« Prev

33. Surah Al­Ahzâb سورة الأحزاب

Next »First Ayah   1   الأية الأولي
بِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ اتَّقِ اللَّهَ وَلَا تُطِعِ الْكَافِرِينَ وَالْمُنَافِقِينَ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمًا
Hausa
 
Yă kai Annabi! Ka bi Allah da taƙawa, kuma kada ka yi ɗă'ă ga kăfirai da munăfukai. Lalle, Allah Ya kasance Mai ilmi, Mai hikima.

Ayah   33:2   الأية
وَاتَّبِعْ مَا يُوحَىٰ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرًا
Hausa
 
Kuma ka bi abin da aka yi wahayi da shi zuwa gare ka daga Ubangijinka. Lalle, Allah Ya kasance Mai labartawa ga abin da kuke aikatawa.

Ayah   33:3   الأية
وَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ ۚ وَكَفَىٰ بِاللَّهِ وَكِيلًا
Hausa
 
Ka dőgara ga Allah. Kuma Allah Ya isa Ya zama wakĩli.

Ayah   33:4   الأية
مَّا جَعَلَ اللَّهُ لِرَجُلٍ مِّن قَلْبَيْنِ فِي جَوْفِهِ ۚ وَمَا جَعَلَ أَزْوَاجَكُمُ اللَّائِي تُظَاهِرُونَ مِنْهُنَّ أُمَّهَاتِكُمْ ۚ وَمَا جَعَلَ أَدْعِيَاءَكُمْ أَبْنَاءَكُمْ ۚ ذَٰلِكُمْ قَوْلُكُم بِأَفْوَاهِكُمْ ۖ وَاللَّهُ يَقُولُ الْحَقَّ وَهُوَ يَهْدِي السَّبِيلَ
Hausa
 
Allah bai sanya zũciya biyu ba ga wani namiji a cikinsa, kuma bai sanya mătanku waɗanda kuke yin zihări daga gare su, su zama uwăyenku ba, kuma bai sanya ɗiyan hankăkarku su zama ɗiyanku ba. wannan abu năku, maganarku ce da băkunanku alhăli kuwa Allah na faɗar gaskiya, kuma Shĩ ne ke shiryarwa ga hanyar ƙwarai.

Ayah   33:5   الأية
ادْعُوهُمْ لِآبَائِهِمْ هُوَ أَقْسَطُ عِندَ اللَّهِ ۚ فَإِن لَّمْ تَعْلَمُوا آبَاءَهُمْ فَإِخْوَانُكُمْ فِي الدِّينِ وَمَوَالِيكُمْ ۚ وَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ فِيمَا أَخْطَأْتُم بِهِ وَلَٰكِن مَّا تَعَمَّدَتْ قُلُوبُكُمْ ۚ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Ku kira su ga ubanninsu, shi ne mafi ădalci a wurin Allah. To, idan ba ku san ubanninsu ba, to, 'yan'uwanku ga addini da dĩmajojinku. Kuma băbu laifi a gare ku ga abin da kuka yi kuskure da shi, kuma amma (akwai laifi) ga abin da zukătanku suka ganganta, kuma Allah Ya kasance Mai găfara, Mai jin ƙai.

Ayah   33:6   الأية
النَّبِيُّ أَوْلَىٰ بِالْمُؤْمِنِينَ مِنْ أَنفُسِهِمْ ۖ وَأَزْوَاجُهُ أُمَّهَاتُهُمْ ۗ وَأُولُو الْأَرْحَامِ بَعْضُهُمْ أَوْلَىٰ بِبَعْضٍ فِي كِتَابِ اللَّهِ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُهَاجِرِينَ إِلَّا أَن تَفْعَلُوا إِلَىٰ أَوْلِيَائِكُم مَّعْرُوفًا ۚ كَانَ ذَٰلِكَ فِي الْكِتَابِ مَسْطُورًا
Hausa
 
Annabi ne mafi cancanta ga mũminai bisa ga su kansu, kuma mătansa uwăyensu ne. Kuma ma'abuta zumunta waɗansunsu sun fi waɗansu a cikin Littăfin Allah bisa ga mũminai da Muhăjirai, făce fa idan kun aikata wani alhẽri zuwa ga majiɓintanku. Wancan yă kasance a cikin Littafi, rubũtacce.

Ayah   33:7   الأية
وَإِذْ أَخَذْنَا مِنَ النَّبِيِّينَ مِيثَاقَهُمْ وَمِنكَ وَمِن نُّوحٍ وَإِبْرَاهِيمَ وَمُوسَىٰ وَعِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ ۖ وَأَخَذْنَا مِنْهُم مِّيثَاقًا غَلِيظًا
Hausa
 
Kuma a lőkacin da Muka riƙi alkawarin Annabawa daga gare su, kuma daga gare ka, kuma daga Nũhu da Ibrăhĩm da Mũsa da kuma Ĩsă ɗan Maryama,kuma Muka riƙi wani alkawari mai kauri daga gare su.

Ayah   33:8   الأية
لِّيَسْأَلَ الصَّادِقِينَ عَن صِدْقِهِمْ ۚ وَأَعَدَّ لِلْكَافِرِينَ عَذَابًا أَلِيمًا
Hausa
 
Dőmin Ya tambayi măsu gaskiya a kan gaskiyarsu, kuma Yă yi tattalin wata azăba mai raɗaɗi ga kăfirai.

Ayah   33:9   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا نِعْمَةَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ جَاءَتْكُمْ جُنُودٌ فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ رِيحًا وَجُنُودًا لَّمْ تَرَوْهَا ۚ وَكَانَ اللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرًا
Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lőkacin da waɗansu rundunőni suka zo muku, sai Muka aika wata iskă a kansu da waɗansu rundunőni waɗanda ba ku gani ba, Kuma Allah Yă kasance Mai gani ga abin da kuke aikatăwa.

