1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
يَسْأَلُونَكَ عَنِ الْأَنفَالِ ۖ قُلِ الْأَنفَالُ لِلَّهِ وَالرَّسُولِ ۖ
فَاتَّقُوا اللهَ وَأَصْلِحُوا ذَاتَ بَيْنِكُمْ ۖ وَأَطِيعُوا اللهَ
وَرَسُولَهُ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
Yas-aloonaka AAani al-anfali qulial-anfalu lillahi warrasooli fattaqooAllaha
waaslihoo thata baynikum waateeAAooAllaha warasoolahu in kuntum mu/mineen
Hausa
Suna tambayar ka ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi
Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga
Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai."
|
Ayah 8:2 الأية
إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ الَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ اللهُ وَجِلَتْ قُلُوبُهُمْ
وَإِذَا تُلِيَتْ عَلَيْهِمْ آيَاتُهُ زَادَتْهُمْ إِيمَانًا وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ
يَتَوَكَّلُونَ
Innama almu/minoona allatheenaitha thukira Allahu wajilat quloobuhum
wa-ithatuliyat AAalayhim ayatuhu zadat-hum eemananwaAAala rabbihim yatawakkaloon
Hausa
Abin sani kawai, nũminai sũ ne waɗanda suke idan an ambaci, Allah, zukãtansu su
firgita, kuma idan an karanta ãyõyinSa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãni, kuma ga
Ubangijinsu suke dõgara.
|
Ayah 8:3 الأية
الَّذِينَ يُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ
Allatheena yuqeemoona assalatawamimma razaqnahum yunfiqoon
Hausa
Waɗanda suke tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azũrtã su sunã ciyarwa.
|
Ayah 8:4 الأية
أُولَٰئِكَ هُمُ الْمُؤْمِنُونَ حَقًّا ۚ لَّهُمْ دَرَجَاتٌ عِندَ رَبِّهِمْ
وَمَغْفِرَةٌ وَرِزْقٌ كَرِيمٌ
Ola-ika humu almu/minoona haqqanlahum darajatun AAinda rabbihim wamaghfiratun
warizqunkareem
Hausa
Waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya. Sunã da darajõji a wurin Ubangijinsu, da wata
gãfara da arziki na karimci.
|
Ayah 8:5 الأية
كَمَا أَخْرَجَكَ رَبُّكَ مِن بَيْتِكَ بِالْحَقِّ وَإِنَّ فَرِيقًا مِّنَ
الْمُؤْمِنِينَ لَكَارِهُونَ
Kama akhrajaka rabbuka min baytika bilhaqqiwa-inna fareeqan mina almu/mineena
lakarihoon
Hausa
Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka da gaskiya, alhãli kuwa
lalle wani ɓangare na mũminai, haƙĩƙa, sunã ƙyãma.
|
Ayah 8:6 الأية
يُجَادِلُونَكَ فِي الْحَقِّ بَعْدَمَا تَبَيَّنَ كَأَنَّمَا يُسَاقُونَ إِلَى
الْمَوْتِ وَهُمْ يَنظُرُونَ
Yujadiloonaka fee alhaqqibaAAda ma tabayyana kaannama yusaqoona ilaalmawti wahum
yanthuroon
Hausa
Sunã jãyayya da kai a cikin (sha'anin) gaskiya a bãyan tã bayYanã, kamar dai
lalle anã kõra su zuwa ga mutuwa ne alhãli kuwa sunã kallo.
|
Ayah 8:7 الأية
وَإِذْ يَعِدُكُمُ اللهُ إِحْدَى الطَّائِفَتَيْنِ أَنَّهَا لَكُمْ وَتَوَدُّونَ
أَنَّ غَيْرَ ذَاتِ الشَّوْكَةِ تَكُونُ لَكُمْ وَيُرِيدُ اللهُ أَن يُحِقَّ
الْحَقَّ بِكَلِمَاتِهِ وَيَقْطَعَ دَابِرَ الْكَافِرِينَ
Wa-ith yaAAidukumu Allahu ihdaatta-ifatayni annaha lakum watawaddoonaanna ghayra
thati ashshawkati takoonu lakumwayureedu Allahu an yuhiqqa alhaqqa
bikalimatihiwayaqtaAAa dabira alkafireen
Hausa
Kuma a lõkacin da Allah Yake yi muku alkawari da ɗayan ƙungiya biyu, cẽwa lalle
ita tãku ce: kuma kunã gũrin cẽwa lalle ƙungiya wadda bã ta da ƙaya ta kasance
gare ku, kuma Allah Yanã nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kuma Ya
kãtse ƙarshen kãfirai;
|
Ayah 8:8 الأية
لِيُحِقَّ الْحَقَّ وَيُبْطِلَ الْبَاطِلَ وَلَوْ كَرِهَ الْمُجْرِمُونَ
Liyuhiqqa alhaqqa wayubtilaalbatila walaw kariha almujrimoon
Hausa
Dõmin Ya tabbatar da gaskiya, kuma Ya ɓãta ƙarya, kuma kõdã mãsu laifi sun ƙi.
|
Ayah 8:9 الأية
إِذْ تَسْتَغِيثُونَ رَبَّكُمْ فَاسْتَجَابَ لَكُمْ أَنِّي مُمِدُّكُم بِأَلْفٍ
مِّنَ الْمَلَائِكَةِ مُرْدِفِينَ
Ith tastagheethoona rabbakum fastajabalakum annee mumiddukum bi-alfin mina
almala-ikatimurdifeen
Hausa
A lõkacin da kuke nẽman Ubangijinku tairnako, sai Ya karɓa muku cẽwa: "Lalle ne
Nĩ, Mai taimakon ku ne da dubu daga malã'iku, jẽre."
|
Ayah 8:10 الأية
وَمَا جَعَلَهُ اللهُ إِلَّا بُشْرَىٰ وَلِتَطْمَئِنَّ بِهِ قُلُوبُكُمْ ۚ وَمَا
النَّصْرُ إِلَّا مِنْ عِندِ اللهِ ۚ إِنَّ اللهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ
Wama jaAAalahu Allahu illabushra walitatma-inna bihi quloobukum wama annasruilla
min AAindi Allahi inna Allaha AAazeezunhakeem
Hausa
Kuma Allah bai sanya shi ba fãce Dõmin bishãra, kuma dõmin zukãtanku su natsu da
shi, kuma taimakon, bai zama ba fãce daga wurin Allah; Lalle ne Allah Mabuwãyi
ne, Mai hikima.
|
Ayah 8:11 الأية
إِذْ يُغَشِّيكُمُ النُّعَاسَ أَمَنَةً مِّنْهُ وَيُنَزِّلُ عَلَيْكُم مِّنَ
السَّمَاءِ مَاءً لِّيُطَهِّرَكُم بِهِ وَيُذْهِبَ عَنكُمْ رِجْزَ الشَّيْطَانِ
وَلِيَرْبِطَ عَلَىٰ قُلُوبِكُمْ وَيُثَبِّتَ بِهِ الْأَقْدَامَ
Ith yughashsheekumu annuAAasaamanatan minhu wayunazzilu AAalaykum mina
assama-imaan liyutahhirakum bihi wayuthhiba AAankumrijza ashshaytani waliyarbita
AAalaquloobikum wayuthabbita bihi al-aqdam
Hausa
A lõkacin da (Allah) Yake rufe ku da gyangyaɗi, ɗõmin aminci daga gare Shi, kuma
Yanã saukar da ruwa daga sama, a kanku, dõmin Ya tsarkake ku da shi, kuma Ya
tafiyar da ƙazantar Shaiɗan daga barinku, kuma dõmin Ya ɗaure a kan zukãtanku,
kuma Ya tabbatar da ƙafãfu da shi.
