First Ayah 1 الأية الأوليبِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الر ۚ تِلْكَ آيَاتُ الْكِتَابِ وَقُرْآنٍ مُّبِينٍ
Hausa
A. L̃. R. Waɗancan ăyoyin littăfi ne da abin karantăwa mai bayyanăwa.
|
Ayah 15:2 الأية
رُّبَمَا يَوَدُّ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوْ كَانُوا مُسْلِمِينَ
Hausa
Da yawa waɗanda suka kăfirta suke gũrin dă dai sun kasance Musulmi.
|
Ayah 15:3 الأية
ذَرْهُمْ يَأْكُلُوا وَيَتَمَتَّعُوا وَيُلْهِهِمُ الْأَمَلُ ۖ فَسَوْفَ
يَعْلَمُونَ
Hausa
Ka bar su su ci kuma su ji dădi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da
sannu ză su sani.
|
Ayah 15:4 الأية
وَمَا أَهْلَكْنَا مِن قَرْيَةٍ إِلَّا وَلَهَا كِتَابٌ مَّعْلُومٌ
Hausa
Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba făce tană da littafi sananne.
|
Ayah 15:5 الأية
مَّا تَسْبِقُ مِنْ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسْتَأْخِرُونَ
Hausa
Wata al'umma bă ta gabătar ajalinta, kuma bă ză su jinkirta ba.
|
Ayah 15:6 الأية
وَقَالُوا يَا أَيُّهَا الَّذِي نُزِّلَ عَلَيْهِ الذِّكْرُ إِنَّكَ لَمَجْنُونٌ
Hausa
Suka ce: "Yă kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ăni) a kansa! Lalle ne kai,
haƙĩƙa, mahaukaci ne."
|
Ayah 15:7 الأية
لَّوْ مَا تَأْتِينَا بِالْمَلَائِكَةِ إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ
Hausa
"Dőmin me bă ză ka zo mana da mală'ĩku ba idan ka kasance daga măsu gaskiya?"
|
Ayah 15:8 الأية
مَا نُنَزِّلُ الْمَلَائِكَةَ إِلَّا بِالْحَقِّ وَمَا كَانُوا إِذًا مُّنظَرِينَ
Hausa
Bă Mu sassaukar da mală'iku făce da gaskiya, bă ză su kasance, a wannan lőkacin,
waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.
|
Ayah 15:9 الأية
إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا الذِّكْرَ وَإِنَّا لَهُ لَحَافِظُونَ
Hausa
Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ăni), kuma lal1e Mũ, haƙĩƙa, Măsu
kiyayẽwane gare shi.
|
Ayah 15:10 الأية
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ فِي شِيَعِ الْأَوَّلِينَ
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyőyin farko, gabăninka.
|
Ayah 15:11 الأية
وَمَا يَأْتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ
Hausa
Kuma wani Manzo bă ya zuwa gare su făce sun kasance sună măsu, izgili a gare
shi.
|
Ayah 15:12 الأية
كَذَٰلِكَ نَسْلُكُهُ فِي قُلُوبِ الْمُجْرِمِينَ
Hausa
Kamar wancan ne Muke shigar da shi a cikin zukătan măsu laifi.
|
Ayah 15:13 الأية
لَا يُؤْمِنُونَ بِهِ ۖ وَقَدْ خَلَتْ سُنَّةُ الْأَوَّلِينَ
Hausa
Bă su yin ĩmăni da shi, kuma haƙĩƙa, hanyar mutănen farko ta shige.
|
Ayah 15:14 الأية
وَلَوْ فَتَحْنَا عَلَيْهِم بَابًا مِّنَ السَّمَاءِ فَظَلُّوا فِيهِ يَعْرُجُونَ
Hausa
Kuma dă Mun bũɗe wata ƙőfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sună tăkăwa.
|
Ayah 15:15 الأية
لَقَالُوا إِنَّمَا سُكِّرَتْ أَبْصَارُنَا بَلْ نَحْنُ قَوْمٌ مَّسْحُورُونَ
Hausa
Lalle ne dă sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idănuwanmu ne. Ă'a, mũ mutăne ne
waɗanda aka sihirce."
|
Ayah 15:16 الأية
وَلَقَدْ جَعَلْنَا فِي السَّمَاءِ بُرُوجًا وَزَيَّنَّاهَا لِلنَّاظِرِينَ
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawăta
ta ga masu kallo.