Ayah   33:10   الأية
إِذْ جَاءُوكُم مِّن فَوْقِكُمْ وَمِنْ أَسْفَلَ مِنكُمْ وَإِذْ زَاغَتِ الْأَبْصَارُ وَبَلَغَتِ الْقُلُوبُ الْحَنَاجِرَ وَتَظُنُّونَ بِاللَّهِ الظُّنُونَا
Hausa
 
A lőkacin da suka zo muku daga samanku da kuma ƙasa daga gare ku, kuma a lőkacin da gannai suka karkata kuma zukăta suka kai ga maƙősai, kuma kuka yi zaton zace-zace, game da Allah.

Ayah   33:11   الأية
هُنَالِكَ ابْتُلِيَ الْمُؤْمِنُونَ وَزُلْزِلُوا زِلْزَالًا شَدِيدًا
Hausa
 
A can aka jarrabi mũminai, kuma aka yi girgiza da su, girgiza mai tsanani.

Ayah   33:12   الأية
وَإِذْ يَقُولُ الْمُنَافِقُونَ وَالَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ مَّا وَعَدَنَا اللَّهُ وَرَسُولُهُ إِلَّا غُرُورًا
Hausa
 
Kuma a lőkacin da munafukai da waɗanda akwai cũta a cikin zukătansu ke cẽwa, Allah da ManzonSa, "Ba su yi mana wa'adin kőme ba, făce rũɗi."

Ayah   33:13   الأية
وَإِذْ قَالَت طَّائِفَةٌ مِّنْهُمْ يَا أَهْلَ يَثْرِبَ لَا مُقَامَ لَكُمْ فَارْجِعُوا ۚ وَيَسْتَأْذِنُ فَرِيقٌ مِّنْهُمُ النَّبِيَّ يَقُولُونَ إِنَّ بُيُوتَنَا عَوْرَةٌ وَمَا هِيَ بِعَوْرَةٍ ۖ إِن يُرِيدُونَ إِلَّا فِرَارًا
Hausa
 
Kuma a lőkacin da wata ƙungiya daga gare su, ta ce, "Ya mutănen Yasriba! Bă ku da wani matsayi, sabőda haka ku kőma." Kuma wata ƙungiya daga gare su na nẽman izni ga Annabi sunăcẽwa, "Lalle gidăjenmu kuranye suke," alhăli kuwa bă kuranye suke ba, bă su da nufin kome făce gudu.

Ayah   33:14   الأية
وَلَوْ دُخِلَتْ عَلَيْهِم مِّنْ أَقْطَارِهَا ثُمَّ سُئِلُوا الْفِتْنَةَ لَآتَوْهَا وَمَا تَلَبَّثُوا بِهَا إِلَّا يَسِيرًا
Hausa
 
Kuma dă an shige ta (Madĩna) a kansu, daga sasanninta, sa'an nan aka tambaye su fitina (kăfirci), lalle dă sun jẽ mata, kuma dă ba su zauna a cikinta (Madĩna) ba făce kaɗan.

Ayah   33:15   الأية
وَلَقَدْ كَانُوا عَاهَدُوا اللَّهَ مِن قَبْلُ لَا يُوَلُّونَ الْأَدْبَارَ ۚ وَكَانَ عَهْدُ اللَّهِ مَسْئُولًا
Hausa
 
Kuma lalle haƙĩƙa, sun kasance sună yi wa Allah alkawari, a gabănin wannan; Bă ză su jũya dőmin gudu ba, kuma alkawarin Allah ya kasance abin tambaya.

Ayah   33:16   الأية
قُل لَّن يَنفَعَكُمُ الْفِرَارُ إِن فَرَرْتُم مِّنَ الْمَوْتِ أَوِ الْقَتْلِ وَإِذًا لَّا تُمَتَّعُونَ إِلَّا قَلِيلًا
Hausa
 
Ka ce: "Gudun nan bă zai amfăne ku ba daga mutuwa ko kisa. Kuma har in kun gudu, bă ză a jĩshe ku dăɗĩ ba făce kaɗan."

Ayah   33:17   الأية
قُلْ مَن ذَا الَّذِي يَعْصِمُكُم مِّنَ اللَّهِ إِنْ أَرَادَ بِكُمْ سُوءًا أَوْ أَرَادَ بِكُمْ رَحْمَةً ۚ وَلَا يَجِدُونَ لَهُم مِّن دُونِ اللَّهِ وَلِيًّا وَلَا نَصِيرًا
Hausa
 
Ka ce: "Wăne ne wanda yake tsare ku daga Allah, idan Yă yi nufin wata cũta game da ku?" Kuma bă ză su sămar wa kansu wani majiɓinci ba, banda Allah, kuma bă ză su sămar wa kansu wani mataimaki ba.

Ayah   33:18   الأية
قَدْ يَعْلَمُ اللَّهُ الْمُعَوِّقِينَ مِنكُمْ وَالْقَائِلِينَ لِإِخْوَانِهِمْ هَلُمَّ إِلَيْنَا ۖ وَلَا يَأْتُونَ الْبَأْسَ إِلَّا قَلِيلًا
Hausa
 
Lalle Allah Ya san măsu hana mutăne fita daga cikinku, da măsu cẽwa ga 'yan'uwansu,"Ku zo nan a wurinmu." Kuma bă ză su shiga yăƙi ba făce kaɗan.

