First Ayah 1 الأية الأوليبِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
Ayah 29:2 الأية
أَحَسِبَ النَّاسُ أَن يُتْرَكُوا أَن يَقُولُوا آمَنَّا وَهُمْ لَا يُفْتَنُونَ
Hausa
Ashe, mutăne sun yi zaton a bar su su ce: "Mun yi ĩmăni," alhăli kuwa bă ză a
fitine su ba?"
|
Ayah 29:3 الأية
وَلَقَدْ فَتَنَّا الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۖ فَلَيَعْلَمَنَّ اللَّهُ الَّذِينَ
صَدَقُوا وَلَيَعْلَمَنَّ الْكَاذِبِينَ
Hausa
Kuma lalle Mun fitini waɗanda ke a gabăninsu, dőmin lalle Allah Ya san waɗanda
suka yi gaskiya, kuma lalle Ya san maƙaryata.
|
Ayah 29:4 الأية
أَمْ حَسِبَ الَّذِينَ يَعْمَلُونَ السَّيِّئَاتِ أَن يَسْبِقُونَا ۚ سَاءَ مَا
يَحْكُمُونَ
Hausa
Kő waɗanda ke aikata miyăgun ayyuka sun yi zaton su tsẽre Mana? Abin da suke
hukuntăwa ya mũnana.
|
Ayah 29:5 الأية
مَن كَانَ يَرْجُو لِقَاءَ اللَّهِ فَإِنَّ أَجَلَ اللَّهِ لَآتٍ ۚ وَهُوَ
السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Hausa
Wanda ya kasance yană fătan gamuwa da Al1ah to lalle ajalin Allah mai zuwa ne,
kuma (Allah) Shĩ ne Mai ji, Masani.
|
Ayah 29:6 الأية
وَمَن جَاهَدَ فَإِنَّمَا يُجَاهِدُ لِنَفْسِهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ لَغَنِيٌّ عَنِ
الْعَالَمِينَ
Hausa
Kuma wanda ya yi jihădi, to, yană yin jihădin ne dőmin kansa. lalle Allah haƙĩƙa
waɗatacce ne daga barin tălikai.
|
Ayah 29:7 الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَنُكَفِّرَنَّ عَنْهُمْ
سَيِّئَاتِهِمْ وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَحْسَنَ الَّذِي كَانُوا يَعْمَلُونَ
Hausa
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Mună kankare
musu miyăgun ayyukansu, kuma lalle Mună săka musu da mafi kyaun abin da suka
kasance sună aikatăwa.
|
Ayah 29:8 الأية
وَوَصَّيْنَا الْإِنسَانَ بِوَالِدَيْهِ حُسْنًا ۖ وَإِن جَاهَدَاكَ لِتُشْرِكَ بِي
مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ فَلَا تُطِعْهُمَا ۚ إِلَيَّ مَرْجِعُكُمْ
فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Hausa
Kuma Mun yi wa mutum wasiyyar kyautatăwa ga uwayensa, kuma idan sun tsananta
maka dőmin ka yi shirki da Ni game da abin da bă ka da ilmi gare shi, to, kada
ka yi musu ɗă'ă. Zuwa gare Ni makőmarku take sa'an nan In bă ku lăbari ga abin
da kuka kasance kună aikatăwa.
|
Ayah 29:9 الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَنُدْخِلَنَّهُمْ فِي الصَّالِحِينَ
Hausa
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Mună shigar
da su a cikin mutănen kirki.
|
Ayah 29:10 الأية
وَمِنَ النَّاسِ مَن يَقُولُ آمَنَّا بِاللَّهِ فَإِذَا أُوذِيَ فِي اللَّهِ جَعَلَ
فِتْنَةَ النَّاسِ كَعَذَابِ اللَّهِ وَلَئِن جَاءَ نَصْرٌ مِّن رَّبِّكَ
لَيَقُولُنَّ إِنَّا كُنَّا مَعَكُمْ ۚ أَوَلَيْسَ اللَّهُ بِأَعْلَمَ بِمَا فِي
صُدُورِ الْعَالَمِينَ
Hausa
Kuma daga cikin mutăne akwai mai cẽwa, 'Mun yi ĩmăni da Allah" sa'an nan idan
aka cũce shi wajen aikin Allah, sai ya sanya fitinar mutăne kamar azăbar Allah
kuma lalle idan taimakon Ubangijinka ya zo, haƙĩƙa, ya kan ce: "Lalle mũ mun
kasance tăre da ku." shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga abin da ke a cikin
ƙirăzan halittunSa?
