A gabãni, suna shiryar da mutãne, kuma Ya saukar da littattafai mãsu rarrabẽwa.
Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, suna da azãba mai tsanani. Kuma
Allah Mabuwayi ne, Ma'abucin azãbar rãmuwa.
Shi ne wanda ya saukar da Littãfi a gare ka, daga cikinsa akwai ãyõyi
bayyanannu, su ne mafi yawan Littãfin, da wasu mãsu kamã da jũna. To, amma
waɗanda yake a cikin zukãtansu akwai karkata sai suna bin abin da yake da kamã
da jũna daga gare shi, dõmin nẽman yin fitina da tãwĩlinsa. Kuma bãbu wanda ya
san tãwĩlinsafãce Allah. Kuma matabbata a cikin ilmi sunã cẽwa: "Mun yi ĩmãni da
Shi; dukkansa daga wurin Ubangijinmu yake." Kuma bãbu mai tunãni fãce ma'abũta
hankula.
Kamar ɗabi'ar mutãnen Fir'auna da waɗanda ke a gabãninsu, sun ƙaryata ãyõyinMu,
sai Allah Ya kãmã su sabõda zunubansu, kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne.
"Lalle ne wata ãyã tã kasance a gare ku a cikin ƙungiyõyi biyu da suka haɗu;
ƙungiya guda tana yãƙi a cikin hanyar Allah, da wata kãfira, suna ganin su ninki
biyu nãsu, a ganin ido. Kuma Allah Yana ƙarfafa wanda Yake so da taimakonSa.
Lalle ne a cikin wannan, hakĩƙa, akwai abin kula ga maabũta basĩra.
An ƙawata wa mutãne son sha'awõyi daga mãtã da ɗiya da dũkiyõyi abũbuwan tãrãwa
daga zinariya da azurfa, da dawãki kiwãtattu da dabbõbin ci da hatsi. Wannan shi
ne dãɗin rãyuwar dũniya. Kuma Allah a wurinsa kyakkyãwar makõma take.
Ka ce: Shin kuma, in gaya muku mafi alhẽri daga wannan? Akwai gidãjen Aljanna a
wurin Ubangiji sabõda waɗanda suka bi Shi da taƙawa, kõguna suna gudãna daga
ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, da mãtan aure tsarkakakku, da yarda daga
Allah. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa.
Allah Ya shaida cẽwa: Lalle ne bãbu abin bautãwa fãce Shi kuma malãiku da
ma'abũta ilmi sun shaida, yana tsaye da ãdalci, bãbu abin bautãwa face Shi,
Mabuwãyi, Mai hikima.
Lalle ne, addini a wurin Allah, Shi ne Musulunci. Kuma waɗanda aka bai wa
Littafi ba su sãɓã ba, fãce a bãyan ilmi ya je musu, bisa zãlunci a tsakãninsu.
Kuma wanda ya kãfirta da ãyõyin Allah, to, lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako
ne.
To, idan sun yi musu da kai, sai ka ce: "Nã sallama fuskata ga Allah, kuma wanda
ya bi ni (haka)." Kuma ka ce wa waɗanda aka bai wa littãfi da Ummiyyai: "Shin
kun sallama?" To, idan sun sallama, haƙĩƙa, sun shiryu kuma idan sun jũya, to,
kawai abinda ke kanka, shi ne iyarwa. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa.
Lalle ne waɗanda suke kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Annabãwa bã da
wani hakki ba, kuma suna kashe waɗanda ke umurni da yin ãdalci daga mutãne, to,
ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
Shin, ba ka ga waɗanda aka bai wa rabo daga littãfi ba ana kiran su zuwa ga
Littãfin Allah dõmin ya yi hukunci a tsakãninsu sa'an nan wata ƙungiya daga
cikinsu ta jũya bãya, kuma sunã mãsu bijirẽwa?
Wannan kuwa, dõmin lalle ne su sun ce: "Wutã bã zã ta shãfe mu ba, fãce a 'yan
kwãnaki ƙidãyayyu." Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya rũɗẽ su
a cikin addininsu.
To, yãya idan Mun tãra su a yini wanda bãbu shakka a cikinsa, kuma aka cikã wa
kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta, alhãli kuwa, sũ bã zã a zãlunce su
ba?
