First Ayah 1 الأية الأولي
بِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
تَبَارَكَ الَّذِي نَزَّلَ الْفُرْقَانَ عَلَىٰ عَبْدِهِ لِيَكُونَ لِلْعَالَمِينَ
نَذِيرًا
Hausa
Albarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da (Littãfi) mai rarrabẽwa a kan bãwanSa,
dõmin ya kasance mai gargaɗi ga halitta.
Ayah 25:2 الأية
الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَلَمْ يَتَّخِذْ وَلَدًا وَلَمْ
يَكُن لَّهُ شَرِيكٌ فِي الْمُلْكِ وَخَلَقَ كُلَّ شَيْءٍ فَقَدَّرَهُ تَقْدِيرًا
Hausa
wanda Yake da mulkin sammai da ƙasa kuma bai riƙi abin haihuwa ba, kuma abõkin
tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa kuma Ya halitta dukan kowane
abu, sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarãwa.
Ayah 25:3 الأية
وَاتَّخَذُوا مِن دُونِهِ آلِهَةً لَّا يَخْلُقُونَ شَيْئًا وَهُمْ يُخْلَقُونَ
وَلَا يَمْلِكُونَ لِأَنفُسِهِمْ ضَرًّا وَلَا نَفْعًا وَلَا يَمْلِكُونَ مَوْتًا
وَلَا حَيَاةً وَلَا نُشُورًا
Hausa
Kuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, bã su yin halittar kõme alhãli sũ
ne ake halittãwa kuma bã su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma bã
su mallakar mutuwa kuma bã su mallakar rãyarwa, kuma bã su mallakar tãyarwa.
Ayah 25:4 الأية
وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا إِنْ هَٰذَا إِلَّا إِفْكٌ افْتَرَاهُ وَأَعَانَهُ
عَلَيْهِ قَوْمٌ آخَرُونَ ۖ فَقَدْ جَاءُوا ظُلْمًا وَزُورًا
Hausa
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Wannan bã kõme ba ne fãce ƙiron ƙarya da
(Muhammadu) ya ƙirƙira shi, kuma waɗansu mutãne na dabam suka taimake shi a
kansa." To, lalle ne sun jẽ wa zãlunci da karkacẽwar magana.
Ayah 25:5 الأية
وَقَالُوا أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ اكْتَتَبَهَا فَهِيَ تُمْلَىٰ عَلَيْهِ
بُكْرَةً وَأَصِيلًا
Hausa
Kuma suka ce: "Tatsũniyõyi ne na farko ya rurrbũta, sai sũ ake shibtarsu a gare
shi sãfe da yamma."
Ayah 25:6 الأية
قُلْ أَنزَلَهُ الَّذِي يَعْلَمُ السِّرَّ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ إِنَّهُ
كَانَ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
Ka ce: "wanda Yake sanin asĩri a cikin, sammai da ƙasane Ya saukar da shi. Lalle
ne shĩ Ya kasance Mai gãfara, Mai, jin ƙai."
Ayah 25:7 الأية
وَقَالُوا مَالِ هَٰذَا الرَّسُولِ يَأْكُلُ الطَّعَامَ وَيَمْشِي فِي الْأَسْوَاقِ
ۙ لَوْلَا أُنزِلَ إِلَيْهِ مَلَكٌ فَيَكُونَ مَعَهُ نَذِيرًا
Hausa
Kuma suka ce: "Mẽne ne ga wannan Manzo, yanã cin abinci, kuma yanã tafiya a
cikin kãsuwanni! Don me ba a saukar da malã'ika zuwa gare shi ba, dõmin ya
kasance mai gargaɗi tãre da shi?
Ayah 25:8 الأية
أَوْ يُلْقَىٰ إِلَيْهِ كَنزٌ أَوْ تَكُونُ لَهُ جَنَّةٌ يَأْكُلُ مِنْهَا ۚ
وَقَالَ الظَّالِمُونَ إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا رَجُلًا مَّسْحُورًا
Hausa
"Kõ kuwa a jẽfo wata taska zuwa gare shi, kõ kuwa wata gõna ta kasance a gare
shi, yanã ci daga gare ta?" Kuma azzãlumai suka ce: "Bã ku bin kõwa, fãce mutum
sihirtacce:"
Ayah 25:9 الأية
انظُرْ كَيْفَ ضَرَبُوا لَكَ الْأَمْثَالَ فَضَلُّوا فَلَا يَسْتَطِيعُونَ سَبِيلًا
Hausa
Ka dũba yadda suka buga maka misãlai sai suka ɓace, dõmin haka bã su iya bin
tafarki.
Ayah 25:10 الأية
تَبَارَكَ الَّذِي إِن شَاءَ جَعَلَ لَكَ خَيْرًا مِّن ذَٰلِكَ جَنَّاتٍ تَجْرِي
مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ وَيَجْعَل لَّكَ قُصُورًا
Hausa
Albarka ta tabbata ga wanda idan Ya so, Yã sanya maka mafi alhẽri daga wannan
(abu): gõnaki, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma Ya sanya maka manyan
gidãje.
Ayah 25:11 الأية
بَلْ كَذَّبُوا بِالسَّاعَةِ ۖ وَأَعْتَدْنَا لِمَن كَذَّبَ بِالسَّاعَةِ سَعِيرًا
Hausa
Ã'a, sun ƙaryata game da Sã'a, alhãli kuwa Mun yi tattalin wuta mai tsanani ga
wanda ya ƙaryata (manzanni) game da Sa'a.
Ayah 25:12 الأية
إِذَا رَأَتْهُم مِّن مَّكَانٍ بَعِيدٍ سَمِعُوا لَهَا تَغَيُّظًا وَزَفِيرًا
Hausa
Idan ta gan su daga wani wuri mai nĩsa, sai su ji sautin fushi da wani rũri
nãta.
Ayah 25:13 الأية
وَإِذَا أُلْقُوا مِنْهَا مَكَانًا ضَيِّقًا مُّقَرَّنِينَ دَعَوْا هُنَالِكَ
ثُبُورًا
Hausa
Kuma idan an jẽfa su a wani wuri mai ƙunci daga gare ta, sunã waɗanda aka ɗaure
ciki daidai, sai su kirãyi halaka a can.