|
Ayah 29:11 الأية
وَلَيَعْلَمَنَّ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَلَيَعْلَمَنَّ الْمُنَافِقِينَ
Hausa
Kuma lalle Allah na sanin waɗanda suka yi ĩmăni kuma lalle Yană sanin munfukai.
|
Ayah 29:12 الأية
وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِلَّذِينَ آمَنُوا اتَّبِعُوا سَبِيلَنَا وَلْنَحْمِلْ
خَطَايَاكُمْ وَمَا هُم بِحَامِلِينَ مِنْ خَطَايَاهُم مِّن شَيْءٍ ۖ إِنَّهُمْ
لَكَاذِبُونَ
Hausa
Kuma waɗanda suka kăfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmăni, "Ku bi hanyarmu,
kuma Mu ɗauki laifuffukanku," alhăli kőwa ba su zamo măsu ɗauka da a kőme ba
daga laifuffukansu. Lalle sũ maƙaryata ne.
|
Ayah 29:13 الأية
وَلَيَحْمِلُنَّ أَثْقَالَهُمْ وَأَثْقَالًا مَّعَ أَثْقَالِهِمْ ۖ وَلَيُسْأَلُنَّ
يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَمَّا كَانُوا يَفْتَرُونَ
Hausa
Kuma lalle sună ɗaukar kăyan nauyinsu da waɗansu nauyăyan kăya tăre da kăyan
nauyinsu, kuma lalle ză a tambaye su a Rănar ˇiyama game da abin da suka kasance
sună ƙirƙirăwa na ƙarya.
|
Ayah 29:14 الأية
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِ فَلَبِثَ فِيهِمْ أَلْفَ سَنَةٍ
إِلَّا خَمْسِينَ عَامًا فَأَخَذَهُمُ الطُّوفَانُ وَهُمْ ظَالِمُونَ
Hausa
Kuma lalle Mun aika Nũhu zuwa ga mutănensa, sai ya zauna a cikinsu shẽkara dubu
făce shẽkara hamsin, sa'an nan cikowar (¦ũfăna) ta kămă su, alhăli kuwa sũ ne
măsu zălunci.
|
Ayah 29:15 الأية
فَأَنجَيْنَاهُ وَأَصْحَابَ السَّفِينَةِ وَجَعَلْنَاهَا آيَةً لِّلْعَالَمِينَ
Hausa
Sa'an nan Muka tsĩrar da shi da mutănen jirgin, kuma Muka sanya jirgin ya zama
wata ăyă ga tălikai.
|
Ayah 29:16 الأية
وَإِبْرَاهِيمَ إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاتَّقُوهُ ۖ ذَٰلِكُمْ
خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Hausa
Da Ibrăhĩm a lőkacin da ya ce wa mutănensa, "Ku baută wa Allah ku bĩ Shi da
taƙawa. Wannan Shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kună sani.
|
Ayah 29:17 الأية
إِنَّمَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ أَوْثَانًا وَتَخْلُقُونَ إِفْكًا ۚ إِنَّ
الَّذِينَ تَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ لَا يَمْلِكُونَ لَكُمْ رِزْقًا
فَابْتَغُوا عِندَ اللَّهِ الرِّزْقَ وَاعْبُدُوهُ وَاشْكُرُوا لَهُ ۖ إِلَيْهِ
تُرْجَعُونَ
Hausa
"Abin da dai kuke bautăwa, baiein Allah, gumaka ne, kuma kun ƙirƙira ƙarya.
Lalle waɗannan da kuke bauta wa baicin Allah, bă su mallakă muku arziki. Sabőda
haka ku nẽmi arziki a wurin Allah kawai, kuma ku bauta Masa, kuma ku yi gődiya
zuwa gare Shi. Zuwa gare Shi ake mayar da ku.
|
Ayah 29:18 الأية
وَإِن تُكَذِّبُوا فَقَدْ كَذَّبَ أُمَمٌ مِّن قَبْلِكُمْ ۖ وَمَا عَلَى الرَّسُولِ
إِلَّا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ
Hausa
"Kuma idan kun ƙaryata, to, lalle waɗansu al'ummőmi a gabăninku sun ƙaryata,
kuma băbu abin da ke kan Manzo, făce iyar da manzanci, iyarwa bayyananna."