Ayah   33:19   الأية
أَشِحَّةً عَلَيْكُمْ ۖ فَإِذَا جَاءَ الْخَوْفُ رَأَيْتَهُمْ يَنظُرُونَ إِلَيْكَ تَدُورُ أَعْيُنُهُمْ كَالَّذِي يُغْشَىٰ عَلَيْهِ مِنَ الْمَوْتِ ۖ فَإِذَا ذَهَبَ الْخَوْفُ سَلَقُوكُم بِأَلْسِنَةٍ حِدَادٍ أَشِحَّةً عَلَى الْخَيْرِ ۚ أُولَٰئِكَ لَمْ يُؤْمِنُوا فَأَحْبَطَ اللَّهُ أَعْمَالَهُمْ ۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرًا
Hausa
 
Suna măsu rőwa gare ku, sa'an nan idan tsőro ya zo, sai ka gan su sună kallo zuwa gare ka, idănunsu sună kẽwaya, kamar wanda ake rufe hankalinsa sabőda mutuwa. Sa'an nan idan tsőron ya tafi,sai su yi muku miyăgun maganganu da harussa măsu kaifi, sună măsu rőwa a kan dũkiya. Waɗannan, ba su yi ĩmani ba, sabőda hakaAllah Ya ɓăta ayyukansu. Kuma wannan ya kasance mai sauƙi ga Allah.

Ayah   33:20   الأية
يَحْسَبُونَ الْأَحْزَابَ لَمْ يَذْهَبُوا ۖ وَإِن يَأْتِ الْأَحْزَابُ يَوَدُّوا لَوْ أَنَّهُم بَادُونَ فِي الْأَعْرَابِ يَسْأَلُونَ عَنْ أَنبَائِكُمْ ۖ وَلَوْ كَانُوا فِيكُم مَّا قَاتَلُوا إِلَّا قَلِيلًا
Hausa
 
Sună zaton ƙungiyőyin kăfirai ba su tafi ba. Kuma idan ƙungiyőyin kăfirai sun zo, sună gũrin da dai sun zama a karkara a cikin ƙauyăwa, sună tambayar lăbăranku. Kuma kő dă sun kasance a cikinku, bă ză su yi yăƙi ba, făce kaɗan.

Ayah   33:21   الأية
لَّقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ لِّمَن كَانَ يَرْجُو اللَّهَ وَالْيَوْمَ الْآخِرَ وَذَكَرَ اللَّهَ كَثِيرًا
Hausa
 
Lalle, abin kőyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasanee yană fătan rahamar Allah da Rănar Lăhira, kuma ya ambaci Allah da yawa.

Ayah   33:22   الأية
وَلَمَّا رَأَى الْمُؤْمِنُونَ الْأَحْزَابَ قَالُوا هَٰذَا مَا وَعَدَنَا اللَّهُ وَرَسُولُهُ وَصَدَقَ اللَّهُ وَرَسُولُهُ ۚ وَمَا زَادَهُمْ إِلَّا إِيمَانًا وَتَسْلِيمًا
Hausa
 
Kuma a lőkacin da mũminai suka ga ƙungiyőyin kăfirai, sai suka ce, "Wannan ne abin da Allah da ManzonSa suka yi mana wa'adi, Allah da ManzonSa sunyi gaskiya." Kuma wannan bai ƙăra musu kőme ba făce ĩmăni da sallamăwa.

Ayah   33:23   الأية
مِّنَ الْمُؤْمِنِينَ رِجَالٌ صَدَقُوا مَا عَاهَدُوا اللَّهَ عَلَيْهِ ۖ فَمِنْهُم مَّن قَضَىٰ نَحْبَهُ وَمِنْهُم مَّن يَنتَظِرُ ۖ وَمَا بَدَّلُوا تَبْدِيلًا
Hausa
 
Daga mũminai akwai waɗansu mazăje da suka gaskata abin da suka yi wa Allah alkwari a kansa, sa'an nan a cikinsu, akwai wanda ya biya bukătarsa, kuma daga cikinsu akwai wanda ke jira. Kuma ba su musanya ba, musanyawa.

Ayah   33:24   الأية
لِّيَجْزِيَ اللَّهُ الصَّادِقِينَ بِصِدْقِهِمْ وَيُعَذِّبَ الْمُنَافِقِينَ إِن شَاءَ أَوْ يَتُوبَ عَلَيْهِمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Dőmin Allah Ya săka wa masu gaskiya da gakiyarsu, kuma Ya azabtar da munafukai idan Ya so, ko Ya karɓi tũba a kansu. Lalle, Allah Ya kasance Mai găfara, Mai jin ƙai.

Ayah   33:25   الأية
وَرَدَّ اللَّهُ الَّذِينَ كَفَرُوا بِغَيْظِهِمْ لَمْ يَنَالُوا خَيْرًا ۚ وَكَفَى اللَّهُ الْمُؤْمِنِينَ الْقِتَالَ ۚ وَكَانَ اللَّهُ قَوِيًّا عَزِيزًا
Hausa
 
Kuma Allah Yă mayar da waɗanda suka kăfirta da fushinsu, ba su sămi wani alhẽri ba. Allah Ya isar wa mũminai daga barin yăƙi. Kuma Allah Ya kasance Mai ƙarfi, Mabuwăyi.

Ayah   33:26   الأية
وَأَنزَلَ الَّذِينَ ظَاهَرُوهُم مِّنْ أَهْلِ الْكِتَابِ مِن صَيَاصِيهِمْ وَقَذَفَ فِي قُلُوبِهِمُ الرُّعْبَ فَرِيقًا تَقْتُلُونَ وَتَأْسِرُونَ فَرِيقًا
Hausa
 
Kuma Ya saukar da waɗannan da suka taimake su daga mazőwa Littăfi, daga birănensu, kuma Ya jẽfa tsőro a cikin zukatansu; wata ƙungiya kună kashẽwa, kuma kună kăma wata ƙungiyar.

