« Prev

36. Surah Yâ­Sîn سورة يس

Next »First Ayah   1   الأية الأولي
بِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
يس
Hausa
 
Y. S̃.

Ayah   36:2   الأية
وَالْقُرْآنِ الْحَكِيمِ
Hausa
 
Ină rantsuwa da Al-ƙur'ăni Mai hikima.

Ayah   36:3   الأية
إِنَّكَ لَمِنَ الْمُرْسَلِينَ
Hausa
 
Lalle kai, haƙĩƙa kană cikinManzanni.

Ayah   36:4   الأية
عَلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Hausa
 
A kan hanya madaidaiciya.

Ayah   36:5   الأية
تَنزِيلَ الْعَزِيزِ الرَّحِيمِ
Hausa
 
(Allah Ya saukar da Al-kur'ăni) saukarwar Mabuwăyi, Mai jin ƙai.

Ayah   36:6   الأية
لِتُنذِرَ قَوْمًا مَّا أُنذِرَ آبَاؤُهُمْ فَهُمْ غَافِلُونَ
Hausa
 
Dőmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutăne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabőda haka sũmasu rafkana ne.

Ayah   36:7   الأية
لَقَدْ حَقَّ الْقَوْلُ عَلَىٰ أَكْثَرِهِمْ فَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ
Hausa
 
Lalle, haƙĩƙa, kalma tă wajaba a kan mafi yawansu, dőmin sũ, bă ză su yi ĩmăni ba.

Ayah   36:8   الأية
إِنَّا جَعَلْنَا فِي أَعْنَاقِهِمْ أَغْلَالًا فَهِيَ إِلَى الْأَذْقَانِ فَهُم مُّقْمَحُونَ
Hausa
 
Lalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyőyinsu, sa'an nan sũ (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓőɓinsu, sabőda haka, sũ banƙararru ne.

Ayah   36:9   الأية
وَجَعَلْنَا مِن بَيْنِ أَيْدِيهِمْ سَدًّا وَمِنْ خَلْفِهِمْ سَدًّا فَأَغْشَيْنَاهُمْ فَهُمْ لَا يُبْصِرُونَ
Hausa
 
Kuma Muka sanya wata tőshiya a gaba gare su, da wata tőshiya a băyansu, sabőda haka Muka rufe su, sai suka zama bă su gani.

Ayah   36:10   الأية
وَسَوَاءٌ عَلَيْهِمْ أَأَنذَرْتَهُمْ أَمْ لَمْ تُنذِرْهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ
Hausa
 
Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kő ba ka yi musu gargaɗi ba, sũ bă ză su yi ĩmăni ba.

Ayah   36:11   الأية
إِنَّمَا تُنذِرُ مَنِ اتَّبَعَ الذِّكْرَ وَخَشِيَ الرَّحْمَٰنَ بِالْغَيْبِ ۖ فَبَشِّرْهُ بِمَغْفِرَةٍ وَأَجْرٍ كَرِيمٍ
Hausa
 
Kană yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ăni ne, kuma ya ji tsőron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushăra da găfara da wani sakamako na karimci.

Ayah   36:12   الأية
إِنَّا نَحْنُ نُحْيِي الْمَوْتَىٰ وَنَكْتُبُ مَا قَدَّمُوا وَآثَارَهُمْ ۚ وَكُلَّ شَيْءٍ أَحْصَيْنَاهُ فِي إِمَامٍ مُّبِينٍ
Hausa
 
Lalle Mũ, Mũ ne ke răyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabătar, da gurăbunsu, kuma kőwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littăfi Mabayyani.

Ayah   36:13   الأية
وَاضْرِبْ لَهُم مَّثَلًا أَصْحَابَ الْقَرْيَةِ إِذْ جَاءَهَا الْمُرْسَلُونَ
Hausa
 
Kuma ka buga musu misăli: Waɗansu ma'abũta alƙarya, a lőkacin da Manzanni suka jẽ mata.

Ayah   36:14   الأية
إِذْ أَرْسَلْنَا إِلَيْهِمُ اثْنَيْنِ فَكَذَّبُوهُمَا فَعَزَّزْنَا بِثَالِثٍ فَقَالُوا إِنَّا إِلَيْكُم مُّرْسَلُونَ
Hausa
 
A lőkacin da Muka aika (Manzannin) biyu zuwa gare su, sai suka ƙaryata su, sa'an nan Muka ƙarfafa (su) da na uku, sai suka ce: "Lalle mũ, Manzanni ne zuwa gare ku."

