First Ayah 1 الأية الأوليبِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الْحَمْدُ لِلَّهِ فَاطِرِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ جَاعِلِ الْمَلَائِكَةِ
رُسُلًا أُولِي أَجْنِحَةٍ مَّثْنَىٰ وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ ۚ يَزِيدُ فِي الْخَلْقِ
مَا يَشَاءُ ۚ إِنَّ اللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Hausa
Gődiya ta tabbata ga Allah, Mai făra halittar sammai da ƙasă, Mai sanya mală'iku
manzanni măsu fukăfukai, bibbiyu, da uku-uku da hurhuɗu. Yană ƙărăwar abin da Ya
ke so a cikin halittar. Lalle Allah Mai ĩkon yi ne a kan kőme.
|
Ayah 35:2 الأية
مَّا يَفْتَحِ اللَّهُ لِلنَّاسِ مِن رَّحْمَةٍ فَلَا مُمْسِكَ لَهَا ۖ وَمَا
يُمْسِكْ فَلَا مُرْسِلَ لَهُ مِن بَعْدِهِ ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Hausa
Abin da Allah Ya buɗa wa mutăne daga rahama, to, băbu mai riƙewa a gare shi,
kuma abin da Ya riƙe, to, băbu mai saki a gare shi, waninSa, kuma Shĩ ne
Mabuwăyi, Mai hikima.
|
Ayah 35:3 الأية
يَا أَيُّهَا النَّاسُ اذْكُرُوا نِعْمَتَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ ۚ هَلْ مِنْ خَالِقٍ
غَيْرُ اللَّهِ يَرْزُقُكُم مِّنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ ۚ لَا إِلَٰهَ إِلَّا
هُوَ ۖ فَأَنَّىٰ تُؤْفَكُونَ
Hausa
Yă kũ mutăne! Ku tuna ni'imar Allah a kanku. Shin, akwai wani mai halitta wanin
Allah da zai azurta ku daga sama da, ƙasă? Băbu wani abin bautăwa, făce Shi. To,
yăya ake karkatar da ku?
|
Ayah 35:4 الأية
وَإِن يُكَذِّبُوكَ فَقَدْ كُذِّبَتْ رُسُلٌ مِّن قَبْلِكَ ۚ وَإِلَى اللَّهِ
تُرْجَعُ الْأُمُورُ
Hausa
Kuma idan sun ƙaryata ka, to, lalle, an ƙaryata waɗansu Manzanni a gabăninka,
kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura.
|
Ayah 35:5 الأية
يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقٌّ ۖ فَلَا تَغُرَّنَّكُمُ
الْحَيَاةُ الدُّنْيَا ۖ وَلَا يَغُرَّنَّكُم بِاللَّهِ الْغَرُورُ
Hausa
Yă kũ mutăne! Lalle wa'adin Allah gaskiya ne, sabőda haka kada răyuwar dũniya ta
rũɗar da ku, kuma kada marũɗi ya rũɗe ku game da Allah.
|
Ayah 35:6 الأية
إِنَّ الشَّيْطَانَ لَكُمْ عَدُوٌّ فَاتَّخِذُوهُ عَدُوًّا ۚ إِنَّمَا يَدْعُو
حِزْبَهُ لِيَكُونُوا مِنْ أَصْحَابِ السَّعِيرِ
Hausa
Lalle Shaiɗan maƙiyi ne a gare ku, sai ku riƙe shi maƙiyi. Yană kiran ƙungiyarsa
kawai ne, dőmin su kasance 'yan sa'ir.
|
Ayah 35:7 الأية
الَّذِينَ كَفَرُوا لَهُمْ عَذَابٌ شَدِيدٌ ۖ وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا
الصَّالِحَاتِ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ كَبِيرٌ
Hausa
Waɗanda suka kăfirta suna da azăba mai tsanani kuma waɗanda suka yi ĩmăni, kuma
suka aikata ayyukan ƙwarai, sună da wata găfara da sakamako mai girma.