Ayah   33:27   الأية
وَأَوْرَثَكُمْ أَرْضَهُمْ وَدِيَارَهُمْ وَأَمْوَالَهُمْ وَأَرْضًا لَّمْ تَطَئُوهَا ۚ وَكَانَ اللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرًا
Hausa
 
Kuma Ya gădar da ku gőnakinsu da gidăjensu da dũkiyőyinsu, da wata ƙasa wadda ba ku taɓa tăkarta bă. Kuma Allah ya kasance Mai ĩkon yi ne a kan kőme.

Ayah   33:28   الأية
يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُل لِّأَزْوَاجِكَ إِن كُنتُنَّ تُرِدْنَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا وَزِينَتَهَا فَتَعَالَيْنَ أُمَتِّعْكُنَّ وَأُسَرِّحْكُنَّ سَرَاحًا جَمِيلًا
Hausa
 
Yă kai Annabi! Ka ce wa matanka, "Idan kun kasance kună nufin răyuwar dũniya da ƙawarta, to, ku zo in yi muku kyautar ban kwăna kuma in sake ku, saki mai kyau."

Ayah   33:29   الأية
وَإِن كُنتُنَّ تُرِدْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَالدَّارَ الْآخِرَةَ فَإِنَّ اللَّهَ أَعَدَّ لِلْمُحْسِنَاتِ مِنكُنَّ أَجْرًا عَظِيمًا
Hausa
 
"Kuma idan kun kasance kună nufin Allah da Manzonsa da gidan Lăhria, to, lalle, Allah Yă yi tattalin wani sakamako mai girma ga măsu kyautatăwa daga gare ku."

Ayah   33:30   الأية
يَا نِسَاءَ النَّبِيِّ مَن يَأْتِ مِنكُنَّ بِفَاحِشَةٍ مُّبَيِّنَةٍ يُضَاعَفْ لَهَا الْعَذَابُ ضِعْفَيْنِ ۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرًا
Hausa
 
Yă mătan Annabi! Wadda ta zo da alfăsha bayyananna daga cikinku ză a ninka mata azăba ninki biyu. Kuma wancan yă kasance mai sauƙi ga Allah.

Ayah   33:31   الأية
وَمَن يَقْنُتْ مِنكُنَّ لِلَّهِ وَرَسُولِهِ وَتَعْمَلْ صَالِحًا نُّؤْتِهَا أَجْرَهَا مَرَّتَيْنِ وَأَعْتَدْنَا لَهَا رِزْقًا كَرِيمًا
Hausa
 
Kuma wadda ta yi tawăli'u daga cikinku ga Allah da ManzonSa, kuma ta aikata aiki na ƙwarai, ză Mu bă ta sakamakonta ninki biyu, kuma Mun yi mata tattalin arziki ma karimci.

Ayah   33:32   الأية
يَا نِسَاءَ النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِّنَ النِّسَاءِ ۚ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَّعْرُوفًا
Hausa
 
Yă mătan Annabĩ! Ba ku zama kamar kőwa ba daga mătă, idan kun yi taƙawa, sabőda haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cũta a cikin zuciyarsa ya yi ɗammani, kuma ku faɗi magana ta alheri.

Ayah   33:33   الأية
وَقَرْنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الْأُولَىٰ ۖ وَأَقِمْنَ الصَّلَاةَ وَآتِينَ الزَّكَاةَ وَأَطِعْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ ۚ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا
Hausa
 
Kuma ku tabbata a cikin gidăjenku, kuma kada ku yi fitar găye-găye irin fitar găye-găye ta jăhiliyyar farko. Kuma ku tsaĩ da salla, kuma ku băyar da zakka, ku yi ɗă,ă ga Allah da ManzonSa. Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, yă mutănen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa.

Ayah   33:34   الأية
وَاذْكُرْنَ مَا يُتْلَىٰ فِي بُيُوتِكُنَّ مِنْ آيَاتِ اللَّهِ وَالْحِكْمَةِ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ لَطِيفًا خَبِيرًا
Hausa
 
Kuma ku tuna abin da ake karantawa a cikin ɗăkunanku daga ăyőyin Allah da hukunci. Lalle Allah Yă kasance Mai tausasăwa Mai labartawa.

Ayah   33:35   الأية
إِنَّ الْمُسْلِمِينَ وَالْمُسْلِمَاتِ وَالْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ وَالْقَانِتِينَ وَالْقَانِتَاتِ وَالصَّادِقِينَ وَالصَّادِقَاتِ وَالصَّابِرِينَ وَالصَّابِرَاتِ وَالْخَاشِعِينَ وَالْخَاشِعَاتِ وَالْمُتَصَدِّقِينَ وَالْمُتَصَدِّقَاتِ وَالصَّائِمِينَ وَالصَّائِمَاتِ وَالْحَافِظِينَ فُرُوجَهُمْ وَالْحَافِظَاتِ وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا
Hausa
 
Lalle, Musulmi maza da Musulmi mătă da muminai maza da muminai mătă, da măsu tawăli'u maza da măsu tawălĩu mătăda măsu gaskiya maza da măsu gaskiya mătă, da măsu haƙuri maza da măsu haƙuri mătă, da măsu tsőron Allah maza da măsu tsőron Allah mătă, da măsu sadaka maza da măsu sadaka mătă, da măsu azumi maza da măsu azumi mătă da măsu tsare farjőjinsu maza da măsu tsare farjőjinsu mătă, da măsu ambaton Allah da yawa maza da măsu ambatonsa mătă, Allah Ya yi musu tattalin wata găfara da wani sakamako mai girma.

