First Ayah 1 الأية الأوليبِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
اقْتَرَبَ لِلنَّاسِ حِسَابُهُمْ وَهُمْ فِي غَفْلَةٍ مُّعْرِضُونَ
Hausa
Hisăbin mutăne ya kusanta gare su, ahăli kuwa sună a cikin gafala, sună măsu
bijirẽwa.
|
Ayah 21:2 الأية
مَا يَأْتِيهِم مِّن ذِكْرٍ مِّن رَّبِّهِم مُّحْدَثٍ إِلَّا اسْتَمَعُوهُ وَهُمْ
يَلْعَبُونَ
Hausa
Wani ambatő daga Ubangijinsu săbo, bă ya zuwa gare su făce sun saurăre shi,
alhăli kuwa sună măsu yin wăsa.
|
Ayah 21:3 الأية
لَاهِيَةً قُلُوبُهُمْ ۗ وَأَسَرُّوا النَّجْوَى الَّذِينَ ظَلَمُوا هَلْ هَٰذَا
إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُكُمْ ۖ أَفَتَأْتُونَ السِّحْرَ وَأَنتُمْ تُبْصِرُونَ
Hausa
Sană măsu shagaltacin zukătansu, kuma su asirta gănăwa: Waɗanda suka yi zălunce
(sună cẽwa) "Wannan bă Kőwa ba ne făce mutum misălinku. Shin, to, kună jẽ wa
sihiri, ahăli kuwa kũ, kună fahimta?"
|
Ayah 21:4 الأية
قَالَ رَبِّي يَعْلَمُ الْقَوْلَ فِي السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ ۖ وَهُوَ السَّمِيعُ
الْعَلِيمُ
Hausa
Ya ce: "Ubangijina Yană sanin magana a cikin sama da ƙasa kuma Shi ne Mai ji,
Masani."
|
Ayah 21:5 الأية
بَلْ قَالُوا أَضْغَاثُ أَحْلَامٍ بَلِ افْتَرَاهُ بَلْ هُوَ شَاعِرٌ فَلْيَأْتِنَا
بِآيَةٍ كَمَا أُرْسِلَ الْأَوَّلُونَ
Hausa
Ă'a, suka ce: "Yăye-yăyen mafarki ne. Ă'a, yă ƙirƙira shi ne. Ă'a, shi mawăƙi
ne. Sai ya zo mana da wata ăyă kamar yadda aka aiko manzanni na farko."
|
Ayah 21:6 الأية
مَا آمَنَتْ قَبْلَهُم مِّن قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَاهَا ۖ أَفَهُمْ يُؤْمِنُونَ
Hausa
Wata alƙarya da Muka halaka ta a gabăninsu, ba ta yi ĩmăni ba. Shin, to, sũ,
sună yin ĩmăni?
|
Ayah 21:7 الأية
وَمَا أَرْسَلْنَا قَبْلَكَ إِلَّا رِجَالًا نُّوحِي إِلَيْهِمْ ۖ فَاسْأَلُوا
أَهْلَ الذِّكْرِ إِن كُنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ
Hausa
Kuma ba Mu aika ba a gabăninka făce mazăje, Mună yin wahayi zuwa gare su. Ku
tambayi ma'abũta ambato idan kun kasance ba ku sani ba.
|
Ayah 21:8 الأية
وَمَا جَعَلْنَاهُمْ جَسَدًا لَّا يَأْكُلُونَ الطَّعَامَ وَمَا كَانُوا خَالِدِينَ
Hausa
Kuma ba Mu sanya su jiki, bă su cin abin ci ba, kuma ba su kasance madawwama ba.
|
Ayah 21:9 الأية
ثُمَّ صَدَقْنَاهُمُ الْوَعْدَ فَأَنجَيْنَاهُمْ وَمَن نَّشَاءُ وَأَهْلَكْنَا
الْمُسْرِفِينَ
Hausa
Sa'an nan kuma Muka gaskata musu alkawari; sai Muka tsẽrar da su da wanda Muke
so, kuma Muka halakar da măsu yawaităwa.
|
Ayah 21:10 الأية
لَقَدْ أَنزَلْنَا إِلَيْكُمْ كِتَابًا فِيهِ ذِكْرُكُمْ ۖ أَفَلَا تَعْقِلُونَ
Hausa
Lalle haƙĩƙa Mun saukar da wani littăfi zuwa gare ku, a cikinsa akwai ambatonku.
Shin, to, bă ku hankalta?
|
Ayah 21:11 الأية
وَكَمْ قَصَمْنَا مِن قَرْيَةٍ كَانَتْ ظَالِمَةً وَأَنشَأْنَا بَعْدَهَا قَوْمًا
آخَرِينَ
Hausa
Kuma da yawa Muka karya wata alƙarya tă kasance mai zălunci, kuma Muka ƙăga
halittar waɗansu mutăne na dabam a băyanta.
|
Ayah 21:12 الأية
فَلَمَّا أَحَسُّوا بَأْسَنَا إِذَا هُم مِّنْهَا يَرْكُضُونَ
Hausa
Sai a lőkacin da suka hangi azăbarMu, sai gă su sună gudu daga gare ta.
|
Ayah 21:13 الأية
لَا تَرْكُضُوا وَارْجِعُوا إِلَىٰ مَا أُتْرِفْتُمْ فِيهِ وَمَسَاكِنِكُمْ
لَعَلَّكُمْ تُسْأَلُونَ
Hausa
"Kada ku yi gudu. Ku kőmo zuwa ga abin da aka ni'imtar da ku a cikinsa da
gidăjenku tsammăninku ană tambayar ku."
|
Ayah 21:14 الأية
قَالُوا يَا وَيْلَنَا إِنَّا كُنَّا ظَالِمِينَ
Hausa
Suka ce: "Kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance măsu zălunci."
|
Ayah 21:15 الأية
فَمَا زَالَت تِّلْكَ دَعْوَاهُمْ حَتَّىٰ جَعَلْنَاهُمْ حَصِيدًا خَامِدِينَ
Hausa
Sa'an nan waccan ba ta gushe ba, ita ce da'awarsu har Muka mayar da su girbabbu,
bitattu.
|
Ayah 21:16 الأية
وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاءَ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَاعِبِينَ
Hausa
Kuma ba Mu halitta sama da ƙasa da abin da ke a tsakăninsu Muna Măsu wăsă ba.
|
Ayah 21:17 الأية
لَوْ أَرَدْنَا أَن نَّتَّخِذَ لَهْوًا لَّاتَّخَذْنَاهُ مِن لَّدُنَّا إِن كُنَّا
فَاعِلِينَ
Hausa
Da Mun yi nufin Mu riƙi wani abin wăsa dă Mun riƙe shi daga gunMu, idan Mun
kasance măsu aikatăwa.
|
Ayah 21:18 الأية
بَلْ نَقْذِفُ بِالْحَقِّ عَلَى الْبَاطِلِ فَيَدْمَغُهُ فَإِذَا هُوَ زَاهِقٌ ۚ
وَلَكُمُ الْوَيْلُ مِمَّا تَصِفُونَ
Hausa
Ă'a, Mună jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkăke ta, sai ga tă halakakka.
Kuma bone yă tabbata a gare ku sabőda abin da kuke siffantăwa.
|
Ayah 21:19 الأية
وَلَهُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَمَنْ عِندَهُ لَا يَسْتَكْبِرُونَ
عَنْ عِبَادَتِهِ وَلَا يَسْتَحْسِرُونَ
Hausa
Kuma shĩ ne da mallakar wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma waɗanda suke
wurinSa (watau mală'iku), bă su yin girman kai ga ibădarSa. kuma bă su gajiya.
|
Ayah 21:20 الأية
يُسَبِّحُونَ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ لَا يَفْتُرُونَ
Hausa
Sună tasbĩhi dare da rănă, bă su yin rauni.
|
Ayah 21:21 الأية
أَمِ اتَّخَذُوا آلِهَةً مِّنَ الْأَرْضِ هُمْ يُنشِرُونَ
Hausa
Kő (kăfirai) sun riƙi waɗansu abũbuwan bautăwa ne ga ƙasă, su ne măsu tăyarwa
(gare su)?
|
Ayah 21:22 الأية
لَوْ كَانَ فِيهِمَا آلِهَةٌ إِلَّا اللَّهُ لَفَسَدَتَا ۚ فَسُبْحَانَ اللَّهِ
رَبِّ الْعَرْشِ عَمَّا يَصِفُونَ
Hausa
Dă waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da ƙasa) făce Allah,
haƙĩƙa dă su biyun sun ɓăci. Sabőda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin
Al'arshi daga abin da suke siffantăwa.
|
Ayah 21:23 الأية
لَا يُسْأَلُ عَمَّا يَفْعَلُ وَهُمْ يُسْأَلُونَ
Hausa
Bă a tambayar Sa ga abin da Yake aikatăwa, alhăli kuwa sũană tambayar su.
|
Ayah 21:24 الأية
أَمِ اتَّخَذُوا مِن دُونِهِ آلِهَةً ۖ قُلْ هَاتُوا بُرْهَانَكُمْ ۖ هَٰذَا ذِكْرُ
مَن مَّعِيَ وَذِكْرُ مَن قَبْلِي ۗ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ الْحَقَّ ۖ
فَهُم مُّعْرِضُونَ
Hausa
Kő sun riƙi waɗansu abũbuwan bautăwa baicinSa? Ka ce: "Ku kăwo hujjarku, wannan
shi ne ambaton wanda yake tăre da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabănĩna.
Ă'a, mafi yawansubă su sanin gaskiya, sabőda haka sũ măsu bijirẽwa ne."
|
Ayah 21:25 الأية
وَمَا أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِي إِلَيْهِ أَنَّهُ لَا
إِلَٰهَ إِلَّا أَنَا فَاعْبُدُونِ
Hausa
Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabăninka făce Mună yin wahayi zuwa gare shi,
cẽwa "Lalle ne Shi, băbu abin bautăwa făce Nĩ, sai ku bauta Mini."
|
Ayah 21:26 الأية
وَقَالُوا اتَّخَذَ الرَّحْمَٰنُ وَلَدًا ۗ سُبْحَانَهُ ۚ بَلْ عِبَادٌ
مُّكْرَمُونَ
Hausa
Kuma suka ce: "Mai rahama ya riƙi ɗă." Tsarkinsa, ya tabbata! Ă'a, (mală'iku)
băyi ne măsu daraja.
|
Ayah 21:27 الأية
لَا يَسْبِقُونَهُ بِالْقَوْلِ وَهُم بِأَمْرِهِ يَعْمَلُونَ
Hausa
Bă su gabătarSa da magana, kuma su da umurninSa suke aiki.
|
Ayah 21:28 الأية
يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلَا يَشْفَعُونَ إِلَّا لِمَنِ
ارْتَضَىٰ وَهُم مِّنْ خَشْيَتِهِ مُشْفِقُونَ
Hausa
Yană sanin abin da yake gaba gare su da abin da yake a băyansu, kuma bă su yin
cẽto făce ga wanda Ya yarda, kuma sũmasu sauna ne sabőda tsőronSa.
|
Ayah 21:29 الأية
وَمَن يَقُلْ مِنْهُمْ إِنِّي إِلَٰهٌ مِّن دُونِهِ فَذَٰلِكَ نَجْزِيهِ جَهَنَّمَ
ۚ كَذَٰلِكَ نَجْزِي الظَّالِمِينَ
Hausa
Kuma wanda ya ce daga gare su, "Lalle nĩ abin bautăwa ne baicinSa," to, wannan
Mună săkă masa da, Jahannama. Kamar haka Muke săkă wa azzălumai.
|
Ayah 21:30 الأية
أَوَلَمْ يَرَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَنَّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ كَانَتَا
رَتْقًا فَفَتَقْنَاهُمَا ۖ وَجَعَلْنَا مِنَ الْمَاءِ كُلَّ شَيْءٍ حَيٍّ ۖ
أَفَلَا يُؤْمِنُونَ
Hausa
Shin kuma waɗanda suka kăfirta ba, su gani da cẽwa lalle sammai da ƙasa sun
kasance ɗinke, sai Muka bũɗe su, kuma Muka sanya dukan kome mai rai daga ruwa?
Shin, bă ză su yi ĩmăni ba?
|
Ayah 21:31 الأية
وَجَعَلْنَا فِي الْأَرْضِ رَوَاسِيَ أَن تَمِيدَ بِهِمْ وَجَعَلْنَا فِيهَا
فِجَاجًا سُبُلًا لَّعَلَّهُمْ يَهْتَدُونَ
Hausa
Kuma Mun sanya tabbatattun duwătsu a cikin ƙasa dőmin kada ta karkata da su kuma
Mun sanya ranguna, hanyőyi, a cikinsu (duwătsun), tsammăninsu sună shiryuwa.
|
Ayah 21:32 الأية
وَجَعَلْنَا السَّمَاءَ سَقْفًا مَّحْفُوظًا ۖ وَهُمْ عَنْ آيَاتِهَا مُعْرِضُونَ
Hausa
Kuma Mun sanya sama rufi tsararre, alhăli kuwa su daga ăyőyinta măsu bijirẽwa
ne.
|
Ayah 21:33 الأية
وَهُوَ الَّذِي خَلَقَ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ ۖ كُلٌّ فِي
فَلَكٍ يَسْبَحُونَ
Hausa
Kuma shĩ ne wanda Ya halitta dare da yini da rănă da wată dukansu a cikin wani
sarari suKe iyo.
|
Ayah 21:34 الأية
وَمَا جَعَلْنَا لِبَشَرٍ مِّن قَبْلِكَ الْخُلْدَ ۖ أَفَإِن مِّتَّ فَهُمُ
الْخَالِدُونَ
Hausa
Kuma ba Mu sanya dawwama ga wani mutum ba, a gabăninka. Shin to idan ka mutu to
sũ ne madawwama?
|
Ayah 21:35 الأية
كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ ۗ وَنَبْلُوكُم بِالشَّرِّ وَالْخَيْرِ فِتْنَةً
ۖ وَإِلَيْنَا تُرْجَعُونَ
Hausa
Kőwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Mună jarraba ku da sharri da alhẽri
dőmin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku.
|
Ayah 21:36 الأية
وَإِذَا رَآكَ الَّذِينَ كَفَرُوا إِن يَتَّخِذُونَكَ إِلَّا هُزُوًا أَهَٰذَا
الَّذِي يَذْكُرُ آلِهَتَكُمْ وَهُم بِذِكْرِ الرَّحْمَٰنِ هُمْ كَافِرُونَ
Hausa
Kuma idan waɗanda suka kăfirta suka gan ka, bă su riƙon ka făce da izgili (sună
cẽwa), "Shin, wannan ne ke ambatar gumăkanku?" Alhăli kuwa sũ, ga ambatar Mai
rahama, măsu kăfirta ne.
|
Ayah 21:37 الأية
خُلِقَ الْإِنسَانُ مِنْ عَجَلٍ ۚ سَأُرِيكُمْ آيَاتِي فَلَا تَسْتَعْجِلُونِ
Hausa
An halitta mutum daga gaggăwa, zan nũna muku ăyőyiNa. Sabőda haka kada ku
nẽmiyin gaggăwa.
|
Ayah 21:38 الأية
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا الْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Hausa
Kuma sună cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi zai tabbata, idan kun kasance măsu
gaskiya?"
|
Ayah 21:39 الأية
لَوْ يَعْلَمُ الَّذِينَ كَفَرُوا حِينَ لَا يَكُفُّونَ عَن وُجُوهِهِمُ النَّارَ
وَلَا عَن ظُهُورِهِمْ وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ
Hausa
Dă waɗanda suka kăfirta sună sanin lőkacin da bă su kange wuta daga fuskőkinsu,
kuma haka daga băyayyakinsu, alhăli kuwa ba su zama ana taimakon su ba.
|
Ayah 21:40 الأية
بَلْ تَأْتِيهِم بَغْتَةً فَتَبْهَتُهُمْ فَلَا يَسْتَطِيعُونَ رَدَّهَا وَلَا هُمْ
يُنظَرُونَ
Hausa
Ă'a, tană jẽ musu bisa ga auke sai ta ɗimautar da su, sa'an nan bă su iya mayar
da ita, kuma ba su zama ană yi musu jinkiri ba.
|
Ayah 21:41 الأية
وَلَقَدِ اسْتُهْزِئَ بِرُسُلٍ مِّن قَبْلِكَ فَحَاقَ بِالَّذِينَ سَخِرُوا مِنْهُم
مَّا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili ga waɗansu Manzanni daga gabăninka, sai abin
da suka kasance sună izgili da shi ya auku ga waɗanda suka yi izgilin daga gare
su.
|
Ayah 21:42 الأية
قُلْ مَن يَكْلَؤُكُم بِاللَّيْلِ وَالنَّهَارِ مِنَ الرَّحْمَٰنِ ۗ بَلْ هُمْ عَن
ذِكْرِ رَبِّهِم مُّعْرِضُونَ
Hausa
Ka ce: "Wăne ne yake tsare ku a dare da yini daga Mai rahama?" Ă'a, sũ măsu
bijirẽwa ne daga ambaton Ubangijinsu.
|
Ayah 21:43 الأية
أَمْ لَهُمْ آلِهَةٌ تَمْنَعُهُم مِّن دُونِنَا ۚ لَا يَسْتَطِيعُونَ نَصْرَ
أَنفُسِهِمْ وَلَا هُم مِّنَّا يُصْحَبُونَ
Hausa
Ko kuwa sună da waɗansu abũbuwan bautăwa waɗanda ke tsare su, daga gare Mu? Bă
su iya taimakon kansu kuma ba su kasance ană abũtar su ba daga gareMu.