Ayah 25:14 الأية
لَّا تَدْعُوا الْيَوْمَ ثُبُورًا وَاحِدًا وَادْعُوا ثُبُورًا كَثِيرًا
Hausa
Kada ku kirãyi halaka guda, kuma ku kirãyi halaka mai yawa.
Ayah 25:15 الأية
قُلْ أَذَٰلِكَ خَيْرٌ أَمْ جَنَّةُ الْخُلْدِ الَّتِي وُعِدَ الْمُتَّقُونَ ۚ
كَانَتْ لَهُمْ جَزَاءً وَمَصِيرًا
Hausa
Ka ce: "Shin, wancan ne mafi alhẽri, kõ kuwa Aljannar dawwama wadda aka yi
wa'adi ga mãsu taƙawa? Tã zama, a gare su, sakamako da makõma."
Ayah 25:16 الأية
لَّهُمْ فِيهَا مَا يَشَاءُونَ خَالِدِينَ ۚ كَانَ عَلَىٰ رَبِّكَ وَعْدًا
مَّسْئُولًا
Hausa
"Sunã da abin da suke so, a cikinta sunã madawwama. Wannan ya kasance wa'adi
abin tambaya a kan Ubangijinka."
Ayah 25:17 الأية
وَيَوْمَ يَحْشُرُهُمْ وَمَا يَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ فَيَقُولُ أَأَنتُمْ
أَضْلَلْتُمْ عِبَادِي هَٰؤُلَاءِ أَمْ هُمْ ضَلُّوا السَّبِيلَ
Hausa
Kuma rãnar da Yake tãra su da abin da suke bauta wa, baicin Allah sai Ya ce:
"Shin kũ nekuka ɓatar, da bãyiNa, waɗannan, ko kuwa su ne suka ɓata daga hanya?"
Ayah 25:18 الأية
قَالُوا سُبْحَانَكَ مَا كَانَ يَنبَغِي لَنَا أَن نَّتَّخِذَ مِن دُونِكَ مِنْ
أَوْلِيَاءَ وَلَٰكِن مَّتَّعْتَهُمْ وَآبَاءَهُمْ حَتَّىٰ نَسُوا الذِّكْرَ
وَكَانُوا قَوْمًا بُورًا
Hausa
suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka, bã ya kasancẽwa agare mu, mu riƙi waɗansu
majiɓinta, baicin Kai, kuma amma Kã jiyar da su dãɗi sũ da ubanninsu har suka
manta da Tunãtarwa, kuma sun kasance mutãne ne halakakku."
Ayah 25:19 الأية
فَقَدْ كَذَّبُوكُم بِمَا تَقُولُونَ فَمَا تَسْتَطِيعُونَ صَرْفًا وَلَا نَصْرًا ۚ
وَمَن يَظْلِم مِّنكُمْ نُذِقْهُ عَذَابًا كَبِيرًا
Hausa
To, lalle ne, sun ƙaryata game da abin da kuke cẽwa,sabõda haka bã ku iya
karkatarwa ga (maganarsu), kuma ba ku iya taimako (ga hana azãba), kuma wanda ya
yi zãlunci a cikinku zã Mu ɗanɗana masa azãba mai girma.
Ayah 25:20 الأية
وَمَا أَرْسَلْنَا قَبْلَكَ مِنَ الْمُرْسَلِينَ إِلَّا إِنَّهُمْ لَيَأْكُلُونَ
الطَّعَامَ وَيَمْشُونَ فِي الْأَسْوَاقِ ۗ وَجَعَلْنَا بَعْضَكُمْ لِبَعْضٍ
فِتْنَةً أَتَصْبِرُونَ ۗ وَكَانَ رَبُّكَ بَصِيرًا
Hausa
Kuma ba Mu aika ba, a gabãninka daga Manzanni, fãce lalle sũ haƙĩƙa sunã cin
abinci kuma sunã tafiya a cikin kasuwõyi. Kuma Mun sanya sãshen mutãne fitina ga
sãshe. Shin kunã yin haƙuri? Kuma Ubangijia Ya kasance Mai gani.
Ayah 25:21 الأية
وَقَالَ الَّذِينَ لَا يَرْجُونَ لِقَاءَنَا لَوْلَا أُنزِلَ عَلَيْنَا
الْمَلَائِكَةُ أَوْ نَرَىٰ رَبَّنَا ۗ لَقَدِ اسْتَكْبَرُوا فِي أَنفُسِهِمْ
وَعَتَوْا عُتُوًّا كَبِيرًا
Hausa
Kuma waɗanda bã su fatan haɗuwa da Mu suka ce: "Don me ba a saukar da malã'ĩku
ba a kanmu, kõ kuwa mu ga Ubangijinmu?" Lalle ne sun kangara a cikin rãyukansu,
kuma suka yi tsaurin kai, tsaurin kai mai girma.
Ayah 25:22 الأية
يَوْمَ يَرَوْنَ الْمَلَائِكَةَ لَا بُشْرَىٰ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُجْرِمِينَ
وَيَقُولُونَ حِجْرًا مَّحْجُورًا
Hausa
A rãnar da suke ganin malã'iku bãbu bushãra a yinin nan ga mãsu laifi kuma sunã
cẽwa,"Allah Ya kiyãshe mu!"
Ayah 25:23 الأية
وَقَدِمْنَا إِلَىٰ مَا عَمِلُوا مِنْ عَمَلٍ فَجَعَلْنَاهُ هَبَاءً مَّنثُورًا
Hausa
Kuma Muka gabãta zuwa ga abin da suka aikata daga aiki, sai Muka sanya shi ƙũra
wãtsattsiya.
Ayah 25:24 الأية
أَصْحَابُ الْجَنَّةِ يَوْمَئِذٍ خَيْرٌ مُّسْتَقَرًّا وَأَحْسَنُ مَقِيلًا
Hausa
Ma'abũta Aljanna a rãnar nan sũ ne mafi alhẽri ga matabbata kuma mafi kyaun
wurin ƙailũla.