Ayah   33:36   الأية
وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَن يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ ۗ وَمَن يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا مُّبِينًا
Hausa
 
Kuma ba ya halatta ga mũmini kuma haka ga mũmina, a lőkacin da Allah da Manzonsa Ya hukunta wani umurni, wani zăɓi daga al'amarinsu ya kasance a gare su. Kuma wanda ya săɓă wa Allah da ManzonSa, to, yă ɓace, ɓacẽwa bayyananna.

Ayah   33:37   الأية
وَإِذْ تَقُولُ لِلَّذِي أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَيْهِ وَأَنْعَمْتَ عَلَيْهِ أَمْسِكْ عَلَيْكَ زَوْجَكَ وَاتَّقِ اللَّهَ وَتُخْفِي فِي نَفْسِكَ مَا اللَّهُ مُبْدِيهِ وَتَخْشَى النَّاسَ وَاللَّهُ أَحَقُّ أَن تَخْشَاهُ ۖ فَلَمَّا قَضَىٰ زَيْدٌ مِّنْهَا وَطَرًا زَوَّجْنَاكَهَا لِكَيْ لَا يَكُونَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ حَرَجٌ فِي أَزْوَاجِ أَدْعِيَائِهِمْ إِذَا قَضَوْا مِنْهُنَّ وَطَرًا ۚ وَكَانَ أَمْرُ اللَّهِ مَفْعُولًا
Hausa
 
Kuma a lőkacin da kake cẽwa ga wanda Allah Ya yi ni'ima a gare shi kai kuma ka yi ni'ima a gare shi, "Ka riƙe mătarka, kuma ka bi Allah da taƙawa," kuma kana ɓőyẽwa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana shi, kană tsőron mutăne, alhăli kuwa Allah ne Mafi cancantar ka ji tsőronSa. to a lőkacin da zaidu ya ƙăre bukătarsa daga gare ta, Mun aurar da kai ita, dőmin kada wani ƙunci ya kasance a kan mũminai a cikin (auren mătan) ɗiyan hankăkarsu, idan sun ƙăre bukăta daga gare su. Kuma umurnin Allah yă kasance abin aikatăwa.

Ayah   33:38   الأية
مَّا كَانَ عَلَى النَّبِيِّ مِنْ حَرَجٍ فِيمَا فَرَضَ اللَّهُ لَهُ ۖ سُنَّةَ اللَّهِ فِي الَّذِينَ خَلَوْا مِن قَبْلُ ۚ وَكَانَ أَمْرُ اللَّهِ قَدَرًا مَّقْدُورًا
Hausa
 
Wani ƙunci bai kasance a kan Annabi ba ga abin da Allah Ya faralta a kansa, a kan ƙă'idar, Allah a cikin (Annabăwa )waɗanda suka shige daga gabăninsa. Kuma umurnin Allah yă kasance abin ƙaddarăwa tabbatacce.

Ayah   33:39   الأية
الَّذِينَ يُبَلِّغُونَ رِسَالَاتِ اللَّهِ وَيَخْشَوْنَهُ وَلَا يَخْشَوْنَ أَحَدًا إِلَّا اللَّهَ ۗ وَكَفَىٰ بِاللَّهِ حَسِيبًا
Hausa
 
Waɗanda ke iyar da Manzancin Allah, kuma sună tsőronSa, kuma bă su tsőron kőwa făce Allah, Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai hisabi.

Ayah   33:40   الأية
مَّا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَا أَحَدٍ مِّن رِّجَالِكُمْ وَلَٰكِن رَّسُولَ اللَّهِ وَخَاتَمَ النَّبِيِّينَ ۗ وَكَانَ اللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمًا
Hausa
 
Muhammadu bai kasance uban kőwa ba daga mazanku, kuma amma shĩ yă kasance Manzon Allah kuma cikon Annabăwa. Kuma Allah Ya kasance Masani ga kőme.

Ayah   33:41   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا
Hausa
 
Ya ku waɗanda suka yi ĩmăni! Ku ambaci Allah, ambata mai yawa.

Ayah   33:42   الأية
وَسَبِّحُوهُ بُكْرَةً وَأَصِيلًا
Hausa
 
Kuma ku tsarkake shi, a săfiya da maraice.

Ayah   33:43   الأية
هُوَ الَّذِي يُصَلِّي عَلَيْكُمْ وَمَلَائِكَتُهُ لِيُخْرِجَكُم مِّنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ ۚ وَكَانَ بِالْمُؤْمِنِينَ رَحِيمًا
Hausa
 
(Allah) Shĩ ne Wanda ke tsarkake ku, da mala'ikunSa (sună yi muku addu'a), dőmin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske. Kuma (Allah) Yă kasance Mai Jĩn ƙai ga mũminai.

Ayah   33:44   الأية
تَحِيَّتُهُمْ يَوْمَ يَلْقَوْنَهُ سَلَامٌ ۚ وَأَعَدَّ لَهُمْ أَجْرًا كَرِيمًا
Hausa
 
Gaisuwarsu a rănar da suke haɗuwa da shi "Salăm", kuma Yă yi musu tattalin wani sakamako na karimci.

Ayah   33:45   الأية
يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ إِنَّا أَرْسَلْنَاكَ شَاهِدًا وَمُبَشِّرًا وَنَذِيرًا
Hausa
 
Yă kai Annabi! Lalle Mũ Mun aike ka kană mai shaida, kuma mai băyar da bushăra kuma mai gargaɗi.

