« Prev

25. Surah Al-Furqân سورة الفرقان

Next »First Ayah   1   الأية الأولي
بِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
تَبَارَكَ الَّذِي نَزَّلَ الْفُرْقَانَ عَلَىٰ عَبْدِهِ لِيَكُونَ لِلْعَالَمِينَ نَذِيرًا
Hausa
 
Albarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da (Littăfi) mai rarrabẽwa a kan băwanSa, dőmin ya kasance mai gargaɗi ga halitta.

Ayah   25:2   الأية
الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَلَمْ يَتَّخِذْ وَلَدًا وَلَمْ يَكُن لَّهُ شَرِيكٌ فِي الْمُلْكِ وَخَلَقَ كُلَّ شَيْءٍ فَقَدَّرَهُ تَقْدِيرًا
Hausa
 
wanda Yake da mulkin sammai da ƙasa kuma bai riƙi abin haihuwa ba, kuma abőkin tărayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa kuma Ya halitta dukan kowane abu, sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarăwa.

Ayah   25:3   الأية
وَاتَّخَذُوا مِن دُونِهِ آلِهَةً لَّا يَخْلُقُونَ شَيْئًا وَهُمْ يُخْلَقُونَ وَلَا يَمْلِكُونَ لِأَنفُسِهِمْ ضَرًّا وَلَا نَفْعًا وَلَا يَمْلِكُونَ مَوْتًا وَلَا حَيَاةً وَلَا نُشُورًا
Hausa
 
Kuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, bă su yin halittar kőme alhăli sũ ne ake halittăwa kuma bă su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfăni, kuma bă su mallakar mutuwa kuma bă su mallakar răyarwa, kuma bă su mallakar tăyarwa.

Ayah   25:4   الأية
وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا إِنْ هَٰذَا إِلَّا إِفْكٌ افْتَرَاهُ وَأَعَانَهُ عَلَيْهِ قَوْمٌ آخَرُونَ ۖ فَقَدْ جَاءُوا ظُلْمًا وَزُورًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suka kăfirta suka ce: "Wannan bă kőme ba ne făce ƙiron ƙarya da (Muhammadu) ya ƙirƙira shi, kuma waɗansu mutăne na dabam suka taimake shi a kansa." To, lalle ne sun jẽ wa zălunci da karkacẽwar magana.

Ayah   25:5   الأية
وَقَالُوا أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ اكْتَتَبَهَا فَهِيَ تُمْلَىٰ عَلَيْهِ بُكْرَةً وَأَصِيلًا
Hausa
 
Kuma suka ce: "Tatsũniyőyi ne na farko ya rurrbũta, sai sũ ake shibtarsu a gare shi săfe da yamma."

Ayah   25:6   الأية
قُلْ أَنزَلَهُ الَّذِي يَعْلَمُ السِّرَّ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ إِنَّهُ كَانَ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Ka ce: "wanda Yake sanin asĩri a cikin, sammai da ƙasane Ya saukar da shi. Lalle ne shĩ Ya kasance Mai găfara, Mai, jin ƙai."

Ayah   25:7   الأية
وَقَالُوا مَالِ هَٰذَا الرَّسُولِ يَأْكُلُ الطَّعَامَ وَيَمْشِي فِي الْأَسْوَاقِ ۙ لَوْلَا أُنزِلَ إِلَيْهِ مَلَكٌ فَيَكُونَ مَعَهُ نَذِيرًا
Hausa
 
Kuma suka ce: "Mẽne ne ga wannan Manzo, yană cin abinci, kuma yană tafiya a cikin kăsuwanni! Don me ba a saukar da mală'ika zuwa gare shi ba, dőmin ya kasance mai gargaɗi tăre da shi?

Ayah   25:8   الأية
أَوْ يُلْقَىٰ إِلَيْهِ كَنزٌ أَوْ تَكُونُ لَهُ جَنَّةٌ يَأْكُلُ مِنْهَا ۚ وَقَالَ الظَّالِمُونَ إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا رَجُلًا مَّسْحُورًا
Hausa
 
"Kő kuwa a jẽfo wata taska zuwa gare shi, kő kuwa wata gőna ta kasance a gare shi, yană ci daga gare ta?" Kuma azzălumai suka ce: "Bă ku bin kőwa, făce mutum sihirtacce:"

Ayah   25:9   الأية
انظُرْ كَيْفَ ضَرَبُوا لَكَ الْأَمْثَالَ فَضَلُّوا فَلَا يَسْتَطِيعُونَ سَبِيلًا
Hausa
 
Ka dũba yadda suka buga maka misălai sai suka ɓace, dőmin haka bă su iya bin tafarki.