|
Ayah 35:8 الأية
أَفَمَن زُيِّنَ لَهُ سُوءُ عَمَلِهِ فَرَآهُ حَسَنًا ۖ فَإِنَّ اللَّهَ يُضِلُّ
مَن يَشَاءُ وَيَهْدِي مَن يَشَاءُ ۖ فَلَا تَذْهَبْ نَفْسُكَ عَلَيْهِمْ حَسَرَاتٍ
ۚ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ بِمَا يَصْنَعُونَ
Hausa
Shin to, wanda aka ƙawăta masa aikinsa, har ya gan shi mai kyau (yană daidai da
waninsa)? Sabőda haka, lalle, Allah Yană ɓatar da wanda Yake so, kuma Yană
shiryar da wanda Yake so, sabőda haka kada ranka ya halaka a kansu dômin baƙin
ciki. Lalle Allah Masani ne ga abin da suke sană'antawa.
|
Ayah 35:9 الأية
وَاللَّهُ الَّذِي أَرْسَلَ الرِّيَاحَ فَتُثِيرُ سَحَابًا فَسُقْنَاهُ إِلَىٰ
بَلَدٍ مَّيِّتٍ فَأَحْيَيْنَا بِهِ الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا ۚ كَذَٰلِكَ
النُّشُورُ
Hausa
Kuma Allah ne Ya aika da iskőki har su mőtsar da girgije, sa'an nan Mu kőra shi
zuwa ga gari matacce, sa'an nan Mu răyar da ƙasă game da shi a bayan mutuwarta.
Kamar wancan ne Tăshin ˇiyăma yake.
|
Ayah 35:10 الأية
مَن كَانَ يُرِيدُ الْعِزَّةَ فَلِلَّهِ الْعِزَّةُ جَمِيعًا ۚ إِلَيْهِ يَصْعَدُ
الْكَلِمُ الطَّيِّبُ وَالْعَمَلُ الصَّالِحُ يَرْفَعُهُ ۚ وَالَّذِينَ يَمْكُرُونَ
السَّيِّئَاتِ لَهُمْ عَذَابٌ شَدِيدٌ ۖ وَمَكْرُ أُولَٰئِكَ هُوَ يَبُورُ
Hausa
Wanda ya kasance yană nẽman wata izza, to, Allah ne da izza gabă ɗaya. zuwa gare
Shi magana mai dăɗi ke hawa, kuma aiki na ƙwarai Yană ɗaukar ta Kuma waɗanda ke
yin măkircin mũnanan ayyuka, sună da wata azăba mai tsanani, kuma măkircin
waɗannan yană yin tasgaro.
|
Ayah 35:11 الأية
وَاللَّهُ خَلَقَكُم مِّن تُرَابٍ ثُمَّ مِن نُّطْفَةٍ ثُمَّ جَعَلَكُمْ أَزْوَاجًا
ۚ وَمَا تَحْمِلُ مِنْ أُنثَىٰ وَلَا تَضَعُ إِلَّا بِعِلْمِهِ ۚ وَمَا يُعَمَّرُ
مِن مُّعَمَّرٍ وَلَا يُنقَصُ مِنْ عُمُرِهِ إِلَّا فِي كِتَابٍ ۚ إِنَّ ذَٰلِكَ
عَلَى اللَّهِ يَسِيرٌ
Hausa
Kuma Allah ne Ya halitta ku daga turɓăya, sa'an nan daga ɗigon maniyyi, sa'an
nan Ya sanya ku surkin maza da mătă. Kuma wata mace bă ta yin ciki, kuma bă ta
haihuwa, făce da saninSa, kuma bă ză a răyar da wanda ake răyarwa ba, kuma bă ză
a rage tsawon ransa ba făce yană a cikin Littăfi. Lalle, wancan mai sauki ne ga
Allah.