Ayah   33:46   الأية
وَدَاعِيًا إِلَى اللَّهِ بِإِذْنِهِ وَسِرَاجًا مُّنِيرًا
Hausa
 
Kuma mai kira zuwa ga Allah da izninSa, kuma fitila mai haskakăwa.

Ayah   33:47   الأية
وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ بِأَنَّ لَهُم مِّنَ اللَّهِ فَضْلًا كَبِيرًا
Hausa
 
Kuma ka yi bushăra ga mũminai cẽwa, sũnă da falalamai girma daga Allah.

Ayah   33:48   الأية
وَلَا تُطِعِ الْكَافِرِينَ وَالْمُنَافِقِينَ وَدَعْ أَذَاهُمْ وَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ ۚ وَكَفَىٰ بِاللَّهِ وَكِيلًا
Hausa
 
Kuma kada ka yi ɗă'a ga kăfirai da munăfukai, kuma ka ƙyă1e cũtarsu (gare ka), kuma ka dőgara ga Allah. Allah Yă isa zama wakĩli.

Ayah   33:49   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نَكَحْتُمُ الْمُؤْمِنَاتِ ثُمَّ طَلَّقْتُمُوهُنَّ مِن قَبْلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ فَمَا لَكُمْ عَلَيْهِنَّ مِنْ عِدَّةٍ تَعْتَدُّونَهَا ۖ فَمَتِّعُوهُنَّ وَسَرِّحُوهُنَّ سَرَاحًا جَمِيلًا
Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! idan kun auri mũminai mătă, sa'an nan kuka sake su a gabănin ku shăfe su, to, bă ku da wata idda da ză ku lissafa a kansu, kuma ku yi musu kyautar jin dăɗi kuma ku sake su saki mai kyau.

Ayah   33:50   الأية
يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ إِنَّا أَحْلَلْنَا لَكَ أَزْوَاجَكَ اللَّاتِي آتَيْتَ أُجُورَهُنَّ وَمَا مَلَكَتْ يَمِينُكَ مِمَّا أَفَاءَ اللَّهُ عَلَيْكَ وَبَنَاتِ عَمِّكَ وَبَنَاتِ عَمَّاتِكَ وَبَنَاتِ خَالِكَ وَبَنَاتِ خَالَاتِكَ اللَّاتِي هَاجَرْنَ مَعَكَ وَامْرَأَةً مُّؤْمِنَةً إِن وَهَبَتْ نَفْسَهَا لِلنَّبِيِّ إِنْ أَرَادَ النَّبِيُّ أَن يَسْتَنكِحَهَا خَالِصَةً لَّكَ مِن دُونِ الْمُؤْمِنِينَ ۗ قَدْ عَلِمْنَا مَا فَرَضْنَا عَلَيْهِمْ فِي أَزْوَاجِهِمْ وَمَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ لِكَيْلَا يَكُونَ عَلَيْكَ حَرَجٌ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Yă kai Annabi! Lalle Mũ, Mun halatta maka mătanka waɗanda ka bai wa sadăkőkinsu da abin da hannun dămanka ya mallaka daga abin da Allah Ya bă ka na ganĩma, da 'yă'yan baffanka,da 'ya'yan goggonninka da 'yă'yan kăwunka da 'yă'yan innőninka waɗanda suka yi hijira tăre da kai, da wata mace mũmina idan ta băyar da kanta ga Annabi, idan shi Annabi yană nufin ya aure ta (hălin wannan hukunci) kẽɓe yake gare ka,banda gamũminai. Lalle Mun san abin da Muka faralta a kansu (smũminai) game da mătansuda abin da hannayensu suka mallaka. Do min kada wani ƙunci ya kasance a kanka, kuma Allah Yă kasance Mai găfara, Mai jin ƙai.

Ayah   33:51   الأية
تُرْجِي مَن تَشَاءُ مِنْهُنَّ وَتُؤْوِي إِلَيْكَ مَن تَشَاءُ ۖ وَمَنِ ابْتَغَيْتَ مِمَّنْ عَزَلْتَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكَ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَن تَقَرَّ أَعْيُنُهُنَّ وَلَا يَحْزَنَّ وَيَرْضَيْنَ بِمَا آتَيْتَهُنَّ كُلُّهُنَّ ۚ وَاللَّهُ يَعْلَمُ مَا فِي قُلُوبِكُمْ ۚ وَكَانَ اللَّهُ عَلِيمًا حَلِيمًا
Hausa
 
Kană iya jinkirtar da wadda ka ga dămă daga gare su, kuma kană tăro wadda kake so zuwa gare ka. Kuma wadda ka nẽma daga waɗanda ka nĩsantar, to, băbu laifi agare ka. Wannan yă fi kusantar da sanyaya idănunsu, kuma bă ză su yi baƙin ciki ba, kuma su yarda da abin da ka bă su, sũ duka. Kuma Allah Yană sane da abin da yake a cikin zukătanku. Kuma Allah Ya kasance Masani, Mai haƙuri.

Ayah   33:52   الأية
لَّا يَحِلُّ لَكَ النِّسَاءُ مِن بَعْدُ وَلَا أَن تَبَدَّلَ بِهِنَّ مِنْ أَزْوَاجٍ وَلَوْ أَعْجَبَكَ حُسْنُهُنَّ إِلَّا مَا مَلَكَتْ يَمِينُكَ ۗ وَكَانَ اللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ رَّقِيبًا
Hausa
 
Waɗansu mătă bă su halatta a gare ka a băyan haka, kuma ba ză ka musanya su da mătan aure ba, kuma kő kyaunsu yă bă ka sha'awa, făce dai abin da hannun dămanka ya mallaka. Kuma Allah Yă kasance Mai tsaro ga dukan kőme.

