Mazinãciya da mazinãci, to, ku yi bũlãla ga kõwane ɗaya daga gare su, bũlãla
ɗari. Kuma kada tausayi ya kãma ku game da su a cikin addinin Allah idan kun
kasance kunã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wani yankin jama, a daga
mũminai, su halarci azãbarsu.
Mazinãci bã ya aure fãce da mazinãciya kõ mushirika, kuma mazinãciya bãbu mai
aurenta fãce mazinãci kõ mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan mũminai.
Kuma waɗanda ke jĩfar mãtã masu kãmun kai, sa'an nan kuma ba su jẽ da shaidu
huɗu ba to, ku yi musu bũlãla, bũlãla tamãnin, kuma kada ku karɓi wata shaida
tãsu, har abada. Waɗancan su ne fãsiƙai.
Kuma waɗanda ke jĩfar mãtan aurensu kuma waɗansu shaidu ba su kasance a gare su
ba, fãce dai kansu, to, shaidar ɗayansu, shaida huɗu ce da Allah, 'Lalle shĩ,
haƙĩƙa, yanã daga magasganta.'
Lalle ne waɗanda suka zo da ƙiren ƙarya waɗansu jama'a ne daga gare ku, kada ku
yi zatonsa sharri ne a gare ku. Ã'a, alhẽri ne gare ku. Kõwane mutum daga gare
su na da sakamakon abin da ya sanã'anta na zunubi, kuma wanda ya jiɓinci
girmansa, daga gare su, yanã da azãba mai girma.
Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa a cikin dũniya da Lãhira.
Lalle ne,dã azãba mai girma ta shãfe ku a cikin abin da kuka kũtsa da magana a
cikinsa.
A lõkacin da kuke marãbarsa da harsunanku kuma kunã cẽwa da bakunanku abin da bã
ku da wani ilmi game da shi, kuma kunã zaton sa mai sauƙi alhãli kuwa, shi a
wurin Allah, babba ne.
Kuma don me a lõkacin da kuka ji shi, ba ku ce ba, "Bã ya yiwuwa a gare mu, mu
yi magana a game da wannan. Tsarki ya tabbata a gare Ka, wannan ƙiren ƙarya ne
mai girma"?
Lalle ne waɗanda ke son alfãsha ta wãtsu ga waɗanda suka yi ĩmãni sunã da azãba
mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira. KumaAllah, Shi ne Ya sani, alhãli kuwa, kũ
ba ku sani ba.
Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni, kada ku bi hanyõyin Shaiɗan. Kuma wanda ke bin
hanyõyin Shaiɗan, to, lalle ne shi, yanã umurni da yin alfãsha da abin da ba a
sani ba, kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa, bãbu wani mutum
daga gare ku da zai tsarkaka har abada, kuma amma Allah Yanã tsarkake wanda Yake
so kuma Allah Mai ji ne, Masani.
Kuma kada ma'abũta falala daga gare ku da mawadãta su rantse ga rashin su bãyar
da alhẽri ga ma'abũta zumunta da miskĩnai da muhãjirai, a cikin hanyar Allah.
Kuma su yãfe, kuma su kau da kai. shin, bã ku son Allah Ya gãfarta muku, alhãli
Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai?
Miyãgun mãtã dõmin miyagun maza suke, kuma miyãgun maza dõmin miyãgun mãtã suke
kuma tsarkãkan mãtã dõmin tsarkãkan maza suke kuma tsarkãkan maza dõmin
tsarkãkan mãtã suke. waɗancan sũ ne waɗanda ake barrantãwa daga abin da (mãsu
ƙazafi) suke faɗa kuma sunã da gãfara da arziki na karimci.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku shiga gidãje waɗanda bã gidãjenku ba sai
kun sãmi izni, kuma kun yi sallama a kan ma'abũtansu. Wannan ne mafi alhẽri gare
ku, tsammaninku, zã ku tuna.
To, idan ba ku sãmi kõwa a cikinsu ba, to, kada ku shige su, sai an yi muku
izni. Kuma idan an ce muku, "Ku kõma." Sai ku kõma, shi ne mafi tsarkaka a gare
ku. Kuma Allah game da abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
Bãbu laifi a kanku, ga ku shiga gidãje waɗanda bã zaunannu ba, a cikinsu akwai
waɗansu kãya nãku. Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke nũnãwa, da abin dakuke
ɓãyẽwa.
Ka ce wa mũminai maza su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjõjinsu. wannan
shĩ ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da
suke sanã'antãwa.
Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu
kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka
da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko
ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko
ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kõ mãtan ƙungiyarsu, ko abin da hannãyensu na dãma suka
mallaka, ko mabiya wasun mãsu bukãtar mãta daga maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su
tsinkãya a kan al'aurar mãtã. Kuma kada su yi dũka da ƙafãfunsu dõmin a san abin
da suke ɓõyẽwa daga ƙawarsu.Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai!
Tsammãninku, ku sãmi babban rabo.
Kuma ku aurar da gwaurãye daga gare ku, da sãlihai daga bãyinku, da kuyanginku.
Idan sun kasance matalauta Allah zai wadãtar da su daga falalarSa. Kuma Allah
Mawadãci ne, Masani.
Kuma waɗannan da ba su sãmi aure ba su kãme kansu har Allah Ya wadãtar da su
daga, falalarsa. Kuma waɗanda ke nẽman fansa daga abin da hannuwanku na dãma
suka mallaka, to, ku ɗaura musu fansã idan kun san akwai wani alhẽri a cikinsu
kuma ku bã su wani abu daga dũkiyar Allah wannan da Ya bã ku. Kuma kada ku
tĩlasta kuyanginku a kan yin zina, idan sun yi nufin tsaron kansu, dõmin ku nẽmi
rãyuwar dũniya, kuma wanda ya tĩlasta su to, lalle Allah, a bãyan tĩlasta su,
Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Allah ne Hasken sammai da ƙasa, misãlin HaskenSa, kamar tãgã, a cikinta akwai
fitila, fitilar a cikin ƙarau, ƙarau ɗin kamar shi taurãro ne mai tsananin
haske, anã kunna shi daga wata itãciya mai albarka, ta zaitũni, bã bagabashiya
ba kuma bã bayammaciya ba, manta na kusa ya yi haske, kuma kõ wuta ba ta shãfe
shi ba, haske a kan haske, Allah na shiryar da wanda Yake so zuwa ga HaskenSa.
Kuma Allah na buga misãlai ga mutãne, kuma Allah game da dukan kõme, Masani ne.
Waɗansu maza, waɗanda wani fatauci bã ya shagaltar da su, kuma sayarwa bã ta
shagaltar da su daga ambaton Allah, da tsai da salla da bãyar da zakka, sunã
tsõron wani yini wanda zukãta sunã bibbirkita a cikinsa, da gannai.
Kuma waɗanda suka ƙãfirta ayyukansu sunã kamar ƙawalwalniyã ga faƙo, mai
ƙishirwa yanã zaton sa ruwa, har idan ya jẽ masa bai iske shi kõme ba, kuma ya
sãmi Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisãbinsa. Kuma Allah Mai gaggãwar
sakamako ne.
Kõ kuwa kamar duffai a cikin tẽku mai zurfi, tãguwar ruwa tanã rufe da shi, daga
bisansa akwai wata tãguwa, daga bisansa akwai wani girgije, duffai sãshensu a
bisa sãshe, idan ya fitar da tãfinsa ba ya kusa ya gan shi. Kuma wanda Allah bai
sanya masa haske ba, to, bã ya da wani haske.
Shin, ba ka gani ba (cẽwa) lalle ne Allah, Wanda yake a cikin sammai da ƙasa
sunã yi Masa tasbĩhi, kuma tsuntsaye sunã mãsu sanwa, kõwane lalle ya san
sallarsa da tasbĩhinsa kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa?
Ashe, ba ka ganĩ ba, lalle ne Allah Yanã kõra girgije, sa'an nan kuma Ya haɗa a
tsakãninsa sa'an nan kuma Ya sanya shi mai hauhawar jũna? Sai ka ga ruwa yanã
fita daga tsattsakinsa, kuma Ya saukar daga waɗansu duwãtsu a cikinsa na ƙanƙarã
daga sama, sai ya sãmu wanda Yake so da shi, kuma Ya karkatar da shi daga barin
wanda Yake so. Hasken walƙiyarsa Yanã kusa ya tafi da gannai.
Kuma Allah ne Ya halitta kõwace dabba daga ruwa. To, daga cikinsu akwai waɗanda
ke tafiya a kan cikinsu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan ƙafãfu
biyu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya akan huɗu. Allah Yãna halitta
abin da Yake so, lalle Allah, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne.
Kuma sunã cẽwa, "Mun yi ĩmãni da Allah da kuma Manzo, kuma mun yi ɗã'ã." Sa'an
nan kuma wata ƙungiya daga gare su,su jũya daga bãyan wancan. Kuma waɗancan ba
mũminai ba ne.