|
Ayah 35:12 الأية
وَمَا يَسْتَوِي الْبَحْرَانِ هَٰذَا عَذْبٌ فُرَاتٌ سَائِغٌ شَرَابُهُ وَهَٰذَا
مِلْحٌ أُجَاجٌ ۖ وَمِن كُلٍّ تَأْكُلُونَ لَحْمًا طَرِيًّا وَتَسْتَخْرِجُونَ
حِلْيَةً تَلْبَسُونَهَا ۖ وَتَرَى الْفُلْكَ فِيهِ مَوَاخِرَ لِتَبْتَغُوا مِن
فَضْلِهِ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Hausa
Kuma kőguna biyu ba su daidaita: Wannan mai ruwan dăɗi, mai zăƙi, mai sauƙin
haɗiya kuma wannan mai ruwan gishiri mai zartsi, kuma daga kőwane, kună cin wani
nama săbo, kuma kună fitar da kawa wadda kuke tufantarta, kuma kană ganin jirăge
a cikinsa sună măsu gudăna, dőmin ku nẽmo daga falalarSa, kuma ɗammăninku ză ku
dinga gődẽwa.
|
Ayah 35:13 الأية
يُولِجُ اللَّيْلَ فِي النَّهَارِ وَيُولِجُ النَّهَارَ فِي اللَّيْلِ وَسَخَّرَ
الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ كُلٌّ يَجْرِي لِأَجَلٍ مُّسَمًّى ۚ ذَٰلِكُمُ اللَّهُ
رَبُّكُمْ لَهُ الْمُلْكُ ۚ وَالَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِهِ مَا يَمْلِكُونَ مِن
قِطْمِيرٍ
Hausa
Yană shigar da dare a cikin răna, kuma Yană shigar da răna a cikin dare. Kuma Ya
hőre rănă da wată kőwannensu yană gudăna zuwa ga ajali ambatacce Wannan Shĩ ne
Allah, Ubangijinku, gare Shi mulki yake, kuma waɗanda kuke kira waninSa bă su
mallakar kő fătar gurtsun dabĩno.
|
Ayah 35:14 الأية
إِن تَدْعُوهُمْ لَا يَسْمَعُوا دُعَاءَكُمْ وَلَوْ سَمِعُوا مَا اسْتَجَابُوا
لَكُمْ ۖ وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ يَكْفُرُونَ بِشِرْكِكُمْ ۚ وَلَا يُنَبِّئُكَ
مِثْلُ خَبِيرٍ
Hausa
Idan kun kira su, bă ză su ji kiranku ba, kuma kő sun jiya, bă ză su karɓa muku
ba, kuma a Rănar ˇiyăma ză su kăfirce wa shirkinku, kuma băbu mai bă ka lăbări,
kamar wanda ya sani.
|
Ayah 35:15 الأية
يَا أَيُّهَا النَّاسُ أَنتُمُ الْفُقَرَاءُ إِلَى اللَّهِ ۖ وَاللَّهُ هُوَ
الْغَنِيُّ الْحَمِيدُ
Hausa
Yă kũ mutăne! Kũ ne măsu bukăta zuwa ga Allah, kuma Allah, Shĩ ne Mawadăci,
Gődadde.
|
Ayah 35:16 الأية
إِن يَشَأْ يُذْهِبْكُمْ وَيَأْتِ بِخَلْقٍ جَدِيدٍ
Hausa
Idan Ya so, zai tafi da ku, kuma Ya zo da wata halitta săbuwa.
|
Ayah 35:17 الأية
وَمَا ذَٰلِكَ عَلَى اللَّهِ بِعَزِيزٍ
Hausa
Kuma wancan bai zama mabuwăyi ba ga Allah.
|
Ayah 35:18 الأية
وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَىٰ ۚ وَإِن تَدْعُ مُثْقَلَةٌ إِلَىٰ
حِمْلِهَا لَا يُحْمَلْ مِنْهُ شَيْءٌ وَلَوْ كَانَ ذَا قُرْبَىٰ ۗ إِنَّمَا
تُنذِرُ الَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُم بِالْغَيْبِ وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ ۚ وَمَن
تَزَكَّىٰ فَإِنَّمَا يَتَزَكَّىٰ لِنَفْسِهِ ۚ وَإِلَى اللَّهِ الْمَصِيرُ
Hausa
Kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bai ɗaukar nauyin wani rai. Kuma idan ran da aka
nauyaya wa kăya ya yi kira (ga wani mataimaki) zuwa ga kăyansa, bă ză a dauki
kőme ba daga gare shi, kuma kő dă (wanda ake kiran) yă kasance makusancin
zumunta ne. Kană gargaɗi kawai ne ga waɗanda ke tsoron Ubangijinsu a fake, kuma
suka tsayar da salla. Kuma wanda ya tsarkake, to, yană tsarkaka ne dőmin kansa.