|
Ayah 15:17 الأية
وَحَفِظْنَاهَا مِن كُلِّ شَيْطَانٍ رَّجِيمٍ
Hausa
Kuma Muka kiyăye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa.
|
Ayah 15:18 الأية
إِلَّا مَنِ اسْتَرَقَ السَّمْعَ فَأَتْبَعَهُ شِهَابٌ مُّبِينٌ
Hausa
Făce wanda ya săci saurăre sai wutar yũlă bayyananniya ta bĩ shi.
|
Ayah 15:19 الأية
وَالْأَرْضَ مَدَدْنَاهَا وَأَلْقَيْنَا فِيهَا رَوَاسِيَ وَأَنبَتْنَا فِيهَا مِن
كُلِّ شَيْءٍ مَّوْزُونٍ
Hausa
Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwătsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar
a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunăwa da sikẽli.
|
Ayah 15:20 الأية
وَجَعَلْنَا لَكُمْ فِيهَا مَعَايِشَ وَمَن لَّسْتُمْ لَهُ بِرَازِقِينَ
Hausa
Kuma Muka sanyă muku, a cikinta, abũbuwan răyuwă da wanda ba ku zamă măsu
ciyarwa gare shi ba.
|
Ayah 15:21 الأية
وَإِن مِّن شَيْءٍ إِلَّا عِندَنَا خَزَائِنُهُ وَمَا نُنَزِّلُهُ إِلَّا بِقَدَرٍ
مَّعْلُومٍ
Hausa
Kuma băbu wani abu făce a wurinMu, akwai taskőkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba
făce kan gwargwado sananne.
|
Ayah 15:22 الأية
وَأَرْسَلْنَا الرِّيَاحَ لَوَاقِحَ فَأَنزَلْنَا مِنَ السَّمَاءِ مَاءً
فَأَسْقَيْنَاكُمُوهُ وَمَا أَنتُمْ لَهُ بِخَازِنِينَ
Hausa
Kuma Muka aika iskőki măsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga
sama, sa'an nan Muka shăyar da ku shi, kuma ba ku zama măsu taskacẽwa a gare shi
ba.
|
Ayah 15:23 الأية
وَإِنَّا لَنَحْنُ نُحْيِي وَنُمِيتُ وَنَحْنُ الْوَارِثُونَ
Hausa
Kuma lalle ne Mu Muke răyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada.
|
Ayah 15:24 الأية
وَلَقَدْ عَلِمْنَا الْمُسْتَقْدِمِينَ مِنكُمْ وَلَقَدْ عَلِمْنَا
الْمُسْتَأْخِرِينَ
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san măsu gabăta daga cikinku, kuma Mun san măsu
jinkiri.
|
Ayah 15:25 الأية
وَإِنَّ رَبَّكَ هُوَ يَحْشُرُهُمْ ۚ إِنَّهُ حَكِيمٌ عَلِيمٌ
Hausa
Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tăra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani.
|
Ayah 15:26 الأية
وَلَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنسَانَ مِن صَلْصَالٍ مِّنْ حَمَإٍ مَّسْنُونٍ
Hausa
Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lăka, daga baƙin yumɓu wanda
ya canja.
|
Ayah 15:27 الأية
وَالْجَانَّ خَلَقْنَاهُ مِن قَبْلُ مِن نَّارِ السَّمُومِ
Hausa
Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabăni, daga wutar iskar zafi.
|
Ayah 15:28 الأية
وَإِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلَائِكَةِ إِنِّي خَالِقٌ بَشَرًا مِّن صَلْصَالٍ مِّنْ
حَمَإٍ مَّسْنُونٍ
Hausa
Kuma a lőkacin da Ubangijinka ya ce wa mală'iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani
jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja."
|
Ayah 15:29 الأية
فَإِذَا سَوَّيْتُهُ وَنَفَخْتُ فِيهِ مِن رُّوحِي فَقَعُوا لَهُ سَاجِدِينَ
Hausa
"To idan Na daidaită shi kuma Na hũra daga RũhĩNa a cikinsa, to, ku făɗi a gare
shi, kună măsu yin sujada."
|
Ayah 15:30 الأية
فَسَجَدَ الْمَلَائِكَةُ كُلُّهُمْ أَجْمَعُونَ
Hausa
Sai mală'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya.