|
Ayah 29:19 الأية
أَوَلَمْ يَرَوْا كَيْفَ يُبْدِئُ اللَّهُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ ۚ إِنَّ
ذَٰلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرٌ
Hausa
Shin, ba su ga yadda Allah ke făra yin halitta ba, sa'an nan kuma Ya mayar da
ita? Lalle wannan abu ne mai sauƙi ga Allah.
|
Ayah 29:20 الأية
قُلْ سِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَانظُرُوا كَيْفَ بَدَأَ الْخَلْقَ ۚ ثُمَّ اللَّهُ
يُنشِئُ النَّشْأَةَ الْآخِرَةَ ۚ إِنَّ اللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Hausa
Ka ce: "Ku yi tafiya cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda (Allah) Ya făra yin
halitta, sa'an nan kuma Allah Yană ƙăga wata halittar mayarwa. Lalle Allah Mai
ikon yi ne a kan kőme.
|
Ayah 29:21 الأية
يُعَذِّبُ مَن يَشَاءُ وَيَرْحَمُ مَن يَشَاءُ ۖ وَإِلَيْهِ تُقْلَبُونَ
Hausa
"Yană azabta wanda Ya so, kuma Yană jin ƙan wanda Ya so. Kuma zuwa gare shi ake
jũyaku."
|
Ayah 29:22 الأية
وَمَا أَنتُم بِمُعْجِزِينَ فِي الْأَرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ ۖ وَمَا لَكُم مِّن
دُونِ اللَّهِ مِن وَلِيٍّ وَلَا نَصِيرٍ
Hausa
"Kuma ba ku zamo măsu buwăya ba a cikin ƙasă, kuma haka a cikin sama kuma bă ku
da wani majiɓinci wanda ba Allah ba, kuma ha ku da wani mataimaki."
|
Ayah 29:23 الأية
وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِ اللَّهِ وَلِقَائِهِ أُولَٰئِكَ يَئِسُوا مِن
رَّحْمَتِي وَأُولَٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Hausa
Kuma waɗanda suka kăfirta da ăyőyin Allah da gamuwa da shi, waɗannan sun yanke
ƙauna daga rahamaTa kuma waɗannan sună da wata azăba mai raɗaɗi.
|
Ayah 29:24 الأية
فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ إِلَّا أَن قَالُوا اقْتُلُوهُ أَوْ حَرِّقُوهُ
فَأَنجَاهُ اللَّهُ مِنَ النَّارِ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ
يُؤْمِنُونَ
Hausa
Sa'an nan băbu abin da ya kasance jawăbin mutănensa (Ibrăhĩm) făce dai suka ce:
"Ku kashe shi kő, ku ƙőnă shi," Sai Allah Ya tsĩrar da shi daga wută. Lallea
cikin wannan akwai ayőyi ga mutănen da ke yin ĩmăni.
|
Ayah 29:25 الأية
وَقَالَ إِنَّمَا اتَّخَذْتُم مِّن دُونِ اللَّهِ أَوْثَانًا مَّوَدَّةَ بَيْنِكُمْ
فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۖ ثُمَّ يَوْمَ الْقِيَامَةِ يَكْفُرُ بَعْضُكُم
بِبَعْضٍ وَيَلْعَنُ بَعْضُكُم بَعْضًا وَمَأْوَاكُمُ النَّارُ وَمَا لَكُم مِّن
نَّاصِرِينَ
Hausa
Kuma Ibrahĩm ya ce "Băbu abin da kuka yi sai dai kub bar Allah kun riƙi gumăka
sabőda sőyayyar tsakăninku a cikin răyuwar dũniya, a'an nan a Rănar ˇiyăma
săshinku zai kăfirce wa săshi, kuma makőmarku ita ce wută kuma bă ku da waɗansu
mataimaka."
|
Ayah 29:26 الأية
فَآمَنَ لَهُ لُوطٌ ۘ وَقَالَ إِنِّي مُهَاجِرٌ إِلَىٰ رَبِّي ۖ إِنَّهُ هُوَ
الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Hausa
Sai Lũɗu ya yi ĩmăni da shi. Kuma Ibrăhĩm ya ce: "Lallenĩ mai ƙaura ne zuwa ga
Ubangijina. Lalle Shĩ Shĩ ne Mabuwăyi, Mai hikima."
