. Kuma dă na kasance ină sanin gaibi, dă lalle ne, nă yawaita daga alhẽri kuma cũta bă ză ta shăfe ni ba, nĩ ban zama ba fĩce mai gargaɗi, kumamai băyar da bishăra ga mutăne waɗanda suke yin ĩmăni."

Ayah  7:189  الأية
هُوَ الَّذِي خَلَقَكُم مِّن نَّفْسٍ وَاحِدَةٍ وَجَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَا لِيَسْكُنَ إِلَيْهَا ۖ فَلَمَّا تَغَشَّاهَا حَمَلَتْ حَمْلًا خَفِيفًا فَمَرَّتْ بِهِ ۖ فَلَمَّا أَثْقَلَت دَّعَوَا اللهَ رَبَّهُمَا لَئِنْ آتَيْتَنَا صَالِحًا لَّنَكُونَنَّ مِنَ الشَّاكِرِينَ
Huwa allathee khalaqakum min nafsinwahidatin wajaAAala minha zawjaha liyaskunailayha falamma taghashshaha hamalathamlan khafeefan famarrat bihi falamma athqalatdaAAawa Allaha rabbahuma la-in ataytanasalihan lanakoonanna mina ashshakireen

Hausa
 
Shĩ ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kumaYa sanya, daga gare ta, ma'auranta, dőmin ya natsu zuwa gare ta. Sa'an nan a lőkacin da ya rufe ta, ta yi ciki, ciki sassauƙa, sai ta shũɗe dashi. Sa'an nan a lőkacin da ya yi nauyi, sai suka rőƙi Allah, Ubangijinsu: "Lalle ne idan Ka bă mu abin ƙwarai, haƙĩƙa, ză mu kasance dagamăsu gődiya."

Ayah  7:190  الأية
فَلَمَّا آتَاهُمَا صَالِحًا جَعَلَا لَهُ شُرَكَاءَ فِيمَا آتَاهُمَا ۚ فَتَعَالَى اللهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Falamma atahumasalihan jaAAala lahu shurakaa feemaatahuma fataAAala AllahuAAamma yushrikoon

Hausa
 
To, a lőkacin da Ya bă su abin ƙwarai, suka sanya Masa abőkan tarayya a cikin abin da Ya ba su. To, Allah Yă tsarkaka daga abin da suke yi na shirki.

Ayah  7:191  الأية
أَيُشْرِكُونَ مَا لَا يَخْلُقُ شَيْئًا وَهُمْ يُخْلَقُونَ
Ayushrikoona ma la yakhluqushay-an wahum yukhlaqoon

Hausa
 
Shin, sună shirki da abin da bă ya halittar kőme, kuma sũne ake halittăwa?

Ayah  7:192  الأية
وَلَا يَسْتَطِيعُونَ لَهُمْ نَصْرًا وَلَا أَنفُسَهُمْ يَنصُرُونَ
Wala yastateeAAoona lahum nasranwala anfusahum yansuroon

Hausa
 
Kuma ba su iya băyar da taimako gare su, kuma kansu ma, bă su iya taimaka!

Ayah  7:193  الأية
وَإِن تَدْعُوهُمْ إِلَى الْهُدَىٰ لَا يَتَّبِعُوكُمْ ۚ سَوَاءٌ عَلَيْكُمْ أَدَعَوْتُمُوهُمْ أَمْ أَنتُمْ صَامِتُونَ
Wa-in tadAAoohum ila alhuda layattabiAAookum sawaon AAalaykum adaAAawtumoohum am antum samitoon

Hausa
 
Kuma idan kun kirăye su zuwa ga shiriya, bă ză su bĩ ku ba, daidai ne a gare ku, shin, kun kirăye su, kő kuwa kũ măsu kawaici ne!

Ayah  7:194  الأية
إِنَّ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِ اللهِ عِبَادٌ أَمْثَالُكُمْ ۖ فَادْعُوهُمْ فَلْيَسْتَجِيبُوا لَكُمْ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Inna allatheena tadAAoona min dooniAllahi AAibadun amthalukum fadAAoohumfalyastajeeboo lakum in kuntum sadiqeen

Hausa
 
Lalle ne waɗannan da kuke kira, baicin Allah, băyĩ ne misălanku: to, ku kirăye su, sa'an nan su karɓa muku, idan kun kasance măsu gaskiya!

Ayah  7:195  الأية
أَلَهُمْ أَرْجُلٌ يَمْشُونَ بِهَا ۖ أَمْ لَهُمْ أَيْدٍ يَبْطِشُونَ بِهَا ۖ أَمْ لَهُمْ أَعْيُنٌ يُبْصِرُونَ بِهَا ۖ أَمْ لَهُمْ آذَانٌ يَسْمَعُونَ بِهَا ۗ قُلِ ادْعُوا شُرَكَاءَكُمْ ثُمَّ كِيدُونِ فَلَا تُنظِرُونِ
Alahum arjulun yamshoona biha amlahum aydin yabtishoona biha am lahum aAAyunun yubsiroonabiha am lahum athanun yasmaAAoona biha quliodAAoo shurakaakum thumma keedooni fala tunthiroon

Hausa
 
Shin sună da ƙafăfu da suke yin tafia da su? Kő sună da hannăye da suke damƙa da su? Kő sună da idănu da suke gani da su? Ko sună da kunnuwa da suke saurăre da su? Ka ce: "Ku kirăwo abũbuwan shirkinku sa'an nan kuma ku yi mini kaidi, sa'an nan kada ku saurăra mini."

