First Ayah 1 الأية الأوليبِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
قَدْ أَفْلَحَ الْمُؤْمِنُونَ
Hausa
Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ.
|
Ayah 23:2 الأية
الَّذِينَ هُمْ فِي صَلَاتِهِمْ خَاشِعُونَ
Hausa
Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne.
|
Ayah 23:3 الأية
وَالَّذِينَ هُمْ عَنِ اللَّغْوِ مُعْرِضُونَ
Hausa
Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne.
|
Ayah 23:4 الأية
وَالَّذِينَ هُمْ لِلزَّكَاةِ فَاعِلُونَ
Hausa
Kuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne.
|
Ayah 23:5 الأية
وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ
Hausa
Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne.
|
Ayah 23:6 الأية
إِلَّا عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ
مَلُومِينَ
Hausa
Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle
sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne.
|
Ayah 23:7 الأية
فَمَنِ ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُونَ
Hausa
Sabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu
ƙẽtarẽwar haddi.
|
Ayah 23:8 الأية
وَالَّذِينَ هُمْ لِأَمَانَاتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَاعُونَ
Hausa
Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
|
Ayah 23:9 الأية
وَالَّذِينَ هُمْ عَلَىٰ صَلَوَاتِهِمْ يُحَافِظُونَ
Hausa
Kuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarẽwa.
|
Ayah 23:10 الأية
أُولَٰئِكَ هُمُ الْوَارِثُونَ
Hausa
Waɗannan, sũ ne magãda.
|
Ayah 23:11 الأية
الَّذِينَ يَرِثُونَ الْفِرْدَوْسَ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Hausa
Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi, su a cikinta madawwama ne.
|
Ayah 23:12 الأية
وَلَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنسَانَ مِن سُلَالَةٍ مِّن طِينٍ
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga lãka.
|
Ayah 23:13 الأية
ثُمَّ جَعَلْنَاهُ نُطْفَةً فِي قَرَارٍ مَّكِينٍ
Hausa
Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya.
|
Ayah 23:14 الأية
ثُمَّ خَلَقْنَا النُّطْفَةَ عَلَقَةً فَخَلَقْنَا الْعَلَقَةَ مُضْغَةً
فَخَلَقْنَا الْمُضْغَةَ عِظَامًا فَكَسَوْنَا الْعِظَامَ لَحْمًا ثُمَّ
أَنشَأْنَاهُ خَلْقًا آخَرَ ۚ فَتَبَارَكَ اللَّهُ أَحْسَنُ الْخَالِقِينَ
Hausa
Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin
tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da
ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda
haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun mãsu halittawa.
|
Ayah 23:15 الأية
ثُمَّ إِنَّكُم بَعْدَ ذَٰلِكَ لَمَيِّتُونَ
Hausa
Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne.
|
Ayah 23:16 الأية
ثُمَّ إِنَّكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ تُبْعَثُونَ
Hausa
Sa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar ¡iyãma, za a iãyar da ku,
|
Ayah 23:17 الأية
وَلَقَدْ خَلَقْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعَ طَرَائِقَ وَمَا كُنَّا عَنِ الْخَلْقِ
غَافِلِينَ
Hausa
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta, a samanku, hanyõyi bakwai, kuma ba Mu kasance,
daga barin halittar, Mãsu shagala ba.
|
Ayah 23:18 الأية
وَأَنزَلْنَا مِنَ السَّمَاءِ مَاءً بِقَدَرٍ فَأَسْكَنَّاهُ فِي الْأَرْضِ ۖ
وَإِنَّا عَلَىٰ ذَهَابٍ بِهِ لَقَادِرُونَ
Hausa
Muka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado, sa'an nan Muka zaunar da shi a
cikin ƙasa alhãli, lalle ne Mũ, a kan tafiyar da shi, Mãsu iyãwa ne.
|
Ayah 23:19 الأية
فَأَنشَأْنَا لَكُم بِهِ جَنَّاتٍ مِّن نَّخِيلٍ وَأَعْنَابٍ لَّكُمْ فِيهَا
فَوَاكِهُ كَثِيرَةٌ وَمِنْهَا تَأْكُلُونَ
Hausa
Sai Muka ƙãga muku, game da shi (ruwan), gõnaki daga daĩnai da inabõbi, kunã da,
a cikinsu, 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, kuma daga gare su kuke ci.
|
Ayah 23:20 الأية
وَشَجَرَةً تَخْرُجُ مِن طُورِ سَيْنَاءَ تَنبُتُ بِالدُّهْنِ وَصِبْغٍ
لِّلْآكِلِينَ
Hausa
Da wata itãciya, tanã fita daga dũtsin Sainã'a, tanã tsira da man shãfãwa, da
man miya dõmin masu cĩ.