|
Ayah 29:27 الأية
وَوَهَبْنَا لَهُ إِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ وَجَعَلْنَا فِي ذُرِّيَّتِهِ النُّبُوَّةَ
وَالْكِتَابَ وَآتَيْنَاهُ أَجْرَهُ فِي الدُّنْيَا ۖ وَإِنَّهُ فِي الْآخِرَةِ
لَمِنَ الصَّالِحِينَ
Hausa
Kuma Muka bă shi Ishăƙa da Ya'aƙũba, kuma Muka sanya Annabci da littăfi a cikin
zuriyarsa. Kuma Mun bă shi sakamakonsa a dũniya, kuma lalle shĩ a Lăhira,
tabbas, yană a cikin sălihai.
|
Ayah 29:28 الأية
وَلُوطًا إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ إِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الْفَاحِشَةَ مَا سَبَقَكُم
بِهَا مِنْ أَحَدٍ مِّنَ الْعَالَمِينَ
Hausa
Da Lũɗu, a lőkacin daya ce wa mutănensa, "Lalle kũ, haƙĩƙa kună jẽ wa alfăsha
wadda wani mahalũƙi daga cikin dũniya bai riga ku gare ta ba.
|
Ayah 29:29 الأية
أَئِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الرِّجَالَ وَتَقْطَعُونَ السَّبِيلَ وَتَأْتُونَ فِي
نَادِيكُمُ الْمُنكَرَ ۖ فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ إِلَّا أَن قَالُوا ائْتِنَا
بِعَذَابِ اللَّهِ إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ
Hausa
"Ashe, lalle kũ kună je wa maza, kuma ku yi fashin hanya kuma ku je, a cikin
majalisarku da abin da bă shi da kyau? To, jawăbin mutănensa bai kasance ba făce
dai sun ce: 'Ka zo mana da azăbar Allah, idan ka kasance daga măsu gaskiya.'"
|
Ayah 29:30 الأية
قَالَ رَبِّ انصُرْنِي عَلَى الْقَوْمِ الْمُفْسِدِينَ
Hausa
Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni a kan mutănen nan maɓarnata."
|
Ayah 29:31 الأية
وَلَمَّا جَاءَتْ رُسُلُنَا إِبْرَاهِيمَ بِالْبُشْرَىٰ قَالُوا إِنَّا مُهْلِكُو
أَهْلِ هَٰذِهِ الْقَرْيَةِ ۖ إِنَّ أَهْلَهَا كَانُوا ظَالِمِينَ
Hausa
Kuma a lőkacin da ManzanninMu suka jẽ wa Ibrăhĩm da bushăra suka ce: "Lalle mu
măsu halaka mutănen, wannan alƙarya ne. Lalle mutănenta sun kasance măsu
zălunci."
|
Ayah 29:32 الأية
قَالَ إِنَّ فِيهَا لُوطًا ۚ قَالُوا نَحْنُ أَعْلَمُ بِمَن فِيهَا ۖ
لَنُنَجِّيَنَّهُ وَأَهْلَهُ إِلَّا امْرَأَتَهُ كَانَتْ مِنَ الْغَابِرِينَ
Hausa
Ya ce: "Lalle akwai Lũɗu a cikinta!" Suka ce: "Mũ ne mafiya sani ga waɗanda suke
a cikinta, lalle mună tsĩrar da shi da mutănensa, făce fa mătarsa ta kasance a
cikin măsu wanzuwa."
|
Ayah 29:33 الأية
وَلَمَّا أَن جَاءَتْ رُسُلُنَا لُوطًا سِيءَ بِهِمْ وَضَاقَ بِهِمْ ذَرْعًا
وَقَالُوا لَا تَخَفْ وَلَا تَحْزَنْ ۖ إِنَّا مُنَجُّوكَ وَأَهْلَكَ إِلَّا
امْرَأَتَكَ كَانَتْ مِنَ الْغَابِرِينَ
Hausa
Kuma a lőkacin da ManzanninMu suka je wa Lũɗu ya ɓăta rai sabőda su, kuma yă
ƙuntata ga kirji sabőda su. Kuma suka ce: "Kada ka ji tsőro kuma kada ka yi
baƙin ciki lalle mũ măsu tsĩrar da kai ne da iyălanka, făce dai matarka ta
kasance daga măsu wanzuwa.
|
Ayah 29:34 الأية
إِنَّا مُنزِلُونَ عَلَىٰ أَهْلِ هَٰذِهِ الْقَرْيَةِ رِجْزًا مِّنَ السَّمَاءِ
بِمَا كَانُوا يَفْسُقُونَ
Hausa
"Lalle mũ, măsu saukar da azăba ne daga sama a kan mutănen wannan alƙarya sabőda
abin da suka kasance sună yi na făsiƙanci."