Ayah   25:10   الأية
تَبَارَكَ الَّذِي إِن شَاءَ جَعَلَ لَكَ خَيْرًا مِّن ذَٰلِكَ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ وَيَجْعَل لَّكَ قُصُورًا
Hausa
 
Albarka ta tabbata ga wanda idan Ya so, Yă sanya maka mafi alhẽri daga wannan (abu): gőnaki, ƙőramu na gudăna daga ƙarƙashinsu, kuma Ya sanya maka manyan gidăje.

Ayah   25:11   الأية
بَلْ كَذَّبُوا بِالسَّاعَةِ ۖ وَأَعْتَدْنَا لِمَن كَذَّبَ بِالسَّاعَةِ سَعِيرًا
Hausa
 
Ă'a, sun ƙaryata game da Să'a, alhăli kuwa Mun yi tattalin wuta mai tsanani ga wanda ya ƙaryata (manzanni) game da Sa'a.

Ayah   25:12   الأية
إِذَا رَأَتْهُم مِّن مَّكَانٍ بَعِيدٍ سَمِعُوا لَهَا تَغَيُّظًا وَزَفِيرًا
Hausa
 
Idan ta gan su daga wani wuri mai nĩsa, sai su ji sautin fushi da wani rũri năta.

Ayah   25:13   الأية
وَإِذَا أُلْقُوا مِنْهَا مَكَانًا ضَيِّقًا مُّقَرَّنِينَ دَعَوْا هُنَالِكَ ثُبُورًا
Hausa
 
Kuma idan an jẽfa su a wani wuri mai ƙunci daga gare ta, sună waɗanda aka ɗaure ciki daidai, sai su kirăyi halaka a can.

Ayah   25:14   الأية
لَّا تَدْعُوا الْيَوْمَ ثُبُورًا وَاحِدًا وَادْعُوا ثُبُورًا كَثِيرًا
Hausa
 
Kada ku kirăyi halaka guda, kuma ku kirăyi halaka mai yawa.

Ayah   25:15   الأية
قُلْ أَذَٰلِكَ خَيْرٌ أَمْ جَنَّةُ الْخُلْدِ الَّتِي وُعِدَ الْمُتَّقُونَ ۚ كَانَتْ لَهُمْ جَزَاءً وَمَصِيرًا
Hausa
 
Ka ce: "Shin, wancan ne mafi alhẽri, kő kuwa Aljannar dawwama wadda aka yi wa'adi ga măsu taƙawa? Tă zama, a gare su, sakamako da makőma."

Ayah   25:16   الأية
لَّهُمْ فِيهَا مَا يَشَاءُونَ خَالِدِينَ ۚ كَانَ عَلَىٰ رَبِّكَ وَعْدًا مَّسْئُولًا
Hausa
 
"Sună da abin da suke so, a cikinta sună madawwama. Wannan ya kasance wa'adi abin tambaya a kan Ubangijinka."

Ayah   25:17   الأية
وَيَوْمَ يَحْشُرُهُمْ وَمَا يَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ فَيَقُولُ أَأَنتُمْ أَضْلَلْتُمْ عِبَادِي هَٰؤُلَاءِ أَمْ هُمْ ضَلُّوا السَّبِيلَ
Hausa
 
Kuma rănar da Yake tăra su da abin da suke bauta wa, baicin Allah sai Ya ce: "Shin kũ nekuka ɓatar, da băyiNa, waɗannan, ko kuwa su ne suka ɓata daga hanya?"

Ayah   25:18   الأية
قَالُوا سُبْحَانَكَ مَا كَانَ يَنبَغِي لَنَا أَن نَّتَّخِذَ مِن دُونِكَ مِنْ أَوْلِيَاءَ وَلَٰكِن مَّتَّعْتَهُمْ وَآبَاءَهُمْ حَتَّىٰ نَسُوا الذِّكْرَ وَكَانُوا قَوْمًا بُورًا
Hausa
 
suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka, bă ya kasancẽwa agare mu, mu riƙi waɗansu majiɓinta, baicin Kai, kuma amma Kă jiyar da su dăɗi sũ da ubanninsu har suka manta da Tunătarwa, kuma sun kasance mutăne ne halakakku."