|
Ayah 23:21 الأية
وَإِنَّ لَكُمْ فِي الْأَنْعَامِ لَعِبْرَةً ۖ نُّسْقِيكُم مِّمَّا فِي بُطُونِهَا
وَلَكُمْ فِيهَا مَنَافِعُ كَثِيرَةٌ وَمِنْهَا تَأْكُلُونَ
Hausa
Kuma lalle ne kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'imõmi Munã shãyar da ku daga
abin da yake a cikinsu, kuma kunã da a cikinsu abũbuwan amfãni mãsu yawa, kuma
daga gare su kuke cĩ
|
Ayah 23:22 الأية
وَعَلَيْهَا وَعَلَى الْفُلْكِ تُحْمَلُونَ
Hausa
Kuma a kansu da a kan jirgin ruwa ake ɗaukar ku.
|
Ayah 23:23 الأية
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِ فَقَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ
مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۖ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Hausa
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna!
Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa waninsa. Shin, to, bã za ku yi
taƙawa ba?"
|
Ayah 23:24 الأية
فَقَالَ الْمَلَأُ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن قَوْمِهِ مَا هَٰذَا إِلَّا بَشَرٌ
مِّثْلُكُمْ يُرِيدُ أَن يَتَفَضَّلَ عَلَيْكُمْ وَلَوْ شَاءَ اللَّهُ لَأَنزَلَ
مَلَائِكَةً مَّا سَمِعْنَا بِهَٰذَا فِي آبَائِنَا الْأَوَّلِينَ
Hausa
Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Wannan ba kõwa ba
ne, fãce mutum misãlinku, yanã nufin ya ɗaukaka a kanku. Dã Allah Yã so, lalle
ne dã Yã saukar da Malã'iku, Ba muji (kõme)ba, game da wannan, a cikin ubanninmu
na farko."
|
Ayah 23:25 الأية
إِنْ هُوَ إِلَّا رَجُلٌ بِهِ جِنَّةٌ فَتَرَبَّصُوا بِهِ حَتَّىٰ حِينٍ
Hausa
"Shi bai zamo kõwa ba fãce wani namiji ne, a gare shi akwai hauka, sai ku yi
jinkiri da shi har wani lõkaci."
|
Ayah 23:26 الأية
قَالَ رَبِّ انصُرْنِي بِمَا كَذَّبُونِ
Hausa
Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimakeni sabõda sun ƙaryatani."
|
Ayah 23:27 الأية
فَأَوْحَيْنَا إِلَيْهِ أَنِ اصْنَعِ الْفُلْكَ بِأَعْيُنِنَا وَوَحْيِنَا فَإِذَا
جَاءَ أَمْرُنَا وَفَارَ التَّنُّورُ ۙ فَاسْلُكْ فِيهَا مِن كُلٍّ زَوْجَيْنِ
اثْنَيْنِ وَأَهْلَكَ إِلَّا مَن سَبَقَ عَلَيْهِ الْقَوْلُ مِنْهُمْ ۖ وَلَا
تُخَاطِبْنِي فِي الَّذِينَ ظَلَمُوا ۖ إِنَّهُم مُّغْرَقُونَ
Hausa
Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idonMu, da
wahayinMu. To, idan umuminMu ya jẽ, kuma tandã ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar
a cikinta daga kõme, ma'aura biyu, da iyãlanka, sai wanda Magana ta gabãta a
kansa, daga gare su, kuma kada ka rõƙẽ Ni (sabõda wani) a cikin waɗanda suka yi
zãlunci, lalle ne sũ waɗanda ake nutsarwa ne.
|
Ayah 23:28 الأية
فَإِذَا اسْتَوَيْتَ أَنتَ وَمَن مَّعَكَ عَلَى الْفُلْكِ فَقُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ
الَّذِي نَجَّانَا مِنَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ
Hausa
"Sa'an nan idan ka daidaitu kai da waɗanda ke tãre da kai a kan jirgin, sai ka
ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya tsĩrar damu daga mutãne azzãlumai."
|
Ayah 23:29 الأية
وَقُل رَّبِّ أَنزِلْنِي مُنزَلًا مُّبَارَكًا وَأَنتَ خَيْرُ الْمُنزِلِينَ
Hausa
"Kuma ka ce: 'Ya Ubangijĩna! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne
Mafi alhẽrin mãsu saukarwa.'"
|
Ayah 23:30 الأية
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ وَإِن كُنَّا لَمُبْتَلِينَ
Hausa
Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi, ko da yake Mun kasance, haƙẽƙa' Mãsu
jarrabãwa.
|
Ayah 23:31 الأية
ثُمَّ أَنشَأْنَا مِن بَعْدِهِمْ قَرْنًا آخَرِينَ
Hausa
Sa'an nan kuma Muka ƙãga wani ƙarni na waɗansu dabam daga bãyansu.
|
Ayah 23:32 الأية
فَأَرْسَلْنَا فِيهِمْ رَسُولًا مِّنْهُمْ أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُم مِّنْ
إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۖ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Hausa
Sai Muka aika a cikinsu Manzo daga gare su. "Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani
abin bautãwa, sai Shi. Shin to, bã zã ku yi taƙawa ba?"