Ayah  7:196  الأية
إِنَّ وَلِيِّيَ اللهُ الَّذِي نَزَّلَ الْكِتَابَ ۖ وَهُوَ يَتَوَلَّى الصَّالِحِينَ
Inna waliyyiya Allahu allatheenazzala alkitaba wahuwa yatawalla assaliheen

Hausa
 
"Lalle ne, Majiɓincĩna Allah ne Wanda Ya saukar da Littăfi kuma Shĩ ne Yake jiɓintar sălihai,"

Ayah  7:197  الأية
وَالَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِهِ لَا يَسْتَطِيعُونَ نَصْرَكُمْ وَلَا أَنفُسَهُمْ يَنصُرُونَ
Wallatheena tadAAoona mindoonihi la yastateeAAoona nasrakum walaanfusahum yansuroon

Hausa
 
"Kuma waɗanda kuke kira, baicinSa, bă su iya taimakőn ku, kuma kansu ma, bă su iya taimaka."

Ayah  7:198  الأية
وَإِن تَدْعُوهُمْ إِلَى الْهُدَىٰ لَا يَسْمَعُوا ۖ وَتَرَاهُمْ يَنظُرُونَ إِلَيْكَ وَهُمْ لَا يُبْصِرُونَ
Wa-in tadAAoohum ila alhuda layasmaAAoo watarahum yanthuroona ilayka wahumla yubsiroon

Hausa
 
Kuma idan ka kirăye su zuwa ga shiriya, bă ză su ji ba, kuma kană ganin su, sună dũbi zuwa gare ka, alhăli kuwa sũ, bă su gani.

Ayah  7:199  الأية
خُذِ الْعَفْوَ وَأْمُرْ بِالْعُرْفِ وَأَعْرِضْ عَنِ الْجَاهِلِينَ
Khuthi alAAafwa wa/mur bilAAurfiwaaAArid AAani aljahileen

Hausa
 
Ka riƙi abin da ya sauƙaƙa; Kuma ka yi umurni da alhẽri, Kuma ka kau da kai daga jăhilai.

Ayah  7:200  الأية
وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ الشَّيْطَانِ نَزْغٌ فَاسْتَعِذْ بِاللهِ ۚ إِنَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
Wa-imma yanzaghannaka mina ashshaytaninazghun fastaAAith billahi innahusameeAAun AAaleem

Hausa
 
Kuma imma wata fizga daga Shaiɗan ta fizge ka, sai ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle ne shi, Mai jĩ ne, Masani.

Ayah  7:201  الأية
إِنَّ الَّذِينَ اتَّقَوْا إِذَا مَسَّهُمْ طَائِفٌ مِّنَ الشَّيْطَانِ تَذَكَّرُوا فَإِذَا هُم مُّبْصِرُونَ
Inna allatheena ittaqaw ithamassahum ta-ifun mina ashshaytani tathakkaroofa-itha hum mubsiroon

Hausa
 
Lalle ne waɗanda suka yi taƙawa idan wani tăshin hankali daga Shaiɗan ya shăfe su, sai su tuna (Allah) sai gă su, sun zama masu basĩra.

Ayah  7:202  الأية
وَإِخْوَانُهُمْ يَمُدُّونَهُمْ فِي الْغَيِّ ثُمَّ لَا يُقْصِرُونَ
Wa-ikhwanuhum yamuddoonahum feealghayyi thumma la yuqsiroon

Hausa
 
Kuma 'yan'uwan su (shaiɗanu) sună taimakon su a cikin ɓata, sa'an nan kuma bă su taƙaităwa.

Ayah  7:203  الأية
وَإِذَا لَمْ تَأْتِهِم بِآيَةٍ قَالُوا لَوْلَا اجْتَبَيْتَهَا ۚ قُلْ إِنَّمَا أَتَّبِعُ مَا يُوحَىٰ إِلَيَّ مِن رَّبِّي ۚ هَٰذَا بَصَائِرُ مِن رَّبِّكُمْ وَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Wa-itha lam ta/tihim bi-ayatinqaloo lawla ijtabaytaha qul innamaattabiAAu ma yooha ilayya min rabbee hathabasa-iru min rabbikum wahudan warahmatun liqawminyu/minoon

Hausa
 
Kuma idan ba ka je musu da wata ăyă ba, su ce: "Don me ba ka ƙăga ta ba?" Ka ce: "Abin sani kawai, ină biyar abin da aka yő wahayi zuwa gare ni ne, daga Ubangjina. Wannan abũbuwan kula ne daga Ubangijinku, da shiriya da rahama ga mutăne waɗanda suke yin imăni."

Ayah  7:204  الأية
وَإِذَا قُرِئَ الْقُرْآنُ فَاسْتَمِعُوا لَهُ وَأَنصِتُوا لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ
Wa-itha quri-a alqur-anu fastamiAAoolahu waansitoo laAAallakum turhamoon

Hausa
 
Kuma idan an karanta Alƙur'ăni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammăninku, ană yi muku rahama.

Ayah  7:205  الأية
وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعًا وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالْآصَالِ وَلَا تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ
Wathkur rabbaka fee nafsikatadarruAAan wakheefatan wadoona aljahri mina alqawli bilghuduwwiwal-asali wala takun mina alghafileen

Hausa
 
Kuma ka ambaci Ubangijinka, a cikin ranka da ƙanƙan da kai, da tsőro, kuma kőmabăyan bayyanawa na magana, da săfe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu.

Ayah  7:206  الأية
إِنَّ الَّذِينَ عِندَ رَبِّكَ لَا يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِهِ وَيُسَبِّحُونَهُ وَلَهُ يَسْجُدُونَ ۩
Inna allatheena AAinda rabbika layastakbiroona AAan AAibadatihi wayusabbihoonahuwalahu yasjudoon

Hausa
 
Lalle ne, waɗanda ke wurin Ubangijinka bă su yin girman kai ga bauta Masa, kuma sună tsarake shi da tasbĩhi, kuma a gare shi suke yin sujada. 





© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us