Ayah   25:19   الأية
فَقَدْ كَذَّبُوكُم بِمَا تَقُولُونَ فَمَا تَسْتَطِيعُونَ صَرْفًا وَلَا نَصْرًا ۚ وَمَن يَظْلِم مِّنكُمْ نُذِقْهُ عَذَابًا كَبِيرًا
Hausa
 
To, lalle ne, sun ƙaryata game da abin da kuke cẽwa,sabőda haka bă ku iya karkatarwa ga (maganarsu), kuma ba ku iya taimako (ga hana azăba), kuma wanda ya yi zălunci a cikinku ză Mu ɗanɗana masa azăba mai girma.

Ayah   25:20   الأية
وَمَا أَرْسَلْنَا قَبْلَكَ مِنَ الْمُرْسَلِينَ إِلَّا إِنَّهُمْ لَيَأْكُلُونَ الطَّعَامَ وَيَمْشُونَ فِي الْأَسْوَاقِ ۗ وَجَعَلْنَا بَعْضَكُمْ لِبَعْضٍ فِتْنَةً أَتَصْبِرُونَ ۗ وَكَانَ رَبُّكَ بَصِيرًا
Hausa
 
Kuma ba Mu aika ba, a gabăninka daga Manzanni, făce lalle sũ haƙĩƙa sună cin abinci kuma sună tafiya a cikin kasuwőyi. Kuma Mun sanya săshen mutăne fitina ga săshe. Shin kună yin haƙuri? Kuma Ubangijia Ya kasance Mai gani.

Ayah   25:21   الأية
وَقَالَ الَّذِينَ لَا يَرْجُونَ لِقَاءَنَا لَوْلَا أُنزِلَ عَلَيْنَا الْمَلَائِكَةُ أَوْ نَرَىٰ رَبَّنَا ۗ لَقَدِ اسْتَكْبَرُوا فِي أَنفُسِهِمْ وَعَتَوْا عُتُوًّا كَبِيرًا
Hausa
 
Kuma waɗanda bă su fatan haɗuwa da Mu suka ce: "Don me ba a saukar da mală'ĩku ba a kanmu, kő kuwa mu ga Ubangijinmu?" Lalle ne sun kangara a cikin răyukansu, kuma suka yi tsaurin kai, tsaurin kai mai girma.

Ayah   25:22   الأية
يَوْمَ يَرَوْنَ الْمَلَائِكَةَ لَا بُشْرَىٰ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُجْرِمِينَ وَيَقُولُونَ حِجْرًا مَّحْجُورًا
Hausa
 
A rănar da suke ganin mală'iku băbu bushăra a yinin nan ga măsu laifi kuma sună cẽwa,"Allah Ya kiyăshe mu!"

Ayah   25:23   الأية
وَقَدِمْنَا إِلَىٰ مَا عَمِلُوا مِنْ عَمَلٍ فَجَعَلْنَاهُ هَبَاءً مَّنثُورًا
Hausa
 
Kuma Muka gabăta zuwa ga abin da suka aikata daga aiki, sai Muka sanya shi ƙũra wătsattsiya.

Ayah   25:24   الأية
أَصْحَابُ الْجَنَّةِ يَوْمَئِذٍ خَيْرٌ مُّسْتَقَرًّا وَأَحْسَنُ مَقِيلًا
Hausa
 
Ma'abũta Aljanna a rănar nan sũ ne mafi alhẽri ga matabbata kuma mafi kyaun wurin ƙailũla.

Ayah   25:25   الأية
وَيَوْمَ تَشَقَّقُ السَّمَاءُ بِالْغَمَامِ وَنُزِّلَ الْمَلَائِكَةُ تَنزِيلًا
Hausa
 
Kuma a rănar da sama take tsattsăgewa tăre da gizăgizai, kuma a saukar da mală'iku, saukarwa.

Ayah   25:26   الأية
الْمُلْكُ يَوْمَئِذٍ الْحَقُّ لِلرَّحْمَٰنِ ۚ وَكَانَ يَوْمًا عَلَى الْكَافِرِينَ عَسِيرًا
Hausa
 
Mulki a rănar nan, na gaskiya, yană ga Mai rahama, kuma ya zama yini, a kan kăfirai, mai tsanani.