Kuma zuwa ga Allah kawai makőma take.
|
Ayah 35:19 الأية
وَمَا يَسْتَوِي الْأَعْمَىٰ وَالْبَصِيرُ
Hausa
Kuma makăho bă ya daidaita da mai gani.
|
Ayah 35:20 الأية
وَلَا الظُّلُمَاتُ وَلَا النُّورُ
Hausa
Kuma duffai bă su daidaita, kuma haske bă ya daidaita.
|
Ayah 35:21 الأية
وَلَا الظِّلُّ وَلَا الْحَرُورُ
Hausa
Kuma inuwa bă ta daidaita, kuma iskar zăfi bă ta daidaita.
|
Ayah 35:22 الأية
وَمَا يَسْتَوِي الْأَحْيَاءُ وَلَا الْأَمْوَاتُ ۚ إِنَّ اللَّهَ يُسْمِعُ مَن
يَشَاءُ ۖ وَمَا أَنتَ بِمُسْمِعٍ مَّن فِي الْقُبُورِ
Hausa
Kuma răyayyu bă su daidaita kuma matattu ba su daidaita. Lalle Allah Yană jiyar
da wa'azi ga wanda Ya so, kuma ba ka jiyar da waɗanda suke a cikin kaburbura.
|
Ayah 35:23 الأية
إِنْ أَنتَ إِلَّا نَذِيرٌ
Hausa
Ba ka zama ba făce mai gargaɗi kawai.
|
Ayah 35:24 الأية
إِنَّا أَرْسَلْنَاكَ بِالْحَقِّ بَشِيرًا وَنَذِيرًا ۚ وَإِن مِّنْ أُمَّةٍ إِلَّا
خَلَا فِيهَا نَذِيرٌ
Hausa
Lalle Mũ Mun aike ka da gaskiya, kană mai băyar da bushăra kuma mai gargaɗi.
Kuma băbu wata al'umma făce wani mai gargaɗi yă shũɗe a cikinta.
|
Ayah 35:25 الأية
وَإِن يُكَذِّبُوكَ فَقَدْ كَذَّبَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ جَاءَتْهُمْ رُسُلُهُم
بِالْبَيِّنَاتِ وَبِالزُّبُرِ وَبِالْكِتَابِ الْمُنِيرِ
Hausa
Kuma idan sună ƙaryata ka, to, haƙĩƙa, waɗanda suke a gabăninsu sun ƙaryata.
Manzanninsu sun jẽ musu da hujjőji, kuma da takardu, kuma da Littafi mai haske.
|
Ayah 35:26 الأية
ثُمَّ أَخَذْتُ الَّذِينَ كَفَرُوا ۖ فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ
Hausa
Sa'an nan Na kăma waɗanda suka kăfirta. To, yăya musũNa yake?
|
Ayah 35:27 الأية
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللَّهَ أَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَخْرَجْنَا بِهِ
ثَمَرَاتٍ مُّخْتَلِفًا أَلْوَانُهَا ۚ وَمِنَ الْجِبَالِ جُدَدٌ بِيضٌ وَحُمْرٌ
مُّخْتَلِفٌ أَلْوَانُهَا وَغَرَابِيبُ سُودٌ
Hausa
Ba ka gani ba, lalle Allah Ya saukar da ruwa daga sama? Sai Muka fitar, game da
shi,'yă'yan ităce măsu săɓanin launuka kuma daga duwatsu akwai zane-zane,
farfaru da jăjăye, măsu săɓanin launin, da măsu launin baƙin ƙarfe, baƙăƙe.
|
Ayah 35:28 الأية
وَمِنَ النَّاسِ وَالدَّوَابِّ وَالْأَنْعَامِ مُخْتَلِفٌ أَلْوَانُهُ كَذَٰلِكَ ۗ
إِنَّمَا يَخْشَى اللَّهَ مِنْ عِبَادِهِ الْعُلَمَاءُ ۗ إِنَّ اللَّهَ عَزِيزٌ
غَفُورٌ
Hausa
Kuma daga mutăne da dabbőbi da bisăshen gida, măsu săɓănin launinsu kamar
wancan. Malamai kawai ke tsőron Allah daga cikin băyinSa. Lalle, Allah, Mabuwăyi
ne, Mai găfara.