Ka ce: "Yã Allah Mamallakin mulki, Kanã bayar da mulki ga wanda Kake so, Kanã
zãre mulki daga wanda Kake so, kuma Kanã buwãyar da wanda Kake so, kuma Kanã
ƙasƙantar da wanda Kake so, ga hannunKa alhẽri yake. Lalle ne Kai, a kan kõwane
abu, Mai ĩkon yi ne." "Kanã shigar da dare a cikin yini, kuma Kanã shigar da
yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga mamaci, kuma Kanã fitar da
mamaci daga mai rai, kuma Kanã azurta wanda Kake so bã da lissafi ba."
"Kanã shigar da dare a cikin yini, kuma Kanã shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga mamaci, kuma Kanã fitar da mamaci daga mai rai, kuma Kanã azurta wanda Kake so bã da lissafi ba."
Kada mũminai su riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Kuma wanda ya yi wannan,
to, bai zama a cikin kõme ba daga Allah, fãce fa dõmin ku yi tsaro daga gare su
da 'yar kãriya. Kuma Allah yana tsõratar da ku kanSa. Kuma zuwa ga Allah makõma
take.
Ka ce: "Idan kun ɓõye abin da ke a cikin ƙirãzanku, kõ kuwa kun bayyana shi,
Allah Yana sanin sa. Kuma Yana sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasa. Kuma
Allah a kan kõwane abu Mai ĩkon yi ne."
A Rãnar da kõwane rai yake sãmun abin da ya aikata daga alhẽri, a halarce, da
kuma abin da ya aikata daga sharri, alhãli yana gũrin, dã dai lalle a ce akwai
fage mai nĩsa a tsakãninsa da abin daya aikata na sharrin! Kuma Allah Yanã
tsõratar da kũ kanSa. Kuma Allah Mai tausayi ne ga bãyinSa.
A lõkacin da mãtar Imrãna ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ni, nã yi bãkancen abin
da ke cikin cikĩna gare Ka; ya zama 'yantacce, sai Ka karɓa daga gare ni. Lalle
ne Kai, Kai ne Mai ji, Masani."
To, a lõkacin da ta haife ta sai ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne nĩ, nã haife ta
mace!"KumaAllah ne Mafi sanin abin da ta haifa." Kuma namiji bai zama kamar mace
ba. Kuma nĩ nã yi mata suna Maryamu kuma lalle ne ni, ina nẽma mata tsari gare
Ka, ita da zũriyarta daga Shaiɗan jẽfaffe."
Sai Ubangijinta Ya karɓe ta karɓa mai kyau. Kuma Ya yabanyartar da ita
yabanyartarwa mai kyau, kuma Ya sanya rẽnonta ga Zakariyya. Ko da yaushe
Zakariyya ya shiga masallãci, a gare ta, sai ya sãmi abinci a wurinta. (Sai
kuwa) ya ce: "Yã Maryamu! Daga ina wannan yake gare ki?" (Sai) ta ce: "Daga
wurin Allah yake. Lalle ne Allah yana azurta wanda Ya so ba da lissafi ba."
Sai malã'iku suka kirãye shi, alhãli kuwa shĩ yanã tsaye yana salla a cikin
masallãci. (Suka ce), "Lalle ne Allah yana bã ka bushãra da Yahaya, alhãli yana
mai gaskatãwar wata kalma daga Allah, kuma shugaba, kuma tsarkakke kuma annabi
daga sãlihai."
Ya ce: "Yã Ubangijina! Yãya yãro zai sãmu a gare ni, alhãli kuwa, lalle tsũfa ya
sãme ni,kuma mãtãta bakarãriya ce?" Allah ya ce, "Kamar hakan ne, Allah yana
aikata abin da Yake so."
Ya ce: "Yã Ubangijinã! Ka sanya mini wata alãma!" (Allah) Ya ce "Alãmarka ita ce
ba zã ka iya yi wa mutãne magana ba har yini uku face da ishãra. Sai ka ambaci
Ubangijinka da yawa. Kuma ka yi tasbĩhi da marece da sãfe."
Wannan yana daga lãbarun gaibi, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka (Muhammadu). Ba
ka kasance ba a wurinsu a lõkacin da suke jẽfa alƙalumansu (domin ƙuri'a) wãne
ne zai yi rẽnon Maryam. Kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke ta yin
husũma .
A lõkacin da malã'iku suka ce "Yã Maryamu! Lalle ne Allah Yana bã ki bushãra da
wata kalma daga gare Shi; sũnansa Masĩhu ĩsa ɗan Maryama, yana mai daraja a
dũniya da Lãhira kuma daga Makusanta.