|
Ayah 21:44 الأية
بَلْ مَتَّعْنَا هَٰؤُلَاءِ وَآبَاءَهُمْ حَتَّىٰ طَالَ عَلَيْهِمُ الْعُمُرُ ۗ
أَفَلَا يَرَوْنَ أَنَّا نَأْتِي الْأَرْضَ نَنقُصُهَا مِنْ أَطْرَافِهَا ۚ
أَفَهُمُ الْغَالِبُونَ
Hausa
Ă'a, Mun yalwata wa waɗannan da ubanninsu ni'imarMu, har răyuwa ta yi tsawo a
kansu. Shin, to, bă su ganin cẽwa lalle Mũ, Mună je wa ƙasarsu, Mună rage ta
daga săsanninta? Shin, to, su ne marinjaya?
|
Ayah 21:45 الأية
قُلْ إِنَّمَا أُنذِرُكُم بِالْوَحْيِ ۚ وَلَا يَسْمَعُ الصُّمُّ الدُّعَاءَ إِذَا
مَا يُنذَرُونَ
Hausa
Ka ce: "Abin sani, ină yi muku gargaɗi kawai da wahayi," kuma kurma ba ya jin
kira a lőkacin da ake yi musu gargaɗi.
|
Ayah 21:46 الأية
وَلَئِن مَّسَّتْهُمْ نَفْحَةٌ مِّنْ عَذَابِ رَبِّكَ لَيَقُولُنَّ يَا وَيْلَنَا
إِنَّا كُنَّا ظَالِمِينَ
Hausa
Kuma haƙĩƙa idan wata iska daga azăbar Ubangiji ta shăfe su, haƙĩƙa sună cẽwa,
"Yă kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance măsu zălunci."
|
Ayah 21:47 الأية
وَنَضَعُ الْمَوَازِينَ الْقِسْطَ لِيَوْمِ الْقِيَامَةِ فَلَا تُظْلَمُ نَفْسٌ
شَيْئًا ۖ وَإِن كَانَ مِثْقَالَ حَبَّةٍ مِّنْ خَرْدَلٍ أَتَيْنَا بِهَا ۗ
وَكَفَىٰ بِنَا حَاسِبِينَ
Hausa
Kuma Mună aza ma'aunan ădalci ga Rănar ˇiyăma, sabőda haka ba a zăluntar rai da
kőme. Kuma kő dă ya kasance nauyin ƙwăya daga kőmayya ne Mun zo da ita. Kuma Mun
isa zama Măsu hisăbi.
|
Ayah 21:48 الأية
وَلَقَدْ آتَيْنَا مُوسَىٰ وَهَارُونَ الْفُرْقَانَ وَضِيَاءً وَذِكْرًا
لِّلْمُتَّقِينَ
Hausa
Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun kăwo wa Mũsă da Hărũna Rarrabewa da haske da ambato ga
măsu aiki da taƙawa.
|
Ayah 21:49 الأية
الَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُم بِالْغَيْبِ وَهُم مِّنَ السَّاعَةِ مُشْفِقُونَ
Hausa
Waɗanda suke tsăron Ubangijinsu a fake, alhăli kuwa sũ, măsu sauna ne daga Sa'a.
|
Ayah 21:50 الأية
وَهَٰذَا ذِكْرٌ مُّبَارَكٌ أَنزَلْنَاهُ ۚ أَفَأَنتُمْ لَهُ مُنكِرُونَ
Hausa
Kuma wannan ambato ne mai albarka Mun saukar da shi. Shin, to, kũ măsu musu ne
gare shi?
|
Ayah 21:51 الأية
وَلَقَدْ آتَيْنَا إِبْرَاهِيمَ رُشْدَهُ مِن قَبْلُ وَكُنَّا بِهِ عَالِمِينَ
Hausa
Kuma lalle haƙĩƙa Mun kăwo wa Ibrăhĩm shiryuwarsa daga gabăni, kuma Mun kasance
Masana gare shi.
|
Ayah 21:52 الأية
إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ مَا هَٰذِهِ التَّمَاثِيلُ الَّتِي أَنتُمْ لَهَا
عَاكِفُونَ
Hausa
Ya ce wa ubansa da mutanensa, "Mẽne ne waɗannan mutummutumai waɗanda kuke măsu
lazimta a kansu?"
|
Ayah 21:53 الأية
قَالُوا وَجَدْنَا آبَاءَنَا لَهَا عَابِدِينَ
Hausa
Suka ce: "Mun sămi Ubanninmu măsu lazimta a kansu."
|
Ayah 21:54 الأية
قَالَ لَقَدْ كُنتُمْ أَنتُمْ وَآبَاؤُكُمْ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Hausa
Ya ce: "Lalle, haƙĩƙa, kun kasance kũ da Ubanninku a cikin ɓata bayyananna."
|
Ayah 21:55 الأية
قَالُوا أَجِئْتَنَا بِالْحَقِّ أَمْ أَنتَ مِنَ اللَّاعِبِينَ
Hausa
Suka ce: "Shin kă zo mana da gaskiya ne, Kő kuwa kai kană daga măSu wăsă ne?"
|
Ayah 21:56 الأية
قَالَ بَل رَّبُّكُمْ رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الَّذِي فَطَرَهُنَّ وَأَنَا
عَلَىٰ ذَٰلِكُم مِّنَ الشَّاهِدِينَ
Hausa
Ya ce: "Ă'a, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, wanda Ya ƙăga
halittarsu. Kuma Ni ină daga măsu shaida a kan haka."
|
Ayah 21:57 الأية
وَتَاللَّهِ لَأَكِيدَنَّ أَصْنَامَكُم بَعْدَ أَن تُوَلُّوا مُدْبِرِينَ
Hausa
"Kuma ină rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga gumăkanku a băyan kun
jũya kună măsu băyar da băya."