|
Ayah 29:35 الأية
وَلَقَد تَّرَكْنَا مِنْهَا آيَةً بَيِّنَةً لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ
Hausa
Kuma lalle Mun bar wata ăyă bayyananna daga gare ta ga mutăne măsu hankalta.
|
Ayah 29:36 الأية
وَإِلَىٰ مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْبًا فَقَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ
وَارْجُوا الْيَوْمَ الْآخِرَ وَلَا تَعْثَوْا فِي الْأَرْضِ مُفْسِدِينَ
Hausa
Kuma zuwa ga Madyana, Mun aika ɗan'uwansu shu'aibu, sai ya ce: "Ya mutănena! Ku
bauta wa Allah kuma ku yi fatan (rahamar) Rănar Lăhira, kuma kada ku yi ɓarna a
cikin ƙasă, alhăli kuwa kună măsu lălătarwa."
|
Ayah 29:37 الأية
فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ
Hausa
Sai suka ƙaryata shi, sabőda haka tsăwa ta kămă su, dőmin haka suka wăyi gari
sună guggurfăne.
|
Ayah 29:38 الأية
وَعَادًا وَثَمُودَ وَقَد تَّبَيَّنَ لَكُم مِّن مَّسَاكِنِهِمْ ۖ وَزَيَّنَ لَهُمُ
الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَصَدَّهُمْ عَنِ السَّبِيلِ وَكَانُوا مُسْتَبْصِرِينَ
Hausa
Da Ădawa da Samũdăwa alhăli kuwa lalle alămun azăba sun bayyana a gare su daga
gidăjensu kuma Shaiɗan ya ƙawăta musu ayyukansu, sabőda haka ya kange su daga
hanyar Allah, kuma sun kasance măsu basĩra!
|
Ayah 29:39 الأية
وَقَارُونَ وَفِرْعَوْنَ وَهَامَانَ ۖ وَلَقَدْ جَاءَهُم مُّوسَىٰ بِالْبَيِّنَاتِ
فَاسْتَكْبَرُوا فِي الْأَرْضِ وَمَا كَانُوا سَابِقِينَ
Hausa
Kuma ˇărũna da Fir'auna da Hămăna, kuma lalle Mũsaya je musu da hujjőji, sai
suka yi girman kai a cikin ƙasă kuma ba su kasance măsu tsẽrẽwa ba.
|
Ayah 29:40 الأية
فَكُلًّا أَخَذْنَا بِذَنبِهِ ۖ فَمِنْهُم مَّنْ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِ حَاصِبًا
وَمِنْهُم مَّنْ أَخَذَتْهُ الصَّيْحَةُ وَمِنْهُم مَّنْ خَسَفْنَا بِهِ الْأَرْضَ
وَمِنْهُم مَّنْ أَغْرَقْنَا ۚ وَمَا كَانَ اللَّهُ لِيَظْلِمَهُمْ وَلَٰكِن
كَانُوا أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
Hausa
Sabőda haka kőwanensu Mun kama shi da laifinsa. Watau daga cikinsu akwai wanda
Muka aika iskar tsakuwa a kansa kuma daga cikinsu akwai wanda tsăwa ta kămă,
kuma daga cikinsu akwai wanda Muka birkice ƙasă da shi kuma daga cikinsu akwai
wanda Muka nutsar. Bă ya yiwuwa ga Allah Ya zălunce su, amma sun kasance kansu
suke zălunta.
|
Ayah 29:41 الأية
مَثَلُ الَّذِينَ اتَّخَذُوا مِن دُونِ اللَّهِ أَوْلِيَاءَ كَمَثَلِ الْعَنكَبُوتِ
اتَّخَذَتْ بَيْتًا ۖ وَإِنَّ أَوْهَنَ الْبُيُوتِ لَبَيْتُ الْعَنكَبُوتِ ۖ لَوْ
كَانُوا يَعْلَمُونَ
Hausa
Misălin waɗanda suka riƙi waɗansu masőya waɗanda bă Allah ba, kamar misălin
gizőgizo ne wanda ya riƙi wani ɗan gida, alhăli kuwa lalle mafi raunin gidăje,
shĩ ne gidan gizogizo, dă sun kasance sună sane.
|
Ayah 29:42 الأية
إِنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا يَدْعُونَ مِن دُونِهِ مِن شَيْءٍ ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ
الْحَكِيمُ
Hausa
Lalle Allah Yană sane da abin da suke kira wanda bă Shi ba na wani abu duka kuma
shĩ ne Mabuwăyi, Mai hikima.