Ayah 25:25 الأية
وَيَوْمَ تَشَقَّقُ السَّمَاءُ بِالْغَمَامِ وَنُزِّلَ الْمَلَائِكَةُ تَنزِيلًا
Hausa
Kuma a rãnar da sama take tsattsãgewa tãre da gizãgizai, kuma a saukar da
malã'iku, saukarwa.
Ayah 25:26 الأية
الْمُلْكُ يَوْمَئِذٍ الْحَقُّ لِلرَّحْمَٰنِ ۚ وَكَانَ يَوْمًا عَلَى
الْكَافِرِينَ عَسِيرًا
Hausa
Mulki a rãnar nan, na gaskiya, yanã ga Mai rahama, kuma ya zama yini, a kan
kãfirai, mai tsanani.
Ayah 25:27 الأية
وَيَوْمَ يَعَضُّ الظَّالِمُ عَلَىٰ يَدَيْهِ يَقُولُ يَا لَيْتَنِي اتَّخَذْتُ
مَعَ الرَّسُولِ سَبِيلًا
Hausa
Kuma rãnar da azzãlumi yake cĩzo a kan hannayensa, yanã cẽwa "Ya kaitõna! (A ce
dai) na riƙi hanya tãre da Manzo!
Ayah 25:28 الأية
يَا وَيْلَتَىٰ لَيْتَنِي لَمْ أَتَّخِذْ فُلَانًا خَلِيلًا
Hausa
"Ya kaitõna! (A ce dai) ban riƙi wãne masõyi ba!
Ayah 25:29 الأية
لَّقَدْ أَضَلَّنِي عَنِ الذِّكْرِ بَعْدَ إِذْ جَاءَنِي ۗ وَكَانَ الشَّيْطَانُ
لِلْإِنسَانِ خَذُولًا
Hausa
"Lalle ne, haƙĩƙa ya ɓatar da ni daga Tunãwa a bãyan (Tunãwar) ta je mini."Kuma
Shaiɗan ya zama mai zumɓulẽwa ga mutum.
Ayah 25:30 الأية
وَقَالَ الرَّسُولُ يَا رَبِّ إِنَّ قَوْمِي اتَّخَذُوا هَٰذَا الْقُرْآنَ
مَهْجُورًا
Hausa
Kuma Manzo ya ce: "Ya Ubangijĩna! Lalle mutãnena sun riƙi wannan Alƙur'ãni abin
ƙauracẽwa!"
Ayah 25:31 الأية
وَكَذَٰلِكَ جَعَلْنَا لِكُلِّ نَبِيٍّ عَدُوًّا مِّنَ الْمُجْرِمِينَ ۗ وَكَفَىٰ
بِرَبِّكَ هَادِيًا وَنَصِيرًا
Hausa
Kuma kamar haka ne, Muka sanya maƙiyi daga mãsu laifi ga kõwane Annabi. Kuma
Ubangijinka Ya isa ga zama Mai Shiryarwa, kuma Mai taimako.
Ayah 25:32 الأية
وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوْلَا نُزِّلَ عَلَيْهِ الْقُرْآنُ جُمْلَةً
وَاحِدَةً ۚ كَذَٰلِكَ لِنُثَبِّتَ بِهِ فُؤَادَكَ ۖ وَرَتَّلْنَاهُ تَرْتِيلًا
Hausa
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Don me ba a saukar da Alƙur'ãni a kansa ba,
jimla guda?" kamar wancan! Dõmin Mu ƙarfafa zũciyarka game da shi, kuma Mun
jẽranta karanta shi da hankali jẽrantawa.
Ayah 25:33 الأية
وَلَا يَأْتُونَكَ بِمَثَلٍ إِلَّا جِئْنَاكَ بِالْحَقِّ وَأَحْسَنَ تَفْسِيرًا
Hausa
Kuma bã zã su zo maka da wani misãli ba, fãce Mun je maka da gaskiya da mafi
kyau ga fassara.
Ayah 25:34 الأية
الَّذِينَ يُحْشَرُونَ عَلَىٰ وُجُوهِهِمْ إِلَىٰ جَهَنَّمَ أُولَٰئِكَ شَرٌّ
مَّكَانًا وَأَضَلُّ سَبِيلًا
Hausa
Waɗanda ake tãyarwa a kan fuskõkinsu, zuwa ga Jahannama, waɗancan sũ ne mafi
sharri ga wuri, kuma mafi ɓacẽwa ga hanya.
Ayah 25:35 الأية
وَلَقَدْ آتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ وَجَعَلْنَا مَعَهُ أَخَاهُ هَارُونَ وَزِيرًا
Hausa
Kuma lalle ne, Mun bai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun sanya ɗan'uwansa, Hãrũna,
mataimaki tãre da shi.
Ayah 25:36 الأية
فَقُلْنَا اذْهَبَا إِلَى الْقَوْمِ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا
فَدَمَّرْنَاهُمْ تَدْمِيرًا
Hausa
Sai Muka ce: "Ku tafi, kũ biyu, zuwa ga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata game da
ãyõ yinMu." sai Muka darkãke su, darkãkewa.
Ayah 25:37 الأية
وَقَوْمَ نُوحٍ لَّمَّا كَذَّبُوا الرُّسُلَ أَغْرَقْنَاهُمْ وَجَعَلْنَاهُمْ
لِلنَّاسِ آيَةً ۖ وَأَعْتَدْنَا لِلظَّالِمِينَ عَذَابًا أَلِيمًا
Hausa
Kuma mutãnen Nũhu, a lõkacin da suka ƙaryata Manzanni, Muka nutsar da su, kuma
Muka sanya su wata ãya ga mutãne, kuma Muka yi tattalin azãba mai raɗaɗi ga
azzãlumai.
Ayah 25:38 الأية
وَعَادًا وَثَمُودَ وَأَصْحَابَ الرَّسِّ وَقُرُونًا بَيْنَ ذَٰلِكَ كَثِيرًا
Hausa
Da Ãdãwa da Samũdãwa, da mutanen Rassi, da waɗansu al'ummomi, a tsakãnin wannan,
mãsu yawa.