Ayah   36:15   الأية
قَالُوا مَا أَنتُمْ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُنَا وَمَا أَنزَلَ الرَّحْمَٰنُ مِن شَيْءٍ إِنْ أَنتُمْ إِلَّا تَكْذِبُونَ
Hausa
 
Suka ce: "Kũ ba ku zamo bafăce mutăne ne kamarmu kuma Mai rahama bai saukar da kőme ba, ba ku zamo ba făce ƙarya kuke yi."

Ayah   36:16   الأية
قَالُوا رَبُّنَا يَعْلَمُ إِنَّا إِلَيْكُمْ لَمُرْسَلُونَ
Hausa
 
Suka ce: "Ubangijinmu Yă sani, lalle mũ, haƙiƙa Manzanni nezuwa gare ku."

Ayah   36:17   الأية
وَمَا عَلَيْنَا إِلَّا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ
Hausa
 
"Kuma băbu abin da ke kanmu, făce iyar da manzanci bayyananne."

Ayah   36:18   الأية
قَالُوا إِنَّا تَطَيَّرْنَا بِكُمْ ۖ لَئِن لَّمْ تَنتَهُوا لَنَرْجُمَنَّكُمْ وَلَيَمَسَّنَّكُم مِّنَّا عَذَابٌ أَلِيمٌ
Hausa
 
Suka ce: "Lalle mũ mună shu'umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba, haƙĩƙa, ză mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azăba mai raɗaɗi daga gare mu ză ta shăfe ku."

Ayah   36:19   الأية
قَالُوا طَائِرُكُم مَّعَكُمْ ۚ أَئِن ذُكِّرْتُم ۚ بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ مُّسْرِفُونَ
Hausa
 
Suka ce: "Shu'umcinku, yană tăre da ku. Ashe, dőmin an tunătar da ku? Ă'a, kũ dai mutăne ne măsu ƙẽtare haddi."

Ayah   36:20   الأية
وَجَاءَ مِنْ أَقْصَى الْمَدِينَةِ رَجُلٌ يَسْعَىٰ قَالَ يَا قَوْمِ اتَّبِعُوا الْمُرْسَلِينَ
Hausa
 
Kuma wani mutum daga mafi nĩsan birnin ya je, yană tafiya da gaggăwa, ya ce: "Ya mutănẽna! Ku bi Manzannin nan.

Ayah   36:21   الأية
اتَّبِعُوا مَن لَّا يَسْأَلُكُمْ أَجْرًا وَهُم مُّهْتَدُونَ
Hausa
 
"Ku bi waɗanda bă su tambayar ku wata ijăra kuma sũ shiryayyu ne."

Ayah   36:22   الأية
وَمَا لِيَ لَا أَعْبُدُ الَّذِي فَطَرَنِي وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Hausa
 
"Kuma mene ne a gare ni, bă zan bauta wa Wanda Ya ƙăga halittata ba, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku?"

Ayah   36:23   الأية
أَأَتَّخِذُ مِن دُونِهِ آلِهَةً إِن يُرِدْنِ الرَّحْمَٰنُ بِضُرٍّ لَّا تُغْنِ عَنِّي شَفَاعَتُهُمْ شَيْئًا وَلَا يُنقِذُونِ
Hausa
 
"Shin, zan riƙi waninSa abũbuwan bautăwa? Idan Mai rahama Ya nufe ni da wata cũta, to cẽtonsu bă ya amfanĩna da kőme, kuma bă za su iya tsămar da ni bă."

Ayah   36:24   الأية
إِنِّي إِذًا لَّفِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Hausa
 
"Lalle nĩ, a lőkacin nan, tabbas, ină a cikin ɓata bayyananna."

Ayah   36:25   الأية
إِنِّي آمَنتُ بِرَبِّكُمْ فَاسْمَعُونِ
Hausa
 
"Lalle ni, nă yi ĩmăni da Ubangijinku, sabőda haka ku saurăre ni."