|
Ayah 29:43 الأية
وَتِلْكَ الْأَمْثَالُ نَضْرِبُهَا لِلنَّاسِ ۖ وَمَا يَعْقِلُهَا إِلَّا
الْعَالِمُونَ
Hausa
Kuma waɗancan misălan Mună bayyana su ga mutăne kuma băbu mai hankalta da su sai
măsu ilmi.
|
Ayah 29:44 الأية
خَلَقَ اللَّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِالْحَقِّ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً
لِّلْمُؤْمِنِينَ
Hausa
Allah Ya halitta sammai da ƙasa da gaskiya. Lalle cikin wancan akwai ăyă ga
mũminai.
|
Ayah 29:45 الأية
اتْلُ مَا أُوحِيَ إِلَيْكَ مِنَ الْكِتَابِ وَأَقِمِ الصَّلَاةَ ۖ إِنَّ
الصَّلَاةَ تَنْهَىٰ عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنكَرِ ۗ وَلَذِكْرُ اللَّهِ أَكْبَرُ
ۗ وَاللَّهُ يَعْلَمُ مَا تَصْنَعُونَ
Hausa
Ka karanta abin da ake yin wahayi zuwa gare ka daga Littăfi, kuma ka tsayar da
salla. Lalle salla tană hanăwa daga alfăsha da abni ƙyăma, kuma lalle ambaton
Allah ya fi girma, kuma Allah Yană sane da abin da kuke aikatăwa.
|
Ayah 29:46 الأية
وَلَا تُجَادِلُوا أَهْلَ الْكِتَابِ إِلَّا بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ إِلَّا
الَّذِينَ ظَلَمُوا مِنْهُمْ ۖ وَقُولُوا آمَنَّا بِالَّذِي أُنزِلَ إِلَيْنَا
وَأُنزِلَ إِلَيْكُمْ وَإِلَٰهُنَا وَإِلَٰهُكُمْ وَاحِدٌ وَنَحْنُ لَهُ
مُسْلِمُونَ
Hausa
Kada ku yi jayayya da mazowa Littăfi sai fa da magana wadda ta fi kyau, sai fa
waɗanda suka yi zălunci daga gare su, kuma ku ce, "Mun yi ĩmăni da abin da aka
saukar a gare mu kuma aka saukar a gare ku, kuma Abin bautăwarmu da Abin
bautăwarku Guda ne, kama mũ măsu sallamăwa ne a gare shi."
|
Ayah 29:47 الأية
وَكَذَٰلِكَ أَنزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ ۚ فَالَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ
يُؤْمِنُونَ بِهِ ۖ وَمِنْ هَٰؤُلَاءِ مَن يُؤْمِنُ بِهِ ۚ وَمَا يَجْحَدُ
بِآيَاتِنَا إِلَّا الْكَافِرُونَ
Hausa
Kuma kamar haka Muka saukar da Littafi a gare ka, to, waɗannan da Muka bai wa
Littăfi sană ĩmăni da shi, daga cikin wăɗannan akwai mai ĩmăni da shi, kuma băbu
mai musun ăyőyinMu, făce kăfirai.
|
Ayah 29:48 الأية
وَمَا كُنتَ تَتْلُو مِن قَبْلِهِ مِن كِتَابٍ وَلَا تَخُطُّهُ بِيَمِينِكَ ۖ إِذًا
لَّارْتَابَ الْمُبْطِلُونَ
Hausa
Kuma ba ka kasance kana karătun wani littăfi ba a gabăninsa, kuma bă ka
rubũtunsa da dămanka dă haka yă auku, dă măsu ɓarnă sun yi shakka.
|
Ayah 29:49 الأية
بَلْ هُوَ آيَاتٌ بَيِّنَاتٌ فِي صُدُورِ الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ ۚ وَمَا
يَجْحَدُ بِآيَاتِنَا إِلَّا الظَّالِمُونَ
Hausa
Ă'a, shĩ ăyőyi ne bayyanannu a cikin ƙirăzan waɗanda aka bai wa ilmi. Kuma băbu
mai musun ăyőyinMu făce azzălumai.
|
Ayah 29:50 الأية
وَقَالُوا لَوْلَا أُنزِلَ عَلَيْهِ آيَاتٌ مِّن رَّبِّهِ ۖ قُلْ إِنَّمَا
الْآيَاتُ عِندَ اللَّهِ وَإِنَّمَا أَنَا نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Hausa
Kuma suka ce: "Don me ba a saukar masa da ăyői ba daga Ubangijinsa? "Ka ce: "Su
ăyőyi a wurin Allah kawai suke, kuma lalle ni mai gargaɗi kawai ne, mai
bayyanăwa."
|
Ayah 29:51 الأية
أَوَلَمْ يَكْفِهِمْ أَنَّا أَنزَلْنَا عَلَيْكَ الْكِتَابَ يُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ ۚ
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَرَحْمَةً وَذِكْرَىٰ لِقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Hausa
Shin bai ishe su ba cẽwa lalle Mũ, Mun saukar da Littăfin akanka, ană karanta
shi a kansu? Lalle a cikin wancan haƙĩƙa akwai rahama da tunătawa ga mutanen da
ke yin ĩmăni.
|
Ayah 29:52 الأية
قُلْ كَفَىٰ بِاللَّهِ بَيْنِي وَبَيْنَكُمْ شَهِيدًا ۖ يَعْلَمُ مَا فِي
السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۗ وَالَّذِينَ آمَنُوا بِالْبَاطِلِ وَكَفَرُوا
بِاللَّهِ أُولَٰئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ
Hausa
Ka ce: "Allah Yă isa shaida a tsakănĩna da tsakănĩnku Yană sane da abin da ke a
cikin sammai da ƙasă, kuma waɗanda suka yi ĩmăni da ɗarya kuma suka kăfirta da
Allah, waɗannan sũ nemăsu hasăra."
|
Ayah 29:53 الأية
وَيَسْتَعْجِلُونَكَ بِالْعَذَابِ ۚ وَلَوْلَا أَجَلٌ مُّسَمًّى لَّجَاءَهُمُ
الْعَذَابُ وَلَيَأْتِيَنَّهُم بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
Hausa
Kuma suna nẽman ka da gaggauta azăba, to, bă dőmin ajali ƙayyadadde ba, dă azăba
ta jẽ musu kuma lalle dă tană iske su bisa ia abke, alhăli kuwa sũ ba su sani
ba.
|
Ayah 29:54 الأية
يَسْتَعْجِلُونَكَ بِالْعَذَابِ وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمُحِيطَةٌ بِالْكَافِرِينَ
Hausa
Sună nẽman ka da gaggauta azăba, kuma lalle Jahannama, tabbas, mai kẽwayewa ce
gakăfirai.
|
Ayah 29:55 الأية
يَوْمَ يَغْشَاهُمُ الْعَذَابُ مِن فَوْقِهِمْ وَمِن تَحْتِ أَرْجُلِهِمْ وَيَقُولُ
ذُوقُوا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Hausa
Rănar da azăba ke rufe su daga samansu da kuma ƙasan ƙafafunsu kuma Ya ce: "Ku
ɗanɗani abin da kuka kasance kună aikatăwa."
|
Ayah 29:56 الأية
يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ أَرْضِي وَاسِعَةٌ فَإِيَّايَ فَاعْبُدُونِ
Hausa
Yă băyiNa, waɗanda suka yi ĩmăni! Lalle fa ƙasăTa mai yalwă ce, sabăda haka ku
bauta Mini.
|
Ayah 29:57 الأية
كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ ۖ ثُمَّ إِلَيْنَا تُرْجَعُونَ
Hausa
Kőwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne, sa'an nan zuwa gare Mu ake mayar da ku.
|
Ayah 29:58 الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَنُبَوِّئَنَّهُم مِّنَ الْجَنَّةِ
غُرَفًا تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ نِعْمَ أَجْرُ
الْعَامِلِينَ
Hausa
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle ză Mu zaunar
da su daga cikin Aljanna a gidăjen bẽne, ƙoramu nă gudăna daga ƙarƙashinsu, sună
madawwama a cikinsu. To, madalla da sakamakon măsu aikin ƙwarai.
|
Ayah 29:59 الأية
الَّذِينَ صَبَرُوا وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ
Hausa
Waɗanda suka yi haƙuri, kuma sună dőgara ga Ubangijinsu kawai.
|
Ayah 29:60 الأية
وَكَأَيِّن مِّن دَابَّةٍ لَّا تَحْمِلُ رِزْقَهَا اللَّهُ يَرْزُقُهَا
وَإِيَّاكُمْ ۚ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Hausa
Kuma da yawa dabba wadda bă ta ɗaukar abincinta Allah Yană ciyar da ita tăre da
ku, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai ilmi.
|
Ayah 29:61 الأية
وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَسَخَّرَ الشَّمْسَ
وَالْقَمَرَ لَيَقُولُنَّ اللَّهُ ۖ فَأَنَّىٰ يُؤْفَكُونَ
Hausa
Lalle idan ka tambaye su: "Wăne ne ya halitta sammai da ƙasă kuma ya hőre rănă
da wată?" Lalle sună cẽwa Allah ne. TO, yăya ake karkatar da su ?
|
Ayah 29:62 الأية
اللَّهُ يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ وَيَقْدِرُ لَهُ ۚ إِنَّ
اللَّهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ
Hausa
A1lah ne ke shimfiɗa arziki ga wanda Yake so daga cikin băyinsa kuma Yană
ƙuntătăwa ga (wanda, Yake so). Lalle Allah, Masani ne ga dukan kőme.
|
Ayah 29:63 الأية
وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّن نَّزَّلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَحْيَا بِهِ الْأَرْضَ
مِن بَعْدِ مَوْتِهَا لَيَقُولُنَّ اللَّهُ ۚ قُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ ۚ بَلْ
أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ
Hausa
Kuma lalle idan ka tambaye su. "Wăne ne ya saukar da ruwa daga sama, har ya
răyar da ƙasă game da shi a băyan mutuwarta?" Lalle sună cẽwa, "Allah ne." Ka
ce: "Gődiya tă tabbata ga Allah." Ă'a, mafi yawansu bă su hankalta.
|
Ayah 29:64 الأية
وَمَا هَٰذِهِ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلَّا لَهْوٌ وَلَعِبٌ ۚ وَإِنَّ الدَّارَ
الْآخِرَةَ لَهِيَ الْحَيَوَانُ ۚ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ
Hausa
Kuma wannan răyuwa ta dũniya ba ta zamo ba, făce abar shagala da wăsă kuma lalle
Lăhira tabbas, ita ce răyuwa, dă sun kasance sună sani.
|
Ayah 29:65 الأية
فَإِذَا رَكِبُوا فِي الْفُلْكِ دَعَوُا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ
فَلَمَّا نَجَّاهُمْ إِلَى الْبَرِّ إِذَا هُمْ يُشْرِكُونَ
Hausa
To, a lőkacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirăyi Allah sună măsu
tsarkake addini a gare shi, to, a lőkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudun ƙasă,
sai gă su sună shirki.
|
Ayah 29:66 الأية
لِيَكْفُرُوا بِمَا آتَيْنَاهُمْ وَلِيَتَمَتَّعُوا ۖ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ
Hausa
Dőmin su kăfirce wa abin da Muka bă su kuma dőmin su ji dăɗi sa'an nan kuma ză
su sani.
|
Ayah 29:67 الأية
أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّا جَعَلْنَا حَرَمًا آمِنًا وَيُتَخَطَّفُ النَّاسُ مِنْ
حَوْلِهِمْ ۚ أَفَبِالْبَاطِلِ يُؤْمِنُونَ وَبِنِعْمَةِ اللَّهِ يَكْفُرُونَ
Hausa
Shin, ba su ga cẽwa, lalle Mun sanya Hurumi amintacce ba alhăli kuwa ană fisge
mutăne a gẽfensu? Shin, da ɓătaccen abu suke ĩmăni kuma da ni'imarAllah suka
kăfirta?
|
Ayah 29:68 الأية
وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَىٰ عَلَى اللَّهِ كَذِبًا أَوْ كَذَّبَ بِالْحَقِّ
لَمَّا جَاءَهُ ۚ أَلَيْسَ فِي جَهَنَّمَ مَثْوًى لِّلْكَافِرِينَ
Hausa
Kuma wăne ne ya fi zălunci bisa ga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga
Allah, kő kuma ya ƙaryata gaskiya a lőkacin da ta je masa? Ashe a cikin
Jahannama băbu mazauna ga kăfirai?
|
Ayah 29:69 الأية
وَالَّذِينَ جَاهَدُوا فِينَا لَنَهْدِيَنَّهُمْ سُبُلَنَا ۚ وَإِنَّ اللَّهَ
لَمَعَ الْمُحْسِنِينَ
Hausa
Kuma wadannan da suka yi ƙőƙari ga nẽman yardarMu, lalle Mună shiryar da su ga
hanyőyinMu, kuma lalle Allah, tabbas, Yană tăre da măsu kyautatăwa (ga
addĩninsu).
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|