|
Ayah 23:33 الأية
وَقَالَ الْمَلَأُ مِن قَوْمِهِ الَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِلِقَاءِ
الْآخِرَةِ وَأَتْرَفْنَاهُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا مَا هَٰذَا إِلَّا بَشَرٌ
مِّثْلُكُمْ يَأْكُلُ مِمَّا تَأْكُلُونَ مِنْهُ وَيَشْرَبُ مِمَّا تَشْرَبُونَ
Hausa
Mashãwarta daga mutãnensa, waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da haɗuwa
da Lãhira, kuma Muka ni'imtar da su a cikin rãyuwar dũniya, suka ce: "Wannan bã
kõwa ba fãce wani mutum ne kamarku, yanã cĩ daga abin da kuke cĩ daga gare shi,
kuma yanã shã daga abin da kuke shã."
|
Ayah 23:34 الأية
وَلَئِنْ أَطَعْتُم بَشَرًا مِّثْلَكُمْ إِنَّكُمْ إِذًا لَّخَاسِرُونَ
Hausa
"Kuma lalle ne idan kun yi ɗã' a ga mutum misãlinku, lalle ne, a lõkacin nan,
haƙĩƙa, kũ mãsu hasãra ne."
|
Ayah 23:35 الأية
أَيَعِدُكُمْ أَنَّكُمْ إِذَا مِتُّمْ وَكُنتُمْ تُرَابًا وَعِظَامًا أَنَّكُم
مُّخْرَجُونَ
Hausa
"Shin, yanã yi muku wa'adin (cẽwa) lalle kũ, idan kun mutu kuma kuka kasance
turɓãya da ɓasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne?"
|
Ayah 23:36 الأية
هَيْهَاتَ هَيْهَاتَ لِمَا تُوعَدُونَ
Hausa
"Faufau faufau ga abin da ake yi muku wa'adi da shi."
|
Ayah 23:37 الأية
إِنْ هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا الدُّنْيَا نَمُوتُ وَنَحْيَا وَمَا نَحْنُ
بِمَبْعُوثِينَ
Hausa
"Rãyuwa ba ta zama ba fãce rãyuwarmu ta dũniya, munã mutuwa kuma munã rãyuwa,
kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."
|
Ayah 23:38 الأية
إِنْ هُوَ إِلَّا رَجُلٌ افْتَرَىٰ عَلَى اللَّهِ كَذِبًا وَمَا نَحْنُ لَهُ
بِمُؤْمِنِينَ
Hausa
"Bai zama kõwa ba fãce namiji, ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma ba mu zama,
sabõda shi, mãsu ĩmãni ba."
|
Ayah 23:39 الأية
قَالَ رَبِّ انصُرْنِي بِمَا كَذَّبُونِ
Hausa
Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni sabõda sun ƙaryatã ni."
|
Ayah 23:40 الأية
قَالَ عَمَّا قَلِيلٍ لَّيُصْبِحُنَّ نَادِمِينَ
Hausa
Ya ce: "Daga abu kaɗan, lalle ne zã su wãyi gari sunã mãsu nadãma."
|
Ayah 23:41 الأية
فَأَخَذَتْهُمُ الصَّيْحَةُ بِالْحَقِّ فَجَعَلْنَاهُمْ غُثَاءً ۚ فَبُعْدًا
لِّلْقَوْمِ الظَّالِمِينَ
Hausa
Sai tsãwa ta kãma su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Sabõda haka nĩsa ya
tabbataga mutãne azzãlumai!
|
Ayah 23:42 الأية
ثُمَّ أَنشَأْنَا مِن بَعْدِهِمْ قُرُونًا آخَرِينَ
Hausa
Sa'an kuma Muka ƙãga halittar wasu ƙarnõni dabam daga bayãnsu.
|
Ayah 23:43 الأية
مَا تَسْبِقُ مِنْ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسْتَأْخِرُونَ
Hausa
Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
|
Ayah 23:44 الأية
ثُمَّ أَرْسَلْنَا رُسُلَنَا تَتْرَىٰ ۖ كُلَّ مَا جَاءَ أُمَّةً رَّسُولُهَا
كَذَّبُوهُ ۚ فَأَتْبَعْنَا بَعْضَهُم بَعْضًا وَجَعَلْنَاهُمْ أَحَادِيثَ ۚ
فَبُعْدًا لِّقَوْمٍ لَّا يُؤْمِنُونَ
Hausa
Sa'an nan kuma Muka aika da ManzanninMu jẽre a kõda yaushe Manzon wata al'umma
ya jẽ mata, sai su ƙaryata shi, sabõda haka Muka biyar da sãshensu ga sãshe,
kuma Muka sanya su lãbãrun hĩra. To, nĩsa ya tabbata ga mutãne (waɗanda) bã su
yin ĩmãni!