Ayah   25:27   الأية
وَيَوْمَ يَعَضُّ الظَّالِمُ عَلَىٰ يَدَيْهِ يَقُولُ يَا لَيْتَنِي اتَّخَذْتُ مَعَ الرَّسُولِ سَبِيلًا
Hausa
 
Kuma rănar da azzălumi yake cĩzo a kan hannayensa, yană cẽwa "Ya kaitőna! (A ce dai) na riƙi hanya tăre da Manzo!

Ayah   25:28   الأية
يَا وَيْلَتَىٰ لَيْتَنِي لَمْ أَتَّخِذْ فُلَانًا خَلِيلًا
Hausa
 
"Ya kaitőna! (A ce dai) ban riƙi wăne masőyi ba!

Ayah   25:29   الأية
لَّقَدْ أَضَلَّنِي عَنِ الذِّكْرِ بَعْدَ إِذْ جَاءَنِي ۗ وَكَانَ الشَّيْطَانُ لِلْإِنسَانِ خَذُولًا
Hausa
 
"Lalle ne, haƙĩƙa ya ɓatar da ni daga Tunăwa a băyan (Tunăwar) ta je mini."Kuma Shaiɗan ya zama mai zumɓulẽwa ga mutum.

Ayah   25:30   الأية
وَقَالَ الرَّسُولُ يَا رَبِّ إِنَّ قَوْمِي اتَّخَذُوا هَٰذَا الْقُرْآنَ مَهْجُورًا
Hausa
 
Kuma Manzo ya ce: "Ya Ubangijĩna! Lalle mutănena sun riƙi wannan Alƙur'ăni abin ƙauracẽwa!"

Ayah   25:31   الأية
وَكَذَٰلِكَ جَعَلْنَا لِكُلِّ نَبِيٍّ عَدُوًّا مِّنَ الْمُجْرِمِينَ ۗ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ هَادِيًا وَنَصِيرًا
Hausa
 
Kuma kamar haka ne, Muka sanya maƙiyi daga măsu laifi ga kőwane Annabi. Kuma Ubangijinka Ya isa ga zama Mai Shiryarwa, kuma Mai taimako.

Ayah   25:32   الأية
وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوْلَا نُزِّلَ عَلَيْهِ الْقُرْآنُ جُمْلَةً وَاحِدَةً ۚ كَذَٰلِكَ لِنُثَبِّتَ بِهِ فُؤَادَكَ ۖ وَرَتَّلْنَاهُ تَرْتِيلًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suka kăfirta suka ce: "Don me ba a saukar da Alƙur'ăni a kansa ba, jimla guda?" kamar wancan! Dőmin Mu ƙarfafa zũciyarka game da shi, kuma Mun jẽranta karanta shi da hankali jẽrantawa.

Ayah   25:33   الأية
وَلَا يَأْتُونَكَ بِمَثَلٍ إِلَّا جِئْنَاكَ بِالْحَقِّ وَأَحْسَنَ تَفْسِيرًا
Hausa
 
Kuma bă ză su zo maka da wani misăli ba, făce Mun je maka da gaskiya da mafi kyau ga fassara.

Ayah   25:34   الأية
الَّذِينَ يُحْشَرُونَ عَلَىٰ وُجُوهِهِمْ إِلَىٰ جَهَنَّمَ أُولَٰئِكَ شَرٌّ مَّكَانًا وَأَضَلُّ سَبِيلًا
Hausa
 
Waɗanda ake tăyarwa a kan fuskőkinsu, zuwa ga Jahannama, waɗancan sũ ne mafi sharri ga wuri, kuma mafi ɓacẽwa ga hanya.

Ayah   25:35   الأية
وَلَقَدْ آتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ وَجَعَلْنَا مَعَهُ أَخَاهُ هَارُونَ وَزِيرًا
Hausa
 
Kuma lalle ne, Mun bai wa Mũsă Littăfi, kuma Mun sanya ɗan'uwansa, Hărũna, mataimaki tăre da shi.

Ayah   25:36   الأية
فَقُلْنَا اذْهَبَا إِلَى الْقَوْمِ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا فَدَمَّرْنَاهُمْ تَدْمِيرًا
Hausa
 
Sai Muka ce: "Ku tafi, kũ biyu, zuwa ga mutănen nan waɗanda suka ƙaryata game da ăyő yinMu." sai Muka darkăke su, darkăkewa.