Ayah   36:26   الأية
قِيلَ ادْخُلِ الْجَنَّةَ ۖ قَالَ يَا لَيْتَ قَوْمِي يَعْلَمُونَ
Hausa
 
Aka ce (masa), "Ka shiga Aljanna." Ya ce, "Dă dai a ce mutănẽna sună iya sani."

Ayah   36:27   الأية
بِمَا غَفَرَ لِي رَبِّي وَجَعَلَنِي مِنَ الْمُكْرَمِينَ
Hausa
 
"Game da găfarar da Ubangijjĩna ya yi mini, kuma Ya sanya ni a cikin waɗanda aka girmama."

Ayah   36:28   الأية
وَمَا أَنزَلْنَا عَلَىٰ قَوْمِهِ مِن بَعْدِهِ مِن جُندٍ مِّنَ السَّمَاءِ وَمَا كُنَّا مُنزِلِينَ
Hausa
 
Kuma ba Mu saukar da waɗansu runduna ba daga sama a kan (halaka) mutănensa, daga băyansa, kuma bă ză Mu kasance. Măsu saukarwa ba.

Ayah   36:29   الأية
إِن كَانَتْ إِلَّا صَيْحَةً وَاحِدَةً فَإِذَا هُمْ خَامِدُونَ
Hausa
 
Ba ta kasance ba face tsawa guda, sa'an nan sai gă su sőmammu.

Ayah   36:30   الأية
يَا حَسْرَةً عَلَى الْعِبَادِ ۚ مَا يَأْتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ
Hausa
 
Yă nadăma a kan băyĩNa! Wani Manzo bă ya zuwa gare su făce sun kasance sună măsu yi masa izgili.

Ayah   36:31   الأية
أَلَمْ يَرَوْا كَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّنَ الْقُرُونِ أَنَّهُمْ إِلَيْهِمْ لَا يَرْجِعُونَ
Hausa
 
Ba su gani ba, da yawa Muka halakar da (mutănen) ƙarnőni a gabăninsu kuma cẽwa su bă ză su kőmo ba?

Ayah   36:32   الأية
وَإِن كُلٌّ لَّمَّا جَمِيعٌ لَّدَيْنَا مُحْضَرُونَ
Hausa
 
Kuma lalle băbu kőwa făce waɗanda ake halartarwa ne a wurinMu.

Ayah   36:33   الأية
وَآيَةٌ لَّهُمُ الْأَرْضُ الْمَيْتَةُ أَحْيَيْنَاهَا وَأَخْرَجْنَا مِنْهَا حَبًّا فَمِنْهُ يَأْكُلُونَ
Hausa
 
Kuma ăyă ce a gare su: ˇasă matacciya, Mu răyar da ita, Mu fitar da ƙwăya daga gare ta, sai gă shi daga gare ta suke ci.

Ayah   36:34   الأية
وَجَعَلْنَا فِيهَا جَنَّاتٍ مِّن نَّخِيلٍ وَأَعْنَابٍ وَفَجَّرْنَا فِيهَا مِنَ الْعُيُونِ
Hausa
 
Kuma Muka sanya, a cikinta (ƙasă), waɗansu gőnaki na dabĩno da inabőbi, kuma Muka ɓuɓɓugar da ruwa daga marẽmari a cikinta.

Ayah   36:35   الأية
لِيَأْكُلُوا مِن ثَمَرِهِ وَمَا عَمِلَتْهُ أَيْدِيهِمْ ۖ أَفَلَا يَشْكُرُونَ
Hausa
 
Dőmin su ci 'ya'yan ităcensa, alhăli kuwa hannăyensu ba su aikata shi ba. Shin, to, bă ză su gődẽ ba?

Ayah   36:36   الأية
سُبْحَانَ الَّذِي خَلَقَ الْأَزْوَاجَ كُلَّهَا مِمَّا تُنبِتُ الْأَرْضُ وَمِنْ أَنفُسِهِمْ وَمِمَّا لَا يَعْلَمُونَ
Hausa
 
Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya halitta nau'uka, namiji da mace, dukansu, daga abin da ƙasă ke tsirarwa, kuma daga kansu, kuma daga abin da ba su sani ba.