|
Ayah 15:31 الأية
إِلَّا إِبْلِيسَ أَبَىٰ أَن يَكُونَ مَعَ السَّاجِدِينَ
Hausa
Făce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga măsu yin sujadar.
|
Ayah 15:32 الأية
قَالَ يَا إِبْلِيسُ مَا لَكَ أَلَّا تَكُونَ مَعَ السَّاجِدِينَ
Hausa
Ya ce: "Yă Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tăre da măsu yin sujuda ba?"
|
Ayah 15:33 الأية
قَالَ لَمْ أَكُن لِّأَسْجُدَ لِبَشَرٍ خَلَقْتَهُ مِن صَلْصَالٍ مِّنْ حَمَإٍ
مَّسْنُونٍ
Hausa
Ya ce: "Ban kasance ină yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga
bũsasshen yumɓun lăka wadda ta canja."
|
Ayah 15:34 الأية
قَالَ فَاخْرُجْ مِنْهَا فَإِنَّكَ رَجِيمٌ
Hausa
Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dőmin lalle kai abin jĩfa ne."
|
Ayah 15:35 الأية
وَإِنَّ عَلَيْكَ اللَّعْنَةَ إِلَىٰ يَوْمِ الدِّينِ
Hausa
"Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rănar sakamako."
|
Ayah 15:36 الأية
قَالَ رَبِّ فَأَنظِرْنِي إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ
Hausa
Ya ce: "Yă Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rănar da ake tăshin su."
|
Ayah 15:37 الأية
قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ الْمُنظَرِينَ
Hausa
Ya ce: "To, lalle ne kană daga waɗanda ake yi wa jinkiri."
|
Ayah 15:38 الأية
إِلَىٰ يَوْمِ الْوَقْتِ الْمَعْلُومِ
Hausa
"Zuwa ga Yinin Lőkacin nan sananne."
|
Ayah 15:39 الأية
قَالَ رَبِّ بِمَا أَغْوَيْتَنِي لَأُزَيِّنَنَّ لَهُمْ فِي الْأَرْضِ
وَلَأُغْوِيَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ
Hausa
Ya ce: "Yă Ubangijina! Ină rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa ină
ƙawăta musu (răyuwa) a cikin ƙasă kuma haƙĩƙa ină ɓatar da su gabă ɗaya."
|
Ayah 15:40 الأية
إِلَّا عِبَادَكَ مِنْهُمُ الْمُخْلَصِينَ
Hausa
"Făce băyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake."
|
Ayah 15:41 الأية
قَالَ هَٰذَا صِرَاطٌ عَلَيَّ مُسْتَقِيمٌ
Hausa
Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici."
|
Ayah 15:42 الأية
إِنَّ عِبَادِي لَيْسَ لَكَ عَلَيْهِمْ سُلْطَانٌ إِلَّا مَنِ اتَّبَعَكَ مِنَ
الْغَاوِينَ
Hausa
"Lalle ne băyĩNa, bă ka da ĩkő a kansu, făce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."
|
Ayah 15:43 الأية
وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمَوْعِدُهُمْ أَجْمَعِينَ
Hausa
Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'a1kawartarsu gabă ɗaya.
|
Ayah 15:44 الأية
لَهَا سَبْعَةُ أَبْوَابٍ لِّكُلِّ بَابٍ مِّنْهُمْ جُزْءٌ مَّقْسُومٌ
Hausa
Tană da ƙőfőfi bakwai, ga kőwace ƙőfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe.
|
Ayah 15:45 الأية
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ
Hausa
Lalle măsu taƙawa sună a cikin gidăjen Aljanna mai idandunan ruwa.
|
Ayah 15:46 الأية
ادْخُلُوهَا بِسَلَامٍ آمِنِينَ
Hausa
"Ku shigẽ ta da aminci, kună amintattu."
|
Ayah 15:47 الأية
وَنَزَعْنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنْ غِلٍّ إِخْوَانًا عَلَىٰ سُرُرٍ
مُّتَقَابِلِينَ
Hausa
Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukătansu na daga ƙullin zũci, suka zama
'yan'uwa a kan gadăje, sună măsu fuskantar jună.
|
Ayah 15:48 الأية
لَا يَمَسُّهُمْ فِيهَا نَصَبٌ وَمَا هُم مِّنْهَا بِمُخْرَجِينَ
Hausa
Wata wahala bă ză ta shăfe su bă a cikinta kuma ba su zama măsu fita daga,
cikinta ba.
|
Ayah 15:49 الأية
نَبِّئْ عِبَادِي أَنِّي أَنَا الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
Hausa
Ka bai wa băyiNa lăbari cẽwa lalle ne Ni, Mai găfarane, Mai jin ƙai.
|
Ayah 15:50 الأية
وَأَنَّ عَذَابِي هُوَ الْعَذَابُ الْأَلِيمُ
Hausa
Kuma azăbăTa ita ce azăba mai raɗaɗi.
|
Ayah 15:51 الأية
وَنَبِّئْهُمْ عَن ضَيْفِ إِبْرَاهِيمَ
Hausa
Kuma ka bă su lăbărin băƙin Ibrăhĩm.
|
Ayah 15:52 الأية
إِذْ دَخَلُوا عَلَيْهِ فَقَالُوا سَلَامًا قَالَ إِنَّا مِنكُمْ وَجِلُونَ
Hausa
A lőkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga
gare ku, măsu firgita ne."
|
Ayah 15:53 الأية
قَالُوا لَا تَوْجَلْ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَامٍ عَلِيمٍ
Hausa
Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, mună yi makabushăra game da wani yăro
masani."
|
Ayah 15:54 الأية
قَالَ أَبَشَّرْتُمُونِي عَلَىٰ أَن مَّسَّنِيَ الْكِبَرُ فَبِمَ تُبَشِّرُونَ
Hausa
Ya ce: "Shin kun bă ni bushăra ne a kan tsũfa yă shăfe ni? To, da me kuke bă ni
bushara?"
|
Ayah 15:55 الأية
قَالُوا بَشَّرْنَاكَ بِالْحَقِّ فَلَا تَكُن مِّنَ الْقَانِطِينَ
Hausa
Suka ce: "Mună yi maka bushăra da gaskiya ne, sabőda haka, kada da kasance daga
măsu yanke tsammăni."
|
Ayah 15:56 الأية
قَالَ وَمَن يَقْنَطُ مِن رَّحْمَةِ رَبِّهِ إِلَّا الضَّالُّونَ
Hausa
Ya ce: "Kuma wăne ne yake yanke tsammăni daga rahamar Ubangijinsa, făce
ɓatattu?"
|
Ayah 15:57 الأية
قَالَ فَمَا خَطْبُكُمْ أَيُّهَا الْمُرْسَلُونَ
Hausa
Ya ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yă kũ manzanni!"
|
Ayah 15:58 الأية
قَالُوا إِنَّا أُرْسِلْنَا إِلَىٰ قَوْمٍ مُّجْرِمِينَ
Hausa
Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutăne măsu laifi."
|
Ayah 15:59 الأية
إِلَّا آلَ لُوطٍ إِنَّا لَمُنَجُّوهُمْ أَجْمَعِينَ
Hausa
"Făce mutănen Lũɗu, lalle ne mũ,haƙĩƙa, măsu tsĩrar dasu ne gabă ɗaya."
|
Ayah 15:60 الأية
إِلَّا امْرَأَتَهُ قَدَّرْنَا ۙ إِنَّهَا لَمِنَ الْغَابِرِينَ
Hausa
"Făce mătarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tană daga măsu halaka."
|
Ayah 15:61 الأية
فَلَمَّا جَاءَ آلَ لُوطٍ الْمُرْسَلُونَ
Hausa
To, a lőkacin da mazannin suka jẽ wa mutănen Lũɗu,
|
Ayah 15:62 الأية
قَالَ إِنَّكُمْ قَوْمٌ مُّنكَرُونَ
Hausa
Ya ce: "Lalle ne ku mutăne ne waɗanda ba a sani ba."
|
Ayah 15:63 الأية
قَالُوا بَلْ جِئْنَاكَ بِمَا كَانُوا فِيهِ يَمْتَرُونَ
Hausa
Suka ce: "Ă'a, mun zo maka sabőda abin da suka kasance sună shakka a cikinsa."
|
Ayah 15:64 الأية
وَأَتَيْنَاكَ بِالْحَقِّ وَإِنَّا لَصَادِقُونَ
Hausa
"Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, măsu gaskiya ne."