Ayah 25:39 الأية
وَكُلًّا ضَرَبْنَا لَهُ الْأَمْثَالَ ۖ وَكُلًّا تَبَّرْنَا تَتْبِيرًا
Hausa
Kuma kõwannensu Mun buga masa misãlai, kuma kõwanne Mun halakar da (shi),
halakarwa.
Ayah 25:40 الأية
وَلَقَدْ أَتَوْا عَلَى الْقَرْيَةِ الَّتِي أُمْطِرَتْ مَطَرَ السَّوْءِ ۚ
أَفَلَمْ يَكُونُوا يَرَوْنَهَا ۚ بَلْ كَانُوا لَا يَرْجُونَ نُشُورًا
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, (¡uraishi) sun jẽ a kan alƙaryar nan wadda aka yi wa
ruwa, ruwan azãba. Shin, ba su kasance sun gan ta ba? Ã'a, sun kasance bã su
ƙaunar tãyarwa (a ¡iyãma).
Ayah 25:41 الأية
وَإِذَا رَأَوْكَ إِن يَتَّخِذُونَكَ إِلَّا هُزُوًا أَهَٰذَا الَّذِي بَعَثَ
اللَّهُ رَسُولًا
Hausa
Kuma idan sun gan ka, bã su rikon ka fãce da izgili, (sunã cẽwa) "Shin, wannan
ne wanda Allah Ya aiko, Manzo?
Ayah 25:42 الأية
إِن كَادَ لَيُضِلُّنَا عَنْ آلِهَتِنَا لَوْلَا أَن صَبَرْنَا عَلَيْهَا ۚ
وَسَوْفَ يَعْلَمُونَ حِينَ يَرَوْنَ الْعَذَابَ مَنْ أَضَلُّ سَبِيلًا
Hausa
"Lalle ne, yã yi kusa ya ɓatar da mu daga Ubangijinmu, in bã dõmin da muka yi
haƙuri a kansu ba."Kuma zã su sani a lõkacin da suke ganin azãba, wãne ne mafi
ɓacẽwa ga hanya!
Ayah 25:43 الأية
أَرَأَيْتَ مَنِ اتَّخَذَ إِلَٰهَهُ هَوَاهُ أَفَأَنتَ تَكُونُ عَلَيْهِ وَكِيلًا
Hausa
Shin, kã ga wanda ya riƙi UbangiJinsa son zuciyarsa? shin, to, kai ne ke
kasancẽwa mai tsaro a kansa?
Ayah 25:44 الأية
أَمْ تَحْسَبُ أَنَّ أَكْثَرَهُمْ يَسْمَعُونَ أَوْ يَعْقِلُونَ ۚ إِنْ هُمْ إِلَّا
كَالْأَنْعَامِ ۖ بَلْ هُمْ أَضَلُّ سَبِيلًا
Hausa
Ko kanã zaton cẽwa mafi yawansu sunã ji, kõ kuwa sunã hankali? sũ ba su zama ba
fãce dabbõbin gida suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa ga hanya.
Ayah 25:45 الأية
أَلَمْ تَرَ إِلَىٰ رَبِّكَ كَيْفَ مَدَّ الظِّلَّ وَلَوْ شَاءَ لَجَعَلَهُ
سَاكِنًا ثُمَّ جَعَلْنَا الشَّمْسَ عَلَيْهِ دَلِيلًا
Hausa
Ashe, ba ka dũba ba zuwa ga Ubangijinka, yadda Ya miƙe inuwa? Kuma dã Yã so dã
Yã bar ta tsaye cif, sa'an nan Muka sanya rãnã mai nũni a kanta.
Ayah 25:46 الأية
ثُمَّ قَبَضْنَاهُ إِلَيْنَا قَبْضًا يَسِيرًا
Hausa
Sa'an nan Muka karɓe ta (inuwa) zuwa gare Mu, karɓa mai sauƙi.
Ayah 25:47 الأية
وَهُوَ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ اللَّيْلَ لِبَاسًا وَالنَّوْمَ سُبَاتًا وَجَعَلَ
النَّهَارَ نُشُورًا
Hausa
Kuma shĩ ne wanda Ya sanya muku dare ya zama tũfa da barci ya zama hũtãwa, dã
yini ya zama lokacin tãshi (kamar Tashin ¡iyãma).
Ayah 25:48 الأية
وَهُوَ الَّذِي أَرْسَلَ الرِّيَاحَ بُشْرًا بَيْنَ يَدَيْ رَحْمَتِهِ ۚ
وَأَنزَلْنَا مِنَ السَّمَاءِ مَاءً طَهُورًا
Hausa
Kuma Shi ne Ya aika iskõkin bushãra gaba ga rahamarSa, kuma Muka saukar da ruwa
mai tsarkakẽwa daga sama.
Ayah 25:49 الأية
لِّنُحْيِيَ بِهِ بَلْدَةً مَّيْتًا وَنُسْقِيَهُ مِمَّا خَلَقْنَا أَنْعَامًا
وَأَنَاسِيَّ كَثِيرًا
Hausa
Dõmin Mu rãyar, game da shi, gari matacce, kuma Mu shayar da shi dabbõbi da
mutãne mãsu yawa daga abin da Muka halitta.
Ayah 25:50 الأية
وَلَقَدْ صَرَّفْنَاهُ بَيْنَهُمْ لِيَذَّكَّرُوا فَأَبَىٰ أَكْثَرُ النَّاسِ
إِلَّا كُفُورًا
Hausa
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sarrafa shi (Alƙur'ãni) a tsakãninsu, dõmin su yi
tunãni, sai dai mafi yawan mutãnen sun ƙi fãce kãfirci.
Ayah 25:51 الأية
وَلَوْ شِئْنَا لَبَعَثْنَا فِي كُلِّ قَرْيَةٍ نَّذِيرًا
Hausa
Kuma da Mun so, haƙĩƙa dã Mun aika da mai gargaɗi a ciƙin kõwace alƙarya.
Ayah 25:52 الأية
فَلَا تُطِعِ الْكَافِرِينَ وَجَاهِدْهُم بِهِ جِهَادًا كَبِيرًا
Hausa
Sabõda haka kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai, ka yãke su, da shi, yãƙi mai girma.