|
Ayah 23:45 الأية
ثُمَّ أَرْسَلْنَا مُوسَىٰ وَأَخَاهُ هَارُونَ بِآيَاتِنَا وَسُلْطَانٍ مُّبِينٍ
Hausa
Sa'an nan kuma Muka aika Mũsã da ɗan'uwansa Hãrũna, game da ãyõyinMu da, dalĩli
bayyananne.
|
Ayah 23:46 الأية
إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِ فَاسْتَكْبَرُوا وَكَانُوا قَوْمًا عَالِينَ
Hausa
Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka kangara, alhãli sun kasance mutãne ne
marinjãya.
|
Ayah 23:47 الأية
فَقَالُوا أَنُؤْمِنُ لِبَشَرَيْنِ مِثْلِنَا وَقَوْمُهُمَا لَنَا عَابِدُونَ
Hausa
Sai suka ce: "Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli
kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne."
|
Ayah 23:48 الأية
فَكَذَّبُوهُمَا فَكَانُوا مِنَ الْمُهْلَكِينَ
Hausa
Sai suka ƙaryata su sabõda haka suka kasance halakakku.
|
Ayah 23:49 الأية
وَلَقَدْ آتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ لَعَلَّهُمْ يَهْتَدُونَ
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi tsammaninsu zã su shiryu.
|
Ayah 23:50 الأية
وَجَعَلْنَا ابْنَ مَرْيَمَ وَأُمَّهُ آيَةً وَآوَيْنَاهُمَا إِلَىٰ رَبْوَةٍ ذَاتِ
قَرَارٍ وَمَعِينٍ
Hausa
Kuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã Kuma Muka tattara su zuwa ga
wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari.
|
Ayah 23:51 الأية
يَا أَيُّهَا الرُّسُلُ كُلُوا مِنَ الطَّيِّبَاتِ وَاعْمَلُوا صَالِحًا ۖ إِنِّي
بِمَا تَعْمَلُونَ عَلِيمٌ
Hausa
Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle
Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
|
Ayah 23:52 الأية
وَإِنَّ هَٰذِهِ أُمَّتُكُمْ أُمَّةً وَاحِدَةً وَأَنَا رَبُّكُمْ فَاتَّقُونِ
Hausa
Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai
ku bĩ Ni da taƙawa.
|
Ayah 23:53 الأية
فَتَقَطَّعُوا أَمْرَهُم بَيْنَهُمْ زُبُرًا ۖ كُلُّ حِزْبٍ بِمَا لَدَيْهِمْ
فَرِحُونَ
Hausa
Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu, kõwace
ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su.
|
Ayah 23:54 الأية
فَذَرْهُمْ فِي غَمْرَتِهِمْ حَتَّىٰ حِينٍ
Hausa
To, ka bar su a cikin ɓatarsu har a wani lõkaci.
|
Ayah 23:55 الأية
أَيَحْسَبُونَ أَنَّمَا نُمِدُّهُم بِهِ مِن مَّالٍ وَبَنِينَ
Hausa
Shin, sunã zaton cẽwa abin da Muke taimakon su da shi daga dũkiya da ɗiya,
|
Ayah 23:56 الأية
نُسَارِعُ لَهُمْ فِي الْخَيْرَاتِ ۚ بَل لَّا يَشْعُرُونَ
Hausa
Munã yi musu gaggãwa ne a cikin alhẽrõri?
|
Ayah 23:57 الأية
إِنَّ الَّذِينَ هُم مِّنْ خَشْيَةِ رَبِّهِم مُّشْفِقُونَ
Hausa
Lalle ne waɗanda suke mãsu sauna sabo da tsõron Ubangijinsu,
|
Ayah 23:58 الأية
وَالَّذِينَ هُم بِآيَاتِ رَبِّهِمْ يُؤْمِنُونَ
Hausa
Da waɗanda suke, game da ãyõyin Ubangijinsu sunã ĩmãni,
|
Ayah 23:59 الأية
وَالَّذِينَ هُم بِرَبِّهِمْ لَا يُشْرِكُونَ
Hausa
Da waɗanda suke game da Ubangijinsu bã su yin shirki,
|
Ayah 23:60 الأية
وَالَّذِينَ يُؤْتُونَ مَا آتَوا وَّقُلُوبُهُمْ وَجِلَةٌ أَنَّهُمْ إِلَىٰ
رَبِّهِمْ رَاجِعُونَ
Hausa
Da waɗanda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace
dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu,
|
Ayah 23:61 الأية
أُولَٰئِكَ يُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَهُمْ لَهَا سَابِقُونَ
Hausa
Waɗancan sunã gaggãwar tsẽre a cikin ayyukan alhẽri, alhãli kuwa sunã mãsu
tsẽrẽwa zuwa gare su (ayyukan alhẽri).