Ayah   25:37   الأية
وَقَوْمَ نُوحٍ لَّمَّا كَذَّبُوا الرُّسُلَ أَغْرَقْنَاهُمْ وَجَعَلْنَاهُمْ لِلنَّاسِ آيَةً ۖ وَأَعْتَدْنَا لِلظَّالِمِينَ عَذَابًا أَلِيمًا
Hausa
 
Kuma mutănen Nũhu, a lőkacin da suka ƙaryata Manzanni, Muka nutsar da su, kuma Muka sanya su wata ăya ga mutăne, kuma Muka yi tattalin azăba mai raɗaɗi ga azzălumai.

Ayah   25:38   الأية
وَعَادًا وَثَمُودَ وَأَصْحَابَ الرَّسِّ وَقُرُونًا بَيْنَ ذَٰلِكَ كَثِيرًا
Hausa
 
Da Ădăwa da Samũdăwa, da mutanen Rassi, da waɗansu al'ummomi, a tsakănin wannan, măsu yawa.

Ayah   25:39   الأية
وَكُلًّا ضَرَبْنَا لَهُ الْأَمْثَالَ ۖ وَكُلًّا تَبَّرْنَا تَتْبِيرًا
Hausa
 
Kuma kőwannensu Mun buga masa misălai, kuma kőwanne Mun halakar da (shi), halakarwa.

Ayah   25:40   الأية
وَلَقَدْ أَتَوْا عَلَى الْقَرْيَةِ الَّتِي أُمْطِرَتْ مَطَرَ السَّوْءِ ۚ أَفَلَمْ يَكُونُوا يَرَوْنَهَا ۚ بَلْ كَانُوا لَا يَرْجُونَ نُشُورًا
Hausa
 
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, (ˇuraishi) sun jẽ a kan alƙaryar nan wadda aka yi wa ruwa, ruwan azăba. Shin, ba su kasance sun gan ta ba? Ă'a, sun kasance bă su ƙaunar tăyarwa (a ˇiyăma).

Ayah   25:41   الأية
وَإِذَا رَأَوْكَ إِن يَتَّخِذُونَكَ إِلَّا هُزُوًا أَهَٰذَا الَّذِي بَعَثَ اللَّهُ رَسُولًا
Hausa
 
Kuma idan sun gan ka, bă su rikon ka făce da izgili, (sună cẽwa) "Shin, wannan ne wanda Allah Ya aiko, Manzo?

Ayah   25:42   الأية
إِن كَادَ لَيُضِلُّنَا عَنْ آلِهَتِنَا لَوْلَا أَن صَبَرْنَا عَلَيْهَا ۚ وَسَوْفَ يَعْلَمُونَ حِينَ يَرَوْنَ الْعَذَابَ مَنْ أَضَلُّ سَبِيلًا
Hausa
 
"Lalle ne, yă yi kusa ya ɓatar da mu daga Ubangijinmu, in bă dőmin da muka yi haƙuri a kansu ba."Kuma ză su sani a lőkacin da suke ganin azăba, wăne ne mafi ɓacẽwa ga hanya!

Ayah   25:43   الأية
أَرَأَيْتَ مَنِ اتَّخَذَ إِلَٰهَهُ هَوَاهُ أَفَأَنتَ تَكُونُ عَلَيْهِ وَكِيلًا
Hausa
 
Shin, kă ga wanda ya riƙi UbangiJinsa son zuciyarsa? shin, to, kai ne ke kasancẽwa mai tsaro a kansa?

Ayah   25:44   الأية
أَمْ تَحْسَبُ أَنَّ أَكْثَرَهُمْ يَسْمَعُونَ أَوْ يَعْقِلُونَ ۚ إِنْ هُمْ إِلَّا كَالْأَنْعَامِ ۖ بَلْ هُمْ أَضَلُّ سَبِيلًا
Hausa
 
Ko kană zaton cẽwa mafi yawansu sună ji, kő kuwa sună hankali? sũ ba su zama ba făce dabbőbin gida suke. Ă'a, sũ ne mafi ɓacẽwa ga hanya.