|
Ayah 35:29 الأية
إِنَّ الَّذِينَ يَتْلُونَ كِتَابَ اللَّهِ وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَأَنفَقُوا
مِمَّا رَزَقْنَاهُمْ سِرًّا وَعَلَانِيَةً يَرْجُونَ تِجَارَةً لَّن تَبُورَ
Hausa
Lalle waɗanda ke karătun Littăfin Allah kuma suka tsayar da salla, kuma suka
ciyar daga abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, sună fătan
(sămun) wani fatauci ne wanda bă ya yin tasgaro.
|
Ayah 35:30 الأية
لِيُوَفِّيَهُمْ أُجُورَهُمْ وَيَزِيدَهُم مِّن فَضْلِهِ ۚ إِنَّهُ غَفُورٌ شَكُورٌ
Hausa
Dőmin (Allah) zai cika musu sakamakonsu, kuma Ya ƙară musu daga falalarSa. Lalle
Shi Mai găfara ne, Mai gődiya.
|
Ayah 35:31 الأية
وَالَّذِي أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ مِنَ الْكِتَابِ هُوَ الْحَقُّ مُصَدِّقًا لِّمَا
بَيْنَ يَدَيْهِ ۗ إِنَّ اللَّهَ بِعِبَادِهِ لَخَبِيرٌ بَصِيرٌ
Hausa
Kuma abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, daga Littăfi,
|
Ayah 35:32 الأية
ثُمَّ أَوْرَثْنَا الْكِتَابَ الَّذِينَ اصْطَفَيْنَا مِنْ عِبَادِنَا ۖ فَمِنْهُمْ
ظَالِمٌ لِّنَفْسِهِ وَمِنْهُم مُّقْتَصِدٌ وَمِنْهُمْ سَابِقٌ بِالْخَيْرَاتِ
بِإِذْنِ اللَّهِ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَضْلُ الْكَبِيرُ
Hausa
Sa'an nan Mun gădar da Littăfin, ga waɗanda Muka zăɓa daga băyinMu, sa'an nan
daga cikinsu, akwai mai zălunci ga kansa, kuma daga cikinsu akwai mai
tsakaităwa, kuma daga cikinsu akwai mai tsẽrẽwa da ayyukan alhẽri da iznin
Allah. Waccan ita ce falalar (Allah) mai girma.
|
Ayah 35:33 الأية
جَنَّاتُ عَدْنٍ يَدْخُلُونَهَا يُحَلَّوْنَ فِيهَا مِنْ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٍ
وَلُؤْلُؤًا ۖ وَلِبَاسُهُمْ فِيهَا حَرِيرٌ
Hausa
Gidăjen Aljannar zamă sună shigar su. Ană ƙawăce su a cikinsu, da ƙawă ta
mundăye daga zĩnăriya da lu'ulu'u, kuma tufăfinsu, a cikinsu alharĩni ne.
|
Ayah 35:34 الأية
وَقَالُوا الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَذْهَبَ عَنَّا الْحَزَنَ ۖ إِنَّ رَبَّنَا
لَغَفُورٌ شَكُورٌ
Hausa
Kuma suka ce: "Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya tafiyar da baƙin ciki daga
gare mu. Lalle Ubangijinmu, haƙĩƙa Mai gafarane, Mai godiya."
|
Ayah 35:35 الأية
الَّذِي أَحَلَّنَا دَارَ الْمُقَامَةِ مِن فَضْلِهِ لَا يَمَسُّنَا فِيهَا نَصَبٌ
وَلَا يَمَسُّنَا فِيهَا لُغُوبٌ
Hausa
"Wanda Ya saukar da mu a gidan zamă, daga falalarSa, wata wahala bă ta shăfar mu
a cikinsa, kuma wata kăsăwa bă ta shăfar mu a cikinsa."