|
Ayah 23:62 الأية
وَلَا نُكَلِّفُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا ۖ وَلَدَيْنَا كِتَابٌ يَنطِقُ
بِالْحَقِّ ۚ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ
Hausa
Kuma bã Mu kallafa wa rai fãce abin iyawarsa, kuma a wurinMu akwai wani Littãfi
wanda yake magana da gakiya, kuma sũ bã a zãluntar su.
|
Ayah 23:63 الأية
بَلْ قُلُوبُهُمْ فِي غَمْرَةٍ مِّنْ هَٰذَا وَلَهُمْ أَعْمَالٌ مِّن دُونِ ذَٰلِكَ
هُمْ لَهَا عَامِلُونَ
Hausa
Ã'a, zukãtansu sunã cikin jãhilci daga wannan (magana), kuma sunã da waɗansu
ayyuka, baicin wancan, sũ a gare su,mãsu aikatãwa ne.
|
Ayah 23:64 الأية
حَتَّىٰ إِذَا أَخَذْنَا مُتْرَفِيهِم بِالْعَذَابِ إِذَا هُمْ يَجْأَرُونَ
Hausa
Har idan Mun kãma mani'imtansu da azãba, sai gã su sunã hargõwa.
|
Ayah 23:65 الأية
لَا تَجْأَرُوا الْيَوْمَ ۖ إِنَّكُم مِّنَّا لَا تُنصَرُونَ
Hausa
Kada ku yi hargowa a yau, lalle ne kũ, daga gare Mu bã a taimakon ku.
|
Ayah 23:66 الأية
قَدْ كَانَتْ آيَاتِي تُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ فَكُنتُمْ عَلَىٰ أَعْقَابِكُمْ
تَنكِصُونَ
Hausa
Lalle ne, ãyõyĩNa sun kasance anã karãtun su a kanku, sai kuka kasance, a kan
dugãduganku, kunã kõmãwa bãya.
|
Ayah 23:67 الأية
مُسْتَكْبِرِينَ بِهِ سَامِرًا تَهْجُرُونَ
Hausa
Kunã mãsu girman kai gare shi (Annabi), da hĩrã kunã alfãsha.
|
Ayah 23:68 الأية
أَفَلَمْ يَدَّبَّرُوا الْقَوْلَ أَمْ جَاءَهُم مَّا لَمْ يَأْتِ آبَاءَهُمُ
الْأَوَّلِينَ
Hausa
Shin fa, ba su yi ta'ammalin maganar (Alƙur'ãni) ba, kõ abin da bai jẽ wa
ubanninsu na farko ba ne ya jẽ musu?
|
Ayah 23:69 الأية
أَمْ لَمْ يَعْرِفُوا رَسُولَهُمْ فَهُمْ لَهُ مُنكِرُونَ
Hausa
Kõ ba su san Manzonsu ba ne dõmin haka suke mãsu musu a gare shi?
|
Ayah 23:70 الأية
أَمْ يَقُولُونَ بِهِ جِنَّةٌ ۚ بَلْ جَاءَهُم بِالْحَقِّ وَأَكْثَرُهُمْ لِلْحَقِّ
كَارِهُونَ
Hausa
Kõ sunã cẽwa, "Akwai hauka gare shi?" Ã'a, yã zo musu da gaskiya, alhãli kuwa
mafi yawansu, ga gaskiya, mãsu ƙi ne.
|
Ayah 23:71 الأية
وَلَوِ اتَّبَعَ الْحَقُّ أَهْوَاءَهُمْ لَفَسَدَتِ السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ
وَمَن فِيهِنَّ ۚ بَلْ أَتَيْنَاهُم بِذِكْرِهِمْ فَهُمْ عَن ذِكْرِهِم
مُّعْرِضُونَ
Hausa
Kuma dã gaskiya (Alƙur'ãni) yã bi son zuciyoyinsu, haƙĩƙa dã sammai da ƙasa da
wanda yake a cikinsu sun ɓãci. Ã'a, Mun tafo musu da ambaton (darajar) su, sa'an
nan sũ daga barin ambaton su mãsu bijirẽwa ne, bijirẽwa.
|
Ayah 23:72 الأية
أَمْ تَسْأَلُهُمْ خَرْجًا فَخَرَاجُ رَبِّكَ خَيْرٌ ۖ وَهُوَ خَيْرُ الرَّازِقِينَ
Hausa
Kõ kanã tambayar su wani harãji ne (a kan iyar da Manzanci a gare su)? To,
harãjin Ubangijinka ne mafi alhẽri kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu ciyarwa.
|
Ayah 23:73 الأية
وَإِنَّكَ لَتَدْعُوهُمْ إِلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Hausa
Kuma lalle ne kai haƙĩƙa kanã kiran su zuwa ga hanya madaidaiciya.
|
Ayah 23:74 الأية
وَإِنَّ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ عَنِ الصِّرَاطِ لَنَاكِبُونَ
Hausa
Kuma lalle waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba mãsu karkacẽwa daga hanya ne.