Ayah   25:45   الأية
أَلَمْ تَرَ إِلَىٰ رَبِّكَ كَيْفَ مَدَّ الظِّلَّ وَلَوْ شَاءَ لَجَعَلَهُ سَاكِنًا ثُمَّ جَعَلْنَا الشَّمْسَ عَلَيْهِ دَلِيلًا
Hausa
 
Ashe, ba ka dũba ba zuwa ga Ubangijinka, yadda Ya miƙe inuwa? Kuma dă Yă so dă Yă bar ta tsaye cif, sa'an nan Muka sanya rănă mai nũni a kanta.

Ayah   25:46   الأية
ثُمَّ قَبَضْنَاهُ إِلَيْنَا قَبْضًا يَسِيرًا
Hausa
 
Sa'an nan Muka karɓe ta (inuwa) zuwa gare Mu, karɓa mai sauƙi.

Ayah   25:47   الأية
وَهُوَ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ اللَّيْلَ لِبَاسًا وَالنَّوْمَ سُبَاتًا وَجَعَلَ النَّهَارَ نُشُورًا
Hausa
 
Kuma shĩ ne wanda Ya sanya muku dare ya zama tũfa da barci ya zama hũtăwa, dă yini ya zama lokacin tăshi (kamar Tashin ˇiyăma).

Ayah   25:48   الأية
وَهُوَ الَّذِي أَرْسَلَ الرِّيَاحَ بُشْرًا بَيْنَ يَدَيْ رَحْمَتِهِ ۚ وَأَنزَلْنَا مِنَ السَّمَاءِ مَاءً طَهُورًا
Hausa
 
Kuma Shi ne Ya aika iskőkin bushăra gaba ga rahamarSa, kuma Muka saukar da ruwa mai tsarkakẽwa daga sama.

Ayah   25:49   الأية
لِّنُحْيِيَ بِهِ بَلْدَةً مَّيْتًا وَنُسْقِيَهُ مِمَّا خَلَقْنَا أَنْعَامًا وَأَنَاسِيَّ كَثِيرًا
Hausa
 
Dőmin Mu răyar, game da shi, gari matacce, kuma Mu shayar da shi dabbőbi da mutăne măsu yawa daga abin da Muka halitta.

Ayah   25:50   الأية
وَلَقَدْ صَرَّفْنَاهُ بَيْنَهُمْ لِيَذَّكَّرُوا فَأَبَىٰ أَكْثَرُ النَّاسِ إِلَّا كُفُورًا
Hausa
 
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sarrafa shi (Alƙur'ăni) a tsakăninsu, dőmin su yi tunăni, sai dai mafi yawan mutănen sun ƙi făce kăfirci.

Ayah   25:51   الأية
وَلَوْ شِئْنَا لَبَعَثْنَا فِي كُلِّ قَرْيَةٍ نَّذِيرًا
Hausa
 
Kuma da Mun so, haƙĩƙa dă Mun aika da mai gargaɗi a ciƙin kőwace alƙarya.

Ayah   25:52   الأية
فَلَا تُطِعِ الْكَافِرِينَ وَجَاهِدْهُم بِهِ جِهَادًا كَبِيرًا
Hausa
 
Sabőda haka kada ka yi ɗă'ă ga kăfirai, ka yăke su, da shi, yăƙi mai girma.

Ayah   25:53   الأية
وَهُوَ الَّذِي مَرَجَ الْبَحْرَيْنِ هَٰذَا عَذْبٌ فُرَاتٌ وَهَٰذَا مِلْحٌ أُجَاجٌ وَجَعَلَ بَيْنَهُمَا بَرْزَخًا وَحِجْرًا مَّحْجُورًا
Hausa
 
Kuma shĩ ne Ya garwaya tẽkuna biyu, wannan mai dădi, mai sauƙin haɗiya, kuma wannan gishiri gurɓatacce, kuma Ya sanya wani shămaki a tsakăninsu da kăriya mai shămakacẽwa.

Ayah   25:54   الأية
وَهُوَ الَّذِي خَلَقَ مِنَ الْمَاءِ بَشَرًا فَجَعَلَهُ نَسَبًا وَصِهْرًا ۗ وَكَانَ رَبُّكَ قَدِيرًا
Hausa
 
Kuma Shi ne Ya halitta mutum daga ruwa, sai Ya sanya shi nasaba da surukuta, kuma Ubangijinka Ya kasance Mai ĩkon yi.