|
Ayah 15:65 الأية
فَأَسْرِ بِأَهْلِكَ بِقِطْعٍ مِّنَ اللَّيْلِ وَاتَّبِعْ أَدْبَارَهُمْ وَلَا
يَلْتَفِتْ مِنكُمْ أَحَدٌ وَامْضُوا حَيْثُ تُؤْمَرُونَ
Hausa
"Sai ka yi tafiya da iyălinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi băyansu, kuma
kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku."
|
Ayah 15:66 الأية
وَقَضَيْنَا إِلَيْهِ ذَٰلِكَ الْأَمْرَ أَنَّ دَابِرَ هَٰؤُلَاءِ مَقْطُوعٌ
مُّصْبِحِينَ
Hausa
Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan
abin yankẽwa ne a lőkacin da suke măsu shiga asuba.
|
Ayah 15:67 الأية
وَجَاءَ أَهْلُ الْمَدِينَةِ يَسْتَبْشِرُونَ
Hausa
Kuma mutănen alƙaryar suka je sună măsu bushăra.
|
Ayah 15:68 الأية
قَالَ إِنَّ هَٰؤُلَاءِ ضَيْفِي فَلَا تَفْضَحُونِ
Hausa
Ya ce: "Lalle ne waɗannan băƙĩna ne, sabőda haka kada ku kunyata ni."
|
Ayah 15:69 الأية
وَاتَّقُوا اللَّهَ وَلَا تُخْزُونِ
Hausa
"Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki."
|
Ayah 15:70 الأية
قَالُوا أَوَلَمْ نَنْهَكَ عَنِ الْعَالَمِينَ
Hausa
Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tălikai ba?"
|
Ayah 15:71 الأية
قَالَ هَٰؤُلَاءِ بَنَاتِي إِن كُنتُمْ فَاعِلِينَ
Hausa
Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yăna idan kun kasance măsu aikatăwa ne."
|
Ayah 15:72 الأية
لَعَمْرُكَ إِنَّهُمْ لَفِي سَكْرَتِهِمْ يَعْمَهُونَ
Hausa
Rantsuwa da răyuwarka! Lalle ne sũ a cikin măyensu sună ta ɗĩmuwa.
|
Ayah 15:73 الأية
فَأَخَذَتْهُمُ الصَّيْحَةُ مُشْرِقِينَ
Hausa
Sa'an nan tsăwa ta kăma su, sună măsu shiga lőkacin hũdőwar rănă.
|
Ayah 15:74 الأية
فَجَعَلْنَا عَالِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِمْ حِجَارَةً مِّن
سِجِّيلٍ
Hausa
Sa'an nan Muka sanya samanta ya kőma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwătsu na
lăkar wuta a kansu.
|
Ayah 15:75 الأية
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّلْمُتَوَسِّمِينَ
Hausa
Lalle ne a cikin wancan akwai ăyőyi ga măsu tsőkaci da hankali.
|
Ayah 15:76 الأية
وَإِنَّهَا لَبِسَبِيلٍ مُّقِيمٍ
Hausa
Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sună a gẽfen wata hanyă tabbatacciya.
|
Ayah 15:77 الأية
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً لِّلْمُؤْمِنِينَ
Hausa
Lalle ne a cikin wancan akwai ăyă ga măsu ĩmăni.
|
Ayah 15:78 الأية
وَإِن كَانَ أَصْحَابُ الْأَيْكَةِ لَظَالِمِينَ
Hausa
Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika sun kasance, haƙĩƙa, măsu zălunci!
|
Ayah 15:79 الأية
فَانتَقَمْنَا مِنْهُمْ وَإِنَّهُمَا لَبِإِمَامٍ مُّبِينٍ
Hausa
Sai Muka yi azăbar rămuwă a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sună a gẽfen
wani tafarki mabayyani.
|
Ayah 15:80 الأية
وَلَقَدْ كَذَّبَ أَصْحَابُ الْحِجْرِ الْمُرْسَلِينَ
Hausa
Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri sun ƙaryata Manzanni.
|
Ayah 15:81 الأية
وَآتَيْنَاهُمْ آيَاتِنَا فَكَانُوا عَنْهَا مُعْرِضِينَ
Hausa
Kuma Kuka kai musu ăyőyinMu, sai suka kasance măsu bijirẽwa daga gare su.
|
Ayah 15:82 الأية
وَكَانُوا يَنْحِتُونَ مِنَ الْجِبَالِ بُيُوتًا آمِنِينَ
Hausa
Kuma sun kasance sună sassaƙa gidăje daga duwătsu, alhăli sună amintattu.
|
Ayah 15:83 الأية
فَأَخَذَتْهُمُ الصَّيْحَةُ مُصْبِحِينَ
Hausa
Sai tsăwa ta kăma su sună măsu shiga asuba.
|
Ayah 15:84 الأية
فَمَا أَغْنَىٰ عَنْهُم مَّا كَانُوا يَكْسِبُونَ
Hausa
Sa'an nan abin da suka kasance sună tsirfantăwa bai wadătar ga barinsu ba.
|
Ayah 15:85 الأية
وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ ۗ
وَإِنَّ السَّاعَةَ لَآتِيَةٌ ۖ فَاصْفَحِ الصَّفْحَ الْجَمِيلَ
Hausa
Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakăninsu ba făce da
gaskiya. Kuma lalle ne Să'a (Rănar Alƙiyăma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabődahaka ka
yi rangwame, rangwame mai kyau.
|
Ayah 15:86 الأية
إِنَّ رَبَّكَ هُوَ الْخَلَّاقُ الْعَلِيمُ
Hausa
Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.
|
Ayah 15:87 الأية
وَلَقَدْ آتَيْنَاكَ سَبْعًا مِّنَ الْمَثَانِي وَالْقُرْآنَ الْعَظِيمَ
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bă ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu da
Alƙur'ăni mai girma.
|
Ayah 15:88 الأية
لَا تَمُدَّنَّ عَيْنَيْكَ إِلَىٰ مَا مَتَّعْنَا بِهِ أَزْوَاجًا مِّنْهُمْ وَلَا
تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَاخْفِضْ جَنَاحَكَ لِلْمُؤْمِنِينَ
Hausa
Kada lalle kaƙĩƙa idănunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dăɗi game da
shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta
fikăfikanka ga măsu ĩmăni.
|
Ayah 15:89 الأية
وَقُلْ إِنِّي أَنَا النَّذِيرُ الْمُبِينُ
Hausa
Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyananne."
|
Ayah 15:90 الأية
كَمَا أَنزَلْنَا عَلَى الْمُقْتَسِمِينَ
Hausa
Kamar yadda Muka saukar a kan măsu yin rantsuwa,
|
Ayah 15:91 الأية
الَّذِينَ جَعَلُوا الْقُرْآنَ عِضِينَ
Hausa
Waɗanda suka sanya Alƙur'ăni tătsuniyőyi.
|
Ayah 15:92 الأية
فَوَرَبِّكَ لَنَسْأَلَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ
Hausa
To, rantsuwa da Ubangijinka! Haƙĩƙa, Mună tambayarsugabă ɗaya.
|
Ayah 15:93 الأية
عَمَّا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Hausa
Daga abin da suka kasance sună aikatăwa.
|
Ayah 15:94 الأية
فَاصْدَعْ بِمَا تُؤْمَرُ وَأَعْرِضْ عَنِ الْمُشْرِكِينَ
Hausa
Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu
shirki.
|
Ayah 15:95 الأية
إِنَّا كَفَيْنَاكَ الْمُسْتَهْزِئِينَ
Hausa
Lalle ne Mũ Mun isar maka daga măsu izgili.
|
Ayah 15:96 الأية
الَّذِينَ يَجْعَلُونَ مَعَ اللَّهِ إِلَٰهًا آخَرَ ۚ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ
Hausa
Waɗanda suke sanyăwar wani abin bautăwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da
sannu ză su sani.
|
Ayah 15:97 الأية
وَلَقَدْ نَعْلَمُ أَنَّكَ يَضِيقُ صَدْرُكَ بِمَا يَقُولُونَ
Hausa
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mună sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yană yin ƙunci game da
abin da suke faɗă (na izgili).
|
Ayah 15:98 الأية
فَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ وَكُن مِّنَ السَّاجِدِينَ
Hausa
Sabőda haka ka yi tasbĩhi game da gőde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga măsu
sujada.
|
Ayah 15:99 الأية
وَاعْبُدْ رَبَّكَ حَتَّىٰ يَأْتِيَكَ الْيَقِينُ
Hausa
Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|