|
Ayah 8:12 الأية
إِذْ يُوحِي رَبُّكَ إِلَى الْمَلَائِكَةِ أَنِّي مَعَكُمْ فَثَبِّتُوا الَّذِينَ
آمَنُوا ۚ سَأُلْقِي فِي قُلُوبِ الَّذِينَ كَفَرُوا الرُّعْبَ فَاضْرِبُوا فَوْقَ
الْأَعْنَاقِ وَاضْرِبُوا مِنْهُمْ كُلَّ بَنَانٍ
Ith yoohee rabbuka ilaalmala-ikati annee maAAakum fathabbitoo allatheena
amanoosaolqee fee quloobi allatheena kafaroo arruAAba fadriboofawqa al-aAAnaqi
wadriboo minhum kulla banan
Hausa
A lõkacin da Ubangijinka Yake yin wahayi zuwa ga Malã'iku cẽwa: "Lalle ne Ni,
Inã tãre da ku, sai ku tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni: Zã Ni jẽfa tsõro a
cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta, sai ku yi dũka bisa ga wuyõyi kuma ku yi
dũka daga gare su ga dukkan yãtsu .
|
Ayah 8:13 الأية
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ شَاقُّوا اللهَ وَرَسُولَهُ ۚ وَمَن يُشَاقِقِ اللهَ
وَرَسُولَهُ فَإِنَّ اللهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ
Thalika bi-annahum shaqqoo Allahawarasoolahu waman yushaqiqi Allaha
warasoolahufa-inna Allaha shadeedu alAAiqab
Hausa
Wancan ne, dõmin lalle ne sũ, sunã sãɓa wa Allah da ManzonSa. Kuma wanda ya sãɓa
wa Allah da ManzonSa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
|
Ayah 8:14 الأية
ذَٰلِكُمْ فَذُوقُوهُ وَأَنَّ لِلْكَافِرِينَ عَذَابَ النَّارِ
Thalikum fathooqoohu waannalilkafireena AAathaba annar
Hausa
Wancan ne: "Ku ɗanɗane shi, kuma lalle ne akwai azãbar wuta ga kãfirai."
|
Ayah 8:15 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا لَقِيتُمُ الَّذِينَ كَفَرُوا زَحْفًا فَلَا
تُوَلُّوهُمُ الْأَدْبَارَ
Ya ayyuha allatheena amanooitha laqeetumu allatheena kafaroo zahfan
falatuwalloohumu al-adbar
Hausa
Yã kũ wacɗanda suka yiĩmãni! Idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta ga yãƙi, to,
kada ku jũya musu bãyayyakinku.
|
Ayah 8:16 الأية
وَمَن يُوَلِّهِمْ يَوْمَئِذٍ دُبُرَهُ إِلَّا مُتَحَرِّفًا لِّقِتَالٍ أَوْ
مُتَحَيِّزًا إِلَىٰ فِئَةٍ فَقَدْ بَاءَ بِغَضَبٍ مِّنَ اللهِ وَمَأْوَاهُ
جَهَنَّمُ ۖ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ
Waman yuwallihim yawma-ithin duburahuilla mutaharrifan liqitalin aw
mutahayyizanila fi-atin faqad baa bighadabin mina Allahiwama/wahu jahannamu
wabi/sa almaseer
Hausa
Kuma duka wanda ya jũya musu bãyansa a yinin nan, fãce wanda ya karkata dõmin
kõɗayya, kõ kuwa wanda ya jẽ dõmin haɗuwa da wata ƙungiya, to, lalle ne ya kõma
da fushi daga Allah, kuma matattararsa Jahannama, kuma tir da makõma ita!
|
Ayah 8:17 الأية
فَلَمْ تَقْتُلُوهُمْ وَلَٰكِنَّ اللهَ قَتَلَهُمْ ۚ وَمَا رَمَيْتَ إِذْ
رَمَيْتَ وَلَٰكِنَّ اللهَ رَمَىٰ ۚ وَلِيُبْلِيَ الْمُؤْمِنِينَ مِنْهُ بَلَاءً
حَسَنًا ۚ إِنَّ اللهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
Falam taqtuloohum walakinna Allahaqatalahum wama ramayta ith ramayta
walakinnaAllaha rama waliyubliya almu/mineena minhu balaanhasanan inna Allaha
sameeAAun AAaleem
Hausa
To, bã kũ ne kuka kashe su ba; kuma amma Allah ne Ya kashe su: kuma ba ka yi
jĩfa ba a lõkacin da ka yi jĩfa; kuma amma Allah ne Ya yi jĩfar. Kuma dõminYa
jarraba Musulmi da jarrabãwa mai kyau daga gare shi. Kuma Allah Mai ji ne,
Masani.
|
Ayah 8:18 الأية
ذَٰلِكُمْ وَأَنَّ اللهَ مُوهِنُ كَيْدِ الْكَافِرِينَ
Thalikum waanna Allaha moohinukaydi alkafireen
Hausa
Wancan ne, kuma lalle ne, Allah Mai raunana kaidin kãfirai ne.
|
Ayah 8:19 الأية
إِن تَسْتَفْتِحُوا فَقَدْ جَاءَكُمُ الْفَتْحُ ۖ وَإِن تَنتَهُوا فَهُوَ خَيْرٌ
لَّكُمْ ۖ وَإِن تَعُودُوا نَعُدْ وَلَن تُغْنِيَ عَنكُمْ فِئَتُكُمْ شَيْئًا
وَلَوْ كَثُرَتْ وَأَنَّ اللهَ مَعَ الْمُؤْمِنِينَ
In tastaftihoo faqad jaakumualfathu wa-in tantahoo fahuwa khayrun lakum
wa-intaAAoodoo naAAud walan tughniya AAankum fi-atukum shay-an walawkathurat
waanna Allaha maAAa almu/mineen
Hausa
Idan kun yi alfãnun cin nasara to lalle nasarar tã je muku, kuma idan kun hanu,
to Shi ne Mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun kõma zã Mu kõma, kuma jama'arku
bã zã ta wadãtar muku da kõme ba, kõ dã tã yi yawa. Kuma lalle ne cẽwa Allah
Yanã tãre da mũminai!
|
Ayah 8:20 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللهَ وَرَسُولَهُ وَلَا تَوَلَّوْا
عَنْهُ وَأَنتُمْ تَسْمَعُونَ
Ya ayyuha allatheena amanooateeAAoo Allaha warasoolahu wala tawallawAAanhu
waantum tasmaAAoon
Hausa
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku jũya
daga barinSa, alhãli kunã ji.
|
Ayah 8:21 الأية
وَلَا تَكُونُوا كَالَّذِينَ قَالُوا سَمِعْنَا وَهُمْ لَا يَسْمَعُونَ
Wala takoonoo kallatheenaqaloo samiAAna wahum la yasmaAAoon
Hausa
Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka ce: "Mun ji, alhãli kuwa sũ bã su ji."