Ayah   36:37   الأية
وَآيَةٌ لَّهُمُ اللَّيْلُ نَسْلَخُ مِنْهُ النَّهَارَ فَإِذَا هُم مُّظْلِمُونَ
Hausa
 
Kuma ăyă ce a gare su: Dare Muna feɗe răna daga gare shi, sai gă su sună măsu shiga duhu.

Ayah   36:38   الأية
وَالشَّمْسُ تَجْرِي لِمُسْتَقَرٍّ لَّهَا ۚ ذَٰلِكَ تَقْدِيرُ الْعَزِيزِ الْعَلِيمِ
Hausa
 
Kuma rănă tană gudăna zuwa ga wani matabbaci năta. Wannan ƙaddarăwar Mabuwăyi ne, Masani.

Ayah   36:39   الأية
وَالْقَمَرَ قَدَّرْنَاهُ مَنَازِلَ حَتَّىٰ عَادَ كَالْعُرْجُونِ الْقَدِيمِ
Hausa
 
Kuma da wată Mun ƙaddara masa manzilőli, har ya kőma kamar tsumagiyar murlin dabĩno wadda ta tsũfa.

Ayah   36:40   الأية
لَا الشَّمْسُ يَنبَغِي لَهَا أَن تُدْرِكَ الْقَمَرَ وَلَا اللَّيْلُ سَابِقُ النَّهَارِ ۚ وَكُلٌّ فِي فَلَكٍ يَسْبَحُونَ
Hausa
 
Rănă bă ya kamăta a gare ta, ta riski wată. Kuma dare bă ya kamăta a gare shi ya zama mai tsẽre wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo.

Ayah   36:41   الأية
وَآيَةٌ لَّهُمْ أَنَّا حَمَلْنَا ذُرِّيَّتَهُمْ فِي الْفُلْكِ الْمَشْحُونِ
Hausa
 
Kuma ăyă ce a gare su. Lalle Mũ, Mun ɗauki zuriyarsu a cikin jirgin, wanda aka yi wa lődi.

Ayah   36:42   الأية
وَخَلَقْنَا لَهُم مِّن مِّثْلِهِ مَا يَرْكَبُونَ
Hausa
 
Kuma Muka halitta musu, daga irinsa, abin da suke hawa.

Ayah   36:43   الأية
وَإِن نَّشَأْ نُغْرِقْهُمْ فَلَا صَرِيخَ لَهُمْ وَلَا هُمْ يُنقَذُونَ
Hausa
 
Kuma idan Mun so, ză Mu nutsar da su, har băbu kururuwar neman ăgaji, a gare su, kuma ba su zama ană tsirar da su ba.

Ayah   36:44   الأية
إِلَّا رَحْمَةً مِّنَّا وَمَتَاعًا إِلَىٰ حِينٍ
Hausa
 
Sai fa bisa ga wata rahama daga gare Mu, da jiyarwa dăɗi zuwa ga wani ɗan lőkaci.

Ayah   36:45   الأية
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ اتَّقُوا مَا بَيْنَ أَيْدِيكُمْ وَمَا خَلْفَكُمْ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ
Hausa
 
Kuma idan aka ce musu, "Ku kăre abin da ke a gaba gare ku da abin da yake a băyanku, dőmin tsammăninku a ji tausayinku."

Ayah   36:46   الأية
وَمَا تَأْتِيهِم مِّنْ آيَةٍ مِّنْ آيَاتِ رَبِّهِمْ إِلَّا كَانُوا عَنْهَا مُعْرِضِينَ
Hausa
 
Kuma wata ăyă daga ăyőyin Ubangijinsu bă ta zuwa a gare su, sai sun kasance sună măsu bijirẽwa daga gare ta.

Ayah   36:47   الأية
وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ أَنفِقُوا مِمَّا رَزَقَكُمُ اللَّهُ قَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِلَّذِينَ آمَنُوا أَنُطْعِمُ مَن لَّوْ يَشَاءُ اللَّهُ أَطْعَمَهُ إِنْ أَنتُمْ إِلَّا فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Hausa
 
Kuma idan aka ce musu, "Ku ciyar daga abin da Allah Ya azurta ku," sai waɗanda suka kăfirta su ce ga waɗanda suka yi ĩmăni, "Ashe, ză mu ciyar da wanda idan Allah Ya so Yană ciyar da shi? Ba ku zama ba făce a cikin ɓata bayyananniya."