Maganar mũminai, idan aka kira su zuwa ga Allah da ManzonSa dõmin Ya yi hukunci
a tsakãninsu takan kasance kawai su ce "Mun ji, kuma mun yi ɗã'ã, Kuma waɗannan
sũ ne mãsu cin nasara."
Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu, 'Lalle ne idan ka umurce su haƙĩƙa
sunã fita.' Ka ce, "Kada ku rantse, ɗã'ã sananna ce! Lalle ne, Allah Mai
ƙididdigewã ne ga abin da kuke aikatãwã."
Ka ce: "Ku yi ɗã'ã ga Allah kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo. To, idan kun jũya, to, a
kansa akwai abin da aka aza masa kawai, kuma a kanku akwai abin da aka aza muku
kawai, Kuma idan kun yi masa ɗã'ã za ku shiryu. Kuma bãbu abin da yake a kan
Manzo fãce iyarwa bayyananna."
Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare. Ku, kuma suka aikata
ayyukan ƙwarai, lalle zai shugabantar da su a cikin ƙasa kamar yadda Ya
shugabantar da waɗanda suke daga gabãninsu, kuma lalle ne zai tabbatar musu da
addininsu wanda Ya yardar musu, kuma lalle ne Yanã musanya musu daga bãyan
tsõronsu da aminci, sunã bauta Mini bã su haɗa kõme da Nĩ. Kuma wanda ya kãfirta
a bãyan wannan, to, waɗancan, su ne fãsiƙai.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Waɗannan da hannuwanku na dãma suka mallaka da
waɗanda ba su isa mafarki ba daga cikinku, su nẽmi izni sau uku; daga gabãnin
sallar alfijir da lõkacin da kuke ajiye tufãfinku sabõda zãfin rãnã, kuma daga
bãyan sallar ishã'i. Sũ ne al'aurõri uku a gare ku. Bãbu laifi a kanku kuma bãbu
a kansu a bãyansu. Sũ mãsu kẽwaya ne a kanku sãshenku a kan sãshe. Kamar wannan
ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa a gare ku. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
Kuma idan yãra daga cikinku suka isa mafarki to su nẽmi izni, kamar yadda
waɗanda suke a gabãninsu suka nẽmi iznin. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana
ãyõyinSa a gare ku, kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
Kuma tsõfaffi daga mãtã, waɗanda bã su fatan wani aure to, bãbu laifi a kansu su
ajiye tufãfinsu, bã sunã mãsu fitar da ƙawa ba, kuma su tsare mutuncinsu shĩ ne
mafi alhẽri a gare su. Kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.
Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan
majiyyaci, kuma bãbu laifi a kan kõwanenku, ga ku ci (abinci) daga gidãjenku, kõ
daga gidãjen ubanninku, kõ daga gidãjen uwãyenku, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku
mazã, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mãtã, kõ daga gidãjen baffanninku, kõ daga
gidãjen gwaggwanninku, kõ daga gidãjen kãwunnanku, kõ daga gidãjen innõninku kõ
abin da kuka mallaki mabũɗansa kõ abõkinku bãbu laifi a gare ku ku ci gabã ɗaya,
kõ dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidãje, ku yi sallama a kan kãwunanku,
gaisuwã ta daga wurin Allah mai albarka, mai dãɗi. Kamar wancan ne Allah Yake
bayyana muku ãyõyinSa, tsammãninku ku yi hankali.
Waɗanda ke mũminai sõsai, su ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, kuma
idan sun kasance tãre da shi, a kan wani al'amari na aikin gayya, bã su tafiya
sai sun nẽme shi izni. Lalle ne, waɗanda suke biɗar ka izni waɗancan sũ ne suke
yin ĩmãni da Allah da ManzonSa. To, idan sun nẽme ka izni sabõda wani
sha'aninsu, to, ka yi izni ga wanda ka so daga gare su, kuma ka nẽmã musu gãfara
daga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai .
Kada ku sanya kiran Manzo a tsakãninku kamar kiran sãshenku ga sãshe. Lalle ne
Allah Yanã sanin waɗanda ke sancẽwa daga cikinku da saɗãɗe. To, waɗanda suke
sãɓãwa daga umurninSa, su yi saunar wata fitina ta sãme su, kõ kuwa wata azãba
mai raɗãɗi ta sãme su.
To! Lalle Allah ne Yake da mulkin abin da ke a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙa,
Yanã sanin abin da kuke a kansa kuma a rãnar da ake mayar da su zuwa gare shi,
sai Yanã bã su lãbãri game da abin da suka aikata. Kuma Allah, ga dukkan kõme,
Masani ne.