Ayah   33:53   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَدْخُلُوا بُيُوتَ النَّبِيِّ إِلَّا أَن يُؤْذَنَ لَكُمْ إِلَىٰ طَعَامٍ غَيْرَ نَاظِرِينَ إِنَاهُ وَلَٰكِنْ إِذَا دُعِيتُمْ فَادْخُلُوا فَإِذَا طَعِمْتُمْ فَانتَشِرُوا وَلَا مُسْتَأْنِسِينَ لِحَدِيثٍ ۚ إِنَّ ذَٰلِكُمْ كَانَ يُؤْذِي النَّبِيَّ فَيَسْتَحْيِي مِنكُمْ ۖ وَاللَّهُ لَا يَسْتَحْيِي مِنَ الْحَقِّ ۚ وَإِذَا سَأَلْتُمُوهُنَّ مَتَاعًا فَاسْأَلُوهُنَّ مِن وَرَاءِ حِجَابٍ ۚ ذَٰلِكُمْ أَطْهَرُ لِقُلُوبِكُمْ وَقُلُوبِهِنَّ ۚ وَمَا كَانَ لَكُمْ أَن تُؤْذُوا رَسُولَ اللَّهِ وَلَا أَن تَنكِحُوا أَزْوَاجَهُ مِن بَعْدِهِ أَبَدًا ۚ إِنَّ ذَٰلِكُمْ كَانَ عِندَ اللَّهِ عَظِيمًا
Hausa
 
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! Kada kũ shiga gidăjen Annabi, făce fa idan an yi izni a gare ku zuwa ga wani abinci, bă da kun tsaya jiran nunarsa ba, kuma amma idan an kira ku, to, ku shiga, sa'an nan idan kun ci, to ku wătse, kuma bă da kun tsaya kună masu hĩra da wani Iăbări ba. Lalle wannan yană cũtar da Annabi, to, yană jin kunyarku, alhăli kuwa Allah bă Ya jin kunya daga gaskiya. Kuma idan ză ku tambaye su waɗansu kăyă, to, ku tambaye su daga băyan shămaki. Wannan ya fi muku tsarki ga zukătanku da zukătansu. Kuma bă ya halatta a gare ku, ku cũci Manzon Allah, kuma bă ya halatta ku auri mătansa a băyansa har abada. lalle wannan a gare ku yă kasance babban abu a wurin Allah.

Ayah   33:54   الأية
إِن تُبْدُوا شَيْئًا أَوْ تُخْفُوهُ فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمًا
Hausa
 
Idan kun bayyana wani abu, kő kuma kuka ɓőye shi, to, lalle Allah Ya kasance Masani ga kőme.

Ayah   33:55   الأية
لَّا جُنَاحَ عَلَيْهِنَّ فِي آبَائِهِنَّ وَلَا أَبْنَائِهِنَّ وَلَا إِخْوَانِهِنَّ وَلَا أَبْنَاءِ إِخْوَانِهِنَّ وَلَا أَبْنَاءِ أَخَوَاتِهِنَّ وَلَا نِسَائِهِنَّ وَلَا مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُنَّ ۗ وَاتَّقِينَ اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدًا
Hausa
 
Băbu laifi a kansu game da ubanninsu, kuma băbu game da ɗiyansu, kuma băbu game da 'yan'uwansu maza, kuma băbu game da ɗiyan 'yan'uwansu maza, kuma băbu game da ɗiyan 'yan'uwansu mătă, kuma băbu game da mătan mũminai, kuma băbu game da abin da hannăyensu suka mallaka, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Yă kasance Mahalarci a kan kőme.

Ayah   33:56   الأية
إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ ۚ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا تَسْلِيمًا
Hausa
 
Lalle, Allah da mală'ikunSa sună salati ga Annabi. Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni!Ku yi salăti a gare shi, kuma ku yi sallama dőmin amintarwa a gare shi.

Ayah   33:57   الأية
إِنَّ الَّذِينَ يُؤْذُونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ لَعَنَهُمُ اللَّهُ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ وَأَعَدَّ لَهُمْ عَذَابًا مُّهِينًا
Hausa
 
Lalle waɗanda ke cũtar Allah da MauzonSa Allah Yă la'ane su, a cikin dũniya da Lăhira, kuma Yă yi musu tattalin azăba mai wulăkantarwa.

Ayah   33:58   الأية
وَالَّذِينَ يُؤْذُونَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ بِغَيْرِ مَا اكْتَسَبُوا فَقَدِ احْتَمَلُوا بُهْتَانًا وَإِثْمًا مُّبِينًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suke cũtar mũminai maza dă muminai mătă, bă da wani abu da suka aikata ba to, lalle sun ɗauki ƙiren ƙarya da zunubi bayyananne.

Ayah   33:59   الأية
يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُل لِّأَزْوَاجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَاءِ الْمُؤْمِنِينَ يُدْنِينَ عَلَيْهِنَّ مِن جَلَابِيبِهِنَّ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَن يُعْرَفْنَ فَلَا يُؤْذَيْنَ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Yă kai Annabi! Ka ce wa mătan aurenka da 'yă'yanka da mătan mũminai su kusantar da ƙasă daga manyan tufăfin da ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su dőmin kada a cũce su. Kuma Allah Yă kasance Mai găfara, Mai Jin ƙai.

Ayah   33:60   الأية
لَّئِن لَّمْ يَنتَهِ الْمُنَافِقُونَ وَالَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ وَالْمُرْجِفُونَ فِي الْمَدِينَةِ لَنُغْرِيَنَّكَ بِهِمْ ثُمَّ لَا يُجَاوِرُونَكَ فِيهَا إِلَّا قَلِيلًا
Hausa
 
Lalle, idan munăfukai da waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukătansu, da măsu tsẽgumi a cikin Madĩna, ba su hanu ba (daga hălăyensu), lalle, ză Mu shũshũta ka a gare su, sa'an nan bă ză su yi maƙwabtaka da kai ba, a cikinta, făce kaɗan.