Ta ce: "Yã Ubangijina! Yãya yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa wani mutum
bai shãfe ni ba?" (Allah) Ya ce: "Kamar wannan ne, Allah yana halittar abin da
Yake so. Idan Ya hukunta wani al'amari, sai ya ce masa, "Ka kasance!, Sai yana
kasancẽwa."
Kuma (Ya sanya shi) manzo zuwa ga Bani Isrãila'ĩla (da sãko, cẽwa), Lalle ne, ni
haƙĩƙa nã zõ muku, da wata ãyã daga Ubangijinku. Lalle ne ni ina halitta muku
daga lãka, kamar siffar tsuntsu sa'an nan in hũra a cikinsa, sai ya kasance
tsuntsu, da izinin Allah. Kuma ina warkar da wanda aka haifa makãho da kuturu,
kuma ina rãyar da matottu, da izibin Allah. Kuma ina gayã muku abin da kuke ci
da abin da kuke ajiyẽwa acikin gidãjenku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyã a
gare ku, idan kun kasance mãsu yin ĩmãni.
"Kuma inã mai gaskatãwa ga abin da yake a gabãnina daga Taurata. Kuma (nãzo)
dõmin in halatta muku sãshen abin da aka haramta muku. Kuma nã tafo muku da wata
ãyã daga Ubangijinku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.
To, a lõkacin da Ĩsa ya gane kãfirci daga gare su, sai ya ce: "Su wãne ne
mataimakãna zuwa ga Allah?" Hawãriyãwa suka ce: "Mu ne mataimakan Allah. Mun yi
ĩmani da Allah. Kuma ka shaida cẽwa lalle ne mu, mãsu sallamãwa ne.
A lõkacin da Ubangiji Ya ce: "Ya Ĩsa! Lalle NĨ Mai karɓar ranka ne, kuma Mai
ɗauke ka ne zuwa gare Ni, kuma Mai tsarkake ka daga waɗanda suka kãfirta, kuma
Mai sanya waɗanda suka bĩ ka a bisa waɗanda suka kãfirta har Rãnar ¡iyãma. Sa'an
nan kuma zuwa gare Ni makõmarku take, sa'an nan in yi hukunci a tsakãninku, a
cikin abin da kuka kasance kuna sãɓã wa jũna.
Lalle ne misãlin Ĩsã a wurin Allah kamar misãlin Ãdama ne, (Allah) Yã halitta
shi daga turɓãya, sa'an nan kuma Ya ce masa: "Ka kasance: "Sai yana kasancewa.
To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, to
ka ce: "Ku zo mu kirãyi, 'yã'yanmu da 'yã'yanku da mãtanmu da mãtanku da kanmu
da kanku sa'an nan kuma mu ƙanƙantar da kai sa'an nan kuma mu sanya la'anar,
Allah a kan maƙaryata."
Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi! Ku tafo zuwa ga kalma mai daidaitãwa a tsakã
ninmu da ku; kada mu bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme da Shi,
kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe Ubangiji, baicin Allah." To, idan sun jũya bã
ya sai ku ce: "ku yi shaida cẽwa, lalle ne mu masu sallamã wa ne."
Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuke hujjacẽwa a cikin sha'anin lbrãhĩma, alhãli kuwa
ba a saukar da Attaura da injĩla ba fãce daga bãyansa? Shin bã ku hankalta?
Gã ku yã waɗannan! Kun yi hujjacẽwa a cikin abin da yake kunã da wani ilmi game
da shi, to, don me kuma kuke yin hujjacẽwa a cikin abin da bã ku da wani ilmi
game da shi? Allah yana sani, kuma kũ, ba ku sani ba!
Ibrãhĩma bai kasance Bayahũde ba, kuma bai kasance Banasãre ba, amma yã kasance
mai karkata zuwa ga gaskiya, mai sallamãwa, kuma bai kasance daga mãsu shirki
ba.
Lalle ne mafi hakkin mutãne da Ibrãhĩma haƙĩƙa, sũ ne waɗanda suka bi shi a
(zamaninsa) da wannan Annabi (Muhammadu) da waɗanda suka yi ĩmãni.Kuma Allah ne
Majiɓincin mũminai.
Kuma wata ƙungiya daga Mutãnen Littãfi ta ce: "Ku yi ĩmãni da abin da aka saukar
a kan waɗanda suka yi ĩmãni (da Muhammadu) a farkon yini, kuma ku kãfirta a
ƙarshensa; tsammãninsu, zã su kõmõ."