|
Ayah 35:36 الأية
وَالَّذِينَ كَفَرُوا لَهُمْ نَارُ جَهَنَّمَ لَا يُقْضَىٰ عَلَيْهِمْ فَيَمُوتُوا
وَلَا يُخَفَّفُ عَنْهُم مِّنْ عَذَابِهَا ۚ كَذَٰلِكَ نَجْزِي كُلَّ كَفُورٍ
Hausa
Kuma waɗanda suka kăfirta sună da wutar Jahannama, bă a yin hukunci a kansu
balle su mutu kuma bă a sauƙaƙa musu daga azăbarta. Kamar haka Muke săka wa
kőwane mai yawan kăfirci.
|
Ayah 35:37 الأية
وَهُمْ يَصْطَرِخُونَ فِيهَا رَبَّنَا أَخْرِجْنَا نَعْمَلْ صَالِحًا غَيْرَ
الَّذِي كُنَّا نَعْمَلُ ۚ أَوَلَمْ نُعَمِّرْكُم مَّا يَتَذَكَّرُ فِيهِ مَن
تَذَكَّرَ وَجَاءَكُمُ النَّذِيرُ ۖ فَذُوقُوا فَمَا لِلظَّالِمِينَ مِن نَّصِيرٍ
Hausa
Kuma sũ, sună hargőwar nẽman ăgaji a cikinta. (Sună cẽwa) "Yă Ubangijinmu! Ka
fitar da mu, mu aikata aiki mai kyau, wanin wanda muka kasance mună aikatăwa."
Ashe, kuma, ba Mu răyar da ku ba, abin da mai tunăni zai iya yin tunăni a ciki,
kuma mai gargaɗi yă jẽ muku? To, ku ɗanɗana, sabőda haka băbu wani mataimaki, ga
azzălumai.
|
Ayah 35:38 الأية
إِنَّ اللَّهَ عَالِمُ غَيْبِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ إِنَّهُ عَلِيمٌ بِذَاتِ
الصُّدُورِ
Hausa
Lalle Allah ne Masanin gaibin sammai da ƙasă. Lalle Shĩ ne Masani ga abin da
yake ainihin zukata.
|
Ayah 35:39 الأية
هُوَ الَّذِي جَعَلَكُمْ خَلَائِفَ فِي الْأَرْضِ ۚ فَمَن كَفَرَ فَعَلَيْهِ
كُفْرُهُ ۖ وَلَا يَزِيدُ الْكَافِرِينَ كُفْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ إِلَّا مَقْتًا
ۖ وَلَا يَزِيدُ الْكَافِرِينَ كُفْرُهُمْ إِلَّا خَسَارًا
Hausa
Shĩ ne Wanda Ya sanya ku măsu maye wa jună, a cikin ƙasă. To, wanda ya kăfirta,
to, kăfircinsa yană a kansa. Kuma kăfircin kăfirai bă ya kăra musu kőme făce
baƙin jini, kuma kăfircin kăfirai bă ya kăra musu kőme face hasăra.
|
Ayah 35:40 الأية
قُلْ أَرَأَيْتُمْ شُرَكَاءَكُمُ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِ اللَّهِ أَرُونِي
مَاذَا خَلَقُوا مِنَ الْأَرْضِ أَمْ لَهُمْ شِرْكٌ فِي السَّمَاوَاتِ أَمْ
آتَيْنَاهُمْ كِتَابًا فَهُمْ عَلَىٰ بَيِّنَتٍ مِّنْهُ ۚ بَلْ إِن يَعِدُ
الظَّالِمُونَ بَعْضُهُم بَعْضًا إِلَّا غُرُورًا
Hausa
Ka ce: "Shin, kun ga abũbuwan shirkinku, waɗanda kuke kira, wasun Allah? Ku nũna
mini, mẽne ne suka halitta daga ƙasă? Kő sună da tărayya ne a cikin sammai? Kő
kuma Mun bă su wani littăfi ne sabőda haka sună a kan wata hujja ce daga gare
shi? Ă'a, azzălumai bă su yin wani wa'adi, săshensu zuwa ga săshe, făce rũɗi."