Ayah   36:48   الأية
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا الْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Hausa
 
Kuma sună cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi yake (aukuwa) idan kun kasance măsu gaskiya?"

Ayah   36:49   الأية
مَا يَنظُرُونَ إِلَّا صَيْحَةً وَاحِدَةً تَأْخُذُهُمْ وَهُمْ يَخِصِّمُونَ
Hausa
 
Bă su jiran (kőme) făce wata tsăwa guda, ză ta kăma su, alhăli kuwa sună yin husũma.

Ayah   36:50   الأية
فَلَا يَسْتَطِيعُونَ تَوْصِيَةً وَلَا إِلَىٰ أَهْلِهِمْ يَرْجِعُونَ
Hausa
 
Bă ză su iya yin wasiyya ba, kuma bă ză su iya kőmăwa zuwa ga iyălansu ba.

Ayah   36:51   الأية
وَنُفِخَ فِي الصُّورِ فَإِذَا هُم مِّنَ الْأَجْدَاثِ إِلَىٰ رَبِّهِمْ يَنسِلُونَ
Hausa
 
Kuma aka yi bũsa a cikin ƙaho, to, sai gă su, daga kaburbura zuwa ga Ubangijinsu, sună ta gudu.

Ayah   36:52   الأية
قَالُوا يَا وَيْلَنَا مَن بَعَثَنَا مِن مَّرْقَدِنَا ۜ ۗ هَٰذَا مَا وَعَدَ الرَّحْمَٰنُ وَصَدَقَ الْمُرْسَلُونَ
Hausa
 
Suka ce: "Yă bonenmu! Wăne ne ya tăyar da mu daga barcinmu?" "Wannan shi ne abin da Mai rahama ya yi wa'adi da shi, kuma Manzanni sun yi gaskiya."

Ayah   36:53   الأية
إِن كَانَتْ إِلَّا صَيْحَةً وَاحِدَةً فَإِذَا هُمْ جَمِيعٌ لَّدَيْنَا مُحْضَرُونَ
Hausa
 
Ba ta kasance ba făce wata tsăwa ce guda, sai gă su duka, sună abin halartarwa a gare Mu.

Ayah   36:54   الأية
فَالْيَوْمَ لَا تُظْلَمُ نَفْسٌ شَيْئًا وَلَا تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Hausa
 
To, a yau, bă ză a zălunci wani rai da kőme ba. Kuma bă ză a săkă muku ba făce da abin da kuka kasance kună aikatăwa.

Ayah   36:55   الأية
إِنَّ أَصْحَابَ الْجَنَّةِ الْيَوْمَ فِي شُغُلٍ فَاكِهُونَ
Hausa
 
Lalle, 'yan Aljanna, a yau, sună cikin shagali, sună măsu nishăɗi.

Ayah   36:56   الأية
هُمْ وَأَزْوَاجُهُمْ فِي ظِلَالٍ عَلَى الْأَرَائِكِ مُتَّكِئُونَ
Hausa
 
Sũ da mătan aurensu sună cikin inuwőwi, a kan karagai, sună măsu gincira.

Ayah   36:57   الأية
لَهُمْ فِيهَا فَاكِهَةٌ وَلَهُم مَّا يَدَّعُونَ
Hausa
 
Sună da, 'ya'yan ităcen marmari a cikinta kuma sună sămun abin da suke kiran a kăwo.

Ayah   36:58   الأية
سَلَامٌ قَوْلًا مِّن رَّبٍّ رَّحِيمٍ
Hausa
 
"Aminci," da magana, daga Ubangiji Mai jin ƙai.

Ayah   36:59   الأية
وَامْتَازُوا الْيَوْمَ أَيُّهَا الْمُجْرِمُونَ
Hausa
 
"Ku rarrabe dabam, a yau, yă kũ măsu laifi!"

Ayah   36:60   الأية
أَلَمْ أَعْهَدْ إِلَيْكُمْ يَا بَنِي آدَمَ أَن لَّا تَعْبُدُوا الشَّيْطَانَ ۖ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُّبِينٌ
Hausa
 
"Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, yă ɗiyan Ădamu? Cẽwa kada ku bauta wa Shaiɗan, lalle shĩ, maƙiyi ne a gareku bayyananne?"

Ayah   36:61   الأية
وَأَنِ اعْبُدُونِي ۚ هَٰذَا صِرَاطٌ مُّسْتَقِيمٌ
Hausa
 
"Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya."

Ayah   36:62   الأية
وَلَقَدْ أَضَلَّ مِنكُمْ جِبِلًّا كَثِيرًا ۖ أَفَلَمْ تَكُونُوا تَعْقِلُونَ
Hausa
 
"Kuma lalle haƙĩƙa, (Shaiɗan) yă ɓatar da jama'a măsu yawa daga gare ku. Ashe to ba ku kasance kună yin hankali ba?"

Ayah   36:63   الأية
هَٰذِهِ جَهَنَّمُ الَّتِي كُنتُمْ تُوعَدُونَ
Hausa
 
"Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance ană yi muku wa'adi da ita."

Ayah   36:64   الأية
اصْلَوْهَا الْيَوْمَ بِمَا كُنتُمْ تَكْفُرُونَ
Hausa
 
"Ku shigẽ ta a yau, sabőda abin da kuka kasance kună yi na kăfirci."

Ayah   36:65   الأية
الْيَوْمَ نَخْتِمُ عَلَىٰ أَفْوَاهِهِمْ وَتُكَلِّمُنَا أَيْدِيهِمْ وَتَشْهَدُ أَرْجُلُهُم بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ
Hausa
 
A yau, Mună sanya hătimin rufi a kan băkunansu, kuma hannăyensu su yi Mana magana, kuma ƙafăfunsu su yi shaidu da abin da suka kasance sună aikatăwa.

Ayah   36:66   الأية
وَلَوْ نَشَاءُ لَطَمَسْنَا عَلَىٰ أَعْيُنِهِمْ فَاسْتَبَقُوا الصِّرَاطَ فَأَنَّىٰ يُبْصِرُونَ
Hausa
 
Dă Mun so, dă Mun shăfe gani daga idănunsu, sai su yi tsẽre ga hanya, to, yaya ză su yi gani?

Ayah   36:67   الأية
وَلَوْ نَشَاءُ لَمَسَخْنَاهُمْ عَلَىٰ مَكَانَتِهِمْ فَمَا اسْتَطَاعُوا مُضِيًّا وَلَا يَرْجِعُونَ
Hausa
 
Kuma da Mun so, da Mun juyar da halittarsu a kan halinsu, saboda haka ba ză su iya shuɗewa ba, kuma ba ză su komo ba.

Ayah   36:68   الأية
وَمَن نُّعَمِّرْهُ نُنَكِّسْهُ فِي الْخَلْقِ ۖ أَفَلَا يَعْقِلُونَ
Hausa
 
Kuma wanda Muka răya shi, Mană sunkuyar da shi ga halittarsa. Ashe, bă su hankalta?

Ayah   36:69   الأية
وَمَا عَلَّمْنَاهُ الشِّعْرَ وَمَا يَنبَغِي لَهُ ۚ إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ وَقُرْآنٌ مُّبِينٌ
Hausa
 
Ba Mu sanar da shi (Annabi) wăkă ba, kuma wăkă ba ta kamăta da shi (Annabi) ba. Shi (Al-ƙur'ăni) bai zama ba făce tunătarwa ce, da abin karătu bayyananne.

Ayah   36:70   الأية
لِّيُنذِرَ مَن كَانَ حَيًّا وَيَحِقَّ الْقَوْلُ عَلَى الْكَافِرِينَ
Hausa
 
Dőmin ya yi gargaɗi ga wanda ya kasance mai rai, kuma magana ta wajaba a kan kăfirai.

Ayah   36:71   الأية
أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّا خَلَقْنَا لَهُم مِّمَّا عَمِلَتْ أَيْدِينَا أَنْعَامًا فَهُمْ لَهَا مَالِكُونَ
Hausa
 
Shin, ba su gani ba (cẽwa) lalle Mun halitta musu dabbőbi daga abin da HannayenMu suka aikata, sai sună mallakar su?

Ayah   36:72   الأية
وَذَلَّلْنَاهَا لَهُمْ فَمِنْهَا رَكُوبُهُمْ وَمِنْهَا يَأْكُلُونَ
Hausa
 
Kuma Muka hőre su, sabőda su, sabőda haka daga gare su abin hawansu yake, kuma daga gare su suke ci.