|
Ayah 21:58 الأية
فَجَعَلَهُمْ جُذَاذًا إِلَّا كَبِيرًا لَّهُمْ لَعَلَّهُمْ إِلَيْهِ يَرْجِعُونَ
Hausa
Sai ya sanya su guntu-guntu făce wani babba gare su, tsammăninsũ sună Kőmăwa
zuwa gare shi.
|
Ayah 21:59 الأية
قَالُوا مَن فَعَلَ هَٰذَا بِآلِهَتِنَا إِنَّهُ لَمِنَ الظَّالِمِينَ
Hausa
Suka ce: "Wane ne ya aikata wannan ga gumăkanmu? Lalle shĩ, haƙĩƙa, yană daga
azzălumai."
|
Ayah 21:60 الأية
قَالُوا سَمِعْنَا فَتًى يَذْكُرُهُمْ يُقَالُ لَهُ إِبْرَاهِيمُ
Hausa
Suka ce: "Mun ji wani saurayi yană ambatar su. Ană ce masa Ibrahĩm."
|
Ayah 21:61 الأية
قَالُوا فَأْتُوا بِهِ عَلَىٰ أَعْيُنِ النَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَشْهَدُونَ
Hausa
Suka ce: "To, ku zo da shi a kan idanun mutăne, tsammănin su ză su băyar da
shaida."
|
Ayah 21:62 الأية
قَالُوا أَأَنتَ فَعَلْتَ هَٰذَا بِآلِهَتِنَا يَا إِبْرَاهِيمُ
Hausa
Suka ce: "Shin kai ne ka aikata wannan ga gumăkanmu? Yă Ibrahĩm!"
|
Ayah 21:63 الأية
قَالَ بَلْ فَعَلَهُ كَبِيرُهُمْ هَٰذَا فَاسْأَلُوهُمْ إِن كَانُوا يَنطِقُونَ
Hausa
Ya ce: "Ă'a, babbansu, wannan, shĩ ya aikata, shi. Sai ku tambaye su idan sun
kasance sună yin magana."
|
Ayah 21:64 الأية
فَرَجَعُوا إِلَىٰ أَنفُسِهِمْ فَقَالُوا إِنَّكُمْ أَنتُمُ الظَّالِمُونَ
Hausa
Sai suka kőma wa jũnansu suka ce: "Lalle ne kũ, kũ ne azzălumai."
|
Ayah 21:65 الأية
ثُمَّ نُكِسُوا عَلَىٰ رُءُوسِهِمْ لَقَدْ عَلِمْتَ مَا هَٰؤُلَاءِ يَنطِقُونَ
Hausa
Sa'an nan kuma aka sunkuyar da su a kan kăwunansu (sukace,) "Lalle, haƙĩƙa, kă
sani waɗannan bă su yin magana."
|
Ayah 21:66 الأية
قَالَ أَفَتَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكُمْ شَيْئًا وَلَا
يَضُرُّكُمْ
Hausa
Ya ce: "Shin to, kună baută wa abin da, bă ya, amfănin ku da Kőme kuma bă ya
cũtar da ku baicin Allah?"
|
Ayah 21:67 الأية
أُفٍّ لَّكُمْ وَلِمَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ ۖ أَفَلَا تَعْقِلُونَ
Hausa
"Tir da ku, kuma da abin da kuke bauta wa, baicin Allah! Shin to, bă ku
hankalta?"
|
Ayah 21:68 الأية
قَالُوا حَرِّقُوهُ وَانصُرُوا آلِهَتَكُمْ إِن كُنتُمْ فَاعِلِينَ
Hausa
Suka ce: "Ku ƙőne shi kuma ku taimaki gumăkanku, idan kun kasance măsu
aikatăwa."
|
Ayah 21:69 الأية
قُلْنَا يَا نَارُ كُونِي بَرْدًا وَسَلَامًا عَلَىٰ إِبْرَاهِيمَ
Hausa
Muka ce: "Yă wuta! Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm."
|
Ayah 21:70 الأية
وَأَرَادُوا بِهِ كَيْدًا فَجَعَلْنَاهُمُ الْأَخْسَرِينَ
Hausa
Kuma suka yi nufin wani mũgun shiri da shi, sai Mukasanya su mafiya hasăra.
|
Ayah 21:71 الأية
وَنَجَّيْنَاهُ وَلُوطًا إِلَى الْأَرْضِ الَّتِي بَارَكْنَا فِيهَا لِلْعَالَمِينَ
Hausa
Kuma Muka tsẽrar da shi da Lũɗu zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a
cikinta ga tălikai.
|
Ayah 21:72 الأية
وَوَهَبْنَا لَهُ إِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ نَافِلَةً ۖ وَكُلًّا جَعَلْنَا صَالِحِينَ
Hausa
Kuma Muka ba shi Is'haka da Ya'aƙuba a kan daɗi alhăli kuwa dukansu Mun sanya su
sălihai.
|
Ayah 21:73 الأية
وَجَعَلْنَاهُمْ أَئِمَّةً يَهْدُونَ بِأَمْرِنَا وَأَوْحَيْنَا إِلَيْهِمْ فِعْلَ
الْخَيْرَاتِ وَإِقَامَ الصَّلَاةِ وَإِيتَاءَ الزَّكَاةِ ۖ وَكَانُوا لَنَا
عَابِدِينَ
Hausa
Kuma Muka sanya su shugabanni, sună shiryarwa da umurninMu. Kuma Muka yi wahayi
zuwa gare su da ayyukan alhẽri da tsayar da salla da băyar da zakka. Kuma sun
kasance măsu bauta gare Mu.
|
Ayah 21:74 الأية
وَلُوطًا آتَيْنَاهُ حُكْمًا وَعِلْمًا وَنَجَّيْنَاهُ مِنَ الْقَرْيَةِ الَّتِي
كَانَت تَّعْمَلُ الْخَبَائِثَ ۗ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمَ سَوْءٍ فَاسِقِينَ
Hausa
Kuma Lũɗu Mun bă shi hukunci da ilmi. Kuma Mun tsĩrar da shi daga alƙaryar nan
wadda ke aikata mũnănan ayyuka. Lallesũ, sun kasance mutănen mũgun aiki,
făsiƙai.
|
Ayah 21:75 الأية
وَأَدْخَلْنَاهُ فِي رَحْمَتِنَا ۖ إِنَّهُ مِنَ الصَّالِحِينَ
Hausa
Kuma Muka shigar da shi a cikin rahamarMu. Lalle ne shĩ, yană daga sălihai.
|
Ayah 21:76 الأية
وَنُوحًا إِذْ نَادَىٰ مِن قَبْلُ فَاسْتَجَبْنَا لَهُ فَنَجَّيْنَاهُ وَأَهْلَهُ
مِنَ الْكَرْبِ الْعَظِيمِ
Hausa
Kuma Nũhu, a sa'ad da ya yi kira a gabăni, sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka
tsirar da shi da mutănensa daga baƙin ciki mai girma.
|
Ayah 21:77 الأية
وَنَصَرْنَاهُ مِنَ الْقَوْمِ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا
قَوْمَ سَوْءٍ فَأَغْرَقْنَاهُمْ أَجْمَعِينَ
Hausa
Kuma Muka taimake shi daga mutănen nan waɗanda suka ƙaryata da ăyőyinMu. Lalle
ne sũ, sun kasance mutănen mugun aiki. Sai Muka nutsar da su gabă ɗaya.
|
Ayah 21:78 الأية
وَدَاوُودَ وَسُلَيْمَانَ إِذْ يَحْكُمَانِ فِي الْحَرْثِ إِذْ نَفَشَتْ فِيهِ
غَنَمُ الْقَوْمِ وَكُنَّا لِحُكْمِهِمْ شَاهِدِينَ
Hausa
Kuma Dăwũda da Sulaimăn sa'ad da suke yin hukunci a cikin sha'anin shũka a
lőkacin da tumăkin mutăne suka yi kiĩwon dare a cikinsa. Kuma Mun kasance Măsu
halarta ga hukuncinsu.
|
Ayah 21:79 الأية
فَفَهَّمْنَاهَا سُلَيْمَانَ ۚ وَكُلًّا آتَيْنَا حُكْمًا وَعِلْمًا ۚ وَسَخَّرْنَا
مَعَ دَاوُودَ الْجِبَالَ يُسَبِّحْنَ وَالطَّيْرَ ۚ وَكُنَّا فَاعِلِينَ
Hausa
Sai Muka fahimtar da ita (mats'alar) ga Sulaiman. Kuma dukansu Mun bă su hukunci
da ilmi kuma Muka hőre duwatsu tăre da Dăwũda, sună tasbĩhi, da tsuntsăye. Kuma
Mun kasance Măsu aikatăwa.
|
Ayah 21:80 الأية
وَعَلَّمْنَاهُ صَنْعَةَ لَبُوسٍ لَّكُمْ لِتُحْصِنَكُم مِّن بَأْسِكُمْ ۖ فَهَلْ
أَنتُمْ شَاكِرُونَ
Hausa
Kuma Muka sanar da shi sana'ar wata tufa sabőda ku dőmin ya tsare ku daga
makăminku. To, shin, ku măsu gődẽwa ne?
|
Ayah 21:81 الأية
وَلِسُلَيْمَانَ الرِّيحَ عَاصِفَةً تَجْرِي بِأَمْرِهِ إِلَى الْأَرْضِ الَّتِي
بَارَكْنَا فِيهَا ۚ وَكُنَّا بِكُلِّ شَيْءٍ عَالِمِينَ
Hausa
Kuma (Muka hőre) wa Sulaimăn iska mai tsananin bugăwa, tană gudăna da umuruinsa
zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta. Kuma Mun kasance Masana ga
dukkan Kőme.
|
Ayah 21:82 الأية
وَمِنَ الشَّيَاطِينِ مَن يَغُوصُونَ لَهُ وَيَعْمَلُونَ عَمَلًا دُونَ ذَٰلِكَ ۖ
وَكُنَّا لَهُمْ حَافِظِينَ
Hausa
Kuma daga Shaiɗannu (Mun hőre) wanda ke nutso sabőda shi. Kuma sună yin wani
aiki baicin wancan. Kuma Mun kasance Măsu tsaro a gare su.
|
Ayah 21:83 الأية
وَأَيُّوبَ إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُ أَنِّي مَسَّنِيَ الضُّرُّ وَأَنتَ أَرْحَمُ
الرَّاحِمِينَ
Hausa
Kuma da Ayyũba a să'ad da ya yi kiran Ubangijinsa, (ya ce:) "Lalle nĩ, cũta ta
shăfe ni, alhăli kuwa Kai ne Mafi rahamar măsu rahama."
|
Ayah 21:84 الأية
فَاسْتَجَبْنَا لَهُ فَكَشَفْنَا مَا بِهِ مِن ضُرٍّ ۖ وَآتَيْنَاهُ أَهْلَهُ
وَمِثْلَهُم مَّعَهُمْ رَحْمَةً مِّنْ عِندِنَا وَذِكْرَىٰ لِلْعَابِدِينَ
Hausa
Sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka kuranye abin da ke a gare shi na cũta, kuma
Muka kăwo masa mutănesa da kwatank wacinsu tăre da su, sabőda rahama daga
wurinMu da tunătarwa ga măsu ibăda.
|
Ayah 21:85 الأية
وَإِسْمَاعِيلَ وَإِدْرِيسَ وَذَا الْكِفْلِ ۖ كُلٌّ مِّنَ الصَّابِرِينَ
Hausa
Kuma da Ismăĩla da Idrĩsa da Zulkifli, dukansu sună daga măsu haƙuri.
|
Ayah 21:86 الأية
وَأَدْخَلْنَاهُمْ فِي رَحْمَتِنَا ۖ إِنَّهُم مِّنَ الصَّالِحِينَ
Hausa
Kuma Muka shigar da su a cikin rahamarMu. Lalle ne, sună daga sălihai.
|
Ayah 21:87 الأية
وَذَا النُّونِ إِذ ذَّهَبَ مُغَاضِبًا فَظَنَّ أَن لَّن نَّقْدِرَ عَلَيْهِ
فَنَادَىٰ فِي الظُّلُمَاتِ أَن لَّا إِلَٰهَ إِلَّا أَنتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي
كُنتُ مِنَ الظَّالِمِينَ
Hausa
Kuma mai kifi a să'ad da ya tafi yană mai hushi, sai ya yi zaton cẽwa ba ză Mu
ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cẽwa, "Băbu abĩn bautăwa făce
Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzălumai."
|
Ayah 21:88 الأية
فَاسْتَجَبْنَا لَهُ وَنَجَّيْنَاهُ مِنَ الْغَمِّ ۚ وَكَذَٰلِكَ نُنجِي
الْمُؤْمِنِينَ
Hausa
Sai Muka karɓa masa kuma Muka tsĩrar da shi daga baƙin ciki. Kamar haka ne Muke
tsĩrarda masu ĩmăni.
|
Ayah 21:89 الأية
وَزَكَرِيَّا إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُ رَبِّ لَا تَذَرْنِي فَرْدًا وَأَنتَ خَيْرُ
الْوَارِثِينَ
Hausa
Kuma da Zakariyya a sa'ad da ya kirăyi Ubangijinsa cẽwa, "Ya Ubangiji! Kada Ka
bar ni makaɗaici alhăli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin măsu gădo."
|
Ayah 21:90 الأية
فَاسْتَجَبْنَا لَهُ وَوَهَبْنَا لَهُ يَحْيَىٰ وَأَصْلَحْنَا لَهُ زَوْجَهُ ۚ
إِنَّهُمْ كَانُوا يُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَيَدْعُونَنَا رَغَبًا وَرَهَبًا
ۖ وَكَانُوا لَنَا خَاشِعِينَ
Hausa
Sai Muka karɓa masa kuma Muka kyautata masa mătarsa. Lalle ne sũ, sun kasance
sună gudun tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri. Kuma sună kiran Mu a kan kwaɗayi da
fargaba. Kuma sun kasance măsu saunar (aikata săɓo) gare Mu.
|
Ayah 21:91 الأية
وَالَّتِي أَحْصَنَتْ فَرْجَهَا فَنَفَخْنَا فِيهَا مِن رُّوحِنَا وَجَعَلْنَاهَا
وَابْنَهَا آيَةً لِّلْعَالَمِينَ
Hausa
Kuma da wadda ta tsare farJinta daga alfăsha. Sai Muka hũra a cikinta daga
rũhinMu. Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ăyă ga dũniya.
|
Ayah 21:92 الأية
إِنَّ هَٰذِهِ أُمَّتُكُمْ أُمَّةً وَاحِدَةً وَأَنَا رَبُّكُمْ فَاعْبُدُونِ
Hausa
Lalle ne wannan ita ce al'ummarku ta zama al'umma guda, kuma Nĩ ne Ubangijinku.
Sai ku bauta Mini.
|
Ayah 21:93 الأية
وَتَقَطَّعُوا أَمْرَهُم بَيْنَهُمْ ۖ كُلٌّ إِلَيْنَا رَاجِعُونَ
Hausa
Kuma suka kakkătse al'amarinsu a tsakaninsu. Dukan Kőwanensu măsu Kőmőwa zuwa
gare Ni
|
Ayah 21:94 الأية
فَمَن يَعْمَلْ مِنَ الصَّالِحَاتِ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَا كُفْرَانَ لِسَعْيِهِ
وَإِنَّا لَهُ كَاتِبُونَ
Hausa
Dőmin wanda ya aikata daga ayyukan kwarai alhăli kuwa yană mai ĩmăni, to, băbu
musu ga aikinsa, kuma Mu Măsu rubũtăwa gare shi ne.
|
Ayah 21:95 الأية
وَحَرَامٌ عَلَىٰ قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَاهَا أَنَّهُمْ لَا يَرْجِعُونَ
Hausa
Kuma hananne ne a kan wata alƙarya da Muka halakar cẽwa lalle sũ, bă su kőmőwa.
|
Ayah 21:96 الأية
حَتَّىٰ إِذَا فُتِحَتْ يَأْجُوجُ وَمَأْجُوجُ وَهُم مِّن كُلِّ حَدَبٍ يَنسِلُونَ
Hausa
Har sa'ad da aka bũde Yăjũju da Măjũju alhăli kuwa sună gaggăwa daga kőwane
tudun ƙasa.
|
Ayah 21:97 الأية
وَاقْتَرَبَ الْوَعْدُ الْحَقُّ فَإِذَا هِيَ شَاخِصَةٌ أَبْصَارُ الَّذِينَ
كَفَرُوا يَا وَيْلَنَا قَدْ كُنَّا فِي غَفْلَةٍ مِّنْ هَٰذَا بَلْ كُنَّا
ظَالِمِينَ
Hausa
Kuma wa'adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gă ta idănun waɗanda suka kăfirta
sună bayyanannu, (sună cẽwa), "Yă kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala
daga wannan! Ă'a, mun kasance dai măsu zălunci!"
|
Ayah 21:98 الأية
إِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنتُمْ لَهَا
وَارِدُونَ
Hausa
(A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin da kuke bautăwa, baicin Allah makămashin
Jahannama ne. Kũ măsu tusgăwa gare ta ne."
|
Ayah 21:99 الأية
لَوْ كَانَ هَٰؤُلَاءِ آلِهَةً مَّا وَرَدُوهَا ۖ وَكُلٌّ فِيهَا خَالِدُونَ
Hausa
Dă waɗannan (abũbuwanbautăwar) sun kasance abũbuwan bautăwar gaskiya ne, dă ba
su tusga mata ba, alhăli kuwa dukansu madawwama a cikinta ne.
|
Ayah 21:100 الأية
لَهُمْ فِيهَا زَفِيرٌ وَهُمْ فِيهَا لَا يَسْمَعُونَ
Hausa
Sună da wata hargőwa a cikinta, alhăli kuwa sũ, a cikinta, bă su saurăren kőme.
|
Ayah 21:101 الأية
إِنَّ الَّذِينَ سَبَقَتْ لَهُم مِّنَّا الْحُسْنَىٰ أُولَٰئِكَ عَنْهَا
مُبْعَدُونَ
Hausa
Lalle ne waɗanda kalmar yabo tă gabăta a garẽ su daga garẽ Mu, waɗannan waɗanda
ake nĩsantarwa daga barinta ne.
|
Ayah 21:102 الأية
لَا يَسْمَعُونَ حَسِيسَهَا ۖ وَهُمْ فِي مَا اشْتَهَتْ أَنفُسُهُمْ خَالِدُونَ
Hausa
Bă su jin sautin mőtsinta alhăli kuwa sũ madawwamăne a cikin abin da răyukansu
suka yi marmarinsa.
|
Ayah 21:103 الأية
لَا يَحْزُنُهُمُ الْفَزَعُ الْأَكْبَرُ وَتَتَلَقَّاهُمُ الْمَلَائِكَةُ هَٰذَا
يَوْمُكُمُ الَّذِي كُنتُمْ تُوعَدُونَ
Hausa
Firgitar nan mafi girma, bă ză ta baƙantă musu rai ba. Kuma mală'iku na yi musu
marăba (sună cẽwa) "Wannan yininku nẽ wanda kuka kasance ană yi muku wa'adi da
shi."
|
Ayah 21:104 الأية
يَوْمَ نَطْوِي السَّمَاءَ كَطَيِّ السِّجِلِّ لِلْكُتُبِ ۚ كَمَا بَدَأْنَا
أَوَّلَ خَلْقٍ نُّعِيدُهُ ۚ وَعْدًا عَلَيْنَا ۚ إِنَّا كُنَّا فَاعِلِينَ
Hausa
A rănar da Muke naɗe săma kamar neɗẽwar takarda ga abũbuwan rubũtăwa kamar yadda
Muka făra a farKon halitta Muke măyar da ita. Wa'adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun
kasance Măsu aikatăwa.
|
Ayah 21:105 الأية
وَلَقَدْ كَتَبْنَا فِي الزَّبُورِ مِن بَعْدِ الذِّكْرِ أَنَّ الْأَرْضَ يَرِثُهَا
عِبَادِيَ الصَّالِحُونَ
Hausa
Kuma lalle haƙĩƙa Mun rubũta a cikin Littăfi baicin Ambato (Lauhul Mahfũz) cẽwa
ƙasă, bayĩNa sălihai, sună gădonta.
|
Ayah 21:106 الأية
إِنَّ فِي هَٰذَا لَبَلَاغًا لِّقَوْمٍ عَابِدِينَ
Hausa
Lalle ne a cikin wannan (Alƙur'ăni), haƙĩƙa, akwai iyarwa (ga maganar da ta
gabăta ga waɗansu mutăne măsu ibăda.
|
Ayah 21:107 الأية
وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِينَ
Hausa
Kuma ba Mu aike ka ba făce dőmin wata rahama ga talikai.
|
Ayah 21:108 الأية
قُلْ إِنَّمَا يُوحَىٰ إِلَيَّ أَنَّمَا إِلَٰهُكُمْ إِلَٰهٌ وَاحِدٌ ۖ فَهَلْ
أَنتُم مُّسْلِمُونَ
Hausa
Ka ce: "Abin sani kawai, ană yin wahayi zuwa gare ni ne, cẽwa, lalle ne, Abin
bautăwarku, Abin bautăwa ne Guda. To shin kũ măsu mĩƙa wuya ne?"
|
Ayah 21:109 الأية
فَإِن تَوَلَّوْا فَقُلْ آذَنتُكُمْ عَلَىٰ سَوَاءٍ ۖ وَإِنْ أَدْرِي أَقَرِيبٌ أَم
بَعِيدٌ مَّا تُوعَدُونَ
Hausa
Sa'an nan idan suka jũya, to, ka ce: "Nă sanar da ku, a kan daidaita, kuma ban
sani ba, shin, abin da ake yi muku wa'adi makusanci ne Kő kuwa manĩsanci?"
|
Ayah 21:110 الأية
إِنَّهُ يَعْلَمُ الْجَهْرَ مِنَ الْقَوْلِ وَيَعْلَمُ مَا تَكْتُمُونَ
Hausa
"Lalle ne Shĩ (Allah) Yană sanin bayyane daga magana, kuma Yană sanin abin da
kuke ɓőyẽwa.
|
Ayah 21:111 الأية
وَإِنْ أَدْرِي لَعَلَّهُ فِتْنَةٌ لَّكُمْ وَمَتَاعٌ إِلَىٰ حِينٍ
Hausa
"Kuma ban sani ba, tsammăninsa ya zama fitina a gare ku, kő kuma don jin dăɗi,
zuwa ga wani ɗan lőkaci."
|
Ayah 21:112 الأية
قَالَ رَبِّ احْكُم بِالْحَقِّ ۗ وَرَبُّنَا الرَّحْمَٰنُ الْمُسْتَعَانُ عَلَىٰ
مَا تَصِفُونَ
Hausa
Ya ce: "Yă Ubangiji! Ka yi hukunci da gaskiya. Kuma Ubangijinmu Mai rahama ne
Wanda ake nẽman taimakonSa a kan abinda kuke siffantăwa."
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|