|
Ayah 23:75 الأية
وَلَوْ رَحِمْنَاهُمْ وَكَشَفْنَا مَا بِهِم مِّن ضُرٍّ لَّلَجُّوا فِي
طُغْيَانِهِمْ يَعْمَهُونَ
Hausa
Kuma dã Mun ji tausayinsu, kuma Muka kuranye musu abin da yake tãre da su na
cũta, lalle ne dã sun yi zurfi a cikin ɓatarsu, sunã ɗimuwa.
|
Ayah 23:76 الأية
وَلَقَدْ أَخَذْنَاهُم بِالْعَذَابِ فَمَا اسْتَكَانُوا لِرَبِّهِمْ وَمَا
يَتَضَرَّعُونَ
Hausa
Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã kãma su da azãba sai dai ba su saukar da kai ba, ga
Ubangijinsu, kama bã su yin tawãli'u.
|
Ayah 23:77 الأية
حَتَّىٰ إِذَا فَتَحْنَا عَلَيْهِم بَابًا ذَا عَذَابٍ شَدِيدٍ إِذَا هُمْ فِيهِ
مُبْلِسُونَ
Hausa
Har idan Mun bũɗe, akansu, wata ƙõfa mai azãba mai tsanani sai gã su a cikinta
sunã mãsu mugi.
|
Ayah 23:78 الأية
وَهُوَ الَّذِي أَنشَأَ لَكُمُ السَّمْعَ وَالْأَبْصَارَ وَالْأَفْئِدَةَ ۚ
قَلِيلًا مَّا تَشْكُرُونَ
Hausa
Kuma Shi ne Wanda Ya ƙãga halittar ji da gani da zukãta dominku. Kaɗan ƙwarai
kuke gõdẽwa.
|
Ayah 23:79 الأية
وَهُوَ الَّذِي ذَرَأَكُمْ فِي الْأَرْضِ وَإِلَيْهِ تُحْشَرُونَ
Hausa
Kuma Shĩ ne Ya halitta ku a cikin ƙasa, kuma zuwa gare Shi ake tãyar da ku.
|
Ayah 23:80 الأية
وَهُوَ الَّذِي يُحْيِي وَيُمِيتُ وَلَهُ اخْتِلَافُ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ ۚ
أَفَلَا تَعْقِلُونَ
Hausa
Kuma Shĩ ne Wanda Yake rãyarwa, kuma Yanã matarwa, kuma a gare Shi ne sãɓawar
dare da yini take. Shin, to, bã zã ku hankalta ba?
|
Ayah 23:81 الأية
بَلْ قَالُوا مِثْلَ مَا قَالَ الْأَوَّلُونَ
Hausa
Ã'a, sun faɗi misãlin abin da na farko suka faɗa.
|
Ayah 23:82 الأية
قَالُوا أَإِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَإِنَّا لَمَبْعُوثُونَ
Hausa
Suka ce: "Shin idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasũsuwa shin lal1e ne
mu haƙĩƙa waɗanda ake tãyarwa ne?
|
Ayah 23:83 الأية
لَقَدْ وُعِدْنَا نَحْنُ وَآبَاؤُنَا هَٰذَا مِن قَبْلُ إِنْ هَٰذَا إِلَّا
أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ
Hausa
"Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi, mũ da ubanninmu ga wannan a gabãni, wannan
abu bai zama kõme ba, fãce tãtsũniyõyin na farko."
|
Ayah 23:84 الأية
قُل لِّمَنِ الْأَرْضُ وَمَن فِيهَا إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Hausa
Ka ce: "Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikinta, idan kun kasance kunã
sani?"
|
Ayah 23:85 الأية
سَيَقُولُونَ لِلَّهِ ۚ قُلْ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Hausa
Zã su ce: "Ta Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku yi tunãni ba?"
|
Ayah 23:86 الأية
قُلْ مَن رَّبُّ السَّمَاوَاتِ السَّبْعِ وَرَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ
Hausa
Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al'arshi mai girma?"
|
Ayah 23:87 الأية
سَيَقُولُونَ لِلَّهِ ۚ قُلْ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Hausa
Zã su ce: "Na Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku bĩ Shi da taƙawa ba?"
|
Ayah 23:88 الأية
قُلْ مَن بِيَدِهِ مَلَكُوتُ كُلِّ شَيْءٍ وَهُوَ يُجِيرُ وَلَا يُجَارُ عَلَيْهِ
إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Hausa
Ka ce: "Wãne ne ga hannunsa mallakar kõwane abu take alhãli kuwa shi yanã
tsarẽwar wani, kuma ba a tsare kõwa daga gare shi, idan kun kasance kunã sani?"
|
Ayah 23:89 الأية
سَيَقُولُونَ لِلَّهِ ۚ قُلْ فَأَنَّىٰ تُسْحَرُونَ
Hausa
Zã su ce: "Ga Allah yake." Ka ce: "To, yãya ake sihirce ku?"