Ayah   36:73   الأية
وَلَهُمْ فِيهَا مَنَافِعُ وَمَشَارِبُ ۖ أَفَلَا يَشْكُرُونَ
Hausa
 
Kuma sună da waɗansu amfănőni a cikinsu, da abũbuwan shă. Ashe fa, bă ză; su gődẽ ba?

Ayah   36:74   الأية
وَاتَّخَذُوا مِن دُونِ اللَّهِ آلِهَةً لَّعَلَّهُمْ يُنصَرُونَ
Hausa
 
Kuma suka riƙi waɗansu abũbuwan bautăwa wanin Allah, ɗammăninsu ză su taimake su.

Ayah   36:75   الأية
لَا يَسْتَطِيعُونَ نَصْرَهُمْ وَهُمْ لَهُمْ جُندٌ مُّحْضَرُونَ
Hausa
 
Bă ză su iya taimakonsu ba, alhăli kuwa sũ runduna ce wadda ake halartarwa (a cikin wută).

Ayah   36:76   الأية
فَلَا يَحْزُنكَ قَوْلُهُمْ ۘ إِنَّا نَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ
Hausa
 
Sabőda haka, kada maganarsu ta ɓăta maka rai. Lalle Mũ, Mună sanin abin da suke asirtăwa da abin da suke bayyanăwa.

Ayah   36:77   الأية
أَوَلَمْ يَرَ الْإِنسَانُ أَنَّا خَلَقْنَاهُ مِن نُّطْفَةٍ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٌ مُّبِينٌ
Hausa
 
Ashe, kuma mutum bai ga (cẽwa) lalle Mũ, Mun halitta shi daga maniyyi ba, sai gă shi mai yawan husũma, mai bayyanăwar husũmar.

Ayah   36:78   الأية
وَضَرَبَ لَنَا مَثَلًا وَنَسِيَ خَلْقَهُ ۖ قَالَ مَن يُحْيِي الْعِظَامَ وَهِيَ رَمِيمٌ
Hausa
 
Kuma ya buga Mana wani misăli, kuma ya manta da halittarsa, ya ce: "Wăne ne ke răyar da ƙasũsuwa alhăli kuwa sună rududdugaggu?"

Ayah   36:79   الأية
قُلْ يُحْيِيهَا الَّذِي أَنشَأَهَا أَوَّلَ مَرَّةٍ ۖ وَهُوَ بِكُلِّ خَلْقٍ عَلِيمٌ
Hausa
 
Ka ce: "Wanda ya ƙăga halittarsu a farkon lőkaci Shĩ ke răyar da su, kuma Shi, game da kőwace halitta, Mai ilmi ne."

Ayah   36:80   الأية
الَّذِي جَعَلَ لَكُم مِّنَ الشَّجَرِ الْأَخْضَرِ نَارًا فَإِذَا أَنتُم مِّنْهُ تُوقِدُونَ
Hausa
 
"Wanda ya sanya muku wută daga ităce kőre, sai gă ku kună kunnăwa daga gare shi."

Ayah   36:81   الأية
أَوَلَيْسَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِقَادِرٍ عَلَىٰ أَن يَخْلُقَ مِثْلَهُم ۚ بَلَىٰ وَهُوَ الْخَلَّاقُ الْعَلِيمُ
Hausa
 
"Shin, kuma Wanda Ya halitta sammai da ƙasă bai zama Mai ĩkon yi ba ga Ya halitta kwatankwacinsu? Na'am, zai iya! Kuma Shĩ Mai yawan halittăwa ne,Mai ilmi."

Ayah   36:82   الأية
إِنَّمَا أَمْرُهُ إِذَا أَرَادَ شَيْئًا أَن يَقُولَ لَهُ كُن فَيَكُونُ
Hausa
 
UmurninSa idan Yă yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, "Ka kasance," sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi).

Ayah   36:83   الأية
فَسُبْحَانَ الَّذِي بِيَدِهِ مَلَكُوتُ كُلِّ شَيْءٍ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Hausa
 
Sabőda haka, tsarki yă tabbata ga Wanda mallakar kőwane abu take ga HannăyenSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku. 
 


© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us