Ayah 25:53 الأية
وَهُوَ الَّذِي مَرَجَ الْبَحْرَيْنِ هَٰذَا عَذْبٌ فُرَاتٌ وَهَٰذَا مِلْحٌ
أُجَاجٌ وَجَعَلَ بَيْنَهُمَا بَرْزَخًا وَحِجْرًا مَّحْجُورًا
Hausa
Kuma shĩ ne Ya garwaya tẽkuna biyu, wannan mai dãdi, mai sauƙin haɗiya, kuma
wannan gishiri gurɓatacce, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãninsu da kãriya mai
shãmakacẽwa.
Ayah 25:54 الأية
وَهُوَ الَّذِي خَلَقَ مِنَ الْمَاءِ بَشَرًا فَجَعَلَهُ نَسَبًا وَصِهْرًا ۗ
وَكَانَ رَبُّكَ قَدِيرًا
Hausa
Kuma Shi ne Ya halitta mutum daga ruwa, sai Ya sanya shi nasaba da surukuta,
kuma Ubangijinka Ya kasance Mai ĩkon yi.
Ayah 25:55 الأية
وَيَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ مَا لَا يَنفَعُهُمْ وَلَا يَضُرُّهُمْ ۗ وَكَانَ
الْكَافِرُ عَلَىٰ رَبِّهِ ظَهِيرًا
Hausa
Kuma sunã bauta wa, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin su, kuma bã ya cũtar su,
kuma kãfiri ya kasance mai taimakon (Shaiɗan) a kan Ubangijinsa.
Ayah 25:56 الأية
وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا مُبَشِّرًا وَنَذِيرًا
Hausa
Ba Mu aika ka ba sai kana mai bãyar da bushãra, kuma mai gargaɗi.
Ayah 25:57 الأية
قُلْ مَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِلَّا مَن شَاءَ أَن يَتَّخِذَ إِلَىٰ
رَبِّهِ سَبِيلًا
Hausa
Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa fãce wanda ya so ya riƙi wata hanya
zuwa ga Ubangijinsa."
Ayah 25:58 الأية
وَتَوَكَّلْ عَلَى الْحَيِّ الَّذِي لَا يَمُوتُ وَسَبِّحْ بِحَمْدِهِ ۚ وَكَفَىٰ
بِهِ بِذُنُوبِ عِبَادِهِ خَبِيرًا
Hausa
Kuma ka dõgara a kan Rãyayye wanda bã Ya mutuwa, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde
Masa. Kuma Yã isa zama Mai ƙididdigewa ga laifuffukan bãyinSa.
Ayah 25:59 الأية
الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ
ثُمَّ اسْتَوَىٰ عَلَى الْعَرْشِ ۚ الرَّحْمَٰنُ فَاسْأَلْ بِهِ خَبِيرًا
Hausa
Wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, a cikin kwãnuka
shida sa'an nan Yã daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai bãyar
da lãbãri game da Shi.
Ayah 25:60 الأية
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ اسْجُدُوا لِلرَّحْمَٰنِ قَالُوا وَمَا الرَّحْمَٰنُ
أَنَسْجُدُ لِمَا تَأْمُرُنَا وَزَادَهُمْ نُفُورًا ۩
Hausa
Idan aka ce musu, "Ku yi sujada ga Mai rahama." Sai su ce: "Mene ne Mai rahama?
Ashe zã mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu?"Kuma wannan (magana ta ƙãra
musu gudu.
Ayah 25:61 الأية
تَبَارَكَ الَّذِي جَعَلَ فِي السَّمَاءِ بُرُوجًا وَجَعَلَ فِيهَا سِرَاجًا
وَقَمَرًا مُّنِيرًا
Hausa
Albarka ta tabbata ga Wanda Ya sanya masaukai (na tafiyar wata) a cikin sama
kuma Ya sanya fitila da watã mai haskakewa a cikinta.
Ayah 25:62 الأية
وَهُوَ الَّذِي جَعَلَ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ خِلْفَةً لِّمَنْ أَرَادَ أَن
يَذَّكَّرَ أَوْ أَرَادَ شُكُورًا
Hausa
Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya dare da yini a kan mayẽwa,ga wanda yake son ya yi
tunãni, kõ kuwa ya yi nufin ya gõde.
Ayah 25:63 الأية
وَعِبَادُ الرَّحْمَٰنِ الَّذِينَ يَمْشُونَ عَلَى الْأَرْضِ هَوْنًا وَإِذَا
خَاطَبَهُمُ الْجَاهِلُونَ قَالُوا سَلَامًا
Hausa
Kuma bãyin Mai rahama su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan
jãhilai sun yi musu magana, sai su ce: "Salãma" (a zama lafiya).
Ayah 25:64 الأية
وَالَّذِينَ يَبِيتُونَ لِرَبِّهِمْ سُجَّدًا وَقِيَامًا
Hausa
Kuma waɗanda suke kwãna sunã mãsu sujada da tsayi a wurin Ubangijinsu.
Ayah 25:65 الأية
وَالَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا اصْرِفْ عَنَّا عَذَابَ جَهَنَّمَ ۖ إِنَّ
عَذَابَهَا كَانَ غَرَامًا
Hausa
Kuma waɗanda suke cẽwa "Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azãbar Jahannama daga
gare mu. Lalle ne, azãbarta tã zama tãra
Ayah 25:66 الأية
إِنَّهَا سَاءَتْ مُسْتَقَرًّا وَمُقَامًا
Hausa
"Lalle ne ita ta mũnana ta zama wurin tabbata da mazauni."
Ayah 25:67 الأية
وَالَّذِينَ إِذَا أَنفَقُوا لَمْ يُسْرِفُوا وَلَمْ يَقْتُرُوا وَكَانَ بَيْنَ
ذَٰلِكَ قَوَامًا
Hausa
Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma
(ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa.
Ayah 25:68 الأية
وَالَّذِينَ لَا يَدْعُونَ مَعَ اللَّهِ إِلَٰهًا آخَرَ وَلَا يَقْتُلُونَ
النَّفْسَ الَّتِي حَرَّمَ اللَّهُ إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَا يَزْنُونَ ۚ وَمَن
يَفْعَلْ ذَٰلِكَ يَلْقَ أَثَامًا
Hausa
Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda
Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan,
zai gamu da laifuffuka,
Ayah 25:69 الأية
يُضَاعَفْ لَهُ الْعَذَابُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَيَخْلُدْ فِيهِ مُهَانًا
Hausa
A riɓanya masa azãba a Rãnar ¡iyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã
wulakantacce.
Ayah 25:70 الأية
إِلَّا مَن تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ عَمَلًا صَالِحًا فَأُولَٰئِكَ يُبَدِّلُ
اللَّهُ سَيِّئَاتِهِمْ حَسَنَاتٍ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan
Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara
Mai jin ƙai.
Ayah 25:71 الأية
وَمَن تَابَ وَعَمِلَ صَالِحًا فَإِنَّهُ يَتُوبُ إِلَى اللَّهِ مَتَابًا
Hausa
Kuma wanda ya tũba, kuma ya aikata aiki mai kyau, to, lalle ne sai ya tũba zuwa
gaAllah.
Ayah 25:72 الأية
وَالَّذِينَ لَا يَشْهَدُونَ الزُّورَ وَإِذَا مَرُّوا بِاللَّغْوِ مَرُّوا
كِرَامًا
Hausa
Kuma waɗanda suke bã su yin shaidar zur, kuma idan sun shũɗe ga yasassar magana
sai su shũɗe suna mãsu mutumci.
Ayah 25:73 الأية
وَالَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُوا بِآيَاتِ رَبِّهِمْ لَمْ يَخِرُّوا عَلَيْهَا صُمًّا
وَعُمْيَانًا
Hausa
Kuma waɗanda suke idan an tunãtar da su da ãyõyin Allah,bã su saukar da kai,
sunã kurame da makãfi.
Ayah 25:74 الأية
وَالَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا هَبْ لَنَا مِنْ أَزْوَاجِنَا وَذُرِّيَّاتِنَا
قُرَّةَ أَعْيُنٍ وَاجْعَلْنَا لِلْمُتَّقِينَ إِمَامًا
Hausa
Kuma waɗanda suke cẽwa "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da
zũriyarmu, kuma Ka sanya mu shũgabanni ga mãsu taƙawa."
Ayah 25:75 الأية
أُولَٰئِكَ يُجْزَوْنَ الْغُرْفَةَ بِمَا صَبَرُوا وَيُلَقَّوْنَ فِيهَا تَحِيَّةً
وَسَلَامًا
Hausa
Waɗannan anã sãka musu da bẽne, sabõda haƙurin da suka yi, kuma a haɗa su, a
cikinsa, da gaisuwa da aminci.
Ayah 25:76 الأية
خَالِدِينَ فِيهَا ۚ حَسُنَتْ مُسْتَقَرًّا وَمُقَامًا
Hausa
Suna madawwama a cikinsa. Ya yi kyau ga zama matabbaci da mazauni.
Ayah 25:77 الأية
قُلْ مَا يَعْبَأُ بِكُمْ رَبِّي لَوْلَا دُعَاؤُكُمْ ۖ فَقَدْ كَذَّبْتُمْ
فَسَوْفَ يَكُونُ لِزَامًا
Hausa
Ka ce: "Ubangijĩna ba Ya kula da ku in bã dõmin addu'arku ba. To, lalle ne, kun
ƙaryata, sabõda haka al'amarin zã ya zama malizimci."
« Prev
26. Surah Ash-Shu'arâ' سورة الشعراء
Next » Other Surahs - Quran Mas'haf السور الأخرى - مصحف القرآن Other Tarjumat - Quran Mas'haf التراجيم الأخرى - مصحف القرآن Refresh Or Reload This Quran Recitation Page Quran Chapter 1. Surah Al-Fâtihah سورة الفاتحة Quran Chapter 2. Surah Al-Baqarah سورة البقرة Quran Chapter 3. Surah Âl-'Imrân سورة آل عمران Quran Chapter 4. Surah An-Nisâ' سورة النساء Quran Chapter 5. Surah Al-Mâ'idah سورة المائدة Quran Chapter 6. Surah Al-An'âm سورة الأنعام Quran Chapter 7. Surah Al-A'râf سورة الأعراف Quran Chapter 8. Surah Al-Anfâl سورة الأنفال Quran Chapter 9. Surah At-Taubah سورة التوبة Quran Chapter 10. Surah Yûnus سورة يونس Quran Chapter 11. Surah Hûd سورة هود Quran Chapter 12. Surah Yûsuf سورة يوسف Quran Chapter 13. Surah Ar-Ra'd سورة الرعد Quran Chapter 14. Surah Ibrahîm سورة إبراهيم Quran Chapter 15. Surah Al-Hijr سورة الحجر Quran Chapter 16. Surah An-Nahl سورة النحل Quran Chapter 17. Surah Al-Isrâ' سورة الإسراء Quran Chapter 18. Surah Al-Kahf سورة الكهف Quran Chapter 19. Surah Maryam سورة مريم Quran Chapter 20. Surah TâHâ. سورة طه Quran Chapter 21. Surah Al-Anbiyâ' سورة الأنبياء Quran Chapter 22. Surah Al-Hajj سورة الحج Quran Chapter 23. Surah Al-Mu'minûn سورة المؤمنون Quran Chapter 24. Surah An-Nûr سورة النّور Quran Chapter 25. Surah Al-Furqân سورة الفرقان Quran Chapter 26. Surah Ash-Shu'arâ' سورة الشعراء Quran Chapter 27. Surah An-Naml سورة النّمل Quran Chapter 28. Surah Al-Qasas سورة القصص Quran Chapter 29. Surah Al-'Ankabût سورة العنكبوت Quran Chapter 30. Surah ArRûm سورة الرّوم Quran Chapter 31. Surah Luqmân سورة لقمان Quran Chapter 32. Surah AsSajdah سورة السجدة Quran Chapter 33. Surah AlAhzâb سورة الأحزاب Quran Chapter 34. Surah Saba' سورة سبأ Quran Chapter 35. Surah Fâtir or AlMalâ'ikah سورة فاطر Quran Chapter 36. Surah YâSîn سورة يس Quran Chapter 37. Surah As-Sâffât سورة الصافات Quran Chapter 38. Surah Sâd. سورة ص Quran Chapter 39. Surah Az-Zumar سورة الزمر Quran Chapter 40. Surah Ghâfir سورة غافر Quran Chapter 41. Surah Fussilat سورة فصّلت Quran Chapter 42. Surah Ash-Shûra سورة الشورى Quran Chapter 43. Surah Az-Zukhruf سورة الزخرف Quran Chapter 44. Surah Ad-Dukhân سورة الدّخان Quran Chapter 45. Surah Al-Jâthiya سورة الجاثية Quran Chapter 46. Surah Al-Ahqâf سورة الأحقاف Quran Chapter 47. Surah Muhammad or Al-Qitâl سورة محمد Quran Chapter 48. Surah Al-Fath سورة الفتح Quran Chapter 49. Surah Al-Hujurât سورة الحجرات Quran Chapter 50. Surah Qâf. سورة ق Quran Chapter 51. Surah Az-Zâriyât سورة الذاريات Quran Chapter 52. Surah At-Tûr سورة الطور Quran Chapter 53. Surah An-Najm سورة النجم Quran Chapter 54. Surah Al-Qamar سورة القمر Quran Chapter 55. Surah Ar-Rahmân سورة الرحمن Quran Chapter 56. Surah Al-Wâqi'ah سورة الواقعة Quran Chapter 57. Surah Al-Hadîd سورة الحديد Quran Chapter 58. Surah Al-Mujâdilah سورة المجادلة Quran Chapter 59. Surah Al-Hashr سورة الحشر Quran Chapter 60. Surah Al-Mumtahinah سورة الممتحنة Quran Chapter 61. Surah As-Saff سورة الصف Quran Chapter 62. Surah Al-Jumu'ah سورة الجمعة Quran Chapter 63. Surah Al-Munâfiqûn سورة المنافقون Quran Chapter 64. Surah At-Taghâbun سورة التغابن Quran Chapter 65. Surah At-Talâq سورة الطلاق Quran Chapter 66. Surah At-Tahrîm سورة التحريم Quran Chapter 67. Surah Al-Mulk سورة الملك Quran Chapter 68. Surah Al-Qalam سورة القلم Quran Chapter 69. Surah Al-Hâqqah سورة الحاقة Quran Chapter 70. Surah Al-Ma'ârij سورة المعارج Quran Chapter 71. Surah Nûh سورة نوح Quran Chapter 72. Surah Al-Jinn سورة الجن Quran Chapter 73. Surah Al-Muzzammil سورة المزّمّل Quran Chapter 74. Surah Al-Muddaththir سورة المدّثر Quran Chapter 75. Surah Al-Qiyâmah سورة القيامة Quran Chapter 76. Surah Al-Insân or Ad-Dahr سورة الإنسان Quran Chapter 77. Surah Al-Mursalât سورة المرسلات Quran Chapter 78. Surah An-Naba' سورة النبأ Quran Chapter 79. Surah An-Nazi'ât سورة النازعات Quran Chapter 80. Surah 'Abasa سورة عبس Quran Chapter 81. Surah At-Takwîr سورة التكوير Quran Chapter 82. Surah Al-Infitâr سورة الإنفطار Quran Chapter 83. Surah Al-Mutaffifîn سورة المطفّفين Quran Chapter 84. Surah Al-Inshiqâq سورة الإنشقاق Quran Chapter 85. Surah Al-Burûj سورة البروج Quran Chapter 86. Surah At-Târiq سورة الطارق Quran Chapter 87. Surah Al-A'lâ سورة الأعلى Quran Chapter 88. Surah Al-Ghâshiyah سورة الغاشية Quran Chapter 89. Surah Al-Fajr سورة الفجر Quran Chapter 90. Surah Al-Balad سورة البلد Quran Chapter 91. Surah Ash-Shams سورة الشمس Quran Chapter 92. Surah Al-Lail سورة الليل Quran Chapter 93. Surah Ad-Duha سورة الضحى Quran Chapter 94. Surah Ash-Sharh سورة الشرح Quran Chapter 95. Surah At-Tin سورة التين Quran Chapter 96. Surah Al-'Alaq سورة العلق Quran Chapter 97. Surah Al-Qadr سورة القدر Quran Chapter 98. Surah Al-Baiyinah سورة البينة Quran Chapter 99. Surah Az-Zalzalah سورة الزلزلة Quran Chapter 100. Surah Al-'Adiyât سورة العاديات Quran Chapter 101. Surah Al-Qâri'ah سورة القارعة Quran Chapter 102. Surah At-Takâthur سورة التكاثر Quran Chapter 103. Surah Al-'Asr سورة العصر Quran Chapter 104. Surah Al-Humazah سورة الهمزة Quran Chapter 105. Surah Al-Fîl سورة الفيل Quran Chapter 106. Surah Quraish سورة قريش Quran Chapter 107. Surah Al-Mâ'ûn سورة الماعون Quran Chapter 108. Surah Al-Kauthar سورة الكوثر Quran Chapter 109. Surah Al-Kâfirûn سورة الكافرون Quran Chapter 110. Surah An-Nasr سورة النصر Quran Chapter 111. Surah Al-Masad سورة المسد Quran Chapter 112. Surah Al-Ikhlâs or At-Tauhîd سورة الإخلاص Quran Chapter 113. Surah Al-Falaq سورة الفلق Quran Chapter 114. Surah An-Nâs سورة النّاس Go To The Surahs Audio Tutorial
First Ayah 1 الأية الأولي
بِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
Ayah 26:2 الأية
تِلْكَ آيَاتُ الْكِتَابِ الْمُبِينِ
Hausa
Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
Ayah 26:3 الأية
لَعَلَّكَ بَاخِعٌ نَّفْسَكَ أَلَّا يَكُونُوا مُؤْمِنِينَ
Hausa
Tsammãninka kai mai halakar da ranka ne, dõmin ba su kasance mũminai ba!