|
Ayah 8:22 الأية
إِنَّ شَرَّ الدَّوَابِّ عِندَ اللهِ الصُّمُّ الْبُكْمُ الَّذِينَ لَا
يَعْقِلُونَ
Inna sharra addawabbi AAindaAllahi assummu albukmu allatheena layaAAqiloon
Hausa
Lalle ne, mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne kurãme, bẽbãye, waɗanda bã,
su yin hankali.
|
Ayah 8:23 الأية
وَلَوْ عَلِمَ اللهُ فِيهِمْ خَيْرًا لَّأَسْمَعَهُمْ ۖ وَلَوْ أَسْمَعَهُمْ
لَتَوَلَّوا وَّهُم مُّعْرِضُونَ
Walaw AAalima Allahu feehim khayranlaasmaAAahum walaw asmaAAahum latawallaw
wahum muAAridoon
Hausa
Dã Allah Yã san wani alhẽri a cikinsu, dã Yã jiyar da su, kuma kõ da Yãjiyar da
su, haƙĩƙa,dã sun jũya , alhãli sũ, sunã mãsu hinjirẽwa.
|
Ayah 8:24 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اسْتَجِيبُوا لِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ إِذَا
دَعَاكُمْ لِمَا يُحْيِيكُمْ ۖ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللهَ يَحُولُ بَيْنَ الْمَرْءِ
وَقَلْبِهِ وَأَنَّهُ إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ
Yaayyuha allatheena amanooistajeeboo lillahi walirrasooli itha daAAakumlima
yuhyeekum waAAlamoo anna Allahayahoolu bayna almar-i waqalbihi waannahu ilayhi
tuhsharoon
Hausa
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku karɓa wa Allah, kuma ku karɓa wa Manzo, idan Ya
kirãye ku zuwa ga abin da Yake rãyar da ku; Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã
shãmakacẽwa a tsakãnin mutum da zũciyarsa, kuma lalle ne Shĩ, a zuwa gare Shi
ake tãra ku.
|
Ayah 8:25 الأية
وَاتَّقُوا فِتْنَةً لَّا تُصِيبَنَّ الَّذِينَ ظَلَمُوا مِنكُمْ خَاصَّةً ۖ
وَاعْلَمُوا أَنَّ اللهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ
Wattaqoo fitnatan la tuseebannaallatheena thalamoo minkum khassatanwaAAlamoo
anna Allaha shadeedu alAAiqab
Hausa
Kuma ku ji tsõron fitina wadda bã ta sãmun waɗanda suka yi zãlunci daga gare ku
kẽɓe, kuma ku sani, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
|
Ayah 8:26 الأية
وَاذْكُرُوا إِذْ أَنتُمْ قَلِيلٌ مُّسْتَضْعَفُونَ فِي الْأَرْضِ تَخَافُونَ أَن
يَتَخَطَّفَكُمُ النَّاسُ فَآوَاكُمْ وَأَيَّدَكُم بِنَصْرِهِ وَرَزَقَكُم مِّنَ
الطَّيِّبَاتِ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Wathkuroo ith antumqaleelun mustadAAafoona fee al-ardi takhafoonaan
yatakhattafakumu annasu faawakumwaayyadakum binasrihi warazaqakum mina
attayyibatilaAAallakum tashkuroon
Hausa
Ku tuna a lõkacin da kuke kaɗan, waɗanda ake raunanarwã a cikin ƙasa kunã tsõron
mutãne su cafe ku, sai Ya tattara ku (a wurin natsuwa, Maɗina), kuma Ya ƙarfafã
ku da taimakonSa kuma Ya azurtã ku daga abũbuwa mãsu dãɗi; Tsammãninku, kunã
gõdẽwa.
|
Ayah 8:27 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَخُونُوا اللهَ وَالرَّسُولَ وَتَخُونُوا
أَمَانَاتِكُمْ وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ
Ya ayyuha allatheena amanoola takhoonoo Allaha warrasoola watakhoonooamanatikum
waantum taAAlamoon
Hausa
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yaudari Allah da ManzonSa, kuma ku yaudari
amãnõninku, alhãli kuwa kunã sane.
|
Ayah 8:28 الأية
وَاعْلَمُوا أَنَّمَا أَمْوَالُكُمْ وَأَوْلَادُكُمْ فِتْنَةٌ وَأَنَّ اللهَ
عِندَهُ أَجْرٌ عَظِيمٌ
WaAAlamoo annama amwalukumwaawladukum fitnatun waanna Allaha AAindahu
ajrunAAatheem
Hausa
Kuma ku sani cẽwa abin sani kawai, dũkiyõyinku da 'ya'yanku, wata fitina ce,
kuma lalle ne Allah, a wurinSa, akwai ijãra mai girma.
|
Ayah 8:29 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِن تَتَّقُوا اللهَ يَجْعَل لَّكُمْ فُرْقَانًا
وَيُكَفِّرْ عَنكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ۗ وَاللهُ ذُو الْفَضْلِ
الْعَظِيمِ
Ya ayyuha allatheena amanooin tattaqoo Allaha yajAAal lakum furqananwayukaffir
AAankum sayyi-atikum wayaghfir lakum wallahuthoo alfadli alAAatheem
Hausa
Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun bi Allah da taƙawa, zai sanyã muku
mararraba (da tsõro) kuma Ya kankare ƙanãnan zunubanku daga barinku. Kuma Ya
gãfartã muku. Kuma Allah ne Ma'abũcin falalã Mai girma.
|
Ayah 8:30 الأية
وَإِذْ يَمْكُرُ بِكَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِيُثْبِتُوكَ أَوْ يَقْتُلُوكَ أَوْ
يُخْرِجُوكَ ۚ وَيَمْكُرُونَ وَيَمْكُرُ اللهُ ۖ وَاللهُ خَيْرُ الْمَاكِرِينَ
Wa-ith yamkuru bika allatheenakafaroo liyuthbitooka aw yaqtulooka aw yukhrijooka
wayamkuroonawayamkuru Allahu wallahu khayru almakireen
Hausa
Kuma a lõkacin da waɗanda suka kãfirta sukẽ yin mãkirci game da kai, dõmin su
tabbatar da kai, kõ kuwa su kashe ka, kõ kuwa su fitar da kai, sunã mãkirci kuma
Allah Yanã mayar musa da mãkirci kuma Allah ne Mafificin mãsu mãkirci.
|
Ayah 8:31 الأية
وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا قَالُوا قَدْ سَمِعْنَا لَوْ نَشَاءُ
لَقُلْنَا مِثْلَ هَٰذَا ۙ إِنْ هَٰذَا إِلَّا أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ
Wa-itha tutla AAalayhim ayatunaqaloo qad samiAAna law nashao laqulnamithla hatha
in hatha illa asateerual-awwaleen
Hausa
Kuma idan aka karanta, ãyõyinMu a kansu, sukan ce: "Lalle ne mun ji dã muna so,
haƙĩƙa, da mun faɗi irin wannan; wannan bai zama ba fãce tãtsunãyõyin mutãnen
farko."
|
Ayah 8:32 الأية
وَإِذْ قَالُوا اللهُمَّ إِن كَانَ هَٰذَا هُوَ الْحَقَّ مِنْ عِندِكَ فَأَمْطِرْ
عَلَيْنَا حِجَارَةً مِّنَ السَّمَاءِ أَوِ ائْتِنَا بِعَذَابٍ أَلِيمٍ
Wa-ith qaloo allahummain kana hatha huwa alhaqqa min AAindika faamtirAAalayna
hijaratan mina assama-iawi i/tina biAAathabin aleem
Hausa
A lõkacin da suka ce: "Yã Allah! Idan wannan ya kasancc shĩ ne gaskiya daga
wurinKa, sai Ka yi ruwan duwãtsu, a kanmu, daga sama, kõ kuwa Kazõ mana da wata
azãba, mai raɗaɗi."
|
Ayah 8:33 الأية
وَمَا كَانَ اللهُ لِيُعَذِّبَهُمْ وَأَنتَ فِيهِمْ ۚ وَمَا كَانَ اللهُ
مُعَذِّبَهُمْ وَهُمْ يَسْتَغْفِرُونَ
Wama kana AllahuliyuAAaththibahum waanta feehim wama kanaAllahu muAAaththibahum
wahum yastaghfiroon
Hausa
Kuma Allah bai kasance Yanã yi musu azãba ba alhãli kuwa kai kanã cikinsu, kuma
Allah bai kasance Mai yi musu azãba ba alhãli kuwa sunã yin istigfãri.
|
Ayah 8:34 الأية
وَمَا لَهُمْ أَلَّا يُعَذِّبَهُمُ اللهُ وَهُمْ يَصُدُّونَ عَنِ الْمَسْجِدِ
الْحَرَامِ وَمَا كَانُوا أَوْلِيَاءَهُ ۚ إِنْ أَوْلِيَاؤُهُ إِلَّا الْمُتَّقُونَ
وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Wama lahum alla yuAAaththibahumuAllahu wahum yasuddoona AAani almasjidi
alharamiwama kanoo awliyaahu in awliyaohu illaalmuttaqoona walakinna aktharahum
la yaAAlamoon
Hausa
Kuma mẽne ne a gare su da Allah ba zai yi musu azãba ba, alhãli kuwa sũ, sunã
kangẽwa daga Masallaci Mai alfarma kuma ba su kasance majiɓintanSa ba? Bãbu
majiɓintanSa fãce mãsu taƙawa. Kuma mafi yawansu ba su sani ba.
|
Ayah 8:35 الأية
وَمَا كَانَ صَلَاتُهُمْ عِندَ الْبَيْتِ إِلَّا مُكَاءً وَتَصْدِيَةً ۚ فَذُوقُوا
الْعَذَابَ بِمَا كُنتُمْ تَكْفُرُونَ
Wama kana salatuhumAAinda albayti illa mukaan watasdiyatan fathooqooalAAathaba
bima kuntum takfuroon
Hausa
Kuma sallarsu a wurin ¦ãkin ba ta kasance ba fãce shẽwa da yãyã; sai ku ɗanɗani
azãba sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci.
|
Ayah 8:36 الأية
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا يُنفِقُونَ أَمْوَالَهُمْ لِيَصُدُّوا عَن سَبِيلِ
اللهِ ۚ فَسَيُنفِقُونَهَا ثُمَّ تَكُونُ عَلَيْهِمْ حَسْرَةً ثُمَّ يُغْلَبُونَ
ۗ وَالَّذِينَ كَفَرُوا إِلَىٰ جَهَنَّمَ يُحْشَرُونَ
Inna allatheena kafaroo yunfiqoonaamwalahum liyasuddoo AAan sabeeli
Allahifasayunfiqoonaha thumma takoonu AAalayhim hasratanthumma yughlaboona
wallatheena kafaroo ilajahannama yuhsharoon
Hausa
Lalle ne waɗanda suka kãfirta, sunã ciyar da dũkiyõyinsu, dõmin su kange daga
hanyar Allah; to, zã a su ciyar da ita, sa' an nan kuma ta kasance nadãma a
kansu, sa'an nan kuma a rinjãye su. Kuma waɗanda suka kãfirta zuwa ga Jahannama
ake tãra su;
|
Ayah 8:37 الأية
لِيَمِيزَ اللهُ الْخَبِيثَ مِنَ الطَّيِّبِ وَيَجْعَلَ الْخَبِيثَ بَعْضَهُ
عَلَىٰ بَعْضٍ فَيَرْكُمَهُ جَمِيعًا فَيَجْعَلَهُ فِي جَهَنَّمَ ۚ أُولَٰئِكَ هُمُ
الْخَاسِرُونَ
Liyameeza Allahu alkhabeetha mina attayyibiwayajAAala alkhabeetha baAAdahu AAala
baAAdinfayarkumahu jameeAAan fayajAAalahu fee jahannama ola-ikahumu alkhasiroon
Hausa
Dõmin Allah Ya rarrabe mummũna daga mai kyau, kuma Ya sanya mummũnan, sãshensa a
kan sãshe, sa'an nan Ya shirga shi gabã daya, sa'an nan Ya sanyã shi a cikin
Jahannama. Waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
|
Ayah 8:38 الأية
قُل لِّلَّذِينَ كَفَرُوا إِن يَنتَهُوا يُغْفَرْ لَهُم مَّا قَدْ سَلَفَ وَإِن
يَعُودُوا فَقَدْ مَضَتْ سُنَّتُ الْأَوَّلِينَ
Qul lillatheena kafaroo in yantahooyughfar lahum ma qad salafa wa-in yaAAoodoo
faqad madatsunnatu al-awwaleen
Hausa
Ka ce wa waɗanda suka kãfirta, idan sun hanu, zã a gãfarta musu abin da ya riga
ya shige, kuma idan sun kõma, to, hanyar kãfiran farko, haƙĩƙa, ta shũɗe.
|
Ayah 8:39 الأية
وَقَاتِلُوهُمْ حَتَّىٰ لَا تَكُونَ فِتْنَةٌ وَيَكُونَ الدِّينُ كُلُّهُ لِلَّهِ ۚ
فَإِنِ انتَهَوْا فَإِنَّ اللهَ بِمَا يَعْمَلُونَ بَصِيرٌ
Waqatiloohum hatta latakoona fitnatun wayakoona addeenu kulluhu lillahifa-ini
intahaw fa-inna Allaha bima yaAAmaloona baseer
Hausa
Kuma ku yãƙe su har wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini dukansa ya
kasance na Allah. To, idan sun hanu to lalle ne, Allah ia abin da kuke aikatãwa
Mai gani ne.
|
Ayah 8:40 الأية
وَإِن تَوَلَّوْا فَاعْلَمُوا أَنَّ اللهَ مَوْلَاكُمْ ۚ نِعْمَ الْمَوْلَىٰ
وَنِعْمَ النَّصِيرُ
Wa-in tawallaw faAAlamoo anna Allahamawlakum niAAma almawla waniAAma annaseer
Hausa
Kuma idan sun jũya, to, ku sani cẽwa lalle Allah ne Majiɓincinku: Mãdalla da
Majiɓinci, kuma mãdalla da Mai taimako, Shĩ.
|
Ayah 8:41 الأية
وَاعْلَمُوا أَنَّمَا غَنِمْتُم مِّن شَيْءٍ فَأَنَّ لِلَّهِ خُمُسَهُ
وَلِلرَّسُولِ وَلِذِي الْقُرْبَىٰ وَالْيَتَامَىٰ وَالْمَسَاكِينِ وَابْنِ
السَّبِيلِ إِن كُنتُمْ آمَنتُم بِاللهِ وَمَا أَنزَلْنَا عَلَىٰ عَبْدِنَا
يَوْمَ الْفُرْقَانِ يَوْمَ الْتَقَى الْجَمْعَانِ ۗ وَاللهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ
قَدِيرٌ
WaAAlamoo annama ghanimtummin shay-in faanna lillahi khumusahu
walirrasooliwalithee alqurba walyatama walmasakeeniwabni assabeeli in kuntum
amantum billahiwama anzalna AAala AAabdina yawmaalfurqani yawma iltaqa
aljamAAani wallahuAAala kulli shay-in qadeer
Hausa
Kuma ka sani, abin sani kawai, abin da kuka sãmi ganĩma daga wani abu, to, lalle
ne Allah Yanã da humusinsa kuma da Manzo, kuma da mãsu zumunta, da marãyu da
miskĩnai da ɗan hanya, idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah da abin da Muka
saukar a kan bãwanMu a Rãnar Rarrabẽwa, a Rãnar da jama'a biyu suka haɗu, kuma
Allah ne, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi.
|
Ayah 8:42 الأية
إِذْ أَنتُم بِالْعُدْوَةِ الدُّنْيَا وَهُم بِالْعُدْوَةِ الْقُصْوَىٰ وَالرَّكْبُ
أَسْفَلَ مِنكُمْ ۚ وَلَوْ تَوَاعَدتُّمْ لَاخْتَلَفْتُمْ فِي الْمِيعَادِ ۙ
وَلَٰكِن لِّيَقْضِيَ اللهُ أَمْرًا كَانَ مَفْعُولًا لِّيَهْلِكَ مَنْ هَلَكَ
عَن بَيِّنَةٍ وَيَحْيَىٰ مَنْ حَيَّ عَن بَيِّنَةٍ ۗ وَإِنَّ اللهَ لَسَمِيعٌ
عَلِيمٌ
Ith antum bilAAudwati addunyawahum bilAAudwati alquswa warrakbuasfala minkum
walaw tawaAAadtum lakhtalaftum feealmeeAAadi walakin liyaqdiya Allahuamran kana
mafAAoolan liyahlika man halaka AAan bayyinatinwayahya man hayya AAan bayyinatin
wa-innaAllaha lasameeAAun AAaleem
Hausa
A lõkacin da kuke a gãɓa ta kusa sũ kuma sunã a gãɓa tanẽsa, kuma ãyarin yana a
wuri mafi gangarãwa daga gare ku, kuma dã kun yi wa jũna wa'adi, dã kun sãɓa ga
wa'adin; kuma amma dõmin Allah Ya hukunta abin da yake ya kasance abin aikatãwa.
Dõmin wanda yake halaka ya halaka daga shaida, kuma mai rãyuwa ya rãyu daga
shaida, kuma lalle Allah ne, haƙĩƙa, Mai ji Masani.
|
Ayah 8:43 الأية
إِذْ يُرِيكَهُمُ اللهُ فِي مَنَامِكَ قَلِيلًا ۖ وَلَوْ أَرَاكَهُمْ كَثِيرًا
لَّفَشِلْتُمْ وَلَتَنَازَعْتُمْ فِي الْأَمْرِ وَلَٰكِنَّ اللهَ سَلَّمَ ۗ
إِنَّهُ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ
Ith yureekahumu Allahu fee manamikaqaleelan walaw arakahum katheeran lafashiltum
walatanazaAAtumfee al-amri walakinna Allaha sallama innahuAAaleemun bithati
assudoor
Hausa
A lõkacin da Allah Yake nũna maka sũ sunã kaɗan, a cikin barcinka, kuma dã Ya
nũna maka su sunã da, yawa, lalle ne dã kun ji tsõro, kuma lalle ne dã kun yi
jãyayya a cikin al'amarin, kuma amma Allah Yã tsare ku: Lalle Shĩ ne Masani ga
abin da yake a cikin ƙirãza.
|
Ayah 8:44 الأية
وَإِذْ يُرِيكُمُوهُمْ إِذِ الْتَقَيْتُمْ فِي أَعْيُنِكُمْ قَلِيلًا
وَيُقَلِّلُكُمْ فِي أَعْيُنِهِمْ لِيَقْضِيَ اللهُ أَمْرًا كَانَ مَفْعُولًا ۗ
وَإِلَى اللهِ تُرْجَعُ الْأُمُورُ
Wa-ith yureekumoohum ithiiltaqaytum fee aAAyunikum qaleelan wayuqallilukum fee
aAAyunihimliyaqdiya Allahu amran kana mafAAoolan wa-ilaAllahi turjaAAu al-omoor
Hausa
Kuma a lõkacin da Yake nũna muku su, a lõkacin da kuka haɗu, a cikin idanunku
sunã kaɗan, kuma Ya ƙarantar da ku a cikin idanunsu dõmin Allah Ya hukunta wani
al'amari wanda ya kasance abin aikatãwa. Kuma zuwa ga Allah ake mayar da
al'umurra.
|
Ayah 8:45 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا لَقِيتُمْ فِئَةً فَاثْبُتُوا وَاذْكُرُوا
اللهَ كَثِيرًا لَّعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Ya ayyuha allatheena amanooitha laqeetum fi-atan fathbutoo wathkurooAllaha
katheeran laAAallakum tuflihoon
Hausa
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun haɗu da wata ƙungiyar yãƙi, to, ku
tabbata, kuma ku ambaci Allah da yawa, tsammãninku kunã cin nasara.
|
Ayah 8:46 الأية
وَأَطِيعُوا اللهَ وَرَسُولَهُ وَلَا تَنَازَعُوا فَتَفْشَلُوا وَتَذْهَبَ
رِيحُكُمْ ۖ وَاصْبِرُوا ۚ إِنَّ اللهَ مَعَ الصَّابِرِينَ
WaateeAAoo Allaha warasoolahuwala tanazaAAoo fatafshaloo watathhaba
reehukumwasbiroo inna Allaha maAAa assabireen
Hausa
Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku yi jãyayya har ku raunana
kuma iskarku ta tafi, kuma ku yi haƙuri. Lalle ne Allah Yanã tãre da mãsu
haƙuri.
|
Ayah 8:47 الأية
وَلَا تَكُونُوا كَالَّذِينَ خَرَجُوا مِن دِيَارِهِم بَطَرًا وَرِئَاءَ النَّاسِ
وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللهِ ۚ وَاللهُ بِمَا يَعْمَلُونَ مُحِيطٌ
Wala takoonoo kallatheenakharajoo min diyarihim bataran wari-aa
annasiwayasuddoona AAan sabeeli Allahi wallahubima yaAAmaloona muheet
Hausa
Kada ku kasance kamar waɗanda suka fita daga gidãjensu , sunã mãsu alfahari da
yin riya ga mutãne, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma Allah ne ga abin
da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa.
|
Ayah 8:48 الأية
وَإِذْ زَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ وَقَالَ لَا غَالِبَ لَكُمُ
الْيَوْمَ مِنَ النَّاسِ وَإِنِّي جَارٌ لَّكُمْ ۖ فَلَمَّا تَرَاءَتِ الْفِئَتَانِ
نَكَصَ عَلَىٰ عَقِبَيْهِ وَقَالَ إِنِّي بَرِيءٌ مِّنكُمْ إِنِّي أَرَىٰ مَا لَا
تَرَوْنَ إِنِّي أَخَافُ اللهَ ۚ وَاللهُ شَدِيدُ الْعِقَابِ
Wa-ith zayyana lahumu ashshaytanuaAAmalahum waqala la ghaliba lakumualyawma mina
annasi wa-innee jarun lakumfalamma taraati alfi-atani nakasaAAala AAaqibayhi
waqala innee baree-on minkum inneeara ma la tarawna innee akhafu Allahawallahu
shadeedu alAAiqab
Hausa
Kuma a lõkacin da Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, kuma ya ce: "Bãbu marinjayi
a gareku a yau daga mutãne, kuma nĩ maƙwabci ne gare ku." To, a lõkacin da
ƙungiya biyu suka haɗu, ya kõma a kan digãdigansa, kuma ya ce: "Lalle ne nĩ
barrantacce ne daga gare ku! Nĩ inã ganin abin da bã ku gani; ni inã tsõron
Allah: Kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne."
|
Ayah 8:49 الأية
إِذْ يَقُولُ الْمُنَافِقُونَ وَالَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ غَرَّ هَٰؤُلَاءِ
دِينُهُمْ ۗ وَمَن يَتَوَكَّلْ عَلَى اللهِ فَإِنَّ اللهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ
Ith yaqoolu almunafiqoona wallatheenafee quloobihim maradun gharra
haola-ideenuhum waman yatawakkal AAala Allahi fa-inna AllahaAAazeezun hakeem
Hausa
A lõkacin da munãfukai da waɗanda suke akwai cũtã a cikin zukãtansu, suke cẽwa:
"Addĩnin waɗannan yã rũɗe su" Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, lalle ne Allah
Mabuwãyi ne, Mai hikima.
|
Ayah 8:50 الأية
وَلَوْ تَرَىٰ إِذْ يَتَوَفَّى الَّذِينَ كَفَرُوا ۙ الْمَلَائِكَةُ يَضْرِبُونَ
وُجُوهَهُمْ وَأَدْبَارَهُمْ وَذُوقُوا عَذَابَ الْحَرِيقِ
Walaw tara ith yatawaffaallatheena kafaroo almala-ikatu yadriboonawujoohahum
waadbarahum wathooqoo AAathaba alhareeq
Hausa
Kuma dã kã gani, a lõkacin da Malã'iku suke karɓar rãyukan waɗanda suka kãfirta,
sunã dukar fuskõkinsu da ɗuwãwunsu, kuma suna cẽwa: "Ku ɗanɗani azãbar Gõbara."
|
Ayah 8:51 الأية
ذَٰلِكَ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيكُمْ وَأَنَّ اللهَ لَيْسَ بِظَلَّامٍ
لِّلْعَبِيدِ
Thalika bima qaddamat aydeekumwaanna Allaha laysa bithallaminlilAAabeed
Hausa
"Wancan sabõda abin da hannãyenku suka gabãtar ne. Kuma lalle ne, Allah bai zama
Mai zãlunci ba ga, bãyinSa."
|
Ayah 8:52 الأية
كَدَأْبِ آلِ فِرْعَوْنَ ۙ وَالَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ كَفَرُوا بِآيَاتِ اللهِ
فَأَخَذَهُمُ اللهُ بِذُنُوبِهِمْ ۗ إِنَّ اللهَ قَوِيٌّ شَدِيدُ الْعِقَابِ
Kada/bi ali firAAawna wallatheenamin qablihim kafaroo bi-ayati Allahi
faakhathahumuAllahu bithunoobihim inna Allaha qawiyyunshadeedu alAAiqab
Hausa
"Kamar al'ãdar mutãnen Fir'auna da waɗanda suke gabãninsu, sun kãfirta da ãyõyin
Allah, sai Allah Ya kãma su da zunubansu. Lalle Allah ne Mai ƙarfi, Mai tsananin
uƙũba.
|
Ayah 8:53 الأية
ذَٰلِكَ بِأَنَّ اللهَ لَمْ يَكُ مُغَيِّرًا نِّعْمَةً أَنْعَمَهَا عَلَىٰ قَوْمٍ
حَتَّىٰ يُغَيِّرُوا مَا بِأَنفُسِهِمْ ۙ وَأَنَّ اللهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
Thalika bi-anna Allaha lamyaku mughayyiran niAAmatan anAAamaha AAala qawmin
hattayughayyiroo ma bi-anfusihim waanna Allaha sameeAAunAAaleem
Hausa
"Wancan ne, dõmin lalle ne, Allah bai kasance Mai canza wata ni'ima wadda ya
ni'imtar da ita a kan wasu mutãne ba fãce sun sãke abin da yake ga rãyukansu,
kuma dõmin lalle Allah ne Mai jĩ,Masani."
|
Ayah 8:54 الأية
كَدَأْبِ آلِ فِرْعَوْنَ ۙ وَالَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ كَذَّبُوا بِآيَاتِ
رَبِّهِمْ فَأَهْلَكْنَاهُم بِذُنُوبِهِمْ وَأَغْرَقْنَا آلَ فِرْعَوْنَ ۚ وَكُلٌّ
كَانُوا ظَالِمِينَ
Kada/bi ali firAAawna wallatheenamin qablihim kaththaboo bi-ayati
rabbihimfaahlaknahum bithunoobihim waaghraqna alafirAAawna wakullun kanoo
thalimeen
Hausa
Kamar al'adar mutãnen Fir'auna da waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata game da
ãyõyin Ubangijinsu, sai Muka halaka su, sabõda zunubansu, kuma Muka nutsar da
mutãnen Fir'auna. Kuma dukansu sun kasance ne mãsu zãlunci.
|
Ayah 8:55 الأية
إِنَّ شَرَّ الدَّوَابِّ عِندَ اللهِ الَّذِينَ كَفَرُوا فَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ
Inna sharra addawabbi AAindaAllahi allatheena kafaroo fahum la yu/minoon
Hausa
Lalle mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne waɗanda suka kãfirta, sa'an nan
bã zã su yi ĩmãni ba.
|
Ayah 8:56 الأية
الَّذِينَ عَاهَدتَّ مِنْهُمْ ثُمَّ يَنقُضُونَ عَهْدَهُمْ فِي كُلِّ مَرَّةٍ
وَهُمْ لَا يَتَّقُونَ
Allatheena AAahadta minhumthumma yanqudoona AAahdahum fee kulli marratin wahum
layattaqoon
Hausa
Waɗanda ka yi ƙullin alkawari da su, daga gare su, sa'an nan kuma sunã
warwarewar alkawarinsu a kõwane lõkaci kuma sũ, bã su yin taƙawa.
|
Ayah 8:57 الأية
فَإِمَّا تَثْقَفَنَّهُمْ فِي الْحَرْبِ فَشَرِّدْ بِهِم مَّنْ خَلْفَهُمْ
لَعَلَّهُمْ يَذَّكَّرُونَ
Fa-imma tathqafannahum fee alharbifasharrid bihim man khalfahum laAAallahum
yaththakkaroon
Hausa
To, in dai ka kãma su a cikin yãƙi, sai ka kõre waɗanda suke a bãyansu, game da
su, tsammãninsu, zã su dinga tunãwa.
|
Ayah 8:58 الأية
وَإِمَّا تَخَافَنَّ مِن قَوْمٍ خِيَانَةً فَانبِذْ إِلَيْهِمْ عَلَىٰ سَوَاءٍ ۚ
إِنَّ اللهَ لَا يُحِبُّ الْخَائِنِينَ
Wa-imma takhafanna min qawminkhiyanatan fanbith ilayhim AAalasawa-in inna Allaha
la yuhibbu alkha-ineen
Hausa
Kuma in ka ji tsõron wata yaudara daga wasu mutãne, to, ka jẽfar da alkawarin,
zuwa gare su, a kan daidaita: Lalle ne Allah, bã Ya son mayaudara.
|
Ayah 8:59 الأية
وَلَا يَحْسَبَنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا سَبَقُوا ۚ إِنَّهُمْ لَا يُعْجِزُونَ
Wala yahsabanna allatheenakafaroo sabaqoo innahum la yuAAjizoon
Hausa
Kuma waɗanda suka kãfirta kada su yi zaton sun tsẽre: Lalle ne sũ, bã zã su
gãgara ba.
|
Ayah 8:60 الأية
وَأَعِدُّوا لَهُم مَّا اسْتَطَعْتُم مِّن قُوَّةٍ وَمِن رِّبَاطِ الْخَيْلِ
تُرْهِبُونَ بِهِ عَدُوَّ اللهِ وَعَدُوَّكُمْ وَآخَرِينَ مِن دُونِهِمْ لَا
تَعْلَمُونَهُمُ اللهُ يَعْلَمُهُمْ ۚ وَمَا تُنفِقُوا مِن شَيْءٍ فِي سَبِيلِ
اللهِ يُوَفَّ إِلَيْكُمْ وَأَنتُمْ لَا تُظْلَمُونَ
WaaAAiddoo lahum ma istataAAtummin quwwatin wamin ribati alkhayli turhiboona
bihiAAaduwwa Allahi waAAaduwwakum waakhareena mindoonihim la taAAlamoonahumu
Allahu yaAAlamuhum wamatunfiqoo min shay-in fee sabeeli Allahi yuwaffa
ilaykumwaantum la tuthlamoon
Hausa
Kuma ku yi tattali, dõminsu, abin da kuka sãmi ĩkon yi na wani ƙarfi, kuma da
ajiye dawaki, kunã tsoratarwa, game da shi, ga maƙiyin Allah kuma maƙiyinku da
wasu, baicin su, ba ku san su ba, Allah ne Yake sanin su, kuma abin da kuka
ciyar daga wani abu a cikin hanyar Allah, zã a cika muku sakamakonsa, kuma kũ ba
a zãluntar ku.
|
Ayah 8:61 الأية
وَإِن جَنَحُوا لِلسَّلْمِ فَاجْنَحْ لَهَا وَتَوَكَّلْ عَلَى اللهِ ۚ إِنَّهُ
هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Wa-in janahoo lissalmi fajnahlaha watawakkal AAala Allahi innahu huwa
assameeAAualAAaleem
Hausa
Kuma idan sun karkata zuwa ga zaman lãfiya, to, ka karkata zuwa gare shi, kuma
ka dõgara ga Allah: Lalle ne Shĩ, Mai ji ne Masani.
|
Ayah 8:62 الأية
وَإِن يُرِيدُوا أَن يَخْدَعُوكَ فَإِنَّ حَسْبَكَ اللهُ ۚ هُوَ الَّذِي
أَيَّدَكَ بِنَصْرِهِ وَبِالْمُؤْمِنِينَ
Wa-in yureedoo an yakhdaAAooka fa-inna hasbakaAllahu huwa allathee ayyadaka
binasrihi wabilmu/mineen
Hausa
Kuma idan sun yi nufin su yaudare ka, to, lalle ma'ishinka Allah ne, Shĩ ne
wanda Ya ƙarfafa ka da taimakonSa, kuma da mũminai.
|
Ayah 8:63 الأية
وَأَلَّفَ بَيْنَ قُلُوبِهِمْ ۚ لَوْ أَنفَقْتَ مَا فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا مَّا
أَلَّفْتَ بَيْنَ قُلُوبِهِمْ وَلَٰكِنَّ اللهَ أَلَّفَ بَيْنَهُمْ ۚ إِنَّهُ
عَزِيزٌ حَكِيمٌ
Waallafa bayna quloobihim law anfaqta mafee al-ardi jameeAAan ma allafta bayna
quloobihimwalakinna Allaha allafa baynahum innahu AAazeezun hakeem
Hausa
Kuma Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu. Dã kã ciyar da abin da yake cikin
ƙasa, gabã ɗaya, dã ba ka sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu ba, kuma amma Allah
Yã sanya sõyayya a tsakãninsu. Lalle Shi ne Mabuwãyi, Mai hikima.
|
Ayah 8:64 الأية
يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ حَسْبُكَ اللهُ وَمَنِ اتَّبَعَكَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ
Ya ayyuha annabiyyu hasbukaAllahu wamani ittabaAAaka mina almu/mineen
Hausa
Ya kai Annabi! Ma'ishinka Allah ne, kai da wanda ya biye maka daga mũminai.
|
Ayah 8:65 الأية
يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ حَرِّضِ الْمُؤْمِنِينَ عَلَى الْقِتَالِ ۚ إِن يَكُن
مِّنكُمْ عِشْرُونَ صَابِرُونَ يَغْلِبُوا مِائَتَيْنِ ۚ وَإِن يَكُن مِّنكُم
مِّائَةٌ يَغْلِبُوا أَلْفًا مِّنَ الَّذِينَ كَفَرُوا بِأَنَّهُمْ قَوْمٌ لَّا
يَفْقَهُونَ
Ya ayyuha annabiyyu harridialmu/mineena AAala alqitali in yakun minkumAAishroona
sabiroona yaghliboo mi-atayni wa-in yakunminkum mi-atun yaghliboo alfan mina
allatheena kafaroobi-annahum qawmun la yafqahoon
Hausa
Ya kai Annabi! Ka kwaɗaitar da mũminai a kan yãƙi. Idan mutum ashirin mãsu
haƙuri sun kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan kuma idan ɗari suka kasance
daga gare ku, zã su rinjãyi dubu daga waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ, mutãne ne
bã su fahimta.
|
Ayah 8:66 الأية
الْآنَ خَفَّفَ اللهُ عَنكُمْ وَعَلِمَ أَنَّ فِيكُمْ ضَعْفًا ۚ فَإِن يَكُن
مِّنكُم مِّائَةٌ صَابِرَةٌ يَغْلِبُوا مِائَتَيْنِ ۚ وَإِن يَكُن مِّنكُمْ أَلْفٌ
يَغْلِبُوا أَلْفَيْنِ بِإِذْنِ اللهِ ۗ وَاللهُ مَعَ الصَّابِرِينَ
Al-ana khaffafa Allahu AAankumwaAAalima anna feekum daAAfan fa-in yakun minkum
mi-atun sabiratunyaghliboo mi-atayni wa-in yakun minkum alfun yaghliboo
alfaynibi-ithni Allahi wallahu maAAa assabireen
Hausa
A yanzu Allah Yã sauƙaƙe daga gare ku, kuma Yã sani cẽwa lalle ne akwai mãsu
rauni a cikinku. To, idan mutum ɗari, mãsu haƙuri, suka kasance daga gare ku, zã
su rinjãyi mẽtan, kuma idan dubu suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu
biyu, da iznin Allah. Kuma Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri.
|
Ayah 8:67 الأية
مَا كَانَ لِنَبِيٍّ أَن يَكُونَ لَهُ أَسْرَىٰ حَتَّىٰ يُثْخِنَ فِي الْأَرْضِ ۚ
تُرِيدُونَ عَرَضَ الدُّنْيَا وَاللهُ يُرِيدُ الْآخِرَةَ ۗ وَاللهُ عَزِيزٌ
حَكِيمٌ
Ma kana linabiyyin an yakoonalahu asra hatta yuthkhina fee al-arditureedoona
AAarada addunya wallahuyureedu al-akhirata wallahu AAazeezun hakeem
Hausa
Bã ya kasancewa ga wani annabi, kãmammu su kasance a gare shi sai (bãyan) yã
zubar da jinainai a cikin ƙasa. Kunã nufin sifar dũniya kuma Allah Yanãnufin
Lãhira. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.
|
Ayah 8:68 الأية
لَّوْلَا كِتَابٌ مِّنَ اللهِ سَبَقَ لَمَسَّكُمْ فِيمَا أَخَذْتُمْ عَذَابٌ
عَظِيمٌ
Lawla kitabun mina Allahisabaqa lamassakum feema akhathtum AAathabunAAatheem
Hausa
Bã dõmin wani Littãfi daga Allah ba, wanda ya gabãta , dã azãba mai girma daga
Allah tã shãfe ku a cikin abin da kuka kãma.
|
Ayah 8:69 الأية
فَكُلُوا مِمَّا غَنِمْتُمْ حَلَالًا طَيِّبًا ۚ وَاتَّقُوا اللهَ ۚ إِنَّ
اللهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Fakuloo mimma ghanimtum halalantayyiban wattaqoo Allaha inna Allahaghafoorun
raheem
Hausa
Sabõda haka, ku ci daga abin da kuka sãmu ganĩma, Yanã halal mai kyau. Kuma ku
bi Allah da taƙawa. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
|
Ayah 8:70 الأية
يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُل لِّمَن فِي أَيْدِيكُم مِّنَ الْأَسْرَىٰ إِن يَعْلَمِ
اللهُ فِي قُلُوبِكُمْ خَيْرًا يُؤْتِكُمْ خَيْرًا مِّمَّا أُخِذَ مِنكُمْ
وَيَغْفِرْ لَكُمْ ۗ وَاللهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Ya ayyuha annabiyyuqul liman fee aydeekum mina al-asra in yaAAlami Allahufee
quloobikum khayran yu/tikum khayran mimma okhithaminkum wayaghfir lakum wallahu
ghafoorun raheem
Hausa
Ya kai Annabi! Ka ce wa wanda yake a cikin hannãyenku daga kãmammu: "Idan Allah
Ya san akwai wani alhẽri a cikin zukãtanku, zai kawo muku mafi alhẽri daga abin
da aka karɓa daga gare ku, kuma Ya yi muku gãfara. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai
jin ƙai."
|
Ayah 8:71 الأية
وَإِن يُرِيدُوا خِيَانَتَكَ فَقَدْ خَانُوا اللهَ مِن قَبْلُ فَأَمْكَنَ
مِنْهُمْ ۗ وَاللهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Wa-in yureedoo khiyanataka faqad khanooAllaha min qablu faamkana minhum
wallahuAAaleemun hakeem
Hausa
Kuma idan sun yi nufin yaudararka, to, haƙĩƙa, sun yaudari Allahdaga gabãni sai
Ya bãyar da dãmã daga gare su: Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.
|
Ayah 8:72 الأية
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَهَاجَرُوا وَجَاهَدُوا بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ
فِي سَبِيلِ اللهِ وَالَّذِينَ آوَوا وَّنَصَرُوا أُولَٰئِكَ بَعْضُهُمْ
أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ ۚ وَالَّذِينَ آمَنُوا وَلَمْ يُهَاجِرُوا مَا لَكُم مِّن
وَلَايَتِهِم مِّن شَيْءٍ حَتَّىٰ يُهَاجِرُوا ۚ وَإِنِ اسْتَنصَرُوكُمْ فِي
الدِّينِ فَعَلَيْكُمُ النَّصْرُ إِلَّا عَلَىٰ قَوْمٍ بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُم
مِّيثَاقٌ ۗ وَاللهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ
Inna allatheena amanoo wahajaroowajahadoo bi-amwalihim waanfusihim fee sabeeli
Allahiwallatheena awaw wanasaroo ola-ikabaAAduhum awliyao baAAdin
wallatheenaamanoo walam yuhajiroo ma lakum min walayatihimmin shay-in hatta
yuhajiroo wa-ini istansarookumfee addeeni faAAalaykumu annasru illaAAala qawmin
baynakum wabaynahum meethaqun wallahubima taAAmaloona baseer
Hausa
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi da
dũkiyõyinsuda rãyukansu, a cikin hanyar Allah, da waɗanda suka bãyar da masauki,
kuma suka yi taimako. Waɗancan, sãshensu waliyyai ne ga sãshe. Kuma waɗanda suka
yi ĩmãni kuma ba su yi hijira ba, bã ku da wani abu daga waliccinsu, sai sun yi
hijira. Kuma idan suka nẽme ku taimako a cikin addini, to taimako yã wajaba a
kanku, fãce a kan mutãne waɗanda a tsakãninku da tsakãninsu akwai wani alkwari.
Kuma Allah ne, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani.
|
Ayah 8:73 الأية
وَالَّذِينَ كَفَرُوا بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ ۚ إِلَّا تَفْعَلُوهُ تَكُن
فِتْنَةٌ فِي الْأَرْضِ وَفَسَادٌ كَبِيرٌ
Wallatheena kafaroo baAAduhumawliyao baAAdin illa tafAAaloohu takunfitnatun fee
al-ardi wafasadun kabeer
Hausa
Kuma waɗanda suka kãfirta sãshensu ne waliyyan sãshe, idan ba ku aikata shi ba,
wata fitina zã ta kasance a cikin ƙasa, da fasãdi babba.
|
Ayah 8:74 الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَهَاجَرُوا وَجَاهَدُوا فِي سَبِيلِ اللهِ وَالَّذِينَ
آوَوا وَّنَصَرُوا أُولَٰئِكَ هُمُ الْمُؤْمِنُونَ حَقًّا ۚ لَّهُم مَّغْفِرَةٌ
وَرِزْقٌ كَرِيمٌ
Wallatheena amanoo wahajaroowajahadoo fee sabeeli Allahi wallatheenaawaw
wanasaroo ola-ika humu almu/minoona haqqanlahum maghfiratun warizqun kareem
Hausa
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka yi hijira, kuma suka yi Jihãdi, a cikin
hanyar Allah, kuma da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi tamiako,
waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya, sunãda gãfara da wani abinci na karimci.
|
Ayah 8:75 الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا مِن بَعْدُ وَهَاجَرُوا وَجَاهَدُوا مَعَكُمْ فَأُولَٰئِكَ
مِنكُمْ ۚ وَأُولُو الْأَرْحَامِ بَعْضُهُمْ أَوْلَىٰ بِبَعْضٍ فِي كِتَابِ اللهِ
ۗ إِنَّ اللهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ
Wallatheena amanoo minbaAAdu wahajaroo wajahadoo maAAakum faola-ikaminkum waoloo
al-arhami baAAduhum awlabibaAAdin fee kitabi Allahi inna Allahabikulli shay-in
AAaleem
Hausa
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni daga bãya, kuma suka yi hijira kuma suka yi jihãdi
tãre da ku, to, waɗannan daga gare ku suke. Kuma ma'abũta zumunta, sãshensu ne
waliyyan sãshe a cikin Littãfin Allah. Lalle Allah ne ga dukkan kõme Masani.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|