Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare da bãwanSa da dare daga Masallaci
mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nĩsa wanda Muka sanya albarka a gefensa dõmin
Mu nũna masa daga ãyõyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai ji, Mai gani.
Kuma Mun hukunta zuwa ga Bani Isrã'ĩla a cikin Littãfi, cewa lalle ne, kunã yin
ɓarna a cikin ƙasa sau biyu, kuma lalle ne kunã zãlunci, zãlunci mai girma.
To idan wa'adin na farkonsu yajẽ, za Mu aika, a kanku waɗansu bãyi Nãmu,
ma'abũta yãƙi mafĩ tsanani, har su yi yãwo a tsakãnin gidãjenku, kuma yã zama
wa'adi abin aikatawa.
Idan kun kyautata, kun kyautata dõmin kanku, kuma idan kun mũnana to dõmĩnsu.
Sa'an nan idan wa'adin na ƙarshe ya jẽ, (za su je) dõmin su baƙanta fuskokinku,
kuma su shiga masallaci kamar yadda suka shige shi a farkon lõkaci, kuma dõmin
su halakar da abin da suka rinjaya a kansa, halakarwa.
Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã shiryarwa ga (hãlayen) waɗanda suke mafi daidaita
kuma yanã bãyar da bushãra ga mũminai waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai
(cẽwa) "Lalle ne sunã da wata ijãra. mai girma."
Kuma Mun sanya dare da rãna, ãyõyi biyu, sa'an nan Muka shãfe ãyar dare, kuma
Muka sanya ãyar rãna mai sanyãwa a yi gani, dõmin ku nẽmi falala daga
Ubangijinku, kuma dõmin ku san ƙidãyar shẽkara da lissafi. Kuma dukan kõme Mun
bayyana shi daki-dakin bayyanãwa.
Wanda ya nẽmi shiryuwa, to, ya nẽmi shiryuwa ne dõminkansa kawai kuma wanda ya
ɓace, to, ya ɓace ne a kansa kawai kuma rai mai ɗaukar nauyi bã ya ɗaukar nauyin
wani ran, kuma ba Mu zama mãsu yin azãba ba, sai Mun aika wani Manzo.
Kuma idan Mun yi nufin Mu halakar da wata alƙarya, sai Mu umurci mawadãtanta,
har su yi fãsicci a cikinta, sa'an nan maganar azãba ta wajaba a kanta, sa'an
nan Mu darkãke ta, darkãkẽwa.
Wanda ya kasance yanã nufin mai gaggãwa, sai Mu gaggauta masa a cikinta, abin da
Muke so ga wanda Muke nufi, sa'an nan kuma Mu sanya masa Jahannama, ya ƙõnu da
ita, yanã abin zargi kuma abin tunkuɗewa.
Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi, kum game da mahaifa
biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga tsũfa a wurinka ko dukansu
biyu, to, kada ka ce musu 'tir' kuma kada ka tsãwace su kuma ka faɗa musu magana
mai karimci.
Kuma kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da haƙƙi, kuma wanda aka
kashe, yanã wanda aka zãlunta to, haƙĩƙa Mun sanya hujja ga waliyyinsa, sai dai
kada ya ƙẽtare haddi a cikin kashẽwar. Lalle shĩ ya kasance wanda ake taimako.
Kuma kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce dai da sifa wadda take ita ce mafi
kyau, har ya isa ga mafi ƙarfinsa. Kuma ku cika alkawari. Lalle alkawari yã
kasance abin tambayãwa ne.
Wancan yãnã daga abin da Ubangijinka Ya yi wahayi zuwa gare ka na hikima. Kuma
kada ka sanya wani abin bautãwa na daban tãre da Allah har a jẽfa ka a cikin
Jahannama kanã wanda ake zargi, wanda ake tunkuɗẽwa
Ka ce: "Dã akwai waɗansu abũbuwan bautãwa tãre da shi, kamar yadda suka faɗa, a
lõkacin, dã (abũbuwan bautãwar) sun nẽmi wata hanya zuwa ga Ma'abũcin Al'arshi."
Sammai bakwai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sunã yi Masa tasbĩhi. Kuma bãbu
wani abu fãce yanã tasbĩhi game da gõde Masa, kuma amma ba ku fahimtar
tasbĩhinsu. Lalle ne shĩ, Ya kasance Mai haƙuri ne, Mai gãfara.
Kuma Mu sanya marufai a kan zukãtansu dõmin kada su fahimce shi, da, wani nauyi
a cikin kunnuwansu, kuma idan ka ambaci Ubangijinka, a cikin Alƙur'ãni shĩ
kaɗai, sai su jũya a kan bayayyakinsu dõmin gudu.
Mũ ne Mafi sani game da abin da suke saurãre da shi a lõkacin da suke yin
saurãren zuwa gare ka, kuma a lõkacin da suke mãsu gãnãwa a tsakãninsu a lõkacin
da azzãlumai suke cẽwa, "Bã ku biyar kõwa fãce wani namiji sihirtacce."
"Kõ kuwa wata halitta daga abin da yake da girma a cikin ƙirazanku." To zã su ce
"Wãne ne zai mayar da mu?" Ka ce: "Wanda Ya ƙaga halittarku a fabkon lõkaci."
To, zã su gyaɗa kansu zuwa gare ka, kuma sunã cẽwa, "A yaushene shi?" Ka ce:
"Akwai tsammãninsa ya kasance kusa."
Kuma ka cẽ wa bãyiNa, su faɗi kalma wadda take mafi kyau. Lalle ne Shaiɗan yanã
sanya ɓarna a tsakãninsu. Lalle ne Shaiɗan ya kasance ga mutum, maƙiyi
bayyananne.
Kuma Ubangijinka ne Mafi sani game da wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma
lalle ne, haƙĩƙa, Mun fĩfĩta sãshen Annabãwa a kan sãshe kuma Mun bai wa Dãwũda
zabũra.
Kuma bãbu wata alƙarya fãce, Mu ne mãsu halaka ta a gabãnin Rãnar ¡iyãma kõ kuwa
Mũ mãsu azãbta ta ne da azãba mai tsanani. Wancan ya kasance a cikin littãfi
rubũtacce.
Kuma bãbu abin da ya hana Mu, Mu aika da ãyõyi fãce sabõda mutãnen farko sun
ƙaryata game da su. Kuma Mun bai wa Samũdãwa tãguwa, ãyã bayyananna, sai suka yi
zãlunci game da ita. Kuma bã Mu aikãwa da ãyõyi fãce dõmin tsõratarwa.
Kuma a lõkacin da Muka ce maka, "Lalle ne Ubangijinka Yã kẽwaye mutãne." Kuma ba
Mu sanya abin da ya gani wanda Muka nũna maka ba, fãce dõmin fitina ga mutãne,
da itãciya wadda aka la'anta a cikin Alƙur'ani. Kuma Munã tsõratar da su, sa'an
nan (tsõratarwar) bã ta ƙãra su fãce da kangara mai girma.
Kuma a lõkacin da Muka cẽ wa malã'iku, "Ku yi sujada ga Ãdamu," sai suka yi
sujada, fãce Ibilĩsa, ya ce: "shin, zan yi sujada ga wanda ka halitta shi yanã
lãka?"
Ya ce: "Shin, kã gan ka ! Wannan wanda ka girmama a kaina, lalle ne idan ka
jinkirtã mini zuwa ga Rãnar ¡iyãma lalle ne, zan tumɓuke zuriyarsa, fãce kaɗan."
"Kuma ka rikitar da wanda ka sãmi ĩko a kansa, daga gare su, da sautinka, kuma
ka yi hari a kansu da dawãkinka da dãkãrunka kuma ka yi tãrẽwa da su a cikin
dũkiyõyi da ɗiyã, kumaka yi musu wa'adi. Alhãli kuwa Shaiɗan bã ya yi musu
wa'adin kõme fãce da ruɗi."
Kuma idan cũta ta shãfe ku, a cikin tẽku, sai wanda kuke kira ya ɓace fãce Shi.
To, a lõkacin da Ya tsira da ku zuwa,ga tudu sai kuka bijire. Kuma mutum ya
kasance mai yawan butulci.
Shin fa kun amince cẽwa (Allah) bã Ya shãfe gẽfen ƙasa game da ku kõ kuwa Ya
aika da iska mai tsakuwa a kanku, sa'an nan kuma bã zã ku sãmi wani wakĩli ba
dõminku?
Ko kun amince ga Ya mayar da ku a cikin tẽkun a wani lõkaci na dabam, sa'an na
Ya aika wata gũguwa mai karya abũbuwa daga iska, har ya nutsar da ku sabõda abin
da kuka yi na kãfirci? Sa'an nan kuma bã ku sãmun mai bin hakki sabõda ku, a
kanMu, game da Shi.
Kuma lalle ne Mun girmama 'yan Adam, kuma Muka ɗauke su a cikin ƙasa da tẽku
kuma Muka azurta su daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma Muka fĩfĩta su a kan mãsu yawa
daga waɗanda Muka halitta, fĩfĩtãwa.
A rãnar da Muke kiran kõwane mutãne da lĩmãminsu to, wanda aka bai wa littafinsa
a dã, mansa, to, waɗannan sunã karãtun littãfinsu, kuma bã a zãluntar su da
zaren bãkin gurtsin dabĩno.
Kuma lalle ne sun yi kusa haƙĩƙa, su fitinẽ ka daga abin da Muka yi wahayi zuwa
gare ka, dõmin ka ƙirƙira waninsa a gare Mu, a lõkacin, haƙĩƙa, dã sun riƙe ka
masoyi.
Kuma lalle ne, sun yi kusa, haƙĩƙa, su tãyar da hankalinka daga ƙasar, dõmin su
fitar da kai daga gare ta. Kuma a lõkacin, bã zã su zauna ba a kan sãɓãninka
fãce kaɗan.