Ayah   25:55   الأية
وَيَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ مَا لَا يَنفَعُهُمْ وَلَا يَضُرُّهُمْ ۗ وَكَانَ الْكَافِرُ عَلَىٰ رَبِّهِ ظَهِيرًا
Hausa
 
Kuma sună bauta wa, baicin Allah, abin da bă ya amfănin su, kuma bă ya cũtar su, kuma kăfiri ya kasance mai taimakon (Shaiɗan) a kan Ubangijinsa.

Ayah   25:56   الأية
وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا مُبَشِّرًا وَنَذِيرًا
Hausa
 
Ba Mu aika ka ba sai kana mai băyar da bushăra, kuma mai gargaɗi.

Ayah   25:57   الأية
قُلْ مَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِلَّا مَن شَاءَ أَن يَتَّخِذَ إِلَىٰ رَبِّهِ سَبِيلًا
Hausa
 
Ka ce: "Bă ni tambayar ku wata ijăra a kansa făce wanda ya so ya riƙi wata hanya zuwa ga Ubangijinsa."

Ayah   25:58   الأية
وَتَوَكَّلْ عَلَى الْحَيِّ الَّذِي لَا يَمُوتُ وَسَبِّحْ بِحَمْدِهِ ۚ وَكَفَىٰ بِهِ بِذُنُوبِ عِبَادِهِ خَبِيرًا
Hausa
 
Kuma ka dőgara a kan Răyayye wanda bă Ya mutuwa, kuma ka yi tasbĩhi game da gőde Masa. Kuma Yă isa zama Mai ƙididdigewa ga laifuffukan băyinSa.

Ayah   25:59   الأية
الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَىٰ عَلَى الْعَرْشِ ۚ الرَّحْمَٰنُ فَاسْأَلْ بِهِ خَبِيرًا
Hausa
 
Wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakăninsu, a cikin kwănuka shida sa'an nan Yă daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai băyar da lăbări game da Shi.

Ayah   25:60   الأية
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ اسْجُدُوا لِلرَّحْمَٰنِ قَالُوا وَمَا الرَّحْمَٰنُ أَنَسْجُدُ لِمَا تَأْمُرُنَا وَزَادَهُمْ نُفُورًا ۩
Hausa
 
Idan aka ce musu, "Ku yi sujada ga Mai rahama." Sai su ce: "Mene ne Mai rahama? Ashe ză mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu?"Kuma wannan (magana ta ƙăra musu gudu.

Ayah   25:61   الأية
تَبَارَكَ الَّذِي جَعَلَ فِي السَّمَاءِ بُرُوجًا وَجَعَلَ فِيهَا سِرَاجًا وَقَمَرًا مُّنِيرًا
Hausa
 
Albarka ta tabbata ga Wanda Ya sanya masaukai (na tafiyar wata) a cikin sama kuma Ya sanya fitila da wată mai haskakewa a cikinta.

Ayah   25:62   الأية
وَهُوَ الَّذِي جَعَلَ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ خِلْفَةً لِّمَنْ أَرَادَ أَن يَذَّكَّرَ أَوْ أَرَادَ شُكُورًا
Hausa
 
Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya dare da yini a kan mayẽwa,ga wanda yake son ya yi tunăni, kő kuwa ya yi nufin ya gőde.

Ayah   25:63   الأية
وَعِبَادُ الرَّحْمَٰنِ الَّذِينَ يَمْشُونَ عَلَى الْأَرْضِ هَوْنًا وَإِذَا خَاطَبَهُمُ الْجَاهِلُونَ قَالُوا سَلَامًا
Hausa
 
Kuma băyin Mai rahama su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan jăhilai sun yi musu magana, sai su ce: "Salăma" (a zama lafiya).

Ayah   25:64   الأية
وَالَّذِينَ يَبِيتُونَ لِرَبِّهِمْ سُجَّدًا وَقِيَامًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suke kwăna sună măsu sujada da tsayi a wurin Ubangijinsu.

Ayah   25:65   الأية
وَالَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا اصْرِفْ عَنَّا عَذَابَ جَهَنَّمَ ۖ إِنَّ عَذَابَهَا كَانَ غَرَامًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suke cẽwa "Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azăbar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azăbarta tă zama tăra

Ayah   25:66   الأية
إِنَّهَا سَاءَتْ مُسْتَقَرًّا وَمُقَامًا
Hausa
 
"Lalle ne ita ta mũnana ta zama wurin tabbata da mazauni."

Ayah   25:67   الأية
وَالَّذِينَ إِذَا أَنفَقُوا لَمْ يُسْرِفُوا وَلَمْ يَقْتُرُوا وَكَانَ بَيْنَ ذَٰلِكَ قَوَامًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bă su yin ɓarna, kuma bă su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakănin wancan da tsakaităwa.

Ayah   25:68   الأية
وَالَّذِينَ لَا يَدْعُونَ مَعَ اللَّهِ إِلَٰهًا آخَرَ وَلَا يَقْتُلُونَ النَّفْسَ الَّتِي حَرَّمَ اللَّهُ إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَا يَزْنُونَ ۚ وَمَن يَفْعَلْ ذَٰلِكَ يَلْقَ أَثَامًا
Hausa
 
Kuma waɗanda bă su kiran wani ubangiji tăre da Allah, kuma bă su kashe rai wanda Allah Ya haramta făce da hakki kuma bă su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka,

Ayah   25:69   الأية
يُضَاعَفْ لَهُ الْعَذَابُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَيَخْلُدْ فِيهِ مُهَانًا
Hausa
 
A riɓanya masa azăba a Rănar ˇiyăma. Kuma ya tabbata a cikinta yană wulakantacce.

Ayah   25:70   الأية
إِلَّا مَن تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ عَمَلًا صَالِحًا فَأُولَٰئِكَ يُبَدِّلُ اللَّهُ سَيِّئَاتِهِمْ حَسَنَاتٍ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmăni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yană musanya miyăgun ayyukansu da măsu kyau. Allah Ya kasance Mai găfara Mai jin ƙai.

Ayah   25:71   الأية
وَمَن تَابَ وَعَمِلَ صَالِحًا فَإِنَّهُ يَتُوبُ إِلَى اللَّهِ مَتَابًا
Hausa
 
Kuma wanda ya tũba, kuma ya aikata aiki mai kyau, to, lalle ne sai ya tũba zuwa gaAllah.

Ayah   25:72   الأية
وَالَّذِينَ لَا يَشْهَدُونَ الزُّورَ وَإِذَا مَرُّوا بِاللَّغْوِ مَرُّوا كِرَامًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suke bă su yin shaidar zur, kuma idan sun shũɗe ga yasassar magana sai su shũɗe suna măsu mutumci.

Ayah   25:73   الأية
وَالَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُوا بِآيَاتِ رَبِّهِمْ لَمْ يَخِرُّوا عَلَيْهَا صُمًّا وَعُمْيَانًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suke idan an tunătar da su da ăyőyin Allah,bă su saukar da kai, sună kurame da makăfi.

Ayah   25:74   الأية
وَالَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا هَبْ لَنَا مِنْ أَزْوَاجِنَا وَذُرِّيَّاتِنَا قُرَّةَ أَعْيُنٍ وَاجْعَلْنَا لِلْمُتَّقِينَ إِمَامًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suke cẽwa "Yă Ubangijinmu! Ka bă mu sanyin idănu daga mătanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya mu shũgabanni ga măsu taƙawa."

Ayah   25:75   الأية
أُولَٰئِكَ يُجْزَوْنَ الْغُرْفَةَ بِمَا صَبَرُوا وَيُلَقَّوْنَ فِيهَا تَحِيَّةً وَسَلَامًا
Hausa
 
Waɗannan ană săka musu da bẽne, sabőda haƙurin da suka yi, kuma a haɗa su, a cikinsa, da gaisuwa da aminci.

Ayah   25:76   الأية
خَالِدِينَ فِيهَا ۚ حَسُنَتْ مُسْتَقَرًّا وَمُقَامًا
Hausa
 
Suna madawwama a cikinsa. Ya yi kyau ga zama matabbaci da mazauni.

Ayah   25:77   الأية
قُلْ مَا يَعْبَأُ بِكُمْ رَبِّي لَوْلَا دُعَاؤُكُمْ ۖ فَقَدْ كَذَّبْتُمْ فَسَوْفَ يَكُونُ لِزَامًا
Hausa
 
Ka ce: "Ubangijĩna ba Ya kula da ku in bă dőmin addu'arku ba. To, lalle ne, kun ƙaryata, sabőda haka al'amarin ză ya zama malizimci."
 


© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us