"Kada ku yi ĩmãni fãce da wanda ya bi addininku." Ka ce: "Lalle ne, shiriya ita
ce shiriyar Allah. (Kuma kada ku yi ĩmãni) cẽwa an bai wa wani irin abin da aka
bã ku, kõ kuwa su yi musu da ku a wurin Ubangijinku." Ka ce: "Lalle ne falala ga
hannun Allah take, yana bãyar da ita ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadãci ne,
Masani."
Kuma daga Mutãnen Littãfi akwai wanda yake idan ka bã shi amãnar kinɗãri , zai
bãyar da shi gare ka, kuma daga gare su akwai wanda idan ka bã shi amãnar
dĩnari, bã zai bãyar da shi gare ka ba, fãce idan kã dawwama a kansa kanã tsaye.
Wannan kuwa, dõmin lalle ne sũ sun ce, "Bãbu laifi a kanmu a cikin Ummiyyai."
Suna faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa suna sane.
Lalle ne waɗanda suke sayen 'yan tamani kaɗan da alkawarin Allah da
rantsuwõyinsu, waɗannan bãbu wani rabo a gare su a Lãhira, Kuma Allah bã Ya yin
magana da su, kuma bã Ya dũbi zuwa gare su, a Rãnar ¡iyãma, kuma bã Ya tsarkake
su, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.
Kuma lalle ne, daga gare su akwai wata ƙungiya suna karkatar da harsunansu da
Littãfi dõmin ku yi zaton sa daga Littãfin, alhãli kuwa bã shi daga Littãfin.
Kuma suna cẽwa: "Shi daga wurinAllah yake." Alhãli kuwa shi, bã daga wurin Allah
yake ba. Sunã faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa sunã sane.
Ba ya yiwuwa ga wani mutum, Allah Ya bã shi Littãfi da hukunci da Annabci, sa'an
nan kuma ya ce wa mutãne: "Ku kasance bãyi gare ni, baicin Allah." Amma (zai
ce): "Ku kasance mãsu aikin ibãda da abin da kuka kasance kuna karantar da
Littãfin, kuma da abin da kuka kasance kuna karantãwa ."
Kuma ba ya umurnin ku da ku riƙi malã'iku da annabãwa lyãyengiji. Shin, zai
umurce ku da kãfirci ne a bãyan kun riga kun zama mãsu sallamãwa (Musulmi)?
Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin Annabãwa: "Lalle ne ban bã ku wani abu
ba daga Littãfi da hikima, sa'an nan kuma wani manzo ya je muku, mai gaskatãwa
ga abin da yake tãre da ku; lalle ne zã ku gaskata Shi, kuma lalle ne zã ku
taimake shi." Ya ce: "Shin, kun tabbatar kuma kun riƙi alkawarĩNa a kan wannan a
gare ku?" suka ce: "Mun tabbatar." Ya ce: "To, ku yi shaida, kuma Nĩ a tãre da
ku Inã daga mãsu shaida."
Shin wanin Addinin Allah suke nẽma, alhãli kuwa a gare Shi ne waɗanda ke cikin
sama da ƙasa suka sallama wa, a kan sõ da ƙĩ, kuma zuwa gare Shi ake mayar da
su?
Ka ce: "Mun yi ĩmãni da Allah kuma da abin da aka saukar mana da abin da aka
saukar wa Ibrãhĩma da Isma'ĩla da Is'hãƙa da Yãƙũba da jĩkõki, da abin da aka
bai wa Mũsã da ĩsã da annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu bambantãwa a tsakãnin
kõwa daga gare su. Kuma mũ, zuwa gare Shi mãsu sallamãwa ne."
Yãya Allah zai shiryar da mutãne waɗanda suka kãfirta a bãyan ĩmãninsu, kuma sun
yi shaidar cẽwa, lalle Manzo gaskiya ne, kuma hujjõji bayyanannu sun je musu?
Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
Lalle ne wanɗanda suka kãfirta, kuma suka mutu alhãli kuwa suna kãfirai to bã zã
a karɓi cike da ƙasa na zinãri daga ɗayansu ba, kõ dã ya yi fansa da shi,
waɗannan sunã da azãba mai raɗaɗi, kuma bã su da wasu mataimaka.
Dukan abinci yã kasance halal ne ga Bani lsrã'ĩla, fãce abinda Isrã'ĩla ya
haramta wa kansadaga gabãnin saukar da Attaura. Ka ce: "To, ku zo da Attaura
sa'an nan ku karantã ta, idan kun kasance mãsu gaskiya ne.
A cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu; (ga misãli) matsayin Ibrãhĩma. Kuma wanda ya
shige shi yã kasance amintacce. Kuma akwai hajjin ¦ãkin dõmin Allah a kan
mutãne, ga wanda ya sãmi ĩkon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lalle
Allah Mawadãci ne daga barin tãlikai.
Ka ce: "Ya ku Mutãnen Littãfi! Don me kuke taushe wanda ya yi ĩmani, daga hanyar
Allah, kuma kunã nẽman ta zama karkatacciya, alhãli kuwa kunã mãsu shaida? Kuma
Allah bai gushe daga abin da kuke aikatãwa ba yana Masani."
Kuma yãyã kuke kãfircẽwa alhãli kuwa anã karanta ãyõyin Allah a gare ku, kuma a
cikinku akwai manzonSa? Kuma wanda ya nẽmi tsari da Allah, to, an shiryar da shi
zuwa ga hanya miƙaƙƙiya.
Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gabã ɗaya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna
ni'imar Allah a kanku a lõkacin da kuka kasance maƙiya sai Ya sanya sõyayya a
tsakãnin zukãtanku sabõda haka kuka wãyi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun
kasance a kan gãɓar rãmi na wutã sai Ya tsãmar da ku daga gare ta, Kamar wannan
ne Allah Yake bayyana muku ayõyinSa, tsammãninku, zã ku shiryu.
Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alhẽri, kuma suna
umurnida alhẽri, kuma suna hani dagaabin da ake ƙi. Kuma waɗannan, sũ ne mãsu
cin nasara.
A rãnar da wasu fuskõki suke yin fari kuma wasu fuskõki suke yin baƙi (zã a ce
wa waɗanda fuskokinsu suke yin baƙin): "Shin kun kãfirta a bayan ĩmãninku? Don
haka sai ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kasance kuna yi na kãfirci."
Kun kasance mafi alhẽrin al'umma wadda aka fitar ga mutãne kuna umurni da alhẽri
kuma kunã hani daga abin da ake ƙi, kuma kunã ĩmãni da Allah. Kuma dã Mutãnen
Littãfi sun yi ĩmãni, lalle ne, dã (haka) yã kasance mafi alhẽri a gare su. Daga
cikinsu akwai mũminai, kuma mafi yawansufãsiƙai ne.
An dõka ƙasƙanci a kansu a inda duk aka sãme su fãce da wani alkawari daga
Allah, da alkawari daga mutãne. Kuma sun kõma da fushi daga Allah, kuma aka dõka
talauci a kansu. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle sun kasance suna kãfirta da ãyõyin
Allah, kuma suna kashe annabãwa, bã da wani haƙƙi ba. Wannan kuwa dõmin sãɓãwar
da suka yi ne, kuma sun kasance suna yin ta'adi.
Ba su zama daidai ba; daga Mutãnen Littafi akwai wata al'umma wadda take tsaye,
suna karãtun ayõyin Allah a cikin sã'õ'in dare, alhãli kuwa sunã yin sujada.
Suna ĩmãni da Allah da Yinin Lãhira, kuma suna umurui da abin da aka sani kuma
suna hani daga abin da ba a sani ba, kuma sunã gaugãwa a cikin alhẽrai. Kuma
waɗannan suna cikin sãlihai.
Lalle ne waɗanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu kõ ɗiyansu bã zã su wadatar musu da
kõme ba daga Allah kuma waɗannan abõkan wuta ne, sũ, acikinta, madawwama ne.
Misãlin abin da suke ciyarwa, a cikin wannan rãyuwar dũniya, kamar misãlin iska
ce (wadda) a cikinta akwai tsananin sanyi, ta sãmi shukar wasu mutãne waɗanda
suka zãlunci kansu, sai ta halakar da ita. Allah bai zãlunce su ba, amma kansu
suka kasance sunã zãlunta.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi abõkan asĩri daga waninku, ba su
taƙaita muku ɓarna. Kuma sun yi gũrin abin da zã ku cũtu da shi. Haƙĩka, ƙiyayya
tã bayyana daga bãkunansu, kuma abin da zukãtansu ke ɓõyẽwane mafi girma. Kuma
lalle ne, Mun bayyana muku ãyõyi, idan kun kasance kunã hankalta.
Gã ku yã waɗannan! Kunã son su bã su son ku, kuma kuna ĩmãni da Littãfi dukansa.
Kuma idan sun haɗu da ku sukan ce "Mun yi ĩmani". Kuma idan sun kaɗaita sai su
ciji yãtsu a kanku don takaici. Ka ce "Ku mutu da takaicinku. Lalle ne, Allah
Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza."