Kuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi dõmin ya ɓatar da mutãne
daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan
sunã da wata azãba mai wulãkantãwa.
Kuma idan an karanta ãyõyinMu a gare shi, sai ya jũya bãya, yanã mai girman kai,
kamar dai bai saurãre su ba kamar dai akwai wanĩ danni a kan kunnuwansa! To, ka
yi masa bushãra da azãba mai raɗaɗi.
(Allah) Ya halitta sammai, bã da ginshiƙi wanda kuke gani ba, kuma Yã jẽfa
duwatsu mãsu kafuwa a cikin ƙasã, dõmin kada ta karkata da ku kuma Ya wãtsa daga
kowanc irin dabba a cikinta, kuma Mun saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka
tsirar a cikinta, daga kõwane nau'i biyu (nami; i da mace) mai ban sha'awa.
Kuma lalle haƙĩƙa Mun bai wa Luƙmãn hikima. (Muka ce masa) Ka gõde wa Allah,
kuma wanda ya gõde, to yanã gõdẽwa ne dõmin kansa kawai kuma wanda ya kãfirta,
to, lalle, Allah Mawadãci ne, Gõdadde.
Kuma a lõkacin da Luƙmãn ya ce wa ɗansa, alhãli kuwa yanã yi masa wa'azi, "Yã
ƙaramin ɗãna! Kada ka yi shirki game da Allah. Lalle shirki wani zãlunci ne mai
girma."
Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu; uwarsa tã ɗauke shi a
cikin rauni a kan wani rauni, kuma yãyensa a cikin shekaru biyu (Muka ce masa)
"Ka gõde Mini da kuma mahaifanka biyu. Makõma zuwa gare Ni kawai take."
"Kuma idan mahaifanka suka tsananta maka ga ka yi shirki game da Ni, ga abin da
bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'a. Kuma ka abũce su a cikin
dũniya gwargwadon sharĩ'a, kuma ka bi hanyar wanda ya mayar da al'amari zuwa
gare Ni, sa'an nan zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbãri game da
abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
"Yã ƙaramin ɗãna! Lalle ita idan gwargwadon ƙwãyar kõmayya ce ta kasance, to, ta
kasance a cikin wani falalen dũtse, kõ a cikin sammai, kõ a cikin ƙasã, Allah
zai kãwo ta Lalle Allah Mai tausasãwa ne, Masani."
"Yã ƙaramin ɗãna! Ka tsai da salla, kuma ka yi umurni da abin da aka sani, kuma
ka yi hani daga abin da ba a sani ba, kuma ka yi haƙuri a kan abin da ya sãme
ka. Lalle, wancan yanã daga muhimman al'amura."
"Kada ka karkatar da kundukukinka ga mutãne, kada ka yi tafiya a cikin ƙasã kanã
mai nũna fãɗin rai. Lalle, Allah bã Ya son dukan mai tãƙama, mai alfahari."
Ashe, ba ku gani ba, cẽwa Allah Yã hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin
da ke a cikin ƙasã, kuma Ya zuba ni'imõminsa a kanku, bayyanannu da ɓõyayyu?
Kuma akwai daga mutãne wanda ke yin jidãli ga al'amarin Allah, bã da wani ilmi
ba, kuma bã da wata shiriya ba, kumã ba da wani littãfi mai haskakãwa ba.
Kuma idan aka ce musu, "Ku bi abin da Allah ya saukar," sai su ce: "Ã'a, munã
bin abin da muka sãmi ubanninmu a kansa." shin kõ dã Shaiɗan nã kiran su ne zuwa
ga azãbar sa'ir,
kuma wanda ya mĩka fuskarsa zuwa ga Allah, alhãli kuma yanã mai kyautatãwa, to,
lalle ya yi riƙo ga igiya amintacciya. Kuma zuwa ga Allah ãƙibar al'amura take.
Kuma wanda ya kãfirta, to, kada kãfircinsa ya baƙanta maka rai, zuwa gare Mu
makõmarsu take, sa'an nan Mu bã su lãbari game da abin da suka aikata. Lalle
Allah, Masani ne ga abin da ke a cikin ƙirãza.
Kuma lalle, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halĩtta sammai da kasa?" Lalle zã su
ce: "Allah ne." Ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah" Ã'a, mafi yawansu ba su sani
ba.
Kuma dã dai abin da ke a cikin ƙasa duka, na itãce, ya zama alƙalumma, kuma tẽku
tanã yi masa tawada, a bayansa da waɗansu tẽkuna bakwai kalmõmin Allah ba zã su
ƙãre ba. Lalle, Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
Ashe, ba ku ga, lalle, Allah Yanã shigar da dare a cikin rãna ba, kuma Yanã
shigar da rãna a cikin dare kuma Yã hõre rãnã da watã kõwane yanã gudãna zuwa a
ajali ambatacce kuma lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa?
Ashe, ba ka ga lalle jirgin ruwa nã gudãna ba a cikin tẽku da ni'imar Allah
dõmin Ya nũna muku daga ãyõyinSa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai
haƙuri, mai gõdiya.
Kuma idan tãguwar ruwa, kamar duwatsu, ta rufe su, sai su kira Allah sunã
tsarkakẽwar addini a gare shi. To, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudu,
sai daga cikinsu akwai mai taƙaitãwa kuma bãbu mai musun ãyõyinMu fãce dukkan
mayaudari mai yawan kãfirci.
Ya ku mutãne! Ku bauta wa Ubangijinku da taƙawa, kuma ku ji tsõron wani yini,
rãnar da wani mahaifi bã ya sãka wa abin haifuwarsa da kõme kuma wani abin
haifuwa bã ya sãka wa mahaifinsa da kõme. Lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Sabõda
haka, kada wata rãyuwa ta kusa ta rũde ku, kuma kada marũɗin nan ya rũɗẽ ku game
da Allah.
Lalle, Allah a wurinsa kawai sanin sa'a yake, kuma Yanã saukar da girgije, kuma
Yanã sanin abin da yake a cikin mahaiffannai kuma wani rai bai san abin da yake
aikatãwa a gõbe ba, kuma wani rai bai san a wace ƙasã yake mutuwa ba. Lalle
Allah Masani ne Mai ƙididdidigẽwa.