|
Ayah 35:41 الأية
إِنَّ اللَّهَ يُمْسِكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ أَن تَزُولَا ۚ وَلَئِن زَالَتَا
إِنْ أَمْسَكَهُمَا مِنْ أَحَدٍ مِّن بَعْدِهِ ۚ إِنَّهُ كَانَ حَلِيمًا غَفُورًا
Hausa
Lalle Allah Yană riƙe sammai da ƙasă dőmin kada su gushe. Kuma haƙĩƙa, idan sun
gushe, băbu wani baicinSa da zai riƙe su. Lalle Shi Yă kasance Mai haƙuri, Mai
găfara.
|
Ayah 35:42 الأية
وَأَقْسَمُوا بِاللَّهِ جَهْدَ أَيْمَانِهِمْ لَئِن جَاءَهُمْ نَذِيرٌ
لَّيَكُونُنَّ أَهْدَىٰ مِنْ إِحْدَى الْأُمَمِ ۖ فَلَمَّا جَاءَهُمْ نَذِيرٌ مَّا
زَادَهُمْ إِلَّا نُفُورًا
Hausa
Kuma suka yi rantsuwa da Allah, mafi nauyin rantsuwarsu, "Lalle, idan wani mai
gargaɗi ya zo musu tabbas ză su kasance mafi shiryuwa, daga ɗayan al'ummőmi."
To, a lőkacin da mai gargaɗi ya jẽ musu, bai ƙară su da kőme ba făce gudu.
|
Ayah 35:43 الأية
اسْتِكْبَارًا فِي الْأَرْضِ وَمَكْرَ السَّيِّئِ ۚ وَلَا يَحِيقُ الْمَكْرُ
السَّيِّئُ إِلَّا بِأَهْلِهِ ۚ فَهَلْ يَنظُرُونَ إِلَّا سُنَّتَ الْأَوَّلِينَ ۚ
فَلَن تَجِدَ لِسُنَّتِ اللَّهِ تَبْدِيلًا ۖ وَلَن تَجِدَ لِسُنَّتِ اللَّهِ
تَحْوِيلًا
Hausa
Dőmin nũna girman kai a cikin ƙasă da măkircin cũta. Kuma măkirci na cũta bă ya
fădăwa făce a kan mutănensa. To shin sună jiran (wani abu ne) făce dai hanyar
(kăfiran) farko. To, bă ză ka sămi musanya ba ga hanyar Allah. Kuma bă ză ka
sămi jũyarwa ba ga hanyar Allah.
|
Ayah 35:44 الأية
أَوَلَمْ يَسِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَيَنظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الَّذِينَ
مِن قَبْلِهِمْ وَكَانُوا أَشَدَّ مِنْهُمْ قُوَّةً ۚ وَمَا كَانَ اللَّهُ
لِيُعْجِزَهُ مِن شَيْءٍ فِي السَّمَاوَاتِ وَلَا فِي الْأَرْضِ ۚ إِنَّهُ كَانَ
عَلِيمًا قَدِيرًا
Hausa
Ashe, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasă, dőmin su dũba yadda ăƙibar waɗannan
da suke a gabăninsu ta kasance? Alhăli kuwa sun kasance mafĩfĩta ƙarfi daga gare
su? Kuma Allah bai kasance wani abu nă iya rinjăyarSa ba, a cikin sammai, kuma
haka a cikin kaƙă. Lalle Shi ne Ya kasance Masani, Mai ĩkon yi.
|
Ayah 35:45 الأية
وَلَوْ يُؤَاخِذُ اللَّهُ النَّاسَ بِمَا كَسَبُوا مَا تَرَكَ عَلَىٰ ظَهْرِهَا مِن
دَابَّةٍ وَلَٰكِن يُؤَخِّرُهُمْ إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى ۖ فَإِذَا جَاءَ
أَجَلُهُمْ فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ بِعِبَادِهِ بَصِيرًا
Hausa
Kuma dă Allah Yană kăma mutăne sabőda abin da suka aikata, dă bai bar wata dabba
ba a kanta (kasă). Amma Yană jinkirta musu zuwa ga ajalin da aka ambată. Sa'an
nan idan ajalinsu ya zo, to, lalle Allah yă kasance Mai gani ga băyinSa.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|