Ayah 26:4 الأية
إِن نَّشَأْ نُنَزِّلْ عَلَيْهِم مِّنَ السَّمَاءِ آيَةً فَظَلَّتْ أَعْنَاقُهُمْ
لَهَا خَاضِعِينَ
Hausa
Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini
sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai.
Ayah 26:5 الأية
وَمَا يَأْتِيهِم مِّن ذِكْرٍ مِّنَ الرَّحْمَٰنِ مُحْدَثٍ إِلَّا كَانُوا عَنْهُ
مُعْرِضِينَ
Hausa
Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance
daga barinta sunã mãsu bijirẽwa.
Ayah 26:6 الأية
فَقَدْ كَذَّبُوا فَسَيَأْتِيهِمْ أَنبَاءُ مَا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ
Hausa
To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da
shi zã ya je musu.
Ayah 26:7 الأية
أَوَلَمْ يَرَوْا إِلَى الْأَرْضِ كَمْ أَنبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍ كَرِيمٍ
Hausa
Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan
nau'i mai kyau?
Ayah 26:8 الأية
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
Hausa
Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba.
Ayah 26:9 الأية
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ
Hausa
Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama.
Ayah 26:10 الأية
وَإِذْ نَادَىٰ رَبُّكَ مُوسَىٰ أَنِ ائْتِ الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ
Hausa
Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai.
Ayah 26:11 الأية
قَوْمَ فِرْعَوْنَ ۚ أَلَا يَتَّقُونَ
Hausa
"Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba?"
Ayah 26:12 الأية
قَالَ رَبِّ إِنِّي أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ
Hausa
Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni.
Ayah 26:13 الأية
وَيَضِيقُ صَدْرِي وَلَا يَنطَلِقُ لِسَانِي فَأَرْسِلْ إِلَىٰ هَارُونَ
Hausa
"Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa
ga Harũna.
Ayah 26:14 الأية
وَلَهُمْ عَلَيَّ ذَنبٌ فَأَخَافُ أَن يَقْتُلُونِ
Hausa
"Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni."
Ayah 26:15 الأية
قَالَ كَلَّا ۖ فَاذْهَبَا بِآيَاتِنَا ۖ إِنَّا مَعَكُم مُّسْتَمِعُونَ
Hausa
Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã
Mãsu saurãre."
Ayah 26:16 الأية
فَأْتِيَا فِرْعَوْنَ فَقُولَا إِنَّا رَسُولُ رَبِّ الْعَالَمِينَ
Hausa
"Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin
halitta ne."
Ayah 26:17 الأية
أَنْ أَرْسِلْ مَعَنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ
Hausa
"Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu."
Ayah 26:18 الأية
قَالَ أَلَمْ نُرَبِّكَ فِينَا وَلِيدًا وَلَبِثْتَ فِينَا مِنْ عُمُرِكَ سِنِينَ
Hausa
Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu
shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?"
Ayah 26:19 الأية
وَفَعَلْتَ فَعْلَتَكَ الَّتِي فَعَلْتَ وَأَنتَ مِنَ الْكَافِرِينَ
Hausa
"Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?"
Ayah 26:20 الأية
قَالَ فَعَلْتُهَا إِذًا وَأَنَا مِنَ الضَّالِّينَ
Hausa
Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin hushi."
Ayah 26:21 الأية
فَفَرَرْتُ مِنكُمْ لَمَّا خِفْتُكُمْ فَوَهَبَ لِي رَبِّي حُكْمًا وَجَعَلَنِي
مِنَ الْمُرْسَلِينَ
Hausa
"Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya
bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni."
Ayah 26:22 الأية
وَتِلْكَ نِعْمَةٌ تَمُنُّهَا عَلَيَّ أَنْ عَبَّدتَّ بَنِي إِسْرَائِيلَ
Hausa
"Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla."
Ayah 26:23 الأية
قَالَ فِرْعَوْنُ وَمَا رَبُّ الْعَالَمِينَ
Hausa
Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?"
Ayah 26:24 الأية
قَالَ رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ
Hausa
Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance
mãsu ƙarfin ĩmãni."
Ayah 26:25 الأية
قَالَ لِمَنْ حَوْلَهُ أَلَا تَسْتَمِعُونَ
Hausa
Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba?"
Ayah 26:26 الأية
قَالَ رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَ
Hausa
Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko."
Ayah 26:27 الأية
قَالَ إِنَّ رَسُولَكُمُ الَّذِي أُرْسِلَ إِلَيْكُمْ لَمَجْنُونٌ
Hausa
Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne."
Ayah 26:28 الأية
قَالَ رَبُّ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ إِن كُنتُمْ
تَعْقِلُونَ
Hausa
Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan
kun kasance kunã hankalta."
Ayah 26:29 الأية
قَالَ لَئِنِ اتَّخَذْتَ إِلَٰهًا غَيْرِي لَأَجْعَلَنَّكَ مِنَ الْمَسْجُونِينَ
Hausa
Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga
ɗaurarru."
Ayah 26:30 الأية
قَالَ أَوَلَوْ جِئْتُكَ بِشَيْءٍ مُّبِينٍ
Hausa
Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?"
Ayah 26:31 الأية
قَالَ فَأْتِ بِهِ إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ
Hausa
Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya."
Ayah 26:32 الأية
فَأَلْقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعْبَانٌ مُّبِينٌ
Hausa
Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne.
Ayah 26:33 الأية
وَنَزَعَ يَدَهُ فَإِذَا هِيَ بَيْضَاءُ لِلنَّاظِرِينَ
Hausa
Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo.
Ayah 26:34 الأية
قَالَ لِلْمَلَإِ حَوْلَهُ إِنَّ هَٰذَا لَسَاحِرٌ عَلِيمٌ
Hausa
(Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci
ne, mai ilmi!
Ayah 26:35 الأية
يُرِيدُ أَن يُخْرِجَكُم مِّنْ أَرْضِكُم بِسِحْرِهِ فَمَاذَا تَأْمُرُونَ
Hausa
"Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke
shãwartãwa?"