A. L̃. R. Littãfi ne mun saukar da shi zuwa gare ka dõmin ka fitar da mutãne
daga duhunhuna zuwa ga haske, da iznin Ubangijinsu, zuwa ga tafarkin
Mabuwãyi,Abin gõdẽwa.
Waɗanda suka fi son rãyuwar dũniya fiye da ta Lãhira, kuma sunã kangẽwa daga
hanyar Allah,kuma sunã nẽman ta karkace. Waɗancan na a cikin ɓata mai nĩsa.
Kuma ba Mu aika wani Manzo ba fãce da harshen mutãnensa dõmin ya bayyanã musu.
Sa'an nan Allah Ya ɓatar da wanda Yake so kuma Ya shiryar da wanda Yake so,Kuma
shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Mũsã game, da ãyõin Mu cẽwa, "Ka fitar da
mutãnenkadaga duhu zuwa ga haske. Kuma ka tunar musu da kwãnukan (masĩfun)
Allah." Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi dõmin dukan mai yawan haƙuri, mai
gõdiya.
Kuma a lõkacin da Mũsã yace wa mutãnensa, "Ku tuna ni'imar Allah a kanku a
lõkacin da Ya tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, sunã yi muku mummunar azãba,
kuma sunã yanyanka ɗiyanku, kuma sunã rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan
akwai jarrabãwa mai girmã daga Ubangijinku."
Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, "Lalle ne idan kun gõde, haƙĩƙa, Inã
ƙãramuku, kuma lalle ne idan kun kãfirta haƙĩƙa azãbãta, tabbas, mai tsanani
ce."
Shin lãbãrin waɗanda suke a gabãninku, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdawa bai
zomuku ba? Kuma da waɗanda suke daga bãyansu bãbu wanda yake sanin su fãce
Allah? Manzanninsu sun jẽ musu da hujjõji mabayyana, sai suka mayar da
hannayensu a cikin bãkunansu, kuma suka ce: "Lalle ne mũ, mun kãfirta da abinda
aka aiko ku da shi. Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa munã a cikin shakkada abin do kuke
kiran mu zuwa gare shi, mai sanya kõkanto."
Manzanninsu suka ce "Ashe, akwai shakka a cikin (sha'anin) Allah, Mai ƙãga
halittar sammai da ƙasa Yanã kiran ku dõmin Ya gãfarta muku zunubanku, kuma Ya
jinkirtã muku zuwa ga ajali ambatacce?" Suka ce: "Ba ku zama ba fãce mutãne
misãlinmu kuma nufinku ku kange mu daga abin da iyãyenmu suka kasance sunã
bautãwa sai ku zo mana da dalĩli mabayyani."
Manzanninsu suka ce musu, "Bã mu zama ba fãce mutãne misã, linku, kuma amma
Allah Yanã yin falala a kan wanda Yake so daga bãyinsa, kuma bã ya kasancẽwa a
gare mu, mu zo muku da wani dalĩli fãce da iznin Allah. Kuma ga Allah sai
mũminai su dõgara.
"Kuma mẽne ne a gare mu, bã zã mu dõgara ga Allah ba, alhãli kuwa haƙĩƙa Yã
shiryar da mu ga hanyõyinmu? Kuma lalle ne munã yin haƙuri a kan abin da kuka
cũtar da mu, kuma ga Allah sai mãsu dõgaro su dõgara."
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa Manzanninsu, "Lalle ne munã fitar da ku
daga ƙasarmu, kõ kuwa haƙĩƙa, kunã kõmowã acikin addininmu." Sai Ubangijinsu Ya
yi wahayi zuwa gare su, "Lalle ne, Munã halakar da azzãlumai."
Yanã kwankwaɗarsa, kuma bã ya jin sauƙin haɗiyarsa, kuma mutuwa ta jẽ masa daga
kõwane wuri kuma bai zama mai mutuwa ba, kuma daga bãyansa akwai azãba mai
kauri.
Misãlin waɗanda suka kãfirta da Ubangijinsu, ayyukansu sun yi kama da tõka wadda
iska ta yi tsananin bugãwa da ita a cikin yini mai gũguwa. Ba su iya amfãni daga
abin da suka yi tsirfa a kan kõme.Wancan ita ce ɓata mai nĩsa.
Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle ne Allah Yã halicci sammai bakwai da ƙasa da
mallakarSa. Idan Yã so zai tafiyar da ku, kuma Ya zo da wata halitta sãbuwa.
Kuma suka bayyana ga Allah gabã daya, sai mãsu rauni suka ce wa waɗanda suka
kangara, "Lalle ne mũ, mun kasance mãsu bi a gare ku, to, shin, kũ mãsu kãrewa
ga barinmu ne daga azãbar Allah daga wani abu?" Suka ce: "Dã Allah Ya shiryar da
mu, dã mun shiryar da ku, daidai ne a kanmu, mun yi rãki ko mun yi haƙuri ba mu
da wata mafaka."
Kuma Shaiɗan ya ce a lõkacin da aka ƙãre al'amarin, "Lalle ne Allah Ya yi muku
wa'adi, wa'adin gaskiyã, kuma na yi muku wa'adi, sa'an nan na sãɓã muku. Kuma
bãbu wani dalĩli a gare ni a kanku fãce na kirã ku, sa'an nan kun karɓã mini.
Sabõda haka kada ku zarge ni, kuma ku zargi kanku. Ban zama mai amfaninku ba,
kuma ba ku zama mãsu amfãnĩna ba. Lalle na barranta da abin da kuka haɗã ni da
shi gabanin wannan(matsayi). Lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi."
Kuma aka shigar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, a
gidãjen Aljanna, kõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwamã a cikinsu da
iznin Ubangijinsu, gaisuwarsu a cikinta "Salãm",(wãtau Aminci).
Shin, ba ka ganĩ ba, yadda Allah Ya buga wani mĩsali, kalma mai kyau kamar
itãciya ce mai kyau, asalinta yanã tabbatacce, kuma rẽshenta yanã cikin sama?
Allah Yanã tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni da magana tabbatacciya a cikin
rãyuwar dũniya, da cikin Lãhira, Kuma Allah Yanã ɓatar da azzãlumai, kuma Allah
Yanã aikata abin da Yake so.
Ka ce wa bãyĩNa waɗanda suka yi ĩmãni su tsayar da salla kuma su ciyar daga abin
da Muka azurtã su,a asirce da bayyane, daga gabãnin wani wuni ya zo, bãbu ciniki
a ciki, kuma bãbu abõtaka.
Allah ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an
nan Ya fitar game da shi, daga 'ya'yan itãce arziki dõminku kuma Ya hõrẽ jirgin
ruwa dõmin ya yi gudu a cikin tẽku da umurninSa, kuma Ya hõrẽ muku kõguna.
Kuma Ya bã ku dukkan abin da kuka rõƙe Shi kuma idan kun ƙidaya, ni'imar Allah
bã zã ku lissafe ta ba. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan zãlunci ne, mai yawan
kãfirci.
"Yã Ubangijina! Lalle ne sũ, sun ɓatar da mãsu yawa daga mutãne sa'an nan wanda
ya bĩ ni, to,lalle shi, yanã daga gare ni, kuma wanda ya sãɓa mini, to, lalle ne
Kai Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
"Yã Ubangijinmu! Lalle ne ni, na zaunar da zuriyata ga rãfi wanda ba ma'abũcin
shũka ba, a wurin ¦ãkinka mai alfarma. Yã Ubangijinmu! Dõmin su tsayar da salla.
Sai Ka sanya zukãta daga mutãne sunã gaggãwar bẽgenzuwa gare su, kuma ka azurtã
su daga 'ya'yan itãce, mai yiwuwã ne sunã gõdẽwã."
"Yã Ubangijinmu! Lalle ne Kai Kanã sanin abin da muke ɓõyẽwa, da abin da muke
bayyanãwa. Kuma bãbu abin da yake ɓõyẽwa ga A1lah, daga wani abu a cikin ƙasa,
kuma bãbu a cikin sama."
"Kuma kada ka yi zaton Allah Mai shagalã ne daga abin da azzalumai suke
aikatãwã. Abin sani kawai, Yanã jinkirta musu ne zuwa ga wani wuni, wanda
idãnuwa suke fita turu- turu a cikinsa."
Kuma ka yi gargaɗi ga mutãne ga rãnar da azãba take jẽ musu, sai waɗanda suka yi
zãlunci su ce: "Yã Ubangijinmu! Ka yi mana jinkiri zuwa ga wani ajali makusanci,
mu karɓa wa kiranKa, kuma mu bi Manzanni."(Allah Ya ce musu) "Ashe, ba ku
kasance kun yi rantsuwã ba daga gabãni, cẽwa bã ku da wata gushẽwa?
Kuma lalle sun yi mãkirci irin makircinSu kuma a wurin Allah makircinsu, yake,
kuma lalle ne makircinsu yã kasance, haƙĩƙa, duwãtsu sunã gushẽwã sabõda shi.
Wannan iyarwa ce ga mutãne, kuma dõmin a yi musu gargaɗi da shi, kuma dõmin su
sani cẽwa, abin sani kawai, shĩ ne abin bautawa guda. Kuma dõmin masu hankali su
riƙa tunãwa.