|
Ayah 23:90 الأية
بَلْ أَتَيْنَاهُم بِالْحَقِّ وَإِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ
Hausa
Ã'a, Mun zo musu da gaskiya, kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
|
Ayah 23:91 الأية
مَا اتَّخَذَ اللَّهُ مِن وَلَدٍ وَمَا كَانَ مَعَهُ مِنْ إِلَٰهٍ ۚ إِذًا
لَّذَهَبَ كُلُّ إِلَٰهٍ بِمَا خَلَقَ وَلَعَلَا بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ ۚ
سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ
Hausa
Allah bai riƙi wani abin haihuwa ba, kuma bãbu wani abin bautãwa tãre da Shi.
Idan haka ne (akwai abin bautawa tare da Shi), lalle ne dã kõwane abin bautawar
ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, dã waɗansu sun rinjãya a kan
waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantãwa.
|
Ayah 23:92 الأية
عَالِمِ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَتَعَالَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Hausa
Masanin ɓõye da bayyane. sa'an nan Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na
shirka.
|
Ayah 23:93 الأية
قُل رَّبِّ إِمَّا تُرِيَنِّي مَا يُوعَدُونَ
Hausa
Ka ce: "Yã Ubangijina! Ko dai Ka nũna mini abin da ake yi musu wa'adi da shi."
|
Ayah 23:94 الأية
رَبِّ فَلَا تَجْعَلْنِي فِي الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ
Hausa
"Yã Ubangijina, to, kada Ka sanya ni a cikin mutãne azzãlumai."
|
Ayah 23:95 الأية
وَإِنَّا عَلَىٰ أَن نُّرِيَكَ مَا نَعِدُهُمْ لَقَادِرُونَ
Hausa
Kuma lalle ne Mũ haƙĩƙa Mãsu iyawa ne a kan Mu nũna maka abin da Muke yi musu
wa'adi da shi.
|
Ayah 23:96 الأية
ادْفَعْ بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ السَّيِّئَةَ ۚ نَحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَصِفُونَ
Hausa
Ka tunkuɗe cũta da wadda take ita ce mafi kyau. Mũ neMafi sani game da abin da
suke siffantãwa.
|
Ayah 23:97 الأية
وَقُل رَّبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنْ هَمَزَاتِ الشَّيَاطِينِ
Hausa
Ka ce: "Yã Ubangijĩna, inã nẽman tsari da Kai daga fizge-fizgen Shaiɗãnu."
|
Ayah 23:98 الأية
وَأَعُوذُ بِكَ رَبِّ أَن يَحْضُرُونِ
Hausa
"Kuma inã nẽman tsari da Kai, ya Ubangijĩna! Dõmin kada su halarto ni, "
|
Ayah 23:99 الأية
حَتَّىٰ إِذَا جَاءَ أَحَدَهُمُ الْمَوْتُ قَالَ رَبِّ ارْجِعُونِ
Hausa
Har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayansu, sai ya ce: "Yã Ubangijina, Ku mayar da ni
(dũniya)."
|
Ayah 23:100 الأية
لَعَلِّي أَعْمَلُ صَالِحًا فِيمَا تَرَكْتُ ۚ كَلَّا ۚ إِنَّهَا كَلِمَةٌ هُوَ
قَائِلُهَا ۖ وَمِن وَرَائِهِم بَرْزَخٌ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ
Hausa
"Tsammãnina in aikata aiki na ƙwarai cikin abin da na bari." Kayya! Lalle ne ita
kalma ce, shĩ ne mafaɗinta, alhãli kuwa a bãya gare su akwai wani shãmaki har
rãnar da zã a tãyar da su.
|
Ayah 23:101 الأية
فَإِذَا نُفِخَ فِي الصُّورِ فَلَا أَنسَابَ بَيْنَهُمْ يَوْمَئِذٍ وَلَا
يَتَسَاءَلُونَ
Hausa
Sa'an nan idan an yi bũsa a cikin ƙaho, to, bãbu dangantakõki a tsakãninsu a
rãnar nan kuma bã zã su tambayi jũnansu ba.
|
Ayah 23:102 الأية
فَمَن ثَقُلَتْ مَوَازِينُهُ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ
Hausa
To, wadanda sikẽlinsu ya yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
|
Ayah 23:103 الأية
وَمَنْ خَفَّتْ مَوَازِينُهُ فَأُولَٰئِكَ الَّذِينَ خَسِرُوا أَنفُسَهُمْ فِي
جَهَنَّمَ خَالِدُونَ
Hausa
Kuma waɗanda sikẽlinsu ya yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasãrar
rãyukansu sunã madawwama a cikin Jahannama.
|
Ayah 23:104 الأية
تَلْفَحُ وُجُوهَهُمُ النَّارُ وَهُمْ فِيهَا كَالِحُونَ
Hausa
Fuskokinsu sunã balbalar wuta, kuma su a cikinta mãsu yãgaggun leɓɓa daga haƙõra
ne.