Ayah   33:61   الأية
مَّلْعُونِينَ ۖ أَيْنَمَا ثُقِفُوا أُخِذُوا وَقُتِّلُوا تَقْتِيلًا
Hausa
 
Sună la'anannu, inda duka aka săme su a kămă su, kuma a karkashe su karkashẽwa.

Ayah   33:62   الأية
سُنَّةَ اللَّهِ فِي الَّذِينَ خَلَوْا مِن قَبْلُ ۖ وَلَن تَجِدَ لِسُنَّةِ اللَّهِ تَبْدِيلًا
Hausa
 
A kan hanyar Allah (ta gyaran jama'a) a cikin waɗanda suka shũɗe gabăninka, kuma bă ză ka sămi musanyăwa ba ga hanyar Allah.

Ayah   33:63   الأية
يَسْأَلُكَ النَّاسُ عَنِ السَّاعَةِ ۖ قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِندَ اللَّهِ ۚ وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّ السَّاعَةَ تَكُونُ قَرِيبًا
Hausa
 
Sună tambayar ka ga Să'a. Ka ce: "Saninta yană wurin Allah kawai." Kuma me yă sanar da kai cẽwa ană tsammănin sa'a ta kasance kusa?

Ayah   33:64   الأية
إِنَّ اللَّهَ لَعَنَ الْكَافِرِينَ وَأَعَدَّ لَهُمْ سَعِيرًا
Hausa
 
Lalle Allah Yă la'ani kăfirai, kuma Yă yi musu tattalin wata wuta mai ƙũna.

Ayah   33:65   الأية
خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۖ لَّا يَجِدُونَ وَلِيًّا وَلَا نَصِيرًا
Hausa
 
Sună madawwama a cikinta har abada, bă su sămun majiɓinci, kuma bă su sămun mataimaki.

Ayah   33:66   الأية
يَوْمَ تُقَلَّبُ وُجُوهُهُمْ فِي النَّارِ يَقُولُونَ يَا لَيْتَنَا أَطَعْنَا اللَّهَ وَأَطَعْنَا الرَّسُولَا
Hausa
 
Rănar da ake jũya fuskőkinsu a cikin wuta sună cẽwa, "Kaitonmu, sabőda,rashin biyarmu ga Allah da rashin biyarmu ga Manzo!"

Ayah   33:67   الأية
وَقَالُوا رَبَّنَا إِنَّا أَطَعْنَا سَادَتَنَا وَكُبَرَاءَنَا فَأَضَلُّونَا السَّبِيلَا
Hausa
 
Kuma suka ce: "Yă Ubangijinmu! Lalle mũ mun bi shugabanninmu da manyanmu! Sai suka ɓatar da mu daga hanya!

Ayah   33:68   الأية
رَبَّنَا آتِهِمْ ضِعْفَيْنِ مِنَ الْعَذَابِ وَالْعَنْهُمْ لَعْنًا كَبِيرًا
Hausa
 
"Yă Ubangijinmu! Ka ba su ninki biyu na azăba, kuma ka la'ane su, la'ana mai girma."

Ayah   33:69   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَكُونُوا كَالَّذِينَ آذَوْا مُوسَىٰ فَبَرَّأَهُ اللَّهُ مِمَّا قَالُوا ۚ وَكَانَ عِندَ اللَّهِ وَجِيهًا
Hausa
 
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku kasance kamar waɗanda suka cũci Mũsă sa'an nan Allah Ya barrantar da shi daga abin da suka ce. Kuma ya kasance mai daraja a wurin Allah.

Ayah   33:70   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَقُولُوا قَوْلًا سَدِيدًا
Hausa
 
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku faɗi magana madaidaiciya.

Ayah   33:71   الأية
يُصْلِحْ لَكُمْ أَعْمَالَكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ ۗ وَمَن يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ فَازَ فَوْزًا عَظِيمًا
Hausa
 
Ya kyautata muku ayyukanku, kuma Ya găfarta zunubanku. Kuma wanda ya yi ɗă'a ga Allah da ManzonSa, to, lalle, yă rabbanta, babban rabo mai girma.

Ayah   33:72   الأية
إِنَّا عَرَضْنَا الْأَمَانَةَ عَلَى السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَالْجِبَالِ فَأَبَيْنَ أَن يَحْمِلْنَهَا وَأَشْفَقْنَ مِنْهَا وَحَمَلَهَا الْإِنسَانُ ۖ إِنَّهُ كَانَ ظَلُومًا جَهُولًا
Hausa
 
Lalle Mũ, Mun gitta amăna ga sammai da ƙasă da duwătsu, sai suka ƙi ɗaukarta kuma sukaji tsőro daga gare ta, kuma mutum ya ɗauke ta, lalle shĩ (mutum) ya kasance mai yawan zălunci, mai yawan jăhilci.

Ayah   33:73   الأية
لِّيُعَذِّبَ اللَّهُ الْمُنَافِقِينَ وَالْمُنَافِقَاتِ وَالْمُشْرِكِينَ وَالْمُشْرِكَاتِ وَيَتُوبَ اللَّهُ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Dőmin Allah Ya azabta munăfukai maza da munăfukai mătă, da mushirikai maza da mushirikai mătă, kuma Allah Yă karɓi tũba ga mũminai maza da mũminai mătă. Kuma Allah Yă kasance Mai găfara, Mai jin ƙai. 
 


© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us