|
Ayah 23:105 الأية
أَلَمْ تَكُنْ آيَاتِي تُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ فَكُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ
Hausa
"Shin, ayõyĩNa ba su kasance anã karanta su a kanku ba sai kuka kasance game da
su kunã ƙaryatãwa?"
|
Ayah 23:106 الأية
قَالُوا رَبَّنَا غَلَبَتْ عَلَيْنَا شِقْوَتُنَا وَكُنَّا قَوْمًا ضَالِّينَ
Hausa
Suka ce: "Yã Ubangijinmu, shaƙãwamiu ce ta rinjãya a kanmu, kuma mun kasance
mutãne ɓatattu."
|
Ayah 23:107 الأية
رَبَّنَا أَخْرِجْنَا مِنْهَا فَإِنْ عُدْنَا فَإِنَّا ظَالِمُونَ
Hausa
"Yã Ubangjinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sa'an nan idan mun kõma, to, lalle
ne, mũ ne mãsu zãlunci."
|
Ayah 23:108 الأية
قَالَ اخْسَئُوا فِيهَا وَلَا تُكَلِّمُونِ
Hausa
Ya ce: "Ku tafi (da wulãkanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana."
|
Ayah 23:109 الأية
إِنَّهُ كَانَ فَرِيقٌ مِّنْ عِبَادِي يَقُولُونَ رَبَّنَا آمَنَّا فَاغْفِرْ لَنَا
وَارْحَمْنَا وَأَنتَ خَيْرُ الرَّاحِمِينَ
Hausa
Lalle ne waɗansu ƙungiyoyi daga bãyiNa sun kasance sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu!
Mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi
alhẽrin mãsu tausayi."
|
Ayah 23:110 الأية
فَاتَّخَذْتُمُوهُمْ سِخْرِيًّا حَتَّىٰ أَنسَوْكُمْ ذِكْرِي وَكُنتُم مِّنْهُمْ
تَضْحَكُونَ
Hausa
Sai kuka riƙe su lẽburõri har suka mantar da ku ambatõNa kuma kun kasance, daga
gare su kuke yin dãriya.
|
Ayah 23:111 الأية
إِنِّي جَزَيْتُهُمُ الْيَوْمَ بِمَا صَبَرُوا أَنَّهُمْ هُمُ الْفَائِزُونَ
Hausa
Lalle ne Nĩ Inã sãka musu a yau, sabõda abin da suka yi wa haƙuri. Dõmin lalle
ne sũ sũ ne mãsu sãmun babban rabo.
|
Ayah 23:112 الأية
قَالَ كَمْ لَبِثْتُمْ فِي الْأَرْضِ عَدَدَ سِنِينَ
Hausa
Ya ce: "Nawa kuka zauna a cikin ƙasa na ƙidãyar shẽkaru?"
|
Ayah 23:113 الأية
قَالُوا لَبِثْنَا يَوْمًا أَوْ بَعْضَ يَوْمٍ فَاسْأَلِ الْعَادِّينَ
Hausa
Suka ce: "Mun zauna a yini ɗaya ko rabin yini, sai ka tambayi mãsu ƙidãyãwa."
|
Ayah 23:114 الأية
قَالَ إِن لَّبِثْتُمْ إِلَّا قَلِيلًا ۖ لَّوْ أَنَّكُمْ كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Hausa
Ya ce: "Ba ku zauna ba fãce kaɗan, dã dai kun kasance kunã sani."
|
Ayah 23:115 الأية
أَفَحَسِبْتُمْ أَنَّمَا خَلَقْنَاكُمْ عَبَثًا وَأَنَّكُمْ إِلَيْنَا لَا
تُرْجَعُونَ
Hausa
"Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare
Mu, bã zã ku kõmo ba?"
|
Ayah 23:116 الأية
فَتَعَالَى اللَّهُ الْمَلِكُ الْحَقُّ ۖ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ الْعَرْشِ
الْكَرِيمِ
Hausa
Allah Mamallaki gaskiya, Yã ɗaukaka. Bãbu abin bautãwa, fãce Shi. Shĩ ne
Ubangijin Al'arshi, mai daraja.
|
Ayah 23:117 الأية
وَمَن يَدْعُ مَعَ اللَّهِ إِلَٰهًا آخَرَ لَا بُرْهَانَ لَهُ بِهِ فَإِنَّمَا
حِسَابُهُ عِندَ رَبِّهِ ۚ إِنَّهُ لَا يُفْلِحُ الْكَافِرُونَ
Hausa
Kuma wanda ya kira, tãre da Allah, waɗansu abũbuwan bautãwa na dabam, bã yanã da
wani dalĩli game da shĩ (kiran) ba, to hisãbinsa yanã wurin Ubangijinsa kawai.
Lalle ne, kãfirai bã su cin nasara.
|
|